Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai kauna yadda suke wasa da yadda yake kula dashi har zuwa jiya dayake cewa yana jindadi ko baya da rai akwai me kula da muneera da kannenshi ,ya cigaba da kuka kanshi na ciwo kamar zai rabe biyu,

Itama tanata kuka tashin hankali bai bari tako tuna da salla ba ,

Har kusan awa biyu suna zaune sunata kuka KHALEED yayi shiru lokaci daya tare da share hawayen shi cikin zuciyar shi ya daukarwa kanshi alkawarin kula da mamanshi fiye da karfinshi kuma bazai bari dan uwanshi yayi kukan rashi ba koda so daya ,

Cikin karfin hali ya tashi ya karasa gefen gadon da muneera ke zaune muryarshi shake idanunshi jawur jijiyoyin kanshi duk a waje ,ya kalli fuskarta tana ta kuka idanunta rufe,

Cikin sassanyar murya yace"mama kiyi hakuri kidena kuka... nasan da Abba zai tashi yanzu abu na farko da zai farayi shine hanaki yi masa kuka...adduarki yake bukata adede wannan lokaci, mama in kin duba rayuwarnan duk mutuwa zamuyi ina mahaifanki? ina kaka ? Duk sun tafi kuma kinyi hakuri ina rokon da kiyi hakuri a wannan karon ma, kinema mishi gafarar Allah ki mishi addua mama kuka bazaiyi ba"

Muneera ta rage kukan Amman hawayenta sun kasa tsayuwa tana matukar kaunar mijinta ya sota ya nunamata duk soyayya da dukkan kulawa,

Muryarshi sanyaye yace"kiyi salla zanje na fadawa Abba farouk da family "

Ta daga mai kai idanunta kasa,

Ya tashi ya fita jikinshi sanyaye,

Ta kara kallon mijinta tana jin kamar tai mishi magana ya amsa amma ba rai ta rufeshi ta tashi dakyar cikinta nata ciwo ta wuce toilet tayo alwala ta dawo ta tsaya yin salla tana yi tana kuka tana masa addua,

cikin kankanin lokaci gidan ya cika da jamaa akai mishi wanka akai masa sutura ba yadda zatai tana gani aka tafi da mijinta makwancinsa ,

Bayan an rufeshi kowa ya tafi amma banda KHALEED ya dade zukunne bakin kabarin yana mishi addua sannan ya tashi ya tafi yana tunanun rayuwar da zasuyi gaba da kuma nauyin dake kansa,

Muneera ta kasa cin abinci har dare kowa ya kwanta tana zaune tana tasbihi KHALEED ya mata knock tabashi izinin shiga ya shigo dauke da plate da ruwa a hannu,

Kallonshi kadai tayi hawaye suka zubomata daganinshi shima baici abincin ba amma bata kanshi yake ba ,

Ya karaso ya zauna kusa daita cikin ladabi yace"mama ki kara hakuri insha Allah Abba yana cikin rahmar ubangiji kidena kuka"

Ta jinjina kai kawai tana ganin bazai fahimci yadda take ji ba,

A hankali yace"ga abinci ki daure kici ko kadanne"

Ta kuma jinjina kai tana tausayin kanta,

Memakon ya bata plate din sai kara matsawa yayi sosai kusa daita ya rika debo abincin yana bata tanaci tana ajiyar zuciya,

Harta danci yabata ruwa sannan ya tashi zai fita,

A hankali tace"KHALEED.. Ka daure ..kaci abincin.. kaima"

Yace"to zanci "ya juya ya fita yaja mata dakin,

Tana mai kallon tausayi tasa hannu ta dauke hawayen da suka gangaromata ta meda hannun kan cikinta daketa harbawa tana tausayin abinda ke ciki,

Kullum KHALEED ke kula daita shi kuwa abincin ma bai samun ci sai ruwa saboda tunani duk yabi ya rame kuwa har akayi kwana bakwai a ranar aka raba gado sannan kowa yayi tafiyarshi akabarsu su biyu cikin gidan,

Majority sede suyi jungum bame magana abinci kuwa dole muneera ta dawo cin shi don shima ya rika ci,

