Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta juya tasoma tafiya har zata fice parlour n tajuyo tace dashi "nagode Bilal wannam itace sakaiyarka akaina ko? Nagode.
Jikinsa kuma sai yayi sanyi amma yana ganin gara haka sabida yaji duk tafita aransa tun bayan dawowanshi daga zaria yakejin canji ajikinsa shi yasa yasa wani malami yayi masa bincike akai yau yakeson zuwa yaji bayanin binciken.

Ta dade tana kuka cikin motarta sannan ta haqura tare da gyara fuskanta tayiwa motar key taja tabar gidan zuciyanta na bugawa ta doshi gidansu.





*Mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(bebeelo)*

©Safiyya.
*43 to 44*

Koda ta isa gida ta cimma mutane suna ta hada hadar shiga motoci bisa ga dukkan alamu party zasu ganin yadda kowa yaci uban gayu.
Can gefen qasar bishiya mango ta gyara parking, wurin ba yalwan mutane haka kuma bakowa ne zai lura da mutum awurinba.
Daga can nesa ta hango Sumy tana hidimar sanya mutane amota.
Ta kife kanta tasaki kuka mai cin rai zuciyarta sai rad'ad'i take yi mata tana qara janwa Bilal Allah ya isa na maidata bazawara da yayi da yarintan ta sai kuma ta dago kanta ta dafe goshinta dake bara zanar rabewa biyu "ohni Bahijja ko mi zance yayi sanadin rabuwarmu in an tambayeni? Ta tambayi kanta, Tayi shiru tana son lalibo amsa zuwa can tace "bazan fada yanxuba Allah, sai angama shagalin bikinnan sabida innafa jama'a zasu sami abin tsegumi wasuma har da qarin onga ciki.

Taqara kife kanta tana ajiyar zuciya bakin ta dauke da tasbihi, sosai taji dadin ranta sakamakon sunayen Allah datayi takira cikin ranta.

Bud'e qafar da da'akayi akayi yasa ta zabura, yasaki dariya yana cewa "ga matsoraciya matar sarakinta ta kalle shi ta kauda kai yayi kamar zau kamota sai kuma yaja baya yana nunata "amma Bahee baki da kirkifa ace sai yau zakizo bikina don baki murna da bin ko? Cikin qaramar murya tace "kayi haquri yaya jaheed, gani nazo yanzu amma inaga nafika murna da aurennan "uhmm waiba tace "da gaske ne fa yaya "ok to naji.
Fito maza muje kishirya yanxu mutafi wurin launching kada in makara.
yafada hakan tare da diba agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa.
Fitowa tayi ya dubeta yace "amma zaki kira mai gidanki yazo wurin ko? Tace "ni ba inda zani "sabida mi? "Bakomi "aiso sai kinje yarinya don kisanima.
bata qara cemishi qalaba tawuce yabiyo bayanta mutane sai kallonsu sukeyi baiko damuba harsuka iso qofar part din mummy yaja ya tsaya , ta sakai zata shiga palaur yace "ina nan tsaye ina jiranki sabida kece babbar qawan aboki don haka kece xakibada tarihina idanu waje tace "Allah kakama kanka yaya jaheed kada sa.... sai kuma ta kasa fad'i ya sosa kansa yace "kada kidamu tare dashi zaku fito kibada shi kuma yayi qarin haske kai, ganin yayi nisa akan lamarin yasa tashige parlour batare da ta sake tankashi.

