Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naje na daukota"

Muneera tace "aa.. ina zakaje kasan jikinka kar wani abun ya sameka ka bari yanzu zata dawo"

Ya kalleta yace"Mama ba matsala"ya koma ciki dasauri ya fito da coat ya nufi kofa dasaurinsa ,

Muneera na jin tsoro tace"KHALEED....!!"bai jira ba ya fita dasauri ya bude gate ya shiga motar ya fita,

Baiyi nisa ba ya hango Zarah na tafiya dasauri cikin ruwa sunata dukan jikinta jikkarta rungume cikin hijab tanata makyarkyata,

Ya karasa yayi parking saitin ta,

Zarah ta kara sauri ganin mota gabanta tana tsoron a saceta, ya bude motar ya fito cikin muryarshi medadi ya kirata"Zarah !!! shigo mu tafi gida"

Ta kara bude idanunta dake cike da ruwa taga dagaske shine ,

Ta nufi motar ya koma ciki ya bude mata ta shiga ya mika hannu ya rufo kofar ya tada motar ya nufi gida,

Zarah na kankame da jikinta tana makyarkyata tasa hannu tana matse idanunta, ya kalleta ya bude loka ya jawo sabon karamin tawul ya mika mata ta kalleshi ta amsa ta fara gogge fuskarta dashi zuciyarta na yaba tausayawarsa akanta,

Baifi four minutes ba suka shigo gida Muneera na bakin kofa hankalinta a tashe kar wani ciwo ya samu KHALEED,Zarah ta bude kofa ta shigo jikinta jagab,

Dedenan WALEED ya fito daga dakinsu bayan yayi Maghreb ya tsaya yana kallonta yanajin tausayinta ganinta sharkaff ,

Muneera tace"Zarah yau kunsha kashin ruwa ki sauri kishiga ki sauya kaya bani jikkar mugani"

Ta mika mata jikkar ta nufi daki,KHALEED ya shigo dasauri ya tsaya yana zare rigar jikinsa,

Muneera ta kalleshi tace"Sannu KHALEED saida dai ka fita"

Yayi murmushi yace "Mama ba kowa a titin sai ita ruwa na dukanta tanata kyarma ya kamata abata paracetamol tunda wuri"

WALEED ya tabe bakinsa yana jin kishi a zuciyarsa yadda Zarah ta wuce kayan sun manne a jikinta kome waje kuma KHALEED ya ganta harma yana fadin jikinta na rawa abun ya bata masa rai sosai,

Ya kalleshi ya zauna kan kujera ya fiddo wayarsa yana latsawa duk da de hankalinsa baya gunta ,

Su kuwa suka shiga don yin salla ,

Suna gama salla muneera tabawa Zarah PCM sannan suka wuce kitchen tana dan kama mata sukai boiling tuwo da miya ,

Suka dawo sukai ishai sannan suka fito falo dukkansu muneera ta zuba musu nasu KHALEED tare suka faraci tasa nata itada zarah tasa hannu tana ci kanta kasa,

Suna gama cin abinci WALEED ya kunna inji suka zauna fira ,

WALEED yaji duk baya jindadin zaman ya tashi ya nufi ciki,

Zarah ta kalleshi tana kara hango bambancinsa da KHALEED ta koina baya da sakin fuska ko tausayi KHALEED ya fishi,

Muneera tace"KHALEED akwai maganar da nakeso muyi amma gwara na bari a kwana biyu ka huta tukun"

Yace "Mama ko yanzu lafiya lau bawata gajiya jikina inajin ma jibi zanje kai takaddun nawa, ba kamar tunanin danayi baya ba sai bayan week"

Zarah ta tashi ta nufi daki jin d'a da Uwa zasuyi sirri ,

Muneera tabi bayanta da kallo tana jin tausayinta tace"Baka tambayi meyasa ba a meda yarinyar nan wurin iyayenta ba "

Yayi murmushi yace "Eh nasan zaki fadamin ko ba yauba inata mamaki idan na kira naji kina magana daita meyasa baku kaita gidansu ba?"

Muneera ta girgizakai tace"Zarah abun tausayice ta rasa iyayenta saboda suna son kare mutuncinta "ta kwashe komi tafada mai,

Idanunshi sukai jawur saboda tausayin Zarah ,Zuciyarshi tana zafi,

Muneera tace" Shiyasa na riketa har ka dawo in komai yayi dai_dai semu je garin nasu mu samu megarin da yanuwanta muyi magana inaso kayi bakin kokarinka kaga ka wanke iyayenta daga zargi barawon shanun nan na konamin zuciya"

Zuciyar shi na zafi yace"Insha Allah mama ai Dole hukuma ta daure azzalumin da ya iya aikata haka baya da imani ko kadan"

Muneera tace"har tsoro nake karta koma can wani abun ya kuma faruwa ,inajin tausayinta inajinta kamar diyata jinake dama ta cigaba da rayuwa tare damu"

Ya kalli Muneera cikin sanyin murya yace"ba abinda zai faru mama zan kula da komi "

Tai shiru ta shiga tunani tana jin inama Zarah zata cigaba da rayuwa acikinsu tanajin sonta sosai bata da hayaniya kuma me ladabi ce da biyayya,

KHALEED kuma yana tunanin rayuwar Zarah a kauyen ba boko ba islamiya rayuwarta bazatai dadi haka ba, yanason ilimi zamanshi a turai ya fahimci wasu abubuwa da dama yana jin inama Zarah tai karatu,

Suna shiru na kusan minti ashirin ya tashi yace"sai da safe kema kishiga ki kwanta"

Ta daga masa kai ya juya ya nufi daki jikinsa sanyaye,

Yana shiga ciki ya samu WALEED zaune jingine da gado fuskarshi daure ya tsunduma cikin tunani yana ganin bazai iya barin Zarah ba ya tafi wata Uwa duniya har wani ya rigashi gwara ta zama tashi sannan,

Ya tsaya ya karanceshi na mintoci ranshi badadi ya nufeshi kokadan bayason ganin damuwar WALEED sai yaji kamar ya gaza wani wuri ,yana tuno maganar daddynsa da yake cewa ko baya raye yasan bazai bari su shiga damuwa ba,

Ya karasa ya hau gadon ya zauna gab dashi ya shafi sumarshi ya dago kanshi yace"My son menene?"

WALEED ya kalleshi ya matse lips dinsa ya turo baki ,

KHALEED yayi karamin murmushi yace" fadamin kome ke damunka danuwana banason ganinka cikin irin wannan yanayin"

WALEED ya kalleshi yace "zakamin ko miye ?"

Ya daga masa kai yana kallon kwayar idanunshi,

WALEED yayi shiru na dan lokaci sannan a hankali yace"Daddy I'm.. I'm.. in love"

Gaban KHALEED ya fadi ya kureshi da ido yana kallonshi maganar tazo masa a bazata kokadan baiyi tunani ba yana cikin mamaki yarasa me zaice masa,

WALEED ya sunkuyar da kai yace"daddy inasonta sosai idan na ganta da wani raina na zafi banaso na tafi na barta ai mata aure I want to marry her....."

A tsawace KHALEED yace"shut up "fuskarshi daure ranshi a matukar bace,

Ranshi bace yace" How old are u ?"

WALEED yayi shiru idanunshi jawur zuciyarshi na zafi,

KHALEED yace"I'm asking u how old are u?????!!!!"

WALEED ya....

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment