Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'yammatansa masu son sa da qaunarshi, buhu buhu. "Eh naji suyi tasan nasa man ina ruwana da mai qaton ciki kamar na mace mai cikin wata uku.
"Uhmm uhmm kishi kikeyi kenan? "Tir inyi kishin wani gani da sarakina d'an sardidi kuma d'n cas abinshi.
Sumy takama haba tana kallonta tana murmushi "eh kalleni da kyau yarinya, banason miji qato mai tumbi, nafison irin sarakina d'an dai dai yanda zai cillani sama ya cafe nima in cillashi, ya goyani ingoyashi, ke komi yayimin inrama mishi bawai inga miji girmansa na bani tsoroba musanman in dare yayi, barimma girma irin na ooo ai inajin matar shi a daren farkonsu sai ankaita hospital sabida yana danneta sai buzunta domin murus zai mata. Kyal kyal kayl!!!! Sumayya tasa dariya ta tsagaita ta dungurewa Bahijja kai tace "amma Adda B ke 'yar air ce, inbanda iskanci yaya Mujaheed ne kikewa wannn fatan. "Ai yacanci hakan ne, kidiba fa sai wani qara bajewa yakeyi kamar kud'in cizo, ga tsawo kamar lishsha, kai wallahi matarsa tana cikin matsala ooo.
"Uhmm Allah ya isheki cin fuskan hakanan to, kuma ai duk girmansa bai kai yaya Bashirba, "wannan kuma matsalarki ce tunda ke kikaga zaki iya dashi, nawa ido ai, amma dai zakisha boni, har kin bani tasusayi. Duka ta taska mata a cinya "Allah zakisani tam.
Tasa dariya "zadai kisani da qaton mijinki "eh d'in, ina son kayana hakanan "to Allah barku tare "Amin.

Sunan suna hiransu ta aminai, ayi fada ashirya har lokacin sallar tayi suka shiga ciki.
Tana zaune tana jan tasbi umma tashigo ta zauna gefen gado tana dubanta tayi saurin shafawa ta matso ta dafa qwaiwar umman tace "umma inayini? "Lafiya lau.
Shiru sukayi nawani lokaci sannan umma ta katse shirun takira sunarta "Bahijja, "na'am umma, "wai dagaske kun had'a kanku ke da Mujaheed? Kallon umma takeyi kamar bata santaba sai da taqara mai maita tambayar sannan ta sauke numfashi ahankali ta amsa "a'a.
"to yayi, yanzu kitashi kije Abbanku nasan magana dake, kuma inhar yanuna da ki amince da Mujaheed to ki amsa batare da musuba, sabida ni kaina nafisonki da Mujaheed akan wannan Bilal d'in. Tayi qasa da kanta tanajin wani daci aranta ga gabanta sai faduwa ya keyi. "Dafatan kinji abinda nace "eh umma naji, ta amsa muryanta narawa.
Umma ta tashi ta fice tabarta nan zaune kamar gari.
Tagumi tasa wani hawaye mai zafi yazubo mata tagoge da bayan hannunta sannan tamiqe tayi part din Abba.

Cikin sanyin jiki ta samu wuri ta zauna bayan ta gaishe da Abban. Batajima da zama ba Mujaheed yayi salma tare da shigowa. Abba ne ya amsa mishi, yasami gefen Bahijja ya zauna.
Kallonsa Bahijja tayi, ta gefen ido, suka hada idonu yasakar mata murmushi dasauri tasunkuyar da kai tana qara jin wani tuquqin hsushinsa aranta.

Gyaran muryan da Abba yayi yasa ta maida hankalinta wurinsa.
yakira sunarta "Bahijja....


