Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyo baya Ummi kunya yahanata daga kai shikuma Dr Safwan tagefen ido yake bin gidan da kallon duk da dai talakawane ammh suna da tsafta ko'ina ashare shima Dr Tahir hakane ammh aransa fadi yake"Kar dai ace Wannan babar itace Safeenar😂😂😂,cikin kunya Ummi tace"Ku zauna kan tabarma bari insa asiyo muku ruwan sanyi' ciccire takalmansu Sukayi suka zazzauna kai aduke Dr Tahir sai dariya yakema Dr Safwan kasakasa shikuwa yanajinsa yama sa banza.




Ummi ta shga daki takwalama Manu kira yazo tabashi kudi tana fadin"Kasan gidan su Gaddafi...?ya amsa da eh tace to maza hanzarta kaje yaya Safeena na gidan kace ta yi hanzari tadawo inzaka dawo ka biya shagon basiru kasiyo min ruwan gora guda biyu.






*Shakira...*


Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞

_*Dedicated to my wattpadians Fans and my Whatsappians Fans ina ganin sakonnin Fatan alheri da Addu"o'inku Allah ya saka da Alheri Tanque so much Allah ya bar Kauna da zaman Tare Ameen..*_




*17*


Yako zura da gudu ya fita Ummi tace"'oh ni Zainabu Allah dai yakai lpy...",gashi tana so tamusu bayanin Safeenar tadan fita zuwa gaida kawarta,ammh kunya ya hanata Fita,uwa uba kuma tana son komawa kichen domin tadora miya aranta tace bari Safeenar ta shigo su dawo daki inba haka ba Takurani zasuyi oh ni Ummi kunya🤔



Manu kuwa da gudu ya shiga gidansu Aisha mamansu Aisha tace'kai daga ina?"yace"Ummi ce tace Yaya Safeena tazo yanzu"Maman Aisha tace"Tom gatanan zuwa kara fice yayi yanufi shago siyan ruwa,itakuwa maman Aisha lekawa tayi dakin da su Aishan ke ciki tace"To iyayan daka kufito kusha iska ke Safeena Ummi ta aiko kije yanzu"Safeena ta mike da sauri tana Fadin"To lafiya...Dan Ummi bata taba aikomin ba"Maman Aisha tace"Nima dai..Ki hanzarta komeye mai mahimmacine kam"Hijabinta ta sanya saboda sauri Nikabin ahannu ta rikoshi.



Tana tafe ahanya tana zencen zucci Allah yasa lafiya domin yadda gabanta ke faduwa tun safe nan da nan ta kawo dayake babu tazara Daga gidansu zuwa gidansu Aisha, taga mota akofar gidansu ammh ko alama bata kawo gidansu tazo ba tasan dai bawani mai zuwa amota balle tasa rai _Allah sarki Safeena to yau gashi mai motarma mallakinkine_



Da siririyar muryanta tayi sallama tasawo kai cikin gidan,kanta na duke shiyaasa bata lura dasu ba ammh kamshin Turaren Dr Safwan ya cika tsakar gidan,da hadaddun takalmansu tafara cin karo binsu da kallo take cikin Mamaki,har zuwa mamallakan takalman idonta yafara Sauka kan wani hadadden Namiji fari mai cikar zati da kamala da haiba mai dauke da doguwar fuskar sajensa ya zagayen bakinsa wanda yakaramasa kwarjini hakiki Allah yayi Halitta Anan gurin sai akayi sa'a tun lokacin da Dr Safwan yaji muryan Safeena cikin sanyi da natsuwa tayi sallama yaji muryan tadakesa yayi saurin dagowa ya zuramata ido yana binta da kallo daga sama har kasa yakasa dauke idanunsa daga kanta duk da babu abunda zai dora da kamanninta ammh zuciyarsa da gangar jikinsa sun Fada masa cewa wanna ce _*SAFEENARSA_ kaji Dr S S Safana wai Safeenarsa🤔



lokacin da idanuwansu suka hadu wani marganet ne yajasu dukkansu Safeena ta tsinci kanta awani yanayi na mutuwar jiki da sauri ta sadda kanta kasa jikinta ya cigaba da rawa kafafunta Sun kasa daukanta Dr Tahir ne yayi gyaran murya saboda yaga yadda Safinar ke gabda faduwa.



