Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne.

Bilal yana son Bahijja sosai kuma kaf gidansu sun sani amma ita bata bashi fuskaba ganin tayi qanqanta da zance kuma ita batason yin aure agarin sam sannan tana da burin samun ilimi mai zurfi wanda tasan in tana garinnan bazata samu yadda take soba.

****** taro yayi taro masu muqamai da dakkatai makwaftar qauyen da kantomar yankin duk sunzo.
Angabatar da addu'oi tare da kiran dalibai suyi karatu da kuma bawa masu hazaqan cikinsu kyauta. Bahijja tasamu kyaututtuka masu yawa sabida hazaqarta. Itama Nana da maryam sun sami irin tasu. Aqarshe aka kira limanmin garin ya rufe taro d addu'a.

Malam yayi muryana sosai ganin su Bahijja sunyi sauka wanda atarihin gidan a yanxu ba yaron da ya sauke komi sabida basa son karatun, sanan iyayensu basa matsama musu dasuyi, zuwan Bahijja ne sukaga tanayi sannan qananan suka soma binta. akullum malam na alfahari da zuwan Bahijja rayuwar gidanshi.
Yanzu yasami abinda yakeso na ganin tayi sauka don haka zaiyi qoqarin ganin yasadata da mahaifiyarta ko da Lanti bata saniba kuwa.
'Daukan hakkin yayi yawa ace tsawon shekaru bakwai bataga uwarta don rashin imani.

*mrs j moon*
[2:38PM, 7/5/2017] mrs j moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya
*06*
Yauma xaune suke qasar bishiyar d'orawa suna cin abin break dasuka sayo.
Bahijja ta dubi maryam tace "don Allah zanbaki littafan yaya Bilal ki kai mishi, kice mishi na gode yabaki wasu ki kawomin. "Tam kawo insa cikin bag kada in manta. Ta miqa mata, maryam tayi quri tana kallon books din sannn tace "amma lallai yaya Bilal naji dake "kamar yafa? Tana tura littafan a bag ta amsa "da yabaki aron books dinsa dayakeji dasu domin akansu sai da ya doki Munirat don kawai ta d'auka ta karanta, dalilin dayasa taqi zuwa hutu wannan karan gidanmu.
Baki Bahijja ta tabe ta kauda fuska gefe "to ai can tamatse mata kuma, dariyan zolaya maryam tayi "uhmm kedai qawata kodai kishin ya motsane? Tana hararanta "kishin wa kuma? "Na yaya Bilal man, sabida naga abu daya kuke aikatawa ke da Munirat, aduk sanda na ambaci sunar daya a gabanku. "Ke ni nafada miki bazanyi aure agarinanba, inkuma yayanki nasona sai ya jira in gama karatuna sai yabiyoni gaban ummata. Marym tasa dariya "to aishima karatun zaiyi kuma maimartaba yasa mishi gida a kano, agidan yake zaune yan karatu kuma gidan mai kyau sanda mukaje nagani. "Uhmm lallai anaji da yayanki kam "soma kuwa domin shi kadaine babba namiji a gidanmi manyan duk matane. "Aikam a soshi dayawa cewar Nana.

"In munsami hutu zantafi gidan qanwar Abbanmu.maryam tace dasu cikin fara"a Bahija tace "kai haba? "Allah kuwa. "To Allah yakaimu amma zakibamu kewa kam

"Wani gari nana ta tambayeta. "Zaria "ayya aibama nisa "eh babu, gidan su Munirat zani innaje zance Bahijja na gaisheki, murmushi Bahijja tayi tawai bamiqe tana cewa ban aikekiba wallahi.
Sun taso zasu koma gida Nana tace "wallahi inaso inje birni inga irinta, dama nice ke Maryam nake da dangi acan da innatafi baxan dawoba saina zama doctor Nana yusuf imam. Bahijja tasa dariya har tana duqawa, maryam ta kaimata duka abaya tace "Allah bahijja ke muguwace bakya dariya sai kinga mugunta kuma baki saniba dariyan tafi yi miki kyau sabida inkinayi kumatunki duka na lotsaya kuma wushiryanki sai yafito, hakan naqara miki kyau dama zaki tayin dariya haka. "Tunda gani shafan almatsutsai ba, tace tana hararan maryam aiko Nana tasa dariya itama tana mai maita kalmar almatsutsai.