*wannan shafin nakine Maryam Qaumi, Allah yabar so da qauna Amin.*


*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.
*22*
"Bahijja "na'am Abba.
Ya muskuta kad'an sannan yasoma cewa "yayanki Mujaheed yaxomin da magana akan kun had'a kanku sannan kin amince da ahada bikin tare danasu Bashir, shine nakiraki inji da bakinki, shin kun had'a kan naku ne ko ya-ya? Tayi shiru kanta sunkuye tana wasa da yatsun hannunta. Tsawon wani lokaci taqi cewa komi.
Abba ya dubeta cikin kulawa yace "Bahijja kada kiji komi kifad'amin gaskiyan zuciyar, bazan miki auren doleba, domin ke amana tace sabida haka abinda kikeso shinakeso illah iyaka inbiki da fatan alkhairi.
Har yasa aya batace komi, yace matsonan Bahijja ta miqe ta isa kusa dashi ta zauna ya dora hannunsa bisa kanta yace "shirunki yanuna alamun amincewa kenan ko? Ta girgiza "to fad'amin abinda keranki kinji. Ahankali tasoma magana "Abban Allah ni bamuyi wani magana dashiba kuma ni ai da yaya Bilal mukayi alqawarin aure, taqara qasa da murya tace "Abba don Allah kayi haquri baqin jininka nakeyi ba ta kallo Mujaheed " kaima don Allah kayi haquri. Wani kallo yawatsa mata ta kauda kanta tana kallon Abba cikin fuskan tausayi. "Bakomi Bahijja, bakiyimin komiba, Allah yayi miki albarka ya tsareki ga duk abin qi arayuwarki "Amin ta amsa tana murmushi jin dad'i.
"Tashi kitafi abinki, Abba ya umurceta, tafice da sauri tana hardewa sakamakon mugun kallon da mujaheed ke watsa mata.

"Kai kuma bani hankalinka nan, maganar Abba yadawo dashi kogin tunnin dayagad'a.
Motsa yatsunsa yayi sukayi qara yana duban Abba fuskansa ba walwala, kamar qadan gare ya kada kansa alamar yana tare da shi.
"Ina son kacire ranka akan Bahijja, kanemi wata sabida tana da zabinta kuma ni bazan tursasata tasoka doleba, innayi haka nazamo azzalumi don haka nace umurtanka daka janye qudurinka kanemi wata insha Allah kans tare da nasara. "To Abba nagode Allah yaqara girma "Amin Allah yayi maka albarka "Amin Abba.

Daganan suka soma hiran business din Abba tare da magnar gina wani company na sarrafa abincin yara dakesonyi, har Bashir yashigo shima yasoma bada nashi shawaran akan abin.


*********** "Mama wallahi Allah nagaji da abinda hamma Bilal keyimin sai kuma tafashe da kuka mai tsanani.
"Munirat!! Maman ta kirata cikin bud'e murya bata amsaba sai dai ta tsagaita da kukan tana sauraron uwarta ta, ganin haka yasa tacigaba "wallahi Allah indai ni hajiya yalwa mace ta haifeni sai kin auri Bilal kuma ke d'aya zaki zauna tare dashi har abadan abidina. Da hanzari Munirat ta dubi maman idanu waje tace "mama zaki iya hanashi auren Bahijja ce? "A'a baruwana da wata Bahijja can, kuma bazan hanasa aureba amma zai soki kamar ransa kuma zai aureki dolensa sannan ke kadai zaki mallake shi, bazan bari kizauna da kishiya ba kamar yadda nake ni d'aya to kema doke kizamo kedaya awurin mijinki.
Ta zubawa maman ido, zuciyanta namata d'aci tace "Uhmm mama don Allah don Annabi SAW kada ki shiga malamai da 'yan tsubbu domin nemomin so wurin hamma Bilala. Harara ta watsa mata tace "sai kiyi kuma amma wallahi duk inda zanshiga sai nashiga naga kin auri Bilal. Cikin bata fuska Munirat tace "wallahi nahaqura dashi tunda ya fadamin yana da zabinsa kuma bazai iya yimata kishiya, to nayanke shawara zan fidda d'aya daga cikin masu sona in aura domin hakan zaifimin kwanciyar hankali akan na auri wanda baya yi dani sai don tursasawa.
"Wayace miki tursasashi za ayi? To kisani da kanshi zai tako yace yana buqatar aurenki ido rufe "kai mama ana ga Annabi kina runtse ido, nifa bansonki da yawon bin malaman nan ne cikin fushi tace "to uwata!!! Sai nabi inkin isa ki hanani, wawiyya kawai gabuwa!! Munirat ta miqe cikin fushi tafice tana cewa wallahi indon ni zaki fad'a halaka to kisha zamanki, bana son hamma Bilal yanzu kuma baba nadawowa zan fad'a mishi zabina.
Mama yalwa tabita da wani mugun harara tace "zanci qaniyarki kuwa dagake har uban naki. Ta figa gyale tare da daukan key din motarta tafice a fusace tana cewa da zafi zafi ake bugun dutse, bari insoma cin uban wanan mai dogon wuyan tukunna kafin indawo kanki 'yar banzan yarinya shasha kawai.
Munirat tanajin tashin motar mahaifiyarta wasu hawaye masu radadi yazubo mata ta share da bayan hannunta, ta daga hannayenta sama tace "Allah yashrya mahaifiyata hanyar gaskiya ka nesanta zuciyar ga bin aikin ashsha, yasa tagane gaskiya, ta amsa Amin.
Kwantawa tayi bisa bed dinta tare da dafe kanta dake barazanar rabewa biyu sabida tsnanin ciwon dake mata.


