Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[4/4, 10:33] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 1&2


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*


Fans gaisuwa ta musamman a gareku ku din masoyane kun nunamin kauna ta hanyar siyen novels dina musamman raggon miji return nagode sosai wannan littafi karamar kyauta ce daga gareni insha Allah zakuji dadinshi sosai ku dai kuyi kokari Ku fara daga farko sannan Ku dage da suburbudomin comments don naji dadin yi maku typing nagode sosai da kauna luv u all🥰


*shafin farko na kine kawata maman mujaheed Allah yabar kauna*😍


*Alhamdulillahi kaseeran*



"Assalamu alaikum, Baban farouk Ina kofar gidan ka"

Baban farouk na kwance idanunshi cike da bacci yayi juyi yace"karfe 7 batayi ba fa"

Yayi yar dariya yace"ka fito plss akwai muhimmiyar maganar da nakeso zamuyi "

Baban farouk yayi hamma yace"to ganinan"

Ibraheem ya katse kiran ya zauna bakin dandamalin dake a kofar gidan yayi shiru yana tunani,

Baban farouk ya tashi batare da yin komi ba yana sanye da jallabiya yana fitowa karamin danshi khaleefa ya rugo aguje wurinshi ya daukeshi yana murmushi yace"har ka tashi ?"

Ya daga masa kai

Yace"ina mama?"

Cikin koyon mgna yace"a kitchen "

Baban farouk yayi murmushi yana dauke dashi ya nufi kofar gida ,

Gida ne karami Wanda baida gate koina sibull shafe da siminti gidan dai kwas da alamu maman farouk nada tsafta sosai,

Ya bude gidan ya fito yaga aminin nashi zaune ya karasa ya zauna yana kallonshi yace"wannan sammako haka kamar zakaje kamun fara?"

Ibrahim yayi karamin murmushi sannan yace"aure nakeso nayi"

Baban farouk yayi mamaki sosai ya bude baki da idanu yana kallonshi babbane sosai yakai 40yrs baki sosai amma kyakkyawan baki yana da hanci sosai shine ya kawata fuskarshi yana da jiki da tsawo ba laifi,

Ganin yanayin kallon da yake masa yasa ya jawo khaleefa jikinshi yace"aboki kayi salla kuwa?"

Khaleefa ya girgizakai yace"mama brush a bani"

Ibraheem ya kuma murmushi yace"ya kamata kai salla ko jeka ciki"

Khaleefa ya nufi ciki dasauri ,

Sannan ibraheem ya juyo wurin Baban farouk yace"kayi shiru banason haka"

Baban farouk yana cigaba da mamaki yace"I'm very surprise ban taba tunanin hakan ba yanzu can baya nayi_nayi kayi aure ka ki amma yau daya kace kanason aure dole nayi mamaki"

Jikin ibrahim sanyaye yace"kasan bani da matsalar shaawa kuma kasan yadda rayuwata ta taso mahaifiyata ta rasu wurin haihuwa da ita da abin da ke cikinta duk sun rasu babana yakasa jurewa da jin labarin ya fadi ya mutu akabarni ni kadai cikin yawan dangi amma rikeni ya gagaresu yau ina wancan gida gobe wancan da sungaji zasu turani wani wajen harnagaji na dawo wurinka da zama kafin kai aure kabarni cikin shagonka na ki yin aurene saboda da manufofi da yawa idan banda abun rike iyalin saboda me zanyi aure ?wasu zakaga daga little three month da aure anfara samun matsala saboda kudi ,na biyunshi yadda na tashi ya zamar min darasi tarin yanuwa baya nufin idan kabar diyanka zasu samu gata zaa kula dasu abu mafi muhimmanci ka Samar masu Uwa ta gari bayan mutuwa mahaifiya zatayi iya kokarinta don ganin yaranta sunyi rayuwa me kyau da inganci "

Baban farouk duk jikinsa yayi sanyi yana ta kallon Ibrahim yace"yanzu kasamu wacce kakeso?"

Ibrahim yayi murmushi yace "kasani bana soyayya auren kawai nakeso nayi "

Baban farouk yayi dariya yace "to taya zakayi auren haka ?ai seka samu wacce kakeso kun dedeta"

Ibraheem yace"ban shaawar yin aure garinnan nafison in auro yar kauye wacce asalinta kauyene"

Baban farouk yace"meyasa? Baka ganin kana iya auro wacce zatai ta baka wuya saboda kauyanci da duhun kai?"

