Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutum ke ciki ne eye"?yafada dadan karfi galala tayi tana kallonsa kan ta kwace kafarta tagyara zama tace"To Habule gani dakeni kaji tunda wuyanka ya isa yanka"tsaki yaja kawai ya mike yana gaida momma kan ya mikamata Adil yana fadin"momma ki rikesa agurinki zan tafi asibiti," tasa hannu ta amsheshi kan tace"Adawo lafy Allah yabada sa"a" ya amsa da Amin



Hajiya mama tafara salallami tana fadin"yau anyi tsinanna yau din ma ficewa tayi tabar d'an oh ni maryama naga takaina"tafada harda dora hannu akai,Dr Safwan ya isa bakin kofar yana fadin"Momma ko anzo karbarsa kar kibada shi.. Wai sakina arniya ta dauko wai ita zata renanmim d'a,dan Allah momma ki rike adil agurinki nasan bazaki gazaba"Ai da sauri Hajiya ta sauko daga kan gado tana fadin"Ar....Me lalle sakina yar tasha ce yanxu haka ta raina mutane to wlh billahil azim sai tabar gidannan bazan zauna da kedara ba agidannan ba wlh"Tana fadar haka tabi bayan Dr safwan tafice fuu.


Yana kokarin shiga mota yaga ta shige sashensa,kada kai kawai yayi ya shige mota yabata wuta don ahalin dayake ciki baida lokacin hajiya mama.

Shazeey taga bala"i domin hajiya mama tadunga mata watsii da kaya bayan tagama tasa yan aikin Sakina sujata sufitar da ita dagan gidan,fadi take"kuja shegiya kafurar banza agidan nan wlh baki isa kizauna ki koyamana kafurci ba kuja shegiya nace🤣🤣🤣sukuwa suna janta tana kuka tana rokon hajiya mama tana fadin"Madam plz help me....Srrry ho..."sorin uwarki inkika kara kirana madam sai kinci ubanki"waje suka watsata sai da kanta yabugu da kasa da sauri tace"jesus ai da wani gudu Hajiya tabita tana fadin"mun shiga uku zata konamu jejesas din babanki😂 agidannan,Ai da gudu shazeey ta rarimi kayanta megadi yabude mata get tayi waje,Hajiya tace"tsinanniya kawai da ki tsaya dasaina na fasa katon kanki kamar na kwakwa🤣🤣🤣🤣kowa na kunshe dariyarsa sabida in Hajiya taganka wlh sai kasani.

Momma tana gani ammh batayi mgana ba saboda sanin halin hajiya yanzunan ta dawo kanta Ranar hajiya wuni tayi tsinema sakina da uwarta daga karshe akace"ai ba shegen d'a irin sufiyanu sai da na hanasa daukoma yarinyannan saboda nasan arina ko ganin uwarta kamar wata tsohuwar kilaki amma dayake kunnen
kashi gareshi ya kwasomana bala'i har gida,daga baya kuma aka hau share hawaye tana fadin"Allah ya jikanka salisu dakana nan a raye dabai auromana tsinanniyan yar"nan ba🤣🤣🤣🤣Haka hajiya ta wuni ashar.


*Hoho sakina kinga ta kanki tunda Hajiya mama ta tsaneki*😂😂😂








*Anitha...*


Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞

*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*

_Ina mata yan kwalisa masu Bukatar su Fito su kere Sa"a cikin Sa"anni ko matan abokai ko cikin kawaye..? Ina Mata wadanda ke Bukatar Gwangwajen ya"yansu cikin kayan alfarma domin kere sa"a da Fitowa cikin Alfarma cikin Sa"aninsu,Toh duk kusha Kuruminku ina tafe muku da Wani Karin Albishir ko kuna da Labarin DIJA COLLECTION,wanda ya Hada komai na kayan kawan Mata da maza domin fitowa Tsab,da Sanya mata suna Dagawa..?Ki hanzarta ko kuma mu hanzarta wajen samun daman zama mace yar Kwalisa muna saida komai na kayan adon mata da maza da yara,Irinsu Atamfa,leshi,Material,Takalman mata dana maza na yara dana manya,akwai dan kunnaye masu kyau da Tsari,kina bukatar mayafai na nuna Tsara..? Toh duk zaki samesu a Dija Collection ,kina bukatar Abaya.. ?shima karki damu duk zaki samu a Dija Collection kayanmu suna da Ingancin Domin ingancinmu ne yasa muka Cigaba,Zaku iya Tuntubarmu ta wannan Nombobin wayar kamar haka 07045112780,ko kuma 09036617473,Sai kunzo...karku Manta Siyan Nagari mai da Kudi Gida.._