Ganin ta dan rage damuwa yasa KHALEED fara cin abincin,

Muneera ta tsaya tai nazari nan tana teaching tana samun albashi kuma rayuwar diyanta zatafi samun inganci a cikin birni ba kamar kauye ba wannan yasa taki komawa kauyen sukai zamansu anan,

Kwana ashirin da mutuwar ibraheem tafara labour cikin dare daga ita sai KHALEED ,KHALEED ya rude ya rasa inda zaisa kanshi brain dinshi na hangomishi zata bi Abbanshi ,ita kuwa tana ta bakin kokarinta wurin ganin ta haihu,

Ya nata mata sannu ya fita ya dauko key dukda bai kware da motar ba hakanan zai dauketa su tafi yana dawowa dede fadowar jaririn yana tsanyala kuka KHALEED yayi saurin nufar kayan haihuwa ya daukosu ya kawo yana tawa mahaifiyarshi sannu ta dauki yaron ta yanke masa cibi ta mika maishi ya daukeshi ya fita tana zukunne har uwa ta fado ta zauna tana meda numfashi tana hawaye ganin Allah yakara bata wani namijin gashi ba bayau ba kunnuwanshi bakake da alamu zaiyi baki sosai,

Ta matse lips ta tashi ta goge jinin jikinta ta fita don dora ruwan zafi ,

Da fitar ta ta samu KHALEED goye da kaninshi harya dora ruwan kasancewar tukunyar karama har sun tafasa,

Ta tsaya kallonshi ya juyo yace"sannu mama"

Tai karamin murmushi tace"kaima sannunka"

Yayi shiru,

Tace"bani ruwan na mishi wanka idan Wadannan sun tafasa se ni kuma nayi kafin su huce"

Yace"to mama"

Ta amshi ruwan ta fita ya zuba wasu ya bita ya bata yaron ya matso da kayan bukata sannan yafara gyara wurin haihuwar,

Ta kalleshi zatai mishi mgna se kuma ta fasa tai shiru,

Kafin ta farga har ya gama gyara wurin ya kunna tsintsiyar kamshi ya dawo ya zauna ya zubawa yaron idanu yana jin mugun sonshi yana ganin yasamu dan'uwa kuma aboki ,

Ta kalleshi tai murmushi tace"sannu KHALEED da kai akayi labourn nan"

Yayi shiru yanata murmushi,

Ta fidda jaririn a ruwa tace"ka sako wasu akwai dauda jikin shi sosai"

Ya dauki robar ya fita ya dawo dasu yayi zaune yanata kallonta har ta gama mishi ta fara sa masa tufafi,

Ya tashi ya kai mata ruwanta toilet yana dawowa ya amshi jaririn ita kuma ta nufi toilet wanka,

KHALEED ya zubawa yaron idanu ,idanunshi tarr yanata kallonshi yana ganin matukar kamar da sukeyi da Abbanshi ya saki murmushi ya dauko ruwan zam_zam ya diga mai sannan ya fara masa huduba,

Yana gamawa ya fita dashi zuwa dakinshi yana rungume dashi,

Ta dade toilet sannan ta fito ta shigo dakin bakowa ciki,ta shirya kanta ta kwanta kan bed tana jin barci,

Ta dan jima kwance KHALEED yafara knocking kofar dakin,

A hankali tace"KHALEED shigo"

Ya bude kofar ya shiga yanata murmushi ,ta tashi zaune tana kallonshi da murmushi tace"nazata kunyi bacci"

Yana cikin tsananin farinciki yace"a,a na kawoshi ne"

Tace"kawoshi"ta karbeshi ta kalli jaririn ta kalleshi tace"kamishi huduba ne koko murna bata bari ba?"

Murmushi sosai a fuskarshi yace"na mishi"

Tai murmushin jindadi tace"inafatan ka zabar masa suna ?"

