Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanyim murya"Bai shafeka ba plz Tahir karabu dani bana son damu"yafada still idanunsa suna rufe shuru Tahir yayi kan ya jinjina kai yace"I can belive my Dr fall in luv wit Safeena....Any why ta cancanta saboda kyawawan halayyata congratulation mr man wlh kadace ta ko'ina"Abun mamaki sai ga Dr Safwa yayi mirmishi yace'Thanks u mr Tahir bello suraj.






_to ya kuka gani kunga yadda soyayyar Allah take ko,sai Allah yabaka wanda ko a mafarki baka taba tsammani ba,juz imaging Dr Safwan yafada tarkon son Safeena konace sun fadama Juna,kuna ganin salon Safeena bakwa ganin lokaci kadan za'a Shafe babin Sakina arayuwar Safwan ba_?



*Shakira..*



Vote
Comments
Share
Like
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_


*Dedicated to my Sisi of Life Aisha Alto*


*19*



----Koda Karfe sha biyun Rana tayi ta musu a kaduna,duk Da sun sharara gudu ko ahanyama haka Dr Safwan yake sukuku dashi bayi da kuzari lokaci bayan lokaci yana sakin ajiyar zuciya shikadai daga karshe kuma yayi mirmishi shi kadai,Dr Tahir yayita kallonsa yana girgiza kai cos yasani tunda yacemai bayasan damu ko ya mai mgana tsiya zasu tafka dat why yakyalesa akwai lokaci.


Asibiti suka wuce saboda sunsan aikwai tarin aiyuka illai kuwa aiki ya rike su sai dare kana,yamaida Dr Tahir gida yamasa godiya da bangajiya,kana ya Nufo gida hon yayima habu maigadi yataso da gudu ya budemai yana mai maraba Abun mamaki yana sulala motar tasa parking space kawai yaga Hajiya mama tafito da sauri zani ahannu tana Fadin"Oyoyo....Safiyanu angon Safeenatu"tafada tana budemasa murfin mota cikin kasala da mamaki ya fito fuskarsa na nuna almar gajiya yace"Hajiya...Wai baki kwanta ba"..?ta rike hannunsa tana fadin"inkwanta banga dan jikalle na guda daya aduniya ba,to ina lbrin Amarya Safeena yaka ganta tayi ko"..?Tafada harda dagamai gira😂dariya takusa kubcemai yace"oh...My god hajiya dawowata fa kenan wlh am tired"yafada yana yamutsa fuska rikosa tayi tana fadin"Koma u taya ne😂wlh alqur"an baka isa ba sai kabani lbri daga farko har karshe karyan tsiya ke dawani turancinka na karya.."'tana fada tana jansa shi saboda mamaki ma yasa yakasa kwatar kansa jaye dashi har falo tana kwalama momma kira"Ke Hadiza ki fito ga danki yadawo dan nasan shigewa cikin duk na kewarsa ne"tafada tana dankwarar dashi akan kujera.



Momma tafito sabe da Adil tana Fadin"Oyoyo....Babana mutanen Zurmi andawo?Ya sauko yana gaida momma ta amsa da fara'a tana tambayan ya ya barosu da kuma Safeenar ya amsa da suna lpy Allah sarki hajiya ashe kichen ta shiga ta zubomai sauran alqubus din da momma ta musu dazu da miyar alaiyahu taji naman rago da man shanu,tahadomai da furarsa masoyiyarsa tana kawowa Adil na hannunsa tace"Maza ijiye yaron nan kazo kaci abinci dan nasan ka kwaso yunwa'baiyi gaddama ba ya mikama momma shi ammh kiri kiri Adil ya noke shi yasan ubanshi Haj.Mama tace"Kai kaci batar ubanka zonan...Inbanda kana butulu Hadizar zakayima kiyawa"Tafada tana rikosa harda dunkurinsa yayi nakwa nakwa yana kallon babansa zai yi kuka Haj.Mama tace"kul kamin kuka wlh in ci ballagazar uwarka"Ashhh....Dr Ya furta kan yace"plz hajiya stop it....Adil iz juzt 6 month fa mai yasani"yafada yananuna rashin jin dadinsa"Haj.Mama tagyara zama ta sunkuyar da kanta tace"Gani dakeni habule ko in kwantama ne..?tafada harda rusunawa,banza da ita yayi kan yayi bismillah yafara cin abincinsa Haj.Mama Tace"Au dan batan uba kawai wlh sufiyanu kafita idona wai tun yaushe nake cema kadaina zagina da wannan yaren eye..?"tafada da karfi,banza yayi da ita cos baisan hayaniya sam itakuwa ta kulu tadinga masifa tanayi tana hadawa da Adil oh ni jami ko meye ruwan Adil anan oho.



