Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

safe badon komiba don su nuna mai dagaske suke,

Suna zuwa seda gaban muneera ya fadi ta riga ta fahimci ganinsu ba alheri bane ta gaishesu tanata murmushi ta mika masu KHALEED yana cikin kayan shi masu kyawun gaske ta wuce kitchen don dauko jug ta kawo masu ruwa da lemu,

Tana basu yaron duk hankalinsu ya dukufa kanshi ganinshi jawur_jawur kamar bature,

Karamar tace"keji yaro kamar diyan turawa"

Dayan tace"kamar zabayane na kega"

Suka kara zubamai idanuwa suna kara dubashi sosai ,

Dayar tace"tabbas kuwa maganarki haka take Allah me iko abinda muke gani wani wuri se gashi yazo kusa"

Dedenan kaka ta shigo cikin gidan ganin ba motar ibraheem yasa ta gane ya fita batai sallama ba ta shigo don ta kama muneera na kuka, tana jin kuskus takara matsawa wurin tayi mamakin ganin takalmansu sede hakan bai hanata tsayawa taji me ake ba,

Babbar ta bude baki sosai bawani tsoro tace"ai ba abun mamaki bane kinsan anfi haihuwar irinsu idan an sadu da mace tana cikin jinin alada, to shi iro an riga an shanyeshi angama dashi ko ana jinin bazaiyi hakuri ba se yayi kinga don sun haifi irinsu ba a bun mamaki bane "

Lokacin muneera ta fito daga kitchen ta nufo dakin jin maganganunsu yasa taja ta tsaya,

Dayar tace"kuma shima dan iskan dai ne dama anbi mata kafin aure an saba lalata inba haka ba ya zaai yakai shekaru arbain beyi aure ba idan ba yana samu awani wuri ba?,yanzu sai Allah ya hadashi da yar'iska irin shi ga sakamako sun fara gani ace mace na alada don jaraba bazaya hakura ba"

Kafafun muneera na rawa zuciyarta na zafi idanunta cike da hawaye tai saurin matsawa ta jingina da bango hawaye masu zafi suka fara zarya akan kumatunta maganganunsu na mata zafi , kokadan ibraheem ba mutumin banza bane shi be damu da sex dinba ma bare harta kai ga yana nema cikin kazanta ,hawaye suka kara zubo mata ta share ta nufi falon,

Suka kalleta suka kalli KHALEED suka tabe baki lokaci daya sukace "Allah de ya kyauta"

Cikin dauriya ta ajiye tray din gabansu ta zuba masu lemu ,

Dayar tai saurin mika mata ibraheem tace"ungo tafiya zamuyi mun koshi dama shi mukazo gani kuma mun ganshi Allah yaraya"suka mike tsaye,

Kaka dake bakin kofa zuciyarta na ciwo tai sallama ta shiga ciki don taga ko su waye,

Ganin manyan mata dattijai iyaye awurin ibraheem yasa ta tausayamai suka gaisa suka fita ita kuwa ta shigo ciki tana kallon kwayar idanun jikartata,

Muneera tai saurin sunkuyar da kai kuka na zuwar mata,

Kaka ta boye duk bacin ranta tana faraa tace"ke mike damun idanun ki haka duk sunyi ja? "

Muneera tai saurin share hawaye ta dago tace"bakomi"

Kaka tace"anya ? To bani angona"

Muneera ta mika shi jikinta sanyaye,

Kaka ta daga shi sama tana mai wasa ta jinjina shi tana faraa tace"tubarkalla angona ya cika baya se wayo yake "

Muneera de tana tsaye batai ko murmushi ba,

Kaka na mai wasa ta meda kallo wurinta ta rage murmushi tace"inafatan kuna lpy?naganki sukuku"

Muneera ta kakaro murmushi tace"lpy kaka ki zauna kisha ruwa bari na kawomiki abinci "

Kaka tace"yi zamanki na koshi ba dadewa zanyi ba tafiya zanyi saboda akwai sabgar da zanje "

Muneera ta kalli kakar tai karamin murmushi ,

Suka zauna ta mika mata ruwa tasha tana rike da KHALEED tanata fadin tubarkalla ta kalli muneera tace"shi yanata kiba ke kina rama ko tsoron tsotso ne?"