Ya daga kai yana annashuwa yace"WALEED"

Ta zubamai ido tana mashi kallon kauna da tarin farinciki.
[4/4, 10:33] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 15&16


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*



KHALEED ya sunkuyar da kanshi yana cikin farinciki cikin zuciyarshi yana jin inama mahaifinsu na raye da faricikin zaifi yawan haka,

Sosai take son KHALEED duk lokacin da ta kalleshi tana jin dadin samun shi a matsayin danta tana murmushi tace"Allah yarayamana WALEED yasa ya zamo jarumi sadauki tamkar yayan shi"

KHALEED yayi murmushin jindadi yace"Allah yabaki lpy mama,seda safe"ya juya ya fita yaja masu kofar,

Tana kallon kofar ta medo hankalinta wurin WALEED dake hannunta yana bacci wasu hawaye suka fara sintiri akan kumcinta ta rasa gane na farinciki ne ko tausayinsa a hankali ta fiddo nono yana baccin ta kanga masa ya farka ya kama yana sha ,hakan ya tuno mata lokacin KHALEED time da take cikin damuwar rashin lpyarsa yanzu kuwa tana cikin tausayinsu da kewar mahaifinsu,

Bayan yasha nonon ta mayar ta kwantar dashi ta kwanta gefen shi tana kallonshi cikin zuciyarta kuwa addua take ta mishi Allah yarayashi ya shirya shi shirin addinin islama,

Ana asubar farko KHALEED ya fito ya fara hada ruwan wanka da breakfast lokaci daya har akayi asuba sannan ya fita masallaci,

Bayan ya fita ne ta farka daga baccin daya dauketa ta nufi kitchen domin hada ruwan wanka Amma sai samu tayi bokiti rufe cike da ruwan ga wasu a sama da Lipton ciki ba shakka na shayi ne,

Wani murmushi ya subucemata tana jin son danta na karuwa a ranta a kowace dakika, a hankali tace"Allah ka mishi albarka ka bashi duk alkhairan rayuwa"tana kara yabawa danta ta dauki ruwan ta nufi toilet wanka,

KHALEED na dawowa yaji kukan yaro ya game gidan ya shiga dakin ya daukeshi lokaci daya WALEED yayi shiru ya fito da shi yana rungume dashi ,

Tana ta saurin ta fito a wankan taji shigowar KHALEED ta karasa wankan ta fito ta saka Kaya sannan ta kwalamishi kira ya shigo yanata faraa yace"mama ina kwana ya jiki ?"

Tana murmushi tace"naji sauki ya naka?"

Yayi murmushi yayi shiru

Tai dariya tace"to sannu Allah yayi maka albarka yabaka Wanda zasu kula da kai fin haka "

Ya fadi amin cikin ransa ya tashi ya fita ya koma kitchen don hada breakfast,

Itako ta fara yiwa WALEED wanka,

Bayan ya hada breakfast yayi saurin yin shara sannan yayi goge_goge da wanke_wanke ya koma bakin dakin yayi knocking,

Ta bashi izinin shiga yana shiga yace"mama zanje na fadawa Baban farouk da gidan kawu"

Tace"saika dawo Amma kayi kalaci ?"

Yace"eh"

Tace"toh seka dawo in kadawo har makwabta kafadamasu"

Yace"to"ya juya ya fita,

Gidan Baban farouk yafara zuwa domin yana yaba kokarinshi akan su suka gaisa da maman farouk ya fadamata haihuwar tana ta murna taje ta fadawa Baban farouk shima yana ta adduar Allah yaraya,

KHALEED ya tashi ya fita yabi gidajen dangi yafadamasu yafadawa makwabtan kamar yadda tace sannan ya koma gida,

Da shigar shi yafara jin surutun mutane ya rasa a ina sukaji haihuwar ya shiga dakin sai ganin dalibanta yayi ya gaidasu ya fita zuwa dakinshi ya kwanta don wani irin bacci yake idanunsa,

Maman farouk ma nagama abinda takeyi ta taho gidan tana murna aka cigaba da hidima ,

Kullum KHALEED shike hadamasu ruwan wanka shine aikin gidan kafin mutane suzo kafin ranar suna Baban farouk ya kawo ragunan suna da kayan sawa nata dana WALEED da kudade a sama ta amsa tana ta godiya ,

Ranar suna akasawa yaro suna WALEED kamar yadda KHALEED yasa masa yan kauye da yanuwan ibraheem wasu sunzo akasha shagalin suna aka tashi,

KHALEED ya kara azamar kula dasu inde ba nono ake ba WALEED ba kodayaushe yana hannunsa yana masa wasa, idan ana masa wanka kuwa zaunawa yake yayita kallo ashe koya yake don yana ganin hakan ma aikine gareta,

