Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gyad'a tace "saraki ban hanaka kainaba ganinan ai.
cikon murna yasoma kaiwa ko ina najikinta subba kamar wani mayunwacin zaki.
Ita kam sai toshe hancinta take tare da qoqarin daurewa tskeyi na najin wani irin wari mara dadi shaqa yana busowa ata ko ina na ckin dakin.

Yana daf dacika burinsa ta zabura ta hankad'ashi gefe bed ya fad'o tim!!
Tayi cikin toilet da gudu ta durqushe tasom kwara amai har da zawo ta zauna dirshan tana kwarawa takai kusan 10mins tana amai da zawo duk jikinta ya saki.
Cike da sanyin jiki ya kamata ya fidda mata kayan jikinta yayi mata wanda da ruwa mai tsafi sosai ya nad'eta a towel ya lalibo rigansa na barci ya zura mata yarufeta da blanket sabida jin da yayi jikinta na rawar sanyi.

Bayan ya gyara wurin tsaf yakoma ya rungumeta yana tunanin mike damunta haka.

Har akayi kiran sallar farko idanunsa biyu. Bai sami ya runtsaba.


*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.

*39 to 40*

"Uhmm yaya kabarni inyi barci don Allah, daren jiya kahani in huta da safenma baza kabarni in hutaba.
Cizo yamanna mata akunni tasaki qara tare da fad'in "wallahi kai kam yaya Bashir kasan kan mugunta salo salo.
Ahankali yace "kibarni insami tsuwa dake jiya kinqi sai uban kuka kikemin don tsaban ragwanci, to yanxu kuwa bazan bari kiyi barci ba ko da kuwa gyan gyad'ine har sai na tabbatar nasami gamsuwa.
Da sauri ta miqe zaune tana dubanshi da kubburarrun idanunta wanda suka ciki da kwalla tace "kasheni kakesonyi kenan? Yakanne mata ido d'aya "a'a zumata bazan kashekiba sai dai zanbaki dad'ine da sauri ta tareshi banson kalan wannan dad'in kariqe kayanta, takoma ta kwanta ta ja bargo ta rufa tana cigaba da cewa "kai inhaka aure yake to gaskiya da wuya kam.

Bargon yashigo ya rungumeta yanayi mata wani salo ita kuwa sai kuka take da bashi hakuri amma bai kojitaba talle tasaran zai sauraramata.
Sai da yasami gamsuwa sannan ya zare jikinsa tare shafa sumar kanta yana cewa "affuwan zumata natuba bazan sakeba kinji, yi haquri Allah yayi miki albarka ya barmu tare da juna har izuwa qarshen rayuwarmu "Amin ta amsa cikin dushewan murya, ta d'ora da cewa "saina fadawa umma kuma ince zaka kasheni da raina da tsaban muguntanka.
Dariya yasa sosai yace "dakuwa insha kunya ace kamarki 'yar jami'a tana abin yara qana 'yan qauye. Shiru tayi mishi, yamiqe yashiga toilet ya tsarkake jikinsa.

"Zumata tashi kiyi wanka, yace da ita "barci zanyi sai anjuma nayi, "a'a zumata ba kyau zama da najasa ajiki yin hakan yana kawo junnu su shigeka kuma in anyima sihiri yana saurin kama mutum, don haka tashi kiyi kada wani abin yasameki.
Ta tashi tana wani yatsina ya d'ata cak zuwa bathroom.



Suna break Bilal sai kallon Bahijja yace yana tasbihi aransa sakamakon ganin ainihin suranta azahiri da yayi yau, sabida duk inyazo zance tana sanyo hijab mai yalwa sannan ko yaganta cikin gyale baifiye kallonta ba amma yau da igiyar aure yashiga tsakaninsu gatanan zaune yayi abinda yaso da ita bamai hanashi.