*08*



------Koda Sakina tadawo ta iske hajiya mama ta kora mata shazeey Ranta yabaci tadinga yada mganganun acikin gida,takira hajiya kari tafadamata,suka taru suka dunga tsinema Hajiya mama ita kuwa Anty laila cewa tayi"Fine and good sai kibarmusu dansu su rena tunda sun raina kokarinmu don dai bazaki zauna ki ijeye kasuwancinki kina masa rainan d'a ba"


Sakina ta shaka game da Hajiya mama Shiyasa ta kudiri niyyar yi musu abunda bazasu manta da ita ba,ammh duk maganganun data keyi,iya shashen ta ne,don tasan wacece hajiya mama,in Taji ta jita bazata ji da dadi ba.

*Zurmi...*


    Usman ne ya sheko da gudu cikin gida,yana haki Ummi dake bakin rariya tana wanke wanke,tasaki aikin tana fadin"Usman...Lafiyarka kuwa?"yana haki yace"Ummi yaya Safina ce nagansu yanzu suka dawo"

Ummi tasaki mirmishi tace"ikon Allah...Allah yadawo dasu kenan"?

"eh...."yabata amsa kan yakara shekawa da gudu,yakara ficewa.

Ummi ta rausayar dakai tace,"oh Usmanu ba dama,ta cigaba da wanke wankenta cikin farin ciki na dawowar yarta daga jigawa gasar karatun qur"ani ta jaha na Fidda gwani kwanansu biyu.

Ta kammallah kenan taji sallaman yar' tata cikin farunciki tareda rakiyar kawarta Aisha,da gudu tarumgume Ummi tana Fadin'oyoyo Ummi nayi kewarku wlh"

Ummi tana dariya tace"Oh Safinatu na barka da dawowa "Safina tace"yauwa Ummi nasameku lafiya"?

Aisha tace"la Ummi shine dan kinga Safina kika manta dani,Ummi tayi mirmishi tana fadin"haba ai har abada Aisha kema diyatace kamar yadda Safina take diyata"Mirmishi sukayi tare Usman kuwa yana jidan kyaututtukanta yana shiga daki dashi


Aisha tace"Ummi ku tayamu murna Safina taci lambar yabo ta daya  a jahar mu ta zamfara"guda Ummi tasaki tana nuna Farincikinta.


Abba daya sawo kai cikin gidan yake fadin"Ash....Ash...Zainabu guda kuma"?

ta amsa da cewa "Nuna farinciki ne Abbah diyarmu tasamu nasarar cin gasan zuwa gasan a kasa  gabadaya zata wakilci jahar zamfara.

Yana kawata fuskarsa da fara'a yana fadin"Masha Allah yakamata ki furta zainabu ba guda ba ko so kike hancinki awuta"yafada da tsigar zolaya gabadaya aka sa dariya.

Safina ta isa kusa dashi ta durkusa tana fadin"sannu dadawo wa Abba"ta fada tana amsan ledar dake hannunsa cikin Annushuwa ya mikata mata yana fadin"Masha Allahu Hafiza safinatu natayaki murna da sauran al"umnah gabadaya Allah yasa abunda kikasa gaba ya amfaneki da sauran al'ummah gabadaya"

Atare suka amsa da Amin Abbah,Aisha ta gaisheshi ya amsa yana samusu albarka kafin Ummi ta zuba masa ruwa  a buta ya gabatar da al'awala shida Usman suka wuce massallachi.


Sai da taraka Aisha gida kana tadawo tayi sallah suka shimfida tabarma suna Hira da Umminta tana bata lbrin abunda ya faru achan gurin gasar fidda gwanin,Abbah ya yo sallama suka shigo Safina ta kawomasa Abincinsa da roban wanke Hannu,sai da ya kammallah,ya wanke Hannu kana yace"Safina..."Ta amsa da Na'am tajuyo tana kallonsa tana basa hankalinta.



