Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mujaheed "barka da zuwa doctor batajira amsa warshiba ta dubi Badi'a tace "Amaryamu ya amarci da kuma haquri da yayan namu? Ta amsa lafiya ata qaice.

Kitchen tanufa tana tabe baki, abin motsa baki ta kawo musu ta dire agabansu tasake komawa kitchen domin d'ora lunch.

Aiki takeyi cikin nushad'i tana rera karatun QUR'ANI cikin suratun Taubah.

Jitayi an rungumeta ta baya ta firgita tasa qara kad'an, dariya yayi mata jin dariyarsa tagane Mujaheed ne.

Tasoma son kwacewa yaqara rungumeta tsam yasoma mata magana ahakali "my Bahee jikinki da d'umi sosai koba kya da lafiya ne? Tayi masa banza ya saketa tare da juyo da ita suna fuskantan juna ya kai hannu kamar zai taba mata boobs ta jabaya tana hararansa "kaka yaya jaheed ka fita katafi wurin matarka kabani iska inyi aikina "nazo tayaki aiki ne "banso to, yasaki murmushi ya matso jikinta ta sa hannnun ta tura qirjinsa tana cewa "kaga banason haka, katafi ni don Allah kada matarka tazo "au tsoron matana kikeji wai? Allah ya sauwaqa inji tsoron wannan abin , kawai dai nasan bazataji dad'in ganinmu haka bane "uhmm to naji amma kisoma shiri zama Amaryanta nan da watanni biyu "kutcy!! Wazai aureka kana second hand? Wani dariya yasa har na duqawa, ya nunata da yatsa "ni da ke waye ragowa? Kau tsaye ta amsa da "kai ne man.
Ya qara sa dariya yace "to naji amma ke kuma sauran Bilal ko? Bata rai tayi ta bud'e murya tace "mummy!!

Ya rankwashi kanta tasa qara yayi sauri ficewa yana dariya. Tabi bayansa da harara "Allah ya kyauta in auri mijin wata.



*kaikai masoya labarin Bahijja ina alfahari daku aduk inda kuke sakonku ya iso gareni, nagode sosai Allah bar qauna*😘



*Mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya

*48*
Mujaheed da Badi'a ce zaune bisa dining suna cika tumbinsu da girkin Bahijja mai dad'i.
Badi'a ta dubi mijinta tace "dear amma gaskiya Bahijja tasan sirrin girki mai dad'i, ya karamata plate yana dariya yace "anyi miki waigi kada ki fad'i don santi ta buge hannunsa tana dariya "bawani santi Allah dear, yanshirin bata amsa wani qamshi mai dad'in shaqa ya doso inda suke dukkansu suka maida hankali inda qamshin yake fitowa.

Bahijja ce ta fito sanye cikin mani tsadajjen material kalan black da yarfin fari anyi mata d'inkin riga da sket sunmata cif cif, sosai yayi mata kyau kayan.

Har taqaraso ta ja kujera ta zauna Mujaheed kallonta yakeyi bako qiftawa.

Cikin murmushi ta dubi Badi'a tace "addarsu Badee yadai banga kinci komiba? Addarsu wato ita banda ita kenan?
Ranta take zancen amma azahiri sai tayi Murmushi na yaqe ta amsa "naci kuwa sosai tambayi dear ma kiji.
Caraf Mujaheed ya amshe "shakka babu ta kwashi girki sosai harma tana santi tace ma kin... badi'a tayi saurin kai hannunta ta rufe mishi baki ta hanashi qarasawa, tare da girgiza masa kai, wai yayi shiru ya manna mata cizo ahannun ta sa qara tare da janye hannun.
ita dai Bahijja sai murmushi take musu don sun burgeta amma aqasan ranta wani zugi takeji murmushin qarfin hali takeyi kawai.

