Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai normal kana suka dawo,mutane sai zuwa barka suke da ganin yara masu kama da ubansu akuma haihuwarne hajiya kari da Anty mariya suka zo harda kwamishina da kayan arziki iri Sunkoma washegari sai ga Anty laila itama harda amaryan da'a mata sunzo barka suna da abun arzikinsu hakika safwan da su hajiya sunji dadi sunkuma yarda yanzu za'ayi zumunchi mai tsafta sakina kuwa Allah kadai zai biyata domin tadaukema su momma hidima ita ke komai na gidan ga dawainiyar mai jagejage Safeena tayi alkwari yadda Sakina take kokarin farantamata ita sai ta faranta mata shikanshi Safwan tun bai sakin jiki da ita har yafara domin alkhairan Sakina yadakushe sharrinta na baya,shikuwa Adil kuka yake dayaga Safeena da dauki yaran sai yahau kuka wai a ijiyesu adaukesa sai Safeena ta mika sakina su tajawoshi ta rumgume tace ya'yanta gaka ma nabata abunta akai kadaine dana ko"sai yahau murna yace"Mami ai ya'yan Ummi ne ko ta gyadamai kai shikuma yana dariya.

Sai ana gobe suna suka samu damar komawa sabon gidansu tareda rakiyar yan"uwa da abokan arziki ciki harda Aisha kawar Safeena da inna husai harda maman Aisha da matan kawu isuhu momma da hajiya sun rakasu suma komai yaji baanda tsiya kowa yaga gidan sai dai kaji ya furta masha Allahu dare nayi su momma suka koma gida su koma akabarsu nan da masu shagalin suna.

Su suka zauna akasa mai dauke da falo guda biyu da manyan dakuna guda hudu kowanne yana dauke da falo da toilet sakina ta dau daya safeena ta dau dayan sauran biyun kuma daya aka barma baki dayan kuma ba'a budesu ba


Commet
Share
Vote




*Shakira...*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_๐Ÿ’ž



*DEDICATED TO:My Mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are*




*37*


"Hakika taro yayi taro domin yan'uwa da abokan arzuka sun hallata bbu laifi Safwan yabaza bajintarsa awannan haihuwar domin sa guda yagada bayan ragunan da'aikata yankawa abun sai wanda yagani.Safeena shiga kawai take tana cirewa domin akwatu guda Safwan yayimata na fitan suna ita da babies sakina ma kala biyar yamata itama na fitar Sunan,baki sunzo tako ina har hajiya kari sai tazo itada Anty mariya wanda suka zo da abun arzikinsu niki niki kafin su wuce gidansu momma don suma achan suke nasu taron.



odar abinci kuwa Restaurant uku suka zo domin bawa jama"a abincin da sukeso,aikuwa anci ansha harda masu guziri baki tako'ina sunzo ciki harda Yan Janaf fans,Hibbatullah fans,yarima suhail fans1&2 da Na tafka kuskure fans,da yan kungiyata Interlligent writers suma sunzo wannan wurin my Anty sis Naja'atu anci harda guziri ajaka my leema ma har ariga su Sahiba kuwa anci kamar za"ayi amai bai isheta ba leda guda tasamu tana guziri,Anty sainah,Anty hafsat,mummy zil,maman kausar,kuwa bayan angama nadan na gidan Dr ai suna ganin mota zata koma gidan Hajiya mama suka shige suna Fadin bari suje suga kuma wata wainar ake soyawa achan kuma....Oh ni jami,Yan sch dinsu wato yan faculty su sunmata kara domin kwansu da karkwatansu su hallarta.





Anrarraba abubuwa irinsu Robobi botikai dinnerset kofuna da jakukkuna masu dauke da hotunan yaran wa"inda sukaci Sunan Hajiya mama da mijinta wato MARYAM SAFWAN SALE DA ABUBAKAR SAFWAN SALE...Hakika Safwan ya farantama Hajiyamama rai wanda farincikinta yaki boyuwa kwatakwata harda kwallanta saboda murna.




Sakina itace kan komai domin tazage ana hidima da ita Anty laila tazo suna ita da amaryanta itama suna zaman lpy abunsu basu kwana ba suka koma Sakina tasani cewa ta tafka kuskure tun abaya domin fadar data ke dashi ada ayanzu banata bane domin safina tarigaya data kamkame ko"ina Dr baya ganin kowa agabansa sai Safeena itadai kawai yana rakatane...Wani lokacin in abun yadameta sai dai tashige daki taita kuka ita kadai gashi kwanakin nan tana ta zubar jini tun abun nazuwa kadan har yafara yawa ada tazata period ne ammh daga baya tasan abun ya wuce haka.





