Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ya kabbara sallah,

Muneera nata jiranshi shiru ganin gari nata haske yasa ta tashi tayo alwala ta dawo ta kabbara sallah,bayan tagama ta koma inda take ta zauna tana jiran ya dawo taje ta hado masu breakfast kafin Zarah ta farka,

Bayan ya gama sallah ya kulle gidan ya nufi asibitin,yana shiga ta tsaya kallonshi ganinshi da sabbin kaya ba wadanda ya fita dasu ba ,

Ya sunkuyar da kai ya karaso ciki a hankali yace"Mama ina kwana"

Tace"Lafiya lau inata jiranka ka dawo nai salla, kaida nace kaje kayi ashe gida ka wuce"

Yace"Kiyi hakuri "

Ta mike tace"Ka zauna gunta inje in hado mana breakfast in samo mata kayan sawa kafin ta farka"

Ya kalli Muneera yace"ko naje na siyo breakfast din?"

Tace"No ka zauna ka kula daita inaso nai wanka dan Allah karka tafi ko ina"

Yace"tom mama"ta kalli Zara ta juya ta fita,

Ya meda hankalinsa kan Zarah yana kallon kyakkyawar fuskarta Sam baiso ya kalli jikinta amma zuciyarsa ta kasa hakura a hankali ya dan kalli small breast dinta yanason dauke idanunsa akai ya kasayin hakan amma bai iya gano dalilin kallon ba,

Muneera ta koma gida ta hado masu tea da Fried egg tai wanka ta dawo asibitin,

Tana gaf shiga wayarta tafara ring ta dauka wani sanyi na ratsa zuciyarta tana murmushi ,

KHALEED yace"Mama ina kwana ?ya ruwa naji ance kunsha ruwa jiya"

Tana murmushi tace"lafiya lau munsha ruwan sama jiya"

Yayi murmushi yace "Alhamdulillah shiyasa jiya naita kira da daren ban samu ba,ina WALEED?"

Tace"yana lafiya"

Yace"alhamdulillah babu wani abu?"

Tace"bakomai Daddy "

Yayi dariya yace "Mama na kusa dawowa maybe kafin next month na dawo"

Tana farinciki tace"Allah yakaimu ina cikin farinciki da dokin ganinka kowane time but kar a mana surprise idan ka kusa u should let me know"

Yayi murmushi yace "To Mama nagode sosai sai na kara kira"

Ta kashe wayan tana murmushi ta shiga asibitin,

KHALEED na kashe wayar ya kira WALEED domin jin lafiyarshi hankalinshi ya kara kwanciya,

KHALEED ya dauka yace"Daddy ina kwana"

KHALEED yace"Lafiya lau WALEED ya zaman gida da yawo?"

Yayi karamin murmushi yace"ba yawo daddy ina gida kullum"

Yace"ihmm to yanzu bani Mama muyi mgna in kana gidan"

WALEED ya kalli Zarah yace"daddy ai muna asibity tun jiya"

Hankalin KHALEED ya matukar tashi yace"waye ba lafiya?"

Yace"wata yarinyace mama ta tsinta kofar gida shine muka kawota"

Hankalinshi ya dan kwanta yace"to Allah yabata lafiya "

WALEED yace"ameen"ya kashe kiran,

Mama ta shigo dakin ta samu WALEED ta kalleshi tace "kaje kaci abincin ko kadan ka kwanta ka huta"

Yace"Na koshi zan zauna anan"

Ranta badadi tace"Saboda me?so kake ciwo ya kamaka kome?to ka zauna anan kaci abincin in yaso ka tafi gidan ka kwanta kaiko tausayin kanka bakaji?"