*uhmm wallahi aure wata babbar ni'imace*
Yaja numfashi tadago ta kalleshi yasakar mata murshi itama murmushin ta maidamishi ya matso yajawota ta hau cinyarsa, ahankaki yasoma latsa mata boobs ta runtse idannu ganin haka yasaki siririyan dariya yace "da zafine? Ko kinfison in tsotsa? Ta kife kanta aqirjinsa tana qunquni cak ya d'agata suka dawo tsakiyar parlour.
Cigaba yayi da wasa da ita ita kuma sai noqewa takeyi na kunya.
Dakansa yagaji ya dakata ya d'agota yace "princess mushiga daki inabaki kyauta, kallaonsa tayi taga kwayar idonshi ta sanja atake tagano nufinsa taji wani mummunar bad'uwan gaba afili ta furta ya salamu!!
Baiko lura da yanayin da ta fad'aba ya miqar da ita ya tallabeta akwaibinsa ya doshi dakinsa da ita.
A bisa bed yayi mata masauki ya kwanta flat a jikinta yana son hada bakinsa da nata tajabura ta fice da gudu sai dakinta ta fada toilet tayi ta kwara amai ba qauqqautawa.
Yana tsaye har tagam ta wanke baki tare da wurin ta fito.
Wani kallo yayi mata mai cike da zargi sannan yajefa mata tambaya "shin ko dai kinbama wani kankine? Arazane ta dago tana dubanshi ya gyad'a kai "eh ina son sanin dadalilin dayasa kike guduna innazo yin sunna da ke?
Kai ta sunkuyar tarasa wacce zata amsa mishi zuwa can tasake d'agowa tana kallon idanunsa tace "inni mara kamun kai ce kaine mutum na farko dazai fara ganowa kuma ni bagudunka nakeyiba kawai wani al'amarine ke faruwa wanda narasa gano ko miye shi.
"Uhmm to naji amma kisani niba dutsebane ina da felling mai qarfi don haka kiyi qoqarin magance wannan matsalar.
Yajuya fuww yafice yana maijin zafin abinda takeyi mishi.

Tagumi Bahijja tayi tana tunanin ta yaya zata magance wannan matsalar ita d'aya alhalin tasan ba tantama matsalar ajikinsa yake, afili tace "kai ni yasu wannan wani irin rayuwace mai cike da rud'ani ace wari mijina kemin kamar anbud'e rubabben masai sannan warin bai tashi sai in yanemi domin muyi sunnah *Ya ilahil Alamina kakawo mana mafita cikin gaggawa*
Amin.


Kimanin watanni hud'u
Abubuwa sun faru masu dadi da kishiyarsu.
Azamanta kewan Bilal da bahijja dai sai haquri domin duk iya yunqurinsa naganin ya maida cikakiyar mace abin yaci tura har yama haqura tunda ya fahimci indai yasa niyya sunna da ita ne take samun matsala sai ya bari illah iyaka suyi wasa da juna sukwanta rungume da juna.
Amma duk da haka sai watarana sutashi suna shanma juna qamshi kamar wasu masu iskokai.

Kamar kullum yauma yadawo da rana ya taddata zaune tana kallo ya zauna gefenta ya kai hannunsa ya matsa cinyarta tasa dariya tanacewa "har ka gudo kenan daga office? Ya d'aga kai "to sannun da hanya "yawwa kema sannu da gida matar saraki murmushi tayi ta jashi zuwa toitet.

Bayan ya kintsa ta gabatar mishi da lunch, ita taciyar dashi har ya qoshi yayi hamdala "Allah yayi miki albarka queen ta amsa "Amin sarakina.

Suna zaunne sunad'an hiransu na masoya ya janyota ya qamqame ta kalleshi yayi saurin ce mata "wai kuwa queen bakyajin komi na dire kuwa? Ta sunne kanta a qirjinsa ta amsa "inajiman amma yazanyi sai haquri mucigaba da fadawa Allah lamarinmu da yardansa zamu sami waraha.
Kai ya kad'a yace "Allah yakawo mana mafitan cikin gaggawa "Amin.
"Amma sweetie wai mikikeji agareni ke saki amai haka? Shiru tayi tanatunanin ya zai dauki maganarta in ta sanar dashi warin qaxantaccen masai takeji yanayi mata duk sanda yayi qoqarin yin sunnah da ita, atake ta sanja shawara tace "saraki kabar yawan bincike domin hakan bayada kyau sam.

