Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wajen karfe 9:30pm na Dare ya Shigo Gidan Habu mai gadi na barka da dawowa ya amsa cikinn Sakin Fuska kafin ya Nufi Shashen Mommah Saboda Sanin Bakin Hajiya mama akwai mgana



Zaune ya iske su suna mgana yayi sallama suka amsa ya cire takalmi ya kariso ciki Kafadansa Sabe da Lapcoat dinsa kusa da Momma ya zauna yana gaisheta ta amsa tana mika masa Adil Haj.Mama dake kan kujera zaune tayi gyaran murya tace"Mgnar dana ce zamuyi mganace data shafemu dukkanmu shiyasa naga yakamata na taraku mu tattauna


"kai Sufiyanu mganar duk akankane..."yadago yana kallonta bai yi ba mgana tacigaba da cewa"kwarai da gaske ni wacece agareka? tafada tana kallonsa Da sigar tambaya cikin daure kai yace"ke kakatace wacce ta haifi mahaifina ammh hajiya mai yakawo wannan m....."?Daga masa hannu tayi kan tace tana kallon momma"Na isa in zartar da hukunci a gidan nan Ko Ban isa ba..?

Momma tace"haba hajiya ai dani da babana a karkashin ikon ki muke...Kifadi bukatarki umarni kawai zaki bada insha Allahu zaki samemu masu biyayyah".



Haj.Mama ta rausayar dakai cikin farinciki tace"Masha Allahu naji dadi dama nasanki Hadiza bazan samu mtsala dake ba,zuwana Safana dalinlinkane Sufiyanu"Ta fada tana kallonshi shima dagowa yayi yana kallonta kan yayi mgana ta rigasa dacewa"Matarka tafadamun mganar daya zaburar dani na farka daga barcin daya kwasheni,na tabbata in sakina tafi karfin iyayenta da mijinta to mu d'anmu bai fi karfin mu ba"



tayi shuru kan taci gaba da cewa"Naje da Niyyar Neman Safiyanu Aure ne....""Arazane Dr Safwan yadago yana fadin"Neman aure kuma hajiya"?

yafada da sigar maimaitawa da Tambaya Haj.Mama tamike tsaye tace"Kwarai kuwa.. kuma sai kayi sa'a gidan dattako,ne daga Neman aure kuma aka Dauro Aure"Ras gaban Dr Safwan ya buga momma tace cikin mamaki"aure...Kina Nufin yanzu Babana mata biyu garesa kenan"Haj.Mama tace"ya wuce wai Hadiza ina fatan wannan aure shi zai kawo chanji arayuwar yaron nan" Nan tashiga labarta musu daga farko har karshen abunda ya Faru takareshe da cewa"Ka shirya ranar sati Attahiru ya raka ka kaje ku ga juna ina so ayi ayi tatare ne cikin lokaci"tafada da bada umarni.


Ajiyar zuciya momma ta sauke tana kallon Dr Safwan dayake kallon Hajiya cikin al"ajabi na abunda take Fada cikin sanyin murya yace"Hajiya wannan tatsuniyace ko kuwa dai wasan da kika sabane"?

Harara ta zabgamai kan tace"kai ashe shashashane ban sani ba ana nema maka mafita da yanci ammh kana sakarci ko?to babu wasa matarka SAFINA ta na chan tana jiranka"zai sake mgana Momma ta girgiza masa kai tayi saurin cewa"Alhamdulillah...Hajiya Allah ubangiji ya sa alkhairi aka kullah....Nasan Safina yarinyar kirkice kwarai matuka"



Haj.Mama tawashe baki tace"kwarai da gaske Safina itace daidai da tsarin Rayuwarka,ayanzu haka tana chan ibadan ita ta wakilci jahar su ta zamfara a gasar alqur'ani ta kasa gabadaya"Momma ta washe baki tace"Kai hajiya alkhairi ya shigomana gida wlh....Allah yasa mu amfana da ilimin nata"hajiya ta amsa da Amin


