Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kula da ita ,

Kaka tace ina tunda sun samu lpy kauye zaa koma ayi suna tagama wanka sannan amedota ,

Ya fadamata likita yace kar abarshi cikin zafi tace ai lokacin sanyine yaso ya shawo kanta amma taki wadda suke tare ta tayata itade muneera iyakarta saurare ba yadda yayi ya hakura ya medasu kauyen,

Sati na zagayowa akai taron suna yaron yaci sunan *KHALEED*

Wurin taron mata surutun farinshi suke tayi kowa dauka yake bayan suna batare da kowa yafada ba suka gano zabayane da sunata zarya diff suka dauke kafa Wanda kaka da muneera basusan me ake ciki ba,

Muneera kuwa se in kaka bata kusa take dan tsayawa kallonshi kafin kakar tazo ta amsheshi bata fahimci komiba duk kauyensu ba zabaya, ba ma ta tabaganin kalarsu ba amma tana mamakin maganin da ake ta bashi kuma bata tambaya ba,

Duk bayan kwana biyu ibraheem na hanyar kauyen zuwa ganinsu sosai yake kulawa dasu,

Haka aka dau kwanaki har ta gama wanka kaka na matukar kokarinta na kula dasu ,

Sai muneera ta fara zuwa yawon arbain wurare da dama in taje basa cewa ta saukoshi su ganshi kuma a aladarsu suna hakan, hakan baisa ta fahimci komi ba seda taje wani gida sannan tasan meke faruwa,

Ta shiga gidan da faraarta ta samu diyar matar ta dawo gida haihuwa,

Yarinyar na murna suka gaisa tanata kallon kayan jikinta da shaawa tace"saukoshi"

Muneera tafara kokarin saukoshin,

Uwarta ta maka mata harara sannan tai karaf tace"tashi kishiga ciki"

Yarinyar ta tsaya kallon fuskar uwartata tagafa dagaske take tafasa amsarshin,

Ran Muneera ya sosu sosai tanata karamin murmushi tai mata bankwana ta tashi ta fito tana tafiya kamar kwai ya fashemata a ciki,

Ko barin gidan ba tai ba matar ta fara wa diyarta fada"saboda me zakice ta saukoshi so kike ki haifi kamarshi ko?"

Yarinyar tace"inna ganinshi kawai zanyi, don na amsheshi aiba yana nufin zan haifi kamarshi ba"

Da masifa matar tace"to dan ubanki ke kikasani irin wadannan in kagansu ai sede ka kauda fuska kayi addua"

Yarinyar ta tabe baki tayi shiru,

Uwar tai tsoki tace"shashasha"

Muneera na niyyar barin zauren gidan taji maganarsu bata fita ba seda suka kare magana kaff sannan ta karasa fita gwiwoyinta sanyaye bata nufi kowane gida ba dukda akwai gidajen da yakamata taje ta nufi gida idanunta jawur,

Da zuwanta gida ta samu kaka itama ta fita makwabta wannan ya bata damar kwanto KHALEED hakan yasa ya farka yanata neman nono ta kuramai ido sosai ko kadan baiyi wani duhu ba yananan de tass dinshi kyakkyawa me hanci da baki masu matukar kyau,

Idanunshi ta kula dasu wasu iri hakan yabata tsoro,

Tana zaunen kaka tai sallama ta shigo dakin tana mamaki tace"harkin dawo?kinje koina kuwa?"

Idanun muneera jawur tace"kaka mike damun KHALEED ne?"

Kakar tace"me ki ka gani?"

Muneera tace"naje gidansu inna jummai bilki nata son daukarshi innar ta hana zan fito kenan naji tana fadamata wai irinsu sede a kauda ido ayi addua dubi idanunshi sosai kaka"ta karasa hawaye na zubomata,

Zuciyar kaka na bugawa ta amsheshi tana dubashi bata taba kawo hakan a ranta ba saboda duk danginsu babu zabaya ko a kauyen kaf babu hankalinta tashe don tagama gano abinda ke damunsa ta kalli muneera tace"wannan ai ba matsala bace ki kwantar da hankalinki sai yanzu na lura sosai na kumayi tunani "

Muneera ta nata ma kaka kallo me dauke da alamar tambaya,

Kakar tace"yanzu de tunda kin kusa komawa kibari idan kuka koma se iro ya kaiku asibity kuga likita"

Muneera tace "saboda mi likita zai dubashi kaka?"