yana kammalla cin Abincin ya wanke hannu ya mike yadauko kwanon furar yana cewa"momma zan je na kwanta wlh gabadaya agajiye nake..But tomorrow zan yi mgana daku"Daga haka yafice momma tanamishi fatan tashi lpy ita kuwa Haj.Mama binsa tayi da tsaki mteswwww tace"Aikin banza da wofi yo harni za'a ma gorin da' dan ubanka inda ban haifi ubanka ba za'a haifekane kuma in kayi zuciya zo kadauki dan kamaida ma uwarsa dama mungaji da reno wlh"Tafada tana dunkurar da Adil akasa ta mike tawuce fuu tana fadin"Ni za'ayima iskanci da bura uba.muda mukaga jiya mukaga yau muna shirin ganin gobe kuma da izinin Allah🤣🤣🤣



Adil kuwa ya fashe dakuka momma tayi saurin daukansa tana jijjiga sa ba daman ta tanka haj.Mama tadawo kanta ta lallaba ta kwashe kayan da Dr yaci ta kai kichen,takoma daki tana lallamin Adil shikuwa yayi luf a kirjin momma yana ajiyar zuciya _ho yahadu da fushin haj.Mama wo_




Yana zuwa sashensa abun mamaki Sakina na hakimce kan kujera tadora kafa daya kan daya sanye take dawata doguwar riga ta kamfanin armani baka rigar ta matseta kannan babu dankwali gashi yaji gashin doki abun haushi abun takaichi yan aikinta guda biyu ke durkushe gabanta daya na mata tsausa daya na sama ta jan kumba wa'iyazubillah tana yar musulma tana salla tana komai kumbanan zaro zaro kamar ta horo tayi wani shame shame kamar sakarya kallon daya yayi musu yayi saurin kauda kai ,ko gaisuwansu bai amsa ba yayi gaggawan shigewa master bedroom dinsa domin jiyayi wani karni karni na tasomai yanaji kamar zaiyi amai.



Sakina tabishi da harara kofin dayake hannunta cike da madarar hollandian ta kurba kan ta furta afili"Rubbish.....Tana kallon yan aikinta dasuka zuramata ido tadaka musu tsawa dole kowacce ta shiga taitayinta.



Yana shiga ya maida kofa Ya rufe fridge yafara isa ya sanya furarsa ciki kafin yafada toilet yayo wanka tareda dauro al'wala daure da tawul ya fito daya akansa yana tsane ruwan kan dressing mirror ya isa yana shafama jikinsa mai sai daya kammallah ya feshe jikinsa da body spry kana ya zura jallabiyan blue ya shimfida sallaya ya data sallah.


sai da yayi shafa'i da wutiri yadade yana addu'a wa kanshi da zuru'arshi gabadaya sai ga _*Dr Safwan sale Safana durkushe gaban rabbil izzati yana rokonma kanshi da Safeena rayuwa mai dorewa ta har Abada*_ yana kammallawa ya ninke sallaya ya ijeye saman stool ya koma ya kwanta kan gado hannu ya mika ya jawo wayarsa dake a ajiye a side drower din gadon kenan ta bude kofa ta shigo babu ko sallama wani kamshi ne mai tare da kwauri kwauri ne yadake hancinsa shyasa yayi saurin dagowa,baki bude yake bin Sakina da kallo sanye cikin wata uban night gwon pick colour kafinka tsirara saboda gabadaya surar jikinta ta bayyana rigar batada hannu daya gareta,tana wani takun yanga adole ita zataja hankali miji ammh kash bata iya abun ba kwata kwata bai mata kyau ba.


