Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"lafiya lau, ya hanya? "Alhamdulillah, ya kika qaraji da jikin? Allah yasa kaffa ne "Amin ta amsa tana hararan Munirat da tabude baki jin ana yiwa mahaifiyanta jajen ciwo Alhalin tasan lafiyanta lau.
Abban Munirat ya dau key din motarsa yafice, su Adnan qannin munirat da ita sukayi mishi adawo lafiya.
Mama yalwa ta miqe tana cewa bari na kawoma wani abu ka taba kafin agama dinner.
"Ina azumi ai yau mama "wa kakashe da kake azumi ba watan ramadam ko shawwal mukeba? Yayi 'yar dariya kadan sannan ya amsa "mama ban kashe kowaba, illah yau ina azumin lada ne ta ranar alhamis, "au natuna kuwa yau alhamis, to Allah bada lada "Amin.
Munirat haushi kamar ya kasheta ganin yadda mama yalwa keyi kamar wata sabuwar tuba, alhalin sarai tana da saninta.

Bilal ya kai dubansa gefen Munirat yace "bako gaisuwa ko 'yar qauye murmushi tayi ta sunne kanta qasa ya matso ya kamo hannunta yace "yau ni kikejin kunya kuma? Janye hannunta tayi ta matsa kad'an tace "hamma ya aiki da kuma sweetie n ka Bahijja.
Wani fara'a yasaki sannan ya amsa da "Aiki Alhdulillah, queen kuma tana lafiya lau, kingama na manta tace innazo in kiramata ita su gaisa da mama tayi mata ya jiki.
Kauda fuska tayi "ok bari inkira maka ita to, ta miqe tashige bedroom inda mama yalwa tashige.

mama yalwa sai kaiwa da komowa ta keyi ita kadai a daki tana ta zundumawa Bilal zagin "kagamin dan iskan yaro mai suffan carrot, dan banza kawai, aiko muzuba ni da kai, komawa zanyi abin da kai ta jininka in kayi nasaran zullewa wannan.

Sai daf daza akira magrib yabar gidan.
Bayadda mama yalwa batayi dashiba ya tsaya yayi buda baki anan ba amma yaqi yace yanxu yanason komawa garin kano ne sabida gobe da aiki.


*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.
*26*
Tsaye take a tsakiyar parlour tana kurban tea, tanayi tana kallon agogo, ganin tea din yaqi hucewa sai qonamata harshe yakeyi yasa ta kaishi dining ta ajiye tafice da hanzari.
Ta taradda Sumy zaune tana jiranta a cikin mota.
bude driver sit tayi ta xauna batare da bata lokaciba suka fice get din gidan ta cilla motar bisa titi.

Tana kallon gabanta tace "yau su ooo anyi abinkai, har jirana akayi.
Sumy ta dalla mata harara "kyace haka man 'yar rainin hankali, kin kwana soyayya da zuqalallen sarakinki kintashi amakare zakizo kinamin wani borin kunya don latsin hammata.

Dariya tasa tace "wallahi sis Sumy komi zaki kira saraki bazan damuba yanzu sabida kema kina tare da abin tsoro kuma fad'i ki qara da ihu munraba dare jiya muna shan hiran soyayya da habibina shi yasa natashi amakaren sai me? "Sai in jibgeki yanxu kuwa tafad'a tana cikin wasa, itama cikin wasan tace "to bissillah kayan qaton mutum mai qaton ciki.

Dariya Sumy tasa sosai cikin dariyan tace "Allah Adda B kina son qaton mutum mai tumbi sabida akullum inbakiyi zancensaba bakayajin dad'i, to yarinya ina baki shawara da ki bar wani d'an waken zagaye ki fito fili kifad'amin gaskiyan zuciyarki.
Bahijja tayi barin iska da ita, ganin haka Sumy cikin son tunzurata ta dafa kafad'anta tace "ok nagane kada kidamu yau zan sami yaya Mujaheed infad'a masa kince yadawo kan dutynsa sabida kingane gaskiya,
zuciyarki shi take muradi sabida ako da yaushe tana cikin begensa sannan gayawan mufarkinsa da kikeyi kullum dare.