Watarana ta shiga wanka ya hada ruwan wankan WALEED ya kawo duk kayan bukata kusa yafara masa wankan,

WALEED yaji sabon wanka na yan koyo ya dage tsanyala kukan da yasa muneera ta kasa hakura harta fito a toilet din dasauri da daurin gaba jikinta duk ruwa,

Tana fitowa ta ganshi yana mishi wanka ta zaro ido ta rike gemu tai tsaye tana kallonsu tana dariya,

KHALEED ya dago ya dan kalleta sannan yace"wanka nake masa"

Tana murmushi tace "wannan fa aikin manyane KHALEED"

Yace "na iya mama kuma idan inayi zan kware"

Tana murmushi ta koma toilet WALEED nata kuka da KHALEED kejin yana dokar masa zuciya harya gama masa wankan ya samu yayi shiru sannan ya shafamasa mai yasa masa tufafi,

Haka suka cigaba da rayuwa lokaci zuwa lokaci Baban farouk na zuwa yayi sallama da KHALEED ya tambayi lpyarsu ya kuma kawomasu abubuwa.

A hankali kwanaki sukaita tafiya tafiyar KHALEED London nata matsowa ,

Tun saura sati tafiyar ya fara ramewa sai ya rungume WALEED yayita kallonshi yana tausaya masa wa zai kira baba?wazai kira danuwa?duk babu sai mahaifiyarshi kadai,ji yake kamar ya fasa tafiyar amma bazata fasu ba saboda yanason ya zama wani abu a rayuwa don jindadin mahaifiyarshi da kaninshi,

Saura kwana biyu ya tafi yaje sallar laasar ya dawo ya samu muneera na hawaye tanajin motsinshi tafara gogesu dasauri,

Yazo ya zauna kusa daita cikin sanyin murya yace "mama kiyi hakuri kamar gobe zakiga nagama karatun insha Allah"

Idanunta jawur tace"Kaine duk wani farincikina KHALEED tafiyarka ta kwana daya ma bazanso ba"

Idanun KHALEED cike da hawaye yace "mama ga WALEED kusa dake zai debemiki duk wata kewa"

Tai murmushi mai ciwo ta jinjina kai don bata jin WALEED a rai kamarshi,yana cigaba da rarrashinta ya tashi ya tafi daki, ya zauna yasha nashi kukan domin dauriya yake ,

Ranar da zai tafi muneera ta rungumeshi tana kuka yana yi saida yaga lokaci zai kure sannan ya dauki jikkarshi ya fita suka tafi airport da Baban farouk,

Tana ta daga masa hannu ta koma cikin gida ta zauna tana matukar kewar KHALEED dinta ,

Bayan tafiyarshi ta cigaba da rayuwa ita kadai daga ita sai WALEED gidan badadi kokadan,

Tun mutuwar ibraheem Baban farouk na bakin kokarinsa wurin kula dasu majority idan yazo gidan yana samun KHALEED seya bashi sako yanzu gidan bakowane namiji ciki tana bukatar Karin kulawa da temako,

Shiyasa duk bayan kwana biyu bayan ishai idan zai wuce gida saiya sai masu abun motsa baki ya shiga yayi sallama ta fito da hijab ta amsa ya kuma tambayi in suna bukatar wani abu idan akwai tafadamai idan babu shikenan iyakarshi cikin gate baya wucenan wani lokaci yakanzo ya tafi amma bata ko kula da wane irin Kayane jikinsa,

Sosai take jindadin kulawar da yake yi dasu domin yafi duk yanuwan ibraheem da yanzu sai a kwashi lokaci bataga kowa ba,

Su kuwa mutane akwaisu da saido da zargi da shiga abinda babu ruwansu,wannan shiga da ficcen da Baban farouk keyi saiya zama surutu wasu na ganin yana zuwane ya biya bukatarshi yayi tafiyarshi duk da rashin dadewar da yake bai hanasu zargin wani abu ba ,muneera batasani ba tana cikin gida abinta amma labari nata yawo,

Bayan watanni ana wani suna da marece maman farouk ta shirya taje tana zuwa ta hadu da wata kawarta yaruwarta kuma makwabciyar muneera,

Bayan sungaisa sunata labari maman farouk tace"kwana biyu kindena kawomin ziyara meyasa?ko bakiso ku hadu da Baban yara?"

Matar tai banzar dariya dama tuni takeso ta fada mata gulmar tace"wane Baban farouk kuma? da kusan kullum yana unguwarmu ai ina ganinsa"

Maman farouk ta kureta da ido zuciyarta na waswasi tace"bangane ba?"

Matar ta gyara zama tace"ai tuntuni nakeso muyi maganar sede nayi shiru ban jeba hausawa sukace abinda babu ruwanka dadin kallo ne dashi"

Maman farouk tace"dan Allah fadamin meke faruwa?"

Matar ta tabe baki tace"kina gida zaune shi kuwa yana faman yawon bin zawara in baki labari kusan kullum sai yazo wurin muneera, yana dauke da ledoji ya bude gate ya shige sai an jima ki ganshi ya fito dasauri ya shiga mota "

Zuciyar maman farouk tafara up and down kishi na taso mata fuskarta daure tamau kamar bata taba murmushi ba,

Wata zuciyar taso karyatawa tana hango fuskar muneera da halayyar mijinta,

Kawartan na ganin haka tace"to meyake zuwayi ?abinda daure kai lokacin da KHALEED na nan ai baya zuwa kullum kuma iyakarshi kofar gida amma yanzu da yake daga ita sai jariri ai kila har uwar daka..."

Tun kafin ta karasa maman farouk ta dauketa da gigitaccen marin da yasata zabura,

jikinta na rawa sosai da alamu tana da zafin kishi sosai ,bata kara mgna ba ranta na suya ta jawo gyalenta ta yafa tai waje ,

Dasauri ta tsaida mashin ta haye tai masa kwatancen inda zata,har kagara tayi ta kai tanata ayyana rashin mutuncin da zata yiwa muneera,

Mashin bai tsaya ba sai kofar gidan muneera ta sauka ta nufi ciki dasauri tana fadin"dan jirani na fito"

Mai mashin yaja ya tsaya domin dole ya jira kudinsa,

Ita kuwa ta shiga ciki da karfi tafara kwalawa muneera kira,

Muneera ta fito cikin kwalliyarta doguwar riga ta atamfa da WALEED dinta dauke a hannu tana ganin maman farouk ce takara yawan faraarta tace"maraba da Hjy,maman farouk ki zauna bari na kawo miki ruwa"

Maman farouk na binta da kaskantaccen kallo ranta na zafi ganinta kwas kamar ba me shekaru arbain ba tana jin mugun kishi har muneera ta juya a tsawace tace "ba ruwa yakawoni ba zuwa nayi nai miki kashedi bake ba mijina ,ki fita harkar shi mijina nawa ne ni kadai wlh idan kika kuskura kika cigaba da kulashi bani ba farouk zansa yazo ya koyamiki hankali"

Muneera har wata juwwa ke daukarta tsabar firgici ta juyo idanunta jawur tafara kallonta itace dai Matar da idan ta sameta cikin damuwa take kwantar mata da hankali, itace dai Matar da ta dauka kamar yar'uwa tana iya fadamata kowace matsala don ta bata shawara shekaru kusan talatin suna tare, amma kashhh,, yau gashi itace ke fadamata bakaken kalamai itace ke tunanin tana cin amanarta ko kuma tana son aure mijinta,

Batasan lokacin da hawayen bakin ciki suka zubomata ba ta matse lips tana sheshsheka tace"maman farouk meke faruwa haka?"