Muneera ta sunkuyar da kai tana karamin murmushi batare da magana ba,

Kakar tace"kirika cin abinci kinji yar kaka kuma ki kara kula da danki domin Allah ya mishi baiwa"

Muneera tadai kara murmushi ,

Suka dan kara labari kaka nata kara jawo hankalinta cikin dubara, ta bata tsarabar data musu muneera tai mata rakiya ta tafi,

Tana dawowa ta zauna tana kallon KHALEED din maganar kaka na dawo mata na cewa Allah ya mishi baiwa bata gane komi akan hakan ba se maganar matan kawu data dawomata ranta badadi idanunta jawur tai tsoki ta fiddo nono tai bismillah tafara bawa KHALEED tana ganin idan har komi na dangin ibraheem zai rika bata mata rai to tabbas bazata kara shekara duniya ba domin kafin shekarar ta mutu,

Ta gama cika mai ciki ta shiga kitchen tana girki tana tunani domin abun yaki barin zuciyarta,

Muneera bata damu da maganganun ba kamar yadda kaka ta damu don tunda ta koma zaune kawai take ta kasa komi maganganun matan sun dagamata hankali matuka, kuma yadda ta samu jikarta bai mata dadi ba ,takasa koda saka wani abu a bakinta kuma dokin ganin muneerar bai bari taci ba dazun tana zaune haka se zuwa dare ta samu shan hura me tsamin gaske ,

Tunda tasha hurar zafin zuciyarta ya karu ta rika taso mata kunsan idan olsa ta hadu da damuwa tana illa sosai ,

Wani irin ciwo ne ya tasowa kaka taita juyi itakadai a gida ,har wanshekare sannan wata kawarta tsohuwa ta shigo ta sameta har lokacin bataci komiba tana fadamata abunda ke damunta abunka da kauye se kawomata sake_saki tayi kakar nata fama har 3days sannan megari yasa aka dauketa suka kaita asibity ,

Bayan an kwantar daita ne aka nemi ibraheem aka fadamai yana wurin aiki ya taho asibitin seda yafara ganinta sannan ya nufi gida ,

Muneera na zaune tana yiwa KHALEED tawai ya shigo jikinshi sanyaye yazo ya zauna tana murmushi tace"sannu da zuwa"

Yace"yawwa "yana kallonta,

Tana kallon yanayinshi tace" yau kagaji sosai kuma naga kayi saurin dawowa"

Cikin sanyin murya yace "ina wurin aiki aka kirani kaka bata lpy ,sun riga sun kaita asibitin naje na samesu"

Tashin hankali muneera batasan time data mike tsaye ba hawaye suka fara mata zarya a fuska ,

Yace"kiyi hakuri jikinta dasauki"

Tana hawaye tace"tafiya zamuyi ko?"

Yace"eh tanata nemanki"

Bata kara magana ba ta nufi ciki two minutes kadai ta fito da gyale tai waje dasauri ,

Ibraheem ya tashi yabi bayanta ya bude motar ta shiga suka tafi asibitin,

Tana shiga dakin tafara sabbin hawaye zuciyarta na up and down a tsorace ta isa wurin kakar tana kuka ta tsaya kallon jikin kakar da drip dake shiga jikinta kuka me karfi ya kufcemata da yayi sanadiyyar budewar idon kakar ,

Tai kneel down tana jikin gadon take kiran "kaka...kaka..don Allah karki tafi kibarni"

Kaka tasa dayan hannunta ta dafa muneera cikin muryar marassa lpy tace"rashin lpy ba mutuwa bace muneera"

Muneera ta dago idanunta jage_jage tana kallon kakar ,

Kakar ta meda ido ta rufe ita kadai tasan yadda take jin jikinta,

Muneera na durkushe ibraheem yazo ya sameta ranshi bace yace "idan har kuka zakiyi tayi anan to kitashi mu koma gida,ba kawoki nayi ki karamata ciwo ba kawoki nayi ki kula daita idan har zaki cigaba da daga mata hankali to kitashi mu koma"

Muneera tai gumm lokaci daya don tabbas seya medata gidan,

Tsohuwar dake tare da kaka tace"sai hakuri addua itace ba kuka ba"

