Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazan dakuba dai" kasa bashi amsa sakina tayi saboda tasan waye Tahir gurin maida magana kamar dan Hausa bakwai.



..Ya rubuta mata maganin karin jini kafin yabata sallama saboda ta haihu lafy ko kari ba'a mata tana haihuwa kaji kwakwazo tsit tamike ras kamar ba ita ba yana tsokananta yasan ya kunnota shiyasa yaketa dariya,ita kuwa Hajiya kari jitake kamar ta shakeshi yacika iyayi ga tsinannan tadi kamar wani aku,momma tana ta zunduma ma Tahir Albarka har suka fito,har mota yarakasu momma dai ita ke rike da jikanta,har sunshiga mota Hajiya kari ta lego tace"Shi wanchan fa koda dan shege aka Haifa mai ai yazo yaganshi balle dan Sunnah ne kuma shi yadigasa"Tafada kanta tsaye Dr Tahir yagyara tsayuwa sanin matan bata da kunya ko kadan yasa kai tsaye yace mata"Wlh aikine yarikesa ammh kema kinsa bakasha wahalar diga abu da kanka ba,kuma ka banzarta dashi ba"Yafada yana kallonta ido cikin ido kasa bashi amsa tayi har dereba yajasu suka bar asibitin yana kallon motan yana killer smile kafin yace'kunyan mara kunya asara.


***


Hajiya mama dake zaune a farfajiyar flat dinsu tana tsinkan zogalanta datazo dashi daga safana radio tane agefenta takure kara tana jin gidan radion freedom ansa wakar sangaya ta daddage, tana bin abinta Mallam Ilaya mai bawa fulawa ruwane agidan,shine aikinsa shike zaune kusa da Hajiya tana zubamai labarin zamanta a safana sukaji hon din motan Mallan Habu mai gadi yayi gaggawan zuwa ya wangale get motar tasu tasawo kai zuwa parking space Momma ce tafara fitowa rike da baby a hannunta kafin Hajiya da sakina wacce tafito tana wani hura hanci kamar wata sakarya,Hajiya mama tai galala tana kallonsu Tunda Hajiya kari tafito taga Hajiya mama tawani hade rai,momma cikin farinciki ta nufi Hajiya mama tana fadin"Hajiya kiyi barka kinyi sabon maigida"Tsuramata ido Hajiya tayi tana kallonta sama da kasa kafin tace"Au....Wai tasauka ne na"aza bazata iya Haihuwa da kanta ba?

tafada tana bin sakinar dawani kallon raini jikin Momma yayi sanyi kafin tayi mgana Hajiya mama taci gaba da cewa" 'au ke kika koma mai renon kuma saboda sunmaidake wata sha katafi ko"?

tafada ranta abace Momma tadago zatayi magana taga mallam iliyasu ya tsuramusu ido da sauri tace"Mallam ilaya kunyi d'a fa "yana washe baki yazo ya amasheshi yana sa masa albarka shima mallam Habu yakariso yana sa albarka.



Hajiya mama tamike tawuce tana fadin"bari naje naji ubanwa zai mata renon dan.."tana fada tawuce fuu sashen sakina wacce tun fitowarsu suka shige ciki,koda ta isa basu afalo cikin bedroom ta samesu sakina kwance share share Akan gado Hajiya kari nagefen suna mgana Hajiya mama tafado dakin,sororo suke binta da kallon Hajiya kari tayi karfin halin cewa"Haba hajiya da girmanki kina shigowa guri babu sallama"tafada tawani cin mgani Hajiya mama ta kallesu a wulakance kan tace"Ana sallama inda akasan darajan sallamane ba inda ba'asan darajarta ba"Cikin kunan rai sakina tace"gaskiya hajiya wlh kija girmanki,kan mene gaskia kija girmanki tunkan na tunkudesa"takareshe fada da rashin kunya Hajiya mama tace"Kin ma uwarki bani ba wlh da ita kikeyi don banace kinma ubanki ba don Kabiru yaron arziki ne, nikam nafi karfinki fitsararriya kawai,kuma wlh kinemi mai miki reno hadizar baiwar uwarkice dazaki barmata rikon jika tareni d'a kuma ta reni jika bazai yuyuba tunda kika iya bin miji kikai ciki to kin ko san yadda ake reno"Tana gama fadar haka ta buga musu tsaki tafice.





