Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta girgizakai ,

Ya cigaba da cin abincinsa don bai wasa da ciki seda ya koshi sannan ya dauke kayan zuwa kitchen bai dawo ba ya fita cuku_cukun sakata makaranta yana da burin matarshi tai ilimi kuma hakan zai ragemata zaman kadaici,

Wata school ya Samar mata babbar makaranta ce me hade da Arabic zata fara JIS har zuwa SIS in tanaso zata iya cigaba aciki suna bada result na diploma fannin Arabic ,

Bai dawo gidan ba se dare tayi wanka tasha Jan baki ja tana falo zaune ya saki murmushi ya zauna gabanta ya ajiye kazar ya zuba mata idanu,

Tai saurin cewa" sannu da dawowa"

Yayi murmushi yana yaba kyanta yace"kinyi kyau sosai"

Ta juyar da kai tana boye murmushin fuskarta,

Yace"ki saki jikinki muneera baki da matsala banason kina takura kanki"

Batace uffan ba ya jawota ya rungumeta tana jin kunya ba yadda ta iya ,

Ya bude leda ya debo kazar yakai bakinta ta kasa amsa zuciyarta na harbawa ya tsaya kallonta wuyar rigarta harya kai can saman wuya sede taji hannunshi dede setin heart dinta, yaji yadda take bugawa sosai,
Ya kalli jikinta yaga yana rawa saboda tabatan da yayi,

Ya meda kallon kan fuskarta yayi murmushi yace"mike damunkine?nace ki saki jikinki ko"

Ya kai nama bakinta ta bude baki tafara cin naman,

Seda yagama bata yaci ya fita ya kuskure baki yayi alwala ya dawo ta tashi ta fita tayo alwalar itama kamar yadda taga yayi yana kwance kan karamin gadonsu idonshi rufe ta lallaba zata dauki pillow kafin ta janye ya rike hannun jikinta yayi wata irin girgiza ya bude ido yace"ina zakije?"

Ta girgizakai,

Yace"to kwanta anan"ya nuna mata gabanshi,

Ba musu ta meda pillown ta kwanta ta kulle ido yanata kallonta yana sake_sake har bacci ya daukeshi,

Haka suka cigaba da rayuwar sosai yake sakarmata fuska yana janta jikinshi da labarai dasauransu amma bata iya sakin jiki dashi sosai ba,

Har bayan sati biyu ya dinka mata uniform ya sai mata littattafai text book exercise da na islamiya tafara zuwa school din daya Samar mata,

Zuwa school din yasa ta fara sakin jiki dashi a hankali wannan yasa shi jindadi sosai,

Ta cigaba da zuwa makarantar data fi ba Arabic karfi,

Seda tayi wata guda sannan ibraheem yafara sauya salon yana neman hakkinsa akai_akai yana nemawa kansa hanya har ya samu nasarar samun kofar data meda muneera cikakkiyar macen aure, ya ritata ya nuna mata soyayya kwananta ukku sannan ta cigaba da zuwa makaranta ,

Bayan wata hudu silent soyayya sukeyiwa juna me tsafta kowanensu na gurin farantawa danuwansa rai dede da rana daya muneera bata taba bata masa rai ba shima hakan suna cike da marmarin juna ,sede shiru har yau babu ciki ba labarinshi itade muneera tana cikin dokin cikin domin farincikin kaka amma shiru kakeji,

Suna kwance hannunsa kan cikinta tana kallon wuri daban yana kallon bayanta a hankali tace"inason zuwa ganin kaka"

Yayi murmushi har yau baida suna yace"ki shirya mutafi ran jumaa mutafi mu kwana biyu mudawo lahadi saboda school"

Tai murmushi tana matukar jindadi tace"nagode sosai"

Shima Yayi murmushin don jin nata,

Tana ta doki ranar jumaa suka tafi kauyen su wagini,

Suna zuwa ta shige gida tana murnar ganin kakarta kaka na zaure kan tabarma tana shan iska ta shigo dasauri ta rungumeta tana murna ,

Kaka na matukar jin farinciki na ganin jikarta so daya taje ganinta ta ganta bul_bul daganan bata sake komawa ba amma tana da niyyar komawa this month dan ta gano jikinta a tunaninta cikinta yayi girma yanzu,