Kafeta yayi da idannu amma sam baijin zai bar binciken sanin misabbabin da ke haifar da faruwan hakanba.

Amma afili sai yayi dariya yace "to nabari sarauniyata itama 'yar dariyan tayi tare da jan hannunsa "zomuje musamo fruits agarden.


Adaren ranar Bilal yaqara tsareta sai tafad'amishi mitakeji ita kuma taqi fad'a sai cemishi take muyi ta addu'a zaifi mana da wannan sonjin kwam d'in naka, haushi ya kamashi yayo kanta ya danne yana mai cewa "Allah yau ko da tsiya sainayi sai dai ki mutu ba amaiba cikin wahala take cewa "saraki kada kayimin haka, barari muyi ta lalama amma ba da qarfiba.
Banza yayi da ita yasoma aika mata da saqo tayi lamo tana amsa domin sosai takejin buqatar na miji amma sabida da warin data keji yasa bata nuna mishi.
Wannan karon bataji warin komiba amma ganin wani baqin abu takeyi na giftawa atake tsoro yazo mata tana qoqarin tureshi amma ta kasa abin har yabata mamaki ashe ba gibane qarfiba abin ajini yake.
Tanaji tana gani ya soma neman hanyar da qarfi domin shi atunaninsa tasan wani ne shi yasa takemishi haka.
Ta matse qafarta da qarfi tana cewa "wallahi saraki bazan yarda kabini da qarfiba salon ka raunatani kabarni da jinya.
afusace ya sa hannu ya bude qafafun nata da qarfi tasaki qara don azaba wanda yayi daidai kuma da gani abinnan yayo kansu da qarfi ta furta "ya Alimu!!! Sai jitayi anyi jifa da abu tim ta tashi da sauri bakinta d'auke da addu'a ta kunna globe.

Idanu waye ta ruga da sauri ta isa wurin Bilal inda ke yashe aqasa bai ko motsin kirki goshinsa ya fashe sai zubda jini yakeyi.
Kuka ta fashe da shi tana kiran sunansa.
Yabud'e idanunsa yana kallonta ta dunqushe agabansa tana cigaba da kuka.
Tana fad'in "mine haka? Wai mike faruwa damu ne?
Wani uban tsaki yaja da qarfi ya miqe tallabe da goshi ya zura rigan barcinsa yabar d'aki yana tangad'I sabi da zuban jinin da goshinsa keyi.
Har tabi bayansa sai kuma tadawo ta gyara wurin da jinin yabata ta kuma tofe d'akin da addu'a.
Ta zube gefen gado ta fad'a kogin tunani sai a lokacin ta tuna batayi arollahba ta kwanta ta zabura da sauri taje ta d'auro sannan tafice zuwa d'akin Bilal.





*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mum Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya
*41 to 42*

Bakinta d'auke da sallama ta shiga yana zaune gaban mirror yana dressing d'in goshinsa da ya fashe, ta tsoge a jikin qofar tana kallonta ba tare da taqarasa inda yakeba.
Shima bai ko kalli inda takeba.
Bayan yagama yatashiga toilet ya shiga ya dade sanan yafito jikinsa da ruwa alamar wanka yayi ya kwanta tare da jan blanket ya rufe jikinsa ruf amma aqasan ransa sam baiji dad'in yadda ya shareta ba.
Ranta ya sosu da barin iskan da yayi da ita amma kuma sai tayi mishi uzuri qila zafi goshinsa keyi masa sosai.

