Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kira KHALEED dashi,

Seda akayi two yrs sannan KHALEED ya dawo gida sunata murna harda hawayen farinciki suka rungume juna kafin KHALEED ya dauki WALEED yana jujjuyasa da yi masa wasa yanata darawa ya ajiye shi ya shiga yayo wanka ya dawo muneera ta hadamai abinci kala_kala ya zauna yanaci yana santi yana dan bawa WALEED a baki,

Sunata surutu sukaji WALEED yace"daddy ....daddyna ..La dawo"

KHALEED ya kalleshi da murmushi fuskarshi ya kalli muneera yana mamaki,

Tace"dole yayi murna tun yana dan months se yau"

KHALEED ya dago fuskarsa yana murmushi yace"Na dawo,bari na gama mufita yawo"

Muneera tace"a,a akwai rana yau karku fita yanzu kubari har marece "

KHALEED yayi karamin murmushi idan yana turai mancewa yake da kalarshi don baya wani ciwo kuma bawani abinda kesa ya tuna hakan ,

Suka cigaba da fira ya gama cin abincin suka dawo falo suna cigaba da farinciki,

Dawowar KHALEED ya dawo da jindadi da walwalar muneera shi kanshi WALEED duk da bai cika dariya ba amma yana danyi akai_akai,

Tunda ya dawo ya cigaba da kula da WALEED yana aiyukan gida wata irin shakuwa ta kara shiga tsakanin shi da WALEED yayi wata biyu ya koma randa ya tafi seda temakon maganin mura WALEED yayi bacci yanata faman kuka shi kanshi KHALEED kewar WALEED ta hanashi sukuni kafin ya warware,

WALEED nada shekara ukku tasa shi makaranta yayinda KHALEED ke waje yanayin tasa,

Bayan 2yrs KHALEED ya gama makarantar shi ya fito da sakamako me kyau wannan yasa jamiar suka rikeshi domin ya rika koyarwa a can,

Bayan yazo yaga family din shi sun sha murna da shagalin kammalawar shi ya koma London badon yaso ba sedan jindadin muneera don aganinta can ne dede da rayuwar shi kuma abinda yafi burgeta shine yadda haryanzu yake a nutse baya wata rayuwa irinta turawa ,

Farawar aikin KHALEED yasa rayuwa ta kara musu dadi lokaci zuwa lokaci yakan turo musu da kudade da kaya kafin ya samu zuwa ,

*BAYAN SHEKARU*

Abubuwa da yawa sun faru daga ciki harda mutuwar Baban farouk ,WALEED nata karatu baida wata matsala a rayuwarshi abokai kala_kala ke bibiyarsa don dai cika son mutane ba da abokinsa Hameed kawai yake sakewa,jikinshi jikin girmane tamkar Abbansa yayi tsawo da dan jiki lokaci daya, bazaa kirasa mummuna ba amma ko kadan bai kamo KHALEED wurin kyau ba ,akwaishi da tsafta da gayu tamkar daddynsa KHALEED dake London,

Time da yake aji shidda KHALEED yayi tunanin kaishi waje yayi karatu sai de bai fadawa muneera ba,

*KUHON KANAWA*

Wani kauye ne dake can cikin daji karamin kauye ne da gidajen suke da nisa tsakani wato akwai tazara tsakanin wannan gida da wannan gari ne na Fulani Wanda suka dogara da noma da kiwon shanu, shine rayuwarsu dasu suke komi,

Acikin garin aka haifi wata kyakkyawar yarinya da mahaifinta yasa mata suna ZARAH,sosai mahaifinta ke sonta fiye da yadda yake son komi bayan haihuwar ta bada dadewa ba mahaifiyarta ta rasu ,mahaifinta ya dade baiyi aure ba sannan ya auri matarshi ta yanzu da Zara ke kira innan mu,

Tunda ya aureta har zuwa lokacin nan bata samu haihuwa ba shiyasa ta rike Zara tamkar yarta ta cikinta tana mugun sonta ,

Bayan aikin gona suna dogara da kiwon sune kadai Wanda idan lokacin Rani yazo har gidajen su suke bari su tafi daji domin kiwon shanun su,