Kakar tai shiru zuciyarta badadi ta kalli KHALEED ta kalleta tace"sai naga kamar zabaya ne"

Muneera tai shiru zuciyarta na cigaba da zafi dukda bata gane miye ba tana tuno maganganun inna jummai,

***********

Tana cikin tunani kullum daga ranar bata kara zuwa koina ba har kwana hudu ranar ta biyar ibraheem ya taho daukarta yana cikin farinciki me tarin yawa,

Yana zuwa kallo daya ya mata ya gane tana cikin damuwa hakan ya rage masa annashuwa,

Bayan sun gaisa da kaka takemai maganar su koma asibity idan sunje akara dubashi tai mishi bayanin abinda take tunani gameda KHALEED din,

Ranshi badadi yafadamata abinda likita yafada ya kuma kara da kwantar mata da hankali taita musu addua suka fito,

Kaka na cikin damuwa suka baro kauyen ,

Tunda suka kama hanya idanun muneera na kan KHALEED shi kuma ibraheem nashi idon na kanta duk ta rame,

Gabadaya ta kasa hakurin har sukai gida sannan ta tambayeshi ta dago ta kalleshi murya sanyaye tace"minene zabaya?"

Hankalinshi a gun driving ya juyo ya kalleta ya bude baki zai magana sai kuma ya fasa ya cigaba da driving dinsa.
[4/4, 10:33] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 7&8


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*



*its ur page kawayen asali na rai da rai mommyn sudes (sweety)&Ummu affan*



Ranar Monday suka tafi asibity kamar yadda ya fadamata ,

Bayan sun fadi matsalarsu akayi masu gwaje_gwaje sannan suka koma wurin likita domin sanin matsalarsu,

Likitan ya gama karanta results yace"sakamakon results din ya nuna cewa duk lafiyarku kalau bakuda matsala wannan ya nuna kowani lokaci matarka zata iya samun ciki shawarar da zan baka shine yawaita kasancewa daita da zaran ta gama period insha Allah zaa dace"

Ibraheem yayi godiya suka fito daga asibityn suka koma gida,

Yayi zaton bayanin likita zaisa muneera ta rage damuwa tunda tasan lafiyarta lau amma ina hankalinta bai kwanta ba,

Haka rayuwar taita tafiya arziki nata karuwa ma ibraheem ba kalar dadin da muneera bata samu amma baisa tadena damuwa akan haihuwa ba,

Wani zuwa da tayi kaka da abun ya dameta sosai ta bata magungunan gargajiya batare da ta fadamata na miye ba ,dukda bata fadamata ba muneera ta san miye damuwarsu ta dage tana shansu amma shiru bata samu ciki ba,

Cikin shekara hudu da aurensu ibraheem ya sake sabon gida me kyau suka koma ciki zamansu lpy lau amma gorin danginsa kadai ya isheta damuwa bayan wacce take ciki, duk time da zaa hadu se an goranta mata sunyi iya kokarinsu ya kara aure amma yaki,

Bayan shekara daya shekaru biyar da aurensu suna kwance da dare suna dan fira kafin bacci ya daukesu ,

A hankali tace"shekaru nata tafiya amma shiru ban haihu ba mezai hana ka kara aure inaga hakan zaifi"

Tunda ta fara magana yake kallonta ranshi na sosuwa da jin zancenta memakon ya bata rai seyayi murmushi domin kuwa karamun abu ke sata kuka ,

Ya jawota jikinshi yana murmushi yace "yayi kyau wato saboda kingaji dani har abokiyar renona kike nema? "

Tai guntun murmushi tace"bahaka bane ...."

Yace"to yane? Ni awurina ba wani dalilin da zaisa na kara aure mena rasa ?meke bakimun?"