Waskewa Dr Safwan yayi yacigaba da latsa wayarsa ammh zuciyarsa na fat Fat kamar wanda yayi gudun famfalaki DrTahir yayi karfin halin cewa"kari so mana malama Safeena"cikin rashin kuzari Safeena tadaga kafa ta kariso sai data danganta da kofar dakin Ummi kana tace cikin rawar murya"Sa....sannunku da....Da zuwa"Yauwa Sannu Dr Tahir ya bata amsa yana kara kallonta yadda Hijabin yake wani zumbudede dashi harda Safa duk da kanta na duke adan kallon dayamata yafahimci yarinta karara atare da ita.



Tana cewa haka tafada daki da gudu tana Haki Ummi tayi Saurin mikewa tajawo hannunta suka shige kuryan daki tace"Safeena mijinkine fa suka zo"sororo Safeena tayi gabanta na tsananta Faduwa tace"mi...Mi...Mijina kuma Ummi..?"Ummi tace"Eh....Nima kwatsam na gansu kinga bbu lokaci na aiki Manu siyo ruwa shuru bai dawo ba bari ni in je inji da abinci da za"a musu,kekuma ki koma gurinsu"Safeena tace"Ammh..Ummi"Ke wai wata irin shashashace ko bakiji menace miki bane,"Ummi tafada ranta ya baci"Safeena tace"yi Hakuri Ummi zanyi yadda kikace daga haka tafice tayi tsaye afalo hannunta dafe da kirji tanajin zuciyarta nawani harbawa.




Sukuwa tana shigewa Dr Tahir ya zunguri Dr Safwan yana Fadin"Kai mijin malama kako ga malamartaka i think fa itace Safeenar"Banza dashi Dr Safwan yayi sai dannan wayansa yakeyi,ganin haka yasa Dr Tahir kama kansa agurguje Safeena tadan kara gyara falon ta shimfida musu darduma kan ledar dake tsakar dakin,cikin sanyin jiki ta leko da kanta tace"ku shigo ciki kuna zaune awaje"Dr Tahir yace"a"a ayi Haka ranki yadade"mirmishi tayi kawai atare suka mike Dr Tahir ne yafara shiga da sallama kana Dr Safwan wanda Safeena ke tsaye akofar dakin har yanzu suka zauna,ita dai Safina kanta aduke takasa motsi Dr Tahir yazauna yana Fadin"Masha Allahu..Amarya baki tambayi wanene angon naki ba"yafada yana kallon Dr Safwan dashima yawani sadda kai



Wuf ta fice tana Rufe fuska dukkansu suka bita da kallo Safwan yanajin wani iri aransa kunya tab to shi ina ma Sakina takeda kunya balle ayi mgana taji kunya,mirmishin gefen baki yayi yana bin inda tabi da kallo.Dr Tahir sai kallonshi yake yana mai dariya kasa kasa.




Ummi ta fito itama cikin kunya suka kara gaisawa kana tafice ta tararda Safeena zaune a kichen tayi tagumi Ummi ta kalleta tace"Ke kam Allah yayi miki Sauki...'Safeena tayi saurin mikewa tana rufe fuskar Ummi tayi dariya kan tace"Allah ya shiryeki..Kinga nifa tuwon shinkafa nakeyi miyar zogale ya kike gani za'a sake yi musu wani Abun ne..?Safeena tace"Ki barshi Ummi wlh sai kiga sunfi son tuwon ma "Ummi tace"ok sai na musu zobe su hada dashi,maza ki koma gurinsu niban ma gane surikin nawa ba duka yaran masha Allah.