Yayi shiru baice komi ba ta hada mai tea ya amsa ya fara sha ,

*Ruga*

Tun washegari aka taru wurin megari ana jimamin abinda ya faru jiya da dare,ga shanun Baban Zarah a daure,

Me gari yabawa duk wadanda shanun su da dabbobinsu suka mutu dabbobin shehu sannan yasa akara binciko masa Zarah a dajin, aka kara bincikowa ba Zarah ba labarinta,

Suna dawowa suka fada yace"tunda haka ta faru zan tura har kauyensu anemota don tazo ta fadi dalilin guduwarsu da daddare idan har baa sameta ba to lalle satar shanun sukazo se a bincika kauyensu idan akwai shanun da aka rasa bayan zuwansu anan idan akwai zamu basu kayansu in kuma babu yan uwanshi sai suzo su kwashe sauran dabbobin nashi amma zaman da zasuyi anan duk abincin da suka ci zaayi lissafi su biya kudinshi"

Mutanen gari sukai naam da hakan haladu dai ya kama bakinsa yayi shiru yana gefen Murtala amma ko kallonshi bai kwatanta yiba saboda tsoro, yana tsorace idan yayi wani motsi shi baisan wane Sheri zaa kulla mai ba amma cike yake da regretting shawarar daya bawa shehu,

Me gari ya zabi mutum ukku akan yau zasuje garinsu Zarah daga ciki kuwa har da Murtala danshi,

Yau din tunda sassafe suka tari mota bakin titi suka nufi garin kuhon kanawa,



*******************


WALEED na komawa gida yayi kwance kan kujera a falo bai dade da kwanciya ba kiran Hameed ya shigo ya dauka yace"Ya akai"

Yace"ka fito dan Allah mu fita kanason zama gida kamar wata mace"

WALEED yayi karamin murmushi yace"Ka shigo ciki ni kadai ne a gidan"

Yace"OK"ya bude gate ya shiga ciki,

Yana shiga falo ya ganshi kwance idanunshi jawur, ya zauna kujerar gefenshi yace"Bakayi barci bane?"

WALEED yace"eh kuma banaji"

Yace"meyasa?"

WALEED yace"Muna da patient a asibity"

Hameed yace"Waye ba lpy da har bakayi bacci ba?"

WALEED yayi shiru kamar bazai magana ba yace"wata ce"

Hameed yace"Wacece ?ko cikin dangin ku na kauye?"

WALEED ya masa wani kallo yace"wallahi ka gane surutun tsiya ga tambaya kamar dan jarida haba"

Hameed yayi dariya yace "so kake naita zama kamar ka ,yanzu ya kamata muje asibitin in dubata"

WALEED yace"ba yanzu ba bacci zanyi sai wani lokaci"

Hameed yace "okay ba matsala kafadamin awace asibitin ne mana"

WALEED ya kura masa idanu yana kallonshi gabadaya HAMEED din yanata sauyawa ba kamar da da suke yara ba shegen son matan tsiyane dashi ,hakanan yaji bai son yaga Zarah don ba shakka yana iya cewa yana sonta don shi kanshi ya sani ta hadu she's cutie,

Yayi tsoki yace "ka bari sai gobe tsohuwa ce sosai tana cikin ciwo sai ta farfado "

Hameed yace"OK bari in kira mama se tafadamin a wace asibitin ce dama ita nakeson gani ai"ya tashi tsaye,

WALEED yayi saurin rike hannunshi yana murmushi yace"ka cika k'wak'wa ka jirani na dan huta sai mu tafi tare"

Hameed yayi dariyar rainin hankali ya koma ya zauna ya jingina da kujera ya lumshe ido ba jimawa bacci ya daukesa,

WALEED yaji dadi a ranshi ya juya kwanciya ya rumtse ido yana fatan baccin yazo masa shima dakyar ya daukesa,

Muneera tasan halin WALEED sarai da wuya ya mata aiki saide ma ita ta rika masa tasan bai iya girki ba balle yayi gashi rana tayi tanaso tai girkin ko don shi ya danci amma dole ta hakura saboda Zarah ta cigaba da zama wurinta,

