Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

UWA tofa mutum bazai ta'ba ganin daidai Arayuwar sabah, Idan kazagi IYAYEN wani wallahi Allah naka kazaga, sai ayi hattara idan kunne yaji jiki ya tsira, Allah yashige manah gaba! Cigaban labari, kukan dah Ummulkhair take k'ok'arin dannewa neh ya ku'buce matah batasan sanda tafashe dah kuka bah, itama Mummyn dajin hankalin Ummulkhair atashe tafashe dah kukan tareda tambayar dalilin kukan dah take, Ummulkhair saida taji hankalin Mummy ya tashi sosai sannan tace, "Mummyn mu kiyi hak'uri ki yafe min Dan Allah nasa kin zubda hawayen ki akaina, "Khairiya nah" Mummy tafad'a cikin kuka, menene kifad'a min kinji, Mummy bkomai Missing d'inki nayi kuma nayi nayi yace bazan zo bah sai nayi wata d'aya, Mummy sam bata gamsu dah amsar bah tace, "Khairiya nice nah haife ki kuma babu abinda zaki b'oye min, kigaya min menene matsalar"?, Mummynah nifa sonake naganki nayi missing d'inki dayawa jinake kamar zan mutu, a'a bar fad'in haka kinji, kin tabbatar min dah iya matsalar kenan? Uhm Mummy ni kawai sonake naganki! toh maza share hawayen ki bazan ta'ba barin Khairiya tabah, mahaifiyar ki tanah kaunar ki haryau har gobe har kullum harta mutu har alahira, kidena kuka Dan Allah khairat kina d'aga min hankali sai naga kamar zaman auren neh baya miki dad'i, a'a Mummy bahaka baneh kiyi hak'uri daman ni sonake nah rungume ki mundad'e bamu had'uba, toh shikenan tunda kin d'an kwana biyu zan tambayi Abbanku Insha Allah zanzo naduba ki kinji koh?, kuma har goya kima zanyi! Dariyan murna tafara yi tanah share hawayen tah, Mummy dagaske? Eh manah Khairiya ke Alkhairi ce arayuwa tah, toh naji Mummynah nagode Sosai Allah yabiya ki dah gidan Aljanna, Ameen toh yanzu hankalin Khairiyan Mummy ya kwanta koh? kuma bazata k'ara kuka bah koh? Eh Mummy bazan k'ara damuwa bah ina sonki sosai rayuwa tah, murmushin farin ciki sukewa junansu kamar suna ganin juna, nan suka d'an ta'ba hirar su kafin suyi sallama inda Mummy take ce matah Allah ya Albarkaci rayuwar itah dah mijin tah yabasu zaman lafiya, koda Ummulkhair tah ajiye waya saida tayi wani kukan sabida tsananin missing Mummyn tah datayi wani kaunar mahaifiyar tah neh yake d'auwainiya dah itah, tashi tayi tayi sujjada cikin kuka tah godewa Allah daya batah Mummy had'e dah Daddy, Gaskia IYAYE NAGARI KAT NEHπŸ‘ŒπŸΎ Muna tafe Sweet Fans Next Episode @Pg.39


Mhiss B~hal CeπŸ’…πŸΎπŸ‘„πŸ’žπŸ’•
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf CeπŸ’…πŸ‘„πŸ‘‘πŸ‘’πŸ’•: 🎍🐚NoVelπŸ‘‡πŸΏWriTter 🐚🎍
β˜£πŸ‘„Mhiss~B~halπŸ™‡πŸ»β€β™€πŸ‘„β˜£

⏳39βŒ›

πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€ 🌑🌑🌑 πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€
πŸ€β˜˜Matar DR. Saiyadeeβ˜˜πŸ€

πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰ πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰

πŸ‘„ πŸ‘„
πŸ’…πŸΎ πŸ’…πŸΎ
πŸ™πŸ» πŸ™πŸ»
(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍🏾[P~M ~L]✍🏾
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the ReadersπŸ“–}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 All MATAN AURE gaskiya kuna k'ok'ari Allah dai yabada lada Allah yaraya yaran Albarka masu nema Allah yabasu, Ina yabo matan aure Allah yasaka dah gidan Aljanna Mhiss~B~hal tanah gaisuwaπŸ˜“πŸ˜ͺ