Hajiya kari takalli sakinar tana fadin"wai wannan tsohuwar anya kanta daya"Sakina tace"lafiyarta kalau Hajiya tsabar iskanci ne wlh,kuma shi safwan din ke dauremata gindi"Cikin takaichi Hajiya kari tace"shegiyar tsohuwa mai shisshigin bala'i"Sakina ta karbe da cewa"ta karshe wlh Hajiya tshohuwarnan tana shigan hanci wlh"Tafada tana bayyana takaichinta.




Hajiya tace"barta mugama da jikanta tukunnah ita karamar alhakice.


Koda Hajiya takoma ta iske momma na tsaye tana jiranta kallonta tayi tana rumgume da baby kan tace"sai ki wuce ki kaimusu dan'su saura kizauna kina musu bauta tunda nasan ki zuciyarki kamar ruwan sanyi take"tana fadar haka ta tattara shimfidanta ta shige ciki,koda momma takai shi itace tamasa wanka tasama sakina nata,ko wankanma saboda lalacewa dakanta tashiga hajiya na kallonta ko ajikinta momma taga abun mamaki ammh sanin halinsu yasa taja bakinta ta tsuke.



*Anitha..*

.Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_


*DEDICATED TO: My Mommah Hajja Hadiza Muhammed Ba"are*



*05*



-----Karfe goma da wani abu Safwan yabaro asibitin sa dake anguwan rimi kaduna daura da iyali hospital kai tsaye anguwan sarki yana nufa cikin motarsa kirar benz baka,cikin slow yake tafe har ya kariso get din gidan nasa hon ya Zuba da hanzari mallam habu ya wangalemasa get yana masa barka da dawowa tareda masa barkan karuwan da'aka samu.



Kai tsaye part din momma yadosa cikin takun isa sanye cikin suit masu ruwan toka rigar likitancinsa sabe a kafadarsa wayarsa ke rike ahannunsa daya kuma yana sanye cikin aljihu,da sallama yashiga falon momma kadaice,afalon zaune kan darduma alamar sallah tagama tana lazimi cikin fara'a ta amsa sallanma tana cigaba da laziminta takalminsa sawu ciki na fatar damusa ya cire kafin ya kariso gabanta ya zauna yana fadin"Momma......"Tadago tana kallonsa cikin Annuri da farinciki,kansa yadora kan cinyanta data tankwashe yagyara kwanciyarsa,itakuma tasanya hannu tana shafa kansa lumshe ido yahau yi yanajin wani farinciki na ratsashi cikin kasala da gajiya yace"momma...Yunwa nakeji"mirmishi tayi kan tashafa addu"an shima yashafa yana fadin "Allah ya karba mommanmu"Allah ya maka albarka babana yajagoranci lamarinka yasama zuru"arka albarka"Atare suka Amsa gabadayansu da Amin harda hajiya mama data fito daga daki tana kallonsu.


Kichen tashiga tadaukomasa dambun zogalan datayimai saboda tasani masoyinshine,ruwa ta hadomai dashi sai furan data damamai don shinema basa rabo da furar'gabansa ta ijeyi tana fadin"kin cikasa da tadi....Maza ci abinci sufiyanu nasan kana jin yunwa"Mikewa yayi yana fadin"kai i so much luvs u Hajiyata kinaji dani"yafada yanajan kulan gabansa fara'arsa takarune dayaci karo da abunda ke ciki yadago cikin Annuri yana kallon momma da Hajiya dasuke kallonsa cike da so da kauna yana fadin"thanks so much hajiyata Allah biyaki da Aljannah"Amin...SufiyanuAllah yayi maka albarka"bata rai yayi yace"kinga hajiya wlh zamu bata basunana sufiyanu ba am Safwan sale safana by name"


