Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sai na kwashewa wannan d'an fillon komi inbarshi da fanko.
Banza tayi mishi, azuciyanta tana yaba rashin kunya irintasa.
Sai da ya jawota jikinsa yad'aura mata d'an kwalinta sannan ya bud'e mata qofar, suna kaiwa qofar kitchen ya damqe hannunta yace "anjuma araund 9:30pm zantafi Bauchi yin wani aiki mai mahinmanci, tace "Allah ya kaika lafiya "Amin ya amsa ya d'ora da cewa "amma banfad'awa kowaba gudun kadasu hanani tafiya sabida haka kema kiyi shiru da bakinki inna isa zan kirasu in sanar dasu, kai ta gyad'a tare da zame hanunta ta tura qofar zata shige yace "Bahijja ta juyo batare da ta amsa ba, ya miqo mata leda mai d'auke da box d'in sarqan ta miqo hannu asanyaye ta amsa tare da cewa thank you idanu ya lumshe ya bud'esu yace "don Allah Bahee yimin kiss akumatuna ko sau d'aya, shiru tayi tana kallon yadda ya lumshe idnunsa yana saurarenta.
Baiji motsin matsowartaba saiji yayi ta manna masa kiss a kumatunsa da lebbansa tare da qirjinsa yana shirin rungumeta ta fad'a cikin kitchen da gudu tana dariya, ya bud'e murya yace "l love you more mai sanyina, kamar daga sama yaji muryan ta ta amsa da "me too da sauri yasoma waige waige sai kuma ya fad'a kitchen d'in wai ko zaiganta amma bai gantaba ya shiga har cikin parlour nanma bata nan sai mutane da yagani sunyi yawa ya juya zai fice ya cinkayi muryan Adda Asma'u tace mishi "a'a horn.. Qato wakake nema haka?
Murmushi yayi mata kawai yasa kai yafice batare da ya ce da ita komiba, Amma aransa yana mamakin jin muryanta ta amsa shi sai kuma yabarma ransa qila ko don yasa abin aransane yaji kamar sautin muryarta.

Tana shiga d'aki Sumayya ta dubeta tace "dana ina kike haka ke kuwa? "Inda kika aike ni hajiyan tambaya, d'an dariya sumy tayi tace "uhmm aikin kyauta da kika shuka bawan Allah yayi tazan jiranki sannan akayi ta kiranki kikaqi d'auka a zabure ta kama kafad'un sumy tana cewa "badai saraki ne yazoba ko? "Shine man, ta zaune gefen bed tadafe kai tana tuno sanda taga Mujaheed yana latsa wayarta tasan shi yasa mata a silent d'an qara min tsaki taja tasoma kiran wayar Bilal tajita switch off, miqewa tayi tashiga bathroom.
Wanka tayi tare da d'uro arollah, bayan ta idar da Sallah Sumy ta miqo mata wata leda tana cewa "gashinan yace abaki bare da ta amsaba ledarba tace "miye a cikinsa? "Duba damasu ganinki man, tace da ita tare da ajiye mata ledar tafice abinda bayanta Bahijja tabi da kallo tana aiyana ko yaushene Sumy zata nuna kulawanta akan Bilal oho.

Zaune take gaban umma ta tura mata wani ferfesun 'yan shila kuma ta tsareta sai ta cinyesu tsaf tare da shanye romon.
Kamar zatayi kuka take cin naman tana wani yamutsa fuska tace "umma wai abinnan kuwa bazai mana illah? Ran kwashinta umma tayi akai tace "sarkin qorafi to bansani ba ta sosai kanta tacigaba da cin naman bata shanye romonba ta miqe tana fad'in "washh wannan shine azaba cin attarugu amdadin carrot, wallahi maza sun huta da irin wad'annan haukatakun kam, dama nine su .
"Kinci gidanku, mune mahaukata ko wa? Ta kama bakinta tana sonyin dariya tace "a'a umma niban ceba harara ta watsa mata ta nuna mata plate d'in romon "oya zoki shanyeshi yanxu ko insaba miki, ta tura baki ta jawo plate d'in kenan mama zulaiha ta shigo d'akin.
Ita d'in yayar umma ce.
Tana ganin hankalinsu ya d'auku akan maganar kayan qamshin d'aki ta fakaicesu ta sulale ta gudu batare da tashanyeba, tana jin umma na kwala mata kira ta arce da gudu tayi part d'in mummy tana dariya.

