Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai inshirya mana tafiya, cikin murna tasaki murmushi "yawwa yayana nagode "shima murmishin yayi tare da miqewa suka fito tare ita tayi cikin gida shi kuma yayi gidan liman.
Yasami malam dai dai yagama sallamar dalibansa masu karatun manyan littafan addini. Bayan sun gaisa cikin mutunci ya fadamasa buqatarasa nason address din inda Bahijja take zaikai maryam ce. Malam yafada masa kamar yadda Bashir yasanar dashi ko da zai dawo nan gaba. Bilal yayiwa malam godiya ya wuce. bai zame ko inaba sai majalisar su.

Majalisar cike take da matasa, yayi musu sallama, suka amsa yasami wuri yazauna.
Jabir ya dafashi yace "ya a kayine angon Bahijja in Allah yaso, murmushi yayi ya amsa "Kai aboki Queen tabar garinan bansaniba sai dazunnan.
Wata uwar dariya Ado yasa har yana tuntsurawa duk matasan suka bishi da kallo saida yayi mai isarsa sannan yayi shiru yana mazurai. Bilal ya watsa mishi harara "hala kwaya kawatsa sannan kazo majalisar kana mana hauka? "Sama nake cizo qarshen hauka, ya amsa yana maida mishi da martanin hararan da yayi mishi.
Jabir ya cukume Ado da sauri Bilal ya shiga tsakaninsu, suka zauna suna maida numfashi kamar wasu zakaru. Adnan mai tea ya dubi Ado yace"kai Ado miye nayi musu dariya irin haka suna cikin maganarsu?
Gyara zama Ado yayi sannan yasoma cewa "dole inyi dariya man, ganin iska na wahalar damai kayan kara, azuciya Bilal yace "mika ke nufi!!? "Ina nufin Bahijja tayimaka nisa fincinkau sabida yanzu tafi qarfin qauye da dan qauye, Bilal yayi shiru, Jabir ya amshe wallahi qarya ne kaji ko, Sarki yafi gaban ka kirashi da d'an qauye sai dai kakira kanka dashi, gidahumin banza da wafi wanda sholisho ta batawa kwakwalwa da soki burutsu!!!! Shewa matasan sukasa suna ihu, ganin haka yasa Ado barin wurin yana tangad'I yana zagin Jabir da Bilal.
(Ado babban d'an gwagwgo lantine, bai sa komi aransaba sai d'an hali da shaye shaye kuma wai ahaka yana son Bahijja, bayanta tafiyanta yasami malam da zancen, aiko malam yayi masa tas ya wankesu shi da uwarsa, yace ko da wasa kada yaqara jin zance makamancin wannan. To wainan kishi yake da Bilal *oooo*
Kwana uku tsakani yashirya yakoma makaranta buk yakeyi dama, yana shekarsa ta biyu. Don haka yasan ganin Bahijja bazai mishi wuyaba.
Sai da yasauke Maryam a gidan qanwar babansu dake zaria, zatayi hutunta acan, sannan ya wuce birnin kano.


****Bahijja tazamo star a school dinsu malamai sunaji da ita sosai sabida hazaqanta ga kuma ladabi. Ranar farko data soma zuwa makarantar a 1st period dinsu malamin lissafine, bayan ya shigo yagama bayaninsa sai ya rubuta wani ya nemi da wa zai iya yi masa.
Duk ajin sukayi tsit zuwa can Bahijja ta daqa hannu, 'yan ajin suka saki baki suna kallonta tare da mamakin baquwar zuwa da iyayi hatta malamin yayi mamaki da yaga baquwa ce zata bashi amsan.
Ya miqa mata chalk ta amsa, cikin mintoci biyar tayi ta gama, malamin yasa tafi sannan 'yan ajin suka d'auka raf raf!!!. ya yaba da kwazonta sosai, tun asannan Bahijja tazama monitor na ajin, kowa Bahijja dai Bahijja sosai take jin dadin karatunta.
Sumayya art class take, don haka basa had'uwa sai antashi break da kuma in anzo daukansu.