Agigice Bahijja tace "a'uzubillahi minal shaid'anin rajin!! Allahumma ajirni da wannan baqaqen zantuntuka naki,
bakinki ya sari bed din barcinki kikoma gida kin gansa yayi rugurugu ba mamora.

Sosai Sumy take dariya har da dafe ciki, Bahijja taja tsaki cikin quluwa tace "muguwa mai fatan alkaba'i.
Sumy ta tsagaita da dariyan tace "aikomi zakice sai dai kice amma tuni nagnoki da duk wani kwane kwane naki, ke!! kisanima daga yanzu nabar kiranki kayan saraki kin koma sirrin jaheed d'an dama dama, sardidi mai 'yammata lodi lodi amma duk cikinsa Bahee d'insa ke haskawa a birnin ruhinsa. Don haushi Bahijja komi takasa ce mata.

Ahaka suka qarasa cikin makarantar.
Sumy nata tsokananar ta,ita kuwa tayi mata banza,
amma ranta kamar wuta domin sosai maganganun Sumy yabata mata rai kuma ta qudurce tana komawa gida zata turawa Bilal message akan ta amince ya turo magabatansa, atsaida lokacin bikinsu tafasa yin degree d'inma.
aurenta zatayi, dama shine darajan duk wata 'ya mace.


*** mama yalwa agaban sabon malaminta ta tankwashe qafafu kamar mai d'aukan darasin Allah da manzonsa.

"Malam so nike kabimin shi da jininsa ka qonamin zuciyarsa a allon qarfe ta yadda zaiji inba ya auri Munirat ba bazai iya rayuwaba.
Malamin yayi 'yan dube dubensa awani baqin qasa zuwa can ya d'ago kai yace "hajiya kiyi haquri ayi auren sabida na gani dole sai sun auri juna amma zan baki wani garin magani ki ajiye ahannunki har sai ana gobe ko ranar d'aurin auren sai ki juba mishi a inda zai taka kuma kizuba mishi awani abinda zaici ko sha, bayan gama bikin kizo ingamiza ayi a gaba domin asiri zaiyi wuyar kamasu, sabida dukkansu suna da riqon addini sannan basa wasa dayin addu'ar neman tsari ga kuma iyayensu natsaye akansu dayi musu addu'a.
Malamin yayi shiru yana karanto damuwa afuskan mama yalwa, yayi murmushi "hajiya ki kwantar da hankalinki yarinyanki fa dole sai ta auri yaron, nagani a bincikena kuma zasuyi zaman lafiya amma sai kinbi asannu domin yin gaggawa zai tona miki asiri sabida ita kanta yarinyan naki bata yarda dakeba tana sa ido akan dukkan motsinki, kuma ki sani yanxu shi yaron baya gabanta nasan ta fadamikan hakan ko? "Eh tafadamin malam "to kirabi da ita nasan yadda zanyi da ita takoma sonshi.
"To malam nagode sosai "bakomi hajiya, ga maganin ki adanashi da kyau sabida amfaninsa yakusa, naga zancen auren zai taso kwanan nan. "To malam sai nakuma dawowa.

