Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

kallah masha Allah, komi yayi ba qarya.

Mummy da umma anrasa wayafi qoqari wurin kyara amaren domin kowa yana bakin qoqarinshi, sunfi maida hankali wurin gyara masu fata sosai fiye da ni'imarsu sabida suna gudun kada yayi musu illah duk da dai sai sun tabbatar da inganci abu sannan suke basu.
Fruits dai sun shasu har sun gode Allah.

Rugun tsumi!! rugun tsumi!! Yazo domin saura kwana tara asha shagali.

Suna zaune d'akin Sumayya.
Bahijja ta ja tsaki tace "wallahi sis Sumy ruwannan dake batamin jiki watarana yasoma isata, dariya Sumy tayi sannan tace "wallahi haka nima "ni kam banqara shan komi daga yanzu "nikam sha zanyi abina inmore, ko na gigita yaya, duka ta kawo mata ta goce tana dariya.
"Jarabbau kawai "eh d'in munji, qilama sarakinki sai yafi, fitina domin ance siraran maza basu da sauqi a bed, "inji qaryanki ba.

Kiran wayar Mujaheed yashigo cikin wayarta tana d'auka taji yace "komi kikeyi kizo yanxu kisameni a d'akina, yana gama fad'a ya kashe.

Shiru tayi tana kallon agogo qarfe biyar dai dai na marece.
Gabanta nafad'i tamiqe tafice ta qofar baya tanufi part d'insu,
sabida gidan yasoma cika da baqi musanman wad'anda suke nesa sunsoma isowa.

*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.
*32*

Koda ta isa qofar d'akin nasa sai taja ta tsaya tayi shiru zuwacan ta murd'a handle d'in ta jita bud'e sai kawai ta tura ta shiga, falon tsit kamar ba mutum ciki, ta zauna bisa hannun kujeran da ke parlorn.

Wayansa ta kira amma bai d'aukaba ta kuma kira akaro nabiyu nanma bai d'agaba, tayi shiru tana 'yan dube dube kamar mai son gano wani abu.

Ta d'auki aqalla mintoci shabiyar tana jiran fitowar Mujaheed amma batakoji motsinsaba.

Asannu ta miqe ta isa bakin bedroom d'insa ta tura qofar ahankali ta shiga gabanta na fad'uwa domin tunda take bata taba shiga bedroom d'insa koda kuwa gyaran d'akin ta rako Sumy zatayi, iyakacinta parlor n take tsayawa.

Wani sansanyar qamshine ya ziyarci qofofin hancinta ta lumshe idanu tana shaqa, tsaf tsaf abinsa kamar dakin mace mai mugun tsafta da kwalisa, ta qarasa tsakiyar d'akin ta tsaya shiru sai kuma ta matsa ta zauna gefen bed d'in ta tsurawa wani frame ido.
Itace jikin frame d'in tana sanye da wando black tare da riga mai dogon hannu amma ta matseta sosai, na shanunnan sun turo kamar zasu faso gaban rigan.
Kauda fuska tayi tana tunanin yaushe tayi wannan pic din kuma?
Ganin batasamo amsaba ta maido fuskanta bangon arewa nanma tayi arba da photonsu ita da shi wanda sukayi ranar da tarakashi yiwa budurwanshi siyayya.
Suna murmushi dukkansu, kuma sunyi kyau sosai.
Ikon Allah ta furta cikin zuciyarta, wai yana nufin duk son dakemin ne yakawo har yake ajiye pictures d'ina haka ko mi?

Tamiqe zata bar d'akin taji anbude qofar toilet ta dakata tare da juyowa.

Shine yafito d'aure da towel a qugunsa wani qarami kuma ahannunsa yana goge sumarsa.
tsura mishi ido tayi tana kallonshi.
Fari sol dashi saima take ganin jikinsa har yafi fuskansa fari gashi Ma'abocin fad'in qirji da wadataccen suma sun kwanta luf luf kamar yana shafa musu mai, ta sauke idanunta zuwa qasan cibiyarsa abinda tagani yasa tayi saurin juya baya ta runtse ido gam tanajin zuciyarta tana bugawa fat!! fat!!.

