Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fice gidan zuciyarsa cike da annashuwa.

Tana shirin shiga part d'in umma taji an fincikota tana yin arba da Mujaheed ta dage bud'e baki ta qallah qara da qarfi mummy ta fito da hanzari dama tana cikin part d'in umman.
kafin mummy ta ganshi ya saketa da hanzari yayi cikin garden har yana tuntube kamar zai fad'i.
Bahijja tasaki murmushi, mummy ta qaraso tana tambayanta mi yafaru? "Bakomi "shi ne zaki qalla wannan uban qaran haka, tana d'an dariya tace "wani qaton bera nagani zai shiga garden shine yabani tsoro "ok Allah ya kyauta, amma kibar ihu haka inkinga abin tsoro, addu'a akeyi, "to mummy, ta amsa.

Sai da ta leqa garden ta bud'e murya da qarfi tace "Allah ya isa bera, mugu kawai d'an masara ana goyonka kana geza.
Mummy tasa mata dariya tace "lallai yaka mata anemo masu ruqiyya agidannan, naga alamar ke da Sumayya kuna da sabbin iskoki marasa kan gado.
Bahijja murmushi tayi tare da cewa "mummy lafiyanmu lau fa.

Ana gobe bikin Nana Bahijja, Sumayya, umma tare da mummy suka isa garin kwara kwara abisa jagorancin Bashir. Yana saukesu ka gaisa da malam ya wuce yace sai kuma gobe zasuzo d'aurin aure tare da Abba da Mujaheed.


Gwg Bintu ta karramasu sosai tayi ta mamakin girman Bahijja sabida tafi Nana jiki da tsayi sosai.

Uhmm gwg Lanti tawani qanjame tayi baqi duk tabi ta lalace takoma kamar birin wasa. Hhhhhhh

Su umma suka bawa gwg Bintu kayan kitchen nazamani masu kyau da tsada shi kuma malam kud'i mai yawa Abba yabada abashi.

Aiko sunyi ta murna, dangi suna ta shigowa yi musu godiya tare da addu'ar gamawa lafiya. Gwg Lanti kuwa baqin ciki kamar ya kasheta ranar ganin yadda gwg bintu ke samun abin arziki ta ko wani lungu da sako na garin da wajen garin.

Gidan hindu su Bahijja da Amarya tare da qawayenta suka kwana. Daren ranar Bahijja tasha aiken kira gurin samarin garin wai tazo tayi biris dasu, Sumayya ansami abinda akeso sai tsokanarta takeyi wai ita jinin 'yan qauye ne tunda gashinan sun hanata sukuni da kira, ita dai kunnin uwar shegu tayi mata.

Washe gari bayan sallar azuhur aka d'aura auren Nana da angonta jabeer.

Shima d'an garinne amma mazaunin garin kaduna domin acan yake aiki.

Abba da su Mujaheed sun hakarci d'aurin auren, sosai malam yaji dad'in ganinsu yayi ta musu godiya yana sawa Bahijja Albarka domin itace sillar had'uwarshi da mutanen kirki da suka zamo tamkar jininsa.

Da yammaci aka d'auki amarya zuwa gidan mijinta dake kaduna.

Bahijja tana cikin motar Bilal tare da maryam da munirat wanda sukazo bikin suma.
Suna shirin bin motar da ya d'auki amarya Sumy tazo da sauri tace "adda B wai kizo inji yaya Mujaheed, ad'an daburce tace "dama batare da su Abba ya wuce ba? "Eh, zaiyi wani aiki a kaduna gobe shiyasa ya tsaya.
"ok ce mishi ganinan zuwa, sumy ta juya abinta batare da ta amsaba.

Kallon Bilal tayi ta marairaice tace "sweet sarakina don Allah ina zuwa yanzu, kai ya d'aga yana murmushin yaqe.