*****tana zaune gefen gadonta ta zuba tagumi bayan tagama turawa Bilal message.
Har zuwa lokacin ranta abace yake kuma tarsa dalilin dayasa maganganun Sumy suka bata ranta haka alhalin tasha fada mata wanda suka fisu zafi.
Ta tura yatsunta cikin sumarta ta runtse idanu ta furta afili "kai amma sis Sumy ta cuceni yau tagama dani, in banda iskance ace tarasa wanda zatace ina mufarkinsa sai wani qato Mujaheed. Ta yamusta fuska tacigaba "to niko sarakina bantaba yin mufarkinsaba balle wani shagaluwan banza.
Taja sirrin tsaki ta kwanta rigingine tana kallon ceiling.
Sosai take son jin muryan Bilal dinta amma tasan yanzu yana tsakiyar aiki, ta saki murmushi ita d'aya tace "ina sonka yaya Bilal sosai a ruhina, Allah yabarmu tare da juna "ba Amin ba!! Tajiyo an amsa a bakin qofar.
Afusace ta juyo taga wani d'an shishshigin ne haka.
dama tasan ba wanda zai ce haka sai Mujaheed. "Kai asuwa to dazaka samin baki cikin maganata? Tace dashi, Yana murmushi yace "ni a mai iko da ke, zatayi magana ya daga mata hannu yace "niba rigima nazo muyiba, nazone ki rakani yiwa sabuwar budurwata shopping.
A d'age ta kalleshi samada qasa tace "indai sai kasami rakiyata zakayi ma wata banzar qatuwa sayayya to zaka shekara bakayi ba kuwa, domin ba inda zani.
Yasa dariya yanunata da yatsa yace "kai haba bahee badai kishi kike da sabuwar budurwan tawaba? "Allah ya tsareni da fadawa halaka, wai kishi uhmm da narako mata duniya kuwa, indai nayi kishinka.
Mujaheed ya daure fuska "to naji ya isa hakanan. Ya juya yana cewa "kiyi sauri ina jiranki a parlour, yayi ficewarshi cike da taqama.
Bayansa tabi da kallo baki bud'e sai kuma takoma ta kwanta. "Sai kazo kajani inje mugani.

Tsawon 1hr Bahijja bata fitoba.

Bakinta ature najin tsiya umma tasameta.
"Miye haka Bahijja? da xaki shanya mutum yanata zaman jiranki don shashanci bakiko shiryaba, to yimaza ki fito kutafi tun kafin in saba miki.
Tamiqe fuww ranta abace tafad'a bathroom.
Umma tabita da addu'ar "Allah yashirya ki. Can cikin bayin Bahijja ta amsa da "Amin!! Ummata.
Girgiza kai umman tayi tare da ficewa,fuskanta d'auke da murmushi.



*Mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

© Safiyya.

*27*
Qanshin turarenta yasanarwa da Mujaheed iso warta parlorn.
Ya juyo yana duban ta sama da qasa. Tayi mishi kyau ainun.
Sanye take cikin atamfa riga da zani kalan lemon green gyalenta tare da flat shoes d'inta duk kalan lemon ne, hannunta dauke da wata had'add'iyar fox fara sol, fuskanta ya qarewa kallo, duk da batayi wani kwalliyaba amma tayi kyau sosai, d'an mitsitsin bakinan sai kyalli yakeyi, shajenta tare da sumar daya wataci kanta sai suka fito suka kwanta luf luf, tabon sallarta dake bisa goshinta sai yaqara fitowa yayi mata kyau, kallo d'aya zakayimata yagano ita d'in wayayyiyace ta gaske kuma 'yar kwalisa.
Ajiyar zuciya Mujaheed ya sauke ahankali tare furta Subbanallah aransa.
"Nidai bancika son kallon haramun irin wannan ba ehe, tace dashi tana murgud'a baki, kansa yasosa cikin jin kunya ganin ta gano ita yake kallo.
"Ke dalla mizan tsaya kallo awannan jikin naki mara shape, harara ta watsa mishi tace "eh din naji ahaka dai ake muradi ni kuma nace kwalelen qato sai d'an siriri mai kyawun sura.
Hade rai yayi yana mata wani mugun kallo ya nunata da yatsa yace "wallahi duk ranar da kika kuma minzancen tsukakken yaronnan sai na baki mamaki, taja baya "aiko sai nayi tunda mijina ne banga mai hanani naganarsa, ya gyad'a "to shikenan muzuba ni da ke, ta murgud'a mishi baki tana hararansa.
"Umma sai mundawo, Mujaheed yace da umma yayin dake tsaye baki bedroom d'inta, daga ciki ta amsa "to Allah dawo daku lafiya "Amin.
Ya janyo hannun ta tana qoqarin kwacewa ya damqe da qarfi ta saki siriyar qara ya kalleta yasaki murmushi wata ta fassarashi dana mugunta.
Yana riqe da hannunta suka fito harabar gidan duk kuwa da qoqarin kufcewan datakeson yi amma ta kasa.