Bayan sallar azahar Zarah ta farka abinda ke cikin zuciyarta tafara tunawa ta fara bude idanunta a hankali sun mata nauyi a haka ta budesu kan Muneera,

Ta dan tsaya tana kallonta tana tuno temakon data mata jiya kanta ya Sara ta dafeshi tana yamutsa fuska,

Muneera ta riketa dasauri tace"sannu"

Ta kuma bude ido ta kalleta ta kalli saman dakin ,

Muneera tace"sannu kina iya tashi? "

Zarah ta fara kokarin tashi amma ba karfi jikinta muneera ta kamata ta tadata zaune tace"mu tafi toilet nai miki wanka da brush jikinki ya danyi dadi"

Zarah ta kalleta jin ta ambaci wanka tai shiru kamar kurma ,

Muneera ta tadata tsaye suka shiga toilet ta tara ruwa tai mata wanka da brush ta sa mata pant da pad sannan ta kamota zasu fito ,

Cikin murya me rauni Zarah tace"zanyi Alwala"

Muneera ta medata tayi suka dawo dakin suna zuwa wurin gadon muneera taga ya dan baci jinin ya dan fito ta linka zanin biyu Zarah ta hau ta dan zauna ,Muneera ta fiddo mata doguwar riga ta sa mata ta hada tea ta zauna tana bata a baki,

Zarah na shan tea din tafara sabbin hawaye tana tuno innarta da take matukar sonta ba abinda take tunowa in ta kalli muneera sai inna ,

Muneera dai ba tace mata komi ba har ta samu ta dansha ta bata magani ta fara kokarin gyara mata kwanciya,

A hankali Zarah tace"sallah..zanyi"domin bata wasa da salla kuma tana so taiwa baffanta addua,

Muneera ta tsaya tana kallonta wani tausayinta yakara mamayeta jin tana sallah da najasa sarai tasan kauye musamman Fulani da kullum ana daji basu damu da neman ilimi ba ,

A hankali cikin dubara tace"ai baki lafiya kiyi kwanciyar ki"

Zarah na hawaye tace"zanyi sallah nide"

Muneera ta kirkiro murmushi tace"Bakiga kina jini ba? idan ana jini baa sallah"

Idanun Zarah jawur ta dan kalleta itade ta fiso tayi salla domin tanayin sallah a kowane hali,har tayi shiru ta kasa hakuri tace"dagaske?"

Muneera tai murmushi tace"Eh Allah ya haramta yin sallah ga masu jinin al'ada Wadda tayi kuma tana sane ya tanadar mata azaba me radadi"

Gaban Zarah ya fadi ta dalo ido tana jin tsoro,

Muneera na cigaba da murmushi cikin kwantar da hankali tace"Kila kinayin sallar idan kinayi amma Allah bazai kamaki da laifin da baki sani ba yanzu tunda kin sani saiki dena kinaji?"

Memakon ta amsa sai kara kwantar da kai tayi jikin gadon dama karfin hali ne, muneera ta gyara mata kwanciyar tana jin son Zarah fatanta ta samu hanyar taimaka mata saboda tana bukatar temako a kowane bangare,

Bata dade da kwanciya ba nurse ta shigo ta tsaya tana dubata tace"ya me jiki?"

Muneera tace "dasauki amma batason cin abinci jikinta kuma ba karfi"

Nurse din na tsaye ta kira Zarah da muneera sunan da sukayi using a file tace"Muneera meke damunki yanzu?"