Kaka kuwa bata kara bude ido ba dukda ba bacci take ba,

Kullum muneera na nan ita ke jinyar kaka se dare ta tafi tunda safe kuma ta dawo har bayan kwana ukku ranar jikin kakar dasauki sosai domin harta tashi zaune ,

KHALEED na rungume daita muneera nata farinciki jikin kakarta dasauki tana kallonsu tana jindadi,

Kakar tace"duk lokacin dana daukeshi se in rika jindadi a zuciya ta ,inaji a jikina yaronnan me jinkai ne"

Muneera tai murmushi tai shiru dai,

Tsohuwar tace"ai KHALEED akwai shiga rai ni kaina jinshi nakeyi sosai"

Muneera nata murmushi kaka tace"Alhamdulillah ko yanzu Allah ya cikamin burina gani rungume da jikana ,nan gaba kirika turominshi kawai idan na ganshi ya wadatar basai na ganki ba"

Muneera tace"haba kaka nice fa"

Sukai dariya gabadaya,

Kaka tace"ade ta hakuri muneera kinsamu miji nagari tun kwanciyata kullum shine keta hidima dani yana matukar sonki ki kara kula dashi sosai ki mishi biyayya, Allah kuma ya maku albarka"

Kawar kaka tace"amin amin"
Sunata labari
Lafiya lau da dare sukai bankwana ibraheem yazo ya dauketa suka tafi,

Bayan sun kwanta cikin dare akaiwa ibraheem waya jikin kakar ya tashi bai tsaya tashinta ba ya tafi yana zuwa ya samu kaka cikin mawuyacin hali,

Duk yadda take ciki bataki tunowa da jikarta ba tana nishi tace"iro nabar maka marainiyar Allah amana ka riketa amana karka bari tai kukan maraici"tana cigaba da nishi tace" nagode ... sosai Allah ya shiryamaka zuria"

Ibraheem sannu kawai yake mata har zuwa lokacin mutuwarta da suka rika karanto kalmatush shahada har ta karba tayi sannan rai yayi halinsa,

Kawarta nata kuka ibraheem ya rufeta hawaye na zubomai yana jin mutuwar sosai a zuciyarshi yana tausayin halin da matarshi zata shiga,

Bai dawo gida ba har asuba muneera ta tashi babu shi ba motar shi,har tagama shiryawa da komi har safe tana jiran yazo ya dauketa su tafi asibity amma shiru shi kuwa sun dauki gawar kaka sun nufi kauye domin yi mata sutura,baisan taya zaifara fadawa muneera mutuwar ba yanajin matukar tsoro,

Muneera tagaji da jiranshi ta fita ta hau mashin ta nufi asibitin da shigarta ciki taga gadon wayam,

Jikinta sanyaye ta tambayi na kusa dasu nan suke fadamata rasuwar kakarta,

Jin abun tayi tamkar tatsuniya kokadan bata yadda ba kaka da jiya ta samu sauki har sunsha labari ?

Ta fita a firgice ta nufi tasha ta hau motar kauyensu batare da wani tunani ba,

Tana ciki har motar ta cika suka dauki hanya lokaci zuwa lokaci tana sharar hawaye tana tausayin kanta fatanta taje ta samu kaka gida lpy ,

Suna isa ta nufi gidansu kai tsaye bata karasa ba taga dandazon mutane zazzaune daga ciki kuwa harda mijinta ya tsunduma cikin tunani baiko kula daita ba,

Ta zuba mai ido duniyar na juyamata dagaske ne kaka ta rasu? Zuciyarta ta kara tabbatar mata da hakan, kanta ya mata nauyi ta dena jin komi tai baya ta fadi kasa wurin ba numfashi jikinta.
[4/4, 10:33] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 13&14


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*



KHALEED ya tsanyala kuka, hakan ya medo hankalin mutane wurinta sukai wajanta suna fadin "subhanallah!!subhanallah!!"