ATTENTION!!!
Agaskia tunda har attention danah rubuta Asama yaja hankalin ki\ka toh ya kamata ku nutsu kuji abinda yake tafe dani, ak'arshe page 38 idan bazaku manta bah nasaka IYAYE NAGARI KAT NEH! Toh wanda bah NAGARI bah fah? Ai akwai su koh? Toh jiya naci karo dawani mumunar labari daya hanani sukuni ku aramun kunnuwan ku Mhiss B~hal tanah neman alfarman hakan pls, Wata baiwar Allah Ce wacce batah wuci shekara sha bakwai bah aduniya tayi aure kuma auren soyayya tayi ahaya suke zaune dah mijinta bayan tah haihu tasamu namiji mijin yafara canzawa kusan meh? sai Allah yad'aura wa d'ansu rashin lafiya yanayin jijjiga sannan kuma wai jini yahaura brain d'inshi sai yaron yafara acting abnormal zance yasha banban Asibiti suka buk'aci kud'i dayawa, shikenan aka nemi miji aka rasa yagudu yabar itah dah yaro kuma gidan haya suke, kunsa mesa yagudu?, an nemi shi sama dah k'asa babu shi duk inda ake tunanin za aganshi anduba babu shi sai awajan wani abokin shi akaji wai baya kano kuma dalilin guduwar sah shine sabida haya yacika za abiya sabo kuma yaro Allah ya jarrabe shi dah cuta, meh gida yak'ara matah hak'uri zuwa d'anwani lokacin kad'an chan kuma yace subar mishi gida saita d'auko yaro tafito bakin titi tazauna tanah rusa kuka nasan kowannen ku zaice toh batada GIDAN UBA, anan inda take kuka wani mai adaidaita yazo yasame tah yake tambayar tah damuwar tah, nan tafad'a masa komai, sai yace toh gidan ku fah kinje gida? Kusan menene masu karatu? Eh taje gida UBANTA yace bazata zauna agidan shiba dah d'anta shi bazai ajiye d'an mara mutunci agidan sabah, saidai taje tasan yanda zatayi dah yaron tah dawo amman sam inda dah yaron nan bazata zauna agidan shiba sabida bashida wajan ajiye yaron, sai wannan bawan Allahn yace "toh ina UWAR KI?" Sai tace banida UWA, MAHAIFIYA tah tarasu, Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun! Wallahi Mata muna shan wahala dole muce zamuyi karatu kafin muyi aure, ai it's because we want to be independent, tsakani dah Allah wasu mazan basa kyautawa matan su, akwai labaran dasuka fi wannan muni, wallahi akwai k'awar Yayata mijin tah sai yaje yasha giya ya k'oshi yake dawowa gida yanah zuwa zaiyi amai ya'bata waje kafin tah tashi tah gyara yajawo tah yayi matah fiyad'e, kuma auren soyayya neh kuma bata sanshi dah halin nanba kafin suyi aure, toh ni agani nah rashin bincike neh daga b'angaran mata sabida zaiyi wahala kaga mace batason namiji tsakani dah Allah tah aure shi, idan kinawa namiji so tsakani dah Allah sai kiga ai bashida aibu toh kina tafka babban kuskure wallahi, ai Allah neh ya Umarce mu muyi bincike, toh mesah bazaki yi bah? Subhanallahi, wlh Allah bai yarda namiji ya kusanci matar shi batare dah amincewar tabah, MAZA MAZA MAZA kuji tsoron Allah dah ranar dazaku bar duniya yanzu macen dah kuke sha'awa itah kuke aure, tabbas auren yanzu nah Sha'awa neh kuma bayan aure dazaran ankauda wannan Sha'awan sai kiga zance yasha banban, toh kusani abinda ka shuka shi zakah girba itah rayuwa haka take duk kunbi kunsa muna tsoron aure sabida bamusan abinda zaibiyo