Wannan shekarar tazo da zafin rana ruwa yayiwa dajin karanci ga ba ciyawa wannan yasa Dabbobin su suka rame saboda babu abinci lokacin Baban Zara ya fara neman inda zasu koma domin cigaba da kiwon su,

Watarana yana zaune abokinsa ya shigo kauyen yana murna ya tarbe shi sunata labari nan Baban Zara yake bashi labarin halin da suke ciki,

Abokinsa kuwa yafadamai dajin da yake akwai ruwa da abinci sosai domin har noma suke duk da ba time na ruwa ba ,

Baban Zara akwaishi da son kudi da dabbobi wannan yasa yayi shaawar komawa da zama dajin amma bai iya jin zai tafi yabar Su Zara su kadai ,su ka gama magana da abokin a kan idan zai tafi zasu koma tare zai tattara dabbobinsa su tafi,

Da hanzarin shi cike da farinciki ya koma gida ya samu innar Zara na dakan masarar da zasuyi tuwo anjima da daddare,

Ta ajiye dakan ta kawo masa ruwa ta samu wuri ta zauna ,

Ya sha ruwa ya dauke kai tare da cewa"Alhamdulillah wato na dade banyi farinciki ba irin na yau"

Da hausarta irinta Fulani tace"Alhamdulillah munko godema Allah "

Yayi yar dariya yace "ina Zara ?kuzo kufara shiri garinsu haladu zamu tafi kafin damuna ta dawo"

Tai shiru tana nazari sannan tace"ban k'i ta taka ba amma da ka tafi ka barmu anan nida Zara duk lokacin da ka samu dama seka leko mu akwai hatsari tafiya inda baka sani ba"

Lokaci daya fuskar shi ta sauya yace"Aradun Allah kafa ta kafar ku ba inda zan tafi na bar marainiyar Allah ita kadai, ki shirya kamar yarda nace"

Ranta ba dadi tace"to amma naso ko aure a yiwa Zara kafin mu tafi"

Yace"Tabbb!!!"da karfi yana wata iriyar dariya ya cigaba da cewa"duk kauyen nan ba wanda zan iya bawa Zara ,kudin auren Zara ba kadan bane"

Tace"Har nawa ne Shehu?"

Yayi dariya yace "kibari har lokaci yayi ,amma da kudin aurenta zan siya mata shanaye"

Tai dariya tace"Allah shi yarda" ta tashi ta koma gun dakan ta,

Bayan kwana biyu suka dauki hanyar dajin ,tafiya ce mai nisa da suka dade suna yi sannan suka isa, tunda suka isa hankalin inna ya kwanta ganin da akwai gidaje jefi_jefi har da yara wannan yasa hankalin ta ya kwanta,

Ba jinkiri shehu yafara abinda ya kawoshi na kiwo har ya samu gona yafara noman rani,

A hankali Zara take binsa tana kula da Dabbobinsa wani lokaci seya barta kula dasu ya nufi gona,

Tana lura da wani bafulatani da abokan shi da suke yawan tsayawa kallonta amma bata damu dasu ba batada hayaniya da son wasanni she's so silent,

Shi kuwa bafulatanin me suna Murtala ba karamin shaawa Zara ke bashi ba Su kansu abokan nasa sosai take burgesu ,

Kyakkyawace fara tass yar karama da bazata haura 14 ba, ba gajera ba ba doguwa ba matsakaiciya batada jiki ko alama breast ma yanzu suke kan tohowa tana da gashi sosai da kullum yake kan kafadunta,tana da kyau da kallo daya zaka mata kagane bafulata nace gaba da baya,

A birni, su WALEED suna kanyin jarabawa saura kwana kadan Su gama school KHALEED ya kira muneera,

Ta dauka ranta na sanyi yace"mama ina wuni?"

Tai murmushi tace "lafiya lau ya kake ya aiki ?"

Yace"lafiya lau mama YA WALEED?"