Surutun jamaa ne ya medo hankalin ibraheem jikinshi don ko kukan KHALEED din baiji ba ya zubama wurin ido se ganin zanin matarshi yayi kwance maza zagaye daita suna mata fita,

Baisan lokacin da ya isa wurin ba saboda sauri da kidima, ya zukunna jikinshi na rawa ya rungumo abarshi jikinshi yayinda KHALEED ke hannun wani yanata rirrigashi,

Baai two minutes ba aka kawo ruwa ya amsa yana cikin tashin hankali ya kwara mata su ta farka firgigit tana haki sai kuma ta fashe da kuka me ban tausayi da duk mutanen wurin seda suka tausaya mata,

Ibraheem baisan lokacin da hawaye suka zubomai ba ya rika sharemata hawayen dake zubarmata a fuska,

Ta cigaba da kuka idanunta warwaje tana tsorace ganin duk idanun jamaa na kanta yasa ibraheem ya jata cikin gida ta bishi jikinta a matukar sanyaye suka shiga ciki suka samu mata nata zubarda hawaye suma wasu sunyi jungum_jungum ba yadda yaso ya ajiyeta ya juya saboda gidan dake cike da mata,

Wanda ya dauki ibraheem ya mikama wata shi ya fita ,

Fitar shi mutane suka fara bawa muneera hakuri hakan yakara daga mata hankali shikenan fa dagaske kakar ta tafi ,jiya bankwanar karshe sukayi da kakar ta hade kai da gwiwa ta fasa kuka tana jin kamar ta fiddo zuciyarta waje saboda tsananin zafin da take mata,

Ta kwashi lokaci tana kuka sannan ta bawa kanta hakuri da kanta ta dago kai tafara bin gidan da kallo tana tunano lokacin da suke rayuwa aciki ita da kaka ,hawaye masu zafi na zubomata idanunta suka sauka kan KHALEED da keta ajiyar zuciya yaci kuka ya gaji,

Ta kuramai ido tana jin tausayin kansu tai saurin mika hannu aka bata shi ta fiddo nono ta fara bashi tana hawaye,

Da rana ibraheem ya koma birni ya dauko mata kayan sawarsu domin su zauna har ayi bakwai ya kawomasu ,

Muneera na zaune kauyen tanavta amsar gaisuwa tana shan kukanta har akai sadakar bakwai sannan ibraheem ya dauketa suka koma gida,

Tunda ta koma gidan ta rage kukanta domin tasan hakan zai damu mijinta ita kuma bazata so ya shiga wani hali ba domin shi kadai ya rage mata shine komai nata a yanzu sai danta KHALEED da take jin tausayin rayuwarshi sosai,

Haka suka cigaba da rayuwa tanata yiwa kaka addua tana kuma kula da iyalanta ibraheem yanata samun arziki ,shi kuwa KHALEED yanata girma da wayau,


*BAYAN 3 YEARS*


Abubuwa da yawa sun faru harda kammala karatunta da zuwanta hajji da umara yayinda KHALEED yake 3yrs amma haryanzu shiru babu wani cikin, wannan karon basu damu ba fatan su Allah yaraya masu KHALEED dinsu sosai suke sonshi yana da shiga rai matuka da kuma saukin hali,

Time dinne akasashi makaranta saboda yayi wayau sosai ,

Tunda safe ta shiryashi ibraheem ya daukeshi a motor har bakin school dinsu sannan ya juya ya tafi yabarshi

KHALEED na shiga duk idanun dalibai suka koma kanshi sunata masa wani kallo tamkar ba mutum ba kamarsu ,

Hakan yasa duk ya tsargu ya takure wuri daya har malami ya shigo class dinsu ,

Abun mamakin malamin na shigowa shima hankalinshi ya karkata wurinshi ya kasa hakuri seda ya tambayeshi "kai ya sunanka?"

KHALEED na takure yace"KHALEED "

Malamin ya kara kallonshi sosai fuska daure yace"tashi ka koma baya"

KHALEED ya tashi ya koma baya yanata bata fuska kamar yayi kuka ,

Seda malamin ya kara kallonshi sannan yafara masu karatu duk rabin kallonshi na wurinshi hakan dalibai ,KHALEED yana takure har akai break kowa yana cin abinci amma shi yakasa cin nasa har zuwa lokacin tashi baici komi ba kuma baiko kula da me ake koya musu ba,

Bayan antashi muneera tazo ta daukeshi yana sukuku tun kafin sukai gida ta fara tambayarshi "KHALEED lpy waya buge ka?"

Ya girgizakai yana kara tabe baki ,

Tai murmushi tace"to ya akai?"