Dr Safwan mutuwar zaune yayi yashiga rudu gani yake kamar amafarki wai ya sake auren wata bayan Sakina abunda bai taba zato ba ko a mafarki baida sha'awar auren mace fiye da daya to dayanma ya yakare da ita balle har yayi Tunanin kari,Haj.Mama ta katsemai Tunani dacewa"baka ce komai ba,ko bakayi murna da alheri dana maka bane"?cikin sanyin murya yace"na isa Hajiya...Allah yasaka da alheri"ta amsa cikin Farinciki dacewa"ko kaifa dan Albarka,Allah yama rayuwarka Albarka ya Sanya Safina abokiyar zamankace"momma ta amsa da Amin mika maka mata Adil yayi kan ya mike ya musu sai da Safe.



Asanyaye ya isa shashensu kai tsaye bedroom din shi ya shiga kan royal bed din dayaji kayataccen zanin gado,yafada zubewa yayi yana sauke Numfashi yakurama saman dakin ido yana tunanin makomar Rayuwarsa baisan dawani ido zai kalli wata mace amatsayin matarshi ba,bawai don yana matukar son sakina ba a"a sai dan gasamasa aya Ahannu da Sakina tayi shiyasa ya cire kowacce mace a lissafi bai ko tunanin kallo wata mace da sunan kallo sha'awa duk halinsu daya yake gani yadade kwance kan ya yunkura yafada toilet,yayo wanka ya dauro al"awala yazo yagabatar da Nafila yadade yana addu',oi kafin ya koma ya kwanta wanda har barci ya kwasheshi bai tantance wani hali yake ciki ba shi dai ba haushi yake ji ba kuma ba murna yakeyi ba



Asuba tagari Dr S S Safana






_*TEAM SAFINA_😍

_*TEAM SAKINA💞_






*Anitha...*




commet
share
And
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*


_*Hohoho ur Durling Safeena Aliyu zurmi tace karkuji komai,kawai ku bata lokaci tayi alkwarin chanza Rayuwar Dr S S Safana....iz juz d begining guyzs*_



*14*



----Koda garin Allah ya waye har saida Dr Safwan ya makara kafin ya tashi shima Dr Tahir ne ya ishesa da kiran kan ankawo musu emergency ,yayi mamakin barcin daya sha wanda rabonsa da irinshi wlh bazai iya tuna waba( lalle Safeena ke haskece arayuwar Dr S S Safana)cikin gaggawa yayi wanka ya shirya cikin suit masu rowan toka samfarin DKNY agurguje ya shiga shashen su momma ya musu sallama suka rakasa da sa albarka.


Wata matace aka kawo zata haifi yan uku to biyu sun danne daya kuma suna kokarin turo kai atare gashi karfin uwar yafara karewa zuwan Dr Safwan cikin kwarewa da taimakon Allah ta haifi yaranta cikin salama da kwanciyar Hankali yan"uwan matan sun matukar jinjinama Dr Safwan ganin yadda tun dazu likitoci ke kara kaina akanta bata haihu ba ammh yana zuwa cikin mintin da bai gaza goma ba ta haihu hakika sun yaba da jajircewa irinta Dr Safwan Sale Safana wanda har sai da suka Furtamai.


Aranar Dr Safwan ya wuni aiki a asibiti operation uku yayi duk agajiye yake komawarsa office kenan ya bude karamin fridge din dake office din ya ciro ruwan faro ya kafa kai sai daya sha fiye da Rabi kana ya ijiye kan kujeran office din yafada yana maida Numfashi.


Dr Tahir ne ya turo kofar office din ya shigo ya kariso yana kallon Dr Safwan dake kwance idanunsa a lumshe duk da yasan ba barci yake yi ba file din daya shigo dashi ya ijiye kan yace"Dr Safana wai meke Faruwa ne yaudin nan naganka kana wani annushuwane"?Dr Safwan yanajinsa yayi masa shuru sai chan yace"Kai fa mugun dan sa"ido ne wlh Tahir"Yafada still bai bude ido ba.



Dr Tahir ya kyalkyace da dariya kan yace"My man...ai indai kaine to momma ce kawai zata Fini saninka common gist me "Mirmishi Dr Safwan yayi kan ya Mike Zaune yana Fadin"Zan yi gisting dinka ammh ba yanzu ba but it only i know yau ina jin yanayi na yana canzawa i dont know may be wani abu something zai Faru dani ne"Dr Tahir yayi galala yana kallonsa cikin farinciki kafin yace"Ko dana ji Dr Safana Dan Allah shafamin nasan komiye yasakaka Annuri yau iz sometin special".


Mikewa Dr Safwan yayi kan ya isa kan teburin dayama office din kwanya yana Fadin"Tsiyana dakai wutar ciki,ba ni nace ba"yafada yana kallonsa tare da dagemai gira guda daya Dr Tahir yace"Sure my Dr nakosa ne"Dr Safwan ya zari wani fayal yana wucewa yace"Nafasa kasan ban san damu"Da sauri yace"Srry..Nadaina damunka but karkajamin rai"Tsaki Dr Safwan yaja kan yace"in kafito ka rufemin office din Aku"Dariya Dr Tahir yayi kan yace"Bakomai indai za"a bani lbr,daga haka ya fada toilet din office din shikuma Dr Safwan ya Fice.



Hmmm Su Dr Safwan tun yanzu tunma baku hadu da Safinar ba kafara zakewa

*******


*Zurmi...*



---Masha Allahu kwanansu Safeena hudu suka dawo jaharsu ayayin da jahar Zamfara tazo na biyu,Hakika Safeena ta godema Allah dayasa iyayenta suka tsaya akanta tasamu limi yau dalilin ilimi tasamu kujerar makka harda motar hawa golf da zunzuruntun kudi har dubu dari biyar tayi kuka,kukan Farinciki da zamowarta wurin dabakowa ke takowa ba sai wanda Allah yabama limi da basira,haka suka dawo cikin Farin ciki kudi dai mkrantansu ta mallakamawa kujerar makka kuma Abbanta ayayinda motar tace Abbanta yabada adinga mishi haya,Hakika Ummi taga Ranar Haihuwa domin makota da yan"uwa da abokan arzika sai shigowa suke tayasu murna,suna cikin amsan baki shyasa Abbah bai samu kebewa da Safeena ba sai da tadawo da kwana uku kana.


Cikin dakinshi yakirata bayan ya yi godiya ga Allah subuhanahu wata'ala daya azurtasa da samun ya irinta,yayi mata Nasiha mai kashe jiki har sai da ta Fitar da kwallah kan ya gangaro kan zence yace'Safeena kinsan dai bazan cutar dake bako?"Yafada yana kallonta gyada kai tayi kawai jikinta yagama Sanyi fatanta Allah yasa bawani abu yafaru ba bayan batanan ba.



Yacigaba da cewa"to duk abunda zan Fada miki ki daukesa matsayin kaddara..Kina gabda tafiya gasar nan na daura miki aure"Dam!dam!gabam Safina ya buga tadago da sauri cikin Rawar murya tace'Aure kuma Abbah'...?kai tsaye yace'Kwarai Safina...Na daura miki aure sati biyu da suka wuce da jikan Hajiyar Safana"yafada yana ciro sadakinta ya kama Hannunta ya Damkamata,Safina taji hawaye ya wanke mata Fuska tana so tayi mgana ammh kuka yaci karfinta mallam Aliyu ya kalleta yaji tsausayinta ya tsirgamasa yace cikin taushin murya"karki ce komai yata Allah yayi miki albarka Safina Ubangiji ya jibanci lamarinki yakuma zaunar dake lafiya agidan aurenki"yafada yana kauda kai kwallah tataru a idanunsa,Safina tayi karfin halin cewa"Hakika Abbah kai yafi chanchanta daka zabamin mijin daya dace dani,na karbi auren nan hannu bibbiyu sai dai ina rokonka dan Allah Abbah kutayani da addu'a Allah ya bani juriya da hakuri"takareshe fada tana kara tsananta kukanta Abbah yace"tashi kije yar albarka da izinin lahi bazaki tabe ba Safina"cikin sanyi ta mike rike da kudin tace" Abbah karike kudin"girgiza kai yayi kan yace"A'a Safeena Hakkinki ne ki mikama Ummanki ta adana miki kan muji daga mijin naki.Kada kai tayi kan tafice tana sharan hawaye.Runtse ido Abbah yayi yanaji har aransa kamar bai kyauta ma Safina ba Sam.