Ibraheem yace"a'a bana nufin auren jahila kauyawa suna da makarantun allo dana islamiyya suna da ta boko primary inaga in na samu me primary ko bayan aurenmu seta cigaba da karatun nafison in auri wacce bata wayen ba me saukin kai wacce zan reneta muyi zaman lpy "

Baban farouk yace"nan a state ma akwai duk Wadannan amma de yadda kakeso yanzu wane kauye zamu dauko matar?"ya karasa da murmushi,

Ibraheem yace"kauyen mu wagini ina da kawu a can yana da kirki sosai inaso ka rakani muje shi nake son ya zabamun Matar "

Baban farouk na masa wani kallo yana wata iriyar dariya yana Sosa gemunsa yace" Allah yasa alheri yaushe zamuje?"

Ibraheem yayi karamin murmushi yace"mu bari se week end kaga time ba aiki amma fa kwana zamuyi lahadi mu dawo "

Baban farouk ya sakeyin dariya yace "Allah yakaimu"

Ibraheem yace"naga kana daukar abun wasa zakayi mamaki "

Baban farouk yayi dariya ya mike tsaye yace"daganan kana jiyo kamshi ko?madam tagama hadamin delicious nayi ciki a je asha tea da bread"yana gama fada ya shige gida,

Ibraheem yayi murmushi ya girgizakai sarai ya gane nufinshi saboda shi matarshi classmate dinsa ce ta kware a komi musamman girki, aganinshi kowa ba da iyawa aka haifeshi ba don haka duk macen da bata iya sanwa ba kowani abu ita taso bayajin matarshi zata dawwama ba iyawar idan harma bata iya ba kenan,

Ya tashi ya nufi mashin dinsa me suna ledis ya hau ya tada ya nufi shagon da yake matsayin gidansa ,

Bayan 3 days

Ya kama ran Saturday tunda safe ya isa kofar gidan abokinsa yana cikin riga da wando shadda ya fito babban mutum kamar magidanci, yaciro wayar shi Nokia ya kirashi ringing biyu ya dauka yace"ango ina shiri yanzun nan zan fito"

Ibraheem yayi murmushi ya kashe kiran,

Bayan mintuna Baban farouk me suna isa ya fito cikin tashi shaddar ya dana hula gaban goshi ibraheem na ganinshi yayi murmushin zuci yace"mu tafi angon zulfau"

Baban farouk yayi dariya yace "bazan ce komi ba se naga lantanar matarka"

Ibraheem yayi murmushi suka dauki hanyar tashar mota don duk mashina garesu,

Suna zuwa suka dau hanyar wagini village,

Tafiyar two hrs ta kaisu kauyen suna sauka suka dauki hanyar gidan kawun nashi,

Yana zaune kasan wata bishiya an shimfida tabarmar kaba ga casbi a hannunsa yana ja ,

Suna isa wurin bishiyar sukayi yayinda kawun ya kara gyara zama yana kallonsu yana murmushi yace"maraba da mutanen birni"

Suka zauna suna ta sunkuyar da kai suka fara gaidashi,

Ya amsa yana faraa yace"iro kwana biyu shiru kadena lekomu lpy de ko?"

Ibraheem yace"ayi hakuri kawu"

Kawun yayi murmushi yace"bari na sa a kawo maku ruwa"

Ya tashi ya nufi cikin gidan da yake na jar kasa ,

Suna zaune ya fito ya dawo ya zauna ,

Suna ta dan labari wani matashi ya fito da kwanon ruwa da kwaryar fura yazo ya ajiye gabansu sannan ya kallesu yace"sannunku da zuwa"

Suka ce "yawwa ya aiyuka?"