Ahankali ta tako zuwa bakin bed din ta zauna tasoma magana "saraki don Allah kayi haquri da abinda yafaru yayi mata banza batayi fushiba ta kuma cewa "lamarinmu da abin rudani ciki sabida haka abinda yafi kawai mufadawa magabatanmu qila zasu samarmana mafita.
Ya ture bargon da yarufa ya tashi zaune yana yimata wani kallo tayi saurin sauke kanta qasa.
"Rud'ani miye alamarinmu namu? To kisami ke ce da kanki abin rud'anin queen don haka ke da kanki zaki nemo mafita amma ni ba abinda zan iya akai tunda na lura kina da almatsutsai masu hanaki bawa mijinki hakkinsa, wata qilama sun aure kine sabida ance sunfi son farar mace kuma mai kyawun sura, kuma ki sani ba wasu magabata da zan fad'a mawa kiji da masu jinki. Yana kaiwa nan ya juya ya kwanta yaa jan tsaki.
Mamaki yagama cika Bahijja tayi shiru zuwa can ta miqe ta kashe mishi globe har ta kama handle sai kuma tace dashi "adai qara addu'a kafin ka koma barci don nasan kasoma wasa da addu'a yanzu tayi ficewanta wani tsaki yaqara ja sannan yace "aikin banza da wofi bazanyiba ai ba kinfini sanin inda kemin ciwo bane, bama dole junnu su shiga jikin kiba wanan kaya haka da kike dauke dashi, ya tsiza lebe yana girgiza kai, dole in kawo mai ruqiyya yayi miki kam.


Washe gari Bahijja tana kitchen tagama hada break fast tana gyara inda ta bata ya shigo.
Qamshin turarensa da taji yasata juyo tace dashi "antashi lafiya? bai amsa ba sai binta da kallo yakeyi ta ko hade rai domin har yanzu bata huce ba. Shima rai ahade yace "zanfita inzo da malamin dazai miki ruqiyya sabida nagano kina da almatsutsai domin jiya sun tashi kasheni don haka bazan bari su kasaarani abanza da wofiba ni ba abarni naji dadin komiba sai dai abarni da jinya to Allah bazai yuwuba hakan sam.

Sai da yasa aya ta dubeshi ido cikin ido tace "kasan Allah saraki ba wanda zaimim wani ruqiyya agidannan,alhalin ina da lafiyata lau, inma zaka nemi malamin da ya taimaka maka da addu'a abisa laluranka dayafi maka domin nima tuni nagano gidanan bai sami wada taccen addu'a ba muka shigo shi.

Cikin qufula da zancenta yace "ni lafiyata lau hakama gida lau yake kece dai baki da isassa ta watsa mishi harara tace "ni wallahi aurenma yafice min a rai yanzu "komi zakice sai dai kice amma mai ruqiyya zaizo yanxunnan yayi miki.
Banza tayi mishi tacigaba da aikinta don ta fahimmci yau da 'yan bala'in ya tashi.
Koda tafito tasame zaune yana kwasan girki sai kada kai yakeyi na santi, ta qaraso ta zauna ta hada tea tasoma kurba ahankali.
"Uhm wallahi princess da ace yadda kika iya girki mai dan karen dadinnan haka kika iya gyara shinfid'a da banga abinda zaisa naji ina son qara aureba kuma k.... tarin da ya sarqeta yasa mishi dakatawa da zancensa, da sauri ya isa wurinta yana yi mata sannu bayan tarin yalafa mata ya bata ruwa tasha ta miqe ya biyo bayanta yana cewa "sweetie baki gama yin break d'in ba, tayi mishi banza ganin zata shige room d'inta yayi saurin shan gabanta yace "baki son inkira mai ruqiyya ko? Tona bari Allah bazai zoba, zo muje in baki abaki kici.
Ta make hannun da yamiqo zai kamata ta nunashi da yatsa "kasan wallahi inma wasa kakemin na batun qarin aure to tun wuri kadaina domin kafi kowa sanin bana son zancenta ko d wasa ne.
Ya jabaya yana dariya "au wai akan haka kikema fushi to nabari amma zan kawo mai gyaramin shunfida dai, duk cikin dariyan yake fad'an haka ganin ya soma maidata wata kwarkwar yasa tashige room d'inta a fusace ta kulle qofar ta muza key sabida bata son yazo yadameta.