Anyi suna lpy an tashi lpy bakin Safana da na zurmi hardama na zamfara sunkoma gidajensu Aisha ce kadai bata wuce ba wai Saita kara kwana biyu...dariya kawai Safeena ta mata kan ta ce"munafuka wlh nasan meya tsaidake"Sakina ce tace"Ai Tahir wlh sai ya gundireki ne"Aisha tace"Daman masoyi na gudinran masoyinshi ne"Dariya suka mata gabadaya.Tabbas soyayyah mai zafi ta kulli tsakanin Dr Tahir da Aisha wanda suka sha tsiya gun Safeena da Sakina yan tagwayen Dr.




Inna zulai kanwatake ga Mallam Aliyu ita akabarma Safeena tana kula da ita Sakina ma ba'a barta abaya ba tana iya bakin kokarinta wurin taimakawa domin in Safeena tatafi mkranta ita da inna zulai suke wahala da yaran....Su momma kuwa kullum kwanan duniya in Safwan zai fita aiki sai ya biya haka kuma inyadawo su Safeena kuwa indai basu dawani abu da zasuyi to haka zasu saka yayan amota su kaima su momma wanda Hajiya mama tahana achanza musu suna ana kiransu da Hajiya da Justice.






Babu wanda yataba lura da halin Da Sakina ke ciki sai Ranar da Safe weekend ne Safwan yana Dakin Sakina yana kwance tundazu tashiga bayi ammh yajita shuru tashi yayi tsam ya bita abunda yaganine yasa shi daskasrewa sakina ke tsungunne cikin bath jini yana zuba guda guda Da Sauri Safwan yace"Sakina....Meye haka kuma jini nagani"Kallonsa tayi idanunta sunkawo kwallah tace"Bansani ba Dr bansani ba wlh"Tafada tana bayyanan da Rauninta kallonta yayi kan yace"Tun yaushe kika fara bleeding din"Sanda kai tayi tace"Bansani ba ammh tun haihuwar Safeena ne".....What...Kina haukane Sakina ace kina zubar jini almost 4weeks ammh kika kasa mgana what wrong wit u ne"Yafada ahasale sakina ta fashe da kuka tace"kayi hakuri naji tsorone..."Juyawa yayi yana Fadin"Ki shirya muje asibiti kawai malama"Yafada yana wucewa sulalewa tayi tana zubar kwallah domin ta tsorata daganin yanayin da Dr ya shiga.




Shiko dakin Safeena ya shiga yake Fadamata salati ta saka har inna zulai taji ta fito shine Safeena take Fadamata ita fadan ta hau Sakina dashi tana cewa"Haba Sakeena wannan ai sakarcine kina ganin halin dakike ciki ammh ki kasa mgana keda kike da likita agida....Haba don Allah karki kara Sakarcin nan"Gyada kai kawai tayi tana hawaye har bakin mota suka rakasu suna daga musu hannu.





Achan hosp.kuwa ba shi kadai ba harda sauran likitochin asibitin suka dukufa kan sakina domin gano meke damunta Safwan tsurama abunda ya bayyana jikin yar"Na'urar datake haskomasa cikin Sakina zuface ta yankomasa siririn gilashinsa ya cire yana share zufa kallon sakina yayi wacce ta zuba mashi ido cikin rashin hayyaci kada kai kawai yayi ya fice shima Tahir binsa yayi da sassarfa Runtse ido Sakina tayi aranta tana ayyana Abubuwa dadama.














commet
And
Share
Vote



*Shakira..*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_๐Ÿ’ž


*DEDICATED TO:My mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are*


*38*




Yana shiga Office dinshi Tahir shima ya shiga yana Fadin"Dr Safana wai Sakina wata irin macece...Ace kidinga ma kanki illar ammh kebaki sani ba kina haukar banza