*Shakira..*




Commet
Share
And
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞




*15*



----Tana isa daki tafada jikin Ummi dake zaune gefen gado,tafashe da kuka Ummi tariketa tana fadin"Ya isa Safina kidaina kuka haka Allah ya kaddara kinsan bawa bai isa ya gujema kaddararsa ba"


Safina tadago tana kallon fuskar Ummi da dan hasken makarfin daya dan haske dakin fuskarta shabe shabe da hawaye ta hade da majina,cikin dashashiyar murya tace"Ummi...Yazanyi da Mallam yahuza,da sonsa yafara samun gurbi azuciyata?


Ummi tace"Hakuri zakiyi Safina shine mafita kawai"Tsuru mata ido tayi tana kallonta hawaye suna kwaranya tace"Ummi taya zaku auramin wanda baku sani ba,bakusan addinin saba balle al'adansa ba,Ummi meyasa? takareshe tana kara fashewa da kuka.


Ajiyar Zuciya Ummi ta Sauke kan tazaunar da Safina kan gadon tamike tana cewa"Hakane...Ammh bakin alkalami yariga ya bushe Allah yaga zukatanmu Badon komai muka bada ke garesu ba sai dan Amanar dake tsakaninmu da Hajiya mama shekara da shekaru bazamu iya ture bukatarta ba"Safina takara jan majina tace"Ummi....Dakata"Ummi tafada tana tsaidata da Hannu kan tacigaba da cewa"Kada fa bacin rai yasa ki manta matsayinmu agareki,munada daman zaba miki mijin daya dace dake...Ki dawo cikin Hayyacin ki Safina ki mika lamarinki ga Allah shine zai taimakeki.



Daga haka tasakai tafice cikin tsausayin yarta mafi soyuwa aranta,tana Fita Safina tafashe da kuka mai cinrai ta sulale kan gadon tana kara volume din kukan,ashe ashe shiyasa mallam yahuza ranar da suka dawo yana mata murna yaki kallon cikin idanunta in baza ta manta ba har kwallah tagani kwance cikin idanunsa,Allah sarki mallam yahuza ashe an rabamu ne wayyo Ni Safina ina zansa kaina"tafada tana kara fashewa da kuka kara dunkulewa tayi tana cigaba da kukan rashin madafa.




Haka Ummi ta tarar da Abbah cikin alhini dataga yadamu ita tadinga kwantar mai da hankali har yadan ware kadan.





Koda gari ya waye Har Abbah yafita kasuwa Safina bata Fito ba yasan zataji badadi shiyasa yace Ummi tabita Ahankali haka yasakai yafice cike da tsausayin yarshi aransa,sai wajen goma Safina tatashi idanunta sun kumbura kanta yamata Nauyi dayake tana Fashin sallah wanka tayi tashirya cikin wani jan material dinkin doguwar riga fuskarta ko hoda bata sanya ba ta fito ta tarar da Ummi A kichen tana gyaran wake tasanya Hannu zata karba Ummi tahanata tadago idanuwanta dasuka kumbura tace"Ummi...Ki.."Bani zaki ba hakuri ba Safina mune zamu baki hakuri dan mun bata miki"Tafada kanta tsaye daga gani ranta abace yake Safeena ta durkusa tace"Dan Allah Ummi ki yafemin wlh baran karaba"tafada hawaye suna zubo mata Ummi ta ijiye waken ta riketa ta data ita tsaye tasa hannu tana share mata hawaye tace"Shikenan Safeena kar ki kara irin wannan...Abbanki da damuwarki yafita inbaki bashi gwarin gwiwa ba yakike so yayi ehe?