Zarah ta bude ido ta kalleta a hankali tace"Juwwa zuciyata na ciwo"

Nurse tace mata"sannu zakiji sauki very soon"ta karasa da murmushi ta juya ta fita,

Zarah ta meda idonta ta rufe tana maimaita beri sun Sam bata gane kowane yare bane,

Ba bata lokaci ta dawo dauke da ledoji ta ajiye kan drawer dinsu ta fiddo drip ta fara hada shi zata sa mata,

Muneera nata kallo ta gama hadawa ta kama hannun Zarah domin sa allurar cikin jijiya muneera ta yamutsa fuska ta rumtse ido tana jin tausayin Zarah itako zaran komi bataji ba har tasa mata tanata mata sannu ta tsaya gyara shigar ruwan,

Muneera ta bude ido tana kallonta idanunta a lumshe ,

Tace"sannu"

Zarah bata amsa ba Nurse ta gama hadawa ta tafi,

Sai bayan azuhur WALEED ya farka ya kalli HAMEED baccinshi kawai yake sha ya tashi ya shiga dakinshi yayo wanka ya fito ya sauya kaya yayi sallah sannan ya fito har lokacin HAMEED na bacci,

Ya girgiza kafarshi da karfi,

HAMEED ya bude idonshi jawur ya kalleshi ,

WALEED yace"kai lafiya wannan bacci haka kamar Wanda yayi sati ba yayi?"

HAMEED yayi hamma yace"Jiya munata free call da baby ba muyi bacci ba"

WALEED yace"Allah ya shirye ka "

HAMEED ya gumtse face yace"Tare da kai"

WALEED yayi tsoki yace"Ka tashi muje asibitin"

HAMEED yace"Wa ?Allah ya kiyaye ni sai wani jikon yunwa nakeji sannan ina jin zafi senayi wanka na sauya kaya"

WALEED yace"to tashi muje fita zanyi"

HAMEED ya tabe baki yace"sai ka jira in yi sallah "ya tashi ya nufi dakinshi yayi sallah ya fito WALEED ya kulle gidan suka shiga mota HAMEED ya tsaya WALEED ya sai musu abinci yana ajiyeshi yawuce gida,

WALEED ya shiga asibitin yana tafiya a natse har dakin yayi sallama ya shiga,

Muneera ta amsa ya shiga ya ajiye ledojin hannun shi yace" Sannu mama ya jikinta?"

Tace"dasauki sosai ruwa suka dora mata"

Ya kalli ruwan har zuwa hannun Zarah ya karasa sauke fuskarsa kan tata idanunta lumshe amma bai iya ganewa ko bacci take ba ko idanunta biyu ya kalli rigar jikinta black da kwalliyar stone farare ta matukar mata kyau ya dauke idanunsa dakyar,

Jikinshi sanyaye yace "Allah ya bata lafiya ga abinci"

Muneera ta kalli bakinshi tace"kai meyasa baka ci ba?"

Yace"naci abinci mama"

Tace"OK nagani ai"tai shiru,

Yayi shiru a hankali yace"yanzu zan fita naci"

Tace "da yafi"

Ya kalleta ya juya ya fita,

Gab Maghreb su Murtala suka iso kuhan kanawa duk da tafiyar motace amma da nisa,

Suna isa sukai sallah sannan suka wuce gidan megari,

Sukai gaisuwa suka koro masa jawabi dalla_dalla,

Me gari yayi jummmm yana ganin da makarkashiya acikin zancen yace"gaskiya...ba Wanda aka satarwa garke har bayan tafiyar shehu kuma ina mamakin abinda ku kace shehu yayi saboda anan ya girma ya tashi bai taba sata ba saide rigimar kudi ko ya amshi kudin mutane yaki basu auren diyarsa"

Murtala yayi dariya yace "Allah na tuba Wanda ke cin amana ai zai iya komi kace zaka bani aure ka cijyemin kudi sannan kazo kace ka fasa ai a wurina gwara barawo"

Na tare da shi suka ce" kwarai ko shiyasa mukeso a fiddo Zarah tazo ta fadi gaskiyar meyafaru"

Me gari yace"to Nide banji labarin dawowar Zarah ba bare inji labarin mutuwar shehu amma bari a kira kaninshi muji koya San inda take "

Ya kalli cikin yaranshi yace"yi sauri kiramun habu"