Bakinsa abude ta kariso kusa dashi ta zauna tare da cewa"Dr nah...Rufe bakin"Tab.....Lalle yarinyarnan yar tasha ne wato Dr na haka yafada aransa,binta yayi da kallo aransa yana ayyana tabbas tana bukatar wani abu ne ammh matar da yadawo ko kallonsa bata yi bane yanzu zata wani kwaso jiki miya miya tanawani fadin wai Dr nah. _kai Dr Safana wai miya miya kamar wata mage_🤣





Shafa sajensa tayi tana fadin"Brk da hutawa likitar zuciyata..."tafada tana wani fari da ido daure fuska yayi yasa hannu ya cire hannunta yana fadin"quickly ask wht u want.....Zan kwanta ne"yafada yana kallon idanunta tsam tayi domin taga yana neman harbo jirginta kanta maze ta yi wuf ta fada jikinsa tana mai kukan kisss biye mata yayi cos yana so yaga inata dosa bakinta tasanya anashi tana sumbatarshi hannunwanta na shafa kwantattacen gashin kirjinsa cikin wani salo yayi kokarin kar ya biyemata ammh ina zuciya da gangan jiki na bukata tuni ya tallabeta yayi saurin birkitata tadawo kasan sa yafara aikamata da nashi zafafan wasannin itama tana maida masa.




Shudewar awanni biyu ya fito daga toilet kansa na digan ruwa Ya kalli Sakina datayi share share kamar jaka yayi tsaki yana duba kirjinsa yace"Sakina kewai wata irin mai kunni kashin ne...Har saunawa zance miki kidaina pixsing din kumbunan kina yar musulma infact ma kina jimin rauni look out"yafada yana nunamata yadda ta karceshi a kirji tayi wani lum da ido kan tace cikin sakarci"Haba my Dr kai komai nayi banyi daidai ba"Tsaki ya sake ja mtsweee kan yace"kinga don Allah ki tashi kiyi wanka kinsan ban hada gado dake da najasa and kuma ki tabbata wlh kin zubar da wannan turaran aljanun nan"Yafada da serious matter Tasan Halinshi dole yasa ta mike tafada toilet tana tuna turaren dayace na aljanune hajiyarta ta kawomanata kan tayi amfani dashi ko me tace Safwan yamata jiki narawa zai mata ammh gashi bata ma kai ga tambayaba ya kushe abun.


Koda ta fito har yakoma ya kwanta ita agurguje tasanya jallabiyansa tahayo gadon tadora kansa akirjinsa tana wasa da gashin daya kwanta da dashin ruwa tafara mgana cikin sanyin murya"My Dr.....Tafada tana dagowa" umhmmm"yace mata kan taciga ba da cewa"ammmh.....Ammmmh....Dama game da businees dina ne"sai kuma tayi shuru yace"inajinki business women zaki kara bude wani reshe ne aturai"yafada da yar dariya tace'No.....Kudi zaka bani 2million ina so na shigo da wasu bags ne zuwa nigeria kuma duka kudaden hannuna in na hada baza su isheni ba shine nake bukatar taimakonka amatsayinka na mijina"Ta fada wit full comfident.



