Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana dariyar farinciki.






gabda la'asar sukayi shirin tafiya bayan sun cika sakina da mugayan shawaransu wanda bazai bulle da ita ba saima karin jawoma kanta wata fitinar...kwamishina bayanan yaraka gwanna jigawa shiyasa sukasamu zuwa domin ido yasanya musu ko laila yace tadaina zuwa sai anyi wani abu kwakkwara tukun..





Sakina ta rakosu kenan suka ga hajiya mama zaune adan barandansu ta shimfida tabarma tana jin radio ta sai gasu sun fito sun yi tsam da suka ga hajiya mama ammh sai suka waske itakuwa hajiya mama harda cemusu bata gansu wurin biki ba adakile hajiya kari tace"Sunyi tafiyane shiyasa...Suka shige motarsu laila ke jan motar suka fice hajiya
mama tabisu da gwalo.





*Anitha...*


commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_πŸ’ž


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*




*31*


"Sai karfe 10 dawani abu na Dare Dr yadawo wanda Safeena da danta sun cakare suna tsumayinshi sanye take dawani riga da wando na pakistan pick colour batasanya gyalen kayan ba sai ta daure gashinta dashi ta sakeshi shikuwa Adil cikin riga da wando yan kati ammh wando gajerene,yau din tuwon semo tayi mishi da miyar kubewa danya sai lemon abarba dayake Dr bai cika cin abinci asama ba dat why take shimfida mai babban darduma afalo su zauna suci ko adaki.


yau din ma haka ta kasance afalon suka baje suna kwasan tuwonsu Dr naci yana zuba santi safeena da danta suna faman mai dariya kallonsu kawai yake azuciyarsa yana godema Allah dabai bijirema hajiya mama Ba dako yayi asara abubuwa mafi muhimmanci yau din kam bbu sauki domin kodaga irin kallon dayake binta dashi tagane akwai bayani dayake yau yadawo dakinta itama binshi take dawani sirrin kallo mai tsayawa azuciyar masoyi mirmishi yayi yana dafa hannunta yace"Ko acikin dubban mata keta dabamce yanmatana shiyasa kullum nake alfaharin samunki amatsayin matar aurena"tsadadden murmishinta ta sakarmai kan tace"Kaima acikin dubban maza ka bambamta wlh tallahi nafi kowacce mace samun sa"ar Adalin miji irinki Uncle"Tafada tana mai kura masa ido kuri sukama juna suna aika ma da juna kalamai wanda baki bai iya furtawa sai dai kawai ido yanuna da kuma hannu ya aikata.


Karar bude kofa ya fargar dasu suka bi inda karan yake Sakina ce tafito cikin wata doguwar rigar less kayan su amsheta duk da ta rame ammh tayi kyau abunta kallon su takeyi kan tawani tabe baki tace"Andai ji kunya....Wlh"Wucewa tayi kichen tana sakin tsaki da kallo safwan ya bita yana mamakin chanzawar sakina kallon Safeena yayi kan yace"Anyi baki ne yau ko..?yafada idonsa anata cikin inda inda tace"Am....Eh Anty tayi baki"Mirmishi yayi yace"no wonder...Safeena ta kallesa shima ya kalleta sai ya waske da daukan Adil yana fadin'!maman Adil me kika ba yaronki ne yazama lukuti haka"Dariya tace"Tuwo miyar kuka"Yace"wow...Gaskiya kam koda nagani kinganni nan dad dina na biyo domin shi abincinsa gargajiyane shiyasa nake kara godema Allah daya bani mata daidai da ra'ayina"mirmishi ta mai kawai mikewa yayi rike da Adil yana fadin"Ke kinga nagaji dawannan jan ran...Kisame ni a dakina"Mikewa safeena tayi tana cewa"Yau kuma mulki akeji yace"Eh...Nima sai naja ajina.



Kwashe kayan tayi dasukayi amfani dashi takai kichen tana shiga taga Sakina na tsaye tasanya latifa yar aikinta tana dafamata indomie sai masifa take wai anmaida su gida gidan tuwo sai rufe hanci take tana fadin"Tsiyar a kawo maka dan kauye agida kenan baisan komai ba sai kauyanci"Ita dai Safeena kala bata ce mata ta ijiye ta fito tawuce dakinta aranta tana fadin"Bazan biye miki ba tunda nagane halinKI ko mijin naki ma baki kyale ba.



wanka tayi da Brush kana tazo ta sanya rigar barci wata karamace mai siririn hannu komai na jikinta ana gani pant kawai tasanya saboda sanin halin dr baison wani abu yamai shamaki, humranta da inna husai tahado mata ta yi ambaliya dashi zani ta dora kan rigar ta sanya hijabi tafito taja kofanta ta nufi dakin Dr.



