Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rantsantsiyar range cover baka tazo tafaka a gabanta aka bude motar akafito wow....Abunda na furta masu karatu kunsan wa Nagani DR SAFWAN ne cikin wata rantsatsiyar farar shadda wacce tafito da zatinsa da kyawunsa lokaci guda tareda murjewa irinta hutu yarinyar naga ya Nufa yana cewa"Am srry yanmatan..Nayi latti ko..?"ai sake baki nayi kardai ace min wannan matar Dana Gani tun dazu SaFeena ce ai bangama mamaki ba naji muryanta cikin wayewa tace"bbu komai..Unku ina yarona"Yace"yanzu zamu biya mudaukosa daga islamiya"mirmishi tamai yana budemata motar tashiga sai alokacin naga dan cikinta dayafara tasawa Araina na Furta masha Allah.

Mkrantansu Adil suka biya suka daukosa wanda yadan kara girma da wayo kana suka nufi gida.



Bayan dawowar Safeena daga Asibiti bata sani ba ashe Safwan ya nemata gurbi karatu ajamiar kadunar sai da ya kammallah komai kawaai yakawomata addimmision letter dinta da time table dinsu na karatu taga zata karanci Nursing wayyo dadi Safeena sai da tayi kukan Farinciki taje shashen su momma ta nuna musu tana murna haka takira su Ummi tana fadamusu suma sun yi murna kwarai.



To daman lokaci yasanya adil wata mkaranta mai Suna command sch dake kaduna yakuma sanyasa a islamiya shiyasa gari na wayewa dasungama abunda zasuyi sai su shirya yadaukesu yafara kai Adil mkrnta kana ya biya ya kai Safeena mkranta ranar kuwa da bayanan direba ya kaisu.


hakika Safeena na jin dadin karatunta sosai shiganta mkranta takara wayewa tasan me yadda ake taraiyaran mji da kwalliya mai tsari da yabawa hakika Saferna tasamu chanji rayuwa mai inganci ga dan cikanta wanda ke cikin wata hudu kenan yanzu.

















Commet
and
Share
Vote

*Janafty*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞



*DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*



*34*



"Kunya tareda Nauyi sun hana Sakeena zuwa tabawa Safwan hakuri duk da Hajiya kari ta Matsamata taje tagwada sa'arta azahirin gaskiya dukkansu sunyi nadama kuma suna ta tuba ga Allah hajiya karima tanemi gafaran yan"uwanta kuma sun yafemata ammh sunce basu da hurumin dazasu roki Kwamishina yamaidata dakinta sai dai ta cigaba da addu'a Allah yasa tsakaninsu akwai Sauran Zama



wuni yana shudewa kwana yana shudewa ahaka har watanni suka shude awannan lokaci Safeena cikinta nada wata takwas aduniya tayi kiba cikin kuma yayi girma sosai kamar dan wata tara gashi tana karatunta cikin nasara da jin dadi tareda taimakon mijinta kuma gwarzonta Dr Safwan Sale Safana wanda duk abunda bata gane ba inta koma gida yana kara koyamata,Shi da kantshi yakemata awo ammh shikanshi girman cikinta na bashi tsoro duk da yamata scan kuma yaga komai lpy.


Su hajiya mama da momma kuwa rayuwa sabuwa domin yanzu basu dawani mtsala sukam damar Sakinace damuwarsu kuma yanzu batanan shiyasa yanzu bakajin Hajiya mama na kwakwazonta na fama sai dai in yan abun sun motsa kunsan mai hali bayasa Halinsa.





KANKIA


awannan watannin in ku ka ga yadda su Sakina suka koma sai kun zubar musu da kwallah saboda yadda suka rame suka kammajame sakina fuska tayi baki ta kuma cika da kuraje ga kan nan yayi duku duku kamar na mahaukaciya kumbuna sun yi baki sunyi datti hajiya kari kuwa kamar tsohuwa takoma saboda wahala.




Yau tunsafe Sakina taje layin bowol ammh sai wurin takwas tasamu zuba ruwanta tadauko daya akanta daya yana hannunta tana tafiya zata gida taji ana mata hon abaya kaucewa tayi domim bata zata da ita ake ba sai da motar tazo daf da ita kana ta tsaya cikin mamaki take bin jeep din da kallo kafin taga anbude murfin mota anfito wazata gani...Daddy ta furta cikin mamaki ya amsa da "Na'am sakina kece kika koma haka "yafada idaninsa sunkawo ruwa zatayi mgana kenan wata farar mata ta bude mota ta fito sanye cikin leshi da mayafinta bawata babba bace bata wuce sa'ar Anty salma ba.


Ta nufe sakina cikin tsausayawa tana fadin"Innalillahi...Sweety badai dota Sakina bace wannan..?"Kwamishina yagyda mata ta yi saurin saukemata ruwan ta rumgumeta tana fadin"Baka kyauta ba Sweet hrt kowa yana kuskure ko Allah muna masa laifi yayafemana ko"baicemata komai ba sai ma cema direba yayi su karisa.


Sakina sai kallan matan take datake rike da hannunta har cikin gida ai sakina sai ta shiga kwalama Hajiya kari kira tana fitowa Daidai kwamishina yana shigowa ai sai tayi cak tana kallonsa shima ita yake kallo yana nuna ta da mamaki hawaye ya zuraroma Hajiya kari sai ta koma daki da gudu tana kuka...dakin matan tabita tana rike da sakina.


Hajiya kari dake durkushe tana kuka tadafa tadago tana kallonta murmishi ta sakarmata kafin tace"Don Allah kibar kukan nan hakanan ko Allah muna masa laifi yayafema na balle mu mutane"Hajiya kari tace cikin kuka wacece ke!...MATATA CE....dana aura bayan Rabuwarmu...atare sakina da hajiya kari suka kara kallonta itakuma tana musu mirmishi.Dady Yafadi haka bayan ya sawo kanshi dakin yakarasa shigowa yana fadin"Bayan na koreku kwana biyu kawai na kara nabar kasar sai da nayi wata uku baninan karkuyi mamaki duk halin dakuke ciki inada lbr...Dagacham saudayi na wuce achan na hadu da Mariyatul kibdiyya wacce asalinta yar gombe ce tayi aure mijinta ya rasu ammh bata taba haihuwa ba mahaifinta shine wazirin masarautar gombe munyi aure wata hudu da suka wuce daman nafadamata yayana hudu shine da bata ganki ba ta tambayeni nikuma na fadamata komai wlh tallahi tunda na fadamata ta kasa sukuni akan lalle Saina yafemuku kuma saina zo mun dauko ku.....mu koma gida.




Sakina tafada cikin rawan murya"mu Dady...Kayafemana mu koma gida harda Hajiya"Dady yace"kwarai ma Sakina tare zamu koma domin tun jiya da asuba na sanya aka maida aurenmu....Da mahaifiyarku nasan ko ahaka na barku kun fahimci rayuwar danike gayamuku"Sakina ta guce da kuka kan zube gaban daddy tana kara basa hakuri dagota yayi ya sharemata hawaye yace"ba'a san raina na muku haka ba wlh sai dan ku gyaru kuma ku gane yadda Rayuwa tasa gaba,sakina tace"Ba komai daddy hakika kaci ka uba nagari...Wlh ko ahaka nagane daddy nagane mutum ba komai bane.


gurin Mariya taje ta durkusa tana fadin"mungode Anty hakika bamu da bakin gode miki Allah ya saka miki Aljannah"kamota tayi ta rumgumeta tana fadin",babu komai yata...Karki damu inaji kamar nina haifeki Sakina.Mirmishi sukama juna lokaci daya kan taja hannunta suka fice.