Jin bataji tsini ko tudu ba cikinta a shafe yadda ta sanshi yasa ta janyeta tana faraa ta kara kai idanunta kan cikin tana boyewa kar muneera tagano manufarta,

Amma tuni tagama ganowa tai karamin murmushi ta matse lips jikinta sanyaye,

Kakar na nuna jindadi tace"sannunku da zuwa yana ina angon kice ya shigo"

Muneera ta tashi jiki sanyaye ta fita amma baya nan da alamu ya tafi gidan kawunsa ta dawo ta zauna tace"ya tafi gidan kawu"

Kaka tana ta bin ta da kallon kurilla ko zataga alamun karamin ciki jikinta amma babu a hankali tace"ya kuke? inafatan kuna lpy "

Muneera ta kwanta kan kafarta ta daga kai idanunta cike da hawaye taso taga murnar kaka a yau sosai zatai farinciki da ganin ciki jikinta,

Kaka na murmushi tace"daga zuwa zaki hayeni ki karasani yadda kikai kibar nan tashi kigani inje in dafama mijina wani abu"

Muneera ta tashi zaune memakon kaka taga dariya a fuskarta se ganin hawaye tayi ,

Gabanta ya fadi tace"minene muneera daga zuwa se kuka?"

Tana hawayen tace"kaka kiyi hakuri insha Allah bazaki mutu ba se kinga jikokin ki"

Kaka ta rike gemu ganin har ta gano manufarta tai dariya kadan tace"amin muneera duka yaushe akai auren ?nan bada jimawa ba zaki dawo gidan nan haihuwa"

Muneera ta rufe fuska tana jindadi.
[4/4, 10:33] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 5&6


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*


*Wannan shafin naki ne kawata momyn mufeeda🥰kinfi karfin page kawalli, inajinki har cikin makogwaron zuciyata fatan Allah yabarmu tare ya sauke ki lpy ya bamu triple masu albarka*



Kamar yadda sukaje da niyyar kwana biyu hakan ta faru ranar lahadi suka koma birni suka cigaba da rayuwa,

Muneera ba inda take zuwa se gidan maman farouk yaran dangin ibraheem suna zuwa wurinta suka dena zuwa lokaci daya,

Ko so daya ibraheem bai taba cewa ta shirya taje zumunci wurin danginshi ba ,hakan yasa yau alhamis bayan ya dawo daga aiki ya gama cin abinci suna zaune kanta kasa tace"yaushe zaka kaini na gaido su kawu? naga yara na zuwa kwana biyu basu zo ba"

Yana kallonta amma yayi shiru bece komiba,

Ta kalleshi tace "kaji"

Yayi murmushi me ciwo yace"muneerat bakisan halin mutanen nan ba amma ki shirya na kaiki"

Tai murmushi batare da damuwa da maganarshi ba tace"nagode sosai ...se gobe zanje"

Ya jinjina kai yana murmushi yana kallonta,

Wanshekare ya kaita kamar yadda ta bukata kowane gida taje kayan jikinta suke fara kallo kafin ita lpy lau suke tarbarta shiyasa bata fahimci komi ba ya kaita gidaje da dama sannan suka koma gida,

Bayan zuwanta yaran suka dawo zuwa gidanta duk jumaa idan anzo da kananu ta daukesu cikin shaawa tai musu kunshi su koma gida kwas Wanda hakan beyiwa iyayensu dadi saboda yadda basu sonta,

Ana haka azumi ya gabato ibraheem yayi mata magana zasuje gun kaka su gaidota sukai mata kayan azumi tunanin bata da ciki kila ganinta yasa kaka taji badadi yasa tace ita bata zuwa kaka zatai fada basu dade da zuwa ba yace toshi zaije jibi ,

Washegari tana dawowa daga makaranta karfe 12 ta cire kaya ta shiga kitchen ko minti 15 batayi ba Sega sallamar kakarta ,

Tai waje da gudu tana murna ta rungumeta,

Kakar ma nata farinciki fitowar da tayi harta fahimci bata da komi jikinta sema rama da taga tayi,

Ta zare jikinta tana murna tace"sannu da zuwa kaka, da kuwa zaije gaido ku gobe "

Kaka nata murmushi tace "koda yazo dole in zo inga lafiyarki"

Muneera tai karamin murmushi ta dauki buhun da kaka tazo dashi tace"kaka kushigo ciki rana"

Suka wuce ciki ta kawowa kaka ruwa jikinta sanyaye faraar da kakar keyi baisa ta kasa tuno abinda take buri akanta ba,

Dasauri ta gama abinci ta zubowa kaka,kaka taki ci tace tazo suci tare suka fara cin abincin kakar nata dan kallonta tace"muneera halan kindawo da dabiar rashin cin abinci?"