Yace"lpy lau "ya tashi ya tafi,

Ibraheem ya dauko ruwan ya mikawa Baban Farouk sannan ya matso da furar sosai gabansa,

Bayan sun dansha kawu ya nata kallon ibraheem yadda ya kara girma ga shekaru nata tafiya amma yaki aure a hankali yace" iro nace se yaushe zakayi aure ne ?gashi de kannan kannan ka har sunyi haihuwa bibiyu "

Kanshi sunkuye yace"kawu nazo ne Ku zabamin mata wacce kuka yarda da tarbiyyarta da asalinta"

Kawun yayi murmushin manya yace"nadade banji labari medadi kamar wannan ba, naji dadi da ka girmamani kabani damar yi maka zabi nagode sosai Allah yajikan mahaifinka"

Ya tsagaita yana murmushi yace "amma baka fadi kalar da kakeso ba kar akawo wacce batai ma ba"

A kunyace Ibraheem yace"kawu yarinya ta gari na keso ko ya take inde tana da tarbiyya "

Kawu yayi shiru har ya gama yiwa dan nasa zabe domin kuwa akwai yarinyar da duk safiya take wucewa makarantar boko sannan Ko giftawa nawa zatai saita gaisheshi kyakkyawace sosai sede ba fara ba black beauty yana jindadin yadda take girmamashi marainiyace amma masu iyayen ma wasu basu kaita tarbiyya ba kakarta na iya kokarinta wurin bata tarbiyya ,

Ya kalli ibraheem yace "insha Allah zanyi iya kokarina wurin zabar maka abokiyar zama ta gari kafin ka dawo"

Ibraheem yayi godiya yace"anan zamu kwana zuwa gobe zamu tafi"

Kawu na kara jin dadi yace"madallah naji dadi sosai Allah ya muku albarka"

Suka ce "ameen" atare,

Kawu ya tashi ya shiga cikin gida yasa a yanka masu agwagi ai musu farfesu a soya don yaji dadi jin zasu kwana ya koma wurinsu suka kara shan hira sannan suka shiga ciki suka gaida tsoffi suka wuce gaido megari,

Da marece kawu Wanda shine autan babansu ibraheem yaje wurin megari abokinsa ya fadamai yadda sukai da ibraheem megari ma yayi farinciki saboda baban ibraheem mutumin kirki ne da son jamaa shima ya bada goyon baya sannan yayi jagora wurin nemarwa ibraheem auren yarinyar,

Kafin dare angama nemawa ibraheem auren aiken kudi kawai ya rage da kuma abubuwan al'ada,

Ibraheem yaji dadin labarin cikin daren ya bada dubu 30 kudin neman aurenta da sadaki a hakan yayi kokari sosai a lokacin nera na da daraja,

Daren ibraheem ya kasa bacci cike yake da d'okin ganin wacece zabin kawunsa ?wacece zaya aura? Juye _juye yayi tayi kafin bacci ya samu daukeshi,

Bayan asuba suka zauna fira abokinshi kuma amininsa nata zaulayarshi da safe suka sha koko da kosai sukai wanka sukaje wurin megari sukai godiya karfe sha daya suka kama hanyar birni batare daya samu damar ganin wacece zai aura ba,

Bayan kwana biyu da tafiyarshi aka saka bikin wata hudu masu zuwa,

Da dare da muneerat da kakarta suna daki suna cin tuwon dawa a tare cikin kwano daya kakarta tanata kallonta tai murmushi tace"muneera kin kusa girma"

Muneera ta kalli kanta shekarunta 14 ciff a duniya duk wani abun da ke nuna girman mace ba abinda bai fito ba sede bata da jiki ta meda kallo gun kakarta tai dariya ta sunkuyar da kai,

Kaka tace"kinason zuwa birni?"

Muneera ta girgizakai tace"kaka ni banason karamin abun da zai rabani dake kullum tare muke kwana banason zuwa koina"

Kaka tai murmushin manya tace"dazun nan kawunki yafadamin sun gama saka ranar aurenki nan da wata hudu"

Muneera tai shiru ta shiga tunani towa zata aura?

Kaka na jindadi tace"zaki tafi birni ki huta da daka da surfe da debo ruwa"

Memakon murna se muneerat ta zare hannunta daga cikin kwano ta fara kuka hawaye suka balle mata kamar famfo ta cigaba da kuka har da sheshsheka sosai take jindadin zama da kakarta wasu na ganin nuna soyayya da yawa ga yaro na lalatashi amma ita hakan bai mata komi ba se gyaran rayuwarta ,

Hankalin kaka yayi mugun tashi don batason ko digon hawaye ya fito daga idon jikarta se taga kamar ta gaza wani wuri bata manta time da uwarta ke labour irin wuyar da tasha kafin ta haifota Wanda sanadiyyar haka ta rasa diyarta guda daya shiyasa ta kwashi duk soyayyar ta meda akan muneerat ,

Tai saurin tande yatsun hannunta ta jawo muneera jikinta murya sarke tace"minene muneera auren ne bakyaso komi ?"