Yafara da" Alhamdulillahi daya nuna min wannan Rana Hakika Allah ne abun godiya,Allah nake roko yasa abunda kikasa gaba ya amfaneki agaba dake da ya'yanki da al'ummah baki daya"Suka amsa da Amin....


Yaja fasali kan yakara kiran sunanta"Safinatu.... Ta amsa kanta na kasa yacigaba da cewa"kafin tafiyarki Malaminku yazo yasameni game da yana neman izini awurina nabashi da dama yanemi auranki"Arazane tadago tana kallon Abban Nata.


Ummi tace"ikon Allah,Safina taji kirjinta na lugude tasaci kallon ummi,Ummi takalli Abbah tace"to kai baka fadama diyar taka ko wanene ba?"Dan murmusa yayi kafin yace"ah nazata tafini saninshi"Da sauri tace"Wlh Abbah ban sani ba"Sai kuma da tafada kana ta Sunne kai a kafadar Ummi tana dariya,Ummi ta dungureta tace"yar nema kawai" Abbah yace"kyalemin uwata,nasan bata sani bane,bakowa bane sai mallam yahuza"tagefen ido ta kalli Abbah kana ta kalli Ummi,Ummi tace"Masha Allah yaro ko mai Hankali Allah yasa albarka"Tafada tana kallon Safinar dake sunne kai tace"to kina sonshi..."?

Abbah yace"Ash...Zainabu kincika azarbabi wlh"Safina tatashi da gudu tashige daki tana dariya,Abbah yabi bayanta da kallo yana Fadin"kin korarmin mamata ko baki kyauta ba,Ummi tace"daga abun arziki yabata amsa da cewa"ba'a son taimakon ki barmu mana"Usman kuwa murna yakeyi wai yaya zatayi aure su Ummi suka bisa da kallo suna dariyar yarintansa.


Safina kan gado tafada tana dariya filo tajawo ta sanya akirjinta,tana lumshe ido tabbas mallam yahuza koda batasan so ba tanajin wani yanayi atare dashi,ta tuna sanda suka dawo yake jifanta da wani shu"umin kallo na wanda ya mutu kan sonka,ita kunya yasata ta kauda kanta,tadade kwance tana saka tana warwara kafin barci yakwasheta.

*Kaduna...*


Yau din Dr Safwan yakasa controlling din kansa tun a asibiti yakejin yanayinsa na chanzawa tabbas yamayi kokari baisan yaushe rabon sa da Sakina ba.

Adaddafe ya isa gida ko sassan momma bai isa ba, ya nufi sashen sa kai tsaye dakin Sakina yama tsinke tana kwance kan gado tayi daidai tana waya ya shigo ta wutsiyar ido ta kallesa taga yazuba mata ido,yana mata wani kallo idanuwansa sun kankace,kallo daya tamai tagane halin dayake ciki,shiyasa tayi mirmishi tagefen baki ta watsar dashi ta cigaba da danna  wayarta.



Yaga bata da alamar sauraransa,yasa ya Nufeta ya fizge wayar yana kallonta da idanuwansa wanda bakomai aciki sai zallar desire tace'Mallam lafiya?

"tafada tana wani binsa da ido cikin zafin Nama ya isa gareta ya fizgota suka kara fadawa kan gadon rumgumeta yayi yana shinshinan wuyanta yace cikin wata murya kamar ta mashaya"No sakina...Karkimin haka kema kinsani....I need u on bed"fizge jikinta tayi kan tace"ahayye....Dama nasan zaka zo ai tunda yanzu ina da amfani to wlh kajima na rantse bazan baka kaina ba ai daman nace nida kai ne acikin gidan nan"


Tsuru yamata da ido yana kallonta jikinsa duk yayi sanyi kasala hadi dawata sha"awa mai karfi ya taru ya dannesa dakyar yayi karfin halin mikewa Ya karisa gareta zai rumgumeta ta dakatar dashi dacewa

"tsaya tsaya karma  kamatso don wlh bazaka samu ba kaje wa'inda suka fini daraja su baka"tafada tana wani gatsina zubewa yayi agabanta yana fadi Cikin kasalallaciyar murya"plz.....Sakina ki mun rai ki tuna rabona dake tun kan ki Haifi Adil...Plz in kika hanani bansan ina zani ba bansan wani hali zan shigaba ko so kike inje inyi zina"?

yafada yana tsareta da ido tsaki ta doka kan tace"to kaje kayi zinar mana ruwan wa?"tafada tana zakuda kafada wayarta ta dauka tafice daga dakin ta bamko kofa jikake bam...!