Suka cigaba da tattaunawa suna cike da al'ajabin mutuwar shehu da kuma satar da akace yayi,

Can suka dawo da habu suka zauna ,

Me gari ya kalleshi yace "Yanzu nan mutanen rugar su shehu suka kawo mummunan labarin cewa shehu yayi satar shanu zai gudu da dare aka kasheshi shi da matarshi ita kuma Zarah ta gudu shine mukeso idan Zarah tazo akawo Zarah muji daga bakinta ya akai meya faru a wannan daren"

Tunda megari ya fara Habu ke kallonshi jijiyoyin kanshi a tashe idanunshi jawur ranshi bace bakin shi na kyarma yace "aradun Allah karyane tuntuni shehu bai sata a nan ba sai acan inda aka sanshi kuma da an wayi gari bashi ba dabbobi dole ace shiya dauka a nemoshi....." Yaja numfashi yana hawaye yace "Aradun Allah an shirya kashe dan'uwana ne amma shehu ba barawo bane bazaiyi sata ba"

Ya tashi tsaye rike da sandarshi ya kallesu daya bayan daya yana hawaye yace"Shegu Munafukai kun kashe shi duka da iyalanshi kuma kun biyo munafurci duk don dukiya, to ku kwashe dabbobinshi duka an bar muku"yana gama fada ya juya yana tafiya yana zubda zafafan hawaye zuciyarshi na kuna don yasan an zalunci yayansa gashi kuma an bata masa suna tare da nasu gabadaya wai shehu ne *Barawon shanu*.
[4/4, 10:34] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 25&26


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*


*Dedicated to Masoyan SHALELE group musamman masu min comments ,Shafaatu, saratu,Soupnas, mom yousup,Ummu affan ,Fatima L yusif,rabi Ahmed,Mrs Sadeek,maman hanan,Ummu hafsat ,anty Hauwa and all*


Yana tafiya Me gari yace"gaskiya abun akwai mamaki da alamu akwai rashin fahimta a ciki"

Wani dattijo cikin su Murtala yace "ba rashin fahimta duk abun tambayar shine meyasa zasu bar gari da daddare? Meyasa ya kora shanun megari dana sahalu acikin nashi? sede aki gaskiya amma shehu yaso satar shanun...Allah ne bai bashi iko ba"

Murtala yace "shine gaskiyar baba mu bamuce dole ku amince ba shiyasa me gari ya turomu don kuji daga bakin Zarah"

Mutanen dake wurin sukace "To ina Zarar? Ai duk ta kare kun kasheta namun jeji sun cinye naman don bata dawo nan ba"

Murtala yayi karaf yace"zata iya yiwuwa tana wani wurin me gari baya zalunci don haka zaku kwaso dabbobin shehu ku dawo dasu nan sannan duk time da Zarah ta dawo zamu dawo domin kuji ta bakinta"yana magana Sam ba rashin gaskiya fuskarsa hankali kwance shide burinshi yaga Zarah ko zaiji sanyi yasan zataji tsoron fadin wani abu game dashi ,fatan shi idan sun hadu ya samu koda damar ganin tsiraicinta ne cike yake da matsananciyar shaawarta har yau,

Me gari yace "Tunda hakane zan aika a kira habu saisu San yadda zasuyi gameda dabbobin waccan maganar kuma zata zauna anan har sai anga Zarah tayi bayanin abinda ya faru da bakinta"

Murtala yayi dariyar rainin wayo suka tashi suka nufi cikin gari cikin ran murtala ya gama tsara yadda zai baza labarin cikin gari,

Habu ya koma gida yana kuka yayi zaune bakin kofar matarsa dogare da sandarshi yanata fidda hawaye,

Matarshi Ladingo ta fito gabanta na faduwa ta zauna kusa dashi tana tambayar "me gida lafiya meyasa kake kuka?"