baya bah zakuzo manah dah farin fuska bayan aure muga bak'ake kuke wulik, toh kuma kunada k'anne kuma zasuyi aure kuma Kunasan ar'ike su dakyau kumesa bazaku rik'e k'annan wasu dakyau bah, Another problem dah ake facing shine RAYUWAR K'AUYE ADAA anayi wa matah auren wuri wanda har yanzu awannan zamanin akwai masu aurar dah 'ya er shekara goma shad'aya wallahi wannan kwata kwata baidace bah karma kucemin Sunnah domin daa dah yanzu bah d'aya bah kuma Shugaban halittun duniya daban yake shi, sannan U guys are after sex not the real sunnah, yarinya er shekara goma shad'aya tsakani dah Allah metah sani?, saikaga yarinya batasan ciwon kanta bah balle left and right d'inta amman tasan d'aa namiji, tasan meh akecewa SEX, dole acutar dah itah gaskia adaina cutar dah k'annen mu mata, wata matar auren dakayi matah Addu'an Allah yabarta dah mijin tah gwanda kah shak'e tah sabida tsananin azabar dah take fama dashi agidan miji, shiyasa mafi akasari nidai Mhiss B~hal nafi yiwa matan aure Addu'ar Aljanna domin indai daman soyayyar su dah mijin su tsakani dah Allah neh, kuma mazajen masu tsoron Allah dah rik'on amana dah gaskia neh toh indai suka samu Aljanna sun samu mazazen su, MATA suna shan wahala agidan aure amman dayawa suna amfani dah kalman HAK'URI suna zama sabida Allah dah yaran su, Ya SalamπŸ˜­πŸ˜“πŸ˜ͺ, MATAN AURE sannun ku dah k'ok'ari Allah ya shige muku gaba ya kauda fitina wlh Inayin kuπŸ˜ͺ, Allah yabarku dah yaranku dah IYAYEN ku kuma UWA kam daban take
Ya ALLAH INA ROK'ON KAH KAH SAKAWA UWA DAH GIDAN ALJANNA, wallahi wallahi duk mai UWA baisan gatan dah Allah yayi masa bah, UWA tafi k'arfin Wulak'anci ku daraja UWA koh wacce UWA d'aya Ce sunan baya canzawa, kuyi biyayya ga kowacce UWA Allah zai baku ladan yin hakan kuma taku UWAR dah nagari Allah zai dinga had'a tah ako ina, yanzu wannan baiwar Allahn daa tanada UWA wlh dah rayuwar tah tayi kyau! Toh wannan matsalan daya faru meya jawo shi, Gurbatattun IYAYE sune SILLA, kamar yanda mukeda yara nagari dah wanda bah nagari bah haka mukeda IYAYE nagari dah wanda bah nagari bah, toh IYAYE sune suka haifi YARA dan haka matsalar daga wajan su take, itah tarbiya nagari yad'uwa take haka zalika wanda bah nagari bah itama yad'uwa take, toh IYAYE kusani wallahi Allah YARA AMANAR Allah Ce, kuma tunda kuna dashi kund'au AMANAR Allah, wasu Iyaye basu san darajar yaransu bah kuma wannan bai dace bah koh kad'an, saikaga 'yar rik'o tafi wacce take gidansu jin dad'i wata agidan su ma karuwanci ake sakata takawo kud'in aci abinci, tarbiyan yara yanah hannun Iyaye maza dah mata aman kuma UWA tafi sanin ciwon kan 'ya'yan tah akan UBA toh yake UWA kisani daga ranar dah kika samu ciki Wallahil Azeem kin d'auki AMANAR Allah, domin yara AMANAR Allah neh kuma AMANAR Allah bah abin wasa baneh ranar dazai tambaye ki yanda kikayi dah AMANAR sah acikin d'unbin jama'a nanan tafe, wasu matan suna neman haihuwa wasu kuma suna tsiyaye CIKI abakin makwarara, kai mata muji tsoron Allah, wallahi masu d'aukan cikin shege daku nake idan har kinsan kin riga kinyi wannan stupid mistake d'in (ZINA) arayuwar ki har kika samu ciki toh kada ki sake ki b'arar wallahi koda kuwa ke karuwa ce bakida hajjar zubar dah wannan cikin, domin kin k'ara wa kanki azabar Allah, gata ZINA bata KISA, dah yaron dah aka Haifa tah hanyar zina dah yaron dah aka Haifa tah hanyar Sunna wallahi duk Amanar Allah neh sabida Allah yafi kowa san kowani bawan sah aduniya, banbancin kawai idan kikayi zina tofah keda Allah dole ki horu tun daga duniya har izuwa lahira saidai idan tuba kikayi, kuma yaron dah kika Haifa tah hanyar zina shima zai fuskanci k'alubalen rayuwa, dan haka masu b'arar dah ciki kuji tsoron Allah abinda yake bani mamaki wai harda matan aure, wai saikaga macce dah auren tah dah mijin tah tasamu ciki tah b'arar, watama mijin tah baisani bah U can Imaging yanda kike kai sahunki hanyar wuta, idan kah tambaye tah hujja sai tace makah ai batasan tayi Konica sabida babu tazara tsakanin d'an dah take goyo dah ciki, toh yake hajiya Konica idan kece kike bada haihuwar saiki bawa wanda suka dad'e suna nema mugani, wai har Allah zai miki kyauta kinuna bakya so sabida jama'a zasuga rashin tazara hhhhh kai kajimin wannan jahilcin har ina, waye yace ki b'arar? Ke kika sakawa kanki d'aa aciki? Yaushe Allah yayi miki alk'awarin zai k'ara miki wasu yaran bayan wanda kika b'arar? kin d'auka SEX is all about getting pregnant? Idan hakan neh mesah wasu matan sun dade suna neman haihuwar basu samu bah? ai idan hakane dah babu wacce bata haihuwa(barren) aduniya kenan koh? toh tunda bakida amsoshin nan bakida damar b'arar dah ciki indai banah lafiya bah sabida akwai cikin dah ake cireshi sabida asamu lafiya, CIKl, HAIHUWA, YARA DUK KYAUTAR ALLAH NEH, kuma AMANAR ALLAH, wacece keh dazaki wulak'anta abu nah Allah?, sabida kin tabbatar bazaki mutu bah balle ki had'u dah ALLAH? Shugaban hallittun duniya baiyi k'arya bah dayace matah sunfi yauwa acikin wutan jahannama Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, wai azamanin daama kenan balle wannan tabararren zamanin namu nah yanzu, Mata Mata Mata! Wallahi Mata kurage buri duk wacce tamutu duniya batayi asaran komai bah sabida akwai dubun ki acikin sah kuma dubun ki suna kan hanyar zuwa, toh wlh yake mace ki kula masu aikata mugayen halayya batare dah sanin mazajen subah ku kula wallahi Allah yana ganin komai fah dan baya bacci kuma Aljannar ki tanah k'ark'ashin tafin kaf'an mijin ki, ki kula dah dukiyar sah dah halin dah yaranku ke ciki, domin kece agida tareda su koda yaushe UBAN mafi Akasari yanah wajan aiki,
Anyway iyayen daa kenan, iyayen yanzu kud'i yarufe masu ido UBA yanah fita aiki UWAR ma hakan kai awani gidan ma UBAN yanah riga UWAR dawowa daga aiki, abin haushi anan shine kwata kwata basuda lokacin yaransu daga an aika su Boko sai Islamiyya sai abasu abinci amusu wanka, shikenan? INJIWA? kin tabbatar babu abinda yake damun yaranki at school koh Islamiyya? kin tabbatar babu targad'e atarbiyyan su? kin zauna kin basu wadatattan tarbiyan dah UWA take bawa yaran tah? Ohh ashe fah kinanan kina neman kud'i koh? toh abinda yake bani mamaki shine duk wanda ya tambaye ki neman kud'in mekike yi? sai kice sabida yara nah, kinga matsalar koh? dan yaran ake neman kud'in amman in the same process ana gurb'ata masu tarbiya iyayen yanzu bakwa bud'e littafan yaranku balle kuga irin Asignments d'insu harku taimaka masu dashi of which baidace bah koh kad'an amakaranta idan anbawa yara news letter wanda school management take calling iyaye for Parentsβ€’ Teachers β€’Association Meeting (PTA Meeting) wlh iyayen yanzu 10% neh suke zuwa 90% suna wajan Neman kud'i Alhalin Iyayen daa they are challenging they voice out their opinions akan yaransu idan abu beyi masu bah they call for PTA Meeting themselves, they care about their children they watch all their moves and activities, kuma adaan ma suma suna zuwa aiki amman sun ware special time for their kids, I Mhiss B~hal call on all parents to be conscious akan yaran su for Future Reference!
Kafin nan idan kinada Uwa TaGaRi kitashi kiyi sujjada kigode wa Allah, dan wallahi yayi miki baiwa sosai, sannan kiji tsoron Allah kid'aura yaranki akan tarbiya nagari dah aka d'aura ki akai kema, d'aya daga cikin hallayar uwa tagari shine Hana erki zuwa kowani biki dah suna sabida ita 'ya mace bah kowani biki take zuwa bah, ki kula dah moves d'in yaran ki musamman 'ya mace, idan erki tah isa zance kada kisake kibata d'aki daga itah sai Saurayi kice suyi zance, kinga tasha wanka anci kwalliya ansha janbaki turare dah hoda, gashi shima saurayin yaci ado dah turare, d'aki yasha shara dah k'amshi fanka yanata wal~wal, erki tayi soye soye dah Lemu mai sanyi, hmmmm hhhhhh, wai shikuma ga shed'an chan agefe yanah tunzura su tunda daman shine nah ukunsu, toh duk abinda yafaru lefin nakine yake UWA, bawa yarinya budurwa d'aki tayi zance sam ba gata baneh, kada ma kiyarda dah zance aduhu idan mutum biyu sun zauna nah ukun su IBLIS neh, koh kuma Saurayi yazo k'ofar gida ya d'auki erki amota su fita inda baki sani bah bayan awa uku adawo dah itah kinanan baki d'auki hakan komai bah saidai tashigo dah Leda kizauna kulashe tare batare dah k'orafi bah koh kin tambaye tah ina taje bah amman idan ana hira agidan biki kinfi kowa tada jijiyoyin wuya akan cewa yaran yanzu sun lalace keh amman taki VIRGIN ce koh? daduk fitan nan dah takeyi dah samari bakya k'orafi? Virgin d'in Ice cream dah kazar dah take shigowa dashi koh? kai MATAπŸ€¦πŸ»β€β™€, kinada k'aramman yarinya kullum idan tafita wasa tanah dawowa babu pant abayan kinsaka matah kafin tafita, amman dazaran tashigo saiki kama dukan tah kina cewa tacire shi wajan wasa, maimakon kiduba jikin tah a'a duk babu wannan mesah? Kin tabbatar dah hannun tah tacire wandon? kintabbatar bawani baneh yacire matah? maza kad'ai neh suke lalata yaran mutane? Mata fah? Toh mesah bazaki tabaye tabah?Mesah bazaki bincika bah? Hmmm er uwa ki kula danni Mhiss B~hal banga amfanin barin 'ya mace fita wasa ak'ofar gida bah, ai 'ya'ya matah daban suke fah, ki kula dah AMANAR Allah sabida itah rayuwa adashi ce, kowa yadinga zubawa ranar daza akwashe tananan tafe! Allah yasah mudace idan mundace mutsira ALLAHUMMA AMEEN!!!

Nice nan Mhiss B~hal Ina gaisuwaπŸ™‹πŸ», tnx all for the unnumbered calls and messages ina kaunar ku I really appreciate ur care berries, CIGABAN LABARIN UMMUSAIYEED @ page 40 tnx 4 ur valuable β±πŸ˜…ANATAREπŸ˜…

Mhiss B~hal CeπŸ’…πŸΎπŸ‘„πŸ’žπŸ’•
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf CeπŸ’…πŸ‘„πŸ‘‘πŸ‘’πŸ’•: 🎍🐚NoVelπŸ‘‡πŸΏWriTter 🐚🎍
β˜£πŸ‘„Mhiss~B~halπŸ™‡πŸ»β€β™€πŸ‘„β˜£

⏳40βŒ›

πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€ 🌑🌑🌑 πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€
πŸ€β˜˜Matar DR. Saiyadeeβ˜˜πŸ€

πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰ πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰

πŸ‘„ πŸ‘„
πŸ’…πŸΎ πŸ’…πŸΎ
πŸ™πŸ» πŸ™πŸ»
(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍🏾[P~M ~L]✍🏾
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the ReadersπŸ“–}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 My lovely Fans All Over biko am sorry ehn, biyan neba dnt be provoked Mhiss B~hal get many things to do make wunna no vex abeg accept my apology kia kia! God bless All! Me love wuna wellaπŸ™ˆπŸ™‰

Ummulkhair tashi tayi tah tsaftace gidan tah gaba d'aya, tadawo tayi wanka taci ado tafara kallo saidai bah ainihin TV take kallo bah future natah take hangowa dah Abusaiyeed d'inta, hmmm koyaya abu zatah kasance, tashi tayi tah soya plantain dah kwai favorite nah Abusaiyeed zataci, wai kaga su Ummulkhair love master dani ce tuwo zanci yasinπŸ˜‚, bayan tagama sai kallon abincin take amman takasa ci, k'aran msg taji awayan tah tayi saurin d'auka ganin Abusaiyeed neh yasata kukan farin ciki, da sauri tah bud'e tagani kamar haka,
"Am pretty sure bakici komai bah, kitashi kici abinci yanzu Dan Allah"!
kukan farin ciki tafashe dashi sosai abincin gabanta tafara kaiwa baki dah hannun tah akai akai, tanaci tanah kuka sosai, ci take badan yunwa bah amman sabida Saiyadee yace taci, anan idan taci abincin koh tashi bata iyayi bah sabida tunanin shi har saida lokacin sallah yayi, bayan tah idar taji ana buga k'ofa tashi tayi duk jikin tah babu k'wari taje tabud'e murna tayi sosai daganin su ZeeSarki dah Nakundu, kushigo Dan Allah, aiko baki fad'a bah shiga zamuyi cewar uwar tsiwa Deejah Nakundu, ni kuma shigo gida nah naku neh, kunyi sallah dai koh? Ummulkhair tah tambaya, "Eh nidai nayi" ZeeSarkie tace, Nakundu tace a'a amman she's ablute, haka tayi sallah suka soma hiran su cike dah farin ciki, bayan Ummulkhair tah d'ebo masu kayan ciye ciye iri~ire tace, "mezan dafa muku", kayan amarci zaki bamu, lallai kayan Amarci nima kuban idan kuna dashi, dariya sukayi dukkah, sukace barmu da wannan kayan kwalamar mah, nan Ummulkhair take tambayar su ina Fateemah Usman dikko dah Miss biey Cholli, ZeeSarki tace kinsan tare muke fitar mu dah Nakundu, zuwa next week suma zaki gansu, toh Allah yakaimu meza kuci? anything eatable cewar Nakundu, a'a shinkafa dah miya zanci cewar Zeesarkie sabida nidai kunsan bansan jellof rice, ahaka suka fad'a kitchen suka had'a abinda zasu ci, sunsha hira kamar kar arabu sai chan kusan magrib suka k'imsa zasu wuce gida tuni Ummulkhair tayi wik'i wik'i dah idanu kamar tayi kuka gabad'aya tayi finding gidan boring, turare, pants dah lipstick tabasu sukayi sallama bayan tarufe gida tadawo tayi sallan magriba sannan takuma gyara gidan tah tsaf, wanke wanke tayi takoma d'aki tayi wanka, sannan tayi sallan Isha, karatun Alkur'ani tayi nah kusan 1hour, kafin tamik'e takoma kan gado, YouTube tashiga tanah kallon comedies tuni tamanta dah damuwar tah tashiga yin dariya sosai, haka tah dinga wannan kallon har bacci yayi awon gaba dah itah, sai chan 11:35pm tafarka dah tunanin bata barwa Abusaiyeed abinci bah, tashi tayi tafad'a bathroom tayi brush sannan tawuce kitchen as usual favorite d'inshi tayi masa fried plantain this time around peppered chicken tayi mashi dah onion sauce, ita kanta dah tayi tasting saida taji dad'in girkin, kayan datayi amfani dashi tah wanke tas tamaida komai position d'inshi, sannan takoma d'aki takuma yin wanka tasaka kayan baccin tah, tanah kwanciya taji Abusaiyeed yadawo, murmushi tayi tah gyara kwanciyar tah dan tasan bazuwa zaiyi bah, wayar tah tah tuno tabari a kitchen hakan yasa cike dah takaici tah tashi ahakan tafice dan duk atunanin tah Abusaiyeed yanah part d'inshi unfortunately yanah parlour azaune ya jingine dah kujera, batah kula dashi bah har tazo tsakiyar parlour saiji tayi ance, "Ummu" kamar daga sama, chak tah tsaya tare dah juyowa atsorace tayi k'asa tanah bugun k'irjin tah ahankali, tasowa yayi dakyar dah alamun agajiye yake, yazo har gaban tah ya durk'usa, rik'e tah yayi, yanah rad'a matah Subhanallahi akunne tareda bugun bayan tah ahankali, Sannu, yace yanah d'ora kanta bissa kafad'ar sah! Fans Next Episode @ page41πŸ™‹πŸ»