Ta girgizakai da murmushi tace"kaka inacin abinci sosai "

Kakar tace"dan Allah ki kwantar da hankalinki ki rika cin abinci sosai "

Tace"to kaka"

Bayan sungama cin abinci kakar tasa ta dauke buhun garar azumi data kawomata takai kitchen ta dawo suka cigaba da fira kafin lokacin salla yayi ,

Bayan antaso masallaci daga sallar jumaa ibraheem ya shigo ya samu kaka har kasa ya zukunna ya gaisheta sannan yawuce ciki ,

Muneera bata kai mishi abinci ba seda kakar ta kalleta da ido sannan ta tashi ta kai mishi abinci yana gama ci ya fita,

Ana gama laasar kaka tafara shirin tafiya time din ibraheem ya shigo ya samu muneera ta rungumeta tanata kuka ,

Shigowarshi yasa ta yin shiru yabawa kakar kudade dakyar ta amsa sannan ya dauketa ya kaita tasha ya dawo gida,

Tunda akai bikinshi kofofin arziki keta budewa amma haihuwa de shiru har akai shekara daya ciff shiru ba labarin haihuwa ,

Shi bai dauki abun wani abu ba yasan haihuwa daga Allah ne yana bawa Wanda yaso kuma shima bai fidda rai ba,

Itako kaka zuwa yanzu zuciyarta tana bata kila burinta bazai cika ba kila se bayan rasuwarta muneera zata samu haihuwa ,

Muneera ko yanzu kunyar ganin kaka take ta damu matuka saboda rashin haihuwar ko baccin kirki batayi kwana take salla tana rokon Allah yabata haihuwa amma bata sanar da ibraheem damuwarta ba yayi tambaya ya gaji idan ya tambayi mike damunta kullim amsarta itace"bakomi"

Kafin shekara ta zagayo ya siyi mota tayi farincikin motar sosai tana ta murna da dare ya siyo kaji masu yawa tai dambunsu da safe suka tafi kauye, kofar gidan kawu yayi parking suka shiga ciki bayan sun gaisa sun basu tsarabarsu sannan suka tafi gidan kaka ta tarbesu tanata murna muneera kuwa kallon tausayi kadai take mata ,

Se marece sannan suka koma birni ,

Bada jimawa ba suka cika shekaru biyu da aure time dinne kuma zaa aurar da wata cikin diyan yanuwansa,

Bikin ranar jumaa ne cikin dare tanajin dadi tace masa"gobe bazanje makaranta ba"

Yace"saboda me?"

Tace"biki mana"tana murmushi

Cikin rashin jindadi yace"amma kinsan test kuke ko?"

Ta gyada kai ,

Yace"to ki shirya kije school bayan kin dawo seki shirya na kaiki gidan bikin"

Ba musu tace"to"duk da aranta bataji dadi ba a ganinta bata kyauta ba kyau tun safe daita zaai aiyuka amma ta lura kamar ibraheem bayason tana zuwa gidajensu ko wata sabgarsu,

Wanshekare harta dawo makaranta ta shirya be dawo ba yana sane bai dawo din ba yafiso taje da marece tadanyi mintoci ta fito lpy ,

Ganin har ukku bai zoba yasa ta kwanciya bacci har laasar tai salla ta sake wanka bai shigo ba se hudu da rabi ya shigo yanata murmushi dan ya rage mata haushi ya zauna gefenta akan cushion ya dora hannu kan kafadarta yace"kiyi hakuri nayi late aiki ya rikeni amma kitashi muje na kaiki sena dawo zanci abinci"

A sannu tace"kaci abincin"

Yace"muje de nafara ajiyeki"

Yana rike da hannunta suka fita yabude mata mota ta shiga suka nufi gidan bikin,

Yana driving yake kallonta fuskarta ba walwala, yayi murmushi yace "nade bada hakuri ai"

Ta kalleshi ta meda kallo gun window sannan tayi murmushi,

Bayan sun isa ta bude zata fito ya Ciro kudi yabata yace"ki shirya karfe 6 zandawo"

Ta jinjina kai ta fita yanata kallonta harta shige gidan sannan ya tafi,

Da shigarta ta samu gidan cike da mata anata kaikawo ana ciye_ciye surutu kuwa kamar kasuwa,

Duk kallo ya dawo gunta saboda kyakkyawan leshin dake jikinta ta shiga sukuku har daki ta gaida uwar bikin tabata kudin da ya bata ta dawo waje ta samu wuri ta zauna ta jima zaune bawanda ya kulata,

Bayan jmawa uwar bikin tasa wata cikin dangi ta kawo mata abinci,tanajin haushinta yadda tafisu memakon ta kaimata abincin seta ja wata cikin diyan kawunnan nashi suka tafi wurinta badon komai ba don su fadamata mgna,

Sukaje har gabanta sunata kus_kus suna dariya daya tace"Matar kawu me zaa kawomiki?"

Muneera tai karamin murmushi tace "nakoshi"

Sukai dariya sukace"gaskiya sekinci abinci gidan biki ne fa"

Muneera ta sakeyin karamin murmushi,

Daya tace"me zaa kawomiki ne akwai tuwon dawa tuwon masara dana shinkafa akwai fate da shinkafa jellop ,akwai miyar kuka ,miyar taushe,miyar kubewa da...."

Dayar ta katseta "kee naji kinata jaye_jaye bafa irinki bace me" ta kalli katon cikin waccan,

Tace"au!!"sukai dariya suka kashe ,

Tace"na mance da ci kawai ake"

Waccan tace"ki kawo mata tuwon dawa kinsan mutanen kauye da tuwo"

Muneera nata kallonsu idanunta cike da hawaye duk ga yanuwa wurin dariya kawai suke sekace sunyi abun arziki,

Suka juya suka tafi ganin ranta ya baci dama hakan sukeso,

Se gashi daya ta dawo da tuwo da miyar kuka ta ajiye gabanta ta juya tai tafiyarta,

So daya muneera ta kalli tuwon maganganunsu na mata yawo zuciyarta na ciwo wani irin kuka ke cinta amma ta daure tana zaune haka har fin minti 40 sannan Sega wani yaro da gudu yazo wurinta yace"kawu yace ki fito"

Ta tashi ta saka takalminta batare da yiwa kowa bankwana ba ta fito a gidan zuciyarta cunkushe ,

Tunda ta fito yake kallonta ganin kamar ranta bace ,

Harta karaso ta bude motar ta shiga bata kalleshi ba tana ta hadiye kukanta,

Idanunshi akanta a sanyaye ya kirata "muneera "

Memakon ta amsa sai fashewa da kuka tayi saboda yadda kukan ke kusa ,

Gaban ibraheem ya fadi ya zuba mata ido zuciyarshi na zafi jikinshi sanyaye,

Baice komi ba ya tada motar ya nufi gidansu,

Itako tana cigaba da kuka kanta kasa fuskarta rufe da abaya,

Har suka isa gida baice komiba yayi parking kofar gidan ya fito ya zagaya ya bude mata kofa ,

Ta fito tana cigaba da kuka ya rufe motar zuciyarshi na kara ta fasa ya bude gida suka shiga ciki,

Tana shiga tai zaune falo kan kujera tana kukan ta,

Ya karaso ya zauna kusa daita murya sanyaye yace"kiyi hakuri hakanan kar kanki yayi ciwo"

Ta rage kukan tana ta ajiyar zuciya,

Ya tashi ya dauko ruwan sanyi yabata tasha sannan tai shiru ,

A hankali yace"meyafaru ?meyasa kike kuka?"

Ta dago ta kalleshi ta meda kanta kasa ,

Ya sake memeta tambayar "meyafaru?"