Sororo yabi bayanta da kallo kafin ya sulale kasa yana dafe da mararsa,ya runtse ido cikin kuna da takaichi ransa na masa kuna yana ji aransa cewa mutuwa zaiyi matukar bai fitar da abunda ke damunsa ba gashi tunda yake bai taba kusantan zina ba.


Yadade zaune kan yararrafa ya mike yana tangadi ya fice daga dakin kai tsaye sashen su momma ya isa yasamesu zaune afalo Hajiya na kan kujera tana kwakulan goranta ita kuwa momma tana bawa Adil madarararsa,yana shigowa yafada kan kujera yaraf yana dafe da mararsa cikin kunan rai da azaba.


Momma tace"Subuhanallah....Hajiya ta mike tana salallami tana fadin"Kai lafiyar ka kuwa mutuwa aka yi Hala.?

*Shakira...*

Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_


*DEDICATED TO: My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*



*09*

-------Kusa dashi haj.Mama takarisa tana Fadin"Kai sufiyanu wai lafiyarka kuwa? ko baka da lafiya ne?

shuru yayi mata yana dafe mararsa cikin azaba,saboda bazai iya bude baki yabata amsa ba cos muryan nasa bazama ta fito ba.




Haj.Mama fusata tayi tace"Kada Allah yasa ka fadamin,Mara mutumci kanaji ana mgana kama mutane banza,chan da tsiyarka.."


Momma dake gefe rike da Adil ta zurama danta ido tsausayinshi na ratsata kwallah tatarun mata cikin kwarmim ido tayi saurin sharewa ta mike ta isa kusa dashi tadafa sa tana cewa"Ayya babana meke damunka? baka ji Hajiya na mgana bane..?

Haj.Mama ta amshe da cewa"yana ji wulakancin sane ya tashi to wlh yafi kowa sanin gidanta ya tarar"..tafada harda buga cinya momma tayi shuru tana kallonsa yana kara dukunkunewa cikin kujera Haj mama tayi tsaki tace"mtwssss....Kawai kazo saboda bakin hali katasamu kana mukurkusu kamar wani mai Nakuda,kaji dashi dai"


Momma dai tayi shuru ba'a bin tayi mgana ba Haj.Mama ta hada da ita,yana jinta yayi banza iska da ita sai da yaji yadan samu dama kana ya mike ya nufi kichen yana tangadi haj.Mama tace'"oh ni maryamu dama yunwa ce tasaka wannan aikin yau ga dan iskan yaro shine kana ji ana mgana kayi mana banza"ko waigowa baiyi ba yakarisa kichen din yafara bude buden durowa haj.Mama tayi firit tabishi tana fadin"wai kai kabamu ajiyane"?

Tsaye ta ganshi yana Neme neme tsayawa tayi sororo tana kallonsa wata durowa yajawo sai ga lemon tsami da sauri ya dauka yadauko kofi ya yanka da wuka yana matse ruwan yakafa kai zai sha Haj.Mama ta rike tana kallonsa ido cikin ido.


Fuska ya daure kan yace"mene....Sakarmin"yafada muryansa ta shake Haj.Mama tace"Anki a saki wlh bazaka shaba ba ka  kashe kanka ba"kara hade rai yayi kan yace"ki rabu dani nace"yafada da tsawa Sakin mai tayi shikuwa ya kafa kai yashanye yana dafe mara,nan kichen din ya sulale yana dafe mararsa data kulle wuri daya.Haj.Mama tayi tsam tana kallonsa ita ba yarinya bace tafahimci halin da jikanta ke ciki tsausayinshi ya rufeta domin tasan gado yayi gun kakansa shima ba dama🙈kaji haj.Mama🤣