Gashi tanagi siriri ya miqe har cikin maransa🙊 yasata juyawa bashiri gudun kada tayi gamo

"Kingama kallacemin tsiraicin ko sai na kwance miki towel d'in kingama gani da kyau?

Ta tsinkayi muryansa yana tambayarta.
Da sauri ta juyo tana zare idanu, ya matso daf da ita yace "oya tube kema inga irintaki halittan, ko yakai nawa tsari da burgewa.

cike da tsoro ta jabaya tafice da gudu, daga can ya bud'e murya sosai yace "kijirani inzo, matsoraciya kawai.

Dariya tasa tana kare fuskanta kamar naganinta wai taji kunya, ahankali kuma ta furta "wallahi yana da bantso kam.

Bai d'auki lokaciba ya fito cikin shigar qananar kaya.

Ya zauna ahannun kujeran datake zaune ya sunkuyo jikinta ta d'ago ta kalleshi zatayi magana yayi sauri ya haska musu plash da wayarsa ta harareshi tare da tura baki nanma ya qara haskasu, ta miqe tana mishi wani kallo yaqara saurin d'aukanta, haushi ya quleta ta juya ta doshi qofar fita yayi saurin shan gabanta ya murza key a qofar tare da zarewa.

Kallon kallo suka soma, tayi qasa da kanta ya jawo hannunta ya zaunar da ita abisa kujera mai cin mutum biyu.

Ahankali ya kira sunarta "Bahijja tayi shiru tsigan jikinta yatashi yarrrr sakamakon yadda ya kira sunarta cikin wani irin siga.
Jintaqi amsawa yasake kiranta, batare da ta d'agoba ta amsa "na'am, jan nunfashi yayi ahankaki yaja hannunta zuwa samar qirjinsa ya d'ora, da qarfi takejin bugun zuciyarsa ta zame hannunta tare da d'aqowa tana kallonsa, idanunsa lumshe,
kurama sajensa ido tayi tana ayyana shi da Bilal wayafi iya gyaran fuska oho.

Bud'e idanunsa yayi ya sauke bisa nata tayi saurin kauda nata gefe tana murmushi, shima murmushin yayi ya matse hannunta cikin nasa yace "muna buqatar zama a inuwa daya sweet bahee amma kinkasa ganewa don tsaban son zuciya irintaki,
wanda narasa gano mikike mufi da aikata hakan.
Ido cikin ido tace "yaushe nace maka ina ina son zama inuwa d'aya dakai?
Ya amsa "Kin dad'e da fad'a ai "uhmm yaya jaheed banson qage nidai, nasan bakina baitaba kuskuren kiranka masoyiba balle inyi tunanin zama inuwarka "eh bakinki bai fad'aba amma jikinki da kwayar idanuwan sun sanarmin da haka.
zabura kad'an tayi tana hararansa tace.
"aisai ka fadamin wani abu sukayi da yanuna hakan.
Saida ya mannawa hannunta kiss tayi saurin janyewa tana yamutsa fuska yasaki murmushi mai sauti sannan yace "kallonki gareni ta dabance diba can ga misali yanuna mata wani picture nasu dasukayi tana tsaye yana bayanta ta d'an juyo tana kallonsa wanda kowa yagani tabbas zaid'auka kallo ne mai dauke da tsantsarso tare da qauna, shi kuma yana dubanta yana murmushi.

Ta yamutsa fuska tace "bai zama hujjaba wannan tunda nasan hararanka nayi ai.
sosa kansa yayi tare da cije lebensa na qasa yace "to naji, amma miyasa kike son nariqa tabamiki jiki da kuma son ganina ako da yaushe?

Tamiqe tsaye da hanzari taja baya kana jifanshi da wani kallo, ta nuna qirjinta tace "nidince nake son kana tabaminjiki da son ganinka kullum? Ya gyad'a mata kai yana dariya.
Jikitayi kamar ta rufeshi da duka don bakin ciki.