A hankali murya dishe tace"bakomi"

Ya zuba mata ido ranshi na kara baci yace"just tell me me sukamiki"

Hawaye suka zubomata ta share tace "gorin haihuwa sukamin" ta karashe da kyar,

Fuskarshi tai jawur tsabar bacin rai yayi shiru na kusan minti biyar yana tunani sannan ya sauke numfashi cikin rarrashi yace"ki kara hakuri muneera Allah shine ke bada haihuwa kuma yana sane dake don baya mantuwa,and I'm begging u karda ki sake tambaya ta zuwa biki kowani suna banaso amma haka na barki don yadda kkdamu dasu,nasan mutanen nan basu da kirki kokadan duk yadda zasu soki ba kamar ni ba to ni dinma ba sona suke ba kiyi hakuri da bukukuwannan"

Ta daga kai ,

Ya cigaba da kallonta na wani lokaci a hankali yace"ki shirya Monday zamuje muga likita idan akwai wata matsala dangane da haihuwar duk zasu bamu magani"

Ta kalleshi tana jin sanyi hangowa take kamar harta haihun ta sakarmasa murmushi,yayi karamin murmushi shima ta sunkuyar da kai tana jindadi.
[4/4, 10:33] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 9&10


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*



*page din kine shema'u hassan ina godiya kwarai da long beautiful comments tnx u sosai*💝


Dakyar yayi hakurin akai kiran farko na asuba yana jin kiran ya shafa adduar da yake ya kwashe carpet ya ajiye ya dauki key daga shi sai jallabiya ya shiga mota ya dauki hanyar kauyen da matukar gudu ,

Gudu yake amma jiyake kamar baya tafiya don haka yaketa kara speed din motar zuciyarshi na cigaba da harbawa fass_fass,

Tafiyar 2hr se gashi ya samu isa cikin kasa da awa daya da rabi wannan ke nuna ya fanfali gudu sosai ,

Da isarshi gidan kakar yayiwa tsinke time din mutane daidaya ke yawo kasancewar gari baiyi haske ba amma abun mamakin gidan kakar mata ne keta shiga da fice aciki yana ganin hakan ya tabbatar da zarginsa dasaurinsa ya bude motar ya nufi cikin gidan a kidime ,

Duk da yana kidime be manta yin sallama ba amma fa bai tsaya neman izini ba ya kutsa kai cikin gidan ,da shigar shi yafara jiyo nishin galabaita da takeyi hankalinshi yakara tashi ya isa bakin kofar dakin da suke ciki yana cigaba da rafka sallama,

Wata mata ta fito dasauri tana kallonshi,

Cikin hanzari jikinshi na rawa yace"ina kaka?"

Ta kara kallonshi batace komi ba ta koma ciki kaka na rike da muneera hankalinta tashe tanata mata sannu da addua Matar tace"ibraheem ne ke sallama waje"

Kaka tai saurin tashi ko sallamar bata jiba saboda tsananin tashin hankali tana tuno mutuwar mahaifiyar muneera a irin wannan yanayin tana matukar firgice ta tashi dasauri ta fita ta sameshi,

Tana fitowa dasauri yace"kaka dan Allah kufito daita mu tafi asibity"

Bata musaba tace"tow_tow "cikin rashin natsuwa ta koma ciki,

Suka kamota tanata zufa da nishi duk ta fita hayyacinta batasan wake kanta ba suka fito waje daita zananta jagab da alamu tuni faya ta fashe,

Ganin yanayinta wata juwa ta dauki ibraheem saboda tashin hankali , zuciyarshi karye kamar yayi ta kuka ya daure yayi gaba yana kagare ya ganshi cikin asibity ,

Yana zuwa bakin moto ya bude masu suka shiga ya koma mazaunin driver ya tada motar ya nufi hanyar local government dake kusa dasu a ganinsa kafin 2hrs kome na iya faruwa,
Tafiyar minti 20 ta kaisu asibityn ya fito yayi ciki dasauri time din gari yayi tangaram nurses da yawa sun fito suka zo da kujera suka dauketa suka shiga daita labour room dasauri,

Su kaka sukai tsai tsaye bakin dakin sunata sallallami a zuciya idanun kaka jawur tana rikice,