Ta zuba abinci tasoma turawa tana had'iyewa kamar nata cin magani, tana jin Mujaheed yana yi mata waiwayi a qafa tayi biris dashi hakan bai mishiba ya taso ya dawo daf da inda take zaune ya matso yana mata magana cikin rad'a ce mata yake "kinyi kyau sosai kamar Amarya a washegarin amarcinta, kinsan ranar komawa takeyi makar wai yaron ciki komi nata yayi fresh.
Tayi masa banza ta bud'e robar ruwa ta zuba a cup ta d'auka zata kai bakinta ya amshe ya shanye ta dubeshi fuska a had'e ya ja hancinta ya dubi Badi'a yace "jibeta sweetie wai rowan ruwa takemin, kau da fuska Badi'a tayi ranta namata d'aci sabida ita bata gamsu da wannan wasan dakema Bahijja ba, aganinta wannan alamar soyayya ce qarara, inko hashashenta haka ne to tabbas da matsala nan gaba.

Juyo da fuskanta yayi ya subbaci labbanta ya kuma ja kunninta yace "ina miki magana kina shareni ko? To zamu had'u anjima domin kinsan karonmu ai, ta marairaice fuska tana yimasa singn da ido yayi shiru saima miqewa yayi yayo kanta, tanaganin haka itama tamiqe tayi sauri tabar dining area d'in tama fice a parlour gaba d'aya sabida tasan halin kayanta yanzu sai yabata kunya agidan surukai.

Yana murmushi yakoma ya zauna yana kallon fuskan Bahijja wacce ta had'e giran sama da qasa tana motsa farfesun hantar da ta zuba zataci amma ta kasa ko lasan romon sakama kon takaicin su Mujaheed daya kamata, jita ke kamar ta rufesu da bugu.

"Kawo inbaki a baki mai sanyina, wani kallo ta watsa mishi yayi saurin rutse idannu ya bud'e yana dafe qirjinsa ya furta "washh Bahee barni haka kada ki zautani da wannan kallon mai ciki ke da bege "wake begen naka!? Tafad'a cikin kaushin murya, "ke man Bahee "uhmm sai kayi ai "zanyi kuwa yarinya domin wannan karan bazan tsaya sanyaba har sai naga na mallakeki na adanaki a gida sannan zanji zam zam,, banza tayi dashi ya kama hannunta ya riqe ta dubeshi, kamar bata son magana tace "ka kiyaye son tabani sannan idan zakuyi kazancinku da matarka kuriqa bari sai kuna gidanku ko don gudun watarana kada kuyi abin kunya agaban su mummy.

Tafi yasa mai qarfi yace "da kyau yarinya tasoma kishina, kai amma naji dad'i sosai alamu yanuna kina sona kamar zaki haukace kenan "hauka kuma? "Eh man wai irin son nan mai hana mutum barci "uhmm kai dai Allah yayi maka sauqi ace mutum ko wata uku baiyi da aureba amma don jaraba har idonsa ya hango wata, waccema batasan kanayiba.
Dariya yasa mai sauti yace "zakisha mamaki yarinya bari dai kigama idda kigani in rufa miki asiri, harara ta dalla mishi ta miqe tsaye tanufi kitchen tana cewa "kadai rufawa kanka asiri amma ni kam asirina arufe yake.

Ta sunkuya zata d'auko fresh milk a cikin frize ya kwanto abayanta cikin fad'a tana nishi sabida ya sakar mata nauyinsa tace "kasan Allah yaya jaheed zan had'aka da Abba ya shiga tsakaninmu da kai, d'agata yana dariya yace "kai amma ke raguwace my badee tafiki jarumta sabida ita tsaf take d'aukeni batare da tagaji ba,
turasa tayi da qarfi yayi baya kamar zai fad'i sai yayi sauri dafa cabinet, ta dubeshi a yatsine tace "yo ni ina ruwana da iskancinku daza kasani a gaba kana fad'amin, taja tsaki tafice tana qunquni komi take cewa oho mata.🤔

Bayanta yabi da kallo yana murmushi na farin ciki domin yaga tsantsan kishinsa a idanunta shi yasa yake qara tunzurata, ya sosa kansa ya daka d'an tsalle kamar wani yaro sai kuma yasa dariya yana cewa "nakusa samun sanyin ruhina, kai nagode maka sandar sunuka daka sakarmin mahad'in ruhina, ya d'an mari kansa, yana mai cewa "sai dai kiyi haquri Badi'a amma kamar na auri mai sanyina my Bahee d'ita da yardan Allah.