Tana tsaye agefen motarshi tace "gani ance kana kirana, harara ya watsa mata yace "zagayo kishigo ciki ta tura baki tace "a'a gaskiya ni ana jirana ne, ya dubeta tana shanye da ankon bikin, atamfa ce pink calour d'inkin ya fitar da suranta sosai, inma ba idonshi ke yi mishi gizoba sai yaga kamar ya matseta a qirji sosai, ta sanya wani ficicin gyale wanda dashi gara babu,
fuskannan tasha make-up tafito fes da ita. Wani ta kaici tare da kishi ya duran mishi aqhon zucci.
Cikin tsawa yace
"Zaki shigo ciki ko sai nafito na turaki da qarfi.
Ba ason rantaba ta shiga gabar motar ta zauna tajuyo tana hararan Sumy tasan duk ita ta had'a mata wannan tuggun.

Fizgan motar yayi da aqarfi yazo wurin su Bilal ya sauke glass d'in motar yace "hy guy miqomin tarkacenta dangin fox da wayoyinta zamu wuce gidane yanxu domin bawani gidan Amaryan da zasuje.

kallon banza Bilal yayi mishi yace "in anqifa?
Ya zunkud'a kafad'a "sai kariqe ka gara guzuri dama kai d'in kayi kama da 'yan maula. Baijira jin komi zai ceba ya bulalesu da qura ya wuce yabar Bilal da baki bud'e.



*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.
*29*
Kuka takeyi mai sauti, bawanda ya kulata cikin Mujaheed da Sumayya, ganinka haushi yaqara quleta taqara fittar da sautin kukanta sosai.

har suka wuce garin zaria bata daina kukan ba, zuwa lokacin har muryanta tasoma dushewa.

Mujaheed ya dallo mata harara yace "malama ya ishemu hakanan, kimin shiru ko intsaya inmiki shegen duka. Banza tayi mishi tacigaba da kukanta tana jan hanci.
Yaja qaramar tsaki ya maida hankakinsa a bisa hanya amma jin zuciyarsa yake kamar wuta sakomakon kukan datakeyi, ya kuma jan tsaki akaro nabiyu ya juyo ya daka mata wani uban tsawa wanda yasa ta tsaya tsak da kukan bashiri,
hatta Sumy dake baya tana chart sai da ta girgiza wayarta ta zame ahannunta ta fad'i.

Ya had'e rai kamar dare, yace "inkuma jin tarinki anan kiga yadda zanyi dake, shasha shan banza kawai, don antaba wancen zuqalallen yaron ne zaki samu agaba kina kuka kamar wata sauna, to kiqara bud'emin baki kiga yadda zamu kwashe.

Ita dai tayi shiru tana sauraren bala'in dake zubamata kamar yasami 'yarshi.
Bata qara yin kukanba amma lokaci lokaci tana sa bayan hannunta ta share hawaye, sai ajiyar zuciya take saukewa.

Sumayya duk sai tausayinta yakamata, ganinta keyi itace sila
sabida dabata cewa Mujaheed kada yabi su Abba ba ya tsaya ya kaisu gidan Amarya da duk hakan bata faruba.

Ahankali ta matsa ta dafo kafad'anta tace "Adda B, sorry please Bahijja ta ture hannunta ta juyo ta watsa mata harara ta maida kanta gefe ta kwantar tana cigaba da hawaye.

Basu iso garin kano ba sai wuraren 9:00pm sabida koda suka baro garin qarfe shida ta wuce.
Yana gyara parking ta kai hannu zata bud'e ta fice yayi gaggawan damqe hannunta da kyau.

Sumayya ta fice tare da kayansu tayi gaba batare da tajira fitowar Bahijja ba.

Hannunta ta kalla da ya riqe, cikin dushewar murya tace "sakeni, yasaketa ta ja qofar tajita kulle gam ta juyo da kubburarrun idanunta tana hararansa baki a ture tace "kaga malam banso wulaqanci, kabud'eni inshaga gida.
Yayi mata shiru yana kallonta, ta kauda fuska gefe tace "wallahi jaheed inbaka fita hanyata sai na had'aka da mummy ko Abba.
Murmushi mai sauti yasaki yace "kafin ki had'ani dasu inaso yanzu ki amince da kina sona kuma zaki aureni.
Wani wula qantaccen kallo ta watsamishi, ya runtse idanunsa yana fatan jin alkahiri abakinta amma sabanin haka sai ji yayi tana cewa "anqi asokan, bana sonka, bazan aureka, kai ba type d'ina bane, nasha gaya maka hakna, natsaneka jaheed, bansonka sam araina indai da aurene, sabida banson miji qato irinka. Taja mumfashi tana kallonsa, shima ita yake kallo fuska ahad'e, ta sunkuyar da kanta tacigaba "wallahi jaheed tsoro girmanka kebani, shiyasa natsani kamin maganar aure sai inji jikina yasoma rawa donmin billahillazi bana qaunar qaton mutum mai tumbi irinka, nafi son siriri kamar yaya Bilal d'ina d'an caras cas abinshi kuma ga shi mai n...... bata qarasa abinda takeson fad'aba taji saukan wani mari mai kyai a fuskanta, arazane da fad'a jikinsa ta cukuicuye shi ta saki wani kuka mai ban tausayi tana goga fuskanta a faffad'an qirjinsa.

Sai kuma jikinsa yayi sanyi, Sosai yaji ba dad'i ganin yadda alokaci d'aya duk ta gigice.
Cike da nadama yakai hannunsa bisa sumar kanta yana shafawa cikin sigar rarrashi yasoma cewa "Affuwan Bahee, kiyi hakuri don Allah zuciya tace takasa jure sauraren jin kina yabon wanin ta.

Ta zame jikinta cikin muryan kuka tace "ahaka kakeson in aureka kana maduki.
Ya sunkuyar da kai "ki hakuri sharrin shaidan ne yasa na mareki amma inbaki hakura ba to ga face d'ina kirama, indai za ki amince da dani, ya matso ta sosai ta kauda fuska "bud'emin qofa infita, tace cikin had'e fuska.

"Sai kin yafemin marin dana yimiki abisa kuskure sannan kuma ki min alqawari baza kifad'ama su mummy ba.
Tayi shiru tana tunani zuwa can tace "na yafe maka kuma bazan fad'iba. Murmushi yayi yashafi fuskanta tare da soka yatsarsa cikin dimple d'inta, taji wani yarr tayi sauri janye fuskanta, ahankali taji yace "nagode tare da bud'e mata qofar tafice da sauri. Yabi bayanta da kallo yana murmushi.


***** Bilal kuwa suna bacewa ganinsa ya kife kansa yana sauke wani zazzafan numfashi ransa in yayi dubu ya baci.

Maryam ce cikin qarfin hali tace "yaya don Allah karabi da Bahijja, kodon tsira da mutuncin ka, jin yayi shiru tacigaba " tunda alamu sun nuna yana sonta ai sai ka kabar mishi ita ka koma inda ake ganin girman ba a akiranka d'an maula akan wasu banzayen wayoyi, ta qarasa maganar tana hararan wayoyin Bahijja.

Wani mugun kallo yayi nata ya nunata da yatsa "kinsan Allah kika kuskura naji wannan zancen a gida wallahi sai jikinki ya gayamiki kuma dakike cewa in rabu da ita, innayi hakan nabashi dama yayi nasara akaina kenan, to kusani yanzu na fara sonta kuma insha Allahu sai na aureta.

Cikin qufula Munirat tace "ta sani dai wanda ta damu da lamarinka amma donni banji ko dar ba,
sabida tuntuni nagane inda kemin ciwo na nemi magani.
Aharzuqe ya juyo zai sauke mata ruwan matsifa ta kafeshi da idanunta masu ban sha'awa, ya koma jiki asanyaye.

"Zaku je gidan amaryan ne ko kuwa? Yace dasu "munfasa zuwa yaya, kaimu gida kawai. Cewar maryam.

Suna isa qofar fada munirat ta dubesh "ni Zaria nake son kwana yau, don Allah inshiga ind'auko kayana mu wuce? "A'a kibari sai gobe.
Ta tura baki "ai nazaci yau kano zakayiwa cinke kakai ma mai son naka wayoyinta.