Ummi tafada tana dariya mirmishi Safeena tayi kan tafice tana fita manu yakawo ruwan swan din guda biyu ta amsa ta sanya cikin faranti tahado da kofuna da sallama tashiga suka amsa,ta durkusa ta ijiye Tahir na mata sannu da aiki tadauki kofi tana tsiyaya musu Dr Safwan yana kallon ta ta wutsiyar idanunsa aransa yana jinjinama Hajiya mama ita aganinta wanna ficilar yarinya ne zata iya dauke Nauyinshi tab shi atunaninshi duk randa ya haikemata zata iya Mutuwa _see dis guy to ka gwadane_🤒



Gefe takoma bayan ta zuba musu ta zauna akasa kanta a duke tana wasa da yatsun hannunta kowani dakika na mintina zuciyarta na bugawa,Dr Tahir yasha ruwa yana fadin"Munsha ruwan Amarya.."Yafada yana mirmishi kan ya cigaba da cewa"an dawo lpy kuma nanawa aka ciyo mana...?"ta gefen ido take kallon Tahir kan tace cikin sanyin muryanta"Na biyu nayi...Lafiya kalau"Yace"Wow..Masha Allahu lallai kin cika Hafiza"Mirmishi kawai tayi Tahir ne keta janta da mgana tana bashi amsa da umh a"a shikuwa Dr Safwan yana ta danne danne awayarsa ammh hankalinshi kaf akansu yake lokaci kankani yaji yarinyar ta burgesa yadda takeda aji da kamun kai.



Mikewa DR Tahir yayi yana Fadin"Bari na baku guri ku zanta.."yafada yana ficewa Safwan yarakasa da Harara,yana waigowa karaf suka hada ido tayi saurin sadda kai kasa mirmishi yayi yasamu kansa da kuramata ido kur yana kallonta jikinta yabata ana kallonta tana dagowa idanunwansu suka sarke ma juna,wani miracle ne ke aiki atare dasu kamar ansa super glue an manne musu sun kasa daina kallon juna.




Safeena taji jikinta na saki da wannan azababban kalon da Dr Safwan ke binta dashi ita tayi saurin jaye idanunta saboda bazata jure wannan kallon daga Dr ba,jikinta yana rawa takara dukar dakai tana kara jin bugawar zuciya.




Dr Safwan kawai yaji yasamu kansa da cewa"An dawo lafiya...?Allah yasa albarka"cikin husky vioce dinsa ya furta haka tadago tana kallonsa aranta tana fadin"So sweet.."Tace"Alhamdulillah nagode..Daganan shuru ya biyo baya Ammh lokaci bayan lokaci suna satan kallon juna,sai suyi mirmishi atare.



Shikuwa D Tahir yana chan yatasa Ummi da hira ita kuwa haka takeso mutum mara bakunta tana bashi lbrin amintar Haj.Mama da iyami shikuwa yanata jinjina girman Amintansu.





Abun Mamaki saiga Dr Safwan yana abunda bai sababa wato mgana sai gashi wai Safeena Ta chanzashi da surutu yana tambayanta kan matakin karatunta tundaga na boko har na arabi yayi mamaki na yadda karamar yarinya kamar Safeena take da ilimin sanin littafan addini haka gaskiya ya jinjinama iyayanta matuka,tadan Sake dashi sama sama ammh ita aranta mamaki take wai yau itace ta mallaki miji iri Dr Safwan miji na Nuna sa'a wanda ko wacce mace take fata ta mallaka amtsayin miji duk ko takamarta da nasabarta da ikonta kallon daya zatamai taji ta raina kanta da duk abunda ta mallaka kuwa.
salla kawai ke tadasu.






Tabbas su Tahir basu Nuna bakunta ba suka zage suka ci tuwonsu Dr Safwan yaji dadin cimar saboda abincinsa duk miyar da akayita da ganye masoyiyarsa ce ga lafiyayyah zobonsu wanda tas suka shanye suna hamdala da wannan gidan irin albarka,saboda dadin Hira basu ankara ba sai da Tahir yaga shida Saura yaleka su Safeena yana cewa"plz amarya ama na hakuri hakanan kada muyi dare a hanya"Safeena tayi yar dariya tace"To ni na rikesa"Dr Tahir yace"kece mana to inbake ba To waye"..?Yafada yana kallonta hannu tasa ta rufe fuskarta Dr Safwan ya tsuramata ido yanajin wani shauki na dibansa domin wannan sa hannun datake tana rufe fuska shike burgesa yakesamasa shauki wanda yarasa ko na menene.





Minti biyar minti goma shuru Dr Safwan yaki fitowa yana chan kawai ya zurama Safeena ido yana kallonta so yake ya fahimci wani yanayi yake tsintar kansa in yana kallonta ammh yagaza fahimta sam,dakyar ya yakice abunda yakeji ya mike yana kallonta yace"to madam mukam munyi harama"Da wutsiyar ido ta kallesa kan tace"daman ba kwana zakuyi ba..?"tafada da wani salo wanda ita batama san ta iya ba,mirmishi yayi kawai yana kallonta kasa mikewa tayi saboda idon daya zuramata yana kallonta yana wani shafa sajensa yana cizan lebensa na kasa yunkurawa tayi tamike tayi gaba tana Fadin"Allah yammh tayi kukoma kaduna yanzu"tafada tana isa kofar dakin da sauri ya isa ya cimmata tana kokarin fita ya bangaji kafardarta atare sukaji wani shock kamar wuta yaja su dagowa tayi tana kallonsa kawai sai yasamu kansa da dagamata gira daya yanajin wani farinciki na shigarsa,sunkuyar dakai tayi ta fice da sauri,Akasalance ya fito yana ma Ummi sallama.


Ummi tace"A"a Tahir dare bai yi ba yanzu fa za'a kira magarib..?'Dr Safwan yace"Babu komai Ummi muna da Aiyuka gobe asibitine infact ma bamuyi shirin kwana ba"Safeena dake gefe tsaye jikinta duk yayi sanyi yanzu shikenan mr handsome zai tafi ya barta _topha safeena har Dr Safwan din yazama mr handsome_😛




Ana haka saiga Abba yayo sallama yashigo hannunsa rike da manu da usman ummi tace"Shikenan ma ga Abbanta nan yadawo, Ummi tanamai Sannu da zuwa tana fadin"Allah yasa zaku hadu mijin Safeena ne sukazo shine wai yanzu zasu tafi"Abbah ya kariso yana fadin"Masha Allah...Sannunku da zuwa' zubewa sukayi suna kwaasan gaisuwa ya amsa yana tambayansu yasuka barosu suka ce suna gaishesu.


Abbah yace"to masha Allahu...Ammh dai zaku fasa tafiyarnan dan magariba ma ake kira'Dr safwan zaiyi mgana Dr Tahir yayi saurin cewa"Toh Abbah matsalar bamuyi buking din gurin kwana na bane"Abbah yace'Haba dan wannan babu matsala akaba na wajema balle ku nagida kuyi sallah Safeena tarakaku nan gidan su baffanta isuhu sai ku kwana"Ummi tace Shikenan kuwa"Abbah yace akawo musu ruwa abuta Safeena tazuba musu ta mikama kowanne tana Zuwan kan Dr Safwan sai da ta duka kana ta mikamasa zuru yamata domin a iya tsawon rayuwarsa Sakina bata taba bashi ruwan alwala ba balle har ta rankwafa karba yayi yana fadin"weldon..yanmatana"yafada ahankali da sauri ta wuce tana rufe fuska,tare sukayi alwala da Abbah dasu usman suka rankaya massallaci abun ya matukar burge su Safwan yadda Abbah yasake jiki dasu yana ta tambayansu aiyukansu abunda Safwan ya fahimta su Safeena talakawane ammh masu wadatar zuciya kaf da kanta har iyayenta lokaci daya yaji sun kwantamai arai,sai sukayi issha'i kana suka dawo koda suka dawo Safeena ta musu jallof din shinkafa da kifi sai kunun aya ta fesa wanka cikin riga da sikat tasauya hijabi humra ta shafa ajikinta tana fitar dawani sirrin kamshi Su Ummi dakin Abbah suka yada zango suka bar Su Safeena dakin Ummi.




Itama shinkafan sunci badayawa ba kunun ayan dai suka sha bil haqqi da gaskiyansu😂tahir gurinsu Abbah yakoma ya bar mata da miji su kebe,to banda kallon juna suna aikin aikama juna mirmishi babu abunda sukeyi kowanne zuciyarsa tab farinciki.anan ne yake Nuna mata hoton dansa hakika kallo daya Safeena tama Adil ahoto taji yashiga aranta duk da lokacin da Ummi tafada mata yanada mata ko ajikinta ammh haduwarta da Dr sai taji dama ita kadai ta mallaki wannan hot guy din🤔🤔



sai after ten Safeena ta rakasu gidan Baba isuhu wanda wa yake ga Abbah gidansu na gaba kadan danasu yafi Abbah abun duniya kuma yanada manya ya"ya maza shiyasa gidansa keda dakunan kofar gida to daman dayake Abbah yamai bayani dasuka hadu a massallaci har suka gaisa da su Safwan din nan suka bar motarsu kofar gidansu safeena koda sukaje anygra musu daya daga cikin dakunan mazan gidan mai dauke da katifa wacce ke kasa sai sai kafet dake dakin sai toilet dakin tsaf dashi gwanin shawa'a Safeena bata wani tsayawa ba ta musu sai da Safe ammh sam Dr Safwan yaki barinta tatafi ita kadai sai da yarakata har kofar gida shima din tsayawa yayi yana kallon fuskarta cikin hasken farin watan daya haske garin..shigewa tayi gida tana masa dariya.




sai da ya koma yasamu sukunin kiran momma yake Fadamata halin da'ake ciki tayi musu fatan dawowa lafiya Haj.Mama na gefe take fadamata abunda Safwan din yacemata haj.Mama tayi tafi tace"Allahu akbar oh ni Maryamu Allah na gode maka kingani ko Hadiza yaushene safiyanu zashi wani guri har ya kwana"tafada harda rike haba kan ta cigaba dacewa"lalle Nasan yayaba da zabina kenan..Allah na godemaka.Itama momma murna take tana kara rumgume adil tanaji aranta komai yakusa zuwa karshe.



Dr Tahir yanata tsokanan Dr Safwan kin tankasa musa yayi wanka yayi yabaje a katifa daga shi sai boxer ya rumgume filo yana wani lumshe ido kamar wani tsohon maye sororo Dr Tahir ke kallonsa kan yadauki filo ya wurga akasa yana Fadin"Bari na barmaka katifan saboda tsaf cikin dare zaka iya turmusheni kazata Safeenar ce,Tunda na lura jaraba ce fal aranka..."Tsaki Dr Safwan yayi kan yace"gwanda dani nasan dadin abun kai kuwa har yanzu kana kasa ne...Banza dan sa ido kawai,Dariya kawai yayi ya juyamasa baya.


Itama Safeena anata bangaren kasa barci tayi tana juye juye data juya ta rufe ido sai taga Dr yana mata wannan tsadaddan mirmishin nashi mai kashemata jiki,dataga barcin yaki zuwa tashi tayi ta dauro alwala tafara Nafila tana godema Allah daya mallakamata Dr safwan amtsayin miji aurenta.Tadade tana addu'a kafin takoma ta kwanta tana mirmishi ita kadai.




*Domin samun Damar Zamay Daya Daga cikin wacce zata Karanta Kayattacen Labarinmu na Silar Hallaci zata iya Tumtubata ta wannan Layin 09069067488 akan Naira 300 kachal*





*Anitha..*


Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*



*18*




----- Dukkansu barcinsu rabi da rabine domin kowani dakika zuciyoyinsu suna bugawa da sunan juna,amassallaci kusa da gidan su Safeena suka yi sallah sun gaisa da Abbah sundade tare suna mgana har Dr Safwan yafadama Abba,da zarar ya koma ammh insha Allahu yana komawa zai tanadarma Safeena inda zata zauna sai susa lokacin da za'a ayi bikin Abbah yafadamasa kar ya takura kansa Safeena kanwa take agurinsa.



suna dawowa sukayi wanka domin yau monday tushen aiki suna da aiyuka a hospital,shiyasa Allah yasa shi Dr yana ijiye kaya amota kamar yasani dinkinsa daya amso wajen kala uku su ya dauko ya sanya daya yabama Tahir daya kafin karfe bakwai sun zama ready.





itakuwa Safeena tana idar da sallar asuba bata komaba,fita tayi ta share gida tagyara dakunan tazo ta musu abun karyawa kunun tsamiya tamusu da kosai daman tana tashi waken tafara wankewa,sai ruwan zafi wanda yaji citta da na'ana'a tashirya cikin riga da sikat na leshi milk and green kayan fiteed ne sun amsheta sun mata das da ita green din hijabinta ta tasaka,dogo har kasa ta dauki kayan akwando tama Ummi Sallama hakika Ummi taji dadin ganin yadda yarta bata Nuna wani damuwa ba duk da dai tasani aurene kawai ammh Dr Safwan ba ajin yarta bane _Abun Allah kenan_





Koda ta isa da kaya niki niki ta iske daga cikin gidan ankawomusu soyayyen arish da kwai harda kayan tea ta iskesu sun shirya ta duka har kasa tana gaishesu Tahir ne ya amsa yana dariya kan yace"Tashi mana amarya mun amsa gaisuwar aie"Shikuwa Dr Safwan tunda Safeena ta shigo kamshim humran data sa yashakeshi yarasa Natsuwarshi kallonta yake cikin wani yanayi wanda ya kasa gane kanshi Dr Tahir daya Fahimci haka ya fice ya basu wuri.





Tana nan durkushen kanta na kasa tana wasa da gefen hijabinta gaban na tsananta faduwa domim tasan wannan kallon nashi mai kadamata yayan Hanji yake mata ahankali tadago kanta caraf suka hada ido yana tsaye sanye cikin wani farin yadi milk mai sansti bayi da kauri tunda har ana hangan farar vest din dake jikinsa hulan kasan zannah bukar ce fuskarsa tayi fayau da ita yana furta da Annuri Kamar daren goma sha tara duka hannuwansa ya rumgume akirjinshi,kasa jaye idanunta tayi jitayi kamar kasa baza ta iya daukanta ba saboda wani kasala ke rufeta tsigar jikinta na tashi yarr!!!



saurin jaye idanunta tayi saboda tana gab da zubewa agurin mirmishi yayi kawai ya jawo kwandon data shigo dashi ransa yamasa dadi dayaga kunun tsamiya da kosai,masha Allahu yasha sosai kosan ma yaci sai ruwan na'ana'a shima yasha kadan ammh kowani lokaci tadago idanunsa na kanta,yana kammalawa yasa tissue yagoge baki ya mike yana fadin"Alhamdulillah...Yafada yana kallonta kai tsaye ya isa kusa da ita bata ankara ba shima ya durkusa har gwiwansu na gogan juna da Hanzari taja baya kallonta yayi kan yace'"yan matana yakamata amin ramgwame naga wannan kwalliyar kan in Tafi"Yafada yana wani lumshe idanunwanshi tuni jikin Safeena yafara rawa takasa dagowa sai ma kara dunkule data keyi cikin hijabi wani yanayi keJan Safwan yayi saurin mikewa kada yabi shawaran zuciyarsa na Rumguman yar mutane.


Wayoyinsa ya Dauka yayi Hanyar ficewa yana fadin"Shikenan tunda kin Hanani ganin Halas dina"yafada muryansa kamar zai yi kuka,taga da gasken ficewa zaiyi da sauri ta mike cikin rawan murya"Am.... _*UNCLE*_"cak ya tsaya kafin ya waigo yana kallonta so yake ya tabbatar da itace takirasa da Unku kai verry interresting.




Cikin kunya matsananci ta yaye hijabinta ta rike hannunta kanta na duke tace"kayi hakuri…"tafada dajan Numfashi kamewa Dr Safwan yayi yana kallon Safeena tun daga sama har kasa yake kallonta idanunsa na yawo ko'ina ajikinta Safeena doguwace mai dauke da doguwar fuskar gashin idanunta sun matukar burgeshi structure din jikinta shi ya tafi dashi uwa uba Nonuwanta dasuke cike tab atsaye suna masa maraba cikin mutuwar jiki da wata irin fitinanniyar murya ya Furta'Tsarki ya tabbata ga ubangijin dayayi wannan Halittar...."Yafada still idanunsa kyam akanta ita kuwa yadda idanunsa ke yawo ajikinta haka takejin wani sanyi na ratsata kamar wacce zata yi masassara,cikin tafiyar kasaita ya karisa kusa da ita yasa hannunsa ya tallabo habanta yana fadin"Baki kyautamin ba Sam Safeena daki Ka hanani ganin wannan kyakyawan suran taki da wuri"Ya fada yana kokarin sa idanunsa anata itakuma taki saima runtse ido da tayi zuciyarta na bugawa tsuru yamata da ido yanajin wani magnet najansa wanda baisan sadda yasa Hannunsa duka biyu ya rumgumota ba yamata kyakyawan tarba afaffadan kirjinsa.



Ya salam Safeena ta furta akasan makoshinta saboda wani schock dayajata kamar ta wutar lantarki tunda take arayuwarta babu Namijin daya taba rike mata hannu balle har ya rumgumeta sai gashi tafada cikin wani yanayi wanda kwKwalwarta tagaza hasaso mata komeye shi,shikuwa Dr wani chemistery ne ke aiki ajikinsa wani dumi mai hadi sanyi dadi ke ratsasa hannunwansa yasa duka yakara matseta gam yana Fidda Numfashi sama sama tuni hijabin Hannun Safeena ya Sulale ya fadi dankwalin kanta yafadi gashinta data dunkule yawarware yarufemata fuska"wow..Shine abunda Safwan ya Furta yayin dayayi tozali da gashin Safeena haka yasanya hannuwansu duka biyu yana lailashi idanunsa arufe yanaji kWakwalwarshi na wani amsawa zut,zut kamar zai shida.



Sun dade ahaka Dr Safwan yakasa sakin ta Saida karar wayarsa ya fargar dashi cikin kasala ya sausautamata rikon yazaro wayar a aljihu yana dubawa yaga Tahir ne yana Dauka Tahir yafara cewa"Kai Dallah mallam kafa shanyani bakasan tafiya ke gabanmu ba"saurin katse wayar yayi saboda bazai iya mgana ahalin daya ke ciko ba so yake su hada ido Safeena taki yarda sai wani sunne kai take kan kirjinsa wayyo Dadi Dr Safwan suma kadai baiyi ba shi yaushe Sakina tatabamai shagwaba juz hug da kiss sai tace duk salon takurane.Mirmishi yayi kawai ya dauko dankwalinta yadora mata bisa kai yana Fadin"Sarkin kunya...Mu zamu wuce Tahir ne yakirani,yana fadar haka yana mika mata hijabinta ta amsa ta sanya tana dukar dakai kallonta yakeyi yanajin wani bakon lamari na ziyartashi kardai ace in yakoma gida wanka yakamasa _Wanka fa Dr Tab koda yake andade ba'a hadu ba_😄




Tare suka fito yana gaba tana binshi baya sai da suka shiga cikin gidan ya musu sallama 20k yabasu suka amsa suna godiya,haka dasuka shiga yima Ummi sallama 30k yabata tace bazata amsa ba ya marairaice yace"Ummi...In baki amsa to kin Nuna min Safeena ce kadai yarki"Ummi tace"Kaima Danane duniya wa lahira Safwan nagode Allah yamuku albarka ya kaiku lapy"Suka amsa Da Amin Abbah kuwa daya bashi 30k kin amsa yayi sukayi sukayi yace'bazai amsa ba shidai burinshi ya rikemai Safeena da Amana"Hakika Mahaifan Safeena sun burge Su Dr Safwan matuka wanda har hakan yayi tasiri aransu.