Tai murmushi tace "Nide dan Allah ka karo aure"

Ya dage kafada yace"bazan kara ba"

Da shagwaba tace"dan Allah "

Bai bata amsa ba se cakulkuli daya faramata yana dariya tanata dariya take cewa"ka bari ...ka bari... banaso"

Ya dakata sunata meda numfashi, yayi hakanne domin kauda maganar bawai don ta mishi dadi ba, a hankali yace"muneera karki kara irin wannan maganar"

Ta kalleshi ta na mamakinsa da wani ne da yanzu ya kara aurensa cikin sanyin murya tace"to....kayi hakuri"

Yayi murmushi ya dora hannunshi a cikinta yana shafawa yace"ki kara hakuri muneera very soon or later zaki samu ciki zaki reni yaranki kamar kowa"

Tai murmushi ta na fatan hakan nan kusa,

Bayan 3yrs muneera tagama school dinta da certificate na diploma ta dawo zaman gida Wanda yakara mata damuwa batare da jimawa ba ibraheem ya Samar mata wata school inda zatayi HND,

Kaka kuwa nata kara tsufa sede ba irin tsufan nan ba domin karamin jiki gareta kuma tana da jiki mekyau amma shekaru sunja sosai,

Sai da ta cika shekara goma da aure harta fara fidda rai da haihuwar watarana ta tashi da masassara da amai da mura me zafin gaske a rikice ibraheem ya kaita asibity bayan an mata test likitoci suka tabbatar masa da tana da cikin wata daya,

Farinciki ya lullube ibraheem har baisan time daya fara hawayen farinciki ba yayita ma likita godiya ya fita dakin da aka sawa muneera drip tana kwance ya zauna gefenta yana cikin farinciki marar misaltuwa ya rike hannunta ta bude ido ta
kalli fuskarshi idanunshi da alamun hawaye acikinsu,

Ya sakarmata murmushi yace "maman baby"

Ta tsaya kallon fuskarshi tana karantar shi,

Yasa dayan hannunshi ya rike nata da hannu biyu yana murmushi yace "muneera u r pregnant nanda wata takwas in Allah yaso zaki haihu zaki samu yaranki kema"

Tafara murna daga kwancen da take tana jin duk ciwon jikinta ya tafi,

Yace "kinga abun Allah ko?gashi yabamu a lokacin da ba muyi tunani ba"

Ta fara hawayen farinciki tana tuno shekarun data dauka tana addua amma shiru sai yanzu Allah ya kawo,tana hawaye tace"alhamdulillahi ..alhamdulillahi..Allah mungode maka"

Tana farinciki tace"cikine jikina zauji... na kusa haihuwa"se kuka

Hawaye suka cika mai ido yasa hannu ya ciresu kafin su fito yace"shitttt baki lafiya kiyi shiru"

Tai saurin rufe bakinta tana jin mugun farinciki,

Ta kalleshi duk idanunsu jawur sukai murmushi,

yace "Allah ya saukeki lafiya yaraya mana abinda zaki haifo"

Zuwa dare kuzarin jikinta ya dawo aka sallamesu ya riketa tana tafiya sannu har mota suka dau hanyar gidansu,

Tana cikin farinciki bataso a kwana kaka bataji kyakkyawan labari ba ko dan tayi bacci medadi, ta kalleshi yanata driving tace"yaushe zamuje kauye ?"

Ya juyo da kai ya kalleta,

Tana murmushi tace "inason gano kaka"

Yayi murmushi ya kalli hannun da aka ciremata drip yace"baki lafiya ko kinmanta? Sannan likita yace karki rika motsi me karfi don gudun zubewar cikin kuma ki kula da cin abinci sosai dan Karin lafiyarshi kinga ina batun tafiya yanzu sede idan ya girma "

Tai shiru badan ranta yaso ba amma taso kaka taji labari medadi,

Suna komawa gida ibraheem abokinsa yafara fadawa daganan bai fadawa kowa ba don aganinsa ba amfanin hakan ,

Muneera bata samu kaka taji labarin ba saboda garinsu har zuwa wannan time din ba service wayarma batayi yawa ba se wane da wane in kanason waya sai kaje wani wuri kasamu network kayi, hakan yasa bata samu fadamata ba,

Cikin nata yazo da wani irin laulayi me wahala amma duk bata damuwa da hakan saboda yadda takeson cikin ,

Ibraheem ne keta kula daita har wankin undies dinta baya barinta yana matukar kula daita seda cikinta ya kai 4 months sannan ya dauketa suka tafi kauye,