Maryam tace "Allah batun gaskiya koni ina son zama abirni inyi karatun likita nima naji ana kirata da doctor Maryam Ahmad sarki.
Bahijja tayi murmushi tare da cewa to "Allah yacika muku burinku "Amin tare da naki.
"Ni burina inga ummata tare da yayana, nasan inaganinsu rayuwa zai sanza, karatu nasan saina ture nace nagaji dayi. Atare suka ce "to Allah yacika miki burinki "Amin.

Suna shan kwana sukayi kicibus da Bilal. Maryam ta qarasa wurinsa cikin murna tace "yaya bilal yaushe kadawo? Yana jifan Bahijja da murmushi ya amsa "yanxu na shigo ko gida ban isaba na hango ku natsa in kai gaisuwa wurin sarauniyata. Bahijja ta boye fuskanta tace "sannu da zuwa ya hanya? "Lafiya lau. Suka gaisa da Nana maryam ta amsa bag dinsa tayi gaba tana cewa "sai kazo, "a'a jirani acan dandamalin yanzu zanzo ta amsa "tam.
Nana tayi gaba itama ta tsaya jiran Bahijja.
Yana shafa sumar kansa yace "Sweet Queen ya karatu kuma, dafatan kunkusa yin hutu? Kamar batason magana ta amsa"Alhamdulillah, netx week zamuyi insha Allah " good gimbiyata, kungama exams kenan "eh yau mukayi last "ok dafatan yayi sauqi? Tasaki murmushi sannan tace "hausa cefa ba wuya shima murmushin yayi yace "kunraina hausa sosaifa. Tayi gaba tana cewa a'a bahaka bane baya da wuyane dai" to haka akeso ai.

Ciwon ciki yahana Bahijja sukuni tun daren jiya har wayewar gari tana fama.
Gwg bintu ta fahimci al'ada zatafara domin haka Nana tayi mata watanni biyu dasuka wuce.
Gashi malam bayanan kuma Lanti tasa jaraba sai tafita tallan fura ganin malam yayi tafiya sai ta dafa furan da yawa amai makon kadan da takeyi agida yaqare.
Kuka Bahijja keyi na azaba tana cewa dada kikaini wurin ummata xanmutu caraf sai akunnin Lanti tashigo dakin tasoma dukanta tana cewa wallahi ke da ganin uwarki sai a qiyoma in kuna da rabon haduwa, bintu tayi watsi da ita gefe tana huci tace "kina qara tabata zan nad'amiki dukan tsiya!! Idanu waje tace "nidin bintu zaki buga? "Eh kefa Lanti. Lanti ta miqe tafice ganin bintu tana daf da bata najaki.

Haka Bahijja ta kwana biyu tana jinya sannan ta warware. Gwg bintu tayi jinyarta sannan ta tarasu ita da Nana tayi tamusu huduba na sukare mutuncinsu domin shine abin tinqahonsu tare da martabansu.
Kwanan malam uku yadowo, ana ta yimasa oyo yo yana tambayar ina bahijja? ta fito daga kitchen duk idanunta na xubar hawaye sakamakon gwg Lanti batanan kuma tabarmata aikin fura gashi itace danyene ko ruwa yaqi tafasawa.
Muryanta na rawa ta amsa "gani malam kadawo lafiya? Bai sami amsa mataba baqon dasuka shigo dashi yace "innalillahi beauty!!! Kece kika koma haka? Arazane ra dago kanta tayi arba da wani dangayun saurayi sai qamshi ketashi jikinsa.
Fuskansa take kallo kamar tasanshi amma tamanta inda ta sanshi."bakigane yayanki Bashirba ko beauty? Tanajin haka ta rugo da gudu ta cukumeshi sai kuma tasaki kuka tana cewa "mutafi wurin ummata bazan qara kwana wurin gwg Lantiba.

*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.