Mummy ce tare da wasu dangi kadai cikin parlour n da sarsarfa ta qarasa wurin mummy ta fad'a jikinta tana fad'in "mummy nayi fushi rungumeta mummy tayi tace "to ayimin affuwa, hidima ne yashamin kai amma kullum kina raina inakuma shirin kawo miki ziyara "uhmm uhmm mummy kodai gan.... "gidanku Bahijja, tace tare dayi mata daquwa fuskanta ta kare tana d'an dariya.
"Sumayya yanxu tafita zuwa gidanki wai ku wuce wurin partyn jinwani fad'uwar gabatayi mara misaltuwa tayi gaggawan ta fidda wayarta ta latsa ta kara akunni "kada kiqarasa yanxu haka na iso gida gani gaban mummy tayi shiru sai tace "a'a ba inda zani kiyi tafiyar inkin dawo ma had'u, "ok tam kidawo lafiya, ta sauke wayar tana ajiyar zuciya.
Mummy ta zuba mata ido sai kuma ta miqe tace "biyoni "tam tamsa tare da bin bayanta suna shiga cikin room wayarta ta d'au qara shima da sauri ta d'aga tace "nace maka ba inda zani ai, kuma ni kaina ciwo yakemin, ta ajiye wayar ta maida hankalinta kan mummy.
" ke dawa kike waya yanzu? "yaya jaheed ne idanu waje tace "au dama bai tafiba? "Eh wai yana jirana nikuma ba inda zani "ok kiramin shi tako kirashi yana dauka tabawa mummy "fad'a tayi masa sosai tare da umurtansa yayi hanzarin tafiya zuwa wurin partyn nan kada ta saba mishi.

Bayan ta gama fad'an ta kalli Bahijja cikin kulawa tace "mike faruwa da ke? Ad'an daburce tace "mikika gani mummy? Daquwa tayimata "gidanku nagani, ina tambayarki kina tambayata ko? Ta sauke kanta qasa tace "sorry mummy, ba'abinda ke damuna kallonta kawai mummy tayi "amma idanunki suka tasa haka ga muryanki bata fita sosai kuma face d'inki baya da walwala alamu yanuna kina tare da damuwa amma kina son boyewa ko miyasa zakimin haka?
Atake wani kuka ya kwace mata ta fad'a jikin mummy tanayi kamar wanda akayiwa wahayinsa.
Qofar mummy tasama key sannan ta dawo ta janyota zuwa jikinta tayi ta bata baki tana shafa mata baya kamar wata baby, amma kamar sake tunzurata takeyi sai da tayi mai isar sannan tayi shiru ta kalli mummy ta sunkuyar da kai tana sau ke aji yar zuciya akai akai.

"Bahijja mi kefaruwa wai? Tayi shiru mummy tasa hannu ta d'ago kanta da ta sunkuyar tace "dubeni nan Bahijja, ta kalleta kad'an ta kauda fuska "wace ce ni agareki? "Uwa ce ta fada ahankaki "to indai nidin ina da wannan matsayin awurinki, lallai kuwa ina buqatar sanin damuwarki yanxu ba sai anjima ba.
Muryan ta narawa tace "mummy zanfad'a miki amma sai kinmin alqawarin baza kisanar da kowaba har sai angama shagalin bikinnan mutane sun watse. "Uhmm fadamin ina saurarenki, "mummy kadafa kifadama kowa nace "eh bazan fad'iba.
Kamar mai rad'a tace "ya sakeni saki d'aya idanu waje hannu bisa qirji mummy ta rafka salati tana qarawa.
"Bahijja mi yahad'a ku haka da yakai har akayi da saki? Duka duka yaushe akayi auren naku amma har ya qare, ikon Allah sai kallo.
"Ba ni takardan ingani, ta lalibo a jakanta tamiqa mata mummy ta warware ta ci karo da rubutu kamar haka *ni Muhammad Bilal Ahmad Sarki na yanke igiyar aurenmu d'aya akan mata ta Bahijja ja'afar,,,, batayimin komiba zamane kawai ya qare atsakanin mu, intasami miji tayi aure.*

Ajiyar zuciya mummy tayi sanda ta gama karantawa.
Ta dafa kan Bahijja tace "kidau dangana kibarma Allah kamarinki haka Allah ya tsara miki Rayuwa, ki yawaita addua ako da yaushe tare da istiggifari mara adadi don zai taimakeki wurin tafiyar miki da bacin rai in abin ya taso miki "tam mummy nagode sosai da samunki a Rayuwata "bakomi tashi kiyi haramar sallah naji ansoma kira, tamiqe tana cewa "mummy alqawarinmu dai murmushi tayi "kada kisami damuwa ba wanda zaiji yarinyata, murmushi tayi itama tare da shigewa toilet.