Hajiya tace"kai kasan wani Safawa, nibansanshi ba sufiyanu nasani Ato"Tafada harda da jaddawa kara bata rai yayi yamata banza yayi bismillah yafara cin abincinsa,har ya kammala bai sake mgana ba sai daya wanke hannunwansa kana yamike zai kwashe kwanukan momma tayi saurin amsa tana fadin"A'a barshi babana,kaje kahuta kuma kaga masu jego da safe ma hadu"Tafada tana amsa farantin ajiyar zuciyar ya sauke yana juyawa yace"Sai Allah ya kaimu momma"ta amsa da"Allah ya tashemu lafy"Hajiya tamike tayi hanyar dakinta tana fadin"muda ba'a son mukwana lafiyan sai mun tashi da izinin Allah ehe"tafada harda buga kafa dariya takusa subucema momma da Safwan sukayi saurin shanyewa saboda sunsan Halin Hajiya yanzunan takara harzuka.




Mirmishi kwance afuskar sa ya isa part dinsu koda ya shiga falon yadau shuru ga wata katuwar plasma tana yi ita kadai,kashewa Yayi kafin ya nufa bedroom din daya zama mallakinsa kan doruwar gadon ya ijeye wayoyinsa guda biyu kirar i phone8+ da lapcoat dinsa ya fada toile wanka yayi kafin ya dauro alwala,daure da tawul ya fito a kugunsa daya kuma yana goge jikinsa kan dressing mirror dake shake da kyan kwalliya kamar za'a bude shago ya isa kan yahau goga jikinsa da man detol,turaren avon yahau fesawa jikinsa sai da ya feshe ko'ina kana ya zura jallabiya ash colour yashimfida sallaya yadata sallah raka'a hudu yayi kafin yayi sallama yadade yana kwararo kirari ga sarki Allah daya bashi wannan kyauta haihuwa tareda addu'an Allah yakarasa masa juriya da hakurin akan sakina.



Kai tsaye bedroom din sakina ya isa ya tura da yar siririyar sallamarsa sakina na kishingide akan gado wayace ahannunta tana latsawa yasani baiwuce chart takeyi da kawayenta ba Hajiya kari na gefe ta baje sai kwasan barci take harda munshari dariya takusa kubcemai ya waske,kai tsaye ya isa ga jaririn dake kan dan gadonsa yaduka yasa hannu yadaukesa yana mai kare masa kallon cikin kauna,tsantsan kamar da yaron yake dashi yake kallo,hatta da yatsunsu iri dayace,sonsa da kaunarsa mai zurfi,yakamashi lokaci daya,rumgumesa yayi cikin shauki,da soyayyah ta har abada


Sakina dake kwance ta tsuramai ido tana kallon kyakyawan mijinta dogon dan safana tasani har abada bazata daina,son mijinta ba, tana sonshi har gobe kuma tana kishinsa batasan sanda tatashi ta isa kusa dashi inda yake tsaye tadafa kafadarsa ahankali ya waiwayo kwallah tataru a idanunwansa da azama yahada ta da yaron ya rumgume yana fadin"Thank u Sakina....thanks so much sakina"yafada yanajin kamar kwalla zata zubo mai.



Jikin sakina yadan yi sanyi shiyasa tayi huging dinsa back,na tsawon lokaci suna rumgume da juna kafin su saki juna suna bin juna da kallo cikin ido itace tayi saurin sadda kanta kasa saboda kar ya sata cikin wani yanayi.



Hannunta kawai yaja kiii.....Tana biye dashi har bedroom dinshi kana ya saketa ya haura gadon ya ijiye yaron yana kallon sakina cikin ido kan yace"Kinga kyautar da Allah yamana ko"?


kallonsa kawai tayi batace komai ba,yacigada da cewa"Sai wanda Allah yaso da rabon yake basa ammh kinaso kimana wasa da damar da Allah ya bamu"yakareshe fada yana sa idonsa anata,Hamma tayi kan tahaye gadon blanket taja tarufe jikinta tana fadin"Kabarni na huta Dr haihuwa fa nayi ko barci bansamu ba"tafada tana runtse ido alaman bata son damu.