Koda taje ta iskeshi har Adil yayi barci ya sanya sa kan dan gadonsa dake dakin dr yana zaune yana duba abu acikin kwanfutarsa tashigo tana shigowa tayi wurgi da zanin da hijabin tataka cikin takun ta na kasaita ta isa garesa kamshin turarenta shiyasa yadago yana binta da mayen kallonsa cikin zakuwa ta rumgumesa ta baya ta sakalo hannunta tazage cikinsa tadora kanta wuyansa tace cikin karyayyiyar murya"Unku...Gani takareshe cikin shagwaba tagama kashe mai jiki dat why yamata shuru kashe na'urar yayi ya ijiyeta kan doruwar dake gefensa ya birkitota yana binta da mayen kallo yace cikin kasala"sai da nagaji da jira to nama fasa"Yafada harda tura baki dariya tayi tace"Sorry zumata....ga madarar ka nan kasha sai kagaji don kanka"matse mata baki yayi yana yana fadin"Nine zuma ko"yafada yana kallonta tace"Kafi zuma dadi ma"Sai da tafada taji kunya dariya yayi yace"ehyye....Yanmatana haka kike"sunne kai tayi akirjinsa tana dariya rumgumeta yayi yana fadin"to shikenan bari in baki zuma ni kuma kibani madara daga haka yasanya hannu ya rage wutan dakin yayi saurin doramata nauyinshi suka fara sumbatar juna cikin kwarewa.




Yau sun makara sai 8,Dr ya fita office cos akwai meeting din da zasuyi da sauran likitochin asibitin breafsat ma a tsaye safeena ta matsa masa yasha ruwan tea...Ko shashen su momma ma a tsaye ya shiga.



Tun fitanshi Safeena takoma daki domin yau tun safe taji zazzabi na neman kamata kana bakinta na tsinkewa batajin dadin komai shiyasa tana yin wanka tama adil takoma ta kwanta ta hadasa ta kekensa da abun wasansa takoma ta kwanta yafita yana ta wasansa.




Sakina sai yanzu ta fito daga daki tana hamma kichen ta shiga ta hado tea tazo ta zauna afalo ta kunna talabijin ana wani film a mbc2 tana nan zaune sai ga Adil ya fito kan kekensa yanata wasansa kuramasa ido sakeena tayi tanajin wani sonsa na kwararamata acikin rai kawai sai ta mike tsam ta isa kusa da shi ta sanya hannu ta daukesa aikuwa tana daukan shi ya tsala ihu ranta ya baci tace"kai rufemin baki ina uwarka indauke ka ka hau ihu",shuru yayi yana kallonta hawaye na zubo masa sai kuma taji tsausayinshi rumgumesa tayi tana fadin"srry my boy...Kaine kaban haushi"ai tana fadin haka yakara tsala ihu safeena dake barci taji ihunshi kamar amafarki zumbur ta mike taji kuwa daga falo ne takejin kukan da gudu ta fice hartana bigewa da gado.



Tana fitowa taganshi hannu Sakina tayi saurin isa tana fadin"Me kika mai...?"tafada arude jin yadda yake tsala kuka yana ko ganinta yafara zillo yana kiran mami yana mika hannu, tasanya hannu zata rikesa sakina ta jaye tana bin safeena dawani matsiyacin kallo tace"kul.....Kada kikara dora ahannuki ajikin dana kuma da kike tambayan mai na mai ai dana ne komai na mai nina haifesa"Galala safeena tayi kwalla ta cika idonta tace"A'a ba nufi kenan Ba...Naji kukansane nazata faduwa yayi"Sakina tace"to yana hannu uwarsane sai ayi gaba"Tana fadar haka ta juya zata koma daki ..Kamar daga sama sukaji muryan Dr cikim dakewa yana fadin"ADIL BA DANKI BANE, SAKINA DAN SAFWAN NE DA SAFEENA"yafada yana takowa tsakiyar falon mantuwa yayi yazo daukan file yadade tsaye tun farkon mganan yanajinsu.