Kamar zai kuka yace"sai kallona suke kowa yanata kallona Malam kuma yace na koma baya"

Ran muneera ya sosu jin yakoma baya saboda me ?don basusan ganinshi kome?

Tai murmushi tace "kayi hakuri karika zama a bayan amma fa ka zama me kokari saboda nangaba karatun zai maka amfani kuma abbanka zai maka kyauta sosai"

Ya daga kai,

Suna ta tafiya yana jikinta tafara tunanin duk yawancin masu zama baya basu cika kokari ba a hankali tace"me aka koya muku?"

Yayi shiru,

Ta bata fuska tace"ka rika karatu dana in kuma so kake raina ya rika baci shikenan"

Yayi saurin girgizakai yace"kiyi hakuri mamana"

Tai murmushi tace "to nayi amma fa seka meda hankali wurin karatu"

Ya jinjina kai tanata mai nasiha cikin dubara har suka isa gida tai masa wanka ta rungumeshi ta bashi abinci bayan yaci ya koshi ta kwantar dashi kafin lokacin islamiya yayi su tafi tare domin can take teaching,

Ba jimawa bacci ya kwashe shi itako tana zaune tana tunani har abbanshi ya dawo dukda ta boye damuwarta seda ya fahimta memakon ya tambayeta me akai sai cewa yayi"ya dan makaranta lpy lau dai ko?"ya dauki spoon yakai baki,

Tai shiru sannan tace"to alhamdulillah zaace amma yace kowa nata kallonshi malaman kuma sun medashi seat na baya kukane kawai baiyi ba"

Ibraheem ya tsaya da cin abincinsa ya danyi tunani sannan yace "idan abun ya dore haka inaga idan yagama primary zan kaishi London yayi karatu n acan cikin turawa bazai samu matsala sosai ba"

Muneera tai karamin murmushi tace" Nagode Allah yakara budi "

Yayi murmushi kawai yace"karki damu kanki"ya cigaba da cin abincinsa,

Hankalinta ya dan kwanta itama har ta danci abincin,

Daga time din kullum kafin KHALEED ya tafi school sai ta bashi hakuri ta masa nasihar karatu sosai sannan wannan yasa ya rika meda hankalinsa kan karatun duk exam shike yin na daya amma irin tambayoyi a class malaman basa ta dashi tun yana daga hannu harya bari baida aboki ko daya daga islamiya har bokon sede wani lokaci diyan Baban farouk su khaleefa suzo koshi akaishi shima ba sosai ba ,

Ibraheem kuwa kullum cikin kwaso masa kayan wasa yake don su rika debe mishi kewa,

Wani lokaci seya tsaya bakin mirror ya rika kallon kanshi yanason sanin me ake kallo a jikinshi dako giftawa sukayi sai mutane sun kalleshi ,amma bai gano komi ba sai farin da ke jikinshi ya matukar shiga rudani,

Yau da gobe tun KHALEED na damuwa harya dena bai damu da kallon mutane ba bai damu da abokai ba kowani abu abinda yasani kawai shine mamarshi da babanshi na sonshi suna masa komi soyayyarsu ta cike masa duk sauran guraben,

Har bayan 6yrs yayi candy suka gama shirin tafiyar shi London duk Hutu zaa rika dauko shi ,

Ranar daren da zai tafi basuyi bacci ba dukkan su more especially su biyun shi kuka muneera kuka tana kuka tana rarrashinsa washegari jirginsu ya daga zuwa London,

Muneera kadai cikin gida tasha kukanta har bacci ya dauketa,

Washegari ibraheem ya dawo taje ta tarbeshi tana murna yana ganin idonta ya gane batai bacci ba,

Suna zama tace"sannu kunsha hanya ya can din?"