Girgiza kai kawai yayi yacigada da kallon dansa har barci ya daukesa yana kan kirjinsa,koda yatashi daddare yana tsala kuka yatashi sakina tabashi nono tsaki ta buga tana fadin"Don Allah kabarni nayi barci mana"tana gama fadar haka takara jan bargo dama tunda yazo duniya bata bashi nono ba,sai ruwa da aka bashi,shi yayi ta girgizasa asaman kafada har yayi barci saman kujerar dake bedroom din yakwanta yadorasa bisa cikinsa hannunsa zagaye dashi har gari ya waye.





Gari na waye momma ta iso part din nasu,ta iske basu tashi ba kichen tashiga tasa ruwa a kittle tazo tazauna tana jiran tashinsu,Dr Safwan ya fito sabe da yaron yana lallashinsa yatashi sai yaga momma da sauri takarisa ta amsheshi tana fadin"Yaya kuma,kuka yakeyi ne"?Sakarmata shi yayi yana fadin"Wlh momma tun jiya yake rigima"momma tace"to yasha mama kuwa"tsuru yayi mata kan yace"indai ba'a asibiti ta bashi ba ba to bata bashi ba momma"ajiyar zuciya ta sauke kan tasabaashi tana aikin jijjiga har yayi shuru.





Yana zaune momma tamasa wanka tashiryasa cikin kayan sanyin masu kyau yafito ras dashi momma tamika ma safwan tana cewa"nono yake bukata ka roketa ta duba wannan yaron karta dau alhakinsa"cikin mutuwar jiki da kunan zuciya ya amsheshi ya rumgumesa yanajin tsausayinsu har cikin ransa itama momma shi take kallo cikin tsausaya aranta tana fadin"insha allahu HASKE yakusa shigowa rayuwarka Safwan".



Huduba yayi mai kan ya mikama momma yana fadin"Sunan dady nasa masa momma"yafada da raunin murya washe baki tayi tana fadin"kai masha allahu da zuwan sabon megida Allah yaraya ka SALISU"..



WHAT....""

Sakina ta furta da karfi wacce fitowarta kenan daga bedroom cikin rigar barci kai a hargitse,.

Taci gaba da cewa cikin karaji"me kace sunan dan sali wa"? Tafada da renin wayau galala momma tayi tana kallonta yayinda mamaki da al'ajabi ya daskarar da Dr safwan,ashe iskancin Sakina ya wuce inda yake tsammani.




Rike kugu tayi kan ta kariso falon tana cewa"tabdijam da sake an ba mai kaza kai,dan kunga nayi banza bawai ina nufin banason abunda na haifa bane balle awani roro sunan yan da na tsoffi a sama y.......SAKINA....!!! Safwan yakatseta da tsawa wanda ya firgitata har momma dake rike da jinjiri balle shi yaron daya yanka ihu tsawar ita ta data Hajiya kari, wacce take sharar barci cikin tashin hankali ta fito falo, dai dai lokacin da Safwan yace cikin bacin rai"na rantse har ga Allah inkika karisa abunda zaki fada sakina sai na baki mamaki inkin musa kuma"yafada yana kadamata hannu


Tadan tsorata ammh tsabar rashin kunya yasa tace"me zaka iya eye "? tafada tanamasa wani kalon sama da kasa juyawa yayi zai koma daki tabishi tana fadin" Wlh ba wanda ya isa yasama d'ana wani rubabban suna wai sal...."jika ke tas!tas! ya wanketa da mari sai da ta kifa yace cikin bacin rai "wlh tallahi babu wanda ya isa ya sauyama yarona suna nine ubansa kuma nace sunan dana SALISU inga uban da isa yachanza masa suna shashasha kawai wacce batason darajan mijinta ba"yana fadar haka ya shige daki harda bango kofa jikake bam!!!!


Kasa Sakina ta zube tana kuka tana fadin"wlh Allah ya isa,kuma zakasan waka mara sai kayi nadama kuma suna baka isa ba kasama dana wannan sunan ba"tafada tana gunjin kuka,momma tadake rike da jariri ta isa kusa da Sakina zata rikota "tayi saurin dagowa tana ballamata Harara kafin ta mike ta shige daki da gudu tana cigaba da kuka,Hajiya kari tabi bayanta.