Tana zaune aqasar bishiyar gwaiba dake cikin garden.
assignment takeyi na chemistry, ta natsu sosai tana aikinta sai calculations takeyi.
bataji motsin mutumba sai ganinsa tayi tsugunne a gabanta ta kwalla qara tana cewa *"wala ya udu hu hifzuma wahuwal aliyul azim!!*

Ganin yadda tayi watsi da books dinta tana tsalle komi na jikinta na motsawa musamman na shanunta, yasa ya kwashe da dariya yana nunata da yatsa "jiba yadda kike tsalle nonuwanki sunayi suma, dalla!! bari haka kada su zube batare da sun nunaba. Cak ta tsaya tana kallonshi cike da mamaki.

*uhmm Readers wai waye wanan mutun d'in???????*👂🏻👂🏻



*Yaya Sadiya (mmn ihsan) wannan shafin nakine,bana da abinda zance miki sai godiya tare da addu'ar Allah ya raya zuria ya kuma bar zumunci Amin.*



*Mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.

*11*
"Mujaheed!! Ta ambaci sunarsa.
Kai ya gyada yana ci gaba da cewa "jibeta kwaila,kwanso kuma bera kawai. Batace dashi komi ba illah duqawa da tayi ta kwashe books dinta da hulan datake sanye dashi wanda yafad'I qasa sakamakon razanar da tayi.
Saida ta rungume littafan a qirjinta sannan ta dubeshi sama da qasa tace "amma dai girma ya riga hankali zuwa, anyi girman giwa ba wayau domin kaza tafita komi dukda tarin qanqantarta. Tayi shiru tana kallon yadda ya d'aure fuska tasaki murmushi ganin ta bata mishirai, "kaya dai nawane to ba zubewa su naskema ina ruwanka kuma ba nunaba tafasane basuyiba, na mamajo kawai to kasani Bahijja kwalelenka ehe. Bata ankaraba taji ya d'alle mata baki da yatsunsa biyu tasaki ihu tana liliya wurin har idanunta sun kawo ruwa don azaba.
"Wallahi jaheed kai azzalumine kuma nabarka da mai duka.
Cikin fushi ya matso ya danqe hannunta da qarfi tsuwwan azaba tasa ki tare da watsar da books din data rungume, tana son kwace hannunta ya take qafarta da covershoe d'in dayake sanye dashi, "ya ilahil Alamina!! Ta fada akidime,ta sunkuya tana jan qafansa, amma yaqi ko motsawa, ganin yana son yi mata illah tasoma bashi haquri "don girman Allah yaya Mujaheed kayi haquri na tuba, saida ya murzasu sannan ya d'aga yana sakin wani murmushi, harara ta watsamishi ta miqe ta qara tattara littafanta ta juya tabar wurin tana sharan hawaye.
Tarasa gane miyasa Mujaheed keson takurama rayuwarta, duk son kauce mishi da takeyi amma shi sai ya nemota yajata da magana.

Bayanta yabi da kallo sai kuma yacije yatsarsa "kai amma yarinyannan tasameni fa wai nine take kira namajo, yafurta afili " zan nunamiki aikin namajo kuwa inhar baki shiga hankalinki daniba, ya sassauta murya "ammafa yin fada dake nasani nushad'i musanman sauraren sautin muryan nan naki mai sanyi dake jefani cikin magagi, sai kuma ya tabe baki yana wani yamutsa fuska yafice ta qofar baya fuww!!

"Yaya mujaheed dazun yazo nemanki, ina kika shiga? "Cikinki na shiga!! "Tofa hajiya maida wuqar daga tambaya cibi yazama qari. "Kunama zai zama ba qariba. "Yau naboni da mata, mike daminki wai? "Shafa kiji. Shiru Sumayya tayi tana kallonta, ita kam tana ta rubutunta ko duban inda Sumayya ke zaune batayiba.

Washe gari Mujaheed yasaukesu a school, batajira kowaba tayi gaba abinta ta bar su Sumayya.
Haka ko da yazo daukansu bata ko kalli inda yakeba ba.