Su Sumy basu dawo ba sai qarfe tara saura.
Ta zube a parlour tana maida numfashi kamar wacce tayi tsiren gudu, Bahijja ta dubeta tasa dariya tace "Allah qara qafafun yawo kawai kamar shan shani, harara Sumy ta aika mata sannan ta miqe tashige bedroom.

Kwantawa tayi a bisa 2sitter ta lumshe idanunta tana sauraren hayaniyar mutane masu dawowa daga party sannan kuma tsigan jikinta yana tashi alamun zazzabi zai kamata mata.

Hannunsa ya d'ora a bisa agoshinta yace "ashe da gaske bakya da lafiya ta bude idanunta ta saukeshi bisa kan mujaheed ta miqe ta gyara zama ta kalli qafar mummy tadawo da kallonta kansa ta batarai tace "amma kasan ina da aure ko? yanzu ba da bane dazaka riqa yawan tabani.
Ya miqe daga durquson da yayi a gabanta yayi fice warshi batare da ya tankata.
Itama miqewantayi tashige bedroom amma qasan ranta ba dad'i.

Mujaheed kuwa ransa ya sosu datace ita matar aure amma kuma sai ya gode da ta tunasar dashi domin shi sam ya manta da tana da wani aure.

Washe gari da safe ta isa part din ummanta baki bude umman ta tace "ainzata sai nazo bikonki tasa dariya ta rungume umma tana gaishe da ita.
Daganan ta fice taje gaidashe da Abba.


Bayan sallar juma'a duban al umma suka shaida daurin auren Mujaheed tare da Amaryansa Badi'atu.

Hayaniya yasa Bahijja komawa cikin garden ta zauna ta zuba uban tagumi tana jimamin lamarinta.
"Uhmm qanwata mike damunki kika zonan kika zauna ke daya?
"Yaya bakomi kawai naji inson inyi nesa da hayaniya ne "ok tam zauna abinki ki huta qanwata tayi masa murmushi tare da jinjina kanta, yayi ficewarsa ya barta ta cigaba da tilawar wasiqan jakita wato tunani ba.


*Ayi manage da wannan please, because ina typing ina gyan gyad'i*




*Mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya
*45*

Batasan iya adadin da ta d'auka zaune a wurinba tasan dai lallai ta jima a zaune dubi da jin yarda taji zaman ya ishe.

Ta bud'e data ko zai d'ebe mata kewa sms suna gama shigowa tasoma bi tana dubawa yawanci na qawayenta ne don ita bata shiga group a ganinta rashin aikin yine, Sumy ta kance mata yana da d'ebe kewa da sa nushad'i, taja tsaki tace "aiko garanarta nan tazo da ace yanxu ina ciki wata qila danasami nutsuwa a zuciya koda su irin funny stories dinnan na karanta.

Haka dai tayi ta dubawa wanda taga dama tayi reply wasu kuma ta dokawa harara ta wuce.
Tana shirin sauka taga wani sms dayaja hankalinta ta bud'e tana kallo baki bud'e sai kuma taja tsaki tace "banziya kawai, munafuka da alama ke kikamana gullin da yakaimu garabuwa da juna, shine don iskanci zaki yimin tambayar rainin wayo to bansani.

Tamiqe fuww tafice daga garden d'in tana ta jera tsaki.

Bakowa takewa wannan bala'inba sai Munirat, wacce tasa alamar firgici tace aunty Bahijja wai da gaske hamma Bilal ya sake ki?

Har tashiga bedroom din umma tsaki take ja, tasami Sumy tana kyalliya domin bata dad'e da fitowa wanka ba.

"Ke da Bilal d'in kunci gidanku, aikin banza da wofi kawai, tace. Ita dai Sumy sukuti tayi tana sauraren abin kamar almara, wai yau adda B, take fadan zancen banza akan sarakinta haka, to ko miyayi zafi? Zancen zuci Sumy keyi.