dawowa sakina tayi kan tace"Da ubanwa ya bata..?"Kai tsaye yace"Uban yaron ya bata shi halak malak.."Sakina tajuya kawai tasanya Adil adaki ta kulle kana ta dawo tana cewa"Baka isa ba safwan wannan karan sai dai duk abunda zakayi kayi ammh na amshi dana"Wani sakaran kallo yake binta dashi kafin yace"Wai ma wanene dan naki ne..?"Cikin dakewa tace"Adil ne dana mana ko inada wani dan ne bayanshi"Cikin fusata yace"au sai yanzu kikasan danki ne sai yanzu kikasan kina da wani dan' kinmanta sanda kika banzarta dashi,kin manta sanda kika hanasa yaji duminko lokacin dayake bukatarki kika ki shayar dashi kikaki rainansa kika ki basa kulawa kika banzarta dashi kika wofantar dashi shine kike kiran kanki a matsayin uwa tirr da mai hallaya irin taki baki dace da akiraki da suna UWA BA"


Hawaye ya gangaroma Sakina ta nuna kanta tana fadin"Nikake ma Tirr Safwan'ko kallonta baiyi ba yawuce ya bude daki ya dauko adil yaci kuka ya koshi ya mikama Safeena yace " _KO BAYAN RAINA KECE ZAI CIGABA DA KALLO A MTSAYIN MAHAIFIYARSA....KEKUMA KI KALLESA A MTSAYIN DA' NA HAR ABADA_ Safeena ta amsheshi tana fadin"Insha Allahu zan kula dashi kamar yadda duk wata uwa zata kula da danta"mirmishi yayi mata kan yace"Nagode hanyar dakinsa yayi aikuwa Sakina tayi kukan kura ta isa kusa da Safeena ta bangajeta ta fadi ita da Adil kan ta daukeshi tana fadin"kunyi kadan na bar miki dana in nabar miki mijina wlh bazan bar miki dana ba.



Safeena dake dafe da ciki da kurma ihu Ai da gudu Dr Safwan ya isa gareta yana rikota tana dafe da ciki tana kuka yana duba kasan kafarta saiga jini cikin tashin hankali da karaji yace" *SAKINA.....!WLH TALLAHI IN KIKAMIN ASARAN KWAN HAIHUWA SAI NA MAKA KI A KOTU* tsam ta tsaya tana kallonsa kan tace"Shege kafasa Safwan dama dan adam da butulci akasansa asibitin dakake takama dashi inace ba ubana yataimaka maka ka bude sa ba to indai har baka sake ni ba BAKA CIKA DAN HADIZA DA SALE BA"cikin wani bakin cikin Safwan ya saki safeena ya isa kusa da Sakina yana kallonta idanunsa sun kawo ruwa yace"Tabbas da taimakon mahaifinki nake wannan matsayin ai banzata kina kallona da abun ba....To ammh yau ya kare ni _*NI DR SAFWAN SALE SAFANA ZAN NUNA MIKI NI DAN HALAS NE....KIJE NA SAKEKI SAKI DAYA!NA SAKEKI SAKI BIYU!NA S........*_ A'a kada ka karisa kada ka karisa Safiyanu"



Hajiya mama tafadi haka da karfi ita da momma ce suka shigo tun bayan ihun da Safeena ta zabga hajiya mama tace"Kabarta haka Safiyanu ko ahaka ka barta kanuna mata kai dan halas ne"Juyawa kawai yayi ya isa inda safeena ke kwance momma na rike da ita ya ciccibeta yana fadi cikin raunin murya'momma muje asibiti inaga Safeena bari zatayi" da sauri momma ta mike tana salati ta rufamasa baya har yakai kofa yace"Hajiya ki karbi Adil don har abada ba danta bane"Yanagama fadar haka ya fice dauke da Safeena.