Mikewa yayi yana tuntsuran dariya harda rike ciki zuru tamai da ido tana kallon sa domin batace tataba ganin Safwan na dariya haka ba daure fuska tayi ta mike tana fadin"Am not a fool....Safwan stop It.."tafada tana kokarin ficewa,saurin mikewa yayi yasha gabanta yana Nuna ta da yatsa yafara mgana"SAKINA KABIR KANKI....gaskiya saiyau na yarda baki da kunya do u think am fool dazan dauki kudi har 2million na baki"yafada yana nuna kanshi kan yadaure fuska yace"oh kin manta sanda keda uwarki kukacemin banida kudin zan iya dawainiyarki sai dai ke kiyi dawainyata to nikuma har abun zuwa anemi wani abu aguna ne ai nazata ke kin isa kima kanki komai"yadakata kan yadaure fuska yace"Yanzu ne nakeda daraja irinta miji agurinki....To bari kji wlh tallahi indai ni Dan Hadiza ne da Sale bazan taba baki kudina ba koda rance ne kuwa",yafada da kakkausan murya sororo tayi idanunta sun ciko da kwallah kam tanuna kanta tace"Baza ka bani ba..?"kai tsaye yace"yes...Ko kudin kine ai kudi yana gurin bussiness women so kiyi amfani da abunda ke hannunki cos Kudin Dr Safwan bana ci bane abi..?"yafada yana zakuda kafada alamar ko ajikinsa .



Idanuwanta yakawo ruwa ta nuna kanta tana fadin"Ni safwan kaci ma mutumci ko...?.Ya amsa da "eh....Ko zaki ramane..?"girgiza kai kawai tayi kan tafice tana kuka tsaki yaja yace"shashasha kawai gobema kidawo ni dake muga wanda zaiyi laushi yana fadar haka yayi swith off din light din ya kunna dumlight ya fada gado yana addu'an kwanciya barci.



sakina nakomawa daki tafada kan gado ta fashe da kuka wayarta tadauka da tsohon daren tadinga kiran hajiya kari no answer dole tayi wurgi da wayar tana shure shure kan katifa maganganun Safwan nakara dafamata zuciya,aranta tanaji kamar takoma tamaidamai martanin mganansa _chai...Daga baya kenan meyasa lokacin dayake miki mganan baki mayar mai stupid kawai_🤨




*******



Koda garin Allah ya waye cikin farin ciki Dr ya tashi domin yayima kansa alkwarin daina damuwa da al'amarin Sakina domin ya shirya tsaf don fito na fito da ita don ya nuna mata kuskurenta dan yasan sakina da taurin kai bata bari aga gazawarta.




Tun 7 ya fita domin yasamu emergency cll daga asibiti ko sashen su momma bai shiga ba bai samu kansa ba sai after 12 office din DR Tahir ya biya suka gaisa kan ya komo nasa isa yayi kan kujerar office din nashi yazauna yana jingina kansa alamar gajiya idanunsa na lumshe cikin sakan uku ya mike firgigit yana fadin"oh my god......Na manta yayi saurin zaro wayarsa yana latsa wasu nombobi kan ya kara akunne.