"Ke!! Get aut. Yace da ita cikin tsawa.
Tafice tana dariya cike da tsokana tace "sorry masoyin Bahijja 'yar gold.
Bayanta yabi da harara sannan ya furta "sai naci gidanku mai kan goruba kawai.

*Hhhhhh sabida da munirat bata da yawan gashi sosai amma dai tubarkallah tunda tafi su ooo 'yan adawan oga Bilal. Lolx*



*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWA BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.

*30*
Tana zaune gefen bed d'inta hannunta d'auke da wani qaramin cup, tea ne cikinsa tana kurba ahankali tana cin cake.
Sumayya ta shigo ta zauna gefenta tana kallonta,ta dubi agogo taga 10:52pm sannan ta dubi Sumy fuska had'e tace " lafiya zaki shigomin d'aki a wannan daren? Banza Sumy tayimata, ta miqe tashige bathroom bata jimaba tafito da alama arolla tayo.
Addu'a ta fofe d'akin dashi sannan ta haye gadon tayi addu'a ta shafe jikinta dashi ta ja blanket ta rufa, duk abinda takeyi Bahijja da idanu ta ke binta,
batace da ita kanzilba haka itama.

Kamar batason magana tace "aramin phone d'inki, Sumy ta janye blanket d'in ta tace "waza ki kira da darennan? "In naji zafin shaqa sai infad'a miki.
Sumy tasa 'yar dariya tace yi haquri hajjaju bani nakar zomonba rataya akabani.
Dan siririn tsaki tayi tace "malama inzakiba kibani banson wulaqanci, tamiqo mata tana cewa "al fitinatu gashi kada ki cinyeni d'anye, banza tayi da ita tasoma latsa wayar, tayi ta ringing ba ad'agaba takuma kira nanma ba ayi picking ba saida ta kira sau biyar ba d'auka.
Cikin fushi ta cilla wayar gefe ta miqe fuu tashige toilet.

Barci yasoma d'aukanta taji ana hura mata iska akunni ta bud'e idanunta ahankali ta saukesu kan Sumy da sauri ta tashi ta kafeta da ido ita kuwa Sumy dariya ta saki tana nunata da yatsa tace " ke matsoraciya ce, daga ina yimiki yadda yaya Bashir zaimin in munyi aure shine zaki wani tashi kina zare idanu haka.
Harara ta zuba mata cikin hasken da bai wadaci d'akin ba.
Tace "kice dai kina fad'amin abinda kukeyi in kun kebe, shi yasa kuke yawan shiga garden inda ba wanda zai gannku ko? To ku sani Allah naganinku.
Sumy ta dallamata duka acinya tace "dalla malamansu kada kimana sharri, ba abinda muke sai hiran da ya halatta.
Bahijja ta juya mata baya "fad'ama k'yeya yariya.

Tanajin Sumy na cewa wallahi bamu yin tabe taben komi illah hiranmu ta ma'abota bege, banza tayi mata taqara yin addu'ar kwanciya ta shafa ta lumshe idanunta tana son barci ya kuma d'aukanta amma da alama bai da niyyar zuwa.
Tsawon lokaci tana juye juye, ganin haka yasa ta tashi ta d'auro arollah tasoma jera nafilfili.
Sumy kuwa tuni tayi nisa da barin garin kano ta kusa kaiwa birnin kebbi hhhhh lolx.