Muneerat na kuka tace"kaka banason auren... nafiso in yita zama tare da ke...ni de kaka karkumin aure banaso"

Kaka tai ajiyar zuciya ita kanta batason ta kifta bataga muneerat ba a hankali cikin rarrashi tace"muneera bakison aure haka zakiyita zama ?bakiso ki taramin jikoki Wanda zan rika gani inajin dadi suna zuwa gaidani suna min wasa suna debemin kewa?ki temakamin muneera kiyi aurenki kiyi zamanki lafiya da mijinki hankalina zaifi kwanciya"

Muneera tai shiru jin Kalmar temako da kaka ta fada take idanunta suka rika hangomata daidaikun gidajen da diyansu da jikoki ke zuwa gaidasu ita kanta abun na bata shaawa,

Take hawayenta suka tsaya babu abinda bazatayi ba don jindadin kakarta, itace uwarta, ubanta, danginta, kawarta kuma aminiya abokiyar wasanta ,

Kaka tace"kiyi hakuri muneera farko hankalina ya tashi jin zaki tafi birni saboda banason bude ido babuke kusa dani amma danayi tunanin zaki huta da wahalar kauyen nan diyanki kuma zasu samu rayuwa me inganci shiyasa nai farinciki matuka karki bani kunya muneera ta"

Muneera ta kara rungume kaka tana sauke ajiyar zuciya,

Kaka tace"kindena kukan ko yanzu ne kadai zaki cigaba?"

Muneera ta boye fuskarta tana dariya abun duk kunya yake bata ,

Kaka tai dariya tana jindadi da karin kaunarta, bata yiwa muneera magana so biyu tana gudun bacin ranta tana kuma son farincikinta sosai, ta shafi kanta tace"Allah ya miki albarka ya baku zuria dayyiba wanda zakuyi alfahari dasu "

Muneera tai gum tana hango ya kalar rayuwar zata kasance nan gaba,

Kaka tace "sakeni na sauyo miki tuwon wannan ya gama sanyi"

Jin haka yasa muneera tashi ta dauki kwanon ta fita zuwa kitchen dinsu abincin ya fita ranta amma dole taci don in bata ci ba hankalin kaka bazai kwanta ba,

Da muneera da ibraheem kowa yanason ganin juna amma basu samu hakan ba har sai saura 1 month bikinsu time din ankawo lefenta akwati guda da kala biyar da kayan shafa dasauransu ,

Ganin lefenta cikin akwati yasa kauyen yagame da zancen aurenta wasu na mata murna wasu na hassada ,

Surutu koina wasu na cewa mijin katone yafi karfinta be kamata a bashi yarinya kamarta ba abun mamakin kuma har kamar megari suna bashi aure wannan kawai aka sawa ido surutu koina Wanda hakan ya daga hankalinta,

Bayan kwana biyu kacal da kawo lefen yazo garin yakasa jurewa har seda yasa aka kaishi gidansu,

Suka tura yaro kiranta se gata ta nufo gidan ta dawo daga school tana sanye da doguwar riga green and white da white hijab,

Yanayin shigarshi yasa ta gane daga birni yake dan rakiyar dan kawune tama sanshi hakan ke mata tabbacin shine Wanda zata aura ganin girmanshi seda gabanta ya fadi yana da jiki sosai tana cikin kallonsu idanunsu suka sauka kanta tai saurin juyawa ta nufi hanyar komawa dasaurinta,

Dan kawu yayi murmushi yace"gata can zata koma"

Ya dage ya kwala mata kira "muneera!!!"