Tai murmushi tace "yana school amma nasan yana gab dawowa"

Yayi murmushi yace "mama inason na nemawa WALEED karatu a India bayan result dinsu ya fito"

Farin cikin muneera ya bace lokaci daya tace"Ni kuma wazan rika kallo yana debemin kewa?kai ka tafi shi kuma saika turashi wata uwa duniyar?to ban yadda ba kabar shi yayi karatun shi anan duk karatu ai karatu ne"

Yayi murmushi yace "mama nafison yayi karatun a waje kamar yadda nayi don Allah mama ki amince"

Da kakkausar murya tace"KHALEED kabar maganar nan don bazata yiwu ba"

Yayi shiru yana nazari sannan yace"Mama ni zan dawo nan shi kuma seya tafi karatunsa"

Gabanta ya fadi haryanzu bata manta baya ba yarda rayuwar shi ta tafi ga zafin da ake ciki shi kuma ga yanayin shi,

Dasauri tace"a'a kayi zamanka anan saboda karatu saika bar aikin ka kazo kaita fama da zafi kuma kasan bakason zafin kabar maganar kawai"

Ya sauke ajiyar zuciya yace"mama ki fahimceni idan na dawo badole in ta yawo ba ko aikin banki ina iya samu zasu daukeni, sannan mama nima inason inyi rayuwa cikin ku inason zama kusa dake tun ina primary rabona daku, don Allah mama kibari na dawo yanzu na girma bazai zama kamar baya ba ,kuma dole watarana na dawo mahaifata kiyi hakuri kibari na dawo"

Tai shiru na wani lokaci tana nazari haryanzu baya maganar aure duk da de shekarunsa talatin ne amma tanaso yayi aure ya samu zuria zai kara natsuwa kuma yakara cika mutum,

Ba don ranta yaso ba se don farin cikinsa da son yayi auren tace"to Allah yazaba mafi alheri"

Yace"Amen mamata nagode sosai shiyasa nake sonki"

Tai murmushi ,lokacin WALEED ya dawo daga school yazo ya zauna kusa daita ya dora kanshi kan kafadarta don duk girmansa baya jin kunyar hakan,

Tai murmushi ta doramai waya a kunne tace"daddynka"

WALEED ya rike wayar ya tashi zaune yana dan murmushi yace"daddy ina wuni? "

Wani sanyi ya ratsa zuciyar KHALEED yanajin hakan duk time da yaji dan'uwan nasa ya kirasa da wannan sunan,

Yace"lafiya lau ya exam?"

WALEED yace"Da wahala daddy"

KHALEED yayi dariya yace"u have to read hard idan kanason tayi maka sauki ba ka rika fadin wahala ba kana ma karatun exam din kuwa?"

Yayi murmushi yace"eh"

KHALEED yace"to ka kara dagewa WALEED so nake kasamu result me kyau nasan kafi son zama likita seka tafi India kayi karatun ka a can"

WALEED na farinciki yace"I love u daddy nagode sosai"

KHALEED na farinciki jin yadda WALEED ke murna yace"so ka rika tuna idan baka ci exam ba babu tafiyar"

WALEED yayi murmushi yace "zanci ta daddy believe me"

KHALEED yace "I hope so ,sena dawo"

WALEED yace"yaushe zaka zo daddy?"

KHALEED yayi dariya yace "tambayi mama I want to hang up bye" ya kashe wayar,

WALEED ya cire wayar a kunne ya kalli muneera yace "mama yaushe daddy zai dawo?"

Tace"ban sani ba amma yana gab dawowa"

Yayi murmushi ya koma ya kwantar da kai a kafadarta yace"I'm tired"

Tai murmushi tace "kamata yayi kaje kai wanka zakaji dama"

Yace"OK "ya tashi ya nufi dakinsa,

Ta bishi da kallo tana tunanin dawowar KHALEED yadda zai cigaba da rayuwa anan,

WALEED na fitowa wanka wayar shi tafara ring,

Ya dauka ya kara a kunne yayi shiru,

Abokinsa Hameed yace"Hi ina waje, ka fito ka rakani wani wuri"

WALEED yace "bazan samu damar zuwa ba"

Hameed yace"to shikenan na tafi "

WALEED yace"wait ganinan fitowa i want to tell u something "ya kashe kiran dasauri ya fiddo wasu kananun kaya a wardrobe ya saka ya gyara sumar shi ya dauki wayarshi ya fita,

Muneera na falo taga fitowarshi tace" har kuma zaka fita?"