Bayan sun isa ta shiga gida tana sallama me cike da farinciki kaka ta fito daga daki se ganinta tayi Wanda kallo daya zakamata kagane tana da ciki ta rame tayi fari cikin kuma ya turo,

Kakar na matukar farinciki tace"aaha...aaha muneera"

Muneerat ta karasa ta rungume kaka tana murna kaka tace"alhamdulillah muneera ciki harya fara girma"

Muneerat ta zare jikinta tana murmushi kanta kasa,

Hakan yasa kaka ta fara karemata kallo tana jin zallar farinciki ta fara zuba adduoi "ubangiji Allah ya albarkaci abinda ke cikinki Allah ya saukeki lpy ya baki zuria ta gari ...."

Kan muneera kasa cikin zuciyarta ameen kawai take fada tana jin mugun dadin yanayin da kakar take ciki na farinciki,

Kaka taja hannunta har daki ta zaunar daita tana farinciki tace"bari na fita na siyomiki awara da dannarogo nasan kinajin yunwa kafin nai maku girki"

Tai murmushi tace "nagode kaka"

Kaka nata kallonta ta dauki mayafi ta yafa ta fita dasauri,

Tana fita muneera ta kwanta kan gadon da take zaune tana ta sakin murmushi ita kadai ,

Kaka ta dawo da awaran ta bata ta kawomata hura da ruwa me sanyi sannan tafara nema masu abinda zasuci,

Daganan suka cigaba da renon cikinsu cikin so da kauna, kowa yasan cewa she's pregnant hakan beko yiwa wasu dadi ba ,

Kaka kullim tana hanyar ganin jikin jikartata tana kawomata kayan kwadayi na masu ciki,

Tun kafin cikin yakai 9months ibraheem yafara siyen kayan haihuwa saboda doki, ita kanta kome tagani saita siye musamman na mata,

Lokacin da cikin ya shiga wata tara watarana yana gida se sallamar kaka sukaji muneera ta fita ta tarota tana murna suka shigo ibraheem ya duka gaisheta muneera ta fita kawomata ruwa ,

Bayan sun gaisa kaka tace "nazo ne inji yaushe muneera zata koma haihuwa ?"

Ya dago ya kalli kaka ya sunkuyar da kai yace"kaka anan zata haihu"

Kaka tace "a'a kabarta taje gida ta haihu batada kowa anan acan zatafi samun kulawa da ita da abinda zata haifa bayan tagama wanka lokacin yaro ya fara wayo se kaje ka dauko matarka"

Ba don ranshi yaso ba don dole yace"to kaka insha Allah zuwa jibi zan kawo ta"

Kaka tace "to ba damuwa Allah yarabasu lpy"

Baice komiba ya tashi ya fita kanshi na wani irin ciwo lokaci daya kokadan baijin dadin bacci in baijishi rungume da cikin shiba,

Muneera na dawowa da ruwa kaka ta amsa tasha tace"yanzu nakewa mijina maganar komawarki gida haihuwa"

Muneera tai saurin cewa"ya amince kuwa?"

Kaka tace"to bahaka akeyi ba ?kima fara shiri yace jibi zai kawoki ko maganin zaki nasan bawani shan kirki kikemasu ba idan kina kusa dole kirika sha"

Muneera tai yake bata farinciki da tafiya kauyen ita kanta shedace akan son da ibraheem kewa cikin kuma yana fada yadda yakeji gameda shi,

Bai dawo gidan ba se dare ya dawo jikinshi gajiye kamar Wanda yayi aikin karfi kuma bakomai ya haddasa hakan ba se damuwar tafiyarta,

Muneerat tazo ta sameshi tana mai kallon tausayi tace"sannu da zuwa "

Ya kalleta ya kalli cikin yayi murmushi yace"yawwa hope kuna lpy? "

Ta gyada masa kai ,

Yayi karamin murmushi ya gyara zama yace"banason komawarki kauye haihuwa amma bazan iya hana hakan ba domin bazan iyawa kaka musu ba"

Murya sanyaye tace"kayi hakuri"

Ya marairaice yace"daga yau shikenan nadena bacci medadi"