Sakina dake tsaye kamar mutum Mutum hajiya mama ta fizge Adil tana cewa"Naso ki gane kuskurenki tunkan saki ya shiga aurenku ammh kash...Kin kasa ganewa ammh ina fatan wannan karon ki gane KIN TAFKA KUSKURE

Daga haka ta fice dauke da Adil....Ai Sakina zubewa tayi cikin firgici da tashin hankali tana fadin"na shiga uku wlh Safwan da wasa nake maka wayace ka sakeni wayyo ni...Sakina na mutu na lalace"








*Hmmmm....Ai kinyi kuskure ba'a wasa da abunda bana wasa ba Allah ya kyauta*



Commet
Share
Vote
Like
Share

*Anitha...*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE.."!*

*Wattpad:Janafnamcy13*
_Mallakar:Janafty_πŸ’ž




*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*




*32*





"Momma ta shiga motar direct suka wuce S&S SAFANA SPECIALIST HOSPITAL Ma'ana asibitinsa suna zuwa suka rufi kanta dashi da Dr. Tahir don bai yarda sauran sun tabamai mata ba Alhamdulillah sun gano ciki dan sati hudu da kwana biyu wata daya kenan,buguwar datayine jini ya yanke mata anyi saurin xuwa asibiti dat why cikin bai zubeba sun yi nasarar tsaida jinin suka mata allurai suka kaita dakin hutu.



Sakina tadade tana kuka nadama mai karfi ta shigeta lokaci daya domin tasan duk takamarta da Safwan take gashii yanzu ya saketa ina zatasa kanta yanzu...yan aikinta ta kira suka hada mata kayanta kaf bazata iya tuka mota ba saboda halin datake ciki direba tasa yakaita tasha ta hau mota sukuma su latifa taba kowannesu na mota tace su koma gida tareda albashi.




Sai yammah ta isa katsina dan adaidaita ya sauketa tabashi kudinsa mai gadi ta kwalama kira yazo ya jidan mata akwatuna yana kaiwa cikin gida Hajiya kari dake zaune afalo tana kallo taga ana shigowa da akwatuna saurin mikewa tayi tana fadin"Kai daga ina kuma..?

"Bai bata amsa ba Sakina ta sawo kai Falon sororo Hajiya kari tayi tana binta da kallo da gudu Sakina ta isa ta fada jinkinta tana Fadin"Hajiya ya Sakeni wlh ya sakeni"Cikin karaji hajiya tace"Yame....."Sakina tace"ya sakeni hajiya safwan ya sakeni"


Ya sakeki kuma shine kika zomin gida"Muryan kwamishina ta katsesu wanda ke kofar falon yana takowa cikin bacin rai sakina da Hajiya suka kalli juna kafin hajiya tace"Haba Alhaji tanada inda yafi nan ne"Kai tsaye yace"Wannan ya rage nata ammah na rantse bazanyi kaffara ba duk randa sakina ta kaso aurenta bawani dalili bazata zaunamin agida ba"Sakina ta sulale akasa tana Fadin"na shiga uku dady in ka koreni ina zani"Ya juyo ransa abace yace'"inda kika zaba sakina...Duk hakurin yaron nan sai da kika kuresa ko..?"girgiza kai tayi tace"Abbah hajiya da Anty lailane sukaje gidana suka na amshi Adil ahannu Safeena wanda Safwan ya bata shi tana rikonsa"Hajya kari tace"Wata Hajiyar don ubanki"Tafada tana ballamata harara.


Sakina tace"Wlh Daddy susaka sani na aikata abunda har Safwan yasakeni"mirmishin takaichi yayi yana fadin"Very gud naji dadin haka kinga yanzu sai itama tabi ki....Sai ku nemi inda zaku"Hajiya kari tace cikin tashin hankali"In bita ina Alhaji...?Ya fara taka step kan ya waigo yace"Ki bita ku tafi koma ina ne Nima na sakeki Saki daya"Hajiya kari tasa ihu tana fadin"na shiga uku ni karima Alhaji ka sakeni fa kace"Yace idanunsa cike da kwallah"Eh....Haka nace ba abunda zance miki sai Allah ya isa tsakani na dake karima aurena dake babu abunda na karu dashi sai tabarbarewan rayuwa kije duniya takoya miki hankali keda yarki.


Yana gama fadar haka ya haye sama yana share kwallan daya ziraromasa hannu akai Hajiya kari ta dora akai tana kwarma uhu tana fadin"Shikenan Sakina kinzo nima kin kashemin aure"Sakina dake gefe tana kuka tace"ni dakuka kashemin nawa fa hajiya"Hambari ta kai mata tana fadin "Don ubanki waya kashe miki aure kika dai kashema kanki...Ai sai ki tashi mu san nayi"




akwati daya Hajiya kari ta dauka sai Atm dinta suka rankaya suka fice cike da takaichi megadi na musu mgana sukayi banza dashi suna fita kwamishina ya kira Anty salma ya labarta mata komai kuma yace ko sun kira ta zasu zo gidanta tace basunan sunyi tafiya Salma saboda bakinciki saida tayi kwallah ta amsa to ammh aranta tana so tasanya mizanin wata irin uwa Allah ya basu.