A zafafe tace"bansani ba Algunguma nadai fadamiki kidena kula mijina munafukar banza munafukar wofi butulu"

Muneera ta karasa fashewa da kuka tana kallonta hawaye kamar famfo suna kwaranya akan fuskarta,

tace"nazata ko wani yafada miki wani abu game dani zaki karyata hakan wallahi ba wani abu tsakanina da Baban farouk"

Maman farouk taja dogon tsoki ta girgizakai cike da zafin kishi tace"shi dan kauye ko shekara nawa yayi a birni sai kagane masa wannan abun da kike ya kara tabbatar da baki da gaskiya ,kiji tsoron Allah ki kama kanki kisani duk lokacin da laifinki ya fito fili hukuncinki shine jifa"tana gama fada ta juya ta fita dasauri tana cigaba da huci don ji take kamar ta karairayata taga dame zata ja hankalin wani namijin,

Muneera ta zauna ragwaf a kan kujera tana kuka tana memeta zina a ranta"Zina!!! Ni muneera?? Ya Allah kana gani"ta cigaba da kukan bakin ciki,

Maman farouk ta koma gida rikice tafara kiran Baban farouk baiko samu damar dauka ba har zuwa dare ya biya kaiwa su muneera naman gasassar kazar daya siyo ya musu nasu ledar ya shiga yanata sallama shiru ,

Muneera naji ta kyaleshi tana jin dama zata iya fadamai basa bukatar komi wurinshi domin yadena zuwa kar abun yayi waste,hakanan badon ta so ba ta fita muryarta shake tace"ina wuni?"

Yace "lpy lau ....lpy lau nayi zaton bakunan ina niyyar tafiya ,ga wannan, ko akwai wani abun da kuke bukata?"

Da muryarta da tasha kuka takoshi tace"babu"

Yace"to madallah agaida WALEED sai da safe "ya juya ya fita dasauri,

Tausayinshi ya kamata mutumin da baiyin good 5minutes a gidan ya fita amma har ake zargi? Ta girgizakai ta koma cikin gida,

Shi kuwa yana shiga gida yawuce yara a falo yayi ciki tana zaune tana banka mai harara ta tashi
ta bishi,

Yana cikin cire kayanshi ta shigo tana huci da jin haushinsa tace" kadawo daga wurin karuwar taka? "

Yayi tsaye yana binta da wani kallo "karuwa?" Ya memeta a zuci yana kallonta kamar marar hankali,

Yana yamutsa fuska yace"karuwa kike fada maman farouk? "

Tace"eh karuwar meye maraba mace da mutuwar miji seki fara bin wasu? koda yake ba laifinta bane Wanda ke bibiyar Matar abokinsa shine yafi laifi"

Wani irin zabura yayi ya fiddo ido waje yace"Whattt!!!!!"

Ya dago hannunsa a fusace ji kake tasss!!! Ya dauketa da mari,

Ta dafe kumcinta idanunta jawur amma Sam ba digon hawaye cikinsu,

Jikinshi na rawa yace"da gani kin fara hauka kiyi gaggawar dawowa hayyacin ki"

Tace"kwarai tunda kasamu wata dole ka kirani mahaukaciya duk shekarunnan bakasan banda hankali ba sai yau to tafiyata zanyi sai kaje ka karata da karuwar taka"

Ya cije lips jijiyoyinshi waje ta wani juya da karfi ta bar dakin ta nufi nata don daukar mayafi,

Baban farouk ya zubawa kofar idanu zuciyarshi nafadamai su mata idan kishinsu ya taso basu da hankali ma bare ace suyi amfani da tunani ba shakka wasu zasu kawomata labarin ita kuma saita dauka ? Ya fara tunanin muryar muneera anya ba kuka tayi ba ?zuciyarshi na zafi ya fita a dakin ya nufi nata.
[4/4, 10:33] Shalele: *SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special


Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*

*Wattpad@mumies122*


*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*


*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*

*Small gift to my real fans*


*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


Page > 17&18


*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*




Yana gaf shiga ta fito a fusace yafe da gyale ta nufi falo ,

Yana tsaidata taki sauraren shi tana tafiya yana biye daita har falo inda yaran su ke kallo,

Ganin halin da suke ciki yasa khaleefa yasha gabanta cikin magiya yace"mama dan Allah karki tafi "

Sauran yaran suka tashi suka bar falon yar babbar diyarta na zaune tana kallo duk da batasan me yafaru ba amma gani takeyi ya zalunci mahaifiyarta ne domin bata tabayin hakan ba,

Baban farouk na bayansu tsaye abun ya girgizashi matuka, yaji?abinda batayi lokacin yarinta ba shine zata yi yanzu?