Mugun karo sukayi da shi yayin da tashigo tsakiyar parlour n da gudu bata lura da shiba.
Kanta ya doki qirjinsa tayi 'yar qaramar qara shi kuma ya furta "ashhh!!.
Taja baya tana shafa goshinta yayi saurin kamo kafad'unta yana jera mata sannu, kallonsa tayi sai kuma ta kalli agogo taga 10:40pm zatayi magana yayi sauri ya ja hannunta suka fita.

"Bansami jirgiba yau sabi da hazo, to gobe qarfe bakwai zan tafi "yaya kabar tafiyan mana, hararan ta yayi yace "sabida in halarci d'aurin aurenki ko? Kauda kai tayi ta amsa "eh harara yaqara watsa mata yasoma tafiya "bazan iyaba kam, sai dai kiyi hakuri "to Allah sai nafad'awa mummy "basai kinfad'aba najishi da kunnina, mummy ce kefad'an haka sanda tafito zuwa part d'in umma.
Da sauri mujaheed yabar gurin, mummy tace "ja iri dani kakeyi ai duk lauye lauyenka sai ka halarci d'aurin aurennan.


**** Mama yalwa takasa zaune ta kasa tsaye, batanan bata can duk don neman hanyar da Bilal zaizo yace yana son Munirat tare da ganin aurensa da Bahijja ya watse.
Amma ina ta Allah ba nataba abu sai cigaba yakeyi lamrin arziki sai matsowa yakeyi domin yanzu haka gobe ne d'aurin aure.
Hankalinta ya tashi najin ba ita awad'anda zasuje kano d'aukan amarya, afirgice ta fice gidan tasami wani wuri mara yalwan mutane ta tsaya ta lalibi numbern malaminta.
Bugu d'aya ya d'auka bako sallama yasoma yi mata kirari "hajjaju babbar mace hakima, giwa mai yawan... baqarasaba ta katseshi "malam da matsalafa "kamar nami?
"Baban yaron ya fidda wad'anda zasu tafi d'aurin auren tare da wanda zasu d'auki amarya sukaita gidanshi nacan, to babu ni cikinsu kaga da matsala babba sabida maganin daka bani kace anaso ya takane kafin d'aurin auren to bansan yanda zanyi dashiba.
Yaja numfashi yace "hajiya kada kidamu nagama aiki akanshi, kijira ganin saka mako kawai. "Tam shikenan malam Allah baka nasara ya amsa"Amin hajjaju.
"Amma ina son daki daina nunawa yarinyrki kinasonta da auren yaron sabida inba haka ko munyi nasaran acan to awurinta zamusami tangard'a don zata iya cewa ke kikayi wani abu akai "ok tam malam zan kiyaye sosai.
Tajuyo ta dawo gidan mai martaba cike da farin ciki.


Alkhawarin Allah yacika domin yau aka d'aura auren Bashir da Sumayya sannan na Bahijja da Bilal.
Sarakuna da manyan malmai da adtajirai hamshaqan 'yan kasuwa tare da y'an siyasa ne suka halarci taron d'aurin auren.
Bayan d'aurin auren angwaye suka zarce wani hotel mai tsada domin yin walimar cin abinci.

Mare sunsha kyau kamar mi mai kyalliya hajiya Jameela A Ladan tazo ta tsantsafa musu kyalliya mai kyau da burgewa sai walwali sukeyi.

Allah sarki Mujaheed maganin barci yasha don kawai kada yaji sanda za a d'aura auren da waninsa,
sannan yashige bedroom d'in Abba ya kwanta domin yasan Bashir sai yazo nemansa inya kwanta a d'akinsa amma inyana part d'in Abba bawanza zai zo sabida baza ayi zaton yana can ba.
Hakako akayi kuwa Bashir yayi tanemansa baigansaba akan dole yacewa abokansu yanaganin aikine yataso mishi a asibiti yatafi ai watarwa sannan suka haqura da son ganinsa.