Sai dare Mujaheed suka tafi, duk yarda yaso suqara had'uwa da Bahijja amma taqi yarda sam, koda zai tafi qin fitowa tayi tayi musu sallama.
tanakwance tajiyo shi yana tambayar mummy ina Bahijja ta amsa mishi da tayi barci, ta tura baki tace "mayen mata kawai.


Yau gidan Sumayya taje, umma ce ta aiketa ta akai mata maganin zaqi.
Suna zaune a parlour suna hira Sumayya tace "adda B, matar yaya fa ciki take dashi cikin halin ko inkula tace "Allah raba lafiya "Amin.
"Adda B, itama watan aurensu watan cikinta, a yatsine Bahijja tace "kamar ke kenan?
had'amanmu banza kawai, Sumy tasa dariya "eh d'in anyi had'amar kema ai don mijinki solobuyo ne bashi da kwazo shi yasa yakasa miki cikin, "ke ni dalla inzancen banza zakiyimin wallahi yanzu zan bar miki gidanki kici tsiyarki ke d'aya "yi haquri adda B d'ina kuma aminiyata muyi fad'a mu shirya abinmu, duka ta kai mata tana dariya tace "shegiyar 'yar jarida qarya duk suka sa dariya.


Kwanci tashi bawuya indai da rai gashi yanzu watannin Bahijja biyar da rabuwa da Bilal, tayi bul bul abinta gawani uban kyau data qara abinta.

Masu son aurenta Allah yayi yawa dasu, ita kuma taqi kula kowa cikinsu su kuma su mummy sunqi cewa ta fidda miji.

Agefe d'aya kuma Mujaheed ya kasa ya tsare ya hanata sukuni shidai sai ta amince zata aureshi dole, ita kuma sai wasa da hankalinsa takeyi.


Tana zaune a gaban umma da hantsi.
umma ta dubeta sosai tace "Bahijja Abbanku yace min Mujaheed yayi masa magnar yana son aurenki akaro nabiyu, shikuma baya son ya takuraki shine yace in tambayeki shin kin amince ko kuwa? Gabanta na fad'uwa tace "umma ni ba sonsa ne banayi ba kawai bana son tashin hankali ne "kamr ya tashin hankali? A tsan qasan maqoshi ta amsa "da matarshi, murmushin manya umma tayi sannan tace "kice dai bakyason auren mai mata, ta sunkuyar da kai tana wasa da zarazaran yatsun hannunta.
Numfashi umma taja sannan takira sunarta "Bahijja ta amsa "na'am.
"Kada ki sake shaid'an ya rinjayi zuciyarki kizamo cikin wad'anda basa son zama da kishiya, ina baki shawara da kiyi watsi da wannan banzan aqidar, ki maida hankalinki wurin addu'ar nema samun zaman lafiya mai d'orewa a tsakaninku, kizamo mai biyayya, haquri tare da juriya kuma kizamo mai d'auke kai akan duk abinda bai shafekiba kamar yadda kikaga muna zaunne da mummy nku.
Ta gyad'a kai tana sharen kwalla.
Umma ta dafa kanta tace "kin amince in sanar da Abbanku? Ta d'aga kai alamar eh.
Cikin wani irin tsan tsar farin ciki umma ta rungumeta tana jera mata albarka.
Ita kam Bahijja mamakin murnan da umma takeyi take, wanda takasa haquri har sai da tace "umma kina ta murna kamar anbaki kujeran makka.