"Safeena tarike Hannu Ummi tace"Naji Ummi kuma insha Allahu zaku sameni mai biyayyah agareku"Ummi tace'ko kefa diyar albarka kisaki ranki kinji...Ubangiji yasa albarka Arayuwarki kinji yata"Tafada tana matsa kumatunta Dariya Safeena tayi har hakoranta suka bayyana tace"Nagode Ummi nagode daya kasance kika zama uwa agareni"Ummi tace"Nima haka Safeena na.


Daga haka suka cigaba da aiki suna hirarsu har lokacin da Usman yadawo daga mkranta,koda Abbah yadawo yaga yadda Safeena tasaki ranta ransa yamasa dadi yaji kaso dayawa na damuwarsa yaragu yadinga sa mata albarka har sai da tafitar da kwallah na tsausayin iyayenta hakika in bata musu biyayyah ba data tabe duniya wa lahira.






•••••••••••••••••




*Kaduna...*




Haka Dr Safwan yadinga janma Dr Tahir rai shikuma yaki Hakura ranar dai suna cikin mota Dr Safwan ke tukawa zasu koma gida Dr Tahir yabiyosa zai gaidasu momma Dr Tahir ya kallesa yana driving ammh hankalinsa na wani wuri,Dr Tahir ya tabasa yana cewa"mr man...Wannan dogon Nazarin naka wai yaushe zai kare ne?"Mirmishi Dr Safwan yayi hankalinsa na kan titi yace"har Abada Tahir...Bansan yaushene zandinga hango kaina amatsayin cikakken Namiji ba"Yafada muryansa na bayyana Rauninsa.


Dr Tahir ya kallesa cikin tsausaya kan yace"verry soon Abokina...Allah nasane dakai kuma inaji ajikina kamar komai yazo karshe"Dr Safwan yayi mirmishin gefen baki yace"Kaji wata chakwakiyar da Haj.Mama takara jefani wai Aure tamin"Zuru Dr Tahir yayi masa yana kallonsa shikuwa yasan yana kallonsa dat why yaki kallonsa.


Cikin mamaki Dr Tahir ya maimata"Aure...Wai Aure na gaske kona wasa?"wai na gaske"kai tsaye ya basa Amsa kan yacigaba da cewa"shine mganar danace zamuyi tun last week aie...Yatabe baki yace"Kasan ma har an daura auren wai" wani uban ihu Dr Tahir yasa har saida Dr Safwan yaci burki yana binsa da kallo.



Cikin matukar murna Dr Tahir yace"Ehyyyyyyye.....Dis iz juz d begining abokina,Wlh wannan mganar kara aure tuni ke Raina kawai saninka ne yasa nakasa kawo maka wannan shawaran.Kai Haj.Mama tagama min komai wlh"Yafada harda buga kafa Dr Safwan yabuga tsaki yace"Mtewwww...Kai fa wlh dan juju ne to meye nawani ihu"Dr Tahir yace'eh naji...Nidai yanzu ina amaryan take infact ma ya'akayi duk wannan abun cikin gaggawa,Dr Safwan ya zabgamasa harara yace"Gata goye abayana uban yan tsegumi.." Dr Tahir ya sheke da dariyar shedanci yace"Kace komai abokina lokacinka ne nawa nanan zuwa wlh sai ka raina kanka yaro"Yafada yana zunguran kafadansa,Banza yayi dashi yacigaba da tukinsa.






Suna isa sai da Dr Tahir yakara kular da Dr Safwan chan ya barshi gun Habu mai gadi yana tsinannan surutunsa ya isa shashen su momma,Hajiya ya tarar afalon tazuba ido tana kallon talabijin a tashar Arewa 24 sallama yayi bata ji ba kawai ya girgiza kai ya wuce dakin momma ya tarar da ita tana goye da adil tana gyara kaya acikin wardrope,da sallama ya shiga ta amsa tana masa maraba da dawowa ya amsa yana fadin"Momma sannunku,da gida"ta amsa da cewa"Yauwa..Babana yawajen aikin"?ya amsa da Alhamdulillah yana tambayan Adil yayi barci ne tace"eh..Yanzu yayi,ficewa yayi yana fadin"Momma kizo ku gaisa da Tahir yazo gaisheku",daga haka ya fice.