*This page nakine Aminiyarta Madam Jameela A Ladan. Sosai nakejin dadin yabawanki agareni. Allah yabar qauna.Allah ya raya zuri'a yakuma barki da Alhajinki ke daya tilo har gidan Aljanna Amin*👏🏼
*07*
Rungumeta yayi sosai hawaye na zubo mishi cikin sarqewar murya yasoma magana "baxan barki ba qanwata, qafata qafarki yau insha Allahu. Zamewa tayi ta dago tana kallonsa fuskanta dauke da murmushi kuma ga hawaye yana xuboewa. Hannu yasa yana share mata hawayen yana kuma mata magana ahankali cewa yake "kibar xubda hawayenki hakanan domin yau kibar zaman qauyennan kuma yau jikin umma xaki kwana da yardan Allahu. Cikin murna tasaki murmushi tana qamqame hannunsa.

Bayan angaisa malam ya dubi Bahijja yace "nagodewa Allah SWA dayanufeni da cika miki alqawarin dana dauka naganin na sadaki da ummanki, fatana yanxu shine inkin koma kada kisa wasa akaratunki ki maida hankali sosai yadda nan bada jumawaba ace nazo taron bikin yayen haddarki kamar yadda akayi na saukanku. "Insha Allah zakazo malam nan bada jumawaba "to Allah ya nufa "Amin.
Bashir yabawa malam kyutar kudi masu yawa da kyar ya amsa sannan yayiwa sauran mutanen gidan kyauta suma gwg Bintu kuwa 50k yabata tare da yimata godiyan na jajircewa datayi na kuka da Bahijja alhali wacce alhakin hakan yarataya awuyanta tagaza yi.
Gwg Bintu tayi ta samishi albarka.
Malam yayi yai dashi su jira gwgnsu lanti tadawo sugaisa yace sam shi bazai tsayaba domin tayi mishi hauka zai takata baruwanshi da shirme sabida dahaka gudun afkuwan abu mara dadi gara ya wuce kawai indai ta dawo ace tajira zuwansa na biyu domin amsar gadon da tamatsa aka bata na Bahijja don kula da lamarinta amma taqiyi mai makon hakama sai ta maidata baiwa mara gata.
Ganin ransa abaci yasa malam yayi ta tausansa har ya sakko.
Bahijja da nana sai kuka sukeyi da kyar aka rabasu da juna. Yayi musu sallama ya wuce suna tayi masa adduar sauka lafiya.

Daf daxasu fita garin maryam da Bilal suka wucesu a babur tana kwaltawa maryam kira amma batajiba ta koma ta lafe cikin site tana cigaba da zubar hawaye sabida ganin maryam da yayanta yaqara tunzura zuciyrta cikin kewa.
Bashir ba hanataba har sai tayi mai isarta ta haqura tana sauke ajiyr zuciya zuwa can barci ya kwasheta.

Har suka iso birnin zazzau bata farkaba. Shagalinku hotel yashiga. Har yagama abinda zaiyi akabashi key din daki number l04 sannan yazo ya dafa kafadanta ya girgiza kadan ta bude idanu wanda har suntasa don kuka. Murmushi yasakar mata yace "oya fito budurwan qauye mai barci amota, salati tayi sannan tace "wai har mun iso kenan? "A'a tukunna dai.

Babban parlour mai dauke da 1bedroom sai toilet yashiga da ita. "Zauna inzo yanzu 'yar qanwata. Kai ta gyada tana qarewa parlour n kallo.
Bai jumaba ya dawo dauke da kedoji manya biyu, ya zubesu agabanta yana kallonta cikin kulawa yace "tashi kiyi wanka sannan muci abinci ko qanwata? Ta motsa bkinta ahankali ta amsa "toh.

Fes tafito cikin riga da wando na Pakistan purple colour tayi rollin da mayafinsa tafito kamar 'yan hindustan *hhhh lol*
Sai qamshi takeyi abinta,gabadaya ta sanza kamar ba itaba, hatta Bashir yasha mamakin ganinta domin tayi wani haske sosai ta saje da 'yan birni kamar ba dazun nan take 'yar qauyeba, ya jinjinawa tsafta da kyalliya na gyara mutum cikin qanqanin lokaci.