Cikin zafin Nama da bacin rai ta fito daga kichen din ta wuce momma dake zaune tana sharan kwallan tsausayin d'anta  kwara daya tal data mallaka aduniya ake neman zauta mata mishi tadaga Hannu sama tace"Ya Allah kana ji kuma kana gani...Ka kawoma wannan bawa naka mafita"takareshe fada hawaye na zuba bisa kuncinta har shima Adil kamar yasani yasa kuka,jin kukansa yasa Dr Safwan fitowa bayan abun ya lafamai kan kujeran ya koma ya zauna yadafe kai,momma ta kallesa tace"kadinga maimata innalillahi wa"inna ilaihirraju"un zaka samu sassauci aikuwa cikin kankanin lokaci yaji komai na sauka kamar ana sacce taya🤣






Sakina Na kan kujera remot ne ahannunta tana sarrafa tashoshin talabijin Haj.Mama ta fado falon bako sallama Sakina tadago tana kallonta da mamakin ganinta tace"lafiya....Uwarki nace"Haj.Mama tabata amsa tana nuna ta da yatsa Sakina tayi tsam tana kallonta kan ta maimaita da sigan tambaya"Uwata fa kikace? eh ita ko zaki rama ne"Sakina tayi mirmishin gefen baki kawai ta maida hankalinta a kallon talabijin din Haj.Mama ta harzuka tace"Uban me kika mai gashi chan ya kwantamana magashiyatan"?shekeke ta kalleta kan tace"Au bai fada muku ba?" Haj.Mama tace"daya fadamana zaki ganni nazo tambayarki rasa kunya meran tanka"shewa sakina ta saki kan ta mike tayi taku zuwa gaban hajiya tace"Naji dadin zuwanki domin dama ke yadace in bama sakon....Kinsan me yake damunsa?

Taci gaba da cewa" kaina yace in basa na hanasa,ko zaki iya bashi naki ne kinga sai ki wuce mai takaichin..."🙆🏽‍♀ tafada tana wani ware hannu alamun ko ajikinta,haj.Mama ta daskare tsaye tana binta da kallo Hawaye yana zuraro mata a idanuwanta.



Sakina tashiga tafa hannu tana fadin"good.....Indai zaki iya bismillah...Bake uwar shisshigi ba ke komai da ruwanki ba,to kinji mtsalar jikanki inkina da maganin mtsalarsa to bismillah"haj.Mama ta share hawayen ta tace"lalle kin cika tabbatacciya sai yau nagane Sufiyanu bai yi dacen mata ba,naji bazanmai maganin mtsalarsa ba ammh ina so kisani zan kawo wacce zata iya mganin mtsalar tasa ke kuma zaki gane *KIN TAFKA KUSKURE*"

Daga haka ta fice tana sharan Hawaye da Haban zaninta,haka ta iske su momma zaune Tatasa Dr Safwan gaba yana cin abinci Adil na goye a bayanta,kallonsu Hajiya mama tayi taji mugun tsausayinsu ya mamayeta ta kasa mgana kawai ta fashe da kuka ta shige daki.



Cikin tashin Hankali momma ta kalli Dr Safwan shima ya kalleta,kan yayi saurin tsame hannunsa cikin abinci ya mike yana Fadin"momma....Me zaisa hajiya kuka"?itama mikewar tayi bata samu zarafin mgana ba tafada dakin Hajiya suna zuwa su isketa tana shirya kayanta cikin bakkonta🤣Allah sarki Hajiya,tana sharan hawaye.


Momma ta durkusa gabanta tana fadin"Hajiya...Lafiya kike kuka ko an miki wani abu ne?"shuru Haj.Mama ta musu tacigaba da hada kayanta Ajiyar zuciya Dr Safwan ya sauke kan ya isa kusa da Hajiya ya riko Hannunta yana Fadin"Hajiyata...."yafada da tsausasawa tadago tana kallonsa idanunta jajir ya cigaba dacewa"Hajiyata mene ya Faru,Rayuwa bazatayi mana dadi ba matukar baki fadamana meke damunki ba"yafada yana kara damke Hannunta,



Rike Hannun nasa tayi kan tace"Babu komai jikana....gobe in Allah ya kaimu zan tafi Safana,da sauri ya kalleta zai yi mgana tace"A"a kar kace komai kwana biyu zan yi in dawo"Ajiyar zuciya ya sauke kan yace"Har naji sanyi hajiya ta nazata zaki barmu ne"Ya kareshe fada da wata raunanniyar murya.