Abun mamaki sai gashi kawai sun bude boot yara na jidan kayan abinci suna shiga dashi buhun shimkafa,katan din taliya katan din makaroni dadai sauransu narike baki cos nikaina bansan yaushe akasa kayan ba,sai dai Ummi su sukaga kaya kawai,Abbah baice komai ba saboda wannan karon in yace bazai amsa ba to surikin nasa bazai ji dadi ba.







Tabbas soyayyah gaskiya Safeena da Dr Safwan zukatansu sun aminta da juna domin daga ita harshi jikinsu yayi sanyi lokaci dasuka shiga mota zasu tafi Safeena na kofar gidansu tana kallonsu batasan sadda hawaye ya gangaro mata ba har Tahir ya tada mota Dr Safwan ya dakatar dashi ya bude mota ya fice sai dai ta ganshi agabanta kama hannunta yayi yana fadin'Kukan mekikeyi yanmatana"..?kallonsa tayi idanunta tab hawaye tace tana turamasa baki"Yaushe zaka dawo"..?tafada da shagwaba tab wlh badon mutane na wucewa ba abunda zai hanasa rumgumeta ya sumbaci bakin nan daya kusa zautar dashi ammh duk da haka sai da yakara matse hannunta yace"Yaushe kike so nadawo'..?kallonsa tayi ido cikin ido kawai sai tasamu kanta da furta"Ko gobene inaso"Mirmishi ya subucemai baisan sadda yace'Gobe. fa kikace,..?tagyada mai kai mirmishin yasake yi mata kan yace" Am srry bazai yuyi in dawo gobe ba,saboda in nadawo wazai kula da patient din..? "yafada yana kallonta kafin ya cigaba da cewa"kiyi hakuri verry soon zan dawo" yanzu tunda baki da waya ga wannan ki rike kan in dawo in siyo miki taki ko..?"yafada yana mikamata dayar wayarsa da hannu biyu ta amsa tace"Na gode Allah ya saka da alkhairi",wow....Shi yaushe Sakina yataba bata abu tagodemai ai gani take dolema yabata ta amsa tana wani bude hanci kamar ta bashi ajiya,kura mata ido kawai yayi yana kallonta zuciyarsa yaji tana zafi in ya tuna Tafiya zai yi Tahir ne yaga abun bana karewa bane yadinga zabgamusu hon,Safeena ce tayi karfin juyawa tana Fadin"ka tafi....Kagaida hajiya da momma harda Adil Allah ubangiji yakaiku lpy"Tafada wasu hawaye na gangaro mata dagudu ta ruga gida wani kuka ya kwacemata.




jikinsa sa babu laka yakoma mota yana Shiga Tahir ya kallesa kawai ya girgiza kai ya tada mota suka dau hanya,sun Fita garin gusau jefi jefi yana kallon shashen Dr Safwan yake wanda yamaida kansa jikin kujera ya lumshe idanunsa kamar mai barci ammh hakika ba barci yakeyi ba gabadaya ransa da tunaninsa naga Safeena kwana daya kacal ammh tasamu wani gurbi mai girma azuciyarsa wanda baisan sanda tasameshi ba,ji yake tamkar yasakota cikin mota yazo kaduna da ita kallonta kawai da yanayinta kansashi nishadi balle yangarta da salon kunyarta.



Dr Tahir yakara kallonsa kan yace"Duk wannan Damuwar ta mecece Dr Safana..?"yafada kansa tsaye shuru yayi masa wanda har ya fitar da rai da zai yi mganasai chan yace cikim

Please Login or Register in order to submit comment