Hajiya kari takasa dagowa ta kalli kwamishina saboda kunya shine yayi gyaran murya yace"Basai kin ce komai ba karima Allah yayafemana gabadaya.."Tadago idanunta jawur tace"Ban chanchanci yafiyarka ba kabiru wlh ban chanchanci yafiyarka ba sam"takareshe fada da kuka takawa yayi ya isa gareta yadagota yana sharemata hawaye yace"ko alama karima duk nasan kin min abubuwa masu yawa ammh tunda kingane kuranki wlh har ga raina na yafemiki kuma nasa anmaida auranmu..da zuciya daya sai dai bansani ba ko zaki iya zama da kishiya"da sauri Hajiya kari tace"wane ni daja da abunda Allah ya halarta...Ai samun abokiyar zama irin mariya sai an tona...Ngd sosai Allah yakara girma.Mirmishi ya sakarmata yana kara gogemata hawaye.



nan suka wuni har su yayyen hajiyan suka dawo sukayi mgana da kwamishina yasaukemusu kayan abincin dayazo dashi sukuwa su sakina yace kada su dau komai aikuwa murna gurinsu ba'a mgana dazasu tafi suka roki gafarar kowa suma mutan gidan suna neman tasu ankara musu fada kan sundai ga rayuwa inzasu natsu yarage nasu,gidansu kwamishina suka biya suma chan din albarka sukaita sanyawa musu har suka tafi.


Amota mariya babu ruwanta sai jan Hajiya take da hira ita da Sakina su kuwa sunkasa sakin jikinsu da ita itakuwa ko ajinkinta sai jansu take ajiki.



Suna komawa takai Sakina har daki ta hadamata ruwan wanka tadauko mata wata doguwar riga ta ijiyemata hakama tama Hajiya kari wacce kunya ya hanata mgana bayan shiganta wankane hawaye ya zuraromata wai yau itada take iko da gidanta sai gashi yau watace ke iko dashi...Ba shakkah duk wanda bai godema Allah da Ni'imar sa ba zai godema wuyarsa.


Ita tai ta dawainiya dasu suna godemata kayanta ta daukoma hajiya kari kafin gobe aje asiyama su nasu kayan.


Allahu akbar Sakina da Hajiya dasuka sa hakarkarunsiu akan katifa suka furta domin ko amafarki basu taba tsammanin zasu dawo rayuwarsu ta baya ba..Koda gari ya waye hakanne yafaru a dining suka ci abinci tun basu sakin jikinsu har dai suka fara sakewa da ita.



Kwanan su biyu dawowa komai yafara zama normal tuni an musi sabbi dinkuna abunsu hajiya kari tazama wata so cool da ita kamar ba itaba itakuwa Sakina Anty na iya bakin kokarinta na ganin ta saki jinkinta,washegari sai ga Laila tazo gidan tana ba su Sakina hakuri na rashin zuwanta kankia Sakina ta mata dariya kawai tace"Anty laila kenam bbu komai Rayuwar kenan...Sai kuma naji ance ya mujaheed yayi aure"tace"eh...Wlh wata biyu dasuka wuce"Sakina tace"to meyasa kika yarda"tazaro ido tace"so kike in tada hankali nima ya sake ni ko"Sakina ta kalleta hawaye ya ciko idanunta tace"oh..Ammh ni kikace in tada hankalina ashe kinsan Safwan zai iya sakina in namai abunda kikace kenan ko"Shuru Laila ta mata mikewa Sakina tayi tace"basai kinyi mgana ba nagane komai domin ni yanzu ashafin rayuwa ba abunda bangani ba"da sauri Laila tasha gabanta tana fadin"kiyi hakuri yar'uwata nima nasan sam ban kyautaba amtsayina na yayarki....Ki yafemin don Allah"Kallonta sakina tayi kan tace'shikenan bbu komai...Harda haihuwar dakikasa na dakatar duk na yafemiki duk da ke kinata haihuwa kamar naga ga wani karuwar nan mun samu"tana gama fadar haka ta fice tana sharan kwallah,hajiya kari dake gefe tace'Mumaka sa sakina ta tafka kuskure mune sila wlh"Anty laila tace"Allah ya yafemana....Ammh tadade tana saka mganar sakina tasan mgana ta saka mata.