Ko kallo inda Sumy batayiba ta shige toilet wanka tayi tare da dauro arollah. Tana zaune tana lazimi kiran Mujaheed yashigo wayarta Sumy ce ta d'auka tace dashi "tana lazimi taji jim da alama saqo yake bata zuwa can tace "to zanfad'a mata, ta ajiye mata wayar agefenta.

Sumy ganin bata da niyyar sallamewa yasa koda tagama shiryawanta sai tayi ficewarta.

Bahijja bata tashi bisa sallayarba saida ta sallaci magriba da isha'I tare da shaf'I ta bar wutri sai tazo kwanci sai tayi.

Sumy kuwa ta leqota yafi a irga.
Yanzuma ta qara leqowan ne taci sa'a lokacin tana nad'e sallaya.
"Allah ya amsa wannan doguwar zama, dafatan dai kinsani a addu'a Allah ya saukeni lafiya ko? Kuma quda na barci,
harara ta watsa mata tace "kedai kin boni, baki kojin kunyan cikin fari "eh banajin, abun arziki ne bana tsiyaba ehe "to Allah baki sa'a kiyi tayin rashin kunyar "Amin.

Ta zauna tasoma shafa lotion batare data qara kulata ba.
"Ke wai d'azun mi sarakin ki yayi miki naji kina za kici gidansu? "Ban sani uwar son jin gulma, Sumy tasa dariya tace "to madam maida wuqar cikin kube "in anqi fa? Dariyan taqara sawa tace "adda B, yau masifarki ya motsa kenan? Tayi mata shiru tacigaba da shafanta.
"Yauwa adda B, yaya Mujaheed yakira yace "kije yana jiran a d'akinsa "ki fada masa bazan zoba "a'a kirashi ki fada masa da kanki sabida yanzuma yaqara kirana yace lallai fa kixo "to banda wannan lokacin, tamiqe ta zira rigar barci ta daura zani akai ta sanya wata huta mai laushi ta rufe sumarta tafice daga dakin.
Sumy tasa dariya har da kwalla bayan ta tsagaita da dariyan tace "kai jama'a duniya labari wai mace da mijinta tana kishin wani, inyi shiru kada tadawo taji ni, taqara sa dariya umma tashigo ta dubeta ta girgiza kai batare da tace da ita komi sabida tasan ita da Bahijja ce don taga tafitowarta rai a bace.

Tana bisa gadon mummy kwance tana sauraron karatun QUR'ANI tana bi asannu idanunta rufe,,
asannu nutsuwa ke shigarta, ta tura yatsunta cikin sumarta tana motsawa, ahaka sarkin sata barci ya saceta zuwa birnin ilimi wata zazzau hhh.

Washe gari ta tashi cikin anna shuwa wanda hakan ba qaramin dad'I yayiwa mummy ba domin sai da tace da ita "yarinyar mummy yau kinfi kullum kyau dakike cikin walwala,, murmushi tayi tace "mummy falalar addu'a kenan "tam aqara dagewa dayinta "to mummyna.

'Yan biki sun watse kowa yayi gidansa anbar ango da Amarya suna ta shan shagalinsu.


"Adda B, kizo mutafi, kinga kowa ya halarta har da yaya mujaheed da yaya Bashir duk sun iso mukad'ai ake jira amma ke kinama kwance ne abinki don isa, taqi kulta, sumy taja tsaki tace "wallahi wannan Bilal din baiyiba da yafito dan sarki, don Allah jiba yarda ya koya miki mulki da wukaqanci, kai tir da wannan rasauta nasu.