Safeena dake cikin dakin Ummi tana muraji'a cikin suratul yusuf taji wayar da Dr safwan yabata tadau tsuwa zumbur ta mike ta ijeye qur'anin tadauki wayan jikinta na rawa taja inda taga kamar nanne wurin dauka cikin sa'a kuwa tana karawa akunno muryashi ta dakin dodon kunnenta"yanmatana....Badai aji ake jamin ba...?" rufe ido tayi kamar tana ganinshi kan tace"Assalamu Alaika...Ina yini"ta fada da siririyar muryanta cikin kasala yace'oh...Srry wa'alaikas salam...Lpy kalau yan matana shine ko ki nemi ko..?"Tura baki tayi kafin tace"to ka nuna min yadda ake bude wayarne"tafada da shagwaba tsam yayi wani abu na zirgamasa kafin yace"oh......Am srry na sha'afane kece kika mantar dani kina ta kuka"la....Ni yaushe nayi kuka..?"yace"la...Akofar gidan Abbah kin tuna.?"yafada yana kwaikwayonta tsuntsurewa tayi da dariya kan tace"kai ko....Yace"ke ko....Yafada yana siririyar dariya"rufe fuska tayi tana mirmishi shima mirmshin yakeyi yana fadin"Yan matana sarkin kunya...Ya Ummi na da Abbana ina usman..?"ta amsa suna lpy ,yace'me kikeyi ne yanzu..?"tace"muraji'a nake tunda yanzu bazuwa mkrantan nake ba kada haddan ta gudu"tafada tana mirmishi da sauri yace"ah..Meyasa kika daina zuwa mkrantan..?"tura baki tayi kamar yana ganinta tace"ba Abbah bane yace nadaina zuwa ba wai yanzu ina karkashin ikon kane"farinciki ya cikamasa ciki ko bakomai an nunamai yanada matsayi rausayawa yayi kan yace"Hakane mganar Abbah don mkranta kigayamasa kicigaba da zuwa kafin nazo nayi caraf dake"yakareshe fada harda kanne ido daya kamar tana ganinsa saurin rufe fuska tayi tana siririyar dariya cikin shagwababbiyar murya tace"Ni....Kabari bani so"shikuma ya amsa da cewa"Nikuma inaso yaza ayi kenan...?Yafada yana dariya itama dariyar take tana rufe fuska janta ya cigaba dayi da hira tun bata saki jiki dashi ba har ta saki jiki suna hira suna dariya sunfi awa suna waya sai da wata Nurse ta shigo tana fadin"Sir....Emergency .....Ok yanmatana i u clll u later daga haka ya ktse kiran ya fice da sassarfa.

Itakuwa Safeena rumgume wayar tayi tana jin wani abu na fitowa daga kasan kirjinta yana kwarara asassan jikinta tafada kan gadon ummi tana fadin"I miss u Uncle....sai da tafada kana ta rufe baki tana kallon kofa sai da tattabar da bakowa kana ta jawo wayar tana kwatanta yadda Dr yafada mata zata bude password din wayar illai kuwa yabude batasan sadda tace eyyyyyyyye...... ba.








*Anitha...*


Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞




*20*



"Wurin ma'ajiyar hotuna tafara shiga domin tadan san kan waya domin Aisha yayanta yataba bata wata tecno D3 _my first phone wo...Ammh sai da akasamu barawo ya saceta_😡abun mamaki hotunan Dr ne dana Adil kawai aciki kala kala iya kallonta wani suna kwance wani suna zaune wani yagoyasa gasunan dai sai iya kallanta,abun da yaba Safeena mamaki shine shin uwar yaron nan basu tare da Dr ne domin taga koda sau daya bata ganta acikin hotunan ba sai dai shi da Dr to kodai ta rasu ne..? tayi saurin rufe baki aranta tana cewa"Da ta rasu da Ummi ta fadamin"haka dai taita kallon hotunan babu hoton daya burgeta sai wani hoton Dr yana sanye da american suit,black and white ya daure wuyansa da tektie baki kansa yasha gyara yana maiko hannunsa sabe da rigar likitocinsa yana mikama Dr Tahir abu abakinn wani office ya juyo da gilashin dayake karamasa da kwarjini yana dariya aka dau hoton hakoransa farare reras suka bayyana hakika yayi kyau matuka a hoton wanda har Safeena tayi serving dinshi a Fuskar wayar saboda kyan dayayimata.