Asatin Anty salma tazo ita da Ummi daman tana hannunta tuni tayi murna matuka kuma ta kara musu fada sosai lalle ta yarda duniya tahora hajiya koda yarda tayi sanyi Anty mariya tana ta fadin"Yaya kaza,yaya kaza...Hajiya na amsawa da kulawa...Zamansu gwanin sha'awa kamar ba kishiyoyi ba,Anty kwananta biyu takoma ammh kafin takoma sai da tace ta shirya taje har gida ta ba Dr hakuri ko ya maidata dakinta tabbas tayi na'am da shawararta shiyasa washegari nayi ta shirya cikin dogon hijabinta har kasa Anty mariya ta aramata motarta tamusu sallama ta fice suna mata fatan sa'a.




Cikin sanyi jiki ta dumfari gidansu Safwan lokacin da Habu mai gadi ya budemata get bai ganeta ba sai da ta paka motar ta fito tana gaisheshi take tambayansa ko Safwan yana gida,ya amsa mata da "eh...Yana nan hajiya mirmishi ta mai kawai tace"Sakina sunana ba hajiya ba"Ai sake baki yayi yana kallonta kan yace"Au...Sak...Oh hajiya barka da zuwa"wucewa kawai tayi ta barsa sake da baki har yana kara lekata.



Shashen su momma ta nufa ta shiga da sallamarta wanda Hajiya mama ke zaune afalon ta amsa tana fadin"Maraba shigo......














Commet
And
Share.
Vote




*Shakira..*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE...!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Dedicated to my momma Hajja khadija muhammd Ba'are*




*35*



"Karisawa tayi cikin falo tasamu gefen hajiya ta zauna kallonta hajiya mama keyi ranta na bata kamar sakina ammh kuma tana karyatawa Sakina tadago ta kalli hajiya kan tace"Hajiya baki ganeni bako..?


.Hajiya mama tace"eh...Kiyi hakuri ban sheda ki ba yan"nan"Mirmishin takaichi Sakina tayi kan tace idanunta na tara kwallah"Sakina ce fa Hajiya"Ai da Hanzari tamike tana salati da karfi ta furta"Sakina...Nashiga uku ni Maryamu Sakina ciwo kikayi naga kin lalace haka"Fashewa da kuka tayi tana Fadin"wlh hajiya nagani kuma nagane koda kika samin tsama sona kike...Don girman Allah Hajiya ki yafemin'Hajiya ta karisa kusa da sakina tadagota tana fadin"Mekika min Sakina wlh bakimin komai ba duk abunda kikaga ina miki don ki gyaru ne...Allah yayafemana gabadaya"Rumgumeta Sakina tayi tana godiya cikin kuka momma dake tsaye tundazu ta kariso tana cewa"Tabbas baki mana komai Sakina har yanzu kallon ya'muke miki"Sakin Hajiya tayi kan ta isa gaban momma ta durkusa tana fadin"Momma...Ban chanchanta kiyi afuwa agareni ba ammh gani durkushe agabanki kiyi duba ga Allah ki gafartamin wlh na tuba nabi Allah baran kara ba nagane kune masoyana na gaskiya"Momma tadagota tana sharemata hawaye tace"Har Abada ban chanzaki ba sakina ki na nan amatsayin yata ta har abada...Karki damu daman baki man komai Allah yayafemana gabadayanmu"Rumgume momma tayi tana Fadin"Nagode momma Allah yakara girma.


Kan kujera suka karisa nan Sakina tabasu lbrinta tun bayan sakin da Safwan ya mata Hajiya mama tace"Allah sarki kabiru hakika ya jarabtu sai dai mu fatan Allah ya kara shiryar damu"Suka amsa Da Amin.