Sai da suka fita suka fara tunanin inda zasu yanke hukunci kiran Laila sukayi Sakina ta kirata take fadamata Abunda yafaru cikin razana laila tace"mun shiga uku Daddy yasaki Hajiya"Sakina tace"eh...Nima fa ai saki na Safwan yayi har Saki biyu"Anty laila tace"garin yaya sakina"Sakina tace cikin fusata"garin bin shawarar dakuka bani....Yanzu Daddy yace bazamu zauna mai agida ba to gamunan zuwa"Zuwa ina......Ta fada cikin firgici cikin mamaki Sakina tace"gidanki mana"Da sauri Laila tace"Kut...Wlh badani ba nima kuzo ku kashemin nawa aure tab...Ku tafi kankia gidansu hajiya zuwa goben ina tafe"daga haka ta kashe wayar sororo Sakina tayi da waya ahannunta tana kallon Hajiya kari dayake wayar a handfree ne taji komai.


laila ta rike baki tace"kutumar uba in barku kuzomin gida yadda mujaheed yake kume dani ai sai yace mu rankaya dukkanmu....Tab....Su karata chan nima ina lallaba rayuwatane


Sakina ta fashe da kuka tace"wlh bazan iya zama a kankia ba hajiya"Cikin bacin rai Hajiya kari tace"to don ubanki sai dai ki nemi gun zuwa domim banda nan bbu inda zamu a amshemu"Sakina batayi mgana ba ta kira Anty salma sai da tabata 2miss cll kana ta dauka cikin kuka take fada mata abunda ke Faruwa mirmishi mai kama da kuka salma tayi kan tace"Ayy bamu kasar mun tafi kasar turkey baban shahid yaje wani aiki ne"daga haka ta yanke wayar.




Basu da zabi illar zuwa tasha suka hau motar kankia sakina kuka taketa yi tana fadi su suka kashe mata aure...Itakuma hajiya tana fadin ita ta kashe mata aure abu har yazaman musu fada amota sai kallonsu ake ana tirr dasu.




Sai bayan issha"i suka isa kanki koda suka isa gidansu Hajiya kari wanda daman iyayanta sun rasu yayyintane agidan wanda ta gujesu sai tayi shekara bata leko ba sunyi mamakin ganinta matuka anan take fada musu karya da gaskiya basu yarda ba adaren sukama kwamishina waya yafada musu komai game da hallayar Karima suna ko jin haka suka ce babu ruwansu da ita sai da ta shiga wani yanayi ne zata nemesu to sukan babu ruwansu da ita gidane tazo ta zauna ga dakin mamansu chan data rasu su share kafa su zauna tunda zaman suka zaba.




Haka suka ja jiki asanyaye suka wuce koda suka shiga dakin sai da suka kusa kuka saboda yadda dakin ya lalace ga ruma tako'ina rufin dakin na azarane duk ya kusa ruftowa ga simintin duk ya banbare beraye na Safara ga gefe daya wasu buhuhunan kaikayi ne bbu ko katifa sakina kan akwatin ta ta haye tana kuka ita kuwa hajiya gyalenta ta shimfida ta zauna ga yunwa na addabansu rabonsu da Abinci tun na safe.




haka suka kwana Sakina kuka ta kwana yi hajiya ko da takaichi ya cika ta dunga durama sakinar zagi tana cewa"ki rufema mutane baki duk wayaja bake ba inda kinyi hakuri agidanki har yaushe za'a sako ki balle har kizo nima kashemin aure"Sakina tace cikin kuka"duk baku kuka kashemin auren ba wlh hajiya keda Anty laila ba abunda zence muku sai Allah ya isa"


Hajiya kari tace"Nima Allah ya isa tsakani da ke inda daya sakeki kin nufi wani wurin har yaushe Alhaji zai sakeni...Duk iya abunda nakemai baitama furta sake agareni sai akanki ni yakamata na miki Allah ya isa sakina"


_Hmmmm haka Rayuwa ta gada daman_


Haka suka kwana wanda Sakina dakyar taga Safe saboda cinnaku da beraye sun hanata sak,ita hajiya haka abun yake agurinta matan gidan kuwa ba wacce ta kallesu saboda daman tuni suka tsaneta domin ko gidanta kaje tadinga kyamatarka kenan.