Bisa mamakinsa sai gani yayi ta rushe mishi da kuka, hawaye rashe rashe.
Balance yayi yana kallonta cike d sha'awa, dama ace matarsa ce dashi kad'ai yasan yadda zai rarrasheta.
Ita kuwa ganin yana murmushi sai taji wani malolon baqin ciki yataso mata ya turnuqe mata zuciya,
waima itace take son ataba mata jiki taf!. Lallai jaheed yagama da ita kam.

Tasowa yayi ya iso gareta ya kai hannunsa bisa kafad'anta ya dafata ta ture hannunsa da sauri yaqara maida hannunnasa bisa kafad'an nata takuma turewa ta nunashi da yatsa muryanta na rawa tace "wallahi jaheed inhar nace banyafemaka akan qazafin da kayimin, to Allah bazai barka ba domin saiyabimin hakkina nayimin sharrin da kayi.

Fizgota yayi da qarfi ta fad'a qirjinsa bashiri ya maida hannayensa ya matseta sosai, tasoma son kwacewa ta kasa, sai kawai taqara sakin kuka, cikin kukan take cewa "nagode jaheed da kakirani mara kamunkai,mara tarbiyya, nagode sosai taja hanci tacigaba "kasakeni intafi hakan, nace kasakeni ko!! tafad'a cikin tsawa, yaqi ko motsi saima qara qamqameta da yayi, "wai mikake nufi dani ne? Koso kake kakuma cewa dani wataraana nakawo maka kaina har d'akinka ko mi?

Cikin rawar murya taji yana cewa "affuwan Bahijja, banufina kenan ba, Allah wasa nake miki don nasan ni shaidane akanki na natsuwanki da tarbiyanki, please Bahee kiyafemin don Allah, yayi shiru yana shafa kanta sannan yacigaba "nine nake son jinki ajikina kuma bana sukuni inhar ban saki a idanuna ba sannan ruhina akullum begenki takeyi.
don Allah don girman zatinsa Bahijja ki amince da ni amatsayin mijinki.

Bugun qirjinta ya qaru fiye da da, ta zame ta zauna bisa carpet ya biyota shima ya zauna agabanta kamar zai shige cikinta.

Fuska ta kauda tanajin wani abu aranta wanda tarasa gano komeye shi.
Cinyarta ya dafa ta kalle shi yayi murmushin qarfin hali yace "yadai kin amince intashi yanxu muje gurin Abban?
Ta girgiza kai yabata fuska,ta cire hannunsa bisa cinyarta ta dubeshi fuska a marai raice tace "intambayeka man "inajinki ya amsa, ta sosa tsinin hancinta sannn tace "shin yazakaji sanda budurwanka dakuke son juna har iyaye sun shiga zancen aqarshema saura kwana hud'u a d'aura muku aure sai kawai kwatsam kasami sakonta akan bazata aureka ba waninka zata aura?
Yayi shiru yana dubanta, tayi murmushi answer me, ina jinka.
Ya kauda fuska yasoma magana cikin kaushi "bazanji dad'i ba, gaskiya kuma zan kirata mayaudariya sannan macuciya kuma bazan taba yafe mataba har abada.

Jinjina tayi masa tace "very good yaya jaheed, kabawa kanka amsan tambayar dakayimin, don haka inhar na amincewa aurenka ayanzu to bamakawa dukkan sunayen da ka kissafo zai tabbata akaina,
dawannan zancen nakeson mukawo qarshen batun in aureka please.

Shiru yayi yana kallonta sannan ya matsa jikinta ya rungumeta tana son kwacewa yace "don Allah kibarni inji d'uminki sannan ki amince inyi kissing d'inki ko da na mintoci biyar ne, ta yi masa shiru yacigaba"nasan kinmin nisa na har a bada, domin kinfini hujja mai qarfi kuma nagamsu dashi dari bisa dari, zanbarki Bahijja batare da son raina ba, Allah zanbarki sweet Bahee!! Bahee zan barki!! Amma kisani ina sonki da qaunarki bazan taba mantawa dakeba.