Adil ne ya shigo da gudu yadane cinyar hajiya mama yana Fadin"Hajiyata...Turesa tayi tana fadin"A'a Alhajine...Kai wai bana ce ka kiyayeni ba"Tura baki yayi yatashi ya isa ga momma ya haye cinyarta yace"Bani chonki...Momma nake cho"Yafada yana rumgumeta Hajiya mama tace"To sai me...Aikin banza chan da tsiyarka ni nan har akwai soyayyar data kai na marigayi Habule na nane wallahi bata"Tafada harda jaddadawa.


Sakina dake gefe tana kallonsu ta share hawaye tana kallon Adil dayakara girma da wayo ga yayi kiba abunshi alamun yana Samun kwanciyar Hankali abun takaichi wao ace danta na cikinta ma baisanta saboda wani sakarci nata...Hannu tasa ta share hawayen daya zubomata kada su hajiya su gani ammh ina sun riga sun ganta.


Sallamar Safwan shi ya dakatar da dramar dake tsakanin Hajiya da Adil Tafe yake shida Safeena dake sanye da doguwar riga baka ta sanya mayafi ya rufema cikin jikinta wanda yakusa rinjayarta saboda girmasa kanta na gefen kafadarshi shima ya zagayo hannnsa ta kugunta yana Sanye cikin bakar jallabiya tunda suka shigo Sakina tayi galala tana binsu da kallo ganin yadda suka chanza cikin lokaci kankani Dr Safwan yayi kiba ya murje yakara haske itama Safeenar,tunda suka shigo momma da Hajiya suka mike suna ma Safeena Sannu shiya taimaka mata ta zauna akasa yana mata Sannu Safwan yace"Momma...Wlh zan dawo muku da Adil damun yanmatana yake d kiriniya wai harda goyasa yakecewa ayi fa"Hajiya mama ta dunguremasa kai tace"kaga min mugu...Don ubanka da uban cikin da ubanka yamata zataji kokuwa da goyaka"😂kunya takama Safeena da momma shiko Safwan ko ajikinsa Tabe baki yayi zai fashe dakuka tace"Kaji gidanku wlh kanamin kuka zaneka zanyi ja'iri kawai"Kuka yasa yatafi da gudu gun momma yarumgumeta Safeena tace'Amana hakuri Hajiya kin manta yace zai Siya miki jirgi"Hajiya tace"Bani so Raggo kawai'dagowa yayi hawaye shabe shabe yace"Ba chan chiyanmiki jigi ba Daddy da mami na jan chiyama wa...Kuma baja ki hau ba"Yafada harda murguda mata baki dariya sukasa mishi gabadaya.


Safwan yadago yana dariya kawai caraf idanunsa suka sauka kan Sakina dake zaune gefe tana ZUBAR KWALLAH...Aziza idiris gombe...Bana gajiya da Novel dinnan walle....Kuramata ido yayi cikin mamaki da firgici kamar fa Sakina yake gani ganin inda yake kallo yasa suka bi gun da kallo Safeena takurama Sakina ido tana kallonta Aranta tana so tace Anty ammh wata zuciyar tana cewa ba ita bace"Sakina tayi saurin mikewa tana fadin"Momma..Zan tafi dama nazo gaishekune"Tafada tanayi hanyar waje...SAKINA..Dr Safwan ya furta da mamaki cak ta tsaya ranta na mata kuna Hajiya mama tace"kwarai...Tun dazu tazo neman gafararmu"Kai tsaye yace"kuma kuka yafemata"Juyowa tayi cikin kuka tace"Daman nasan ban chanchanci yafiyarku ba...Safwan"Tafada kuka yaci karfinta baya ya juyamata kawai ransa namasa kuna rarrafawa tayi ta isa zuwa gabansa tana fadin'Na san ban chanchanta ka kalleni ba Safwan ammh kadubi darajar Allah kadubeni da idon Rahama kayafemi ko naga daidai Rayuwata"shuru yamata Safeena ta mike dakyar ta isa kusa da Sakina ta durkusa tarike hannunta dagowa tayi tana kallonta ita kuma ta mata mirmishi kallonsa tayi tace"UNcle....Saurin jiyowa yayi yana kallonta kan yayi saurin cewa"Ke kina da hankali kuwa bakiga halin dakike ciki ba...Tashi tashi.."Kin tashi tayi saima cewa datayi'Kazama mai yafiya unku...Kaima sai Allah yadubeka da idon Rahama...Anty tayi kuskure kuma tagane kuskurenta Don Allah kabata dama baxata sake ba"Shuru yayi kan yace"ki tashi nace itama kallon idanunsa tayi tace"Bazan tashiba sai ka furta ka yafemata"kallonta shima yakeyi kan yayi ajiyar zuciya yace'Taji albarkacinki....na yafemata Allah ya yafemana gabadaya"Alhamdulillah...Haka cikakken musulmi yake"Hajiya mama ta furta.