Tana kwance tana ta saqe saqen maganar qarin auren Bilal. "Wai to da gaske yakeyi ko wasa? Toma wai duka duka watanmu nawa da aure? Kai Allah bai isaba tafad'i afili "ashe kuwa gidannan da tashin hankali kuwa.


"Assalamu Alaikum masu gida, shiru bako motsi, aka qara doka sallama nanma shiru sai kawai mai sallamar ta sami doguwar kujera ta zauna tare d fad'in "washh!! Allah nagaji d'an wannan driving din danayo jinike kamar nayi wanki, ta zame ta kwanta abinta akujeran, abinka ga mai yaron ciki aituni barci ya lula da ita zuwa garin sokoto ruhinta yana ta bulayi cikinsu tsumi da gumba har da tabaje da mahaukacin ruwa hhh lolx.

Bahijja bata tashi daga barcin da yakwasheta batare da tasani ba sai bayan sallar azuhur. Agaggauce ta watsa ruwa ta gabatar da sallah ta shafa lotion mai kan uban qamshi tayi simple make up tayi ta sanya qananar kaya riga da sket masu ruwan hanta ta nade kanta da gyale light din kayan ta feshe jikinta da turaruka kala kala sannan ta bude qofar tanufi kitchen da sauri sabida wani uban yunwa dake damunta bata ko lura da baquwan da tayiba.
ganin tana da miya yasa ta dafa couscous tana tsaye har ta nuna ta d'iba dai dai cikinta ta dauko ruwan roba mai sanyi tare da maltina ta zauna a dining tayi bismillah taso bawa tumbinta tana cikin ci ta taji sautin tari sai da ta zabura ta miqe ta sauke kallonta akan sumayya dake ta kwasan barci a bisa kujera.
Ita sam bata lura da itaba.
Tari sosai takeyi zuwacan ya lafa mata ta gyara kwanciya tana shafa qirjinta.

Murmushi bahijja ta saki tana mai cewa "masu ciki manya, ni danake son zuwa duba jikinki shike ke kika rigani zuwa kenan.

Abincinta tacigaba da ci bayanta kammala ta kaisu kitchen ta wanke sannan tazo tazauna ta kwantar da fuskan kan na Sumayya.
Sai ji tayi ana shafa mata kai ana magana ahankali "honey Allah tarinnan yana takurani wurin barci, kanemomin maganinsa ko ince nafasa haihuwarma abokin.
Dariya Bahijja tasa sosai. Afirgice Sumy ta falka tana sauke numfashi "affuwan mmn twins, harara Sumy ta watsa mata tana cewa "kunwani qule cikin d'aki anata sallama ba wanda yaji kuna can manne da juna kamar daren jiya ba amanne kuka kwanaba duka bahijja ta kaima "ke dai kam Allah yashiryaki "Amin tare da ke.
"Sis ciki yafara girma masha Allah, murmushi tayi tare damiqewa tace bari in sallah inzo kisha labari "ok tan inajiranki mmn 12 dariya suka atare.


Suna zaune suna hiran zumunci bahijja ta dubi Sumayya tace "sis mizan dafa miki sabida ni couscous nayi kuma nasan bakya cinta "uhmm ke rabi dani bakomi nake iya ciba yanzu ta janyo bag dinta ta zuge ta fiddo ledar masara dafaffiya ta turawa Bahijja ledar tace ga abincina nan muci tare ko kema qila yau azurami miki na 'yan 10 hararanta tayi kawai ta dau masaran ta bare tasoma ci.