Yayi murmushi yace "maman KHALEED"

Tai murmushi ta sunkuyar da kai,

Yace"lpy lau da kaishi har ya samu abokai can din zai saki jiki sosai kuma zaifi samun karatu"

Tana jindadi tace"alhamdulillah KHALEED na son abokai amma bai samu hakan ba"

Yayi murmushi yace "kawomin abincina yunwa nakeji"

Tana murmushi tace"ai ban dafa komi ba duk dokin dawowar ka bai barni nayi ba"

Yana murmushi yace "kode kewar danki? anya muneera akwai dan da zaki so Fiye da KHALEED?"

tai karamin murmushi tace "don de ban kara haihuwa bane shiyasa"

Yayi karamin murmushi yace "zasu zo insha Allah kiduba 10yrs da mukayi ba KHALEED amma yanzu abun yazama labari"

Ta jinjina kai ta tashi tace"bari na kawomaka abincin"ta nufi kitchen,

Ibraheem ya sauke ajiyar zuciya yana kallon gidan se yaga ya mishi fadi duk ta kauda kayan wasan KHALEED se yaji yana son samun wasu yaran kusa,

KHALEED yana matukar jindadin rayuwa a London har akai Hutu sannan ibraheem yaje ya daukoshi ya karayin fesss dashi ya koma kamar baturen yanata annashuwar shi,

Har suka karaso gida ya fita a motar da gudu ya shiga gidan yana k'walawa sweet mom dinshi kira "mama!!!mama where are u ?I'm back!!!!" Sede yajishi caraff a sama duk girman da yafara ta dagashi tana jujjuyashi sunata dariya sannan ta ajiyeshi ta zaunar dashi kan cinyarta yafara kokarin tashi yanajin kunya tace"come on seat properly,bani labarin school da result din ka"

Yayi murmushi yace "mama ina normal life a can " yana murna yace"and na 5th nayi "

Ta fiddo ido tace"5th KHALEED? "

Ya bar murna lokaci daya ya langwabe kai sannan yace"mama nayi kokari sosai"

Tai murmushi tace"eh kayi amma ka kara dagewa ka rika na dayan da ka saba "

Ya jinjina kai,

Tana dariya tace"tsarabar me kayomin?"

Yayi murmushi yace "chocolate"

Tana dariya ta fiddo ido tace"all the way from London? "

Ya bata fuska yace"mama"

Tace"sorry,,sorry muje na maka wanka"

Ya kwalalo ido again yana kallonta yace"naam!!!"da karfi ya zame yayi room dinshi da gudu,

Ta juya taga ibraheem tsaye yanata faraa yace"ki bishi ki mishi wankan ko"

Tai dariya tace"I'm just teasing him ya wuce wanka ai"

Ibraheem yace"to muje ni ki min"

Ta waske tana dariya ta nufi bedroom yayi murmushi ya bita,

Tunda KHALEED ya dawo Hutu kullum yana gida itake koyamishi karatu don anwuce shi, bai shaawar fita sam iyaka ya tuno friends dinshi dake London har ya koma,

Wannan karon da zai dawo na 3 yayi kullum zata nuna mishi ya dawo na dayan bata taba nuna cewa yayi 100% sannan kuma bata nuna baiyi ba bayan lokaci ya rika dauko na dayan wannan yasa yakara yawan abokai domin kokarin shi da faraarshi malamai ma sosai suke son shi,

Yana 15yrs ya gama secondary ya dawo gida he's very _very surprise and happy ranar daya dawo daya samu mamanshi da ciki harya girma murnar dasu muneera sukayi time da suka San da cikin baikai tashi ba ,gabadaya hankalin shi ya koma kan cikin yana kagare ya fito duniya yaga kanwarshi ko kaninshi ,

Baida Hutu shine shara shine wanki shine girki shine tausar mata kafa kokadan bai gajiya tun tana hanashi hartai shiru sede addua da take mai Allah yabashi me mishi fin haka amma tana alfahari da kasancewar shi danta duk wani abu da yasan zai karawa cikin daita lpy shiyake dafawa tana zaune zai yanko fruit yakawo ya hada wannan ya kawo wannan ,

Shi kuwa babanshi hankalin shi kwance ko baya gida domin yasan akwai me kula daita a gidan,

Result dinsu na fitowa ibraheem ya gama shirin tafiyarshi London inda zai cigaba da karatunshi na degree nan da kwana 100 masu zuwa,

Bayan 1month da daddare suna zaune falo suna kallo muneera na zaune kasa ta mike kafafu KHALEED nata danna mata su,

Ta kalleshi tace"KHALEED wai baka gajiya ne?"

Yayi murmushi ya kalli abbanshi yace"mama kema kina gajiya dani time da nake yaro?"

