Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin namu sukaita ihu barayi suka harbe baffa suka kashe innata suka biyoni suna so suyi min fyade sannan su kasheni na gudu na shiga motar shanu har... zuwa nan"ta karasa da matsanancin kuka,

Hawaye ne keta zarya akan fuskar Muneera tana tsananin tausayin Zarah ,

Idanun WALEED jawur yana cije da lips dinsa yana jin bakin ciki yake kallonta,

Zarah na matsanancin kuka muryarta na sarkewa numfashinta na season tace"Baffa na ba barawo bane"
[4/4, 10:34] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 27&28


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*


*Raggon miji fans group ina godiya da comments dinku Mrs yaseen,my son,maman Aisha,hussy sani,Ummu abrar,shema'u hassan,maman sadik,anty zee,feaner and all*


Muneera na hawaye ta matsa ta rungumeta jikinta tana tapping bayanta tana jin matsanancin tausayinta,

Zuciyar WALEED na tsananin zafi yace"wannan wane irin zaluncine?"

Muneera ta kalleshi ta girgiza masa kai,

Ranshi na suya yanajin tarin bakinciki ya tashi ya fita a wurin da sauri yana tafiya yana huci zuciyarshi na kara tuno masa maganar Zarah dake kara rura masa wutar zuciyarsa "Ranar ya tareni yanamin maganganun banza harya..tabamin jikina"

Yanajin matukar bakinciki yake tunanin inane ya taba a jikinta?idanunsa suka hasko masa kyawawan breast dinta masu kyawun gani da daukar hankali cikin zuciyarsa yakejin breast dinta ne ya taba wani irin kishi ya tokare masa makoshi idanunshi suka kara yin ja harya isa gida ya tsaya yana bude kofa yaji ana masa horn daga bayansa ,

Bai waiwayo ba sai HAMEED dinne ya fito yazo ya samesa yana karasowa garesa yace"Amir khan.. zuwa nai na koyama yadda ake soyayyar don nasan baka iya komi ba banaso wani yayi maka shigar sauri"

WALEED ya dago fuskarsa ya kalleshi da jajayen idanunshi ya dauke kai ya tura gidan ya shige ciki,

Jikin HAMEED yayi sanyi yayi kasake yana tunani meke damun abokinsa? zuciyarshi tace"kode ta mutu ne?"ya zabura ya nufi ciki da sauri,

Yana Shiga ya samu WALEED zaune akan seat hannunsa akan kujera dafe da kansa da yake jin yana juyawa tsabar kishi da bakinciki da yakeji har hango irin tabawar da Murtala yayi masu yake,

HAMEED ya zauna kusa dashi jikinshi sanyaye ya dafa shi yace"WALEED meke damunka?"

Bakin WALEED har motsi yake tsabar bacin rai bakinshi na kyarma yace"Zarah.....ya kashe iyayenta don kawai ya cimma kazamin burinsa"

HAMEED na kallonshi yace"bangane ba?"

Ran WALEED bace jiniyoyinsa na tashi ya bashi labari yana gama fada yace"ya kashesu kuma ya tabata....ya taba jikinta"

HAMEED ya dafa kafadarshi yana matse lips yanajin tausayin Zarah yace"Allah zai saka masu kuma nasan mama zatayi wani abu akai ,kayi hakuri ka kwantar da hankalinka"

WALEED ya kalleshi yanajin kamar yayi kuka yace"Dole zasu medata kauyen,bayan sun medata idan wani abu ya faru daita fa?"

HAMEED ya lumshe ido ya bude yace"Trust me ba abinda zai faru mama will help her bazata barta haka ba"

WALEED yayi shiru yana hango yadda Zarah ke bada labarin tana kuka numfashinta na daukewa ji yake kamar ya bude ido ya ganshi a gaban Murtala da sai ya kasheshi kisan wulakanci tare da duk Wanda ke da hannu wurin saka rayuwar Zarah dinsa cikin kunci,

HAMEED ya cigaba da kwantar masa da hankali,

Muneera na rungume da Zarah tana ta ajiyar zuciya tace"kiyi hakuri Zarah insha Allah bazaa kira baffanki barawon shanu ba ,gaskiya zata bayyana nan bada jimawa ba ,amma kafin nan inaso ki rage damuwa ki kwantar da hankalinki ki dawo hayyacinki har zuwa wani lokaci karami da zamuje kauyen naku"

Ta dago fuskar Zarah tana kallonta tace"inasonki tunda naganki naji dama nice mahaifiyarki yarana biyu bani da kamarki inafatan zaki daukeni tamkar uwa"

Zarah ta jinjina kai idanunta kasa suna kawo ruwa,

Muneera ta sake rungumeta tare da cewa"zaki cigaba da zama tare damu kafin KHALEED ya dawo shi zai kula da komi"

A hankali Zarah tace"Nagode Mama"

Muneera tai karamin murmushi ta shafi gashin kanta tana tunanin Me zai faru gaba,

WALEED na tare da HAMEED har sha biyu sannan HAMEED ya tafi ya tashi yayi wanka ya nufi asibitin,

Yana zuwa muneera ta barosu ta dawo gida ,

Suna zaune shi da Zarah dukkansu suna cikin tunani duk hankalinsu baya ga juna har wani lokaci sannan WALEED ya dago ya kalli fuskarta a hankali idanunsa sukai kasa suka sauka kan breast dinta ya dauke fuskarshi yanajin ciwo a zuciyarshi da wani irin kishi tuna kila wani ya taba,

Suna zaune bawanda yayi magana har Muneera ta dawo ta dawo da kulolin abinci tana dan murmushi ta ajiye tana kallon Zarah tace"tunanin ne Zarah? Kiyi hakuri kiyiwa su baffa addua"

Zarah ta dago ta kalleta ta sake sunkuyar da kai,

Muneera ta zuba abinci a plate ta zauna tana bata ta rika amsa tanaci kadan_kadan,

WALEED ya meda kallon sa gun Zarah tana cin abincin a hankali yakara bin jikinta da kallo yana hango tsantsar yarintarta,

Ya sake dauke ido yanajin sonta da tausayinta lokaci daya,

Suna tare da Marece KHALEED ya kira, ta dauka da murmushi suka gaisa ya tambayi yame jiki tafada masa dasauki tanata masa addua ta kashe ,

Zarah nata kallonta yadda taji suna wayar yasa ta tunowa da mahaifiyarta wadda batasan kamarta ba bare har suyi labari ko na dakika hawaye suka zubomata tasa hannu ta share tana tuno me share mata hawayen me kula daita ma Murtala yayi sanadiyyar barinta duniya,

Sai jin nocking sukayi Muneera tace "shigo " tana kallon kofar,

HAMEED ya turo kofar ya shigo yana dan murmushi da sallama bakinsa ya karasa ciki ya sunkuyar da kai yace"Ina yini mama yame jiki?"

Muneera tace"dasauki sosai alhamdulillah"

Yace"Allah ya bata lafiya"yana dan kallon Zarah da take shiru,

Muneera tace "ameen HAMEED"

Ya kalli WALEED yace "Allah ya bata lafiya" ya juya ya fita,

WALEED ya tashi ya bi bayanshi harya sameshi,

HAMEED na kallon abokinsa da tausayi yace "ka kara kwantar da hankalinka "

WALEED yace "Thanks" saboda nuna care da HAMEED yake akansa ,HAMEED yayi murmushi yace"kallon ball zanje ko zakaje?"

WALEED ya daga kai suka nufi motarsa a tare,


Kwanansu 5 asibitin aka sallame su ,suka hada kayansu suka nufi gida WALEED na dauke da kayan muneera na rike da Zarah har suka isa gida,

WALEED ya bude masu gidan suka shiga ciki Zarah nata kara kallon gidan sai yanzu ne take kara ganin haduwarshi suka shiga har falo tanata kalle_kalle muneera ta zaunar daita kan kujera tana murmushi tace"ki huta kadan in kawo abinci"ta nufi hanyar kitchen,

WALEED ya wuce dakinsa batare da ya kara kallon Zarah ba,

Aka barta ita kadai a falon ta kara bude ido ta na bin koina da kallo idanunta suka kai kan pic dinsu Muneera da KHALEED da WALEED sun sata tsakiya duk sun dafata da murmushi fuskarsu,

Idanunta suka tsaya kan KHALEED ganinshi bature cikinsu ta zubawa fuskarshi kallo tana ta kallonshi tana sake_sake a zuciyarta, ko shine dayan dan muneera?zuciyarta tabata amsa da eh duk da dai yafi ta kyau tana ta kallon pic din muneera ta dawo da superghetti a plate ta ajiye kasa tace"Zarah ga abincin ki daure kici "