Sakina gari na waye tafice mota ta hau tatafi banki tayi ciro kudi dubu dari tatafi kasuwa tayo musu siyayyah don tace baza ta iya rayuwa ahaka ba, komai ta siyo su kayan tea indomie macrooni complex kai katifa da fridge saboda bazata iya shan ruwa bbu sanyi ba ta siyo fanka komai da komai mota ta sauketa har kofar gida tasa aka shiga dashi matasan gidan tasa suka kwashe tarkachan daki suka gyara musu kana suka shiga mata da kayan ta biyasu,sai dai Hajiya kari ta ganta da kaya kawai aranta taji dadi domin daman ko ita da'aka haifa anan bazata iya irin rayuwarsu ba.













Commet
And
Share
Vote

*Shakira..*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_πŸ’ž


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*



*33*


"Babu wanda yace musu kala kowa yayi banza dasu to da fari dai sunfara gudanar da rayuwar tasu cikin aminci da jin dadi kadan duk da atakure suke ko wanka sakina zatayi batayi sai dare yayi tayi awaje kan wai bazata iya shiga bayi ba gani take kamar kasa zai rufta da ita hajiya kari kuwa haka dai take lallabawa.

*****



Safeena kuwa sai da ta kwana uku a asibiti kafin a sallamota ta dawo gida wanda momma da Hajiya mama da shikanshi Safwan suka maida hankali gurin bata kulawa Ummi tazo dubata kwananta biyu takoma tareda sha tara na arziki daga sirikinta masha Allah.


Kwamishina da kanshi ya kira Dr yana bashi hakuri inda yake fadamai hukunci daya yanke hakika Dr Safwan ya tsausayama Dady domin shi shekara uku yayi da bakin cikin Sakina shikuwa Daddy shekaru tun ana kurciya bbu jin dadi da kwanciyar hankali hakika shi yafi kamata atsausayamawa.






Koda Safwan ya fadama su momma sun Nuna alhininsu matuka Hajiya mama tayi ajiyar zuciya tace"Hakika kabiru yayi hakuri matuka da karima walh da wanine da bazata kawo warhaka ba....Har ga Allah ba niyyata bakenan karabu da sakina ba A'a kawai so nake tagane kuskurenta to ammh ko yanzu Sakina ta gyara halinta wlh bani da ja zaka dawo da ita"gyada kai momma tayi tace"Tabdijam sakina ce zata iya zaman kauye"Safwan yace"Ai momma awannan lokacin ne zata gane TA TAFKA KUSKURE.

Hajiya kari tace"Kwarai ma kuwa fatan Allah yasa wannan yazama sanadiyar shiryuwansu suka Amsa da Amin.



Allah Sarki Safeena dataji sakin da Safwan yama Sakina sai da tayi kuka taita rokonsa kan yadawo da ita zata bata danta domin tafi ta gaskiya dantane data haifesa da cikinta.Dr yaso ya tsorata ta sai ya sha mur yace"ok kema bazaki rikesa ba kenan gud...Zan kawo wacce zata rikesa aie"To yana fadar haka tayi saurin basa hakura daganan bata karamai mganar ba ammh abun na damunta matuka.




******


KANKIAπŸ˜‚



Tabbas abunda hausawa kan ce komai yayi farko zai yi karshe to hakane tafaru dasu Sakina domin yau da gobe bata bar komai kwanchi tashi sai da suka karar da komai nasu kaf kudaden dake account dinsu suka gama dasu na kokarin su na inganta rayuwarsu shagunan Sakina tuni masu shi suka amshe domin bbu kaya kasuwanci tuni ya rushe,hatta da su Fridge din da suka siya sun saida kayan sawansu da daidai da daidai suke zara wai duk dai karsu bar rayuwar jin dadi.