Aharabar gidan Sumayya da Bashir ne zaune a gefe suna shan hiransu irin ta ma'abota bege, fuskokinsu cike da annuri, gefensu kuma baby khadija ce ke wasanta acikin motar wasan yara.
Hannu ya d'awa Bashir yace "hy bros, ya maido mishi da jinjina yana murmushi, Sumy kuwa dariya takeyi tana fad'ama Bashir wata magana sannan ta had'e yatsunta biyu ta duno Bahijja, cikin haushi Bahijja tayi magana ahankali "zanci gidanku yarinya bari indawo, jin abinda tace da Sumy yasa Mujaheed sakin 'yar dariya tare da bud'e gefen driver yasata ciki yana cewa "hasken ruhina zauna da lafiya, harara tasakar masa tana qunquni.
shi kuma ya zagaya yazauna a mazaunin driver yayiwa motar key suka fice get d'in.

Sunyi tafiya mai nisa batare da kowa yace qalaba.
Ya dubeta yayi murmushi yace "wani super maket yadace muje? Ta yamutsa fuska tace "oho maka, kai ya kad'a yana kallon hanya ya amsa "to kice yau yawo zamusha without limit kenan da hanzari tace "kamar ya? Banza yayi da ita, tabi shi da harara kamar kwayar idonta zai fad'o.

"Allah ni in gantali kafitoyi to kayi hanzarin mai dani gida cikin sutura "in anqi fa? "Inma ihu kasato ni.
Dariya yayi sosai sannan yace "aiko zakiyi kyau da ihu, oya soma yi muji, ta murguda masa baki ya kanne mata ido d'aya yace "baby ina son irin wannan abubuwan da kikemin na tsiwa, sosai yake qaramin sonki da qaunarki a ruhina.
Ta had'e rai tare da kyauda fuskan ta, tana kallon gefen titi tace "iska na wahalar da mai kayan kara. Yana shirin magana phone d'inta yasoma ringing.
Ganin sunar da ya baiyana a screen d'in yasata sakin fuska tare da qayatacciyar murmushi ta kwantar da bayanta a sit d'in sosai tayi picking ta kanga a kunninta tana mai cewa "amincin Allah ya tabbata agareka ya habibina, acan gefen Bilal ya amsa "Amin tare dake mai mulkin zuciyata. Tasa 'yar dariya.

Dagan suka balle da hiransu ta qauna cike da shauqin juna, anan yake tambayarta qarin bayani game da message d'in data tura mishi d'axun, sai da ta kallo gefen Mujaheed taga hankalinsa yana bisa tuqinsa sannan tace "eh duk abinda kagani hakane tayi shiru tana saurarensa zuwacan ta kuma cewa "ok kada kadamu zan sanar da Abba yau da dare insha Allah "aha sai kajini goben ko cikin dare, love you always tace tare da mannawa 4n d'in kiss sai kuma ta rufe fuskanta tana dariya tare da zare wayar akuninta ta d'orata bisa cinyarta,
tana cigaba da murmushinta.

Wani uban tsaki Mujaheed yaja ta waigo tana kallon face d'insa, tasaki dariya ya dubeta a fusace yace "zan gyaramiki zama yarinya, kicigaba damin irin wannan dariyan "a'a kajimin mutum da iyayi, to ina ruwanka dani don nayi dariya zakace wani zaka gyaramin zama, sai kace wata 'yarka.
Kallonta yayi idanunsa sun sanja launi zuwa ja, tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa.