Jin nishinta da ya karu har suna juyowa yasa ibraheem fita daga gurin yana hawaye ya nufi masallaci yayi salla yayi zaune yana share hawaye jefi_jefi zuciyarshi na fadamai mutuwa zatai wata ko tana hangomai dukkansu sun mutu shi kuwa yana son dukkansu su rayu,

Ya dauki tsawon minti 30 sannan ya tashi jikinshi sanyaye zuciyarshi na bugawa a tsorace ya shiga cikin asibitin,

Zuwan shi yayi dede da fitowar wata nurse ta amshi kayan haihuwar ta koma ciki,

Bayan mintuna goma wani likita yazo dasauri ya kutsa kai cikin dakin sude suna tsaye kowane zuciyarshi kamar zata fito bayan mintoci likitan ya fito ,

Can zuwa nurse din ta fito da jariri fari tatas dashi cikin zane kaka tai saurin amsarshi tana dan farinciki,

Nurse din ta kalli ibraheem tace"zakaje kaga likita akwai tests da zai baka"

Ibraheem na jin kamar ya kunna kai cikin dakin yaga halin da matarshi ke ciki ya hakura ya nufi office din likita,

Bayan ya zauna likitan ya kalleshi yace "Kune masu patient muneera?"

Ibraheem ya daga kai dasauri don yagama fahimtar akwai matsala,

Likitan ya jawo paper yafara rubuce_rubuce yana cewa"yanzu zakuje kuyi Wadannan tests din"

Ya karasa rubutawa ya bawa ibraheem ,

Ibraheem ya amsa ya dan karanta ya tashi ya fita ganin test din na jaririn ne yasa yaje wurinsu kaka sunata kallon jaririn ya amshesa ya nufi wurin gwajin dashi,

Bayan an aunashi ya dawo yabawa kaka shi zuciyarshi nata son ganin muneera yana niyyar shiga cikin labour room din aka fito daita kwance kan bed akawuce dakin jinya daita,

Yana ganinta ya matse lips yana jin mugun tausayinta tamkar ya cire ciwon jikinta ya dawo dashi jikinshi yabi bayansu ,

Bayan sun ajiye ta sun fito ya shiga ciki idonta kulle jin kamshinsa yasa ta bude ido a hankali tana kallonshi,

Ya sakarmata karamin murmushi me dauke da tarin tausayi ,

Ta meda idonta ta lumshe tana jin jikinta wani iri,

Ibraheem ya juya ya fita, ya fita ya siyo tea da bread da wainar kwai ya kawowa su kaka be koma dakin ba ya nufi wurin amsar gwajin da sukayi,

Dakyar kaka ta samu muneera tasha tea din kadan ta koma ta kwanta cikinta na tsananin ciwo,

Ibraheem na amsar result ya kaiwa likita,

Likita ya tsaya ya karanci result din da kyau sannan ya kalli ibraheem dake kagare yaji miye matsalar dan yaga wani abu dayasa shi Karin damuwa,

A hankali likitan yace"bai kamata kubar yarinya gida taita labour ba da zaran tafara labourn ya kamata akawota asibity tun kafin ta jigata"

Ibraheem ya jinjinakai,

Doctor yace"mun tura Ku gwaji ne saboda kara tabbatar da lafiyar yaron ,sakamakon gwajin ya nuna cewa yana dauke da cutar Albinoism ,cuta ce da akan haifi mutum daita sakamakon rashin melanocyte cell wannan kesa akan haifesu fari tass wasu tana kama idonsu kadai wasu kuwa har gashin kansu yakan kasance fari ,muna kiran masu cutar *albino*

Cuta ce da baa warkewa bawani magani da zaasha a warke ,yana da kyau Ku kula sosai da yaronku domin cutuka na iya saurin kamashi kuma a kula da shiga dashi cikin rana da barinshi cikin zafi sosai hakan na iya effecting dinsa"

Tunda doctor yafara magana ibraheem ya shiga tsananin tashin hankali ,tausayin danshi ya mugun damkar zuciyarshi albino basuyi yawa ba zakagansu jefi_jefi acikin alumma yau gashi ya haifi da da cutar ,inama ace cutace da ake neman magani da zaiyi duk bakin kokarinsa da duk abinda ya mallaka wurin nemawa danshi lpy sede kash cutace marar magani wadda ake rayuwa ba makawa a cikinta,

Zuciyarshi na ciwo yace"nagode sosai doctor insha Allah zamu kula sosai "

Likitan yace"yanzu zan rubuta maka drugs da zaa rika bashi don su temaka wurin kariya daga cutuka "

Jikin Ibraheem sanyaye yace"ya lafiyar mamanshi ?"