Yana fitowa ya tarar da suda guda biyu Hajiya.Mama da Tahir sun kacema da hira dama mutunintane,kan kujera ya isa yazauna yana Fadin"Hajiya ikon Allah"tace"kwarai yaro nan gani nan bari wlh"Dr Tahir ya sheke dadariya yana Fadin"dole abar Hajiya domin bamai iyawa dake tace"wane mutum Attahiru bawanda ya"isa ne ma"'mirmishi kawai Dr Safwan yayi yafito da wayarsa yana latsawa,momma ta fito suka gaisa kan tashiga kichen zata zubo musu abinci,nan fa Tahir ya gyara zama yace"Hajiya ashe abun alkhairin daya samu abokina kenan?"Haj.Mama tace"Kamar wanne kenan Attahiru..,? yace'Na aure mana"haj.Mama ta washe baki tace'au ashe yagaya maka dan nema ninan dana fadamasa fuskar shanu yamin tundaga ranar ina lura dashi ko kallona baisan yi"tafada tana Nuna sa da baki Dr Tahir yayi dariya yace'ai Hajiya Allah dai ya biyaki da aljannah abunda kikayi yayi dai dai ko Allah yasa yadace wannan karon"Haj.Mama tace cikin jin dadi"Amin..Attahiru shiyasa nake sonka da fahimta...Nan Hajiya ta fede masa biri har watsiya ta kareshe da cewa'Nasan wannan Auren Alheri ne shiyasama nakeso cikin satin nan kuje ku ganta nasan zakuga abunda nake fada muku"Tahir yace"Insha Allahu zamu je hajiya karki wani damu.




Dr Safwan ya tashi yana cewa"ubanwa zaije dakai....Karma kasa rai",Dr Tahir yace'oho.....Haji.Mama tace"Uban wanda yayi mganan tafada tana mai dakuwa'kan tace kagamin ja'irin yaro fitsararre to ubanka zai je dashi'Hanyar fita yayi yana Fadin"kidaina zaganmun uba"Tace"Allah...Habule to zoka dakeni ance Ubankane🤣🤣tafada harda mikewa ficewa yayi yana kunkuni tace"Dawo rasa kunya in nuna maka karyan tsiya kake"tana wani rike kugu,Dr Tahir yana ta kwasan dariya,momma takawomusu abinci ta ga ba Dr Safwan tace'Ina babana yayi ne Haj mama tace'Rashin tarbiya yagwada min na numasa nima A ce🤣"momma tayi mirmishi kawai nan Tahir yaci dambun zogale yayi nak kana yamasu haj.Mama sallama ya wuce.



Shashen Sakina ya shiga yako iske hakiman zaune afalo ta hakimce ana ta zuba lissafi,adakile suka gaisa yake tambayanta Dr Safwan dabaki tanuna masa dakinsa yako wuce yana zolayarta da"Hajiya madam tamu"da harara ta bisa dan taga zuwansu tundazu shine sai da yagama gulmarsa zai zoyana mata wani rawar baki to daga shi har abokin nasa dai dai take dasu🤔





Koda shigansa dakin kwance ya tarar dashi kan gado atsaye Dr Tahir ya tsaya kan yace',plz serious mr man yaushe kake ganin zamuyi tafiyar nan?"banza yayi masa har saida ya fidda rai da zaiyi mgana kan yace"Dis coming weeked nake sa rai daga haka yajuya baya Dr tahir ya fice yana cewa"As u wish Sir...Nina ware,daga haka ya fice.