Time daya ibraheem da muneerat zuciyarsu tai motsi tai saurin juyowa don tasan kaka tagama jin kiran ta nufesu kanta kasa,

Shi ko ibraheem jin sunan ne yasa zuciyar sa motsawa bai taba kawo zaiji sunanta muneera ba farat daya sonta ya mamaye zuciyarshi ya kura mata ido yana karemata kallo tundaga sama zuwa kasa.
[4/4, 10:33] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 3&4


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*


*Wannan shafin na kune manyan mata mutanen Niger😊ina kuke yan Niger 🗣kufito Ku rausaya pagyn mallakinku ne inasonku sosai yan Nijar musamman masoyana my bestybeelat Sarauniya,kawa hjy samira yahya,maman zainab,momyn daughter @Ribar rayuwa,real Ladingo diyarta🤪yan Niger dake group din paid for all da duk yan Niger ina maku sonso da fatan alheri duniya da lahira🥰*


Tana jin matukar kunya ta karaso tana zuwa ta kai kasa zukunne kanta kasa a sannu tace"ina wuni "

Wani sanyi ne ya mamaye zuciyarshi ya cigaba da zuba mata lafiyayyun idanunsa yana jin sonta murmushi dauke da bakinsa da besan yanayi ba,

Dan kawu ne ya amsa gaisuwar yana faraa yace"da guduwa zakiyi ?to ni mijinki na rako zaku gaisa kinga tafiya ta"ya juya ya tafi,

Tana zukunne bata da niyyar dagowa, dakyar ibraheem yace"ya makaranta?"

A hankali tace"lafiya lau"

Yace"Ki kara meda hankali"

Ta jinjina kai tamkar tana gaban iyayenta,

Lura da yadda take matukar jin kunya batare da ya kara cewa komi ba ya juya ya tafi,

Sede jin motsin tafiyarshi tayi, ta dago tabi bayanshi da kallo ganin kamar zai waiwayo yasa ta saurin tashi tai cikin gida dasauri,

Ibraheem ya waiwayo yaga wayam bata gun ya saki murmushin jindadi ya cigaba da tafiya yana matukar farinciki samun kyakkyawa me kunya kamarta ,

Yana zuwa yaci abinci yayiwa su kawu bankwana ya tafi bayan laasar ya isa birni,

Cikin farinciki ya nufi gidan baban farouk cike da dokin bashi labarin ya hadu da Matar aurensa ,

Yana zuwa ya kirashi ba dadewa ya fito yana murmushi yace"ango kasha kamshi"

Ibraheem ya saki murmushi yace "na samu ganinta"

Baban farouk ya gyara tsayuwa dasauri yace "bani labari ya take ?"

Ibraheem ya mishi wani kallo yace"beautiful "a takaice

Baban farouk yace" namaka murna amma baka siffantamin itaba"

Ibraheem ya kalleshi sama da kasa da boyayyen murmushi fuskarsa ya juya yayi tafiyarsa,

Baban farouk yayi murmushi nan kusa bai taba ganin mutum kamarshi ba baya firar mata bedamu da kallonsu ba yanayin da yaganshi yanzu ya tabbatar masa da zafin kishinsa, yana farinciki abokinsa zaiyi aure ya koma cikin gida,

Tun daga time din ibraheem bai sake komawa kauyen ba sai saura sati bikinsu sannan yaje wannan time din ma kanta kasa taki bari su ko hada ido yanason yaji ko akwai abinda takeso bai samu yayi mata mgnar ba sede yabada kudi a bata ya tafi,

Da aka kawomata kudin taji dadi tai ta kallonsu tana murmushi ita kadai

kaka ta kara dagewa da gyaranta irin na gargajiya na can baya don suma basa zama hakanan suna nasu dubarun,

Ibraheem ko yayi kokarin yin gininsa na kasa an shafesa da siminti gwanin kyau bai dauko yin auren ba seda ya shirya,

Ranar biki aka daura auren akan sadaki dubu goma duk da ibraheem bai cika faraa ba amma yau din bakinsa yakasa rufuwa Sam,

Bangaren Amarya tun saura kwana ukku take ta kuka kaka na tausarta data bari ta cigaba daga karshe da taga kakar na tayata seta rika boyewa tanayi ko in taje makaranta tayi abinta,

Bayan an daura aure su ibraheem suka tafi se gobene zaakai Amarya gidanta,

Muneerat tasha dilkar lalle jikinta simul jawur tasha kunshi da tsararren kitso tai kyau amma fuskarta kumbure don kuka kamar wacce zaai wa auren dole ba abinda ke damunta se rabuwa da kaka ,

Da dare kaka ta sameta ta zauna tana bata abinci a baki tana rarrashi da nasiha tanata boye hawayenta bayan ta gama bata ta fita ta shiga toilet ta matse hawayen idanunta ta fito,

Wanshekare aka kawo babbar mota fara J5 ta kwashi Amarya da yanuwanta da mutanen gari dayar motar ta kwashi uwayen kayanta da kaka taketa faman Tarawa tuntuni ,

Da rana suka isa, motocin suka ajiyesu kofar gida suka shiga da Amarya ciki dangin ibraheem daidaya suna cikin gidan domin tarbar baki sunata kumburi da shan kamshi don yanada dan hali ga diyansu bai zabi ko daya ba sannan bai nemi shawarar iyayensa na birni ba sede kawunsa dake kauye ,

Suna shiga suka fara mata Jere da kayan dakinta masu kyau ,

Daga gidan Baban farouk aka kawo abinci matarshi ta girka tuwon shinkafa da miyar taushe suna gama Jere sukaci suka cigaba da labari suna shaawar gidan muneera,

Itako muneera na can kuryan daki a takure tana hawaye akai_akai,

Anyi _anyi taci abinci bataci ba seda maman farouk tazo sannan ta matsa taci saboda kunyarta ta danci, har marece sannan maman farouk ta tafi,

Cikin danginshi bawanda yayo abinci kowani abu maman farouk din ce ta dafo taliya da miya sukaci da dare suka kwanta,

Wansafe tunda wuri suka fara shirin tafiya kauyensu sunata zolayar Amarya ,

Itako ta kara yin zuru_zuru hankalinta tashe har suka gama shiri tana kuka itace rakiya har zaure suka tafi akabarta ita kadai ta koma ciki ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita,

Jim kadan bayan tafiyarsu ibraheem ya shigo gidan yayi sallama volume din kukanta be bari taji ba, ya karasa ciki yanajin tausayinta,

Yana bude labule tai gumm ta dena kukan tana kwance gefen bed tai kasa ta jawo gefen dankwalinta ta fara goge idanunta da suke jawur a kumbure,

Yana jin tausayinta ya karasa kusa da ita ya dagota ya zaunar daita kan gadon,Yana kallonta kanta sunkuye in calm yace"kiyi hakuri kidena kuka, inasonki sosai muneera zan kula dake bakin kokarina bazan bari kiyi kuka ba"

Tai shiru tana saurarenshi ,

Ya dubi agogon hannunshi ya tashi tsaye ya fita,

Ba jimawa ya dawo da tea da bread ya zauna gefen bed din ya mika mata cup ta ansa ba musu ya ajiye mata bread yace"kisha"yana kara hango kasusuwan dake jikinta,

Ta fara sha kamar yadda ya umarce ta,yanata kallonta seda ta shanye ta ajiye kofin,

Yace"ki kwanta ki huta"

Ta kwanta duk ta kankame jikinta wuri daya yana bin ta da kallo ya tashi ya fita,

Ta kwana biyu batai baccin kirki ba saboda yan guje_guje da wasannin kauye tana kwance ba jimawa bacci ya dauketa,

Ibraheem yagama fahimtar tana bukatar hutu da lokaci domin ta warware ta meda jikinta bayason ya zama sanadiyyar karin ciwon ta,

Da rana ya dawo ya samu tana bacci yayi wanka ya sauya Kaya yaje tashinta don tayi salla yana taba ta ta mike zaune kamar wacce aka taba da electric shock kanta kasa,

in calm yace"lokacin salla zai wuce"ya juya ya fita,

Ta tashi tai salla ta koma ta zauna ya dawo da abinci bayan laasar ya ajiyeshi falo ya sameta zaune kurya kan dadduma tayi tagumi ya mika mata hannu ba musu ta dora nata ya tadata suka fita suna zuwa inda silver abinci take ya zaunar daita ya bude abincin yasa cokali ya debo ya kai bakinta,

Ta kara sunkuyar da kai dasauri tana jin kunya,

Yasa dayan hannunsa ya dago fuskarta yayi karamin murmushi yace"kici abinci mana"

Ta bude baki ta fara amsa a kunyace ,

Yana bata yana ci ta koshi amma bata iya kin amsa ba ganin dagaske bazai dena bata ba yasa

Please Login or Register in order to submit comment