Sakina tasa hannu tadago Safeena ta rike hannunta tana fadin"Bansan mezan cemiki ba Safeena...Ban sani ba'Tafada idanunta na kawo ruwa"Safeena ta damke hannunta tace"Basai kin ce komai ba Antyna wlh kin wuce haka agurina ammh alfarma nake nema agunki"Sakina tace"Ki fadi komiye safeena indai baifi karfina ba zan miki shi Safeena"kai tsaye Tafada tana kallon Dr Safwan"Ki dawo kizo mu zauna mu reni ya'yanmu tare kuma mu rumgumi mijinmu...Mu zauna har Abada"Kallon kallon aka hau tsakanin Dr Safwan da Sakina saurin sadda kai yayi yace"A'a.....Safeena tayi gaskiya ka maidata dakinta ku taru ku rufama juna asiri...Ku zauna lafiya da juna"Hajiya mama tace"shikenan kuwa...Allah yayi miki albarka Safeena Allah ya rabaki da cikin jikin ki lpy"gabadayansu suka amsa Da Amin.


Rumgumeta Sakina tayi tana kuka tana mata godiya safeena tadagota tana sharemata hawaye tace"Kidaina godemin Anty kin wuce komai agurina"Itama sai hawaye sharr Adil ne yaga suna hawaye duka biyun zuwa yayi ya rike ma Safeena hannu yana Fadin"Mami...wacece wannan.."yafada yana Nuna Sakina shafa kansa tayi kan tace"UMMINKANE...Itace mahaifiyarka"Kallonta yayi yace yana kallon Sakina"UMMI.....Yafada still yana kallonta sakina ta rumgumesa tana hawaye tace"Ni Umminkane ta haihu Ammh Mami mahaifiyarkace ta har abada"Tafada tana shafa kansa abun mamaki shima rumgumeta yayi yana sharemata hawaye.


_Allah sarki Uwa Uwa ce komai lalacewarta_




Komai ya daidaita cikin lokaci kankani Sakina nan ta wuni tana dawainiya da Safeena da Adil ita tataya momma Aikin girkin dare sai da suka kammallah kunsan Raba dare sukai suna hira kafin safeena ta barota cikin dakinta takoma gun Dr Sakina tayi kuka awannan daren na ganinta kwance kan gadon tabata tsinana komai ba sai lalacewa...Raba dare tayi da ibada da asuban fari tatashi kokan Su Safena su fito Sakina ta tsaftace gida ta hada musu break kwai ta soya musiu da ruwan tea suna karyawa DR yayi harama abun mamaki har Adil na zarin shi zai bita lallabasa sukai suka shiga mota suka kaisa mkranta kana suka biya suka ijiye Safeena asch tana da test tai musu fatan dawowa lpy,suka kama hanya shida Sakina direba yana binsu abaya da motar data zo dashi,Shizai kaita saboda mganar Maida aurensu.