"Ke dai bari kawai adda B, wai yaya Mujaheed zai yi aure amma bamu saniba har saida yau naje gida naga ana shirin kai kaya dana tambaya aka cemin na auren yaya Mujaheed ne kuma yauma saura saki biyu.
"Sati biyu fa sis? "Kwarai sa gaske adda B, saura 2weeks. "Tafdi jan amma su umma basu kyauta mana ba ace abi namu sai ana saura sati 2 zamu sani "uhmm nima haka nacewa mummy shine take ban haquri wai shi yayan ne yace kada afada mana yanason zai bamu mamaki ne,
wallahi don haushi ni ko zama banyiba ina gaidasu nayo gidanki.
"Ayya sannu sis "yawwa.
To amma yaya Bashir yasani ko? "Bazai rasa saniba sabida na lura da rashin zamansa agida yayi yawa yanzu danayi qorafi sai yacemin wai babban abokinsa ne zai yi aure koda nanemi jin sunarsa sai yace wai bansan shi ba.
Bahijja ta ja numfashi tace "to Allah sanya alkhairi ya kuma basu zaman lafiya "Amin.

Sai bayan magriba Sumy ta tafi kamar kada surabu da juna haka suke duk in sun hadu basa san rabuwa.

Sai da tagama duk abinda takeyi ta hau gado ta janyo wayanta tana duba lokaci taga har 10:00pm Bilal bai shigoba alhalin sallar isha'i ma gida yake yinta, taja qaramin tsaki tasoma kiran number nsa qara biyu ya d'aga yana cewa "queen ya akayi ne? taqi cewa komi sabida da haushi jin tambayar rainin sense da yayima. Shi ya qara cewa "Ok sweetie ina zaria gidan mama yalwa bazan sami dawowa yau.... ta tari nunfashinsa cikin fad'a tace "kaga malam banson kwane kwane kawai kacemin katafi zance wurin budurwanka "a'a princess bahaka bane tsaya kiji tayi hanzari kashe wayar batare da ta saurari mizai ce mata ba.
Sai kuma ta lalubo number n Mujaheed ta danna masa kira.

Daf da zai cinke ya d'auka bako sallama yasoma da cewa"la la la laa!! Ke ina kikabar mijinki? cikin darennan mai ni'ima wanda nasan ma'aurata duk sunanan tare cikin bargo manne da juna suna raya daren anbarmu gwafraye agefe sai tunani mukeyi da jin inama inama mune su.
Wani kunya yakamata takasa ce mishi komi can ta kuma jiyoshi "ko yau kina period ne? Cikin shagwaba tace "uhmm nidai yaya jaheed kabari, "to nayi shiru matar jarumin maza saraki tasa dariya sannan tace "ashe kakusa shiga sahun manya? To Allah yabada zaman lafiya "Amin taji ya amsa amma muryanshi tayi qasa.
"Sai dafe yaya "ok Allah tashemu lafiya "Amin.

Suna gama wayan Mujaheed ya dafe kansa afili yace "kai so bala'I ne jifa ita muryanta ras cikin kwnciyan hakali amma ni kullum ina tare da tunaninta, kai jama'a wannan shine so cuta, ya fada bed yayi rigingine dana kallon ceiling.

Itama Bahijja tunaninsa ya dawo mata sabo fil sannan tariqa jin kishin auren da zaiyi sai kuma tasoma istiggifari.

Haka dukkansu suyi barci tare da tunanin juma hatta da Bilal shima da tunanin dawa Bahijja take waya haka da uban darennan sabida yayi ta kiranta yana jin number busy.


Washe gari da hantsi Bilal ya dawo tana kwance parlour yayi sallama ta amsa mishi tare dayimasa sannu da zuwa ya amsa yana yimata kallon qurullah "waye yakwana agidannan jiya ya tambayeta yana cin magani"ni ce man, ko kakawo wata ta tayani kwana ne? Harara ya watsa mata yace cewa zakiyi "na kwana da waninka.
Gano inda ya dosa yasa taji wani jiri na dibanta tayi saurin kwantawa dafe da kanta shi kam dakinsa ya zarce yana ta fad'e fad'e kamar wanda yaci duwawun kaza sanda take kyar kyaran kwai.

Tadad'e zaune sannan tamiqe tanufi dakinsa.