...Momma ta koma ta zauna asanyaye Hajiya mama dake bakin kofa tace tana tafa hannuwa"yayi daidai....abun yayimin dadai wlh dahaka yakema shegiya da tashiga taitayinta"momma tayi shuru tana kallon Hajiya dake ta fada tana habaice habaice amsan dan tayi tana jijjigasa tana fadin"wai shin anbashi nono kuwa,momma tace"ina fa taki bashi...."kutumar ubancan yau ga yar iska"ba'a bada nono uwarta ta bata"tafada ahasale kan ta mika mata dan tana ficewa da sauri.




Kai tsaye dakinta takoma ta dauko wayarta kirar Nokia da Safwan ya siyamata to dayake badamuwa tayi da wayan ba shiyasa bata cika amfani da ita ba,kai tsaye gun Habu mai gadi ta nufa tana fadin"mai sunan megida dan Allah duba ko zaka ga ansa kabiru,ya amsa yana duba mata yace"eh Hajiya gashi...Tace yauwa bugamai "tafada tana bubbuga kafa kamar wacce zatayi dambe




Bugu uku kwamishina ya dauka don yana da Nombar Hajiya maman da sallama yadauka yana gaisheta ta katsesa cikin masifa"kabiru kazo kaci ma yar iskan yarka da tsohuwar kilakin matarka mutumci"cikin al'ajabi kwashima ya mike yace cikin rawar murya"wani....Wani abun ne yafaru Haji....?"kwarai zata kashe min jika kuma ta kashe dan data haifa dan taki bashi nono"tafada kit wayar ta mutu ba chaji Hajiya mama tayi kayfci tace"kazo ayi ta kare ko ta gyara ko tabika kutafi tare ina dalili"mallam Habu dake kallonta yace"Hajiya lafiya mai yafaru"?Harara ta zabgamai kan tace"idon matambayi "Tafada tana wani harararsa afusace ta wuce takoma part din sakina.






*Shakira...*




Commet
And
Share
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE...!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza Muhammed Ba"are*



*06*


-----Aikuwa hankalin kwamishina ya tashi dama meeting suke dashi da gwamnah,suna kammallawa,direba ya wuce dashi,kaduna koda ya isa sashen Hajiya mama yafara isa,aikuwa ta lissafamai kaf abunda sakina tayi,Hajiya mama takareshe da cewa"kaduba kabiru duk tsufana bai isa sakina ta ragamin ba,to wlh tsaf take zageni balle Hadiza ai marainiyarta ce.


Hohoho Sakina taga ta kanta don marika biyu kwamishina ya saukemata sai da momma taita bashi hakuri,yayi mata gargadi da kakkausan murya kan tashiga taitayinta inba haka ba wlh tallahi sai yasa da kanshi safwan ya sauwakemata tadawo gidan,kuma taci ubanta,yasa ta dole taba yaron nono agabanshi yakuma ce inta isa ta sauyama yaron suna,Hajiya kari ba yadda zaiyi da ita illar sata agaba suka wuce katsina,har ya tafi basu hadu da Safwan ba domin kiran gaggawa yasamesa daga asibiti.


Washegari sai ga,laila tazo daga lagos ai kwamishina yace tayi maza takoma don ya haramta mata zuwa gidan sakina tunda yagane itace shedan din itada uwarsu,dole laila takoma da tarin takaichinta,salma ce kawai da ummi suka je sunnan Salisu wanda akama alkunya da Adil,sai kawayenta da yan uwa da abokan arziki,Sakina tashaka matuka shiyasa tayi alkwarin gasama Safwan aya Ahannunsa,badai haihuwa ba to ta haifa masa sai ya rena kayansa kuma haihuwa wlh har abada😳😳domin tuni tasa an juyamata mahaifa ita da haihuwa sai sadda tayi ra"ayi,anya Sakina baki *TAFKA DA KUSKURE BA*?