To daman komai ubangiji yaso ma bawa sai ya amsheshi gashi ayau sun wayi gari basu da komai abincin dazasu ci ma garararsu yakeyi sai da Hajiya kari taita rokon yayyinta kan suma matansu mgana su dinga basu abinci suma din sai da suka ce sai da sudinga fitowa suna tayasu aiki don wallahi bazasu cida kardawa ba dole tasa suke fitowa domin samun abunda zasusa abakinsu Yau sai gashi Sakina ta rame tayi baki domin bbu mayukan da"aka saba shafawa,kayanta duk sun kode sunyi yage saboda wahala haka zaki ga Sakina ta tike tana buga bowol din ruwa ta cika bokitai takai gida ayi tuwa a yarfa musu akwano wanda ko Sakinar tacinye bazata koshi ba agari ko lbrinsu ya bazu duk inda suka bi ana tirr dasu Rayuwa tajuya musu baya domin hajiya kari har gidansu Daddy taje tasamu goggonsa taita rokonta kan tasa baki ya maidata ammh sai ta kalleta tace"Ada dai munmai dole ya aureki ya zauna dake ammh yanzu dayasan halayyanki karima bamu da ikon sashi yakara zama da ke sai dai inhar shi yake Ra'ayi"gwiwa a sacce tadawo da tarin nadama duk ta rame tazama tsohuwar karfi da yaji.Har satan hanya tayi taje katsina ammh sai megadi yake fadamata Alhaji yafi wata biyu bai nan yana london yaje hutun karshen shekara tayi tayi yabarta ta shiga ko kaya tadauka ammh yayi kemene yace"yallabai yace kada ya barta ta shiga"To yazatayi bata da ko sisi tana kuka take rokion maigadi yataimaka mata da na mota kallonta yake aransa yana Fadin"Kowa yaki sharan massallachi yayi na kasuwa yau shi Hajiya kema kuka tana rokon shi kudi,dubu daya ya bata ta amsa tana godiya kamar ta tsugunnah mai saida tatafi ya girgiza kai yace"wlh Hajiya kin tafka kuskure dakika bari kika rabu da gwarzo mai hakuri da nagarta irin yallabai....Allah yasa kin tuba harga Allah.


Sai da tadawo take fadama Sakina ga inda taje da abunda yafaru"Sakina dake zaune akasa bbu ko leda riga dabam zani daban tana ta shoshe soshe tace"Hajiya kinga yadda Allah yamaidamu ko kowa ya gujemu saboda hallayanmu hatta da Anty laila yanzu bama asamunta awaya ita kuwa Anty Salma nasani daddy ne yace karta nememu saboda abunda muka aikata akan son zuciyarmu"Takareshe tana fashewa da kuka hajiya kari tatashi ta isa kusa da ita tadafata tace cikin karyayyan murya tace"Hakika Sakina duk abunda ya Sameki nine sila domin amtsayina na mahaifiyarki banta nuna miki abunda kikayi ba daidai bane saima kara miki gwarin gwiwa danikeyi akan abunda kikeyi tabbas Allah ya nuna mana kuskurenmu tun ba aje ko'ina ba"


Sakina takara fashewa da kuka suka rumgume juna Hajiya kari tace cikin kuka"mun Tafka kuskure sakina...Sai dai munada yadda zamuyi mu gyara kuskurenmu kafin lokaci ya kuremana.


sakina tadago idanunta jawur tace"taya Hajiya taya zamu gyara alhalin bamu da wanda ke goyan bayanmu'Hajiya kari tace"Safwan....Kije kibawa Safwan hakuri ya hakura ya maidake Dakinki indai kika koma dakinki ni ko ban komaba nasan Allah zai dubeni ya yafemin abunda na aikata in cigaba da zaman anan harta Allah ta kasance"rumgumeta Sakina tayi cikin kuka tace"A'a Hajiya wlh bazan iya kallon Safwan da ahalinsa ince su yafemin ba saboda ban kyauta musu wlh bantaba kyautata musu ba koda na rana daya ne.."Hajiya ta runtse ido hawaye na kwaranyomata ranta namata daci Nadama mai tsanani ya baibayeta.


_Allah Sarki ita daman Duniya haka ta gada inkaine yau bakai bakai bane gobe_





*After Three month*





Wata mata nagani chaculate colour Ce sanye cikin wata doguwar rigar abaya tayi rolling din bakin veil din akanta har zuwa wuyanta kafanta sanye da cover baki hannunta rike da jakar gucci baka sannan dayan hannunta rike da wasu littafai kallo daya zakamata kazata yar kasar maroco ne saboda yanayinta.

Tsaye take abakin get din KADUNA STATE UNIVERSITY Wato KASU sai gawata

Please Login or Register in order to submit comment