Zarah ta jinjina kai tace"Nagode"

Muneera tace "kici sosai fa zan shiga in watsa ruwa "

Zarah ta kuma daga kai tana murmushi muneera ta juya ta shiga daki,

Zarah ta kalli abincin daba irinshi ta saba ci ba ta riga ta saba da fura sosai take missing dinta ta sauka ta dauki spoon tana tsakurar abincin,

WALEED ya fito daga daki yana tafiya yana kallonta,

Jin motsi yasa ta dago kanta yayi saurin dauke idonshi a kanta ya nufi kitchen ya dauko abincinsa ya dawo falon ya zauna saman kujera ya kunna TV sannan ya fara cin abincin yanayi yana kallon Zarah dake zaune kasa tana tsakurar abinci ya kula sosai batacin kome sai yaji badadi,

Muneera ta gama wanka ta fito ta sameta bataci komi ba fuskarta bawalwala tace"Zarah meyasa bakison cin abinci?"

Zarah tace "naci"

Muneera tace "a,a bakici komi ba ko akwai abinda kikeso ne?"

Ta girgizakai,

Muneera tace"to dan Allah dai kirika cin abinci idan ba so kike mu koma asibity ba"

Ta daga kai tana lumshe ido tace"to Mama "

Muneera tai murmushi tace"ki shiga kiyi wanka ki sake kaya anjima WALEED zai kara siyo miki wasu"

Tace"Nagode sosai"

Muneera tai murmushi ta nufi kitchen ,Zarah ta tashi ta shiga bedroom,WALEED ya dago yabi bayanta da kallo cikin ransa yasa har da pencil zai siyo mata cikin kayan,

Muneera ta dawo ta zauna cin abinci tanaci ta ajiye cokalin tace"akwai kudi hannunka?"

WALEED ya daga kai,

Tace"Anjima kaje ka samowa Zarah ko kala biyarne ta samu na sauyawa kafin a dinka mata"

Yace"To"yana cigaba da cin abincinsa,

Zarah tai wanka ta fito ta kalli mirror ta zauna ta shafa mai kadai ta saka doguwar riga ta fito falon ,

Su muneera suka dago suna kallonta ,Muneera tai murmushi bayan Zarah ta zauna tace "meyasa baki shafa powder ba?"

Zarah tai murmushi tai shiru ,

Muneera tace"ki rika shafa powder da jan baki zaki fi kyau"

Zarah ta kalleta tai karamin murmushi ta sunkuyar da kai,

WALEED nata kallonta ya tashi ya fita yabar gidan,

Wanshekare tun asuba Muneera taga Zarah ta kabbara sallah ,

Tana zaune tana azkhar ta bari harta gama sannan tace"Zarah kingama al'adar ne?"

Cikin kunya Zarah ta daga kai ,

Muneera tace "kinyi wankan tsarki?"

Zarah ta daga kai jikinta sanyaye,

Muneera tai shiru tace"tam kafin KHALEED ya dawo zaki rika zuwa islamiyya sannan zamu rika karatu gida kafin ki koma saboda ki kara sanin addininki zamu fara da fikhu in mun samu dama angama sai mu fara wani "

Zarah tace "Nagode sosai mama"

Muneera tai murmushi tace "dama zaki cigaba da rayuwa tare damu da zanji dadi sosai amma ko kin koma kice asaki makaranta akwai a kauyen ku ko?"

Ta daga kai tace"akwai"

Muneera tace "kice asaki makaranta ki rika zuwa ko awasu ranakun idan ba kiwo"

Zarah ta kara jinjina kai,


*************************

Tun daga lokacin Zarah na gidan har bayan sati tana sukuku murmushi ne kawai nata tana dan kamawa muneera aiki suje ismiyya sai kallo sai kallon pic din KHALEED da bata gajiya dashi wata zuciyarta har karyata cewa dan muneera ne take, indai tana falo to hankalinta na kan pic din,

WALEED ko yakara tsunduma soyayyarta cikin zuciyarsa jiyake kamar sunyi shekaru goma tare saboda yadda yake jinta cikin ranshi ga matsananciyar shaawarta data tasoshi gaba dare daidayane baya wet dream ,