Kwamishina da kanshi ya dauko mai zama da Sakina goggo Ramatu daga kankia tazo tana kula da Sakina da Adil hakika goggo Ramatu taga duniya agidan sakina rashin arziki kiri kiri yimata takeyi da rashin kunya duk dan tana kokarin gyarata shiyasa datagama abunda zatayi take komawa shashin Hajiya mama su barke da Hira dama zamuce ta tarar da mujemu.


Su sakina nayin arba'in goggo Ramatu,takoma tareda shatara na arzikin da Dr Safwan ya hadamata hakika tayi kewar mutanen kirki hajiya mama da momma tatabbatar da Sakina tana kokarin Tafka kuskure matukar tabari suka sallamata.



kamar jira take tayi arba'in tacigaba daga inda ta tsaya washegarin ranar tatafi kano wai anyo mata odar kaya,haka take kullum cikin yawo,kuma Adil agida take barinshi sai dai kaganshi bayan Hajiya mama ko bayan Momma suna aikin jijjiga in dare yayi Safwan ya amshesu wlh har kwallah sukemai aboye saboda tsausayin Dr safwan bai huta asibiti ba kuma agida ba Hutu,shidai kawai yabarma Allah komai ya yarda cewa wannan itace KADDARARSA.


**************************

*Zamfara*
Zurmi...


  Tafe suke su biyu sanye da dogayen hijabai marun colour har kasa da nikabi kafafunsu sanye cikin safa baka ganin komai sai tafin hannunsu,littafaine a hannunsu sun rumgume alamar daga mkrantan islamia suke.



Aisha ce takauda shirun dacewa'Nikuwa *SAFEENA* ina so in tambayeki"?

wacce aka kira da Safina tajuyo tana kallonta ta cikin nikabin ta tace cikin siririyar muryanta"Nasani daman zaki tambayeni....Nasan mganan bata wuce ta mallam yahuza ko"?

Aisha tace"oh ashe ma kinsani....Ni wai meke tsakaninku anya ba sonki yake yi ba"?

Dariya Safeena tayi mai ban sha'awa kan tace"Nima ban sani ba Aisha....Kawai dai inajin wani iri in ina tare dashi"
Duka Aisha tadakamata kan tace"Yar iska ashe dama kina sonsa"


mirmishi kawai tayi batayi mgana ba har suka iso kofar gidan su Safina,Safinar ce taja ta tsaya tana kara rumgume littafanta tace"To sai gobe Aisha ki gaida mama"

"ALLAH yakaimu nima kigaidamin da Ummi yammah tayi shiyasa bazan shigo ba.."


Mikewa Aisha tayi,ita kuma Safina tashiga wani dan madaidaichin gidan bulo,da sallama tashiga,Ummi dake kichen ta fito tana amsawa,


Safina tace "Sannu da aiki Ummi" amsawa tayi cikin farinciki yauwa"Safinatu baiwar Allah andawo" tace"eh Ummi ina Abbah,tace"Yanzu ya fita zuwa massallachi shida Usman.




Shiga daki tayi ta kware hijabin jikinta da Safa da nikabin,sanye take da riga sikat na atamfa sunmata das da ita fitowa tayi tazari buta tashiga ta kama ruwa kan tafito tayi al"wala tashiga ta gabatar da sallar mangariba tadade tana azkar kafin ta mike ta fice ta iske Ummi na kwashe tuwo ta taimakamata suka kwashe suna Hira.


Ta idar da isha'i kenan taji sallaman Abbanta da shi da Usman kaninta,da sauri ta fito sanye da hijabi tana fadin"Sannu dadawowa ABBAH"

Yadago cikin annuri yace"Yauwa HAFIZA SAFINA brkan ki da gida"

Mirmishi tayi kan ta sunkuyar da kanta tana dariya saboda haka Abbanta ke kiranta saboda zamowarta Hafiza abangaren Alqur'ani mai girma.


da sauri takoma daki ta dauko tabarma ta shimfidamai tare da kawomai abincinsa da roban wanke hannu lokaci Daya tana zauna a gefen tana fadin"Abbah yau aka fada mana amkranta zamu jigawa gasan alqur"ani kuma dani aciki"

"Masha Allahu....Allah Yasa albarka Allah ya albarkaci Rayuwarki" ta amsa da Amin ta na mai jin farinciki bismillah yayi kafin yafaraci shida usman ya kalleta yace"Sako hannunki Safina muci tare ko masamu albarkan ci cikin taro"cike da zumudi ta wanke Hannu ta tsoma suna ci suna Hira sama sama.