Ta tashi zaune tace "ke dalla yanxu ni bata wani abin amai Bilal nake ba, ina tunanin yarda Abba zai d'au maganar ne in angama taruwa.
"Ban fahimcekiba adda B? "Tashi muje parlour n Abba acan zakifi fahinta ta amma a ha qiqanin gaskiya ina jin tsoro kada Abba yayi fushi dani "wai don Allah adda B, mine ne ke faruwa? Ta janyo hannunta zo muje kiji dai.
Suna fitowa su kaci da Mujaheed zaizo kiransu. Wani harara ya watsa musu Sumy tayi gaba da sauri ita ko gimbiyar tafiyan taqama tasoma tana wani motsa mazaunai,
da kallo yabita sai kuma yazo suka jera yace "kina murgud'amin duwaiyu to kisani yanxu ba da bane danike rajinki yanzu ni kayan Badi'a ce, ke kuma ta tsukakken d'an fillo mara kuzari ta juyo a fusace ya bi gefenta da sauri yashige parlour yana dariya qasa qasa.


*shafin nakine Leemet ke d'aya tilo domin jin dad'inki*



*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*


Kainuwa Writers Association.

©Safiyya.

*46 to 47*

Duk sun nutsu suna sauraren Mummy wacce ita ta kira taron.

Bayan ta bud'e taron da addua sai ta d'ora da cewa "abin da yasa na nemi da ayi zama nan shine ::yau kwana uku da Bahijja ta zomin da wannan takardan ta shaidamin sun rabu da mijinta.

Salati parlour n ya d'auka na tsawon wani lokaci sannan Abba ya nemi da mummy tabashi takardan yagani, ta miqa mishi ya dad'e yana nazarinta sannan yaja numfashi yace "bahijja mi yahad'aku har ya kaiku ga rabuwa? Muryanta narawa ta amsa "bakomi Abba.
"to shikenan zamu jira zuwan magabatansa inkuma basuzoba sai muyi addu'ar Allah yasa hakan shinemafi Alkairi.

Daga haka ya sallamesu ya nemi matarsa dasu zauna akwai abinda zasu tattauna.

Suna fitowa daga parlour n Bahijja ta wuce da sauri zuwa part d'in mummy sabida tana hankalce da Bashir yana ta auna mata harara kuma tasan zai iya dukanta in har ya rutsata.

Tana shiga falon Bashir yana damqeta domin yana biye da ita a baya har zuwa parlour n.

Wani mari mai kyau ya sauke mata afuska ta kwalla qara su Mujaheed suka shigo da sauri, ya d'aga hannu zai kuma shara mata mari Mujaheed ya riqe hannun tare da turashi baya ya nunashi yana huci "wallahi bros kasake dukanta Allah sai munyi damben mutuwa da kai, baki bud'e Bashir ke kallonsa dakyar ya bud'e baki yace "bros kana ganin yadace abinda tayi kenan? "Mitayi to? "Kashe aurenta man tana 'yar ficiciyanta amma tasan takomo bazawara, "bazawaran taaa!! Nace koba bazawara baa!!! Mamaki ya kuma cika Bashir ganin yadda Mujaheed yake son zaginsa afakaice, bai gama fita cikin mamakinba ya tsinkayi yana cewa "Bahee kiyi haquri yanxu zan tafi in rama miki dukan da yayi miki akan solobuyon shashashan mai dogon wuyan can, Allah idona idonsa sai na sumar dashi sai yajiyo qamshin qiyoma, yana gama fad'an haka ya fice afusace Bashir yabi bayansa da sauri amma kokafin ya isa ya tada motar ya fice shima mota yafad'a yafi bayansa da gudu.

Adda Asma'u wacce ta iso yanxu tabisu da kallo tana tunanin mike faruwa kuma.

A tsaye ta cimma Sumayya da Bahijja sunyi shiru, ta kalli fuskan Bahijja taga ya kumbura tazo da hanzari ta kama hannunta tana tambayarta mike faruwa ne? Sumayya ce ta labarta mata komi, salati ta saka ta janyo hannun Bahijja suka shiga bedroom.

"Bahijja ki haquri, Allah zai saka miki kinji? "Tam adda Asma'u nagode da kulawanku "bakomi Bahee.

Sumayya takasa cemata komi sai kallonta takeyi cike da tausayi, sosai taji zafin marin da mijinta Bashir yayima 'yar uwanta fiye da sakin.


Abba ya dubi umma yace "umman yara kinqi cewa komi tayi murmushi yaqe sannan tace "mizance Alhaji ai duk abinda kukayi akai daidai ne nidai nawa addua ce kawai "tam mungode sa wannan girma da kike bamu ako da yau she.
Mummy ta d'ora "inaga abinda yafi shine muyi gaggawan kwaso kayanta domin kada yaga kamar muna jiran zuwansa ne "eh hakan yayi mummy yara.
Haka dai tsakanin mummy da Abba sukayi ta tattauna abin ita dai umma tayi shiru tafad'a kogin tunani,, domin haqiqanin gaskiya mutuwan aure ba dad'I musanman in abin ya shafeka.


A tsiyace mujaheed ya taka burki a bakin get din gidan Bilal yafito yasoma buga get d'in da qarfi mai gadi ya bud'e jiki na rawa, wani cakuma yayiwa mai gadin ya shaqe yana tambayar sa "ina mai gidan? Bawan Allah yaji shaqa idanunsa sunyo waje sai kad'a kai yakeyi yakasa magana.
Bashirne ya iso wurin ya bambare hannunsa a wuyan mai gadin dakyat yatura Mujaheed baya da qarfi ya riqe jafad'ansa yana cewa "wai miye kakeyi haka, kamar wani ta babbe, baza kad'au qaddaraba ka barma Allah komi, ko kamanta dacewa haihuwa, aure, mutuwa,samu da rashi dukkansu daga Allah ne, to miyasa kai baza kad'auki qaddara ba? Ya buge hannunta yanayimasa wani kallo yace "au ashe kasan da wad'annan abubuwan amma katake su kasa hannu ka doketa don tsabar mugunta, to kasani kajawa tsakurkurinnan wahala don sai na makeshi nima inga uban da yatsaya nishi agarinnan.

Bashir ganin kamar Mujaheed baya hayyacinsa yasa yasoma lallaminsa cikin sanyin harshe yace "to bros kayi haquri nasan ban kyautaba, sharrin zuciya ne ayimin affuwa.
Mujaheed yasauke numfashi ya juya ya shiga motarsa yafizga da gudu.
Bashir yabisa da kallo sai kuma ya isa wurin mai gadin yasoma bashi haquri ya amsa bakomi, yabashi 5k yasha magani sabida yana ganin shaidan yatsun Mujaheed a wuyar mutumin.

Asannu yaja motarsa ya qaraso gida, baiga motar Mujaheed ba ya jijjiga kai yace afili "kai amma Mujaheed anyi d'an bala'i, jiba yarda duk ya maidani sai kace wani d'an kokawa.


Adda Asma'u da sumayya sukayi ta bawa Bahijja baki tare da qara jaddamata rayuwace wata rana sai labari, ita dai jinsu takeyi kawai amma ita kam bata jin komi akan rabuwarsu sabida ita hakan yafi mata dad'i akan zaman dasukeyi na rashin tabbas.


Mujaheed gidanshi ya isa ya shiga parlour n a fusace ya doshi bedroom d'insa yafad'a gado ya dafe kansa, yaja wani dogon tsaki sai kuma ya miqe ya fad'a toilet.
Bayan kamar mintoci goma yafito jikinsa duk ruwa ya zauna bisa stol yayiwa mirror quri da idanu.

Ta bayata rungumeshi tana shafa sumar qirjinsa ya lumshe idanunsa ya bud'esu yana kallonta ta mirror tasakar masa murmushi "haskena waya tabamin kai? Tace dashi.
Yasauke numfashi ya juyo ya rungumeta yana shaqar qamshinta, can qasan maqoshi yace "kece "ni kuma fa kace? "Eh ke, saida ta tura baki sannan tace "to minayi maka? Ya subbaci wuyanta yace "kinqi qaramin abin yana kashe mata ido d'aya tayi saurin sunne kanta a qirjinsa ya qamqameta yana rad'a mata "wurin ai yawarke yanzu ko? Taqi tankashi, yasaki dariya tare da d'agata cak yayi mata masauki a bisa bed yayi mata rumfa da wadataccen qirjinsa.