Umma ta amsa "Ai ko shi aka bani inaga murnata baza takai hakaba sabida Allah kad'ai yasan yadda naso aurenki da Mujaheed awaccen karon amma Allah bai nufaba, kingako yanzu dole inji farin ciki mara misaltuwa araina ko don karancin iyayensa agaremu.
"Hakane kam umma nima nayi murna daganin yadda nasaki farin ciki.
"Yawwa Bahijja 'yar albarka, Allah ya kad'e fitina azamanku "Amin umma, ta amsa tana wani sunne kai, murmushi umma tayi tana hamdala aranta ganin cikin sauqi ta amince batare da musuba.


*nace uhmm umma, Bahee almunahunhun ce tana son horn.qato d'inta dama can*hhhh




*mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya

*49 to 50*

Kowa yayi farin ciki dajin zancen auren musanman uban gayyan Mujaheed.

Abba yace abari sai bayan Sumayya da matarsa sun haihu sai atsaida rana d'aurin aure da tarewa.

Amma hakan baiyuwa Mujaheed dad'iba don shi ason ransa ne ayi komi agama a cikin sati biyu.

Bahijja kuwa wasan buya somayi da Mujaheed domin duk inda tasan zasu had'u tana kaucewa zuwa wurin inkuma ya rutsala a lungu da gudu take barin wurin tazamar dashi kamar wani dodo.
Shikam dariya take bashi sosai.

Badi'a bata san da labarin ba kuma bawanda yayi mata zancen hattashi Mujaheed d'in bai sanar da itaba.

Tana kwance a cikin d'akinta a part d'in umma, waya take amsawa tana dariya har tana riqe ciki ya turo qafar ya shigo ya tsoge a bakin qofar yana kallonta tayi hanzari cema wadda suke wayar "Nana ina zuwa don Allah tare da ajiye wayar.

Miqewa tayi zata shiga toilet yayi hanxarin kamota ya maidata tsakiyar gadon shima ya hayo ya zauna ya kama kafad'anta yana matsawa ahankali ta tura baki tana hararansa yatsarsa yasa ya make bakin nata tayi saurin dafe wurin idanu waje ya motsa kansa yace "inkina min tsiwa sai na riqa dukanki ta had'e rai tace "ai kuwa da kadaki aurenka don bazan zauna da madokiba kuma ta tashi kafitamin a d'aki "in anqifa? Inma ihun qato yashigomin d'aki ya fizgota ta fad'o kansa yasa hannu ya ja zip d'in dake gaban best d'in dake jikinta Allah yasota tasa bra amma duk da haka sai da yaga boobs d'inta domma tayi sauri jan blanket ta rufe qirjinta.

Cikin matuqar fushi ta dubeshi tace "kasan Allah jaheed inba barmin irin haka ba zan had'aka da mummy "ya had'e rai shima yace "yimaza ki had'anin da ita kuma bazan bar duba lafiyar kayana ba sai dai kiyi duk abinda zakiyi "malam nidai kafice min ad'aki nace in samu in sarara "bazan fitaba sai naji text d'in kayana idanu waje tace "mikenan kake nufi? Ya matso yasoma jan blanket d'in data rufe qirjinta da shi yana cewa "bari in nuna miki su kigani da idonki ganin da gaske yakeyi ta qalla qara yayi saurin rufe mata baki da hannunsa d'aya d'ayan kuma yana qoqarin janye bargon cizo ta manna mishi a hannu mai zafi amma yaqi ko gezau sai dai yabar qoqarin janye bargon dayan hannun nasa dai yana rufe da bakinta yasoma magana "Kika cijeni ko Bahee to ki rubuta ki ajiye lokaci yana nan zuwa da zan rama kuma kinjama kanki don yau zan bugaci Abba da ya d'auramana aure next week Allah barshi bayan haihuwar nasu kya taren, dama haka bikin zarawa yake a d'aura aure bikin tarewa sai wani lokaci to kema haka za ayi ko kya qara samun daman yin gyara da kyau yadda zanji komi yayimin zam zam dafatan kingane ai,, qarasa maganar tare da ka kashe mata ido d'aya.