Ummi Data sallame sallah ta fito tazo tazauna tana fadin"Au abun na ya"ya ne kenan "kai tsaye yace mata"eh na ya"yane iyaye sai su koma baya"

..Safina tace"La Ummi kema fa kinsan tare muke ci da Abbah kema kinso kiyi mgana ne"

"Allah miki albarka,tasani jan magana  ne kawai"

Ummi tayi mirmishi tace tana zama"Ni ne maijan mgana..? yace"to waye,?rigimarki nada yawa Zainabu ko safina bazatayi abunda kikeyi ba"

Kai tsaye tace'Me nakeyi..? tafada tana kallonsa shima kallonta yakeyi kafin yace"Kinfini sani"saurin sunkuyar dakai tayi tana dariya Safina tayi dariya Ummi ta dungureta mata kai tana fadin"Baki da kunya ko"


Yace"kyalemin yata itama tasan gaskiya.Haka suka kammallah cin tuwonsu cikin farinciki da annushuwa.











*Shakira..*


Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy*
_Mallakar:Janafty_💞

*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba"are*



*07*

WACECE SAFINA

*SAFINA ALIYU ZURMI* shine cikakken sunanta,mahaifinta mallam Aliyu zurmi dan asalin garin zurmi ce dake jahar zamfara malami ne wanda ya shahara abangaren ilimin addinin islama,yana da matar aura guda daya wacce ta kasance diyar malaminsane dayayi karatu awurinsa agarin jalingo bafullatanan chan ce,to dayake yakasance na hannu daman mallam alokacin shiyasa ya dauki yarsa zainabu abu ya aura masa batareda yayi duba da shidin marayane wanda baida komai,da kowa ba,hakika zainab tacika ya tama mahaifinta biyayyah,su biyu iyayansu suka haifa ita da yayarta iyami,tare akayi bikinsu da iyamin wacce ta auri wani dan kasuwa a safana ita kuma Aliyu yadaukota suka dawo zurmi da zama.sana'ar saida hatsi yake a kasuwa Allah yasama abun albarka sunada rufin asirinsu.

Aurensu da wata biyu suka samu,lbrin rasuwar mahaifansu,sakamakon gobara takamasu cikin dare hakika anyi matukar rashi,rashi ma mai girma daga baya suka fauwalama Allah komai suka rumgume mazajensu.

sai da Zainab ta shekara,uku kana ta haifi yarta mace wacce aka samata Safina hakika safina tazo dawani al"amari domin soyayyata tuni tayi katutu azuciyar iyayanta,tun tasowarta yarinyace mai hankali da Natsuwa,ga hazaka mahaifinta yazage gurin koyamata ilimin addini tana shekara,goma sha biyu aduniya ta sauke alqur"ani,tana bitan sauran littafai.alokacin ne kuma ta sake haihuwan Usman daganan haihuwa ta tsayamata.


Tana da shekara sha biyar da aduniya ta kammallah sakandiri sch dinta sakamakon yarinyace da duk,garin zurmi ansan da ,da baiwanr da Allah ya bata,tana aji biyu a sakandiri akamata jumping taje ss1,Safina tahaddace sahihul bukhari da muwadda malik tana da sanin kan hadisi sosai gasan alqur"ani kuwa na gari gari ba inda bata zuwa kuma tayi na daya,hatta mkrantansu suna alfahari da ita tuni ta kammallah aji shida yanzu suna ajin manyane.