***** Bahijja tun lokacin tasoma wasan buya da Mujaheed. Taqi barin ko hanya yahadasu sam data hangoshi zata arce da gudu, ganin haka yasa ya maida part dinsu wurin yin break dinsa da kuma dinner, yasan duk tsiyanta tabari su hadu kuma haqiqanin gaskiya yakasa cire sonta aranshi duk da nasihan da Abba tare da Sumayya suke masa na yahaqura da ita, shiko Bashir cewa yayi ya sauke isa da gadara yanemi so da qauna awurinta zaifi masa, jinsa kawai yayi amma yana ganin zubda ajine ya soma lallamin qanwarsa wai ta soshi.

Da sanyin safiyar littini Mujaheed yashigo part din umma, dinning ya nufa yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa.
Tea yahada yasoma kurba ahankali.
Tsam yayi yana sauraron motsin da akeyi a cikin kitchen, sai yasami kanshi da Allah yasa Bahijja ce ke ciki.
Yana shirin tashi ya bar wurin domin sauri yakeyi yana da operation qarfe tara na safe. tafito hannunta dauke da plate, indomie ke cikinsa sai tururi yakeyi tare da tashin qamshi.

Bata lura da mutum a tsayeba sabida kanta na kallon plate din,
tana motsa shi don yayi saurin hucewa.
Shiko dake aikin kallonta ya runtse idanunsa cike da jin tashin tsigan jiki.
Donmin sanye take cikin night wear wacce tabi jikinta ta lafe sannan tsayinta ta wuce gwaiwanta da kad'an, gashinta sanye cikin net. Yaja ajiyar zuciya mai qarfi, da hazari ta d'ago kanta tare da miqewa tana neman hanyar gudu yayi saurin yin bake bake a hanyar dazatabi yana qarewa surarta kallo yace "kingama gudun? Tayi baya tana hararanshi tare da kare qirjinta da hannayenta, murmushi ya saki mai sauti sannan ya matso kamar zai rungumeta ta zaro idanu waje.


*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.
*23*
Ta jabaya yamatso ta goce tana son gudu yayi saurin tareta ya kafeta da idanu, cikin fad'a tasoma cewa "kaga jaheed kakiyayeni, kafita hanyata baruwaka dani banason abinda kakemin. Yana murmushi ya jijjiga kai yace "to minayi miki kuma? Harara ta auna masa ta juya mishi baya ya sa hannusa ya juyo da ita yayi mata rumfa, yarufeta ruf yadda bamai iya hangota sai ya kauce.
Sai taga duk yakoma mata wani qato dama gashi masha Allah.
Jikinta yasoma rawa, taqara qamqame hannayenta abisa qirjinta, idanu waje tace "wai mikake nufine? Dazaka sakani a tsakiyarka kana wani nunamin girmanka, to nagani sai kasami bani hanya in wuce ko, domin ina da abinyi.
Sosa kansa yayi yana qarewa bakinta kallo, ta qara turushi tare da murgud'ashi.
Ya cire hannayen da ta kare qirjinta dasu ya dagasu sama ya riqe da hannunsa na hagu, yazubawa boobs dinta ido quri. Qafafunta tasoma bugawa irin na shagwaba tana cewa "wallahi sai na hadaka da mummy ince iskanci kakemin.
Mujaheed ya susuce ya shagala sakamakon motsin data keyi yasa boobs dinta rawa kad'an. Bai san sadda ya kai hannunsa wurinsuba ya latsa da qarfi tasaki 'yar qara ta fincike jikinta ta zille tabi gefensa ta arce da gudu, asabule yabi bayanta da kallo yanajin wani yanayi ajikinsa.
cikin sanyin jiki ya sunkuya yad'auki wayoyinsa wanda suke zube bisa table, yafice.