Tai dariya ta tashi ta fita kitchen domin kawo masa abinci,

Ya bita da kallo har ta fita ya meda hannunshi akanshi da keta faman ciwo tun dazu yana tunani ,

Ran daren da zata tafi bacci sama_sama ne ya daukeshi wanshekare ya tayata shiri suka dauki hanyar kauyen,

Tunda suka fara tafiya hankalinsu na kan na juna sede bawanda yayi magana sundade haka sannan yace"ki kula da kanki sosai"

Jikinta mace tace"to"

A hankali yace"zanyi kewarki sosai"

Tai karamin murmushi tace "kamar gobene"

Yayi shiru baice komi ba shi kadai yasan yadda yakeji gameda tafiyar don ba yadda zaiyi da bazai barta ba sam,

Suna isa gidan kaka suka wuce tayi musu girki ta dama fura ibraheem ya dan sha furar yanata satar kallon muneera sannan ya tashi zai wuce yaba kaka kudi masu yawa yanata kallon muneera ya juya kai ya fita,

Kaka ta kalli muneera dake zaune dakin tace"kitashi kije ku kara bankwana"

Ta girgizakai tana jin kunyar kakar cikin zuciyarta kuwa tana jin kamar ta bishi su koma gida,

Haka ibraheem ya koma gida shikadai yana cikin kadaici da kewar matarshi,

Itama muneera hakanne bangarenta dukda de tana samun duk kulawar data dace awurin kaka amma sosai take kewar mijinta,

Tunda ya kawota be koma ba saboda kunya amma yanason ganinta yasan halin da take ciki, har zuwa karshen wata shiru bata haihu ba,

Wani dare yana kwance yayi mafarkin muneera na labour me tsanani har sukaje asibity ba jimawa nurse ta fito ta shedamai ta rasu tareda abinda ke cikinta ,

Yayi wata irin kara ya zube kasa hakan yayi dede da farfadowarsa ya farka yana zufa zuciyarshi na lugude ,

Yanata meda numfashi ya taba setin heart dinshi yaji yadda take harbawa ya haska fitila yaga karfe 2 na dare ,ya kara rikicewa domin ji yake kamar ya dauki hanyar kauye yanzu cikin daren ,

Hankalinshi tashe ya sauko daga kan gadon yayo alwala ya dawo yafara salloli ,

A kauye kuwa muneera na cikin mawuyacin hali tun marece take nakuda amma shiru bata haihu ba sunata banka mata maganin hausa amma haihuwa shiru tana ta kara galabaita gashi babu asibity kauyen se local government dake kusa dasu kuma ba lalle bane su samu likita acikin daren, gabadaya basu da niyyar kaita asibityn ma domin sun saba haihuwar gida zuwa asibityn basu daukeshi bakin komi ba.
[4/4, 10:33] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 11&12


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*


*HAPPY BIRTHDAY TO U YAYA HAYAT WE WISH U ALL THE BLESSING OF LIFE)*



Shirun nan da yayi yasa zuciyarta karyewa da bawani abu bane da tabbas zaiyi mata bayani,ta meda hankalinta kan KHALEED zuciyarta na sakamata abubuwa daban _daban,

Baice mata komi ba har suka isa gida jikinta sanyaye ta bude mota ta fita ta nufi cikin gidan tana jin kamar ta fara kuka,

Gidan kwas ibraheem ya gyarashi sosai kafin ya daukota har su kujeru duk an sauya anyi sabon paint duk don murnar dawowarta,itako bata damu da gyaran gidan ba ta zauna kan daya daga cikin kujerun ta cigaba da kallon danta,

Can zuwa yayi sallama ya shigo da kayanta yawuce dasu ciki ya fito yana kallonta yace "zanje na samo miki abinda zakici yanzu zan dawo"ya juya kai zai fita,

Babu tsammani yaji muryarta me cike da rauni ta kirashi" Abban shi""

Ya juyo yana kallonta,

Idanunta cike da hawaye tace"dan Allah ka fadamin ko hankalina zai kwanta inaso insan mike damun dana bazan iya cin komiba batare danasan mike damunsa ba"

Wani irin tausayin ta ya kamashi zuciyarshi badadi ya dawo ya zauna gab daita cikin sanyin murya da kwantar da hankali yace"ki kwantar da hankalinki muneera bawata matsala zabaya mutunne kamar kowa sede lalurar da Allah ya doramasu amma suma mutane ne, dan Allah ya halicci KHALEED cikinsu bai kamata mu rika daga hankali ba domin hakan ba zai sauya komi ba"

Tana kallonshi idanunta taf da hawaye tace"ban fahimta ba kafadamin miye matsalarshi?"