Yace"Hameed ne yazo yana kofar gida"

Tace"OK"

Ya juya ya fita ya samu Hameed yazo da motor babansa ya bude ya shiga ,

Hameed yace"bani labarin I'm eager"

WALEED yace"daddy zai turani India karatu"

Hameed yace"Wow I'm happy for u, gaskiya kayi dacen dan'uwa ban taba ganin Wanda ke samun gata kamar ka ba"

WALEED ya kalleshi yayi dan murmushi yace "I know shiyasa nake son shi sosai"

Hameed yace "aikuwa sede mutafi tare bari nakoma gida zan fadawa dad dina in yaso semu tafi tare"

WALEED yace "OK ina zakaje haka?"

Yace"fira mana "

WALEED ya tabe baki yace"sai ka dawo"ya bude motar ya fita,

Hameed yayi murmushi yace "duka yaushe ne zaka shiga tarkon wata kazo kana begging na raka ka" ya tada motar yabar kofar gidan,

Tun sannan KHALEED yafara fafutukar dawowa gida domin dan'uwanshi ya samu damar tafiya nashi karatun ,bai damu da yadda rayuwar zata kasance ba bayan dawowarshi shide burinshi WALEED ya samu karatu me kyau,

Bayan satika WALEED yagama exam ya dawo kullum yana gida daga gida sai gidansu Hameed shikenan yawon nasa,

A lokacin Su Zara suna da watanni a rugar da suke ,dabbobinsu na samun abinci kuma babanta na aikin nomansa,

Shi kuwa murtala zuciyarshi nata kara shaawar Zara yayin da take kara girma kadan _kadan ,

Yau tunda safe ta koro shanu tayo daji dasu domin suyi kiwo ita kuma tana kula dasu,

Tana tsaye tana kallon shanun murtala ya iso wurin ya tsaya dogare da sandarshi yana karemata kallo daga shafaffun hips dinta zuwa small breast dinta da suke kan fitowa zuwa kyakkyawar fuskarta da take dauke da cute bakin ta,

Har zuwa wani lokaci ya sauke numfashi ya dora sandar shi a kafada ya nufeta karo na farko,

Tana tsaye sede taga mutum gabanta ta kalleshi sama da kasa Sam ba tsoro idanunta,

Murtala na binta da kallon shaawa yace"sannu yanmata"

Ta kalli fuskarshi ta giftashi zata wuce,

Yayi saurin shan gabanta yana cewa "jira kadan mana mu gaisa"

Suna gab da gab ta tsaya tana kallonshi don jin me zaice a iya saninta samari tsoronta suke saboda son kudin babanta zaita tatsar mutum daga karshe yace ya fasa basa,

Murtala na tsaye yana kallon breast dinta kafin ta San me zaiyi sai jin hannunsa tayi ya rike breast dinta daya,

Ta buge masa hannu ta matsa dasauri tana bata fuska tamkar zatayi kuka gabanta na dukan ukku_ukku,

Murtala Yayi dariyar shakiyanci yace"kidena jin tsoro Zara ina sonki zaki aureni?"

Tana hararar shi da murguda baki tace"Allah shi sawwakemin auren dan iska"

Yana kallon yadda lips dinta ke motsawa yana karajin desire dinta yayi dariya jin ta kirashi dan iska,

yace"naji ni dan iskane kuma kema zaki zama yar iska"

Ya fiddo idanunsa da suke jawur cike da bacin rai da zallar shawarta yace"yau dinnan da dare ki sameni dakina dake can bayan gidanku daga yau kin zama matata har zuwa lokacin auren mu, idan kuma har baki zoba zansa yarana su daukomin ke in miki kaca_kaca kuma bazan aure ki ba sai de .....sai de zan tabbatar hakan ta cigaba da faruwa akai_akai"ya karasa yana cije lips dauke da dariyar mugunta ,

ZARAH ta yadda sandar hannunta zuciyarta na mugun bugu cike da tsoro ta fara fallar gudu zuwa gida sanin daji suke ko yanzu yaso zai iya mata illa,

Tasha gudu sannan ta isa gida da zuwanta tafada kan cinyar inna tana matsanancin kuka tace"inna naboni na lalashe"

Hankalin inna tashe tace"Zara ina shanun meya sameki?"