Washe gari da misalin qarfe 10:00am Bilal ne tsaye gaban mirror yana taje sumarshi, taji gyara sai kyalli takeyi.
Fox d'in Bahijja yagani bisa mirror ya d'auka ya bud'e, babbar wayarta ya duba yaga miss call da yawa, amma wanda yafi d'aukan hankalinsa shine wanda yaga ansa Hon. Qato jaheed. Sai da yayi dariya sosai sannan ya zauna bisa stool, ya dannakira saida takusa tsinkewa sannan aka d'auka, cikin alamun barci yaji ance "gabo wayaba izinin yimata kira da waya? Duk da sunar da yakirashi dashi yayi mishi zafi amma sai ya danne yasaki dariya mai qarfi yace "barka da tashi Honourable qato, wahalalle mai son maso wani, cikin fushi mujaheed yace "kai wawa, gabo mara aji kakiyayi had'uwarmu da kai, banza kawai, bai jira komiba ya datse kiran yana huci, shima Bilal hucin yakeyi yace "had'uwarmu bazai maka kyauba wallahi, muzuba mugani.


Hon.qato shine sunar da Mujaheed yayi ta nanatawa aransa. Lallai yarinyannan tagama rainani, yadafe goshinsa zuwa can ya ture bargon da yake ciki yafad'a bathroom.

Da sallama ya shiga part d'in umma, Abba da umma yasama bisa dinning sunayi break fast.

Ya russuna ya gaidasu suka amsa cikin kulawa. Yaja chair yazauna umma ta had'amishi abinda yafiso ya karya dashi ta tura mishi, cikin murmushi yace "nagode umma Allah jamana da ranki cikin amincin Allah. Abba ya amsa "Amin.

Har yagama karyawa baiji motsin Bahijja ba sai yayi tunanin wata qila takoma barci ne.
Yayi musu sallama yafito zuwa part d'in mummy.

Bahijja tana kwace a 2sitter tayi rigingine tana amsa waya da phone d'in mummy.
yayi sallama yashigo, bataji salamarshi ba sabida hankalinta baya tare da ita, yana can wurin Bilal.
Qamshin turarensa data shaqa yasa ta tashi zaune tana cewa
"ok hubby sai kazo anjuman, ban inda zani.
Ta sauke wayar tana kallonsa cike da tsoro domin tunda ya mareta jiya tasoma jin shakkansa.

Murmushi yayi sanda yagano tsoronsa a idanunta.
Ya sunkuyo ya damqe hannunta ya matsa da qarfi zata sa qara yayi saurin toshe mata baki da hannunsa yarad'a mata a kunni waye hon.qato? Tayi shiru tana qifta idanu narashin gaskiya.
Ganin taqi magana ya qara sunkuyawa ya ciza kunninta ta zabura ya maidata ta zauna "zakifad'amin ko sai na qarya miki wannan sillen hannun? Tasoma zubar kwalla, ya matse hannun sosai jin azaba yasa ta manwa hannunsa cizo wanda yasa ya rufe mata baki da shi.
Bashiri ya saketa ta miqe zata gudu yayi saurin kamo kafad'anta, adai dai sanda mummy tafito bedroom d'inta, aiko ta daka mishi tsawa tace "saketa!! Sarkin mugunta, yana sosa kai yace "mummy inguwa zata rakani shine wai zata gudu.
"Eh ba inda zataje don haka kakama gabanka kayi tafiyarka kajiko? Yayi shiru kansa sunkuye yasami wuri yazauna.

"Zo in tsefe miki suman, zuwa anjuma kuje awanke muku "to mummy, ta zame gyalen data d'aura ta zauna tare da kwantar da kanta bisa ciyar mummy.

Har mummy tagama mata tsifan ta tufke mata yana zaune yanata latsa wayarsa.
Mummy ta miqe tana cewa "in anyi sallah sai in kaiku, nima daganan awankemin nawa naji yasomamin qaiqayi.
Cikin dariya tace "mummy furfuran tsufane kesaminki qaiqayi " to yazanyi tsufa lakacinsa ne ai tace tana shigewa kitchen.

Itama Bahijja tashi tayi tana kallon Mujaheed ta gefen ido ganin hankalinsa bai wurinta tayi saurin ficewa zuwa part d'in umma, yana hankalce da ita.
Tana fita ya mara mata baya shima da sauri.