Habu ya sharce hawaye yace "Sun kashe shehu tare da su inna gabadaya kuma sun lak'a musu satar shanu"

Ladingo ta dafe kirji a firgice tace"sun kashesu?"

Yana hawaye da juya kai yace"su shehu ana lahira kuma kowa na masa kallon barawon shanu"

Ladingo tai zaune gun tana sallallami ta buga tagumi tana kuka tana zubda hawaye"Lailaha illallahu mun shiga ukkun mu"

Ta cigaba da matsanancin kuka me sauti da shiga rai,

A hankali Habu yace"bar kuka Allah na nan, ko ba yau ba asiri zai tonu zaa gane gaskiya amma da kwarankwatsa shehu bazai saci shanu ba"suka cigaba da hawaye suna jimami,

Murtala bai wani zauna ba ya fara zuwa wurin samari tsaranshi cikin dubara yake basu labarin dalilin zuwansu wasu nata tirrr wasu na tausayawa,

A birni ,bayan sallar Maghreb muneera ta koma gida ta bar WALEED wurin Zarah dake kwance har ruwan sun kare an cire,

Tunda ya zauna ya rike wayarshi kamar yana kallonta amma idanunshi na kan Zarah ko kyaftawa bayason yi saboda jindadin kallonta da yake,

Yana zaune kiran HAMEED ya shigo masa,

Ya dauka tare da cewa"Hello"

HAMEED yayi murmushi yace"kana asibitin ne?"

WALEED yayi tsoki ranshi na baci yace"ehm"

Hameed yace"wace asibitin?"

Kamar baison fada yace"that private hosp dake nan ka karaso"

Yace"OK ganinan zuwa "

Ya shiga mota ya nufi asibitin yana zuwa ya kirashi ya fito daga dakin zuwa parking lots yana mai wani kallo yace"mushiga"

Yace"hope ba mutane cunkuss kasan kauye"

WALEED yayi murmushi yace"wurin cike yake ko ba ka iyawa?"

HAMEED ya tabe baki yace"muje hakanan dai in samu ladar"

Suka karasa cikin dakin da Zarah ke kwance,duk suka kuramata ido tana kwance idanunta lumshe hannuwanta biyu kan shafaffen cikinta tana meda numfashi a sannu,

HAMEED ya dauke idonsa ya kalli dakin ya kalleshi yace"ina tsohuwar?"

WALEED yayi mishi nuni da Zarah da idanu,

HAMEED yayi murmushi yace "amma ka rainamun hankali wannan little cute angel din zakace wa tso....."

WALEED yayi saurin katseshi da cewa"um_um bacci take karka tadata "ya ja HAMEED din zuwa waje HAMEED nata kara kallon Zarah har suka fita,

Ya kalli WALEED yace" Nide tsohuwar can tamin sosai "

WALEED na jin haushi cikin ranshi yace"an riga ka"baisan maganar ta fito ba ,

HAMEED yace"did u said something?"

WALEED na yamutse da fuska yace" no menace ni? seda safe tunda kaganta"

Harya juya HAMEED ya jawoshi yace"Zo"

WALEED ya tsaya kallonshi, yana murmushi yace"tayi kyau she's young and cute kun matukar dacewa"

WALEED yace "da wa?" Yana mai kallo shekeke,

HAMEED yace"I mean ita da aka rigani dashi Wanda ya riganin"

Murmushi ya subucewa WALEED jin HAMEED yaji abinda ya fada yace"I'm happy dan na sanka"

HAMEED ya daga gira yace"dagaske u r in love? Ina karatun?"

WALEED yayi tsoki yace "ask ur self the question" ya koma dakin yabar HAMEED tsaye yana bin wurin da kallo his best friend is in love yayi two minutes sannan ya saki murmushi yana farinciki ya juya ya tafi,

Bayan ishai muneera ta dawo asibitin ta shigo ta sameshi zaune Zarah na kwance yadda ta barta,

Tai karamin murmushi tace "haryanzu bata tashi ba?"