Yad'au kimanin mintoci goma yana zaune a cikin motar batare da ya kunna ta ba, zucan yasaki ajiyar zuciya afili ya furta "wallahi bazan haqura dakeba Bahijja, don inaji ajikina ked'in tawace, sabida haka jan gwada lallaminki har sai na samo kanki, kin soma sona fiye da wanda kikewa wannan d'an zuqalallen d'an fillon, mai kama da sandar kiwon shanu.

Ita kuwa Bahijja dakinta tashige har da murza key wai koda yabiyo bayanta.
Jikin qofar ta jingina tana maida numfashi zuwa can tasoma bin qirjinta da kallo tayi gaggawan runtse ido ta dafe kanta "ya salam!! Tafurta, ta matsa jikin mirror tana qara kallon jikinta, ta kwabe fuska kamar zatayi kuka tace "yanzu ahaka nake dama? Tayiwa kanta tambaya, ta amsa abinta "ah gaskiya man mai qaton cikin can yayi qoqarin tabamin kayan ruwa, wannan arha haka; takama haba "yo yaga banza ta gad'i.
taqarasa tana wani had'erai. Taja siririn tsaki "kuma banyafe ba ehe, Allah ya isa mai qaton cikin banza kawai, ta figa towel dinta ta fada toilet a fusace.

Sanda tafito bakowa a parlour don haka sai tashige bedroom din umma bakinta dauke da sallama, umma ta amsa mata tana duban agogo tace "na d'auka ai kinfita tun dazun, "a'a ina nan, yanzu dai zan wuce, ina da aji qarfe 11am gashi yanzu 10:25am "eh lallai lokaci yakusa kam, saiki hanzarta ki isa akan lokaci "tam umma sai nadawo "adawo lafiya "Amin.
Ta leqa part din mummy a gurguje ta fito tashiga motarsu tafice da gudu.
Tana gyara parking a harabar makarantar ta hago fitowar Sumayya daga lecture, da hanzari ta kulle motar ta isa kusa da Sumayya "sis harkin fito? kinhuta abinki.
cikin 'yar dariya ta amsa "eh wallahi, yanxu haka gida zan wuce, cikina naji na kiran ciroma, hararan wasa ta sakar mata tare da cillah mata key tana cewa "dalla acici kawai danjin gara, ta cafe tana amsa wa "eh din anyi cin, lafiya ne ai ke kawo hakan tayi gaba tana fadin "To Allah qaremu da lafiya "Amin ya rabbi Sumy ta amsa.

Koda tafito lecture wanda ya dauketa awannin biyu cur.
tasami Sumy zaune cikin mota tana jiranta, murmushi ta saki cikin jin dadi tace "kai sis sannu kinji Allah yabiyaki da Alkhairi, yakuma barki da yaya Bashir har zuwa qarshen numfashinku "Amin ya rabbi kayan saraki mai wu...... sai kuma tasa dariya itama Bahijjan dariyan tasa tana fadin"Allah shiryaki Sumy kibar jan fad'a.