Suna gama cin abinci suka fita basu zame ko inaba sai *Jamcy beauty saloon*

Ba bata lokaci akawanke mata sumarta sai kyalli keyi dama gashi da tsawo tare da cika sannan aka wanke mata qafa tare da yanke mata farce, ai tuni Bahijja taqara sanjawa sosai ta koma 'yar gayu hatta da ita kanta sai kallon kanta takeyi a mirror.
Ahanyarsu na dawowa masaukin su take tambayar Bashir nan kuma wani gari ne? "Birnin ilimi kenan wato Zaria takama baki cike da mamaki tace "ikon Allah dama nanne Zaria? Lallai tacika birni, Bashir yasa dariya ganin yadda take maganar tare da kama haba "ai sai mun isa kano sannan kiga birni na sosai qanwata "kai ta gyada tare da cewa "to yaya yi sauri mu isa kanon sabida Allah naqosa inga ummata da yaran dakace ta haifa. Dariya sosai yasa sannan yace "sai gobe in Allah yakaimu zakiga umma cikin hanzari ta tareshi "sabid mi?"munyi dare yau domin da tafiya kafin mu isa dare yayi kuma ni banason tuqin dare "ok yaya na fahimta "good girl yace yana sa signer zai shiga hotel din dasukayi masauki.

Misalin 9:00pm suna xaune suna kallo Bahijja tace "yaya kiramin umman mugaisa to" tam qanwata yar qauye ta batata rai tana tura baki yasa dariya.
"Ga umman to yace da ita sanda yaji alamar an dauka cikin zumudi ta maqala akunni tasoma sallama sannan ta dan russuna kamar tana kallonta ta gaisheta.
Sosai suka sha hira kamar ba kudi suke ciba domin har Abba da abokiyan zamanta sai da suka gaisa da ita. Aqarshe tamiqawa Bashir wayan shima sun dade suna magana sanan sukayi sallama.

"Yaya mai mi yasa umma bata taba zuwa ganina acan ba sam? "Yayi jim sannan zuwa can yace "tacemin tanayin kewarki amma watarana kuma sai ta manta dake sannan tana son zuwa wurinki sai wani uzuri yazo ya dauke mata hankali ta manta hatta da Abba mijinta shima yayi qoqarin suzo sai duk su shafa'a sai bayan wani lokaci su tuna.
Cikin hawaye tace "Wallahi duk sharrin gwg Lanti ne dama tasha fad'a min wai ni da ganin uwata sai a darul salam inmuna darabon haduwa. " ta Allah ba nataba, muguwar banza kawai; ai ina shirin zuwa daukoki na hadu da malam akasuwar kwari yana tambayar shagon Alhaji sulaiman mai fata inaji nazo wurin ganin kamar yagaji kuma mutumin qauyene sannan wadanda ke tambaya sai shirme suke mishi.
Najashi gefe ina mishi tambayoyi yana kallona naji yasaki hailalah yana kama haba, sai jinayi yace "kai jinin Bahijja ce tabbas, injin ko kaine bashir? Cike da mamaki na amsa "eh.

Gida nakaishi bayan ya huta yace tunjiya yake yawon neman gidanmu nace bwand zaigane kwatancenka kuwa. Kwanarsa biyu muka zo dama yazo ganin wurine sai ya koma ya zo dake. "Allah sarki malam.Allah yabiyaka da Aljanna "Amin

Washe gari qarfe 8:32am suka dauki hanyar kano, duk garin dasuka wuce sai Bahijja ta tambayi sunarsa wani yafada mata wani yace baisaniba shima.