Agida mummy tasata gaba sai tafada abinda akayi mata sabida Sumayya tace yau bata kulaba kowwa ba.
Kanta sunkuye amsa " mummy kaina kemin ciwo da kuma inajin marata na mintsilina "kintabbata iya abinda ke damunki kenan? "Eh. "bawanda yabata miki arai agidannan kuma? Tai jim zuwa can tace "mummy kice yaya mujaheed yabar tsokanata fad'a. Kai mummy ta gyada tana shafa sumarta "zanci gidansu kuwa, kagamin yaron banza, babban kobo kawai.

Tun dganan tasami lafiya da neman fad'an Mujaheed sai dai kuma yawan kallon dakemata na takurata.
Tarsa miyake kallo ajikinta dake yawan kafeta da idanunsa masu bantsoro kamar na mazuru. *hhhhh*

Ranar wata asabar da hantsi suna zaune a part din umma sai hira suke kwasa ana raha.
Baba lado yayi sallam bayan an amsa yace "ga wani saurayi can a bakin get yace inkira mishi Bahija, sunarsa Bilal yacemin.
Wani tsalle tare da tsuwan murna Bahijja tasa tare da cewa "Kaishi parlour n baqi don Allah ganinan zuwa.
Dukkan su baki bud'e suke kallonta. Har tasanja kaya tafito taja hannun Sumayya "zo muje ki rakani.Sun kusa fita, umma tace "dawo kifadamin daga ina kika roroshi? Tana dariya qasa qasa ta amsa "umma surukin kine dan sarkinan dana fadamiki, kin tuno shi ko? Batajira amsawan taba tayi gaba tana cewa "umma baqonka Annabinka, sai nadawo.
"Allah yashirya umma tace tana girgiza kai "Amin Bashir ya amsa. Tsaki Mujaheed yaja alokaci daya kuma yamiqe yafice a parlour n. Su umma suka rakashi da na mujiya wato idanu.


*Ina kike my sis (zainab vc) tare da aunty khady (qamshi) wannan shafin nakune, addu'o'inku tare da yabawarku suna isowa gare. Nagode sosai. Allah ya biyamuku buqatunku na Alkairi, Allah ya bar zumunci Amin.*


*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.
*12*
Suna fita part d'in mummy suka zarce, drinks da snacks suka samo mishi. "A'a 'yanmatana ina kuma zuwa haka da kayan maqulashe? Mummy ke tambayarsu tana fitowa daga bedroom d'inta. Caraf Sumayya ta amsa "Mummy surukinkine yazo zamu kai masa, taqarasa zancen tana kallon Bahijja. Dasauri Bahijja fiace tana dariya, sumayya tabi bayanta nata fad'in kitsa mana kiyiwa mummy rashin kunyan da kika yiwa umma dazun man amma kin wuce kina soke kai waike mai kunya alhalin ta qarya ce. "Eh d'in naji dai iya sharhi kamar 'yar jarida.
Mummy murshi tayi tana kuma tunanin yuwuwar wani abu aranta.

Sun sameshi zaune yana ta latse latse a wayarsa, jin sallamarsu yasa ya dakata ya amsa fuskansa d'auke da murmushi.
Akunya ce Bahijja ta qarasa tana wani noqewa, "barka da zuwa yaya Bilal, ya hanya? "Barka kadai my princess, Alhamdulh, nasameku lafiya? "Lafiya lau "masha Allah. Ta juyo gefen da Sumayya ke tsaye ta dan harareta sai kuma ta dubi Bilal tace "ga qanwata kuma aminiyata Sumayya, 'yarinyar Abbanmu ce itama "ok Sumy ya kike ya karatu? Ataqaice ta amsa "lafiya.
Ya jinjina kai "yayi kyau. Suka zauna Bahijja ta zuba mishi drink ya d'auka ya kurba ya lunshe ido "nagode sweet queen, murmushi tasaki tana qare mishi kallo afakaice. Sanye yake cikin kaftan d'inkin zamani ruwan hanta, abinka da d'an fillo kuma farin mutum sai yayi masa matuqar kyau, sumannan tashi tasha gyara sai kyalli takeyi.
Ido suka had'a da Sumayya ta tabe baki tare da miqewa "inshiga ciki, tace tana duban Bilal "ok tam qanwarmu ki miqamin gaisuwata wurin su umma kafin inzo,"tam zasuji amma ni yayarku ce ba qanwaba domin na girmi yarinya da wata uku, "wa kika girma? "Mai kunyar qarya man, duka Bahijja takawo mata, ta kam ta goce tare da ficewa tana dariya, ta dawo tace "saraki sai gani nabiyu, murmushi yayi tukunna ya amsa "ok aminiyarmu "aha wannan yafi kam akan qanwarnan.ta yi gaba tare da karkad'awa Bahijja yatsu biyu,
harara tabi bayanta dashi.