*inayimiki fatan akhairi bebeelo akan novel d'inki da kika soma mai suna HAJARA Allah yayi miki jagora yadda kika fara lafiya Allah yasa kigama shi lafiya. Allah yaqara basira da kwarin ido tare da juriyan typing Amin. Nagode sosai da sadaukarwa*




*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.

*35 to 36*


'Dakin cike yake da qawayensu 'yan kwalisa sai hira suke suna shewa cike da farin ciki.
Bahijja tafito daga toilet d'aure da gudun towel ta zauna gaban mirror ta jona hand dryer ta busar da gefen sumar da ya jige yayin wanda ta gyara parking d'insa yafito fes sai kyalli keyi.

Tana lalibo kayan daza tasa ta cinkayi qawarta meena nafad'in "uhmm wallahi mijinki Bahee ya gama morewa abinsa,don kin had'a makaman yaqi sosai, hararanta tayi tace "meena kinboni ke kam, tunda bakyagani ki kyale.
"Eh d'in ban kyalewan, ai abin a fad'ane na gani "to sai kiyi tayi ai "ai ko yanzu zan d'ora.

Tawani karkace tana duban surarta sama da qasa sannan tace "ga boobs manya da burgewa ga hips ya cika dam tare da mazaunai masu d'an tsini sannan ga qaramin bakinki wanda zai yi dadin tsotsa, kai wallahi komi naki ya nuna luguf sai kuma kwasar albarkansa ya rage ayi.duk uban hararan da Bahijja ke doka mata bai hanata cigaba ba, sai da ta kama haba ta d'ora da cewa "daren gobe da drama agidanki Bahee, don nasan in d'an fillonnan ya rutsaki a matse matsinsa to sai buzunki domin inajin sai subahi zai saurara miki.

Kyal kyal!!!!!! 'Yanmatan d'akin suka kwasheda dariya suna tafawa da junansu.
Hamee ta cabe "amma dai ke kam meena 'yar buhuce, kinzauna kina tayi mata kallon qurullah abinda bai da kyu sam tare dayi mata zan cen banza.
"Allah Akbar ya sayyada mai 'ya'ayan aike, cewar khady tana jinjina mata afusace hamee takawo mata duka tana cewa "bakyau dai izgili inma shi kikemin, 'yar dariya khadyn tayi "ni kada kikaini inda 'yan quda ke salati.
Nanma qawayen suka qarasa dariya.

Sumy tashigo ta kalli Bahijja ta kama baki "kai keko adda B, ina zaki kai wannan mazaunai haka? "Inda zaki kai nakiman, ta amsa mata cikin fushi.
Tasa dariya "a'a ni kam nawa dai dai mijina ne ba irin nakiba manya wanda nasan mai dogon wuya bazai iya liliyawa da kyau sabida sunfi qarfinsa, banza tayi mata tacigaba da dubo kayanta yayin da mutanen d'akin suketa yima shaqiyanci suna dariya.

Mummy ce tashigo duk suka nutsu kamar basuba, sunata rige rigen gaisheta tana amsa cikin fara'a.

Tadubi Sumy tace "keda nace kikiranmin Bahijja ayi mata wanka matar najiranta shine kika shantake abinki ko?
"Ayya mummy yi haquri na sha'afa ne harara ta wullamata, tatsa takamo hannun Bahijja tana cewa "keda za iyawa wanka na musanman shine zaki wahalar da kanki.
Tura baki tayi tana duban gefe tace "wallahi ni banson wankanta, kawai tayi ta kallonka kamar wata mayuwa, don rainin hanakali irinnata d'azunfa damuks shiga tana cud'ani har tana wani cewa in gyara tayimin tsarki sai kace ta maidani jaririyan goye, to ni kam yanzu ba inda zani, shiyasa nayi wankana tunkafin tazo.
Mummy tayi murmushi "to shikenan tunda bakyaso , dama tacemin kina da gardama baza tazo da kantaba sai dai inzo da kaina intaho mata dake sai gashi kince bakyaso.
"Eh mummy banso tayi tayima Sis, caraf Sumy ta amshe "eh zatayimin kuwa kuma tayi ta koyamin dibarun riqe miji keko kiyi tazama dam kamar kayan wanki.