Tana kuka hawaye masu zafi na gudu kan kumcinta tace"inna murtala ne yakeso ya lalatani"

Gaban inna ya fadi jin ta ambaci murtala zuciyarta na dokawa ta buga tagumi,

Zara tace"inna mutafi gida banason arika cemin yar iska "

Inna tace"kiyi shiru baffanki bazai bari haka ya faru ba kiyi hakuri har ya dawo gida "

Zarah ta cigaba da hawaye yayin da innar ke cikin tashin hankali,

Baban Zara bai dawo gida ba sai gab Maghreb lokacin shanun sun dawo wasu kuma basu dawo ba,

Yana shigowa wurin dabbobin yafara dubawa yaga babu shanu guda ukku da wasu dabbobin,

Dasauri ya shiga dakin da suke zaune sunyi shiru a fadace yace"Zara ina sauran shanayen ? Bana fadamiki ki rika lura da yawan su ba?"

Inna tace"Zara de dakyar tasha gida murtala ya tare ta yana mata maganganun banza"

Jin ta ambaci murtala yasa gabanshi faduwa hankalinshi tashe dasauri yace"ke Zara bai miki komi ba ko?"

Zara nata kuka muryarta dishe tace"ya rikemin nono guda"takara fasa kuka

Zuciyar baffa tai mummunan bugu ya watso zagi "Jar uba" tare da cewa"Aradun Allah saina koya mashi hankali"

Inna na cikin firgici tace"kasan abinda zakayi kasan yaron nan murtala ya gagari kowa, kowa tsoronshi yake yafada mata ta sameshi dakinshi ko kuwa ya turo a daukar masa ita"

Baffa na huci yace"karya yake idan hakan ta faru sai de uwarshi ta haifi wani"jikinshi na rawa ya juya dasauri haryana bugewa da bango ya fita ya nufi gidan abokinsa Haladu,

Yana zuwa bakin gidansa yafara masa sallama da karfi ,

Haladu ya fito dasauri ganin shine yasa yayi dariya yace"Aradun Allah harka bani tsoro"

Baban Zara na cikin firgici yace"Nine zuwa nayi nafadamaka wata babbar magana ,murtala dan me gari ne yake neman Zara da lalata ya umarceta taje dakinshi ta sameshi ya kuma tabbatar idan bata jeba zai turo a dauketa akai mishi ita"

Haladu ya shiga tashin hankali ya sauke kanshi kasa yayi shiru,

Baban Zara yace"Aradun Allah yau da rabon lahira tai bako don idan har yaje gidana yanka shi zanyi"

Dedenan abokin murtala yazo wurin ya labe yana saurarensu,

Haladu ya dago yace"um_um kagade megari shiya baka bukkokin da kuke ciki kuma baida dan da yakeso fiye da murtala idan ka kashe shi wlh kashe ka zaiyi tare dasu, harni dana kawoka saiya ga bayana ,idan kuma har ya samu damar aikata hakan to koda kafadawa megari bazai yarda ba,ko da ya yarda an riga an cuceku, shawara ta shine ku bari gari ya kara lafawa ka kora dabbobin ka ku koma gida"

Abokin murtala na jin haka ya jinjina kai domin har murtala yabasu umarnin daukota anjima yayi saurin barin wurin ya nufi wurin firarsu,

Baban Zara na rungume da sandarshi zuciyarshi na tsananin zafi ga yunwa da yake ji yana dago kai yaga gari yakara duhu kuma yayi tsit,

da sauri idanunshi jawur yace"haladu duk kai ka cuceni da baka fadamin akwai ga gararre cikin rugarku ba danasani daban biyoka ba amma nagode sosai "yajuya yabar wurin dasauri,

Haladu yanata kwala masa kira bai jiyoba saima saurin da yake karawa don ya isa gida.



Toh fa shin murtala zai samu abinda yakeso ? Koko su shehu zasu samu guduwa daga rugar? Saimu hadu a next page🥴



tnx all masu min comments😍
[4/4, 10:33] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 19&20


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*


*Ur page Kawalli Asma'u Ado Matar Malam 😍ina mutukar godiya da jinjina Allah yabar zumunci*



Ya isa gida a fujajan yana rikice ya shiga dakin nasu, ganinsu har yanzu inda yabar su yasa hankalin shi dan kwanciya domin kafin ya iso har hangowa yake murtala ya dauke Zarah ,