Baikuma yimata maganaba itama haka, har suka isa wani wurin shaqatawa yayi parking ya dubeta "fito mushiga, ganin yadda yayi maganar cikin d'aurewar fuska yasata fitowa ba shiri domin sosai yayi mata kwarjini, sai yanzu tagano lallai yayi kama da mummy sosai tagama kamar yafi mummy haske.

Jan hannunta yayi suka isa gefen swim pool suka zauna bisa wasu chairs tsakiyarsu wani d'an madai daicin table ne.
Basu jima da zama ba masu kula da wurin yazo tambayarsu misuke buqata akawo musu, ya dubeta ta kauda fuska, yace da mutumin "ka kawo ice cream roba biyu da malta kwankwani d'aya.

Yana tsotsan malta yana kallon fuskanta wadda yake asake tana ta kalle kalle da alama wurin ya burgeta.
"Kisha ice ceam d'in kada ya narke batare da ta juyo ba ta lalabo robar ta d'auka tasoma sha tana wani lumshe idanu.
Abazata tace "kai yaya jaheed wallahi kasan kan rayuwa, don Allah jiba wurinnan kamar a turai don kyau da tsaruwa ga kuma wani iska mai dad'i dake busawa kai, Allah wurinnan yayi ba qarya.
Shidai saurarenta kawai yakeyi yana muemushi, yanajin lallai komarsa takusa kama kifi.
"Yaya taso muzaya muga yadda wurin yake inna koma inbama sis Sumy labari da kyau. Shiru yayi batare da yamotsaba, ganin haka yasa ta miqe tana riqe da robar ice cream, ta ja hannunsa ya miqe yabiyota suka jera abinsu kamar cikakkun masoya na hakika.

Sunsha yawo sosai abinsu awurin tare da dayin pictures, ganin yamma ta gabato yasa yace da ita "baby mutafi gida yamma tayi "waye babyn? Tace dashi tana had'e rai, "au yanzu kika tuna kenan? Yayi mata tambaya shima.
Banza tayi mishi tayo gaba yabiyo bayanta yana cewa "rigimammiya kawai kamar baby khady.

Bayan sun biya fill d'insu suka fice. Awani super market ya parker yafito yayi gaba sai da zai shiga ciki ya waiwayo yaga bata biyo shiba, cikin takaicin taurin kan irin na Bahijja yasa kai yashige cikin super market d'in.
Baiwani jumaba yafito hannunaa d'auke da ledoji biyu babba da 'yar madai daiciya.
Ya bud'e back sit ya zubasu yakomo mazauninsa ya zauna ya tada motar. Sai da suka hau titi sannan yace "lallai nayarda kina jinkishin budurwan nan tawa sosai a ranki, tabe baki tayi tace "minayi na kishin? dazaka tasani da soki burutsun zancenka mara tushe balle makama.
Yasa qafasa ya take nata, sabida azba bata san sanda ta kaima kafad'ansa buguba ya zare idanunsa "kai kai Bahee!! Nid'in kika doka? Ta sunkuyar da kai cike da borin kunya tace "sorry, wallahi zafi naji har brain d'ita shiyasa bansan sanda na kaima buguba amma don Allah kayi haquri.
Kai ya jijjiga cike da farin ciki najin wai Bahijja ce ke bashi haquri cikin jin kunya,
akaron farko arayuwarsa da tataba yi masa magana cikin jin kunya. Ya cije lip d'insa na qasa yana ayyana lallai zai dage dafita wuraren shaqatawa tare da ita duk kokacin dake free.

"Bakomi babyna duk cikin so ne, yace da ita ta tsuke fuska tace "Allah ni bazanyi soyayya da kaiba, ni din sai sara.... da hazari ya kai hannunsa yabuge mata baki sannan yayi slow ya gangara gyefen titi ya dubeta cikin fushi yace "cire hannunki abakin!! Ta zare ido tana qara damqe bakinta duk da zafin dakema don bugun ya shigeta sosai. Ko bakiji minaceba!? Yafada cikin tsawa, Tazame hannunta kad'an tace mizakayi min bayan wannan bugun dakayimin wanda ke bara zanar maidani mai wawulo bakin qanan qare.