Soyayyarta tasashi kara son yayi karatu saboda ya samu ya mallaketa nan da wasu yan shekaru a shirye yake da jajircewa akan karatun shi don ya samu aiki da wuri, saide yana cike da fargabar rasa ta kafin ya dawo kar ai masa shigar sauri kasancewarta bafulata masu yiwa yara aure tunda wuri,

Da muneera da Zarah dashi suna falo zaune yaga kiran HAMEED bai dauka ba ya fita cikin harabar gidan ya samu HAMEED tsaye ,

Ya mika masa hannu suka gaisa HAMEED na masa wani irin kallon kurilla yana murmushi yace"Ina kanwar mu ?hope tana lafiya?"

WALEED ya saki murmushi yadan hararesa,

HAMEED yace"gaskiya so yayi ma abokina mugun kamu kaga yadda kake kara tsawo kana ramewa kuwa? Bansan yadda zan kira kanwar mu ba?princess, queen kome?"

WALEED yana murmushi yace "she's a star..... d star of my heart"

With excitement HAMEED yace"Wow!!! Abokina"yana dariya yace "ko cikin taurarin itace tafi haske..... Zarah"

WALEED yace "very good" sukai dariya tare hanunsu cikin na juna suka fita,

Haka suka cigaba da rayuwa muneera nata jawo Zarah jikinta har ta saba daita tana jinta kamar mamarta ,kullum suna waya da KHALEED sai de Zarah ta kura musu ido tana kallonsu yadda suke wayar dashi zaka gane suna cikin farinciki itama hakan kesa tata zuciyar yin fari,

Wasa_wasa har akai 1month ranar da watan ya kare KHALEED ya kira Muneera ta dauka sunata labari sai da zasuyi bankwana yace"Mama kuna da special bako gobe don gobe jirginmu zai sauka Nigeria "

Muneera na farinciki tace"ina cikin farinciki marar misaltuwa dana ina kagare na sanyaka idanuna"

Yayi murmushi yace "gobe ne mama, don't for get a hadamin delicious irinsu tuwo miyar kuka"

Tai dariya yana dariya yace "I missed tuwo mama inajin shi zaamin"

Tana dariyar tace"kome kakeso inafatan Allah yakawomin kai lafiya"

Tana dariya ta kashe kiran Zarah na gefe tana kallonta tana murmushi jin baturen gidan zai dawo ganin sun gama wayar ta sunkuyar da kanta kasa,

Muneera na farinciki tace "Zarah gobe daddyn WALEED zai dawo"

Zarah tai murmushi tace"Allah ya kawoshi lpy"

Muneera tace"Ameen"tana lissafa abubuwan da zatai don tarbar babban danta,

KHALEED na gama waya daita ya kira WALEED ya fadamasa ,

WALEED ya shigo falon yana murna ya kwanta ya dora kai kan cinyar muneera yana murna yace"Gobe daddy na zai dawo"yana ta farinciki yana kagare ya dawo yafadamai cewa he's in love,

Zarah ta kalli WALEED dake kan cinyar muneera tana kallonshi dangata,

Muneera ta dora hannunta tana shafar sumar kanshi tace"tashi zakayi ka karomin kaji da nama zanyiwa dana special girki"

WALEED yayi dariya ya tashi ya fita yana cikin farinciki,

Muneera ta tashi tafara kara gyra gidan domin KHALEED akwai tsafta yana iya zuwa yaga wani abu bai masa ba tun kan ya huta ya fara aiki,

Ranar wuni sukai aiki suna cike da dokin gobe yayin da KHALEED ma yana cikin dokinta,

Cikin dare suka taso zuwa Nigeria ,

Washe gari tun asuba suke hidima in banda kamshi ba abinda gidan keyi sunata kai kawo har WALEED daba aikin ya cika yi ba,

Cikin lokaci suka gama sukai setting komi a dining sannan suka fara shirin wanka muneera tafara yowa sannan Zarah ,tana gama shiryawa ta fita can zuwa ta dawo ta samu Zarah na shafa powder tai mata murmushi ta dauki wayarta ta fita ,

Shima WALEED yayi wanka yana cikin kananun kaya yanata baza kamshi,

Wurin karfe 12 suna zaune suna kallo kowane lokaci suna tsammanin ganin KHALEED hankalinsu ya dauku da TV har KHALEED ya shigo gidan ya bude kofar falon da murmushinsa me kyau yace"I'm home...!!!!"