"Yafada yana kallon Safwan dayake kokarin bude karamin fridge din dake kafe a office din ruwan yadauko ya bude ya kafa kai sai daya sha fin rabi kafin ya dire ajiyar zuciya ya sauke kan ya zauna yana cewa"I do'nt know Tahir....Sakina tagama illata kanta tana ganin kamar ni tamawa ko..?Yafada idanunsa sunkawo ruwa Dr Tahir yace"Wlh bakai tamawa ba kanta tama domin awannan stage din da mahaifarta takai masalaha shine fiddata kawai..."Zuru Safwan ya mishi kan yace"A'a Tahir bbu wata dabara da za"ayi sakina fa danta dayane aduniyan nan kuma sai aciremata mahaifa"yafada da jaddadawa Dr Tahir ya gyara tsayuwa yana cewa"Kafini sanin illar cancer mahaifa Dr S S kuma kaganin ma idonka har ta kumbura saboda bayan tasa an mata juyin mahaifa ta cigaba da shan pills cikin rashin akida wannan shiyasa basa zuwa cikin mahaifan sai suka dinga taruwa guri daya suna mata illah shi ya haifarmata da zubar jini mai yawa...Barinshi zuwa wani lokaci Dr zata Fashe ne da kanta kuma in ta fashe am srry to...."Iz ok a shirya mata operation"Dr Safwan ya katsesa cikin rauni kafin yafice daga office din binsa da kallo Tahir yayi kan ya girgiza kai yabi bayansa.





Safwan dakin da Sakina take yakoma tana ganinsa ta mike tana Fadin"Safwan...Meke damuna ne..?Kallonta yayi kai tsaye yace"Abunda kika kullama kanki ne kina ganin nikika mawa to dayake kinsan Allah ba azzalumin bawan sa bane sai abun yakoma kanki"yafada muryansa na rawa cikin rudewa Sakina ta dirko daga gadon datake tana Fadin"Na shiga uku ni Sakina ashe har yanzu bangama kwasan KUSKUREN DANA TAFKA BA"Safwan ya juya baya yana Fadin"Wannan shine kuskuren dazaki Tafka na karshe Sakina domin Yau din za"ayi miki aiki a fidda mahaifarki"Mahaifata....Tafada da karfi kan tasha gaban Dr tana Fadi cikin kuka"Safwan...mahaifata to meyasamu mahaifan Tawa"Shima kallonta yayi kan yace"Bayan kin Haifi Adil kin kara komawa an rufe miki bakin mahaifa ko..?"yafada still idanunsa na kanta sunkuyar dakai tayi tana hawaye tace"eh...Yace kuma bayan nan kin cika gaba da shan pills ko"nan ma tadaga kai wucewa yayi zai fita kana yace"Abunda kika aikata shiya jawo mahaifarki ta kumbura har kikafara zubar jini nan da wani lokaci in aka barta zata fashe ne gabadaya kuma ke zaki rasa ranki...Yadan dakata kafin yace"Kizama cikin shiri karfe biyar za"ayi aiki.Yana gabama fadar haka yafita sulalewa Sakina tayi tana kuka harda kara wani tashin hankali wanda ba'a samasa suna tashiga kuka take harda majina na nadamar abunda ta aikata domin ayanzu itace ta kashe kanta bawani ba.




Shiko Safwan kai tsaye gidansu momma ya nufa yaje yafada musu sallallami kawai suketayi Hajiya mama harda kwallanta na tsausayama Sakina nan da nan ta shirya tace ya kai ta Asibitin taje ta zauna da ita domin awannan halin tana bukatar wani kusa da ita Haka Safeena dataji lbr sai da takusa faduwa imani da tsoron Allah suka shigeta lokaci daya gabadayansu suka dumguma zuwa asibitin koda suka je sun Sami sakina ba yarda take tasha kuka Da Gudu Safeena ta isa ta rumgumeta tana kuka sakina fadi take"Abunda na shukane nake girba Safeena kidaina min kuka ni najama kaina"Hajiya mama da momma ne ke ta bata baki da inna zulai shiyasa tayi shuru duk mai imani yaga Sakina sai ya tsausayamata na halin data ciki,safwan kuwa kasa zama yayi saboda yama rasa wani yanayi yake ciki.




Koda biyar din tayi angama kowani shirye shirye hatta kayan tiyatan asanyamata Dr Safwan da Dr Tahir sai Dr Sainah sune zasuyi aikin suma sun kammallah komai lokacin da'aka gungurota za'a shiga da ita ne ta rike Hannu Safeena tana hawaye tace"Hakika duk wanda yaki godema ni'imar Allah to zai godema akasin haka Safeena koda ban tashi ba banda haufi akanki dama Adil danki ne na har Abada ammh don Allah inaso ko bayan Raina kada kibashi lbrin mugun halina saboda kada ya tsaneni"Kuka ya kwacemata Adil dinma shima kuka yake duk bai fahimtar meke faruwa ammh yasan cewa bbu lpy.