Ya dafa kafadarta cikin rarrashi yace"ba abinda ke matsalarshi sede bazai koma baki ba sannan shidin ba kamar sauran mutane bane"

Tai saurin kallon KHALEED fari tass dashi hankalinta tashe ta dago tace"kana nufin haka zai cigaba da zama?"

Ya jinjina mata kai yana matse da lips dinsa,

Hawayen da suka dade cikin idanunta suka zubo tace"innalillahi wainna ilaihi rajiun !!!!"tana kara kallon KHALEED din hawayen fuskarta na diga a kumcinsa hakan yasa ya bude idanunsa yana kallonta yana wasa da hannuwanshi yana son kaisu bakinshi,

Ba bata lokaci tafara kuka me ban tausayi tana rungume dashi,

Ibraheem ya amshi KHALEED daga hannunta ranshi na suya zuciyarshi na zafi yace"meyasa kike hakane?tunda Ku kaje kauye KHALEED yayi rashin lpy ne?ko ko kinga wani abu da yake nuna cewa shi din ba mutum bane?"

Tana kuka tace"baya rashin lpy amma mutane basa son ganinshi basu ko son daukarshi ta yaya zaiyi rayuwa medadi ?taya zaiyi karatu?taya zaiyi abokai taya zaisamu duk Wadannan abubuwan?"

Tunda tafara yake kallonta zai iya fahimtar yadda takeji domin shima hakan yakeji a ranshi,

Yayi shiru baice mata komi ba, ta cigaba da kukanta ,

Bayan minutes cikin sanyin murya yace"Allah bazai barshi yayi rayuwa cikin kunci ba, mutane bakomi bane a rayuwar mutum idan har Allah yana sonshi don Allah ki kwantar da hankalinki ki kula da danki kibashi tarbiya me kyau kibar batun mutane domin badole seda su zaiyi rayuwa ba"

Tana zubda hawaye take kallonshi daganinshi dauriya ce kawai yake ,

Ya jawota jikinshi yana rarrashi yace"ina son dana zanyi duk bakin kokarina wurin sashi farinciki da debemai duk wata kewa ina rokonki da ki cire tunanin abinda baki da maganinshi ki zauna lpy "

Ta jinjina kai tana rage hawayenta,

Ya tada ta zaune ya dora mata shi a cinya yana karamin murmushi yace"kibashi nononshi yasha kafin na dawo in sameki normal "

Ta jinjina kai kurum, ya tashi ya fita,

Ta fiddo nono tabawa KHALEED ya amsa yana sha sosai hardasu rungume nonon dukda baiyi wani wayau ba,

Tausayinshi yakara taso mata tafara wani kukan tana jin dama ya mutu ya huta aganinta zaifi rayuwa cikin tsangwama da kadaici,

Shi kuwa KHALEED yanata shan nononshi can zuwa ya saki nonon ya fara tsanyara kuka kamar zai shide hankalinta ya tashi tanata mikamasa nonon yaki karba karshe seta rungumeshi ta cigaba da kuka yanayi tanayi,

Ibraheem yaje ya siyo masu abincin ya dawo yana shigowa yafara jiyo kukansu yana shigowa ya samu ta rungumeshi suna tayi ranshi bace yaje ya amshe shi dasauri ya azashi a kafada cikin zafin zuciya yace"muneera so kike ki kashe shi kome?"