Hakika kwamishina yayi murnan dawowar Safwan amtsayin sirikinsa a kashi na biyu...Hajiya kari saboda godiya harda kuka tarokesa gafara kuma tace ya rokan mata su Momma kan tazo...Anta dawainiya dashi an fahimci juna sosai cikin mutumci da girmama juna sai la'asar yayi shirin tafiya rako sa tayi gun motarsa kallonta yakeyi bako kiftawa Kauda ido tayi kan tace"Wannan...Kallon fa"mirmishi yayi yana Shiga mota yace"Mamaki nake wai Ke Sakina kabir kankia ce kika zama ustaziya"Dariya tace"Ka adana mamakinka sai Auren ya maidu tukunnah..."Tafada tana rufemasa murfin mota kallonta yayi yace"Sure....Gyada kanta tayi kawai dagamasa hannu tayi har yafice daga gidan.














commet
And
Share
Vote.


*Anitha...*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE...!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞


*36*

Shirye shirye takowani bangare ya kamkama Tahir dayaci lbrin komai shima kansa yayi mamaki ammh kuma mamakinsa ya gushe domin tare suka koma kt shida Safwan jin shirye shiryen da take gudanarwa abun mamaki Sakina tace bata dawani shiri itakanta walima ce kuma sunyi mgana da Safeena ranar asabar za"a shirya ma'ana bayan ta taren.

Ranar jumma"a Daddy shi yazo kaduna bayan sallar jumma'a amasallachin sultan bello aka maida aurensu akan sadaki dubu talati,kuma ana gama daura auran Tahir ya wuce yaje ya taho da',ita domin daddy yace kada wacce taje Anty salma dama bata samu zuwa ba Anty lailace tazo itama kuma Daddy yace gobe takoma gidanta,Anty mariyace kadai tarakata bayan tarin masihohin data sha gakuma gyaran da Antyn nata ta zage ta Mata.

itakanta Anty mariyan bata jima ba ta musu sallama Daddy ya zo suka wuce...Suka barta nan shashen momma ita dasu Safeena da Adil wanda ke yaketa tsalle Sakina tadawo gidansu bbu wani gyaran da Safwan yayi ma gidan sakamakon yana chan yana kera musu wani gidan a Malali Gra katon gidane sama da kasa shima din bangare biyu yayi musu ammh shi wannan din wlh duniyace ko su hajiya basusan da gidan ba Shida Tahir ne kadai suka Sani.

Sakina Da Safeena sai da Dr Safwan yadawo su hajiya suka tarasu suka musu Nasiha kan su hada kansu su zauna lpy,sai wajen 9 na dare suka Nufi shashensu achan din ma dumguma sukayi dakin Sakina suna hira Safwan duk sanda ya kalli Safeena ransa kara fari yake domin komai yake faruwa ayu wlh itace sillar daidaituwan komai...sai da taga Dare yayi kana ta musu sallama Safwan yadaukan mata Adil dayayi barci yarakata daki wanda Sakina tace ta yafe yaje gun Safeena ya kwana tunda ita tana da lalura...Kin yarda Safeena tayi shiyasa yana kwantar da Adil  tashige bayi tana fadin"Unku mu kwana lpy...girgiza kai kawai yayi yawuce saboda yasan da gangan tashige bayin don karya mata wani mgana ne.

dakinsa ya koma yayi wanka ya sanya jallabiya yafeshe jikinsa da body spry masu kamshi kan ya nufi dakin Sakina da Sallama ya shiga ta amsa tana ninke darduma kallonta yayi kan yace"Me kikayi...?Tace"sallar issha'i...Yace'ok...Koma muyi sallah don yau ta dabam ce you know...Mirmishi tamai kawai yajagorancesu sukayi Ra'ka"a hudu yadade yana musu addu'a kafin su kammallah yasan Sakina nada rauni a addini dat why yai mata alkwarin koyar da ita Insha Allahu.

Tabbas Daren na Alkhairi ne domin Safwan da Sakina sun darji juna iya son ransu an famshe watannin da'aka diba ba'a tare...Tun asuba sakina bata koma ba tahau gyaran gida tana kammallawa takoma kichen doya ta soya musu da kwai sai ruwan tea domin dai girkin ba wani iyawa tayi ba wannan ba don komawarta ne take gani gun Anty mariya yasa ma ta iya wasu Abun.