Matsowa yayi kujeran dake facing d'inta ya zauna yana qare mata kallo.
Tayi masa girma da tsawo tare da haske, gashi ta koma cikakkiyar 'yar birni sosai. Suna hada ido ta tura baki "wannan kallon yayi yawa tace, sosa kansa yayi "uhm anyi 1~1 kenan, kuma ni kayana nake qara tan tancewa, kamarsu diri, sura tare da s..... da sauri ta tareshi "kai yaya Bilal kanan baka sanja ba ko? Dariya yasaki kawai. Takau da zancen wurin cewa
"Ina Maryam da Nana? "Maryam tana Zaria, Nana kuma rabona da ita tun kina can. Ido ta zare "ashe badaga can kake ba? "Eh gaskiya, nadade rabona da gida, ina ga kin wuto da kwana biyar nima na baro garin "tam ya karatu? Alhamdulihha, yanaki? "Lafiyalau.

Sun sha hira sosai har akagama lunch Sumayya ta kawo mishi yayi godiya.
Bashi wuri tayi yaci abinci.

"Wallahi sis guy dincan ya had'u amma sam baku daceba. Sumayya ke fadan haka.
"Kamarya bamu dace ba? Kai tsaye ta amsa "ya fiye siranta da magana kamar aku, sai kace ba jinin sarauta ba; wad'anda aka sansu da aji, kai Allah yaya Mujaheed yafishi komi. Aqufule Bahijja tace "wani abincine haka ko abinsa? "Wa ba? Sai da ta qara bata rai sannan ta fad'a a daqile "mujaheed d'in.
kallo kawai Sumy tabita dashi takasa cewa komi don haushi.
Tacigaba "kuma wallahi kikiyayeni dakiran min habibi da mara aji domin ina sonsa matuqa kuma shid'in jigone na rayuwata, yasani dariya sanda hakan ya qaurcewa fuskata ya kula da karatuna wanda yakaini damowa haziqa acikin karkaran, ta kowani fanni kinga kenan ya taka rawar gani a *Rayuwar Bahijja*

Kuma zancen rashin dacewarmu bai tasoba sai dai ace ya cancanci in soshi.
"Uhmm lallai yazamo wani haske rayuwarki sis Allah yabarku tare to "Amin 'yar uwa.

Saida yashiga yagaisa dasu umma sannan ta rakoshi bakin get.
Suna tsaye Bashir ya shigo, cikin fara'a sukayi musabaha, suka gaisa cikin mutunci.
"Yaya Bashir wannan shime yaya Bilal sannan tadubi Bilal, wannan yayana ne shina kebi. "Basai kin fad'aba queen naga kamanni ai, yafada cikin murmyshi.
" yayarmu ya aiki? Bashir ya amsa Alhmdulh, "yanaka? "Lafiya lau "gud yace tare da qarasawa ciki.