Girgiza kai tayi tace"Inje ina sufiyanu...Har ABADA kune ahalina bayan ku banda kowa"Tafada tana kallon Hadiza rumgumeta yayi yana Fadin"Nima Hajiya bazan iya rayuwa baki cikinta ba,koda fadan damukeyi mudunga yi wlh ina matukar jin dadi"Dunguremasa kai tayi kan tace"Dan Nema wato da gangan kake jana ko"Kansa ya aza kan kafadarta yana fadin"thank u hajiya thanks momma for keeping me Happy"


Hajiya mama ta kalli momma tace"wai meyace Ne naji yana kirana ne Allah yasa bazagina yayi ba wlh inci ubanshi"🤣gabadayansu suka sheke dadariya har Hajiyan.




*Turkashi....Kowani mataki haj.Mama zata dauka sai kun biyoni a shafi na gaba ammh karku manta*

*Commet Share and Vote Domin kwarin gwiwata*



*Anitha...*
[10/14, 20:01] Sis Janafty: _Ina mata yan kwalisa masu Bukatar su Fito su kere Sa"a cikin Sa"anni ko matan abokai ko cikin kawaye..? Ina Mata wadanda ke Bukatar Gwangwajen ya"yansu cikin kayan alfarma domin kere sa"a da Fitowa cikin Alfarma cikin Sa"aninsu,Toh duk kusha Kuruminku ina tafe muku da Wani Karin Albishir ko kuna da Labarin DIJA COLLECTION,wanda ya Hada komai na kayan kawan Mata da maza domin fitowa Tsab,da Sanya mata suna Dagawa..?Ki hanzarta ko kuma mu hanzarta wajen samun daman zama mace yar Kwalisa muna saida komai na kayan adon mata da maza da yara,Irinsu Atamfa,leshi,Material,Takalman mata dana maza na yara dana manya,akwai dan kunnaye masu kyau da Tsari,kina bukatar mayafai na nuna Tsara..? Toh duk zaki samesu a Dija Collection ,kina bukatar Abaya.. ?shima karki damu duk zaki samu a Dija Collection suna da Ingancin Domin ingancinmu ne yasa muka Cigaba,Zaku iya Tuntubarmu ta wannan Nombobin wayar kamar haka 07045112780,ko kuma 09036617473,Sai kunzo...karku Manta Siyan Nagari mai da Kudi Gida.._
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*

_Ina mata yan kwalisa masu Bukatar su Fito su kere Sa"a cikin Sa"anni ko matan abokai ko cikin kawaye..? Ina Mata wadanda ke Bukatar Gwangwajen ya"yansu cikin kayan alfarma domin kere sa"a da Fitowa cikin Alfarma cikin Sa"aninsu,Toh duk kusha Kuruminku ina tafe muku da Wani Karin Albishir ko kuna da Labarin DIJA COLLECTION,wanda ya Hada komai na kayan kawan Mata da maza domin fitowa Tsab,da Sanya mata suna Dagawa..?Ki hanzarta ko kuma mu hanzarta wajen samun daman zama mace yar Kwalisa muna saida komai na kayan adon mata da maza da yara,Irinsu Atamfa,leshi,Material,Takalman mata dana maza na yara dana manya,akwai dan kunnaye masu kyau da Tsari,kina bukatar mayafai na nuna Tsara..? Toh duk zaki samesu a Dija Collection ,kina bukatar Abaya.. ?shima karki damu duk zaki samu a Dija Collection  suna da Ingancin Domin ingancinmu ne yasa muka Cigaba,Zaku iya Tuntubarmu ta wannan Nombobin wayar kamar haka 07045112780,ko kuma 09036617473,Sai kunzo...karku Manta Siyan Nagari mai da Kudi Gida.._

*10*


    -----washegari kuwa da duku duku Haj.Mama tace zata tafi,direba Dr safwan yahada ta dashi haj.Mama ta hau fada kan mene wai ita ake mata haka ne yanzu batada ikon tafiya sai an wani hadata dawani gard,to hala bacewa zatayi ne,dakyar ya lallabata ta shiga motan direba yaja suka lula hanya Momma takoma cikin gida cikin kewar Hajiya.