Ya d'ansaki fuska jin abinda tace, ya tada motar sannan yace wallahi inkika kuma kiran min yaronnan agabana sai nayi kissing din bakinki na 1hr don sai na kumburashi, halittanshi ya sanza zuwa zunguru kamar shantu.

Shiru tayi mishi tare da juya mishi qeya sabida taga take takensa ya wuce da saninta.

Ana kiran magriba suka isa gida, ya miqa mata ledojin yana cewa "babban takice qaramin kibama su baby khady, taqi karba ta tsaya kallonshi shima ita yake kallo, sai kuma ta kai hannu asanyaye ta amsa tace "su khady sun gode, tayi gaba tana wani juya mazaunai.
Sumarsa ya sosa ya furta "anka tafe kan sauqa.

Tana shiga parlor ta bude babbar ledar, kayan kwalliya ne da turaruka irin wand'anda take amfani dasu sai wani seat irin na Sumayya, tasan Sumayya ya sayomawa sai ta fidda mata gefe ta d'auka nata tanufi d'akinta dasu tana murmushi.


*in anga errors bansamu nayi edited ba ne,my b3 low*


*Mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.
*28*
Anaso ana kaiwa kasuwa!! Anaso ana kaiwa ka.... taji fass an taska mata duka abaya.ta tsaya cak da rawa tare da waqar dakeyiwa Bahijja na tsokana.
Mummy ta harareta ta kamo kunninta ta murda tace "shin intambayeki wai Bahijja kakarki ce ko mi? Cikin jin zafi ta amsa "a'a mummy, wayyo zafi mummy nabar tsokanarta daga yau Allah nabari, ta sakaketa tare da dankwashe mata kai tasaki 'yar qara "wayyo mummy zata maidani daqi qiya, tana sosa kai tare da liliya kunni duk alokaci d'aya.

Bahijja tana gefe tana kwasan dariya har da riqe ciki taga mugunta, mummy itama dariyan tayi tace "oya kubiyoni zuwa kitchen yau muna da baqi suka amsa "to.
Mummy nafita Sumy tayokan Bahijja ita kuwa ta kwasa da gudu batai auneba tajita ta buga mutum tayo baya zata fad'i yayi saurin tareta ya maidata qirjinsa yayi mata kyakykyawan runguma.
Jin qamshin turarensa tagano ko waye, da qarfi ta fincike jikinta tana hararansa, nata shirin magana ta tsinkayi muryan mummy tana cewa "wai ina kuka maqale ne? sarakan son jiki.
Da sauri taraba gefenshi ta wuce ya rakata da idanu.

Mummy tana nuna mata aikinta da zatayi Sumy ta shigo tana kyalkyala dariya "ke!! lafiyanki kalau kuwa daza kishigo mana kina wanan irin dariya kamar wata kwancen hauka, Bahijja ta kwashe dariyan itama.
mummy tayi shiru tana kallon ikon Allah ta dubesu tace "inaga sai annemo muku tai mako, qila kuna da shafan junnu, a zabure dukkansu suka ce "wallahi mummy lafiyanmu lau. " to inkuna lafiya mike saku dariya kamar bugun almatsutsai?
Caf Bahijja tace "mummy dariyan Sumy ne yasani darawa nima "naji kefa? "Ni mummy Bahijja ce ta rungume yaya Mujaheed shine abin yasani dariya.

Shiru mummy tayi batare da taqara cewa komiba.

Suna aiki Bahijja na hararan Sumy ita kuwa sai murmushi takeyi, mummy duk tana hankalce da motsinsu tana murmushi domin yadda suke gudanar da rayuwarsu cikin tsokanan juna na burgeta.
Agefe d'aya kuma cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa Bahijja tazamo rabon d'anta.


Sun fito cikin shirin fita unguwa suna ta muha wara na wanda zai ja motar Bahijja tace "kibari in kaimu sai ki dawo damu "a'a wallahi adda B, naqi wayon salon inzamu dawo kibarni da wahala ko alhalin nagajiko "ok to mutafi a nafef kawai "to muje.