Suka juya a tare sai ganinshi sukai tsaye yana fitar da sassanyar murmushi,duk suka bude baki suna farinciki,

WALEED yace"daddy" ya tafi dasauri ya rungumesa ,Muneera da Zarah duk suka mike tsaye suna kallonsu suna sakin murmushi,

KHALEED ya meda kallo gunsu ya janye WALEED a jikinsa ya karaso gaban Muneera yayi hugging dinta yana cikin farinciki,

Zarah na tsaye tana ta kallonsu tana ganin abun kamar yadda take kallo acikin TV ,harya janye jikinshi yana murna yace"Sannun ku Mama "

Muneera tace"Sannu da zuwa KHALEED" tana kallonshi tun daga sama har kasa tana jindadi,

KHALEED ya kalli Zarah yana ta murmushinsa ya dauke idonsa ya meda shi kan WALEED yakara jawoshi jikinshi yana jin farincikin kasancewa tare da danuwansa,

Zarah nata dan murmushi tafara bin KHALEED da kallo tun daga sama sumar shi baka wulik tasha gyara tanata sheki yayinda fatar jikinshi ke fayau da matsanancin fari idanunshi cikinsu da blue _blue da green memakon baki hancinsa straight da murmushinsa me sanyi a bakinsa ,kayan jikinsa kuwa yana cikin dark blue riga da bakin wando sunyi masa matukar kyau yana fidda wani kamshi medadin gaske,

Ta shagaltu da kallonshi, muneera tace............
[4/4, 10:34] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 29&30


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*



*Flasher30 on wattpad thanks u for ur comments keda aysherdanlami ,maryamuba ,dansani and others nagode*



Muneera tace"Ka zauna ka huta mana kasha hanya"

Ya kalli Muneera ya nata murmushi ya jawo WALEED suka zauna seat daya ya dora hannunsa ya rike kafadarshi yace"Mama na sameku lpy?"

Tace"Lafiya lau dana"tana cikin farinciki,

Yayi murmushi ya kalli Zarah ,Zarah ta dauke idonta dasauri tana dan murmushi ta zukunna tace"Ina wuni"

Yana kallonta yace"Lafiya lau"ya dauke idonsa akanta ya kalli WALEED yace "meke damunka duk ka fada?"

WALEED ya daga kai ya kalli Muneera yayi shiru,

Muneera tace"maybe yana tunanin tafiyarshi kasan autane"

KHALEED yakara rikeshi sosai yace"don't worry urself da zaran ka tafi sede kaga kadawo ba wuya"

WALEED yayi gajeren murmushi ya kyallara ido ya kalli Zarah da take ta kallon daddynsa ya matse lips dinsa

Muneera tace "yanzu ka tashi kai wanka ka ci abinci kayo salla kadan kwanta ka huta"

Yayi murmushi yace "Nagode sosai mama"

Ya mike yana rike da KHALEED har bakin kofa ya jawo trolley daya yacewa WALEED ya dauko dayan suka nufi dakinsu kasancewar dakinsu daya,

Suna shiga dakin yana fess yanata kamshi an sauya zanan gado mekyau iskan AC da fanka nata kadawa ,ya saki murmushi ya ajiye trolley ya karasa bakin mirror ya fara cire riga,

WALEED ya juya ya fita yanata murna yana wani tunani a ransa,

Yana dawowa falo ya samesu zaune Zarah ta kafa pic din KHALEED da kallo ,

Ya kalli pic din ya kalleta aganinshi ko tana mamakin halittarshi ko kuma tana masa irin kallon da jamaa suke masa duk in suka ganshi,

KHALEED ya tube ya shiga yayi wanka ya fito ya tsane jikinsa ya bude babban trolley dinsa ya dauko kayansa da man shafawarsa da wanda yake shafawa gashin kansa don yakara baki,

Ya dawo kan mirror ya zauna ya shafa man ya gyara sumarsa ya tashi ya saka kayan dark orange riga da milk din jeans ya fesa turarukansa ya saka takalma ya fita zuwa falon,