Kanta tad'ago ta kalli fuskansa taga idanunsa kulle yana motsa baki atake taji tausayinsa ya kamata kuma akaro na farko arayuwarta taji tausayinsa tun tsawon zaman su tare da juna.

Saukan bakinsa taji a wuyanta tare da sanyin saukan harshensa duk a lokaci d'aya, yasa ta dubeshi da hanzari, ya janye jikinsa daga nata ya kwantar da ita bisa carpet d'in sosai yasoma lasan kuncin ta juwa bakinta ta miqe da qarfi ta zauna ta juya masa baya tasoma magaa ahankali "yaya jaheed dama kirana kayi ka batamin rayuwa ko kuwa so kake ka kwashewa jikina karamarsa?
Bai san sadda yasa dariyaba jin qarshen zancenta.
ya girgiza kai "ko d'aya ba haka bane "miye dalilin kiran nawa? "Ok jirani, ya miqe tare da shigewa bedroom.
Yabarta cikin saqe saqen ko dawani salon zai fito yanzu kuma oho.
'Dauke da wani dan box mai kyau sai kyal kyali yakeyi yaqaraso wurinta ya zauna tare da bud'ewa ta leqa tana son ganin mike cikinsa.

*Ya Allah kabawa mamanmu lafiya cikin ni'imarka tare da amincinka domin Alfarmar manzon Allah S.A.W. Amin.*

Muna baran addu'o,inku 'yan uwa.

*33 to 34*

Idanunta yasauka bisa wani seat d'in sarqan gold mai kyau ainun, tad'ago tana kallonsa tare dayi masa signer da ido don neman qarin bayani.
Sai da ya shafa sajensa sannan ya sa hannu ya d'auko ya d'ora mata atsakiyar hannunta yasoma magana "Bahijja wannan sarqan takice na sayeta nasa akamin working aka rubuta *MB* ma'ana Mujaheed $ Bahijja.
Yayi shiru yana duban yanayinta sannan yacigaba "burina akan sarqan itace duk ranar da mukayi aure aka kawomin ke gidana to washe garin ranar zan sanya miki domin nasan zakisani a farin ciki sosai.
Shiru tayi tana saurarensa zuciyarta na bugawa da qarfi kuma tarasa dalilin dayasa zuciyarta ke yawan bugawa yau haka.
"Swett Bahee, ta tsinkayi yana kiran sunarta tare da zamewa ya kwanta acinyarta ya d'ago idanuna yana kallonta wani abu taji acikin ranta mai tsini ya soki ruhinta tayi gaggawan sunkuyar da kanta qasa.
Yakuma kiranta "my Bahee ta amsa can qasan maqoshi "na'am yasaki murmushi mai sauti yace "dalilin kiranki shine in baki kayanki sabida nasa daqar bazan samekiba, to gashinan kiyi amfani dashi aduk ranar dakike buqata amma ban da ranar da kika bawa wannan solobuyan kanki.
Tayi shiru tana kallon yadda yanayinsa ya sanza kawai don yayi maganar Bilal.
A hanli ta furta "nagode sosai yaya Mujaheed kuma nayi matuqar farin ciki da kyautarnan sosai Allah yasaka da Alkhairi "Amin ya amsa yana gyara kwanciya a jikinta.

Tsawon mintoci biyu bawanda yakuma magana zuwa can Bahijja cikin sanyin muryannan nata tace "yaya jaheed zan shiga ciki kaga magrib ta kawo jiki kada su mummy sunemeni basu ganniba sabida bawan da yasan na taho nan.
"Ok tam tashi inrakaki, ya jawo hannunta ta miqe ya d'an matsa hannun yace "taushifa hannunki kamar na jarirai, ta fizge hannunta tana hararansa yasaki dariya yace l miss this hararannan fa sosai, ita murmushi tayi ta amsa "nima haka zanyi miss cinzalin d'inka da latsamin ehmm "ehmm what? Ta juya baya ta dushi qofa batare da ta amsashi ba.
Yana dariyan tsokana yace "wallahi yarinya badin ina tsoron Allah

Please Login or Register in order to submit comment