Kallonsa kawai takeyi takasa ce mishi komi ganin haka yasa yacigaba da cewa "kuma kisani ni jarumin maza ne mai matuqar kwazo a bisa bed dama ko ina don haka sai ki zage dantse kizamo jaruma mara lalaci don haka kisan ni d'in ba irin gantalallen tsohon mijinki bane mara kuzari mai kama da kazan kwanci.

Ita dai shiru tayi mishi zuciyarta na kai komo akan batun auren da yace zaisa a d'aura wani sati da kuma cemata da yayi bazawara, tunanin abinda zatayi mishi na bacin rai takeyi ko zata sami sauqin cin mata fuskan da yayi amma tagaza samo komi.

Ya kai hannu ya shafa sumar kanta yana cewa "wallahi my Bahee sosai nake son sumarki da beauty dimples d'innan naki sai kuma uwa uba boobs d'inki masu girma da kyauwun qira tare da d'aukan hankali sai kuma d'an mitsitsin bakinan ya kai hannu bisa labbanta ya latsa yana wani lunshe idanu ya ja numfashi yace "kai Allah komi naki my Bahee ina sonsa yana burgeni sosai matuqa.

Har yanzu taqi ce mishi komi sai dai binshi da idanu takeyi a qasan ranta tana jinjina rashin kunya irin nashi kuma tarasa ko wa yabiyo aranshin kunyar oho, tasan dai tsakanin mummy da Abba ba wanda yabiyo sai dai ko a can cikin dangi wataqila ya yibo abinsa.

Yaja hancninta ya sunkuya ya mannawa goshinta kiss sannnan ya sauka a gadon ya bud'e qofa zai fice tana ganin ya kusa fita ta bud'e murya tace "wallahi ban yarda ka fad'ama Abba a d'aura auren ba kuma ni ba bazawara bace sannan kada kaqara tabami jiki don ba jikin baqar matarka bace ehe, jarababbe kawai sarkin mata, ya juyo da sauri ta daka tsalle ta sauka ta shige toilet ta kulle tajina da qofar tana maida numfashi sai kuma taja tsaki ta furta "kai wallah auren mai mata matsala ne ballema irinsu yaya jaheed jarabbu.


Tundaga ranar bata qara sashi a idanuba ashe yayi tafiyane shima mummy taji suna magana da umma, sannan tasan bayanan aranta tace gaskiya naji siqit dama yayi zamanshi acan sai kuma ta girgiza kai tace "kai ba Amin ba tana murmushi.

Tana hanyarta na dawowa daga kasuwa wayarta tayi qara ta gangara gefen hanya ta d'auka saijin kukan jariri tayi ya doki kunninta a zabure tace "Sis kardai kicemin kinyo kashin baby? Dariya Sumy tasa ta amsa "yawuce wai adda B, mun girma sai kinzo ganin photocopy d'inki gashinan sak ke wani qaran murna tasaki tana jera hamdalah tace "ganinan qarasowa dama ina kan hanya ne "ok sai kin iso.

Da gudu ta shiga parlour n bayan ta isa gidan, don sauri ko key din motar bata cireba tayi ciki.

Karo taci da mutum ta d'ago taxa bashi haquri domin atunaninta yaya Bashir ne sai taga Mujaheed tsaye yana kallonta ta yamutsa fuska tace "malam yaushe kadawo kuma? Murd'e kunninta yayi ta runtse ido ya subbaci bakinta ta bud'e ido da sauri tana waige waige yasa dariya ya ja hannunta "zo muje kiga mai kama dake, yana riqe da hannunta suka shiga bedroom d'in ya d'auko babyn ya miqa mata yana cewa "gaskiya da ace babyn nan mace ce to da ko da tsiya sai Bros yayi miki takwara sabida tsananin kamar da kukayi tana murmushi ta kara bakinta akunnin babyn tayi masa addu'a ta kuma yi masa a d'ayan kunnin sannan ta dubi Sumy tace "kinajin abinda yaya jaheed yake cewa ko? "Eh ai gaskiya yafad'i nima nace da mace ce ke za ayiwa ta kwara tana murmushin farin ciki tace "to next year sai kimin takwaran ai, duka Sumy ta faska mata tace "muguwa da yake bakisan bazar wuyan dana shaba dabakice next year in qara ba.