Ya daga mata kai ,

Ta matsa wurin gadon ta kamo hannun Zarah ,

Zarah ta bude ido tana kallonta,

Muneera tace"ya jikinki ?"

Zarah ta matse lips tace"dasauki"

Muneera tace"sannu ga abinci ki tashi na baki kici"

Zarah ta girgizakai,

Muneera tai murmushi tace " kadan zan baki kinji"

Ta kamata ta tashi zaune ta jinginata jikin pillow sannan ta fara zuba abincin a plate,

Zarah ta dan kalli WALEED ta dauke idonta,

WALEED na zaune yana kare mata kallon kurilla muneera ta gama zuba abincin ta kalleshi tace"Ka tashi ka koma gida amma ka tabbatar kaci abinci b4 ka kwanta"

Yana jin kamar karya tafi ya tashi jikinshi sanyaye yace"seda safe "

Tace"Allah yakaimu"

Ya juya ya tafi ita kuma tafara bawa Zarah abinci tana cikin bata Zarah tace"Nagode sosai "

Muneera tai murmushi tace"ke diyata ce ki saki jikinki dani "

Zarah batace komi ba tana taunar abincin bakinta,

Muneera na cikin bata ruwa KHALEED ya kira muneera tai murmushi tace"Dan albarka"ta dauka ,

Yace"Mama ya kuke yame jiki ?"

Tace"Dasauki sosai dana ya aiyuka"

KHALEED ya lumshe ido yana jindadi yace"Lafiya lau Mama "

Tace"Allah ya temaka ya maka albarka"

Yace"Ameen mamata"

Tai murmushi me sauti tace"sai anjima"ta kashe kiran ta kalli Zarah tayi kasake tana tunani ta kamata suka shiga toilet ,

WALEED ya koma gida yana cikin tunanin Zarah yayi sallah ya zubo abinci ya zauna ya tasa shi gaba yana kallo wani tunani ya fado masa sai gani yayi Zarah na bashi abinci a baki tana sakar mishi murmushi tana kashe mai idanunta,

Yayi firgigit daga tunaninsa wurin wayam daga shi sai plate da ruwa, ya bata fuska yanajin haushin heart dinshi saboda me zata rika hanasa sukuni akan wadda bai santa ba wacce zata tafi ta barsu nan bada jimawa ba ,yayi tsoki yana ganin laifin heart dinshi ya danci abincin ya tashi ya meda kayan kitchen ya koma dakinshi ya kunna wayarshi ya fara charting na mintoci ya kashe wayar ya ajiye ya shiga tunani,

Shin dagaske son Zarah yake?wannan dama shine soyayyar ?ya yamutsa fuska to itada zata tafi ?shi kuma da zai tafi wata Uwa duniya karatu?inama ba inda zashi, sai yaji kwata_kwata tafiya karatun ta fita ransa yasan idan yana gari dole watarana su hadu ya ganta idan yana can fa?,

Yana tunani har bacci ya daukeshi,

Cikin dare ya fara mafarki da yake kara sanyashi yanayi, shi da Zarah a zaune cikin wani kayataccen lambu suna cikin yanayi medadi,

Zarah nata sakin murmushi da bai taba gani tayi ba zahiri tace"Ashe haka ka ke sona yaya? Sai jiyane na fahimci hakan naji matukar dadin kasancewa da kai "

WALEED ya lumshe ido ya bude yana kallon kyakkyawar fuskarta yace"I love u Zarah kece rayuwata har inajin bazan iya rayuwa babu keba ,ina son ganinki kina farinciki"

Tai murmushi tace"thank u yayana yanzu Zan shiga ciki nayi wanka na kwanta na huta"

Yayi murmushi yace "bazaki gayyaceni ba?"