Safeena tayi saurin sakamata little Hajiya mama da justice akan jikinta tana kwallah tace"Wlh har Abada sune yayanki Anty nabaki su halas malak...zaki tashi kuma ki renisu da hannuki ni Safeena Uwar Adil ce kadai"Mirmishi da kuka atare suka kama Sakina ta rumgumesu tana Fadin"Da gaske safeena kin bani su 'Tagyada mata kai kawai sai Sakina ta fara dariya tana hawaye tarike hannun safeena kam tana mata godiya kowa awurin saida ya zubar da kwallah tsausayi momma da hajiya suka amshi ya"yan suna Fadin"muma mun yaba da wannan kyauta ya"yan kam na Sakina ne"Dr na gefe baice komai domin shikanshi yana cikin wani yanayi ahaka aka shiga da sakina tana kuka suna kuka.





Shudewar awa hudu kana aka fito da ita lokacin Safeena takoma gida tayo musu abinci koda aka fito da ita kamar matatta aka kaita dakin na mussaman wanda daman don iyalan Dr akayishi Dr Tahir ne yafada masu Hajiya kan su kwantar da Hankalinsu komai ya tafi Normal sunyi hamdala da godiya Ga Allah shikuwa Dr Safwan ko adakin tiyatan bawani abu ya tsinana ba saboda rashin kuzari ace wai yau shine ya jagoranci fidda mahaifan matarsa uwar dansa kai Abun da ciwo wlh.



Sakina Sai washegari ta farfado kuma Alhamdullilah bawata mtsala sai asannan Dr ya kira kwamishina yake Fada masa abunda ke Faruwa aranar kuwa suka iso hajiya kari sai da tayi kuka tana rokon Sakina tayafemata domin harda da ita adorata hanyar datafada to meza"ayi aikin gama ya riga da ya gama komai ya kare Safeena kuwa godiyar tasha babu adadi domin samunta cikin mata sai antona sai washegari Anty laila tazo itama dai Hakurin taita badawa domin itace ummul aba"isin komai.



Sai da Sakina ta shafe Sati kana takoma gida tana cigaba da Shan mgani ya"yanta kuwa in kun gansu gun safeena to nono zata basu suna nan gun Sakina tana lailayansu Tuni inna zulai takoma da sha taran arzikinta daga Safwan da damginsa Allah Sarki Ummi da Abbah sai da suka zo duba Sakina kuma sun yabama diyarsu bisa kyautar yaran data bawa Sakina wacce tazama abun tsausayi,shikanshi Dr yanzu sakina takoma tana bashi tsausayi matuka daman Rayuwar kenan kabi komai Sannu shine daidai.





Satin Sakina uku dadawo wa asibiti Dr yazo musu da wani lbri mai Dadi wani babban Asibiti dake Portugal sun gayyacesa aiki dasu na tsawon shekara biyar tuni upper tadade ahannunsa kawai shine baiba da dama ba ammh ayanzu da yafada mu momma suka bashi gwarin gwiwan zuwa kam yaji yana sha"awar inyin aiki dasu sunbashi gidan zama da motar hawa unyaje chan kuma lasisin zama agarin na dindin..Sunyi murna kwarai da gaske dasa albarka saidai shizai Fara wucewa tukunnah tunda Safeena na shayarwa itakuma Sakina bata da wani ishashen lpy.





Ranar asabar da misalin karfe biyu na dare jirginsu ya tashi a lagos wanda Dr Tahir yamasa Rakiya sun rabu cike da kewar juna domin tunda suka dawo nageria basu taba rabuwa ba yabarmasa Amanar kula da asibiti har zuwa wani lokaci...yatafi yabar Su momma da matansa da kewarsa.