Har bakin titi ta takoshi, suna ta hira kamar kar su rabu. Ahankali motar ta dawo baya, saitinsu ta tsaya suka bi motar da kallo, Bahijja atake tagano mamallakin motar, aiko ta had'erai tana hararan motar, zuwa can Mujaheed ya zuge glass ya keqo da kansa fuska amurtuke "ke mikikeyi anan? Yace da ita. Kamar baza ta amsashiba sai kuma tace "yaya Bilal na takoma yasami abin hawa. Sai da yaqarema Bilal kallo sannan yace "to kiyi kibar wurinnan kafin Abba ya dawo domin yana daf da dawowa.
Asanyaye ta amsa "to. Yayi key zai tafi cikin sarqewar murya tace "yaya Mujaheed d'an saukeshi a buk please
Jim yayi sannan yace "ok bissimillah yana bude masa qafar gefensa. "No barshi, nagode Bilal yace yana murmushi. Bahijja zatayi magana ya rigata "sweetie ba buk nayiba, zan shiga kasuwa tukunna, ta gyad'akai "yaya tafi abinka to, wani kallo ya watsa mata sanan yafizga motar da gudu yabar wurin.
Bilal yabi motar da kallo "waye wannan guy d'in? Ya jefa mata tambayar tare da kafeta da ido. Ta sunyar da kai "yaya Mujaheed ne, yayar Sumayya "ok amma basuyi kamaba, "eh basa dashi kam, ita Abba ta d'auko yayin dashi yabiyo mummy har hasken fatar. "To amma mike tsakaninku? Kallon mamaki tabishi dashi najin wannan bahaguwar tambayan da yayi mata. "Queen ina saurarenki. "Ban fahimci tambayar ba.
"To mubar zancen kawai "hakan yafi kam ta amsa.
Daidainan wani nafef ya tsaya yashiga yana d'aga mata hannu itama hannun ta d'aga mishi tana qarewa face d'insa kallo wanda lokaci daya yakoma ba walwala.


*kai kai billahil azim ciwo ba dad'I ko sunarsa bai da dad'in ji.😩 jiya nakusa marya yawa qiyoma. Don haka ina baran ruwan addu'o,in ku 'yan uwana.*
*Allah kayi mana rowan ciwo Amin*




*Mrs J Moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.
*14*
"Qafafun yawo, kuntafi kun shantake kamar baza kudawoba kunbar baqi sunata jiranku ko? Sumy tana murmushi ta amsa "wallahi yaya Bashir munsami cikowar mutane ne awurin Amare da qawayensu sabida bikukuwa yayi yawa cikin wannan satin, sai da ya harari ta cikin wasa yace "jibi bakinta da sauri ta kai hannunta ta rufe bakin tana dariya qasa qasa. Ya miqe tare da dungure mata kai, ya dubi Bahijja "qanwata sai kinshigo inkingama soyayyar ta ja baya tana kare fuska wai taji kunya. Bilal yasa dariya.
Da dan gudu Sumayya ta bishi, ta kamo hannunsa tana fadamishi wani magana ya kama mata kunni tasoma tsalle bai saketaba har suka bacewa ganin Bahijja.
Ajiyar zuciya ta saki ahankali tana tunanin abin da Sumayya ke nufi da ita naqin kula Bilal alhalin sarai taganshi tare da yaya Bashir. Hannunta ya jawo yazaunar da ita a inda Bashir ya tashi ya zube hannayensa bisa cinyarta ta bi hannun da kallo tana tura baki da sauri ya janye yana murmushi ta d'ago ta kalleshi ya kanne mata ido d'aya tare da cewa "princess kin rame kad'an ko baki da lafiya ne? Bata amsa ba ta gyara zama tace "ashe tunsanda maukayi waya kanan amma kakasa sanar dani ko? ta tsareshi da dara daran idanunta yasaki murmushi mai sauti sannan ya ce "surprise nayi niyyar baki "ta mi? tatari numfashinsa, miqewa yayi yasoma tafiya zuwa inda yayi parking ta biyoshi suka jingina jikin motar yana kallon idanunta "shiga ciki idanunki ya gane miki ta maqe kafad'a cikin shagwaba tace "a'a nidai fara sanar dani tukunna kafin ingani "a'a ni dai kitafi kigani da idanunki yace yana kwaikwayon maganarta yanawani rangwad'a kamar mace, dariya tasa shima dariyan yayi.
"Queen wallahi kina da baqi aciki tun bayan azuhur sukazo donhaka tafi kigansu, nasan suma sunqagara su ganki, gyad'a kai tayi "to sai anjuma Saraki, murmushi yakar mata mai burgewa sannan yashiga motarsa, sai dataga yafice daga gidan sannan tayi ciki, mai makon tayi part din umma sai tashige part din mummy don kawai tasami Sumayya taji dalilinta na wukaqanta mata hubby.
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.