Idanun shi jawur jijiyoyin shi rudu_rudu ya samu wuri ya zauna yayi shiru kuma brain dinshi takasa hangomasa komi tsabar firgici abu guda ya rike da a lalatawa tilon diyarsa rayuwa gwara su gudun,

Dakin shiru kamar ba kowa inna nata kallonshi jin baice mata komi ba ta tashi ta kawo mai fura ta ajiye ta koma ta zauna a sanyaye tace"Jikina duk ya mutu banyi komi ba kasha ko furar ce hakanan"

Zuciyar shi na zafi yace"Jikin ki yadena mutuwa domin doguwar tafiya ce a gaban mu don yau zamu bar rugar nan"

Ta fiddo ido waje tace"cikin dare sai kace barayi?haba shehu kayi tunani bakai kadai bane gani ga Zarah"

Ya tunkudar da kwanon furar har ta zube ranshi bace yace"to ya kikeso ayi ?so kike na zauna kafin gobe yazo ya hallakamu ya nakasa ta? Tafiya zamuyi ku dauki yan kayan ku anjima idan garin yakara lafawa zamu tafi"

Inna tace"dabbobin fa?"

Yace"Har su gabadaya "

Inna tai shiru amma Sam shawarar ba taimata ba tafiya cikin dare ba shiri ba sallama kamar wasu mugaye ?

Shehu ya kwantar da murya cikin rarrashi yace"Zarah ki danyi bacci kafin anjima kinji?"

Ta jinjina kai amma bazata iya bacci ba saboda tsoro da firgicin da take ciki,

Shehu na cikin firgici ganin innar ma ta kasa tashi yasa ya tashi yafara hada masu kaya cikin dan bakko guda kasancewar kayan bamasu yawa ba yana gama hadawa ya ajiye dede bakin kofa ,

Shi kuwa abokin murtala da gudu ya karasa inda suke raba dare suna fira,

Murtala yace"wannan gudun fa haka?"

Ya tsaya yana sauke numfashi sannan yace "na dawo gida ina hanya naji shehu da haladu suna maganar ka na tsaya saurare sai naji yana bashi shawarar ya kora shanunsa subar rugar nan cikin dare don karka samu damar cimma burin ka"

Murtala ya kurawa wuri daya idanu yana jinjina kai na mintuna sannan ya babbake da dariya irin ta mugayen mutane yace"sunyi kuskuren shigowa yankina idan sukai yunkurin guduwa dole su dauki hukunci ina sonta dole saina sameta"

Abokansa su ukku sukace" tabbas kuwa rugar nan taka ce sai yadda kaso take tafiya",

Murtala ya sake darawa yace"dole saina samu biyan bukata ta kota halin kaka"

Yace"kuna jina?"

Suka jinjina kai suna kallonshi,

Ya dafa kafadar daya yace"kai zakaje bayan gidansu ka labe ka jira motsinsu lokacin da zasu fita,da zaran kaji motsinsu saika nufi inda shanun megari suke ka korasu da gudu kubi hanyar da suka bi"

Ya jinjina kai yana amsar ordern shugaban shakiyancin su,

Ya dafa wani yace"da zarar kaji motsin shanun megari saika koro na gidanku gabadaya kabi bayan shi"

Yace"angama"

Ya kalli dayan yace "Da kai dani zamu tsaya se sunyi nisa har sun taddo dabbobin shehu sannan zamu fara yekuwar barayin shanu sun shigo ,lokacin kowa zai fito da makaminsa su kuma zasu fara gudu domin gujewa kisa sai muyi amfani da wannan damar mu daukota my kawota cikin daki muyi yadda muka so gab asuba sai mu kaita daji mu karasa ta tabi mahaifinta"

Suka kwashe da dariya jin wata katuwar mummunar shawara sukace"aradu murtala ka chika mugu"

Yayi dariyar mugaye yace"zaman mu a birni bana banza bane ku tashi muje mu rage bacci kadan"

Suka tashi suka nufi dakin suka shiga sunata dariya,

Bangaren Haladu kuwa tunda ya koma cikin gida yayi zaune wuri daya zuciyarshi na tsananta bugawa yana matukar tsoron wani abu ya faru idan har ba su bar kauyen ba to tabbas akwai abinda zai faru ,bai yi tunanin shawararshi zata zamo matsala ba,