*Safe journey Dr S S Safana*










Commet
Vote
Share



*Anitha...*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_๐Ÿ’ž


*DEDICATED TO:My Mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are*



*Assalamu Alaikum....Kafin naje gaba naji sakonninku masu cewa in ramgwantama Sakina insaka takara haihuwa kuma Dr yadawo yasota...To azahirin gaskiya kuna manta wani abu karka ku f manta Ada Sakina ita kadai ce ke Da Dr taci karanta bbu babbaka baitaba daga ido yakalleta ba cos tanacin darajar mahaifinta tarainasa tarainamasa uwa da kakansa karfa ku manta akaron farkon cikinta agefen mahaifa ya bayyana bayan tasa anrufemata bakin mahaifa sanadin dayaja sai da mahaifinta ya tsawatarmata ammh hakan bai hanata bayan ta haihu takoma asake rufemata....Kada ku manta ada tasamu Dama ammh tayi wasa da damanta dama ita Rayuwa mai dauka da ijiyewa ce,matukar Sakina takara haihuwa kuma mtsayinta ya zarce na Sakina to tabbas KUSKUREN DATA TAFKA BAI MANA AMFANI BA GABADAYANMU....Haka kaddararta take ba"a Bari akwashe duka koda ka kwashe sai ka bar Wani akasa....Janaf*


*39*


"Alhamdulillah Safwan ya isa kasar portugal lafy asibitin yafara isa yayi report kana ya wuce muhallinsa hakika Safwan yayaba da gurin wani upstair ne mai kyau da tsari ga motarsa range cover baka gabadaya yayaba da tsarin komai gabadayan likitochin turawane da larabawa sai shine kadai bakar fata ya kara tabbatar da cewa Allah na sonshi ne daya zabosa zuwa wannan wurin gashi duk wani cigaba sun daramu komai nasu cikin tsari ne da kwarewa,sai da ya kwana da zuwa kana ya chanza layi yakira gida sunyi murna jin ya isa cikin kwanciyar hankali yayimusu fadan zaman lpy itakuma Sakina yace tacigaba da shan mgani yayi musu alqawarin dakomai ya daidaita zaizo yatafi da daya daga cikinsu bayan ya kira su momma Tahir yakira yakai mai bayanin yadda yasamu komai Normal.





Kwanchi tashi asarar mai Rai gashi Dr na neman cin wata bakwai a portugal kullum yayi waya sai dai ya basu hakuri domin aikin yayi masa yawa gashi bakar fata kuma mai kwazo shiyasa asibitin tabasa mtsayi mai girma kwatakwata bayasamun lokacin kansa wani alokacin agidansa na asibitin yake kwana..Sudai kawai addu"a suke ta mai Sakina ta warke garas abunda taciga da taya Safeena kula da yan biyu wa"inda suka girma sukayi bul dasu akallah suna da wattani goma da haihu dayake suna da karambani har sunfara mikewa itakuma Safeena yanzu hakan Pratical take a asibitin barau dikko dake kaduna itama bata da lokacin sai abun yakoma kan Sakina gashi daman sun shaku da ita duk inda tabi suna biye da ita suna Ammi Ammi,shikuwa Adil an girma don shima Akallah yanzu shekararsa biyar primary 3yake domin yaron kaf kwakwalwar ubansa yabiyo amkranta abun alfahari garesu domin SALISU SAFWAN SAFANA badaga nan ba.



Safwan bai Samu damar dawowa gida ba sai daya hada shekara daga cur kana ya iso gida wata daren jumma'a dare masu daraja aranaku ta Abuja ya sauka Tahir yaje ya taho dashi yana shigowa gidansu ya furta no place like home cikin farinciki momma da hajiya tun safe suke gidan haka ya rumgume momma da hajiya yana murnan ganinsu bai ida mamaki ba sai da yaga yanbiyu suna takawa da kafafunsu rumgumesu yayi yanajin farinciki aransa ga Adil dayakusa kamosa shima yana rumgume dashi yana Fadin i miss u Daddy yace miss u too my son....Zaratan matan nasa kowacce taci gayun kece Raina Safeena tana Sanye da wani ubansu Fefe laces dinkin riga da sikat kayan sun amsheta ko"ina ya cika das da ita itakuma sakina sanye take dawani material fari da baki mai duwatsu dinkin doguwar riga ne dama tuni shi yasan zabin matan nasa safeena ita tafi son riga da sikat ayayinda Sakina tafi sanya dogayen riguna kowacce tacika tayi dam da ita lokaci daya yaji sha"awar kasancewa da matansa yakamasa dama kodayake chan sakamakon aikin dayayimasa yawa sai dare yake samun hutawa shima daya kwanta sai barci gari na wayewa kuma ba zama shiyasa sai lokaci bayan lokaci kewar nasu ke bijiromai...Atare sukayi dinner dukkansu kafin Tahir ya kwashi su Hajiya ya maidasu da yaran sukayi barci Sakina ta kwashesu takai Dakinta itakuma Safina tadau danta ita takaisa dakinsa dake gefen nata da'aka barmasa shima tashi yayi ya shiga nasa dakin ya fada wanka abun mamaki har ya kammallah wankan nasa yayi sallah ba wacce talekosa shiyasa yana gamawa yayi kwanciyarsa aransa yana so yaga mesuke nufi.