tana cikin daki taji sallamar Aisha suna gaisawa da Ummi kafin tatambayi Safeena Ummi tace mata tana ciki da Sallama Aisha ta shigo Safeena ta amsa tana fitowa daga uwardakan Ummi hannunta rike da waya tace"Yar halak yanzu nake zencencenki araina"Harara ta sakarmata kan tace tana zama kan kujera"Bawani nan ai ni wlh baruwana dake yanzuma zuwa nayi naji lpy baki zuwa mkranta kwana biyu"..?Zama Safeena tayi kusa da ita tana fadin"Allah sarki kawar arziki...Dalilin dazai kawoni kenan"Tafada tana dafata mikewa tayi ta isa ga botikin dake dakin tasanya kofi ta debo ruwa tana juyowa taga Aisha rike da wayar tana juyawa cike da mamaki gabanta ta ijiye ruwan tana fadin"Sha ruwa Aisha kafin muyi mgana"Shuru Aisha tamata tana bin wayar da kallo chan ta shafa saiga hoton Dr ya bayyana wow...Shine abunda Aisha ta Furta tana bin hotonn Dr da kalon kafin tadago tana kallon Safeena datake kallonta tace"Kawata waye wannan gayen..?...Ke wayarma tawaye wai? Safeena tayi mirmishi ammh aranta taji zafin yadda Aisha take kallon hoton Dr tana Shafawa cike da shawa'a da burgewa _ho kishi🤔 tashi tayi ta isa ga windo Dakin kafin tace *MIJINA NE* da saurin Aisha tace"Mijinki kuma? tafada da sigar tambaya da mamaki juyowa Safeena tayi tana mirmishi tace"Eh...Mijina ne Aisha wanda Abbah yadauramin aure dashi kusan wata daya dawani abu da suka wuce"Sororo Aisha tayi kan ta mike tsam ta ijiye wayar takama hanyar ficewa tana fadin"Kinga nidai nayi gaba don aiki nake na fito ban iyawa da shirmenki Safeena"Safeena tayi mirmishi tace"Wlh da gaske nake Aisha nima yadda kikaji haka naji lokacin da Abbah ke fadamun"cak Aisha ta tsaya kan ta waiwayo tace"Wai da gaske kike Safeena..?"Karasowa tayi tadafata kan tace"Da gaske nake Aisha dama shine abunda zai kaini gidanku kenan".




Tsuru tamata da ido kafin tazame hannun Safeena ta isa ga wayar tashafa hoton Dr ya bayyana ta nuna ma Safeena tace"Kina Nufin wannan balarabe ko ince bature shine mijin naki..?


Dariya Safeena tayi kan ta isa kusa da Aisha ta amshi wayar ta kurama Dr ido tace"Kema kina tamtama ko Aisha..?"tafada tana kallonta kan taja hannunta su isa kan kujera tacigaba dacewa"Nima haka naji lokacin dana fara tozali dashi amatsayin mijina Aisha wlh babu karya Dr Safwan sale Safana shine mijina"Aisha tayi shuru tana kallon Safeena kan tayi wuf ta rumgumeta tana fadin"Kawata u ar so lucky wlh....Nayi murna sosai lalle kin tabbata mai sa'a


Nan Safeena ta warwarema Aisha komai tundaga farko har karshe Aisha ta jinjina kai tace"Ikon Allah kenan Safeena wlh in Allah yaso ka da Ni'imarsa bbu mai hanawa...Kinga abun Allah ko"Safeena tace"wlh ko amafarki bantaba tsammani ba Aisha sai gashi Allah da ikonsa ya zartar da komai"Aisha ta jinjina kai tana kara tabbatarma da Safeena ita mai Sa'ace.




Haka Aisha takoma gida tafadama mamanta ita kin yarda tayi sai da tasawo hijabi tazo ta tambayi ummi,Ummi tace"da gaskene kana ta yarda tasa albarka tareda da addu'an zaman lpy.