Dariya sosai sukasa har da mummyn, itako Bahijja sai harara take watsama Sumy kamar idonta zai fad'o.

Mummy ta d'aga musu hannu tace "Tam ya isheku yi mata dariyan hakanan, ta janyota jikinta ta rungumeta tana yi mata magana ahankali sai gyad'a kai takeyi tana murmushi, ta saketa tare da miqo mata wata jakka tace "kayan daza kiyi amfani dashi yana ciki, ta juyo tace da Sumy "muje kiyi wanka sai kizo kishirya domin kayanki kema na cikin jakan "to mummy ta amsa.
"Oya kuma kushirya domin yanzu za awuce kaisu gidajensu, tace da qawayensu.
dukkansu suka amsa da "to mummynmu, kai ta girgiza fuskanta d'auke da murmushi taja hannun Sumayya suka fice.

Wanka sukayi masu sallah nayi masu hutu kuma da sinyo wanka sai su hau shiryawa abinsu.
'Dakin ya gume da qamshin turaruka kamar gidan aunty khady qamshi hhh.

Mamie tace "kai Allah Bahee kin kwafsamu ace duk wankan nan damu kasha baza muje dinner ba don latsin hammata irin taki. "Uhmm kema kyadai fad'a kam, cewar Safiyya.

Ta amsa da "Aisai kuyi tayi, ba inda zanje in kwasomana kaina sanyi kawai abanza inyi ta atishawa, kuma sannan ai zuwan ba addini bane daza kudamu haka "eh ba addini bane amma rai nason nishad'i ko?
Fidy ke fad'an haka tana hararan Bahijja.
Ita kam dariya tayi kawai taci gaba da goge fuskanta.

Kyalliya mai kyau da burgewa tayi ta kafe d'aurinta na zamani sosai tayi kyau kamar my sis vc. Lolx.

Sadiya ce ta shigo itama cikin kyalliyanta
taja tunja abakin qofa tana qarewa kowa kallo zuwa can tace "kai kai wallahi kunsha kyau 'yammatan Amare, musanman Amarya sha lugude "ai kam za a sha lugude kuwa ajikinta, meena tace tana dariyan tsokana, mamie itama cikin dariyan tace "za adai daita a tsakiyar gadon amarci gobe,
hamee takama baki ta na kallon mamie tace "wai dama haka kice bansani? Bahijja ta amsa "ai kingansu nan duk 'yan kan uba ne wurin shaqiyanci, to duk kuyi kugama abinku sarakina rainona zaiyi sabida yasan nid'in yarinya ce bansan komiba sai dafa food da gyaran gida, "koba gyaran gida baaa!! 'yar rainin hankali kawai, Sumy ce ta amshe yayin data ke shigowa.
"To uwar taran aradu ba basmala, dake akayi? "Eh an taresan.

Dariya kawai qawayen keyi musu ganin sun rikice da rigima kamar wasu yara.

AddaAsma'u ce tashigo ta wuce dasu zuwa wurin su mummy da umma sukayi musu nasihohi tare da shawarwari sannan takuma yi musu jagoranci zuwa d'akin Abba.


Mujaheed bai tashiba barci ba sai bayan magriba. Jikinsa duk yayi wani lakaf ga wani radadi da zuciyarsa keyi ma. yadaure yashiga bathroom ya watsa ruwa sannan ya rama sallar la'asar ya d'ora da magrib yazauna yana azkar har zuwa lokacin isha'i tayi ya gabatar, addu'a sosai yayi akan Allah yaye mishi abinda yakeji aransa yakuma bashi dangana tare da juriyan rashin Bahee d'inta.