Doctor yace"tana bukatar hutu da kuma jini yana da kyau a rika bata abinci masu kara jini zamu barta anan na wani lokaci har ta samu lpy"ya mika mai prescription paper ,

Ya amsa yayi godiya ya tashi ya fita kanshi na mugun ciwo,

Ya samu wuri ya zauna yana tunanin wace irin rayuwa danshi zaiyi nan gaba da kuma kalubalen da zai fuskanta kasancewarshi *albino*

(Albino sune ake kira da *zabaya* da hausa maybe ba haka ake kiransu ba awasu garuruwan,

Sune dai mutanen da zaa gani fari tass kamar turawa wasu farinnasu ya zarce haka wasu zakaga suna da digo_digon baki a jiki ya danganta da gene din mutum,wasu gashinsu yana zama fari wasu kuma baki ,wasu idanunsu kansu ba bakake bane zakagansu wani iri,

To sune albino (zabaya) inafatan kun fahimta) .

Ya jima zaune awurin sannan yaje pharmacy ya sai drugs dinsu ya kai musu yayiwa kaka bayanin yadda zaayi amfani dasu,

Tunda ya shiga dakin idanunshi na kanta tana ta bacci yameda kallonshi gun yaron dake rungume gun Matar da sukazo tare for minutes sannan ya dauke ido Sam baya son muneera tasan yaron nada wata matsala babu shakka zata shiga damuwa yaja numfashi bai fadawa kowa ba ya juya ya fita,

Wunin ranar yayisu babu natsuwa babuci babu sha tunani barkatai a zuciyarshi farincikinshi kalilanne,

Su kaka sunta kallon yaron amma basu gane zabaya bane suna tunanin kila farine zai rage nan gaba,

Sai marece muneera ta farka so daya ta kalli dan nata ta dauke ido kasancewarshi dan farko gasu kaka awurin,

Tasha tea aka bata shi tabashi nono tana dan satar kallonshi ganinshi jawur_jawur baisa takawo wani abu a ranta ba sede tayi mamakin ganin suna bashi magani tuno wuyar da tasha wurin labour yasa hankalinta kwanciya tasha wuya sosai har batai tunanin zata kara awanni a duniya ba ,

Yanayin asibitin baiyiwa ibraheem ba yana kuma tunanin a babban asibity zasufi samun kulawa wannan yasa wanshekare ya samu aka turasu babbar asibiti a birni,

Bayan sunje aka cigaba da kulawa dasu yadda ya dace,

Ya koma gida yayi wanka yaci abinci ya kwanta bacci bayan ya tashi da daddare ya koma asibitin ya kai musu abinci muneera na zaune ta dan kalleshi tai karamin murmushi,

Yana murmushi yace"ya jiki?"

A hankali tace"naji sauki"

Yace"Allah yakara sauki"

Tace"ameen"

Ya dauki yaron ya masa huduba sannan ya musu bankwana ya tafi,

Gidan Baban farouk yayiwa tsinke yamishi waya ya fito ya fada mai haihuwar ,

Baban farouk yana farinciki yace"Allah yarayamana insha Allah gobe maman farouk zataje ganinsu ka kwantar da hankalinka wannan ba abun damuwa bane Allah shine ke halittar mutum yadda yaso hakan baya nuni da cewa baya sonshi ya halicceshi hakanan, idan kana damuwa itama zata shiga damuwa sosai kubar komi ga Allah kuyita masa addua"

Ibraheem yayi godiya ya tafi kuma ya dau shawarar aminin nasa,

Wanshekare su Baban farouk sukaje bayan sun masu siyayya me yawa sunata shaawar yaron,

Kwanansu bakwai asibity sannan aka sallamesu yana zuwa yafadawa kaka yace zai kaita can gidanta se kakar ta

Please Login or Register in order to submit comment