*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.
*31*
Kusan atare suka shiga falon domin tana zama gefen umma wanda ke zaune tana duba wani littafin addu'o,i, shima ya shigo.
Umma tad'ago tana dubanshi tareda amsa sallamar da yayi.
Sai duk kunya takamashi sabida bai tsammaci samun umma a parlour n ba. Ya d'an sosa kai yana duban Bahijja ta gefe yace da umma "dama aronta zakibani tarakani gidan adda Asma'u.
Murmushin manya umma tayi sannan tace "kai da qanwaka sai ka tambayeni don zakufita, yana motsa yatsunsa yace "umma ai qara kisani yafi "to yayi, gatanan ai.

Bahijja tayi narai narai da fuska kamar zatayi kuka tace "wallahi umma ni barci nakeji, yatafi shi kad'ai ko yasami sis Sumy sutafi tare.
Cikin sigan rarrashi umman tace "yi hakuri ki rakashi, inkinje can sai kiyi barcin, kinga Sumayya tana barci kuma bai kamata atashe taba.
Ganin umma tana rarrashinta yasa ta miqe tashige d'akinta bakinta ature.


Suna tafiya tana yimasa qunquni, yayi banza da ita. Wurin wani saloon yayi parking ya dubeta cikin sakin fuska yace "shiga kifito ina jiranki, sabida kada muwuce lokacin da zaku fita da mummy inkoma ta saukemin 60.

Banza tayi mishi, yabud'e wallet d'insa yafidda 5k yace gashi nan ayi miki mai kyau, ta harari kud'in ta kauda fuska.
Yabi kyeyarta da kallo.
Ya sa hannu ya ja d'aurin d'ankwalinta yako warware, ta juyo afusa ce, ya kashe mata ido tare da kai hannunsa samar wuyanta ya sakkoshi bisa gaban riganta ya ja yana shirin leqa mata boobs ta turashi baya cikin fad'a tasoma magana "wallahi jaheed nagaji da abinda kakemin, haba don Allah ace atitinma sai kamin wulaqanci, to Allah nikam nagaji.
Ya kafeta da ido yana shafa sajensa cike da annashuwa yace "dawai dubawa zanyi ingani ko sun nuna.
"Basu nunaba tace dashi cikin qufula. Ido ya zaro yace "kai haba? Duk wannan cikan danaga sunyi kamar zasu faso riga ashe da sauransu, amma kuwa in sunfi haka zasu baki matsala.
Banzatayi mishi tana jinjina rashin kunya irin na wasu mazan.

Yasaki dariya yace "kinsan Allah inbaki je anwanke miki kan nan ba sai munkai magariba zaune anan.
Jin haka yasa ta juyo ta zari 1k tafice tana cewa "jarababbe kawai.
Kai ya gyad'e yace "akanki ba nake haka.

Ya gyara kwanciya jikin sit yabi bayanta da murmushi.

Kimanin 1hr aka gama mata ta fito.
Sun d'auki hanya ya dubeta "bud'emin sumar ingani ko anyi miki mai kyau. Hararansa tayi tace "to mijina. Ya saki murmushi mai sauti yace "insha Allah nakusa zama, akai kaice ta kalleshi tace "uhmm zamuga ikon Allah.

Haka yayi ta yawo da ita, tana mishi qorafin ita tagaji ya maidata gida, barci takeji yayi banza da ita.
Sai da akayi sallar sannan ya nufo gidan adda Asma'u da ita.

Suna shiga parlour n yaran gida suka cukui kuyeta suna kiran "oyoyo aunty B, oyoyo aunty.

Mujaheed yayi tsaye yana kallon yadda take d'aukansu d'aya baya d'aya tana d'agawa sama tare da manna musu kiss a kumatunsu har tazo kan qaraminsu mai suna muhanmad ta d'agashi da kyat ta direshi tana nishi tace "kai dai anyi fimfid'ed'en qato anan irin su ooo tana kallon Mujaheed da yake murmushi yanajin aransa kamar ace yaransu ne shi da ita.

Yaran sukasa dariya suna kallo uncle d'in nasu, badariyya itace mai wayon cikinsu tace "haka ummie ke cewamasa qato sai gayya.
Bahijja tasa dariya tace aiko sai gayya kam, wannan irin gado da yayo haka abin sai addu'a, yaran kuwa suka qara volume d'in dariyansu.

Adda Asma'u tafito daga d'akin mai gidanta tanamusu maraba.
Tajasu zuwa dinning Bahijja tace ita sallah zata farayi tukunna.

Koda ta idarsa da sallar gado ta hau, bata jimaba barci ya d'auketa.

Koda adda Asma'u ta turo badariyya ta kira ta inta idar sai komawa tayi tasanar da ita tayi barci.


Mujaheed yasanar da ita baiyi nasaraba har yanxu kuma shi bazai iya haqura da itaba.
Nasiha tayi mishi dayayi hakuri in rabonsa ce ita d'in zai aureta inkuma barabansa bane to yasa dangana haka Allah yaso, dama bakomi mutum yake samuba a rayuwa,
rayuwa sai da qalu bale dama.
Shiru yayi yana jinta baice komiba, amma sosai yake tunanin irin halin dazai shiga in yarasa Bahee d'insa.


Sai bayan la'asar Bahijja ta tashi daga barci, ruwa ta watsa sannan tagabatar da sallah.

Bakowa a parlour n sanda ta fito.
Dinning ta isa ta zauna ta zuba white rice da vegetable soup. Tana cikin ci adda Asma'u ta iso wurita ta ja jujera ta zauna ta dubeta cikin wasa tace "kasa sarkin barci, murmushi tayi tare sa cewa "kai adda A, nice d'in kasa? "Eh man, inba kasaba wazaizo sada zumunta ya hau barci.
"Uhmm adda A, bakisan gantalin da yaya Mujaheed ya sha dani bane yau kuma gashi nafito ina jin barci, shiyasa naji gajiya sosai. Kai ta jinjina tace lallai kunsha yawo kam, dole ku kwaso gajiya.


Sai bayan magriba Mujaheed yadawo ya d'auketa suka wuce.
Ahanya yatsaya wurin mai saida fruits yasaya suka qarasa gida.

Har qofar parlournsu yarakota, ya miqo mata ledar fruits d'in yana cewa "gashi kisha su qara nuna to tunda har yanzu da sauransu, fizgan ledar tayi tashige parlourn tana fad'in "kai dai Allah yayi maka sauqi.
"Amin ya amsa sannan yawuce ma mummy da nata ledar.

Suna kallo a parlour n mummy Sumayya ta miqo mata fox d'inta da wayoyinta, dafe goshi tayi ta furta "kashhh wallahi naman munyi da saraki zaizo kawomin su.
Sumy tace "aiko yazo bayan la'asar, yayi tajiran dawowanki har yamma, sannan yabani ya wuce, tacigaba amma fa yaji haushi sosai dabai same kiba, donma ban fad'a masa da yaya mujaheed kuka fitaba da qila sai yasamin kuka.
"Allah sarki masoyina, bari inkirashi inbashi hakuri "dayafi dai don nasan har yanzu bai huceba, cewar Sumy.



Kwanci tashi gashi har su Bahijja sun kusa kammala karatunsu.
Abba ya tsaida lakacin bikinsu nan da watanni biyu, wato lokacin sun kammala jarabawansu na qarshe da sati biyu.

Ranar da Abba yasanar da batun auren su Bahijja, Mujaheed sai da zazzabi ya kamashi amma bai bari kowa ya ganeba sabida juriya irin tasa.
Lallai Bahee tayimin nisa abinda yake fad'a aransa kenan.


Sosai ake shirin biki ta ko wanni fanni.
Ana saura wata d'aya biki gidan su Bilal suka kawo akwatinsu seats biyu masu kyau da tsada kuma komi na ciki abin yabawa ne, gaskiya sunyi qoqari ainun.

Itama Sumayya seats biyu Adda Asma'u tare da wasu cikin dangin umma suka kawo.
sabida adda Asma'u tace ita cikin dangin umma take, akayi tayi mata dariya.

Shima bara

Please Login or Register in order to submit comment