Hakika zamansu yana gudana cikin kwanciyar hankali da zaman lpy duk da Sakina na iya bakin kokarinta yanzu ammh duk da hakan tasani kuma tana gani safeena tanada wani mtsayi agidan wanda daga Safwan har su momma girmamata sukeyi...Tasani ita tabar damanta har wata ta kwace sai dai kawai tayi yar hawayenta ta share,kwana uku yabar dakinta bisa na al'ada yakoma suna kwana daya akowani daki.

Bai bafada musu mganar sabon gida ba saida ya bari weekend kana yace kowa ya shirya za'a fita hardasu momma mota biyu sukayi safwan na tuka su momma da hajiya sai Tahir ya tukasu Safeena basu gama mamaki ba sai da suka gansu a wani makeken gida upstair kamar kasar turai ba kai tsayawa bada lbrin wannan gidama kauyancine sai dayagama zagayawa dasu ko'ina na gidan yaji alatun kayan more rayuwa gida dai wallahi ko akasar turai.

Sai da suka koma gida ya tarasu yafada musu cewa achan zasu koma dukkansu bayan haihuwar Safeena kwarai da gaske sunyi murna ammh sai Hajiya mama tace"Hakika naji dadi safiyanu kuma muna maka murna ammh zahirin gaskiya nida Hadiza bazamu biku ba domin me muke nema arayuwa komai kagama yimashi sai muyi ta maka addu"a da fatan dacewa muna nan gidan ya ishemu jin dadin rayuwa ko yi komawarku chan kai da matanka Allah in kunsamu lokaci kwa leko agaisa"Babu yadda sukayi iya domin Hajiya mama da ce wlh baza koma chan ba dole aka barshi ahakan.

yau Sakina keda sati uku da tarewa misalin karfe goma da wani abu na dare barowansu kenan itada Safwan daga dakin Safeena safwan yana bayi itakuma tafito falo daukan wayanta sai kawai taji nishi kuma daga dakin Safeena abun ke fitowa ai da gudu ta shiga dakin ta isketa durkushe tana nishi gashi wani ruwa na biyota ai A sitti takoma daki tana kwalama Safwan kira fitowarsa kenan daga wanka da sauri yazira jallabiya suka rankaya Suna zuwa kofar dakin sukaji kukan jariri ai da gudu suna bugan kafadar juna suka antaya dakin shigansu yayi dai dai da sawo kan dawani jinjirin yayi da sauri Safwan yasa hannu ya jawoshi Safeena takoma ta kwanta tana maida Numfashi cikin farin ciki Sakina tadauki dayan tana fadin"Alhamdulillah Ala kulli Halin Safwan yan biyu ne Safeena ta haifa shima bakinshi yaki rufuwa Safeena kawai yake jerawa sannu harda hawaye da jinin da komai yahada da yayan ya rumgume yana zubamata godiya sakina sai da tayi kwallah tana tuna da itama yamzu Safwan zai ma wannan rawan jikin.

cikin lokaci kankani suka gyara komai Safwan ya yankema yara cibi itakuma Sakina tagyara wurin safwan dakanshi yadauki Safeena sai toilet yahadamata ruwan wanka yahau gasata yabarta ciki saboda taji dadin jikinta,komawa yayi shida Sakina suka zage suka wanke yaran tas suka sanya musu kaya suka jerasu kan gado suna kallo,safeena na fitowa suna rigen rigen mata Sannu sakina tahadomata shayi mai kwauri tasha ...Kai in takaice muku nan suka kwana suna dawainiya da Safeena sai da Safe da Safwan yadawo sallar asuba yashiga yake fadama su momma safeena ta haihu cikin farinciki suka dumguma kan kace kwabo haihuwar Safeena tazagaya dangi shida kanshi suka tafi asibiti yaduba da ita da yaran ya tabbatar da

Please Login or Register in order to submit comment