Sosai Mujaheed da Bahijja suke mata dariya.
Mujaheed yace "my Bahee sister n ki raguwa ce sai ihu take mana a hospital d'azun kamar wacce zata haifi 'y'ya goma, Sumy ta shagwabe fuska tace "yaya haka mukayi da kai? "Au sorry sis namanta ne nafad'a, dariya Bahijja taqara sawa tana cewa "ainaji komi sis mai kukan haihuwa "kinga adda B, kibari ko in had'aki da umma "rabi dasu inajinsu suna miki dariya to gara kowa da kowan wake indai Bahijja ce la shakka babu sai kin fita dauriya, cewar umma wacce ta shigo, dariya suka kuma sawa, Bahijja ta juyo tana murmushi ta dubi umma tace "laaa umma kece kikazo da kanki tarban mijin, a lallai kai miji ka caba da yawa abinka, duka umma takawo mata Mujaheed ya tare yana dariya Umma ta kama baki tafice tana cewama Sumayya "fito kinji ki d'auraye jikinki ki kyale wad'annan shasha shan banza, duk suka kwashe da dariya.

"Malam wai yaushe kadawo ne? Nakai awa biyar da dawowa, ina isowa kiran Bros yasameni na iso muka tafi asibiti, yanxunan mukadawo gida Bros yafita amso mata magani nima gida zani inhuta ajikin matata kika tsai dani ta had'e rai "riqe maka qafafu nayi komi? A'a shauqin begenki dai ya riqeni "to yasake don haka tafi wurin matarka yana murmushi ya fice tabi bayansa da harara.


Mai jego da Babynta suna samun kulawa na musanman.
A part d'in umma suke jego domin sundawo gida tun bayan haihuwar da kwana biyu, gashi har gobe suna.

'Dinki da zatasa ranar suna Sumayya take gwadawa Bahijja tare da matar Mujaheed wato Badi'a suna kallon yadda yayi mata kyau suna kod'ata.

Bahijja ta tube daga tiet sai bra tana shirin gwada wata doguwar rigan shadda akaturo qafar tare da sallama Mujaheed ne tare da Bashir suka shigo tayi sauri ta zura wani dogon hijab har qasa.

Bayan sungama abinda zasuyi Bashir yafara fita Mujaheed kuwa janyo hannun matarsa yayi ya rungumeta a gefensa yana cewa "zo muje ki amsa saqonki, ita kuma sai wani langabewa takeyi masa tana yauqi suka fice shi kima yana wai wayan Bahijja wacce ta had'e rai.

Tsaki taja mai qarfi ta cire hijabin tayi jifa dashi ta zauna ta da dafe kai.
Sumy ce ta dafa d'anta "adda B kiyi qoqarin rage nuna kishinki please "uhmm niba kishi nakeyiba kawai inajin haushin nid'in ce zan auri mijin wata dama ace wata ce zata auri mijina da abin yafimin sauqi.
"Uhmm adda B kenan dukka cikinsu ba sauqi wallahi, kedai muyi ta addu'ar samun zaman lafiya tare da haquri da junanmu kawai shi yafi.

Ranar suna yaro yaci sumar Abba suna kiransa da Abbie.

Suna zaune sukaji gudan wata kakarsu tanayi tana qarawa Bahijja tace "ga kaka indo can tasoma d'abi'an 'yan saqara lazza da hawiya ba,, aiko mutanen d'akin suka kwashe da dariya suna cikin dariyan suka tsin kayi kwakwazonta ta na fad'in Alkawarin Allah yacika yardansa tare da ikonsa yau ya tabbata domin an d'aura auren 'yar albarka Bahijja tare da angonta jarumi doctor Mujaheed Allah yabasu zaman lafiya da zuri'ad'ayyiba yakuma had'e kansu da abokiyar zamanta Badi'atu d'iyar arziki.