Sakina kuwa Dr Safwan na ficewa ta kece dadariya tafada kan gado tana fadin"yaro...Yaro ne inba yarintaba kagama wulakantani sannan kadawo kace in baka ai kayi kadan,Badai haihuwa ba gashi chan na haifa na ijiyema..Sai ka raina d'an nikam nida haihu ho ba yanzu ba"duk ita kadai take magunganunta,takira haj.Kari tana fada mata sai cewa tayi"kinyi daidai yata gwara kinuna masa kincika yar halas".


Hajiya na wucewa ya shirya cikin suit ash and black ya daure wuyansa da tektie kafarsa cikin sawu ciki bakake na fatar damisa,rigar likitocin sane sabe a kafadarsa,hannunsa dake daure da agogon fata na kamfanin Rado ke cikin aljihu daya kuma yana latsa waya yana fitowa sakina dake kwance kan kujera tashaki kamshin turarensa Azzaro visit.


Ta gabanta yabi ya wuce ko kallonta baiyi ba yasakai yafice kwance take ammh sai da ta mike kishi ya turniketa naganin yadda mijinta yahade ammh ya sakai ya fice ko kallonta baiyi ba,tsaki tayi kan tace"chan ta matse maka,takoma ta kwanta tana hammah kan nan kamar anyi wasan kura dashi..Allah ya kyauta.


Sashen momma ya shiga ya karya yama Adil wasa kana yafice zuwa asibiti ta bishi da Allah ya kiyaye.



Ko a Asibitin Dr Tahir ya fahimci Dr Safwan na cikin damuwa ya tambayesa yace babu komai,bai matsamasa ba, ya rabu dashi iyakata dai yasan bata wuce matsalar Sakina kullum addu"an shi shine Allah yadubi abokinsa ya kawo mai mafita ta alheri na alheri.

**********************

*Safana..*

  Misalin karfe 11 na safe Direba ya isa Safana da Haj.Mama bayan ya Sauketa ne  yatambayeta yaushe zata koma yazo yadauketa ballamai harara tayi kan tace

"to Habule randa kace"ta kareshe fada harda murgudamasa baki kama baki yayi yana Fadin Allah yabaki Hakuri Hajiya adawo lpy,ko kallonsa batayi ba tawucewarta,kada kai yayi ya kara gaba.



Ba tsohon gidansu da Dr Safwan ya gyara tafara isa ba,da yake nan suke sauka in sunzo,ba chan tayi ba wai bazata iya zama ita kadai ba,direct gidan kawu Bala ta nufa kani yake agurinta sai dai Uwani matarsa taga hajiya kwatsam,nan ta tarbeta cikin farinciki da jin dadi kawu balan bai nan ya tafi kasuwa bai dawo ba sai dare yazo ya tadda Hajiya yayi murna ganinta bayan ya natsane uwani tashiga ciki ta basu wuri,Ya kalli Haj.Mama yace"Hajiya lafiya irin wannan zuwa..? Ina Fatan wajen Ita Hadizan da Safiyanun duk lafiya suke..?

"Haj.Mama najin haka ta Fashe da kuka tana Fadin"wlh kawu Bala (dayake itama haka take kiranshi) in baku sa hannu arayuwar dan marayan Allah ba Wlh zata kasheshi da bakinciki.." cikin tashin Hankali yace"meya ke Faruwane dashi safiyanun dinne, Hajiya maryam..?

Hajiya mama bata yi jinkiri ba,ta warwaremasa duk abunda ke Faruwa ta karashe da cewa"so nake na nuna yarinyarnan da uwarta sun Tafka kuskure domin sai nasa sunyi kuka da idanunsu"

Kawu bala yayi ajiyar zuciyar yace"Lalle Safiyanu bai yi sa'an mata da suruka ba wlh sam,Haj.Mama tace"wa...?.Tsinannan kenan ai wannan uwar tasu mai kama da ruwan yan duniya itace kesata komai takeyi"

Kawu bala yace"to shi kwamishina yasan abunda ke Faruwa"?Haj.Mama ta tabe baki tace"wannan aie tagama dashi tun yaushe ake fadamai yakasa daukan mataki,mudai da mukasan zafin da'nmu mu zamu nemasa mafita...."Kawu bala yace"to mecece mafita Hajiya Maryam..?