Iyami wacce suke kira inna bata taba haihuwa ba har Allah ya karbi ran mijinsu to dayake kishiyarta nada ya'ya tare da ita suke rike dasu har kwanan gobe,Safina tana bala"in son innanta iyami saboda har hutu take zuwan mata,da kuma Aminyarta Hajiyar safana wacce wanchan zuwan datayi inna iyami ke fadamata,jikanta yadauketa sun koma kaduna duk da bataji dadi ba shiyasa safanar tafita aranta.

Samari dadama suna kawoma safina kai ammh bata basu dama ba saboda burin mahaifinta na zamowarta wacce al"ummah zasuyi alfahari da ita tareda kasarta Nageria,tana son iyayenta saboda suna da kyakyawan alaqa atare dasu inkagansu suna raHa da ya'yansu kace kannensune.


Safina yanzu tana da shekara goma sha bakwai ne aduniya yarinyace doguwa,bakace domin mahaifinta ta dauko sak doguwar fuska gareta tareda dogon hanci tana bakinta dan daidai matsakaitan idanuwa gareta Safina bawata kyakyawan azo aka gani bane ammh kyanta mai tattare da baiwane,tana da dogon gashi har baya baki silik wanda saboda yawansa yasa take kitso biyu ta rabu dashi.

Dirinta mai tsayawa arai ne domin daga kasanta a tsuke take samanta shima atsuke ba kallo daya zakamata kafahimci ta mallaki baiwa mai tarin yawa ba  sai ka zauna da ita,miskilace ta karshe bamai wayan haniya ba tanada zurfafa bincike kullum agida in bata komai to zaka ganta cikin Nazari ne shiyasa iyayanta ke alfahari da ita matuka.



Bata jin wani namiji ya burgeta ba saboda kaf masu cewa suna sonta bbu wanda yadace da tsarinta,tana son Namiji yakasance mai aji ne kuma yakansance yanada fukafukai guda biyu wato ilimin addini dana zamani yakuma kasance yafi zurfafa ana addini,sosai yakuma zamonto mai alkunya,kawaichi,da dattako,kuma bamai yawan kwaranniya ba kuma wanda yaba duniya baya wanda yafi fuskantan lahirarsa yakuma kasance mahaifiyarsa na raye saboda tasamu makwafin Umminta,Nikuwa nace tab anya Safina zaki samu kuwa🤔



Mallam yahuza ne yakusa hada wannan abubuwan duk da baigama hadawa duka ba ammh taji ta natsu dashi duk da bai furta yana sonta ba ammh alamu sun nuna haka,mallam yahuza malaminsu ne amkrantan dasuke karatu wanda kowa yasan matashine jajirtattace mai ilimi da hangen nesa,shiyasa dashi kadai zakaga Safina na mgana harda mirmishi.


WANNAN KENAN



*********************

KADUNA



----Yau din ma Sakina kano ta kama Hanya tatafi tabarma shazeey Adil shazeey wata kedarace mara sallah Sakina ta dauko a mtsayin Nanny wacce zata reni Adil sai da takwana biyu da zuwa kana Dr safwan ya ganta bakinciki kamar yakasheshi yanzu ace arasa wacce zata renin mai d'a sai,kafura mara sallah kuma ace har yakoyi wasu abubuwa atareda da'ita,dawannan bakinciki ya isa shashen momma Adil na sabe akafadarsa wanda yanzu kimanin watansu uku yayi bulbul dashi sai wutsul wutsul yakeyi ahannunsa.


Momma na zaune cikin dakin Hajiya tana shafamata man zafi akafa saboda tace yau kafan ta matsamata,chan kasan makoshi yayi sallaman wanda momma ce kawai taji shi,kai tsaye ya shigo ya zauna kan stool din gadon yana rumgume da Adil momma takallesa tsausayinshi na tsirgamata.




Hajiya mama taja tsaki"mtwssss...Kai wai da girmanka kashigo ma mutane daki babu sallama" banza ya mata bai tankataba takara harzuka tace"Kai tashi kafita tunda ba dakinka bane haba ina dalili kazo kama mutane zaune kamar kabasu ajiya"
A Harzuke yace"Haba Hajiya kewai baki gane yanayin da

Please Login or Register in order to submit comment