Suna zaune kusan 30mnt suna jiranshi yana fitowa kamshinsa ya fara musu sallama suka zuba mai ido sunata kallonshi da murmushi ya karaso ya zauna ,

Zarah ta kara kallonshi taga ya kara fayau akan yadda yazo ya kuma kara haduwa ta sunkuyar da kanta itade bata taba ganin kyakkyawa kamarshi ba,

Muneera tace"Muje kaci abinci sannan sai a zauna fira ko"

Suka nufi dining su ukkun Zarah kuwa bata tashi ba tana zaune wurin,

Suna zuwa suka zauna muneera tafara bude kuloli abinci kala 5 reras gabanshi,fried rice,white rice and pasta,Sakwara,couscous,sai tuwon daya bukata ga kuma farfesun kaji ga soyayyu ga dambunsu duk awurin ,

KHALEED nata kallon abincin ya kalli Muneera yace"Mama kina sona da yawa duk ni kadai wannan garar?"

Tana murmushi tace"seka zaba Wane kake son ci?"

Ya kara kallon abincin yace"Sakwara"

Tafara zubamai tana cewa "da tuwon da kace kadai zanyi ashe na temaka"

Yayi dariya yayi shiru,

Ta gama zubamai ta ajiye gabanshi ta zuba sobo ,kunun aya da ruwa duk a cup ta ajiye ta koma ta zauna kan kujerar tana kallonshi,

Ya dauki abincin ya faraci ya lumshe ido yana fadin "So delicious"

Sunata mai dariya,

Bayan ya gama cin abincin yayi godiya ga Allah ya kalli WALEED yace"Anjima in mun fito sallah zaka rakani wani wuri saika fiddo mashin dina ka gogeshi kafin mu tashi fitar Amma kafin nan kashiga ka daukomin karamin trolley dinnan"

WALEED ya tashi ya nufi ciki don daukowa,

Muneera nata kallonshi lokaci daya fuskarta ta sauya Sanin ko abokai bai dasu yanzu dole yaji rayuwar daban bata tunanin zaiji dadin rayuwa a Nigeria ,

Ganin tana tunani yace"Mama lafiya? "

A hankali tace"inafatan ka cigaba da rayuwa cikin farinciki kamar yadda kake a can "

Yayi murmushi ya rike hannunta yace"Mama kune farincikina zama acikin ku kadai ya isheni farinciki "

Muneera ta girgizakai tace "Abinda ma yafi dagamin hankali aikin da zakai bansan ...kowane iri bane"

Yayi murmushi yace "mama kar ki damu kome zai tafi yadda mukeso wani malamina ya bani no din wani abokinsa yace dazaran nazo in sameshi sunyi mgna dashi zai samar min aiki a Skye bank idan Allah ya yarda ,so nake bayan kwanaki na huta saina fara aikin"

Muneera tai murmushi tace "Naji dadi Allah ya tabbatar da alheri ya biyamishi bukatunshi"

Yace"ameen mama "

WALEED ya dawo da trolley KHALEED yace"kaishi can falon "

Ya karasa dashi suka tashi suka koma falon har lokacin Zarah na zaune wuri daya tanata tunani barkatai ,tana murna da zuwan KHALEED wani bangare kuma bata murna da zuwan shi saboda yadda take jin tsoron kauyensu ta kuma San dole suna da labarin abinda ya faru kuma zasu cewa baffanta barawon shanu ,

Suna zazzaune KHALEED ya bude trolley ya fara fiddo dogayen riguna har kala biyar da wata sarka ta gold me shegen tsada tana cikin karamin akwati ya mikawa Muneera yana murmushi yace"small tsarabarki Mama"

Ta amsa tana murna tana kallo tace"wannan yawuce small harda gold masha Allah "

Ya fiddo wasu kananun kaya riga da sket da turare me sanyin kamshi na mata ya kalli Zarah ya mika mata ,

Zarah ta kalleshi ta kalli kayan taje ta amsa cikin sanyin murya tace"Nagode"

Muneera ta kalli kayan taji matukar dadi dukda baisanta ba yanade jin labarinta amma harda ita a tsaraba,

Ya rufe trolleyn gabadaya ya turashi gaban WALEED yace"here's urs my lovely son"

WALEED na farinciki ya rike trollyn yana godiya" tnx u so much daddy Allah yakara maka budi"yana matukar murna,