*13*
"Kayan Saraki!! Kayan saraki!! Sumy ke fad'an haka tare da bubbuga kafadan Bahijja. Ta bud'e fuskanta tare da motsa bakinta ahankali tace "mi nene Sumy? Jin muryanta irin ta marasa lafiya yasa Sumy ta yaye blanket d'in data rufa tare da hayewa gadon tana taba jikinta "Adda B bakya da lafiya ne? Takan kirata da adda intanajin nushadi, kamar yadda su khady ke kiranta.
Qamqame Sumy tayi muryanta na rawa "Sis rufeni don Allah, sanyi nakeji; washhhh!! Rufeni nace da sauri Sumy ta maida blanket d'in jikinta ta rufeta, jansa ta qarayi ta rufa ruf har kanta tawani cure wuri d'aya. "Mike daminki? Sumy tace tana dafa jikinta muryanta asarqe ta amsa "Sis komima ciwo yakemin, kaina, marata da cinyata, ta dama kamar zasu bar jikina, taqarasa maganar muryanta narawa gakuma haqoranta sai haduwa da juna sukeyi jikinta narawar sanyi shima.

Fita Sumy tayi da sauri bata ga umma a parlour ba sai tayi part din mummy da sauri. Ko gama fad'awa mummy batayiba mummy ta wuce da sauri zuwa part d'in umma, kobi takan umman batayiba wacce ke shirya break fast akan dinning tashige d'akin Bahijja Sumy ta rufa mata baya umma akidime ita ma tabi bayansu tana cewa "lafiya, mike faruwa?
Acan kuma Mujaheed na zaune yana shan tea a dinning area yanajin ance Bahijja ba lafiya ya ture cup din tea gefe ya dafe kai yayi shiru zuwa can kuma ya miqe yayi waje.
'Dakinsa ya shiga ya fito d'auke da fist aid box. Babu kowa a parlour n sai ya doshi d'akin da yakejin alamar mutane ciki, sabida shi baisan wanne ne d'akin Bahijjaba cikin dakunan dake parlour n.
Tsaye yayi a bakin qofar yana kallon yadda mummy take rarrashinta tana share mata hawaye ita kuma sai dafe ciki takeyi tana kuka mara sauti a sannu ya qarasa tare da yin sallama "yawwa Mujaheed dubamin ita ko da taimakon dazaka iya bata. Bai ce komiba ya sunkuya yana kallon fuskanta wanda ke rufe sai ruwan hawaye ke zubowa.
A 'yan mintoci yagano tana d'auke da zazzabi mai zafi wanda ya haddasa mata ciwon kai sannan mp time dinta yayi shiyasa takejin ciwon mara da cinya.
Sai da yayi umurni tasha tea tukunna sannan yayi mata Allura yabata magani tasha bata jimaba barci ya d'auketa.

Bayan sallar azuhur ya shigo parlour n umma. Bashir yasamu yana cin abinci yaqarasa wurinsa, cikin murmushi Bashir yace bokan turai "yau baka leqa asitin bane? Ya mutsa fuska yayi sannan ya amsa "banje ko inaba "ok to bismillah yana yana tura mishi plate girgiza kai yayi "am ok bros.

Hira sukeyi amma hankalinsa na kan d'akin Bahijja, xuwacan yamiqe yana duban Bashir "bari in dubo jikin yarinyan can yace, ya doshi d'akin Bahijja. Bashir murmushi yayi tare da girgiza kai yamiqe yafice daga parlour n.
Barci takeyi har zuwa lokacin, cinyoyinta duk awaje sakamakon rigan dake jikinta ta tattare tayi sama, yad'aga kansa yana qarewa suranta kallo wani dam!! Yaji gabansa ya bada sauti, tayi juyi ta bud'e hannayenta bottom din rigar ta bude boobs dinta suka bayyana afili har yana hango kan daya da sauri ya sunkuyar da kansa tare da furta "ya salam! Ya juya da sauri yabar gakin batare da tasan ya shigoba.
Sai daf da la'asar Bahijja ta farka, taji ta saka yau ba inda kemata ciwo sai mara itama kad'an kad'an. Toilet ta shiga sai da tayi brush sannan ta watsa ruwa tagyara jikinta sabida taga period din yazo.
Tana fitowa ta sami Sumy zaune a bakin gado tana waya ganin fito wanta yasa ta katse wayar ta dubeta cikin kulawa tace "add B ya jikin? "Yayi normal sis "haka akeso, Allah yaqara lafiya "Amin ta amsa yayin datake gyara zama a stool dake gaban mirror.
Simple makeup tayi amma tayi kyau na ban mamaki ta feshe jikinta da perfumes masu qamshi ta dubi Sumy "Mummy tanan kuwa? "A'a tafita yanzu amma nasan kafin magrib xata dawo "ok Allah dawo da ita lafiya "Amin.

Kwanci tashi gashi har su Bahijja ana ss3 suna shirin jarabawar fita.cikin nasara suka gama exams dinsu duka sai adduar samun saka mako mai kyau kuma.

Tsakani sati biyu dagama exams dinsu akasa lokacin yayensu na hadda sabida haka duk sukasa zaune sukasa tsaye, shiri sukeyi sosai.
Ana gobe yayen da yamma Bahijja da Sumy sun dawo daga retouching suka sami yaya Bashir tare da Bilal a harabar gidan zaune suna hira cike da mamaki Bahijja ke kallonshi domin basu jima dayin wayaba amma bai fadamata yana gidanba.
Ko kallon inda suke Sumy batayiba zata wuce Bahijja ta fizgo hannunta ta dawo baya bashiri "mikike nufi wai sis? Tace da ita "Nami ba? Harara ta dalla mata tare da janyota suka nufo su Bashir.


*Masoya naga sakon addu'o'inku agareni, nasami sauqi sosai. nagode da kulawar ku, Allah yabar so da daqauna. Allah ya qara mana lafiya baki daya Amin ya rabbi.*👏🏼


*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.

*16*
Washe gari da 9:00Am akasoma gabatar da taron, harabar makarantar ta *madinatul ahabab* tacika tanqam da mutane, sarakuna da daggatansu tare 'yan siyasa har da hamshaqan 'yan kasuwa sai kuma jigajigan jigon taron wata malamai magada Annabawa duk sun halarta awurin.
Taron yayi taro, manyan baqi sunyi ta gabatar da addu'o,I tare da yabawa dalibai da nuna tsantsar farin cikin su aranar da kuma yiwa makarantar fatan Alkhairi.

'Dalibai sittin da uku aka yaye, arba'in da biyu mahaddata ne yayin da ashirin da d'aya wanda suka sauke ALQUR'ANI ne.

Bayan gama yawabai na shugabanni da manyan baqi sai aka soma kiran dalibai suna fitowa sahu sahu suna gabatar da karatun Alqur'ani mai girma.

Anfitar da dalibai guda biyar masu hazaqa cikin mahaddata hukumar makarantar tabasu kyauta, cikinsu har da Bahijja wacce tazo ta biyu, wani namiji ke gabanta, Sumayya ita kuma ta hud'u tazo.

Su Abba sai murna sukeyi ganin 'ya'yanshi sun zamo abin koyi ga al-umma.
Sai daf da sallar azuhur sannan taron ya tashi kowa ya watse tare da tarin farin ciki musamman ga wad'anda 'ya'yansu ke cikin masu yayen.

Agida Abba ya had'a musu wata kwarya

Please Login or Register in order to submit comment