Ibraheem ya fara dariya yana dariya yace"good answer ,ai KHALEED bata gajiya da kai kuma bazata taba ba"

Muneera ta balla mai harara ya tsaya da tausar ya hade hannuwa yace"sorry mama inaso kigane bana abinda ya dace saboda bana rabin abinda kikaimin"

Tayi murmushi tana tuno firarsu ta karshe da kaka tana cewa zaiyi jinkai, ko yanzu alhamdulillah bare taga dannata yana girma yana kara kaunarta da kula daita,

Ibraheem yace"Allah yayi maka albarka ina alfahari da kai koda yaushe nasan ko bana raye mahaifiyarka tana da me kula daita kuma nasan kannenka baza suyi kuka ba"

KHALEED yace"insha Allah Abba"

Ibraheem yace"Allah ya maka albarka"

Yace"ameen"

Muneera ta juya tana kallon ibraheem maganar shi batai mata dadi ba duk da de medadi ce batace komi ba ta meda kanta wurin KHALEED,

KHALEED na tsaka da mata tausa ya kalli yatsun kafarta ya tashi can zuwa ya dawo da razor ya zukunna ya kama babban dan yatsanta hankalin muneera awurin kallo tai saurin kallonshi jin ana yanke mata akaifa tace"a'a KHALEED arika bari ta fito mana kafin ta fito an fitar arika bari tana fitowa"

Yayi murmushi yace "to mama"duk da ba barin zaiyi ba don ya lura batason wani na yanke mata akaifa shi kuwa baison ladar ta wuce shi,

Suna ta firar su sannan sukaje su ka kwanta bacci,

ibraheem ya rungumeta yanata luliyar cikinta har tai bacci batasan time daya bari ba,

Da asuba alarm dinshi yayi ta ringing bai tashi ba har ita ta tashi tafara tada shi amma bai motsa ba ta sauka ta zagaya ta kashe alarm din ta dawo ta zauna ta cigaba da tashin shi daga barcin a hankali" Abbanshi...Abbanshi asuba fa tayi "

Shiru ba motsin shi hakan ya daga mata hankali ta dalla fitila akan fuskar shi idanun shi kulle kamar mai bacci amma Sam baya numfashi tafara"innalillahi wainna ilaihi rajiun!!! "Cikin kuka tana ta bubbugashi ko zai tashi amma shiru ibraheem baya motsi zuciyarta na tsananin harbawa ta dafe kai tana kuka ,

KHALEED yagama rakaatanil fajr ya fito zai wuce masallaci yaji kukan mamarshin zuciyarshi na mugun bugu yaje bakin kofar dakin har ya daga hannu zaiyi knocking yafasa ya wuce masallaci,

Zuciyarshi na bashi ko labour take shiyasa ya dage yi mata addua acikin salla,

Gari ya fara haske ya nufi gidan jikinsa sanyaye ya samu tanata kuka still, ya shiga ya isa bakin kofar yafara knocking domin kaida dama idan ya dawo yakan shiga ya gaida Abbanshi ya gaido muneera sannan yawuce daki,

Muneera nata kuka bata iya bashi izinin shigowa ba,

Hankalin KHALEED tashe yafara kiran " Abba..Abba !!!!"yanaso yace masa su tafi asibity daita,

Maganar shi ba karamin daga hankalin muneera tayi ba takara yawan kukanta yanzu bawanda KHALEED zai kira Abba domin Abbanshi ya tafi inda baa dawowa ta kalli cikinta zuciyarta na kara tsananta zafi da bugawa,

Jikin KHALEED na kyarma jin kukan na karuwa ya buga kofar da karfi yace"Abba ka fito mu kaita asibity"

Muneera ta bude bakinta na rawa tace"KHALEED ka shigo"

Yayi tsaye jin muryar mamanshin baiji ta abban nashi ba yaki shiga ya kara cewa"Abba!!! ya kamata mutafi asibity"

Muneera na kuka tace"kashigo KHALEED abban naka ya rasu"ta karasa dakyar.

Wani irin kaduwa KHALEED yayi, faduwa kadai ce baiyi ba ya tura dakin dasauri idanunshi na ganin biji_biji ya sauke idanunshi akan gawar mahaifinna shi, kafafun shi na rawa yayi zaune kasan ya saki kuka ,kuka me ban tausayi da karya zuciya yana tuno yadda mahaifinshi ke nuna

Please Login or Register in order to submit comment