****

Itakuwa Sakina tun da tatashi ko takan Dr bata bi ba tashirya kayanta a trolley dinta tafito ta shige motarta ta dinga zabga hon habu mai gadi yana kewaye shikuma iliya bayanan hakanan ta jira domin jin kanta bazai barta ta fito ta bude ba, aikwai Habu yasha tsinuwa kamar itace uwarsa harda cewa zata sallameshi tunda yagaji da aikin tana cikin mai tijaran sai ga Haj.Mama ta fito dama tunda taji hon din namarasa hankali tasan jakarce,aikuwa tana zuwa sakina tayi shuru haj.Mama tana kallonta sama da kasa kafin kafin tace"Ikon Allah ke inbanda rashin kunya da fitsara kitsaya gaban sa'an ubanki kina zagesa harda cewa zai bar gidan ko"..?Takareshe fada ta tana rike da kugu Sakina tace"plz hajiya niban saki cikin shirgina ba plz stay out"Haj.Mama tace"kinci ubanki nikike cema pulaz🤣hala nayi kama da sakaryan uwarki ce to wlh bari kiji ke kanki inbakiyi hankali dani ba to sai kin bar gidanan don banga uwar dakike tsinana mana ba"Sakina tayi tsaki mtseswwww tashige motar ta ta kirar vibe tana fadin"Inkin isa in yadawo kisa ya rubutamin saki uku,sai na tabbatar da kin isa uselless kawai"Tafada tana kokarin zuge glass din motar Haji.Mama takarisa jikin motar tana fadin"Ahayyye....Tayaro kyau take bata karfo ai ni maryamu bazan taba yarda Safiyanu ya sakeki ba yanzu so nake ki kirbi abunda kika shuka da hannunki kuma Alhamdulillah abun da namiki tanadi yakusa isowa gareki wlh sai kin raina kanki tunda ke ballagazar macece wacce batasan darajan kanta ba"Tana gama fadar haka tawuce tana fadin kai megida wuce kakama harkan gabanka tunda ba ita ta daukeka aikin ba aikuwa da gudu ya wuce itama Hajiya ta shigewarta sashensu tana wake wakenta.



Sakina tayi turus acikin mota bakincikin kalaman Hajiya dana Safwan suka taru suka sata fitar da kwallah kamar ita Sakina mai aji da daraja ake cema ballagaza dama jiya Dr yace mata shashasha,tashare hawayenta tace afili wlh both of dem they will pay 4it kafin ta kwarara hon habu yazo da sauri ya budemata saura kadan ta takeshi sai da ya kauce ya rike baki yayi yace"Kai wannan mata baki kyale kowa ba shikanshi yallabai baki kyaleshi ba balle uwarsa da kakarsa balle mu yan aiki,tab...Ubangiji yamana maganinki"yafada da karfinsa kan ya rufe get ya koma kan bencensa.




Katsina ta dikko dakin kara ta nufa saidai haj.Kari taganta kwatsam tana mata kuka dakyar tasamu tafadamata duk abunda ke faruwa Haj.Kari ta mike ta lailayo ashar tace"babban bura ubanchan har ni za'a kawoma iskanci....Shi Safwan din harwani tsiyane balle uwarsa da wannan yamutsatsan tsohuwar har ta isa ta saki kuka, ita din banza to wlh bari Abbanku yazo Sakina nagaji dawannan auren yazo yasan yadda zai yi dashi"tafada tana huci kamar mayunwacin zaki _chau chau Haj.Kari Allah dai ya biya_ Sakeena tayi saurin cewa"a"a Hajiya wannan ba mafita bane kema kinsan wlh in Abbah yaji zai iya tsinemin kema kinsani"haj.Kari tayi shuru kan tace"eh...Kuma hakane shima sun asirceshi ji yake in aka taba yaron nan kamar antaba ubansa"Tafada harda yamutsa fuska Sakeena ta jingina da kujera tace'kyalesu hajiya so suke suga na ijiye kasuwancina indawo ina kula dashi da uwarsa inzamarmusu jaka"Haj.Kari tace"Ina har abada wannan bazai taba faruwa ba domin ni ban haifi malalatan ya"ya ba kudine zan hada na hannuna laila ma zan mata waya takawo abunda take dashi ki wuce kikama hanyar ki tafi ki saro kayanki kizo ki dasa daga inda kika tsaya kibarmin komai ahannuna ninasan matakin da zan dauka"Sakeena ta saki dariya tana fadin"Dat iz my hajiya shiyasa nake sonki"haj.kari tace'karki damu in ban tallafa muku ba wazai muku tunda irin uban da Allah ya baku kenan solobiyo"Sakina tasaki dariya tace"Hajiya Abbane solobiyo kuma ..?tace"kona yi karya"Sakina tace"A"a Hajiya da gaskiyarki"Atare suka sheke da dariya harda tafawa