Dawowar gwg lanti....gari kwara kwara.....🤔

*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.
*08*
Abujajan ta iso sakamakon yaronta musa da yaje ya fesa mata abinda ke faruwa. Tun asoro gwg Lanti tasoma yarfa ruwan bala'I, hindu ce ta tareta tana cewa "haba gwagwgo kibaryin haka, sai kace ba matan liman ba, kai don Allah nibanjin dadin abinda kikeyi kam. Tazaburo kamar zata make hindu tace "nace uwarsa liman din da duk wanda ya rabeshi, hindu taja baya tana qunshe dariya ganin yadda hancin gwg Lanti ke budewa da tsukewa yayin datake bera tsiya ga bakinta na fitar da kumfa kamar taci soap.
"Kinma ubanki dariya 'yarbanza mara zuciya wanda bata kishin uwarta sai na wasu, ban wuri ko in takemiki wuya ahuta, dasauri hindu ta matsa. "Ina kike? Uwar kinibibi, muna fuka akwadaita to za kibani kud'in dayabaki duka tunda ba daga dangin maharba 'yan daji ya fitoba.
Gwg Bintu tayi barin iska da ita. Tayi ta ruwan jarabarta bawanda ya kulata. Hindu ganin taqi yin shiru yasa ta ja mayafinta tayi gidan mijinta tana mai adduar Allah yashirya mahaifiyanta tabar masifa.

Da dare tasawa malam bala'I sai ya fada mata dalilinsa narabata da 'yar dan uwanta uwa daya uba daya.
Baiso tankamataba amma jin tayi tambaya yasa kai tsaye ya amsa "sabida baki cancanci ruqon marayaba, xalinci da cin amanarki akanta yayi yawa, shin ko kina tunanin bansan kinyi surkulle kada wanda ya tuna da ita ba balle azo ganinta, to karkade kunnenki ki saurareni da kyau!! Ni!!! yusufu nakarya komi da hannuna sannan nayi sanadiyar komawarta cikin gatanta. Jiki a sanyaye tasoma borin kunya tana kumfar baki "sharri kakemin kuma kasani gobe kamar yanzu tana gidannan domin zanbi indawo da ita tunda jinina ne bamai rabani da ita.
"To yayi Allah ya kaimu sai inbaki kudin motama kiqara guzuri amma kisani Bashir soja ne zai iya harbeki har lahira kuma ya harbe banza wofi, inkin shirya mutuwa batare da wada taccen istiggifariba to gobe kibisu garin kano, mudai iyakanmu adduar Allah yaji qan musulmi. yana sa aya ya shige d'akinsa yabarta tsaye gabanta na dukan 30~60 hhhh.

Cinkin tsoron mutuwa ta kwanta. Washe gari tayi gum da bakinta batare data qara zancen dauko Bahijja ba.

*Gwg Lanti mutuwa dole ne kam*

10:00am suka isa birnin kano, ta dabo tumbin giwa Jalla babbar hausa ko da mai kazo anfika. *uhmmm ni nace zazzau tafita komi ehee*😏

Cikin murna ummata ta runguneta sai kuma kuka ya kufce mata itama Bahijja n kuka takeyi na murnan ganin ummanta.
Abba yace "to miye na kuka kuma kamar wata yarinya, Hajiya hauwa ce ta janye Bahijja tana share mata hawaye, ahankali take cewa "kukan ya isa haka, ta dubi wata yarinya wacce bazata wuce sa'ar Bahijja n ba tace "Sumayya tafi da ita d'akinki tayi wanka ta huta domin tasha hanya tagaji "to mummy.

Iyalan gida duk suna zaune afalon Abba, bayan angama cin abincin rana. Abba ya nisa sannan yace "Alhamdulilah Allah mungode maka da kanufemu da dawowar yarinyarmu cikinmu bayan barinta ciki na tsawon wani lokaci. Yanisa "Bahijja ta amsa "Na'am Abba "kigafarcemu narashin zuwa inda kike kidauka haka Allah yaso tun fil'azal sai kinyi rayuwa acan. "Bakomi Abba nasan kaddarace zamana acan kuma na dauka. "Allah yayi miki albarka "Amin suka amsa baki dayansu.

"Ga 'yan uwankinan Mujaheed, Bashir, Sumayya sai khaleefa da kuma khadeeja. Auntynku Asma'u tayi aure itama zaki ganta gobe da yar dan Allah. Yajuya yana kallon yaran "ga Bahijja nan tadawo cikinku don haka ina son hadin kanku duk da nasan bana da matsala awannan fannin duk da haka inaso kubata kulawa sosai kamar yadda kuke kula dasauran 'yan uwanku, kuna jina? "eh Abba"to madallah Allah yayi muku Albarka suka amsa "Amin.