Mhiss B~hal CeπŸ’…πŸΎπŸ‘„πŸ’žπŸ’•
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf CeπŸ’…πŸ‘„πŸ‘‘πŸ‘’πŸ’•: 🎍🐚NoVelπŸ‘‡πŸΏWriTter 🐚🎍
β˜£πŸ‘„Mhiss~B~halπŸ™‡πŸ»β€β™€πŸ‘„β˜£

⏳41βŒ›

πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€ 🌑🌑🌑 πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€
πŸ€β˜˜Matar DR. Saiyadeeβ˜˜πŸ€

πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰ πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰

πŸ‘„ πŸ‘„
πŸ’…πŸΎ πŸ’…πŸΎ
πŸ™πŸ» πŸ™πŸ»
(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍🏾[P~M ~L]✍🏾
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the ReadersπŸ“–}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 My lovely Fans All Over biko am sorry ehn, biyan neba dnt be provoked Mhiss B~hal get many things to do make wunna no vex abeg accept my apology kia kia! God bless All! Me love wuna wellaπŸ™ˆπŸ™‰

Kamar tah k'ank'ame shi haka takeji ga k'amshi turaren shi yafara rikita tah tabbas tasan tayi missing d'inshi amman hakan tah daure, tah d'ago kai zatayi magana yariga tah yi, "Ina zakije"?, kitchen tah amsa calmly, what's wrong abinci zakici neh? uhm~uhm waya nah namanta tafad'a tanah kaiwa nan tah mik'e tace, "Sannu dah zuwa kuma nagode" kitchen tawuce tah d'auko wayar tah, har zata wuce saikuma tace, "abincin kah yanakan dinning, goodnight" tabbas yaji k'amshin girki mai dad'i dan sanda yashigo ma he was impressed cax kamshin is Unique and classic amman yaci abinci at office so he's full amman bece matah komai bah harta wuce, d'aki tah koma taje gaban mirror tayi saurin shan ruwan sanyi dan yanda taji zuciyar tah nata bugu dah sauri sauri tasan bakomai baneh illa ganin abinda take murad'i, zama tayi abakin gado sai asannan takula dah rigar dake jikin tah gabad'aya taji kunya takama tah net neh rigar gabad'aya amman duk tamanta sabida yanda taji dad'in ganin mijin tah, take taji tausayin shi yakama tah, dan tasan yakwaso gajiya sosai jitake kamar taje tamishi tausa amman tanah tsoro kuma, waya tah d'auka tanasan kiran shi amman takasa har kusun minti ashirin wayan nah hannun tah, finally tayi deciding takira shi dailing numban shi

Please Login or Register in order to submit comment