Can dare yayi dare koina tsit baka jin kukan ko da tsuntsu, su Zara na zaune shehu yasa suka tashi tana jin juwwa kanta na mugun ciwo ta dauki bakkon inna ko ta yafa mayafinta suka fito,

Shehu yafara kokarin kora shanun cikin sanda batare da hayaniya ba inna ta kama mishi sukai ta korasu,

Murtala da baccinsa baiyi nauyi ba shi yafara jin motsi yayi saurin tada su sukai waje da gudu don gudanar da abunda yasa su ,

Shi da dayan suka tashi suka nufi dajin da gudu batare da yin yekuwar ba kamar yadda suka tsara, domin dauke Zara da Zaran sun samu dama,

Lokaci daya abokan murtala suka koro shanun megari dana gidansu daya daga cikin abokan da gudu suna kusan taddo su kawu suka koma baya suka fara ihu barayin shanu ,

Nan da nan mazajen rugar suka fito da makamai da bindigu domin a wurinsu shanun sune rayuwar,

Su Zara nata tafiya basu koyi nisa sosai ba suka ga tarin shanu da gudu sunyo wurinsu kafin su Ankara kuma suka fara ganin hasken hitilu ana dallasu ana ihu,

Zara ta saki bakkon hannunta jikinta na muguwar rawa ganin wani abu daban dake faruwa,

Ba tsaiko sede suka fara jin bindigu tash tush suna harbi yayin da wasu sukayo wurin aguje gadan_gadan,

Shehu gabadaya rudewa yayi, yayi saurin kama hannun inna yana cewa "mu gudu ...mu gudu"

Zarah na jin haka ta yanki daji da mugun gudunta batare da tasan inda take nufa ba,

Inda Zara tayi daban inda su inna sukayi daban dukkansu suna gudun ceton rai yayinda ake biye dasu,

Suna cikin gudu aka durme shehu da bindiga ya fadi wurin a mace,

Jikin inna yakara daukar rawa duk jijiyoyin jikinta sukayi sanyi bata kara tako ba tai zaune kan gawar shi tana kuka har akazo aka sameta bugu daya wanu ya mata da sanda ta garzaya lahira inda mijinta ya tafi,

Zara kuwa nata gudu cikin daji yayin da su murtala ke cikin dajin sun bazama nemanta ,

Gudu take bata san ina take jefa kafar ba batasan ana biye daita ba ,ba abinda kunnuwanta keji illa karar bindigu da kuma maganar baffanta Mu gudu....Mu gudu,

Tana gudu har ta gaji ta labe jikin wata bishiya tana numfashi tana cikin meda numfashi taji hannun da bazata taba mantawa ba ya birkitota da karfi yana haki yana kwasar dariya,

Ta fiddo idanuwa warwaje tana cikin matsanancin tsoro zuciyarta na mugun gudu kamar zata fito,

Ba shiri tafara fitsari daga tsayen ji kake shaaa!! jikinta na mazari,

Murtala yakara kecewa da dariyar mugunta ,

Saiga abokinsa yazo wurin a guje ya tsaya yana meda numfashi sannan ya fara dariya yace"oga kafara kawai ayi komi anan basai munje can ba"

Murtala ya dalla Zara da fitila yace"kin cika taurin kai, gashi taurin kan yasa Shehu da inna sun bakunci lahira kuma yanzu zanyi abinda naso dake nabawa abokaina sauran, naso ace kinbi umarnina da kin zauna lpy amma yanzu......"

Ya kai hannu zai kuma damkota jikin Zara na rawa ta goce ta yanki daji da gudun tsiya iya karshen iyawarta,

Su murtala sukabi bayanta da gudun tsiya,

Tana ta fallar gudu kunnuwanta na kara fadamata maganganun murtala cewa ya kashe su inna zaiyi abinda yaso daita sannan yabawa abokansa saura ta dage gudu sosai,

Tana ta gudu suna biye na tsawon lokaci batai auneba taga haske gabanta wata katuwar tirela bakin titi ta dan tsaya tana kallon motar tana numfashi kamar ranta zai fita sai hango me motar tayi zukunne da alamu yana biyan bukata ne,

Da gudunta ta isa wurin motar tana galabaice ta samu ta taka ta haye sama

Please Login or Register in order to submit comment