sukuwa matan nasa kowacce ta kullacesa ita safeena tazata dakin Sakina yaje shiyasa tajisa shuru tunda sun saba koda yaushe inkinada girki shi zai biyoki har dakinki sai dai kuma in yan mulkin ne suka motsa duk yadda taso kar abun yamata ciwo sai da yayi mata rabonta da mijinta tunda ta haihu duk da tasan in yaje gun sakina ba laifi bane ammh ko sallama ai yayi mata dataga abun na neman hanata sukuni alwala ta dauro tazo ta hau sallah..Sai wajen uku dawani abu ta kwanta.



Abangararen Sakina na ma haka take domin itama tayi tunanin yana gun Safeenarsa tunda ita yanzu bata dawani amfani abun yamata ciwo wanda sai da tayi kuka saboda bakinciki itama din dai haka takwana cikin jin takaichin Abun da Dr Safwan yayimata.




Yana dawowar sallahr asuba yadau mota yatafi gidansu Hajiya bai dawoba sai wurin takwas na safe koda yadawo ya tarar da Safeena zata kai Adil mkranta ta dawo don yau bazata shiga sch ba,suma koda suka fito suka hadu basu nuna ma juna wani abu ba sungaisa yadda suka saba sakina tahada musu breafast itakuma safeena ta shirya yaran dama haka sukanyi basu ma san baya gidanba sai da yadawo domin kowacce bata kalli ko kofar dakin nasa ba kowacce kishi nacinta shima koda ya shigo Safeena tawani dauke kai Sakina ma datake bama Little hajiya tea tahade rai tayi tagefen ido yake kallonsu aransa yace"Topha...To su wa'innan fa mena musu naga kowacce bata son ganina๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚



Dakinsa ya wuce aransa yana fadin"lallema yaran nan ni zasuyima iskanci ko"uhmm yakada kai wanka yayo yakoma gado ya kwanta abinshi yayi banza dasu,koda safeena tadawo kai Adil gidan Hajiya tabiya wai tabar musu gidan suci kansu to itama din sakinar daki ta shige da yaranta tana fadi aranta"Kada ta takuramusu.




Sai after 12 yatashi yasake wanka ya shirya cikin riga da wando na kamfanin armani wandon blue ne haka zalika rigar farace ammh anyi rubutu da blue an sa HANDSOME.
.Kafarsa sanye cikin buddaden takalmi ya fto hannunsa rike da wayarsa da key din motarsa babu kowa afalon shiyasa shima yasa kai yafice ko kallon abunda suka jeramai baiyiba daman ya karya agidan Hajiya asibitinsu ya nufa achan yayi wuninsa zugunr suna tattauna bikin Tahir din wanda za'ayi nan da two weeks.




Koda Safeena tadawo daga ko taba abinci safwan baiyi ba tayi mamaki harsaida ta tambayi Sakina,sakina ta kalleta cikin mamaki tace"ba tare na barku ba ai inaga zaki fini sani aie"Cikin wani yanayi Saferna tace"Bangane tare kika barmu ba Anty ni rabona da Unku tunjiya daya shiga dakinsa"Kai tsaye Sakina tace"Nima hakan take"Suka kalli juna har suna hada baki"ba"a dakinki ya kwana ba"...?