Muneera tace "ameen_ameen" tana cikin jindadi,

WALEED ya tashi yaja trolleyn ciki ya bude yadan duba sannan ya fita ya buda wani daki acikin gidan ya fiddo mashin dinsa duk yayi kura ya gogeshi tas kamar an wanke sannan ya koma ciki ya samu Zarah bata wurin ya kalli KHALEED yace"Daddy anyi kiran salla"

KHALEED yace"OK "ya tashi ya shiga ciki yayo alwala ya fito harabar gidan yaga WALEED da HAMEED tsaye ya nufesu,

HAMEED na faraa ya sunkuyar da kai yana karasowa yace" barka da dawowa daddy"

KHALEED ya dora hannayensa kan kafadunsu yana faraa suna tafiya yana cewa" ya kake ya karatu da kallon ball da yanmata?"

HAMEED yayi murmushi yace"ba yanmata daddy"

KHALEED yayi dariya yace"anya fadamin WALEED ma ya fara ko? "

WALEED yayi saurin kallon HAMEED ya fiddomai idanu,

HAMEED ya saki murmushi yace"a'a"

KHALEED yayi dariya yace "Its better bin mata at this stage baida amfanin komi se rashinsa, soyayya bazata bari kayi karatu ba ko natsuwa bazaka samuba in har baka samu wacce kakeso ba HAMEED kaima yakamata kadena sakarci "

HAMEED yace "Na dena daddy, ai insha Allah tare da WALEED zamu yi karatu"

KHALEED yayi murmushi yace"yayi kyau" suka fita a gidan,

Bayan sun fita Zarah ta samu Muneera tace "Nagode mama"

Muneera tai mata murmushi tace" ki tashi ki shirya ki tafi makaranta yau bazan samu zuwa ba"

Zarah ta tashi tafara shiri ,

Suna dawowa masallaci suka tafi siyen mota KHALEED ya sai dalleliyar mota baka tanata sheki suka shigo motar suka nufo gida WALEED nata farinciki,

KHALEED ya kalleshi yana murmushi yace "Kafin ka tafi zan koya maka kana dawowa saika fara hawan taka"

WALEED na jindadi yace"Daddy na dan iya dama muna hawan tasu HAMEED "

Lokacin da suka dawo har anyi laasar suka tsaya sukayi salla sannan suka shiga cikin gida WALEED na murna yace"Mama daddy ya sai mota"

Muneera nata murna ta fito ta gani tanata Allah yasa alheri suka koma ciki suna ta labari suna cikin jindadi,

Muneera ta lura yanajin barci tace"ka tashi kadan huta hakanan"

Yace"to Mama"ya tashi ya shiga dakinsu ya kwanta kanshi na ciwo ya lumshe ido bacci ya daukesa,

Zarah na makaranta suna karatu amma idanunta KHALEED kadai suke hangowa ta rasa dalilin hakan tana cigaba da mamakin halittarsa,

Dama akwai hadari a garin lokaci daya ya taso aka fara maka ruwa kamar da bakin kwarya akaita yi ba kakkautawa,

Yadda gari yayi sanyi sosai muneera ta koma daki ta dan shingida saboda ta dan samu bacci ,

WALEED ma ya tashi yawuce nasu dakin ya kwanta bayan daddynsa ,

Anata ruwa a dauke amma shiru har lokacin tashin makaranta yayi duk yara na jira a dauke ruwan su samu fitowa,

Muneera na bacci Zarah ta fadomata a rai ta fito falo tai tsaye tana kallon window ganin yadda garin yayi bakikirin kamar ishai,

sai gab Maghreb ruwan suka dan rage kowa ya fito da gudu ,

Baai minti biyar ba kuma aka kara shakewa da ruwan wasu suka samu wuri suka dan labe wasu su kaita gudu zuwa gida,

Zarah tayo hanyar gida ruwan na dukan jikinta,

A hankali KHALEED ya bude ido ganin duhu yasa shi tashi ya kalli WALEED dake bacci ya fito falo yana mamaki ,

Yana fita ya samu Muneera tsaye ta rike hannuwa ya tsaya gabanta yace"Mama lafiya ?"

Ta kalleshi tace"Ruwa nake kallo Zarah na waje kila ma tana hanya suna bata kashi"

Dasauri yace"Bari

Please Login or Register in order to submit comment