Tana dariya tace"u r welcome "ta tashi ta na tafiya duk jikinta na rawa,

Yana binta da mayen kallo ya tashi ya bita har cikin wani kayataccen daki ya sameta tana kokarin cire kaya yaje ya riketa yana karasa ciremata tana ta shafar jikinshi yana gama ciremata ta nufi toilet ya bita da sutura jikinshi yana shiga ya sameta tana wanka cikin shower tana cuda gashin kanta gwanin ban shaawa ,

Ya karasa cikin shower ya juyo daita suka zubawa juna ido ruwa na dukansu a hankali ya rika matsawa da bakinsa ya kama lips dinta yana tsotsa in a passionate way,

Zarah ta lumshe ido duk jikinta ya saki tana karbar sakonni a hankali ya fara yawo da hannunsa a jikinta har zuwa kan breast dinta sai jin karar alarm dinshi yayi,

Ya bude idanunsa ya sauke su a kan gado baa toilet ba yayi tsoki yanajin bakinciki yana jin dama bai farka ba har sai yaji softness dinta da irin dadin da yaji jiya, cikin takaici wayarshi nata ring ya jawota ya latseta ya tashi zaune yana kallon yanayin shi kamar jiya yayi tsoki ya tashi ya shiga toilet,

Yau tunda safe su Murtala sukabar kauyen kuhan bayan megari ya shawo kan Habu zaije ya siyarda dabbobin shehu ya dawo gida ,

Murtala yana cikin Tunani yaso su samu Zarah amma yasan dole ta dawo mahaifarta watarana yana kagare da zuwan ranar,

Yau Zarah ta tashi jikinta dasauki har ita da kanta tayo wanka ta sako wasu riga da sket din ta dawo ta zauna a gadon,

Muneera da WALEED na zaune suna kallonta ganin dasauki jikinta ta farfado sosai yasa Muneera tace"ya sunanki ne?"

Zarah ta kalleta sosai take jin son Muneera saboda taimakonta da tayi ta matse lips tace"Zarah"

Sunan ya daki zuciyar WALEED ya lumshe ido ya bude yanajin dadin sunan yayi tunanin sunan zai kasance lantana, Zulai,jummai and other

Muneera tace "inane garinku?"

Kan Zarah kasa idanunta na kawo ruwa tace"Kuhon kanawa"

Muneera tace"Da nisa sosai, kedawa ku ka zo nan?"

Hawaye suka zubowa Zarah tace"Ni kadai"

Muneera da WALEED suka kalli juna Muneera tace"Ke daya tun daga can ?Meyasa kika baro gida ?"

Zarah tai shiru tana hawaye,

Muneera tace"Ko zaki fadamin meyafaru dake?"

WALEED ya kalli Muneera yace"Mama ina ganin tana da bukatar karin lokaci"

Muneera tace"a'a yanzu haka nasan iyayenta na nemanta kwana biyu basu san ina take ba duk inda suke hankalinsu a tashe yake"
Zarah ta fara kuka hawaye na kwaranya a fuskarta
WALEED yayi shiru yanajin tausayinta kamar ya jawota ya rarrasheta,

Muneera na tausaya mata tace"kiyi hakuri Zarah inason iyayenki su san inda kike"

Zarah na kuka zuciyarta na zafi tace"Bani da iyaye sun kashe iyayena sun meda mahaifina Barawon shanu"

Idanun muneera cike da hawaye take kallonta WALEED kuwa zuciyarshi na tsananin zafi yace"su waye suka kashe su?"

Zarah tace"Tunda mukaje rugar idanunsa suke kaina suna zuwa da abokansa suna yawan kallona ranar ya tareni yanamin maganganun banza harya...tabamin jikina ya kuma ce in sameshi dakinsa idan banje ba zaisa a daukoni, baffa bai bar hakan tafaru ba yace mu shirya mubar gari da dare munyi niyyar barin rugar da daren wani ya koro shanu

Please Login or Register in order to submit comment