Sunfito bakin get Mujaheed yana zaune bisa motarsa yana amsa waya, ya dubesu ya kirasu da hannu suka qarasa daidai ya gama wayan, "ina xakuje haka? Sumy ce ta amsa "kasuwa zamu, kasan next week bikin Nana "wace ce Nana kuma? "Ta garin su Bilal ya dokawa Sumy uban harara yace "sai naci qaniyarki da kiramin sunan wanan yaron mai kama da sandar suluka a gabana.

Sumy ta qunshe dariyan da yazomata.
"Ina motarku daza kufita titi ahaka bawani mayafen kirki salon mutane sugama kallace muku sura ko? Sukayi shiru, Bahijja ta tsuke baki tana kallon gefe batare da tace qalaba sabida maganar banzan daya fad'a akan Bilal yabata haushi.
Ya duro daga samar motar ya bud'e yashiga sannan yace "kuxo in kaiku.

Suna isa kasuwar ya dubesu "zaku dadene? "Eh, Bahijja tace "ok to inkungama ku kirani in maidaku, "to yaya cewar Sumy.

Suna tafiya zuwa cikin kasuwan Bahijja ta dubi Sumy tace "wallahi sis yaya jaheed yasan kan iskanci, don Allah jifa abin da yacewa Saraki wai sandar suluka, sai da Sumy ta dara sannan tace "aikuwa sunyi kama da sandar,
"shegiya dama nasan abin da zakice kenan 'yar buhu matar bijimin sa kawai. Ita dai Sumy sai dariya takeyi qasa qasa.

Bayan sungama siyayyarsu, Sumy zata kira Mujaheed, Bahijja ta hanata tama kwace wayar ta boye don karda takirashi bata sani ba.

Suna bakin titi jiran nafef, wata mota tadawo da baya ta tsaya dai dai saitinsu, suka kauda fuska, ya bud'e motar yafito yace "princess ya dai kuke tsaye arana? Jin muryansa yasa suka juyo gaba d'aya.

Bahijja ta rangwad'ar da kai tace "munfito kasuwa ne munajiran nafef "ok to kuzo in saukeku.
Bayan sun soma tafiya Sumy tace "Ina yini sarakin add B, Bilal ya waiwayo ya amsa "lafiyalau Sumy, yasu umma? "Suna lafiya "masha Allah.

Sunata hiransu na masoya kad'an kad'an yadda Sumy bazata jiyo suba, har suka iso gida, Sumy tafice da kayansu tayi cikin gida tabar Bahijja suna cigaba da hiransu.

Yana shirin tafiya Mujaheed yadawo, kusa dasu yayi parking ya fito yanufi cikin gida baiko kalli gefen dasuke tsayeba.

Bilal yabi bayansa da kallo yace "queen gaskiya guy d'in can yana da izza "uhmm saraki kenan, sai mun had'u bikin Nan kenan zance ko? yayi murmushi "kindai yi 'yar zagaye kenan kin share xancen yayanki ko? "A'a ba haka bane kawai nagani bashi da amfani ne maganar tunda bayau yasabama haka to kaga yaci ace kasaba,
kadaina qorafi akai.

"eh gaskiya hakane kuma amma kisani sweetie wallahi ina yawanjin bad'uwar gaba duk inna ganshi sai naga kamar yana sonki ne shiyasa yake kishin ganinmu tare.
Cikin murmushin yaqe tace "a'a bakomi tsakaninmu kawai zuciyar kace ke raya maka haka don haka kakwantar da hankalinka ni d'in takace da yardan Allahu, ya d'an sunkuya cikin son tsokana yace "godiya nake shugabata, Allah ya yarda, ta kaimishi duka ya goce yana dariya. Ta amsa "Amin.
Yashiga motar yayi mata kiss ya huro mata tana murmushi ta maida mishi da martani.


Please Login or Register in order to submit comment