Wani dim Bahijja taji domin batayi zaton da gaske za a daura aurenba yau, ta rutse idanunta tana maijin kunyar kallon badi'a, da kyat ta iya bud'e idanu ta sauke su bisa Badi'a wacce ke zaune gefenta tana xuba abin rarraba a take away.


*Mrs j moon*
[10:05AM, 9/4/2017] Mrs J Moon😊: *RAYUWAR BAHIJJA*
Dedicated to Mumm Abdul *(Bebeelo)*

©Safiyya.

*51*

Gani tayi itama ta zubamata idanu kamar yau tasoma ganinta, janye idanunta tayi tare da miqewa zata fice ad'akin.
"Bahijja! Badi'a ta kira sunarta cikin qarfi.
Juyowa tayi amma takasa d'aga idanu ta dubeta sai kawai ta kai dubanta shashin da Sumayya ke zaune tana shayar da babynta hankali kwance abinta.

Kafad'anta Badi'a ta dafa tasoma magana muryanta na rawa "dolle kikasa kallona dama man sabida kinsan kinci amanata kin gama cutata, kinriga da kingama sanin sirrina a inda nasaki baki ina fad'amiki don nad'aukeki tamkar 'yar uwarsa ce Sumayya wanda aure bazai taba shiga tsakanin ku ba dashi ashe kallona kikeyi ad'age kinacan kina fafutikan auremin miji sannan kuma don rainin hankali bawanda ya sanar dani sai kawai naji d'aurin auren asama,, to wallahi ba ki isaba inyi kishi dakeba kuma kisani ni d'aya ce zan mallaki mijina, nice uwar 'ya'yansa kaf don haka basu da 'yan uba, sai kinemawa kanki mafita tun lakaci bai qure mikiba, tana kaiwa nan ta ta turata baya ta koma ta zauna tna sauke numfashi da sauri da sauri kamar wacce tashiga gasan tseren gudu.

'Dakin yayi tsit kamar bakowa ciki, zuciyar Bahijja inyayi dubu yabaci amma kuma takasa yunqurin kare kanta.
Zuwa can Zarah d'iyar yayan umma ta miqe ta nuna Badi'a da yatsa tana mai cewa "ke!! Matar rashin wata, yi maza ki saita kalamar harshenki akan adda B, sannan abinda bakisani to yau zan sanar dake Bahijja itace matar da mijinki yaso tun talintali amma Allah bai nufa shi zata fara auraba sai yanzu Allah yayi ikonsa kinga kenan tsohuwar soyayya ce ta had'a kanta yanzu,
kuma da kike fad'an tagama sanin sirrinki yo wani zace kifad'ama ko dolle tasaki sai kin fad'a matan, ke kika fad'a mata don ra'ayin kanki ba ita tasakiba don haka can tamatse miki amatse matsin matsalarki,, taja numfashi ta d'ora "sannan kisani arashin Adda B, yaya Mujaheed ya aureki sabida mun san komi duka duka watanku uku ana hud'u da had'uwa akayi bikinku kinga tun nan zakigane auren rashin wata akayi dake don haka kisaita kalamanki nacewa bazakiyi zaman kishi da itaba, to yazama miki dolenki kizauna da ita ko kinqi ko kinso sai dai inzaki haqura dashi ne, kuma 'ya'ya dole su sami 'yan uba tunda ubanso yaji yagani, inkuma zakiyi gabane to laba'asa ga hanya nan dama mu fat..... da sauri Bahijja ta rufe mata baki tana girgiza mata kai tace "Zarah ya isa haka ko bakya ganin yanayin datake ciki ne dazaki sata a gaba kina fad'amata maganganun masu d'aci haka?
Rashin kyautawa dai anriga anyi mata don haka kibarta tafad'I duk abinda ke ranta ko hakan zai sata sami sauqi.


Please Login or Register in order to submit comment