Atare kowacce ta girgiza kai ai sai suka dora hannu akai suna sallallami Sakina tace"Haba no wonder naga yana wani cika ashe ashe"Safeena tace "Mun bani Anty to yanzu yazamuyi"Sakina tayi shuru kan tace"mu rabu dashi yadawo yanzu ko munkirasa bazai dauka ba tashi zakiyi mu hadamai soecial delicious kafin yadawo aikuwa haka sukayi suka zage suka mai sakwara da miyar kan agushi sai ferfesun kan rago suka hadamai kunun aya domin yana so sosai kana kowacce taje daki ta chakare sunhada baki yau shigar wasu riga da sikat sukayi yan kanti cikin tsarabar da ya kawomusu ne kowacce tadaure gashinta da band ko dankwali basu saba yau din kara'i zasu sha.




aikuwa kamar yasani yaki dawowa agidansu Tahir yai zamansa yana hira sai wurin goma ya shigo gidan yara harsungaji da jira sunyi barci abun mamaki sakina da Safeena suna falon zaune sunyi tagumi sunzubama kofa ido yana ganinsu yawani hade rai ko kallonsu baiyi ba yashige daki harda bango kofa jikake bam"kallo juna sukayi kafin sumike gabadaya suka nufa dakin.




Suna sallama aciki ya amsa yana daura tawol zai shiga wanka dukkansu suka nufesa Sakina ta rike tawul din tana daidaita zamansa a kugunsa ita kuma Sakina tajawo hannunsa kiiii"suka nufi tiolet dashi shidai binsu kawai yake aransa yana fadin"waya gaya muku barno gabas take cikin bath suka wuntsilasa kafin sukalli juna sukayi sigina Sakina ta saki shower itakuma Safeena ta warwaremasa tawel din suka fara mai wanka atare suna wani ligwigwitasa kallonsu yayi yace"Ku...Lafiyarku kuwa fyade zakumin ne..?

"Dariya suka sheke dashi harda tafawa sukace atare"Srry...Srrry...Atare daure fuska yayi kan yace"kada wacce tasake tabani ku ficemin daga nan...Yanzu ku kasan dani"Kafin yakara wata mgana suka shige bath din suka turmusheshi suna mai Dariya binsu yake da ido wani nishadi na bin ransa shima turmumusa su yayi sai da yajikasu da ruwan kana ahaka dai suka gama mai wanka agantale bayan angama yace sai an daukesa kallon juna sukayi kan suyi hanyar fita suna fadin"Tab...Wazai iya daukan ka kazama lukuti'yace"ku...mekuka ce"suka fice suna tsintsiramai dariya.




Koda yafto su suka shafamai mai suka shiryasa suka jasa har dinner abincin ma susuka dinga basa abaki suna tarairayansa shikuwa sai wani basarwa yake ammh aransa fes suna kamallawa ya mike Ko magana bai musu ba ya nufu hanyar dakinsa suma mikewa sukayi kowacce ta nufi hanyar dakinta basu mai mgana ba sai da Safeena tashiga sai ta leko tace"Unku mu kwana lpy"tana dariya tamaida kofa ta rufe shuru yayi yana ganin shi zasuyi ma wayau kawai sai yanufi kan kujera zai kwanta sai ji yayi sakina tafigesa ta tura dakinta tana mai Dariya kan gado ta turasa kafin ta hayesa tana dukan kirjinsa tana cewa"Sai kadinga wahalar damu ko,"Rike hannunta yayi kafin yace"Ramawa nayi yara..Ni zaku nuna boko"cizansa tayi ahannu shikuma yace sai ya rama daganan kuma wasan yachanza salo...Nidai na fice araina ina Fadin Happy family.



haka rayuwarta take tafiya kwana biyu yayi gun sakina yakoma gun Safeena yanzu Safwan dan gatane domin wankama inyaji tsiya sai yace sai sun mai sukuwa su zage su sullesa tas bikin Tahir fa yazo tun ana saura kwana uku Safeena tatafi zurmi zuwanta na farko tun bayan aurenta sakina kuwa sai ana gobe biki ta isa hajiya kuwa da momma suna gidansu Tahir hakika sunsha biki sun gwangwaje sun dauko amarya sunkawota kaduna cikin aminci da soyayyah,...Bayan bikin safwan yayi shirin komawa a adalci da Sakina yayi shirin komawa domin itace uwargida.




Bayan bikin Da sati daya Suka daga zuwa Portugal shida Sakina itakuma Safeena anbarta da yara saboda sch dinsu da nata ita shida kanshi yatsara duk bayan 6,months zai dinga dawowa suna chanji ita da Sakinar.






Commet
And
Share
Vote


*Anitha...*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty๐Ÿ’ž_


*DEDICATED TO:My mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are*



_*Godiya gareku Masoyana wanda

Please Login or Register in order to submit comment