Yana zaune bisa sallaya Abba yasameshi ya zauna gefensa yana kallonsa zuwa can yace "koda wasa kada kaqara shan maganin barci alhalin kana lafiyanka kamar bakasan illarshi ba, sannan bana son sake ganinka cikin damuwa, inason kacire komi aranka, haka Allah ya tsara ita d'in ba matarka bace, kayi ta addu'a Allah yahad'aka da rabonka na Alkhairi.
Ahanakali ya amsa "to Abba, nagode.
"Tashi kazo muje kaci Abinci, ya miqe yana had'a hanya yabiyo bayansa.
Dakanshi Abba ya had'a mishi ruwan tea bayan ya shanye ya tura mishi plate d'in abinci yaci sosai sabida rabonsa dayaci wani abu tun daren jiya da ya sha coffee.

Suna hira da Abba yana qara yi masa nasiha su Adda Asma'u suka shigo suka zauna.
Ba jimawa Bashir ya shigo yad'ora idanunsa kan Muaheed yako watsa mishi harara, yana gani yasaki dariya yana kallon insa Bahijja ke zaune yace "su Amare da ango ansha qamshi Abba yayi murmushi yace "kaima kaqi 'yar gidan Alhaji kamilu ne ai dayanxu tare zaku bar mana gidanmu mu huta da tazurancin ku. Sosa kai yayi yace "Abba na kusa nima da yardan Allah "to Allah yakaimu lokacin lafiya, suka amsa da"Amin.

Nasiha sosai Abba yayi musu wanda duk dauriyansu sai da sukasa kuka.
Aqarshe yabawa kowa key d'in mota suka amsa suna yimasa godiya.
Da kansa yakaisu bakin motar d zasu shiga ya umurci Mujaheed yaja Bahijja ya kaita gidan mijinta ita kuma Sumayya babban abokin Bashir ya d'auketa ita da hajiya zulaiha yayar umma yayin da mummy suka tafi da Bahijja, sauran motacin suka taho da qawayensu.

Sai kuka Bahijja keyi mummy na rarrashinta taqi daina kukan.
Cikin qufula Mujaheed yace "mummy zan tsaida motarnan inmata dukan tsiya indai batayiwa mutane shiru ba.
"Cikin fad'a mummy ta tari numfashinsa "to ubanta basai ka doketan inganiba.
Yacije labbansa yana jijjiga kai.
Bai qara cewa komiba har suka isa gidan.
Plat mai kyau da tsari dai dai zaman mace d'aya.
Ya gyara parking yafito ya bud'ewa mummy ya sunkuya daidai kunnin Bahijja yace " kifito da bissimillah kuma kiyi addu'a, ta gyada masa kai alamar to.

Yana jingine ajikin motar suka shige da ita.
Dafashi yaji anyi ya waigo yayi arba da Bilal yana jifanshi da wani murmushi mai kama dana mugunta, shima murmushin ya maida masa yad'ora da cewa "ango kasha mai "a'a my inlaw banshaba tukunna sai zuwa kamar gobe dai, kauda fuska mujaheed yayi yanajin kamar ya naushi bakinsa ya maidashi wawulo.
ya saita kansa yace "to madallah , Allah bada zaman lafiya "Amin ya amsa tare da tafiya zuwa fita daga get.

"Wawa mai siffan mata kawai, jibeshi kamar sandar kiwon akuyoyi, mujaheed ya ke furta hakan a fili.


*hhhhhhh kai mujaheed duk kishinne haka*



*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.

*37 to 38*

Yanan zaune asamar motarsa yana jiran fitowar mummy su wuce, wayarsa tasoma tsuwwa ya d'aga da sauri ganin sunan mummyne ya d'aga da sauri.
"Ka tafi da wanda zasufito yanzu gida, ni sai gobe zan dawo sabida har yanzu taqiyin shiru sai kuka takeyi kamar almatsutsai sun shafeta, abida tace dashi kenan.
"Mummy miye kuma almatsutsai? "Junnu nake nufi "subbahanallahi, to Allah ya kyuta, ayi mata ddu'a "shinakeyi mata yanxu haka "ok tam sai goben.


Yana isa gida ya zarce d'akinsa cike da jin kasala sannan sautin kukanta yaqi fita daga kunninsa.
Arollah ya d'auro yasonma nafila sannan ya d'ora da karatun al QUR'ANI.
Sai da yaji barci yasoma kashi sannan yashafa add'a ya kwanta zuciyarsa cike da nutsuwa.


Ganin Bahijja taqi yin shiru yasa mummy janta suka shige d'ayan bedroom d'in.
Jijjigata mummy tayi tana cewa "wai miye haka kikeyi Bahijja? Shin aurennan dole akayi miki ko kuwa zabinkine? Tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.
Mummy tacigaba "kin dagulamin lissafi har ina zaton ko junnu kike dashi suke saki wannan irin kukan ashe bakomi lafiyanki lau, to kimin shiru ko in saba miki.
Bahijja tayi lamo jikin mummy tana jan hanci tare da ajiyar zuciya, mummy ta d'agota idanunta lumshe ruwan hawaye na zubowa, d'an tsaki mummy tayi tace "sarkin kuka kamar baure.
Saida ta zaunar da ita gefen gado sannan ta kira sunarta "Bahijja ta bud'e ido ta amsa "na'am "mike damunki? Tayi raurau da idannu girgiza mata kai mummy tayi "a'a kada kimin kuka, amsa kawai zaki bani.

Ahankali tasoma magana "mummy bansan mike damunaba amma daga jiya zuwa yau zuciyata sai bugawa take da qarfi tare dajin fad'in gaba, inaji ajikina wani abu maradad'i zai faru dani sannan tunda nashigo gidannan sai gaban nawa yaqara tsananta fad'i.
Mummy tayi sukuti tana jinta, zuwa can take addu'a zaki dage dayi ba kukaba sannan duk inkinji fadiwar gaba to ki yawaita istiggifari tare da fad'an lahaula wala quwwata illa billahil aliyul azim, zaki sami sassauci "tam mummy zan dage da fad'a insha Allahu.

Robar fresh milk mummy ta d'auko tare da cup ta zuba mata tashanye, aqallah sai da tasha kusan kofi uku sannan tace "mummy naqoshi.

Tana jingine jikin mummy tace "dukfa bugun da nakeji zuciyata tanayi to yaya mujaheed yake fad'omin arai, wallahi daga jiya zuwa yau na tunoshi yafi ba adadi, kuma narasa wannan dalili.
tsawon lokaci mummy ta d'auka shiru kamar baza tace komi, zuwacan taja numfashi tana kallon Bahijja tace "sonshi kikeyi shine yahaifar miki dajinsa aranki amma kisani duk yanda zakiyi to kiyi ki fiddashi aranki sabida ke d'in yanzu matar aurece yin haka zaisa ki d'aukanma kanki zunubi babba.
Kai ta gyada tana share hawaye.
"Allah mummy bansan ina sonshiba sai da nauyi ya hau kaina amma don Allah mummy kiyi haquri ba qinsa nayiba Allah ne bai nufa muzamo ma aurata ba.
Tana shafa kanta tace "nasan da haka Bahijja shiyasa bandamu ba kuma ina qara jadda miki da kiyi watsi da dukkan wani tunanin banza da shaid'an zai rayamiki,
kizauna lafiya da mijinki kada kisake yagane zuciyarki na begen waninsa inhar kina son zaman lafiya ya d'ore atsakanin ku.
"To mummy, nagode sosai da kulawarki agareni, insha Allah zan kiyaye. Tana murmushi ta amsa "Allah yasa "Amin.


Washe gari akayi bud'an kai yai armashi sosoi.
bayan an watse aka gyara mata gidanta tsaf sai qamshi ke tashi.

Mummy ta kira Mujaheed yazo ya maidata gida amma tace in yazo ya tsaya abakin get don batason Bahijja tasan fitarta.
Kimanin 30mins ya iso ya kira yasanar mata.
Ta sulale bayan ta fakaici idonta sanda take hira cikin qawayenta, tafice tasami mujaheed suka wuce gida.
Mummy na qoqarin fita sanda suka iso gida mujaheed yace "am mummy tabar kukan kuwa? "Tabari tun jiya, yanxu haka nabarota tana ta hira ne cikin qawayenta.
Kai ya kad'a ita kuma tafice tayi ciki abinta amma aqasan ranta tanajin tausayin d'anata sosai.