Yana kwanka sanda tashiga tazauna harya fito bai kalli inda takeba yasoma shafa mai har yagama tana zaune kanta a qasa sai da taga yana shirin fita tamiqe ta tari gabansa tana mai kallosa sama da qasa sannan tace "lallai dan adm butulu ne wato ni Bahijja kake jifa da kalman zina ko? wa'iyazu billah, banyi zatoban hakaba agareka, Bilal zaiyi magana ta d'aga masa hannu "ban sonjin komi daga bakinka amma kasani ni nafi qarfin wulaqancinka kuma zargin dakayimin kaje kai da Allah sanna nibazan zauna a inda ake zarginaba don haka kasan abinyi ko in fadawa magabata na su d'au mataki.
Azuciye yace "kitafi man, kiyi tafad'a masun , nike riqe da aure dai kuma bazan saki ba sai dai ki mutu da aurena akanki kuma maganan qarin aure ne sai nayishi,
kebaki isa ki hanani ba, yawuceta fuww!! Ta bude murya tace "kadade baka auro mata 100 ba amma kasani kafara neman maganin wari mai kama da rubabben masai yayin da zaka sadu dasu domin inba haka ba bamai iya za da a jalinsa kusa.
Cak ya tsaya tare da juyowa zuwa inda take.
Kai hannu yayi zai kamota ta goce ya fizgota da qarfi ta fada qirjinsa ba shiri yasoma magana muryansa na rawa"dagaske kikeyi Bahijja kinajin qazantaccen wari a jikina shine kuma yake sakiyin amai? "Eh ta amsa masa kai tsaye "innallahi wa inna ilaihin raji'un!! Yayi ta nana tawa itama tana tayashi cikin ranta zuwan yace "to inko hakane dake kadai zan zauna tunda nafahimce ke din matar rufin asiri ce ta janye jikinta "a'a wallahi raham wai qiya digan liman, inzauna da mai min kallon ina bin maza wallahi ba zan zauna da kaiba katafi can kanemo irinka mai d'oyi kuma mai kamunkai ba irina ba don zai fi maka sauqi. Sarai yagane magana ta saqa masa amma sai ya share.

"Don girman Allah queen kimin affuwa sharin shaidanne "uhmm naji amma ni bazan zaunaba yaruntse idanunsa ya bude yaja baya cikin kaushin murya tare da nunata da yatsa yace "kada kita ko bakin get da niyyar barin gidan nan tam, daga haka yasa kai yafice zuciyarsa cike da rud'ani.

Kukane yazomata ta zauna anan wurin tayi tayi sai da tayi mai isarta sannan ta share hawayenta.



Saura kwana daya bikin Mujaheed, Bahijja tun ana saura sati take ma Bilal zancen tana son zuwa ana saura kwana biyu ne amma yaqi ce mata uffan gashi yau har sau kwana d'aya, tashirya kayanta tafito tasameshi zaune yana kallo ta zauna gefensa ya juyo yana kallonta yasaki murmushi ya kai hannu yashafi fuskanta ta kauda kai gefe ya juyo da ita yace "queen wai har yanxu baki haqura da zuwa bikin horn. Qato nan ba ko? Ta hade rai sai yanxu takejin haushin sunar, tace "eh yanzuma fadama nazoyi zan tafi "ba inda zaki!! Yafada cikin tsawa taja baya tace "sabida mi? "Ra ayina ne hakan "na raba zumunci ko mi? "Ban sani "ok ko don kada inqi dawowa shine zaka hanani zumunci? Yayi mata banza tamiqe ta janyo trolley dinta ta iso kusa dashi tace "ayanda nakejin raina yau banga mai hanani fitaba sai ikon Allah "to yayi amma jirani inzo ya shige dakinsa bai dadeba yafito da paper ya miqa mata "gashinan na sake ki saki daya sabida bazan yarda ki tafi ki tonamin asiriba alhalin nasoma neman taimako akan matsalata kisa koda na warke ariqa zundena ana cewa ga mai wari can.

Wasu zafafan hawaye ne suka zubomata taba damu data share suba

Please Login or Register in order to submit comment