Jin kalamanshi ya sata yin shiru lokaci daya ta zazzaro ido tana kallonshi,

Yana cigaba da rirriga KHALEED yace"idan har baki sonshi to zan daukeshi daga wurinki saboda karki rudaminshi ki medashi mahaukaci"

Zuciyarta tayi mummunan bugawa ta rufe idanunta da tafin hannunta daya ta saki kuka me sauti tana jujjuya masa kai,

Ibraheem yayi tsoki ya nufi ciki dashi ya kwantar dashi ya hada ruwan wanka ya mishi sannan ya goyashi yafara zarya dashi cikin dakin yana rirrigashi haryayi bacci dukda haka yana cigaba da zarya domin baisan ma yayi baccin ba yadeji yayi shiru,

Muneera tasha kukanta sannan ta shigo bedroom din tana shigowa ya tsaya kallonta yanajin takaici a zuciyarshi,

Ta zube kan gwiwoyinta muryarta dishe tace"don Allah kayi hakuri abbanshi inason dana wannan nema yasa nake damuwa da halin daya samu kanshi ciki ,bawanda zai soshi fiye dani na kasa tsayar da hawayena ne amma bazan sake ba kayi hakuri dani"ta karasa da sharar hawaye

Yana tsaye yana kallonta yanajin tausayinta ya karaso gabanta ya mika mata hannu ta tashi ya jata har gefen bed ya zaunar daita ya zauna cikin sanyin murya yace"I'm sorry nasani kina sonshi amma kiyi hakuri da kaddararshi kowa da tashi kaddarar ki cigaba da mishi addua da kula dashi yafi kukan da zaisa ya taso yana me tsangwamar kanshi"

Ta jinjina kai tare da cewa"nadena"

Ya jinjina kai alamun gamsuwa ya saukoshi yanata baccin shi, ganin yana bacci ya kwantar dashi ya jata zuwa falo suka ci abinci yayi wanka ya fita masallaci yana dawowa ya samu itama tayi wanka tana zaune kan bed kusa da KHALEED tanata kallonshi,

Yayi murmushi ya karasa wurinsu yana tayata kallonshi ,

Bayan ya kuramai ido sosai ya dago ya kalleta da murmushi yace"he's beautiful just like his mom"

Ta saki murmushi ta dora yatsa kan hancinshi zuwa bakinshi tace"ya fini kyau"

Ibraheem na farinciki ganin tana murmushi yace"Allah? "

Ta daga gira tana cigaba da murmusawa,

Ya jawota jikinshi ya rungumeta tsamm jikinshi yana juyi daita daga kwance kafin yafara sauya salon,

Muneera ta riga tasan shawarar da ibraheem yabata shine dede amma still time to time ta kanyi kukan tausayin KHALEED dinta sosai ta dukufa wurin yi masa addua Allah ya saukaka mishi rayuwa,

Maman farouk da tazo taga yadda ta rame ta kara kwantar mata da hankali a matsayinta na mace ta bata shawara sosai ,

Ibraheem bai barta taje wurin danginshi ba ta gwado masu yaro suma tunda suka koma kauye basuje ba har zuwa dawowarsu diff ba kowa Sam hakan bai damu muneera ba don tasan bazasuyi shiru ba idan sukasan waye danta ,sun dage suna kula dashi yanata wayo gashi da yawan dariya gwanin shaawa da shiga rai,

Bayan wata daya ,

Kaka taji shiru batasan ya muneera take ciki ba wata zuciyarta na fadamata tana can tana rusa kuka don hawaye basuyi mata wuya kuma ta kware wurin kebewa tasha kuka harta godewa Allah ,kuma tanason sanin lpyar jikanta wannan yasa ta fara shirin tahowa birni ganinsu a yau dinnan,

A birni tunda safe ibraheem yaje gaida cikin kawunansa ya shiga har cikin gida don ya gaisheda matanshi yana shiga bayan sun gaisa ba alamun kunya suke cewa"yasu KHALEED sun dawo wanka kuwa?"suna nuna basu san komi ba,

Yayi murmushi yace "eh kusan 1month kenan"

Sukace"ikon Allah shine ibraheem baka kawota tazo mana yawan arbain ba? "

Yana murmushi yace "abubuwa ne sukayi yawa"

Suka ce"to shikenan tunda bazata kawo mana shi ba mu zamuje mugano shi"

Yana murmushi yabar gidan bai kara magana ba seda ya shiga cikin motor sannan yayi tsoki ya girgizakai sam beyi tunanin zasuje ba domin sanin halin su,

Su kuwa suna gama abinda suke suka nufi gidan wurin karfe 11 na

Please Login or Register in order to submit comment