Amarya Badi'a duk sai ta gigice masa sabida tasan karon ba dad'i bai ko damu da sautin kukantaba yasoma hawa gajimare ya lula zuwa dashi garin maji dad'i, garin ban ruwa da tsirrai masu ban sha'awa hhhhh.




Mama yalwa zaune gaban malaminta tana tazuba mishi godiya kama zata yi masa sujjada.
Shikam almurin sai washe baki yakeyi yana jan wani tsakurkurin gyemunsa mai kama dana tsohon bunsuru.
Ta zube mishi kud'i mai yawa ya kwashe yana dariya.
"Wai malam ya akayi karabasu ne haka da wuri bazato ba tsanmani?
Dariyan 'yan duniya yayi sannan yaso mata bayani "wato hajiya dana duba naga ita zata bani wuya wurin shigar sihirin jikinta sai na juya wurinsa na tura mishi aljani shasahatau ya mantar dashi yin arollah yayi dazai shiga barci sannan ya hanashi yin addu'a kuma ya sakar mishi da d'oyi yayin da zai kusanceta sakamakon ita bata jure shaqan wari ko yayane batare da cikinta ya burkuceba tasoma gudawa da amai, hajiya ingaya miki har gizo yake musu kuma yasasu tashi suna jin haushin juna in ta qaice miki ya takurasu sosai har sai da ya rabasu tare da taimakon maganin da kika zuba mishi yaci a abinci.
Dariya mama yalwa ta kwashe dashi tace "yayi malam uban malamai, yanxu aurensa da yarinyata zai taso ko? "Eh hajiya yanzu hakama yaron yazo gidanki wurin yarinya domin su dai daita amma ita kuma tace sam bazata aureshiba.
"Malam to miye mafita "kibarni da ita kawai kiyi tafiyarki "to malam sai kajini.
Ta nufo gida cike a farin ciki.

*Allah kashiryar bayinka wanda suka band'arewa koyarwan Annabinka SAW. Amin*

Yau sati hud'u da rabuwar auren Bilal da Bahijja, takoma cikin walwalarta sosai hakan yayiwa su mummy dad'I sosai gashi kuma sun fahimci bata da ciki sai abin yaqara yi musu masha Allah.


Yau ranar hutun qarshen mako suna tare da mummy tana kwance bisa cinyarta tana sosa mata kai wai qaiqayi yake yi mata.
"Wanke mi za ayi "to mummy anjuma sai inje "a'a indai kaiki d kaina sabida gudun fad'an Abbanku "ok mummy Allah yabarmana ke "Amin.

Sallamar Mujaheed da matarsa ya katse musu hira.
Bahijja duk tawani daburce sabida bawani suturar kirki take sanye dashiba.
Suka shigo suka zauna tare da gaida mummy cikin sakewa mummy n ta amsa musu tana tambayar Badi'a ya gida cikin jin kunya ta amsa da Alamdulillah.

Mujaheed kallon Bahijja yakeyi bako qiftawa, ta d'ago ta harareshi ya motsa bakinsa tagane mi yace ta had'e rai ta miqe tashige bedroom da sauri Amarya Badi'a tabita da kallo tana jin wani abu ya tokareta, ta kauda fuska tana jan istiggifari domin koran shaid'an da ya kusan tota.
badi'a tasan komi dangane da rabuwar auren Bahijja amma bata san labarin soyayyarsu da Mujaheed ba ita dai haka kawai taji sam Bahijja batayimataba, haushinta takeji sosai a ranta gashi ta fahinci tana da taqama da izza domin zuwansu nabiyu kenan gidan amma bata taba gaishe da itaba amatsayinta na matar yayanta.

Bahijja ta fito bayan ta dora after dress abisa kayan jikinta.
Ta d'an russuna kad'an tace da

Please Login or Register in order to submit comment