*Anitha...*




Commet
Share
Vote
Like
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*


*16*


"Ranar lahadi tun Safe Dr Tahir yayi ma Dr Safwan sammako,Shima Dr din yasan Halin Tahir din da wutar ciki dat why ya shirya da wuri,Dama gashi jiya da daddare kwana sakina tayi bala'i haka kawai yana Zaune adakinsa yana wani aiki a laptop dinsa ta shigo ta sameshi tace tana son mgana dashi don Sakina bata da kunya wai tafaramai complain yana wulakantata yadaina kulata kana yadaina bata Hakkinta na Aure abun haushi abun takaichi yaji wani bakinciki yayimin shar arai yaso yamata mgama ammh sai ya tuna Neman shiri take shikuwa yayi alkwari nuna ma Sakina shi cikakken Namiji ne _yauwa Namijina_



Kwashe laptop dinsa yayi ya fice ya barmata daki dayan bedroom din ya shige dayake 3 bedroom ne yasaka key cos yasanta yar hayaniyace sai ta samai ciwon kai,aikuwa taita bala'i hartana Fadin dole dai Azauna da ita don babu yadda aka iya da'ita mirmishi yayi aransa yana auna girman rainin da Sakina tayimin lalle kuwa tayi kuskure inhar take Tunanin tafi karfin shi ne kawai kyaleta yakeyi cos darajar mahaifinta ammh shi tuni tagama Siremai da munanan halayyanta shifa baida darajar da Sakina zata fita tafadamai sai dai yazo yaga bata gida,baida kimar da zatayimai abinci balle sauran abunda ba'a rasa ba, ji bi yadda Adil yarasa gatan ta ammh ko ajikinta ko nono sai taga dama in momma ta roketa ta bashi,to har wannan macece,shiyasa yadau ma kansa Nuna mata *TA TAFKA KUSKURE*





Cikin Wata shadda gezner deep blue ya shirya jamface zanna bukar ce bisa kansa itama da zaren blue akayita takalmin kafansa rufaffene na fatar Damisa,baki yafeshe jikinsa da turarensa Azzaro visit Kansa yadau gyara abunka ka mai kyau sai yafito yabada wani sirrin kyau wanda ba kowa ke ganewa ba sai wanda akayi dominshi.



Ko takan Sakina bai bi ba,tana dakinta ta kwana da takaichin wulakancin Da Dr Safwan yamata kuma tayi alkwari kafin ya Fita sai yagayamata meye matsayinta agidan dayakemata halin ko inkula _Topha lalle Sakina kunya bai ishe ki ba_🤔





Sashen Momma ya tarar Da Dr Tahir shima ya Shirya cikin shadda fara wagambari shima cikin dikin muhammd shima zannah bukar din yadora kafarsa shima cikin sawu ciki bakake Sororo yayi yana kallonsa tun shigowarsa momma Dake zaune gefe ita ta tsurama danta ido tana kallon yadda danta yau yake Fitar dawani hasken Annuri na dabam Haj.Mama dake tsaye gefe tasaki guda" Ayyiriri.....!!!!Masha Allahu Safiyanu lalle kanunamin kai jinin justice Habule ne,


Dr Safwan yayi mirmishi kan ya karisa ya duka yana gaida momma ta amsa tana Dafa kansa tace cikin farinciki"Babana nadade ban ganka cikin Annuri irin na yau ba'sunkuyar dakai yayi kan yace"Momma...Bbu komai wlh'tace"unhum...Fadamin gaskiya ko duk murnan zuwa ganin surukar tawace?"tafada tana dago kansa da hannunta,Mirmishi kawai yamata baice komai ba domin shima mamakin farincikin daya tsinci kansa yakeyi ayau din.




Adil dake Hannun Dr Tahir ya amsa yana cillasa sama yana Fadin"Bawan Allah damo sarki hakuri...Zaka bini ne"yafada kamar yana jinsa Haj.Mama tace"Bawan Allah yakusa samin uwata gari ba wacce tambadaddiyar ba"Tafada tana nuna shashenta da Baki Dr Tahir"Yayi dariya yace"Allah barmana Hajiyarmu"Tace"eh...Kona ga karshen tazurancinka ba" tafada harda mele masa baki,dariya yayi kan yace"Haba Hajiyarmu verry soon za'ayi"tace"kai kasan wani vari san ince dai ba zagina kayi ba..?😂😂😂Yace yana Rike baki"Wane ni Tahir"tace"Au na'aza zagina kayi wlh in ci ubanka domin ni ban yadda da wannan gwarancin naku ba"Tafada tana harare harare dariya sukayi gabadayansu





Har wurin mota suka rakosu Haj.Mama na jaddadamusu cewa su fara bi Safana Iyami ta hadasu da wanda zai kaisu zurmin kar suje su bace ko yan kiddappers su sace su😂😂.