Suna hanyar dawowa kiran Bilal ya shigo ta dauka tare da lafewa a site,cikin muryan jan hakali tace "amincin Allah ya tabbata agareka hubbyna, taji jim tana saurarenshi zuwa can ta kyalkyale da dariya tasa hannuta daya tarufe fuskanta,
tana girgiza kai "a'a wallahi a'a nace abinda take fada kenan sannan tacigaba "Allah saraki inkanamin irin wannan zancen zanyi ma yajin d'aukan waya tam.
Sumy ta kalleta ta tabe baki tacigaba da tuqinta. "Ok Allah yakawoka lafiya ta datse kiran tanabin wayar da kallo sai kuma ta sunbaci wayar tare da sakin wani qayataccen murmushi. "uhmm soyayya manja Sumy tace duka Bahijja ta dalla mata acinya agigice tasaki qara ta hade rai "kinga bana son wasa da rayuwa fa Add B.
Kinaga nin dai akan titi muke, kada kijawa yaya Bash asarata. "oh shikadai za ajawa asara kenan? "eh man sabida ke inkin wuce barzahu mai dogon wuya yana da wata safire.
"bala'i!!! Kece safire n kowa? Sumy cike da dariya ta amsa Munirat dai, ni ai sai d'an dama dama bawan Allah kuma jarumi Bashir!! Ta fad'a da qarfi. Bahijja tayi saurin toshe kunninta tana hararanta, dariya ta saki tare da buga staring motar, cike da tsokana tace "wai wai waii!!! Munirta da Bahijja a gida yad'a cashesu kenan ooo.
wani uban tsaki taja ta juya kanta tana kallon titi "kici gaba damin wulaqnci Sumy lokacin kine. Tace.

"Kai sarkin fushi wasa nake miki, banza tayi da ita har suka isa gida taqi kula Sumayya duk da kuwa janta da hiran datake tayi.
Tana yin parking Bahijja tafice fuww, tagumi Sumy tayi tana jinjina wannan irin kishi na Bahijja. Ahankali tace "ya Allah ta bawa baiwarka Bahijja sauqin wannn irin kishin.

Dala'asar sakaliya Bilal ya iso, tayi masa masauki a wurin shaqatawan dake kusa da parking space. Tacika mishi gaba da kayan maqulashe da kuma yankakkun fruits masu sanyi.
Suna hira yana shan fruits ahankali.
Fuskokinsu dauke da fara'a alamar hiran tana musu dad'i. "Sweetie in munyi aure irin dambun meat dinnan zaki riqayimin ta murmusa ta kara mishi glass cup "nayi maka waigi.
yana sosa sumar kansa mai yawan cika yace "Allah princess ba santi bane, yayi dadi ne sosai kamar sabuwar amarya "ya ilahi!! Tace da hanzari ta rufe fuskanta dariya yasaki mai sauti yana tafa hannayensa "uhmm queen sarkin jin kunya, to bude idon nadaina baki kunya, ta bude tana hararansa, "natuba madam yace yana kama kunnensa murmushi tayi tare da kad'a kai.
Sai daf da magriba suka tashi, yana shirin bude mazaunin driver phone dinsa tayi tsuwwa ya jingina jikin motar yana kallon Bahijja.

"Ok to mama Allah yabaki lafiya, insha Allahu zanshigo cikin satin nan indubaki
Aha sai anjuma agaidanin da Abba. Ya maida wayar cikin ajjihunsa.
ya maido hankalinsa kan Bahijja wacce ta harde hannayenta a qirjinta tana kallonsa.
murmusawa yayi yace "queen maman Munirat ce bata da lafiya shine takirani take fadamin, tad'an saki fuska "ayya Allah yabata sauqi "Amin sweetie. "Inkaje wurinnata ka kirani mugaisa inmata jaje "ok sweetie insha Allah zankiraki kuwa.

Suna d'agawa juna hannu yafice a get din.


***** Agefen mamaYalwa kuwa tana ajiye wayar tace "shegen sama mai kama da zabiya zakaci ubanka, lafiyata lau zandai soma d'ura maka sirkullen malam bukar ne wanda zaka gigice akan Munirat kayi watsi da wata Bahijja can.





*Mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.
*24*
Yau hutun qarshen mako wata asabar.
Bahijja da Sumayya gidan Adda Asma'u suka tafi yini, tayi murnan ganinsu dama zaman kadaici ya dameta, mijinta yayi tafiya yara kuma sun tafi gidan kakarsu mahaifiyar dadynsu, sai duk tajj gidan yayi mata girma, ganinsu Bahijja murna ya isheta tarasa ina zata sakasu, nan danan tacika musu gaba da kayan maqulashe.

Bayan sun huta akasoma hiran yaushe gamo. " 'yanmata adon gari, ya Abba da su mummy? Atare suka amsa "suna lpylau, sunce agasheki "ina amsa.
lokacin yin girkin rana nayi, Adda Asma'u tajasu suka shiga kitchen had'a lunch.
Suna aikinsu suna hira, zuwa can tadubesu tace "yau she Abba zai aurad daku? Sukayi shiru wannan ya kalli wanan, wannan ya kalli wannan, sai kallon kallo sukeyi tamkar wasu zakaru masu shirin yin fad'a.
Dariya Adda Asma'u tasa masu ta nunasu da yatsa "anrasa mai bani amsa kenan? dakuke wani kallon kallo atsakaninku, sai kace marasa gaskiya.
"Uhmmm Adda kunya mukaji "Dallah ja can gefe, kedince kike da kunya dawani idonki a tsakarka, cikin jin haushi Sumy ta doki kafad'an Bahee tana cewa "Allah Adda B nafiki kunya ko makaho ya shafa zai gano hakan, bahijja ta tareta da sauri "aiko dana rako mata duniya indai kika fini kunya, "ai kuwa kinko rakosu d'in, sabida rashin ta idonki ko 'yar akuyan kasu albarka "kutcy!! Nidin Sis? Tayi banza da ita, tamaida hanklin ta wurin motsa stew.

Bahijja cikin jin haushi ta kai hannunta ta dallama qyeyar Sumayya duka
"almuna hun hun kawai, ta san bata da gaskiya tayi tsit da mouth dinta.
Tajuyo tana hararanta tare da gyada kai "Add B zansoma hadaki da habibina ya hukunta minki ko gyagane nidin yayarki ce, " koba yaya baaa. Sai kuma tayi saurin cewa "Adda kingano mai kunya yanzu ko a tsakanin mu? Tunda gatanan daga abu ta sako qaton saurayinta ciki ko kunyar ganin kina wurin batayiba.
"Qato hammatarki 'yar rainin hankali kawai, Sumy tace tana hararan Bahijja. "Oho dai nace qato kamar tifa. "Ai sai kiyi tayi matar mai wuya kamar murqin lema kawai "Adda kinji iskancin da Sumy kemin ko?
Ita dai Adda Asma'u sai dariya take musu ganin abu kadan sun maidashi babba.

"To ya isa hakanan muhawaran 'yanmatan mummy da umma, tace dasu. Dukkansu sukayi shiru tare da maida hankali gurin aikin dasu keyi.

Suna cikin cin abimci suka tsinkayi sautin muryan Mujaheed yana sallama a bakin parlour.

Ko kafin Bahee ta jawo doguwan riganta har yashigo, ta daka tsale ta buya bayan Adda Asma'u. Suka sama mata dariya suna amsa sallamarsa

Sarai yaga abinda tayi amma sai yashare, yasami wuri yazauna yana gaida Adda Asma'u ta amsa cikn fara'a.
Sumy ta gaidashi ya amsa yana leqen fuskan Bahijja yace "ke fitonan inji dalilin dayasa kike guduna ko yanzu insaba miki. Tayi quri tana kallonsa. ya miqe yayo kanta ta kwalla qara tare da qanqamewa jikin Adda Asma'u.
Yakai hannu zai kamota Adda Asma'u tabuge hannunsa tace "Au agaban nawa zaka bugeta don rashin ta ido? "A'a Adda A, kawai tambayarta zanyi, "riqe tambayar taka can tunda ita ba 'yar jarida bace.
kwata yayi yakoma ya sami wuri ya zauna.
Sumy ta zubashi abinci yasoma ci yana gyada kai alamar abinci yayi dad'i.
"Ke Bahee zo kibani ruwa mai sanyi "Sumy don Allah ki dauko mishi "ke zakibani ba itaba, ko kinfini idon ganinta ne?
Tura baki tayi, ta marairaice fuska tana kollon Adda Asma'u. Adda takauda fuska tace "tashi kid'auko masa tunda naki yakeso.
"Adda baxan iya tashi ahakaba ai. Dukansu idanunsu yayo kanta, sai alokacin su suka gano boyon datakeyi abayan Adda Asma'u.
Half best ce a jikinta tare da dogon wando amma roba kuma yakamata tsam.
Tacire doguwan rigar shaddan da tasanyo, wai zafi ya isheta kuma bata, taba tunanin zuwan Mujaheed gidanba a wannan lokacin.

*Mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*

*25*
"Sumayya miqo mata riganta ta sanya, Adda Asma'u ta bama Sumy umurni.
Da sauri ta xura rigan ta sunkuya gaban Adda tace "Adda A, kice yabar kallona, kunninta ta kama ta murd'a da qarfi tare da cewa "anqi aced'in, "wayyo Adda A, zakijimin rauni fa, wash Allah da zafi, yaya jaheed ce tasa kin min kunni don Allah yasa dariya yace "sai kin cireshi duk Adda A, maganin mai rashin kunya kenan, harara Adda ta watsa mishi tare da sakin kunnin tace "amma kai babban kwabone shi yasa ta rainaka sosai tsinin hancinsa yasosa yana murmushi batare da yace komiba.

Cikin fushi Bahijja ta tashi tashige bedroom Sumy tabi bayanta.
Ganin haka Mujaheed yatashi da kansa ya d'auko ruwan roba mai sanyi sosai yazuba a cup yasha.
Bayan ya dire cup d'in ya murkuta yanatsu tare da maida hankalinsa kan Adda Asma'u.
"Wallahi Adda A, narasa yadda zanyi yarinyan can tafahimci ina tsananin sonta tare da kaunarta. "Wacce yarinya ba? "Bahijja man adda, "au wai sonta kakeyi nan? "Eh wallahi, so mai yawa "uhmm lallai kana da aiki, "nami? "Nakomi ma d'an uwa, sabida kayi sake ta rainaka sannan wani yarigaka kafa gwafnatinsa azuciyanta.
Shiru yayi zuwa can yace "nasan da haka Adda, yanxu to miye mafita? domin ina son in mallaketa tazamo abokiyar rayuwata na har abada.
Tagumi tazuba tana kallonsa cike da tausayi tace "mafita d'aya ne kadaure kanemi so awurinta zaifi maka ko kafadawa Abba buqatarka" uhmm adda Bahijja ta wuce tunaninki domin kafiya ne da ita kamar me,
nasan baza ta saurareniba sabida nagwada sanar da ita tanuna a'a bata sona dalilin dayasa na fadawa Abba kenan, ya kira ta tabbatar masa da bani gabanta kuma ni inajin kunyar tunkaran umma da zancen.
"Tirqashi!! "To indai hakane abinda yafi ka haqura da ita "no!! Adda A, bazan iya hakuraba Allah, kidai nemonin mafita. Shiru tayi na wani lokaci tana tunani zuwa can tace "to kasauke isa da girman kai ka russuna kanemi soyayyarta "kamar ya adda? "Good bros, kasoma kula da lamarinta kamar kaita school da daukota ko kaimata ziyara acan da kuma fita da ita wuraren shaqatawa, daganan kayi qoqarin samo zuciyarta.
"Zan jaraba hakan adda, nagode Allah bar zumunci "Amin ta amsa.


****** da yammacin ranar alhamis Bilal ya isa gidan su Munirat domin gaishe da mamanta da jiki kamar yadda ta fad'a.

Suna zaune a parlaur dukkansu mutanen gidan yayi sallama ya shigo.
Mama yalwa tarud'e domin batayi zaton zuwansa ranarba, data had'a mishi drink ko dafa mishi abinci da maganin.
Tayi nisa cikin tunani tajiyo yana gaisheta adan da burce ta amsa

Please Login or Register in order to submit comment