Tana zaune gefen umma wacce take bare mata orange tana sha. "Umma dama wai Abban su Sumayya kika aura? Batare da ta kalletaba tace "eh shine, ashe baki mantashiba? "Eh umma naganeshi, abokin Abbanmu mai yawan kyauta. Sosai umma ta yi mamakin rashin mantuwa irin na Bahijja tace "lallai kina da riqe abu sosai, dariya tayi tacigaba da shan fruits dinta.

Bataji Sallamaba sai ji tayi anja hannunta "inata magana kina tunani, to zo muje kasuwa ki zabo kaya mummy najiranmu. Binta kawai tayi batare da tace komiba, dama tana sanye da qaramin gyale ajikinta.

Mujaheed ke jan motar, Sumayya na gefensa, mummy da Bahijja suna baya.
Sai janta da hira mummy keyi amma takasa sakin jiki, Sumayya najinsu tana dariya ganin yadda mummy ke surutu amma Bahijja sai uhmm take cewa.
Bahijja kuwa Mujaheed ne yasa mata ido fa zaran sun hada ido sai ya dalla mata harara yana mazurai ita kam alokaci daya taji yana bata haushi, don haka dasun hada ido itma sai ta harareshi kuma ta murguda mishi baki. Ahaka har suka isa kasuwa suna hararan juna bawanda ya lura da su cikin mummy da Sumayya.


*Autar gwagwgo (mamie waru) wannan shafin nakine. Allah yabar zumunci,nagode da kukawarki sosai*


*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.

*09*
Siyayya sosai mummy tayi mata, sun d'auki aqallah 3hrs acikin kasuwar sannan suka fito.
Zaune cikin mota suka sami Muhaheed yna sauraron karatun AL-QUR'ANI mai girma daya kunna, Manshawiy yana jan qira'ar sa cikin suratul TAUBAH. Yajasu yanayin qorafin sun dade, mummy tayi masa daquwa "gidanku nace sarkin wutar ciki, d'an murmushi yayi tare da duban Sumayya yanayimata magana qasa qasa sukasa dariya "gulmanmun banza mummy tace dasu.

Shiru sukayi dukkansu suna sauraren karatun.
murya qasa qasa Bahijja tasoma bi cikin k'warewa, ta kwantar da kanta jikin mummy.
Mummy tana kallonta tana murmushi a ranta tana mamakin yadda ta iya karatu haka alhalin tana qauye, sai kuma ta tuno mijin gwagwgonta ai limami ne, Don haka ba abin mamaki ba ne don tasamu ilimin addini.

Mujaheed ya saita mirror saitinta sosai yana kallon yadda d'an qaramin bakinta ke motsawa ga idanunta a lumshe gashinsu zara zara, goshinta suma ta kwanta luf luf, alamar atana da wadatacciyar suma akanta.
Baisan sanda yasaki murmushiba ya sa hannunsa yana sosa sumar kansa yana cigaba da murmushi.
Ajikinta taji ana kallonta, tako bude ido tar ta saukeshi akanshi, ya sakar mata murmushi ta daure fuska tana hararanshi saikuma tayi shiru ta bar bin karatun.
Mummy ta dubeta cikin kulawa "cigaba mana Bahijja, muryan tanamin dadin sauraro "ahankali tajuya fuskanta tana kallon titi, tacigaba da karatunta. Sumayya kam kwantawa tayi tana son yin barci sabida ta gaji sosai.

Saida suka biya shagon telarsu suka bashi ya dinka mata kayan sannan suka isa gida.

Kwanarta hud'u Abba yasa Bashir yayi mata registration a makarartan hadda wacce take hade da islamiyya, tasoma zuwa tare dasu Sumayya. Ta maida hankalinta a karatu sosai, sannn tana taimakawa qanninta wurin koyamusu karatu tundaga na islamiyya zuwa na boko.
Shi yasa sukayi shaquwa mai tsanani dasu.