Kai tsaye tace"Mafita ita ce AURE ZAN MASA"....kawu Bala ya kalleta lokaci Daya yana Fadin"Aure kuma Hajiya..?tabashi amsa

" Da kwarai da gaske aure zan nemamasa da wacce tadace da al"adansa da addininsa"kawu Bala yace"To yanzu ina za"asamu yarinyar daa zata dace dashi"?shuru Hajiya mama tayi kan chan tace"bakomai Allah zai kawo wacce ta dace dashi...Daga haka suka cigaba da tattaunawa.


Gari na wayewa Haj.Mama ta shirya tayi ma gidan Aminiyarta tsinke iyami tayi matukar murna da ganin hajiya mama suka kule adaki suna hirar yaushe gamo acikin hirar ne Haj.Mama take tambayan Safina iyami tace"Safina tazo kun koma kaduna da sati daya,taji haushi inaga shiyasa taki dawowa,Haj.Mama tace"Allah sarki diyata Safina tana chan dai ta kammallah karatun ne?"Iyami tace" eh ta kammallah sai dai kisan diyar taki Hafiza ce bana ita zata wakilci zamfara agasan alqur"ani ta kasa.."Haj.Mama tace"masha Allahu Allah yasa albarka iyami ta Amsa da Amin.




Wuni sukayi tare suna hiransu cikin hirar ne iyami ke tambayan Safwan da iyalansa nan Hajiya ta zayyanemata komai da dalilin zuwanta garin ta kareshe da cewa"wlh iyami yarinyarnan in aka barta da yaron zata iya kasheshi da bakincikinta"iyami tayi shuru tana kallon Aminyarta tana sharen hawaye kan ta jinjina kai tarike hannun Hajiya tace"maryama kidaina kuka kin kawo kuka a inda za'a share miki hawayenki.."

haj.Mama ta saurara tana kallon iyami kai ta gyada mata kan tace"kwarai share hawayen ki muyi mgana"ta share hawayenta tagyara zama tana Fuskartanta.


iyami tayi ajiyar zuciya tace"nidai bani dawata y'a balle in dauketa in bawa Safwan domin sharemai hawaye ko? tafada da sigar tambaya haj.Mama tace"Nasani iyami...Meyasa kikace haka.." iyami taci gaba da fadin"Saboda ina so na kore miki damuwar dana gani a idanunwanki,mezai hana mu Nemamasa SAFINA"

Da sauri Haj.Mama tamaimaita"SAFINA..."iyami tace"kwarai Hajiya ita kadai ce zan iya sharemiki hawaye da ita duk da bani na haifeta ba Nasan mahaifinta bazai ki ba"shuru haj.Mama tayi tana bin iyami da kallo iyami tace"maryama ko..."".da sauri Haj.Mama tace"kar kice komai iyami nakasa mgana ne kingama min komai na rasa dawata kalma zan gode miki lalle Safina itace Hasken dana dade ina gani agidan Sufiyanu Allah na godemaka,iyami tace"babu komai ai yadda safina take awurina haka Safwan yake awajena yaron nan duk sanda sakonsa zai iso Safana dani aciki musamman zai zo ya gaisheni to meye ake nema gun Namiji wanda yawuce wannan Allah dai yasa alheri zamu kullah

Cikin farin ciki Haj.Mama ta amsa,da Amin Amin





*Topha ya kuke hango abun yayi,?zai bada kala?kudai ku biyoni dan kuga yadda badakalar zata kaya*









*Commet and share domin shine abincinmu da gwarin gwiwanmu*

*Janafty..*
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*




*13*



----Basu samu zama ba sai zuwa dare,dawowar Dr Safwan kenan daga Asibiti yasamu kiran gaggawa,Shiyasa ya Tafi batare da ya Tsaya jin dame Hajiya mama ta dawo ba




Please Login or Register in order to submit comment