_oh ni jami Duniya harta kaimu ga haka_🤔


****


bayan la'asar Dr yadawo agajiye yake dat why yafara isa shashensu sai da yayi wanka ya huta kana ya fito baiji duriyar Sakeena ba bai damu ba dama kuma ba motsinta yakeji ba har zai fita sai yasamu kansa da tambayan daya daga cikin yan aikinta ina take kai tsaye tacemai tun safe ta fice bai damu ba illa zakuda kafada yayi yafice zuwa massallaci sallar mangariba kana yadawo ya wuce shashen su momma chan ya tarar da haj.Mama da momma suna hira,hajiya dai batai fushi ba saida ta tsaitsayeshi yafada musu yadda sukayi da mahaifin Safeena ya kareshe da cewa"Yanzu na yanke shawarar Safeena zata zauna gidana dake anguwan sarki tunda a nan din babu inda zata zauna.



Haj.Mama tamike tace"kul...Karma ka fara Acikin gidan nan Safeena zata zauna anyi ba'ayi ba kenan ai inhar Safeena tabar gidan nan ban Nunama ballagazan matarka na amsa sunana maryamu ba"Dr Safwan yace"To hajiya ina gun da zaki sata..?Kai tsaye hajiya mama tace"dakuna uku ke shashenka ko?tafada tana kallonsa da kai ya amsa tace"To ka gayamata ta kwashe kayanta adaya ka saka Safeena aciki tunda duk kaine mijinsu in lokacin da Safeena zata koma chan yayi nida kaina zan fada maka"Tana gama fadar haka tatashi tawuce har takai kofar bedroom din tajuyo tace"Umarnine ba shawara ba kafara shiri cikin sati biyu nakeso Safeena tatare,tana fadar haka tashige daki Dr Safwan yayi ajiyar zuciya aransa yace"Hajiya daru....Ita kuma momma tana ta jinjina kai kafin tace"kaji abunda hajiya tace ko"Ya gyada kai tace"to kabi umarninta kazauna lafiya"itama daga haka tashige kichen zata kawomai abinci shikuwa Dr Safwan yayi shuru yana so yagane dalilin hajiya na zartar da wannan hukunci ammh ya kasa.



_hoho hajiya mama kinayi muna jin dadi Jamuje Allah ja da mulikinki haj tamu_✋✋✋










*commet, share Vote domin kwarin gwiwata...*


*Shakira..*
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_



*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*


*Wannan Shafin na yau Gabadayanshi na Masoyan HAJIYA MAMA ne❤️tace na gaya muku Tana godiya da Sakonnin Jinjinawarku gareta Allah ya bar kauna Tace na sanar daku Gabadaya Masoyanta na Wattpad da Whatsap SON SO FISABILILLAH*



*21*


" Koda kwamishina yadawo ya tarar da Sakina agida fada yahau yi yace meya kawota sai ta shirgamasa karya da cewa da izinin Dr Safwan tataho aikuwa baiyi kasa agwiwa ba yakirashi yake tambayansa abun mamaki Dr ya amsa masa da hakane cos bayaso ta dalilin sa Sakina tarasa albarkar mahaifinta.



****


Babu yarda Safwan ya iya da mganar haj.Mama domin ko momma bata tsallake umarninta daya fadama Tahir shima yayi na'am da batun na hajiya domin yace abunda babba ya hango yaro ko yahau rimi bazai hangoshiba.



kullum sai sunkusa raba dare suna waya da Safina sun maida abu kamar ibada

Please Login or Register in order to submit comment