Mummy tana zama kiran Bahijja yashigo wayarta tana dariya ta d'auka.
Kukanta shi yayi mata sallama sosai takeyi kamar wanda akayiwa dukan kawo wuqa.
Cikin shashsheka take cewa "mummy miyasa kika tafi batare dakinmin sallamaba? Cikin fad'a tace "to sarkin kuka qanwar bishiyar baure don natafi ban sanar dakeba shine kike wannan kukan? To Allah tun wuri kikiyayeni da wannan tabaran kuma kiyi sauri ki shanye kukanki tunkafin mubata da ke. Bahijja tayi shiru tana ajuyar zuciya, dan tsaki mummy tayi cike dajin tausayinta tasoma rarrashinta har saida ta tabbatar ta haqura sannan sukayi sallama.
Tagumi mummy tasa tafad'a kogin tunani wai mike damun yarinyannan haka ne? Ta tambayi kanta.
Ga 'yar uwanta can banji ance ko tari tayiba amma ita kam daga daren jiya zuwa yau tayi kuka yafi shurin masaqi, kai Allah yasa dai Alkhairi ne. "Amin ta amsa afili.


9:30pm abokanan ango suka rakosa gida, bayan angabatar da addu'o,i tare da 'yan barkawanci sukayi musu sallama tare da d'aukan qawayenta suka maidasu gidajen iyayensu bayan sun cikasu da abin arziki.

Bilal bakinsa yaqi rufuwa don tsananin murna, ya qaraso wurin datake zaune ya d'ago kanta ya manna mata kiss agoshi sannan ya jawota zuwa jikinsa ya rungumeta, akunninta yake rad'a mata "sweetie yau zan shayar dake madarar qauna mai wuyar mancewa. Tad'an janye jijinta ya qara kamota ya matseta sosai wanda sai da tayi qara da sauri ya sake yana murmushi, hannunta yaja zuwa d'akinsa bayi ya shiga dasu basu jimaba suka fito d'aure da arollah.
Sallah yajasu raka'a biyu donmi nuna godiyansu ga Allah SWA dayanufesu da zamowa ma aurata.
Addu'a sosai yayi musu sannan suka shafa ya juyo yayi mata tambayoyi akan addini tana bashi amsa.

Shi ya ciyar da ita da zalla tsokar naman kaza wacce taji g yara da kaya na musanman sai da yatabbatar ta qoshi ya dauka cup daya cika da holandia milk yabata tashayen ya qara mata da ruwan swan mai sanyi tasha sannan yasoma bawa nasa cikin hakkinsa.

Brush sukayi sannan ta sanza kaya zuwa night wear shima haka kaya yasanza ya hayo bisa bed d'in yana cewa "princess zo inbaki ajiyarki boy or girl wanne kike so? Quri tayi masa da ido takasa ce masa komi, yasaki siririyar dariya ya janyota jikinsa tare da kashe full light.

Wasa yake da ita son ransa takasa hanashi zuwacan ya dakata ya rungumeta.
abin al'ajabi sai jitayi kanta na sara mata sai kuma tashin zuciya tasoma qoqarin kwace jikinta ya qara qamqameta tare da tura kansa tsakiyan qirjinta ya dawo da bakinsa bisa boobs d'inta yana tsotsa numfashi take fitar da sauri tana cigaba da tureshi bata ankaraba ya had'e bakinsa da nata wani abu taji yataso mata da qarfi tasa hannunta ta tureshi tasauka da gudu ta fad'a toilet tayi ta kwara amai tabaki ta hanci kamar za mata a amayar da kayan cikinta.

Jikinsa narawa yazo ya d'agata ya taimaka mata ta wanke bakinta
ya dauketa cak ya maida bisa bed sannan yakoma ya gyara wurin data bata.


Can tsakiyar dare Bilal yagaza haquri yasoma yamutsata ta falka afirgice zata miqe yayi saurin maidata yana cewa "don Allah queen kimin rai kibarni inji d'uminki ta hanyar raya darennan mai matuqar muhimmanci agaremu.
Kai

Please Login or Register in order to submit comment