Ranta bace tace"bani wuri in wuce don ubanka"

Khaleefa ya langwabe kai yace"mama don Allah kiyi hakuri Ku sasanta basai wani yaji komiye ba"

Ta daga hannu zata kai mishi mari a tsawace Baban farouk ya katseta yace"khaleefa bata wuri ta tafi duk inda zata"

Khaleefa ya meda hankalinsa wurin shi,

ya daga masa kai yace"bata hanya"

Ba don yaso ba ya matsa tana niyyar fita farouk ya shigo gidan ya girma sosai har yayi aure da yara, yatsaya kallon su daya bayan daya kafin yace"mama lafiya ina zakije da dare haka?"

Ranta bace tace"bansani ba matsamin hanya"

Cikin sanyin murya yace"mama bazan bari ki fita ko ina ba kiyi hakuri"

Ta tsaya tana mai wani kallo me cike da bacin rai,

Farouk bai damu ba ya kalli kanwar shi yace"ke shiga ciki"ta tashi ta wuce tana turo baki,

Ya kalli mahaifiyar shin cikin ladabi yace"mama don Allah ki zauna"

Taki tana jin mugun takaicin su tana ganin don basu san me ke faruwa ba,

Ganin dai bazata zauna ba yasa Baban farouk cewa "kabarta taje ta zubarmin da mutunci zata dawo tana nadama nan gaba kadan,inba shirme ba ta yaya har zaa kawo mata wata magana kaina ta yadda?kuma ki rasa wacce zaki zargeni da ita sai muneera?wacce inba ta dalilin amintaka ba ba abinda zaisani zuwa wurin ta ,to ki tafi duk inda zaki je kuma wlh idan har kika fita bazanje dawo dake ba sede diyanki su medoki"

Farouk ya cije lips dinsa zuciyarshi na zafi yama zaai tayi wannan tunanin? ya kalleta a hankali yaja hannunta jikinta duk ya mutu jin cewar shi sai de diyanta su dawo da ita ,

Farouk ya zaunar daita ya zauna gefe cikin sanyin murya yace"mama idan har wani yafadamiki haka to ba gaskiya bane idan kuma ke kikayi tunanin hakan badede bane ,kullum kina yabon baba yau daya ki sauya haba mama"

Ta dafe kanta tai shiru maganganun kawarta suna dawo mata zuciyarta na zafi ta dago tace"don me zai rika zuwa gidanta da dare? bayan yasan bakowa gidan kuma shi ba muharraminta bane idan wani abu zai bata meyasa bazaya rika aiken khaleefa kowani cikin ku ba? Koma miye ai an de ganshi yana zuwa gunta"

Baban farouk ya yamutsa fuska ya girgizakai yace"ba wani abu makamancin haka a zuciyata tunda hakane daga yanzu zan rika Aiken su khaleefan shikenan Allah ya kyauta"ya juya ya koma ciki,

Khaleefa da Farouk na zaune sunajin bakin ciki suka ce"mama don Allah kidena yarda da maganar kowa mutane ba abun yarda bane"

Tai tsoki ta tashi tabar su ta shige dakinta koma de yane tade yi maganin matsalar idan har bai dena zuwa ba zata sani,

Sosai Baban farouk yayi fushi daita yabar ko amsa gaisuwar ta ya kuma rika bawa khaleefa na kaiwa muneera sako Wanda hakan ya matukar kwantar wa muneera hankali ,

Maman farouk kuwa ganin dai itace bata da gaskiya yasa ta sauko taita rarrashin shi harya sauko suka cigaba da rayuwa amma muneera bata kara nufo gidan ba duk da dama ba zuwa take ba saboda school ita kuma maman farouk kunya tasa bataje ba sai bayan lokaci sannan suka fara ziyartar juna amma mutuncin ba kamar da can ba,

Haka rayuwar ta cigaba da tafiya daga school sai gida a wurin muneera da kudin albashin ta da wanda baban farouk yabada take masu cefane da hidima bata taba kudin su na gado,

Idan ta dawo gida bata komi se yiwa WALEED wasa bai cika dariya ba don yayi gadon abbansa sai jefi_jefi yakeyi hakan baisa tadena ba sosai take koyamai fadin *Daddy* aganinta shine sunan da yafi cancantar ya

Please Login or Register in order to submit comment