Koda tara tayi suna Safana dayake da benz din Dr akayi Tafiyan sai da suka fara biyawa gun kawu bala suka gaishesu yayi murna da ganin Dr yayi mai Nasiha sosai kan yarike wannan aure da hannu bibbiyu saboda yarinyace data Fito yar babba gida,Jikinsu yayi Sanyi da Nasihar kawu kuma daman shi baija da wannan aure cos har aransa baiji Haushi ba saima wani Annushuwa.





Iyami sai dai taga su Dr Safwan kwatsam taita ina tasaka dasu basu wani jima ba tahadasu da dan kishiyarta manu tace yakaisu gashi anyi ta neman mallam Aliyu awaya Afadamai ba'a sameshi ba gashi ita Ummi bata da waya balle Safina.




Karfe10:30 suka Dau hanyar Zamfara sai muyi Fatan isarsu lafiya.



*****

*Zurmi..*





Yau tun Safe Safeena taji gabanta na Faduwa bata kawo komai ba tayi addu'a taci gaba da sabgoginta,tana kammallah aiyukanta tayi wanka ta shirya cikin bakar doguwar riga da farin hijabinta har kasa da safa ta daura Nikabinta ta Fito tana Ma Ummi sallama kan zata Duba Aisha bata jin dadi Ummi tamata adawo lafiya.saboda taji dakyar Abbanta yabarta fita dan tunda tadawo bata sake fita ko'ina ba saboda akwai Hakkin wani akanta.








Tafita badadewa Ummi tana bakin kichen tana tsinkan zogale domin shi yau mallam yace yana sha'awa wato tuwon shinkafa miyar zogale kawai taga Manu ya fado da gudu manu dai bazai wuce shekara tara aduniya ba sa'an Usman ne Ummi ta saki tsigan zogale tana Fadin"Kai Manu daga ina? kuma kai dawane? ajere ta jefamai tambayoyin haki yakeyi kan yace'goggo Iyami ce tace na kawo wasu baki"Ummi tace"Baki..Kuma"Ta maimata da sigar tambaya.



Manu yace'eh...Tace mijim yaya Safeena ne"Ummi ta mike dafe da kirji tace mijin wa?"tafada tana zaro ido yace"Mijin Yaya Safeena tace"Ummi tayi daki da Sauri tana fadin"na shiga Uku ni zainabu zuwa ba shiri😂😂Ummi ta rude taji zuwan siriki.




Hijabi ta yaya tasanya kan tajawo tabarma ta Shimfida kan shararran simintin dake tsakar gidan tana Fadin",Maza manu ce su shigo.Yako ruga da gudu ya fice yana murna yasha dadin mota.






Suna tsaye ajikin motar Dr Safwan yana bin dan gidan su Safeena da kallo aransa yana fadin"wai daman akwai masu rayuwa a irin gidan nan" _Tab...Lallenema Dr to dankai kana gida mai kyau sai yazamana kowama hakane_


Shiko Dr Tahir anguwan yake bi da kallo dagani dai anguwan ta masu rufin asiri ce ba'a fadi dayan ba kofar gidansu Safeenar agyare tsaf dashi aransa yace"Tab....Nan gidan kuma Hajiya mama takawomu" _Kaniyarka Tahir Gidansu Safeenar kake zagewa_😛



Suna zencen zucci ne manu yafito da gudu yana fadin"ance ku shigo"Dr Tahir yakalli D Safwan yace"to bismillah...Kaine maigidan aie"yafada yana dariya kasa kasa Harara ya wurgamasa kafin ya wuce ya rufamasa baya da sallama suka shiga abakinsu Ummi dake kofar daki ta amsa kanta na kasa tana masu maraba dukkansu zubewa sukayi suna kwasan gaisuwa Ummi ta amsa tana tambayan su Hajiya Dr Tahir ya amsa da "Suna gaisheku"


Shuru ya

Please Login or Register in order to submit comment