Zuwa yanzu Bahijja anzama 'yan gida, ta saba da kowa na gidan, kowa agidan na sonta domin tana da shiga rai, ga ladabi da hankali, Sun shaqu da Sumayya sosai, haka mummy, komi tasamu sai tace Bahijja amsa Sumayya tayi ta qorafi, wai tafi son Bahijja ita kam dariya takeyi mata intaji haka.
mummy tayi ta qara tunzurata har sai tayi fushi ta tafi part din umma, itama acan umma zata karramata, tayi tama Bahijja kwalo. Haka suke rayuwarsu abin sha'awa da burgewa.

Kaf gidan Mujaheed ne kawai basa wani shiri da shi.
Ko hira takeyi dazaran yazo wurin zatayi shiru haka in nushadi takeyi da ta hangosa zata hade rai tabar fara'a. Haka kawai takejin haushinsa aranta, sam jininsu bai had'uba.

Shi kam dariya take bashi sosai intana cin magani kuma duk bata ranta dazatayi inyaso sai yajata da fada kawai don yaji muryanta sabida shikam muryan ta nayi masa dadi, asannu yake fita koda kuwa fad'a takeyi. wanda shi ke janta fad'an inda ke cemata budurwan qauye ita kuma bataso sam, shi yasa bata damu tace mishi yaya ba sai dai in agaban su umma ne.

Sanda aka koma makaranta Abba dakanshi yagama komi na karatunta, ya nemi abarta ajin da take ss1 dama ajin daza shiga kenan, sunce sai sunmata interview.
Mujaheed yakaita, yasha mamaki dayaga ana tambayarta tana watso amsa bako gargada. Gashi turancinta mai kyau, da dad'in saurare, su kansu malaman sunji mamaki tare da yabama kwazonta kamar ba makar government tayiba. Atake suka bata aji ss1 science.

Ahanyarsu nadawowa yayi tajanta da hira tayi mishi shiru yaqarata surutunsa bace dashi cikan kaba. Hasalima ita haushinsa takeji agefe daya kuma zuciyarta tafad'a kogin tunanin Bilal ne.


*Haermeebrah (Hameeda) wannan shafin nakine,ina jin kinfi kowa son labarinnan, don haka ina godiya da yabawarki Allah yabar so da qauna Amin.*



*mrs j moon*
[9:56AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*
©Safiyya.

*10*
Bilal baisan Bahijja tabar garinsuba sai bayan kwana biyu awani yammaci ta ranar Alhamis.
Tsaye yake yana feshe jikinsa da turare na incidence, sai murmushi yake dokawa xuwacan ya gama ya dubi kansa a mirror ya jinjina kai afili ya furta "yau gidanku zanje my Bahijja sabida kada natsaya kallon ruwa kwad'o yayimin qafa.
Sai kuma yayi jim yana tunani, nasan baza ta fitoba amma bari infara ganin malam wata qila zai ciyo kanta tafito insoma kafa gwabnatina da tushe.
yana kaiwanan atunaninsa ya saki murmushi har da tsalle. Sallamar Maryam yasa ya natsu tare da amsa mata tashigo jiki asanyaye tasami gefen bed tazauna tana jan hanci alamar taci kuka domin idanunta har sunkoma kalan ja.
Zuba mata ido yayi yana nazarinta sannan yace "ke da waye haka, har idanunki suka sanja launi don kuka? Cikin son kuka ta amsa Bahijja ta bar garinmu har abada, batare da munyi sallamaba, taqarasa maganar tana share hawaye. A firgice ya dafa kafadanta yana jijjigata "wata Bahijjan kike magana akai maryam? "Ta gidan liman, yasaketa yana dubanta yakasa cewa komi. Ahankali tacigaba da cewa "kasan kwana biyu bana da lafiya banje islamiyyaba to yau danaji sauqi sai nace bari inje gidansu inji dalilin dayasa bataxo dubaniba alhalin taga bana zuwa makaranta, ina hanya zanje nahad'u da qanwarta Nana shine take fad'amin itama taso zuwa ta fadamin Bahijja yayanta yazo ya dauketa amma Allah bai nufaba.
Bilal yakoma ya zauna bisa stool ya dafe kansa wanda ke sara masa, "wani gari takoma tace miki? "Ban tambaye taba "ok bari inje naga malam sai insamo address dinta

Please Login or Register in order to submit comment