Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata lafiyayyen jikinta. Na dade ina kallon bangon littafin.
.
.
Lp=39YARO BAI SAN WUTA BA....
.
.
Page 39
.
.
.
Domin kuwa dan guntun kallabin da ta dora akanta bai yi komai ba wajen sakaya mata lafiyayyen jikinta. Na dade ina kallon bangon littafin.
.
Tabbas idan mijinta ya gani ba zai ta6a jin dadi ba. Wannan kadai zai iya tunxura shi ya rabu da ita in har yana da zafin kishi a xuciyarsa.
.
Bayan na gama hada kayan ne nasa aka nemo mani mota, aka xuba mani buhunan littafin Khalil. Na kira Fauziyya na fada mata duk yadda akayi. Ta ce da ni muryarta cike da xumudi.
.
"To me ka ke jira Kamal? Ka je kawai ka qonasu a daji mafi kusa. Na ga ya yamma ta yi sai ka jira gobe sai ka biyo jirgin safe."
.
Ta tambaye ni akwai sauran kudi a waje na? Ko kuwa sun qare? Akwai sauran kimanin naira dubu dari uku da suka ragu a hannuna. Na ce da ita ina da sauran kudi. Ta ce da ni idan na qona litattafan in je in kama Otal in huta. Bata son in dawo mata da ko kwabo washe gari. Na sha wahala sosai. Ta ce duk ragowar kudin in yi masu kisan gilla a dare daya su qare. Komai na ga dama in yi dasu. Nayi mata alqawarin zan kashe baki daya kudin. Amma a can cikin xuciyata na san ba zan ta6a yiwa irin wadannan kudin kisan dare daya ba, sbd na dade ina nemansu amma sun qi taruwa, tunda dai ta bar mani su sun zama nawa, ko in kashe su ko kada in kashe su wannan matsalata ce.
.
Sai da muka bar cikin gari ni da direban motar, muna tafiya yana yi mani hirar za6en shugabani da ya gudana, da irin rigingimun da aka yi. Na bi shi da Eh, ina gyada kai, domin ban san me yake cewa ba, sbd ko sunan gwamnan jiharmu ni ban sani ba. Idan har zan fito kullum in nemi abincina in samu, to ba ruwana da maganar za6e. Na ce dashi ya tsaya a wani daji da muka xo, inda yake da qarancin itatuwa da gonaki.
.
Bayan ya tsaya da motar ne nace masa a nan zan sauke kayan. Dama ba mu riga mu n yi yarjejenir inda zai kai mani kayan ba, tahowa kawai muka yi nace idan mun je ya fadi abin da zan bashi.
.
Direban ya tsayar da motar ya yi fakin a gefen titi, ya dauko mani kayana. Har zai tambayeni dalilin sauke kayan a cikin daji, sai ya ga fuskata bata amince da hakan ba.
.
Ya kashe motar muka fito. Na nuna masa wani fili wanda babu komai a wurin sai qayayuwa da kwazazzabai. Na ce ya tara mani kayan a wurin. Ina gefe a tsaye direban ya riqa mirgino buhunhunan yana fitowa dasu daga cikin motar, ya tara su a inda na nuna masa. Ya xo wajena yana jiran in sallame shi ya tafi.
.
Na ce dashi.
.
"Zan yi wani aiki ne ba zan dade ba. Ka dan jira ni mu koma tare."
.
Na ce ya bani ragowar fetur in akwai a ma'ajiyar sa. Ya dauko mani fetur a jarka ya bani yana kallona da fuskar katako. Naje inda buhunan litattafan suke na kwarara fetur din, na ciro ashana a aljihuna na qyasta wuta na jefa na koma baya. Wutar ta kama buhunan da ci bal-bal. Tun kafin in dawo wurin da direban yake a jikin motarsa. Na ji ya dago murya yana tambayana.
.
"Mai gida ya naga haka kuma? Na dauka sayen su kayi a kasuwa za ka je ka sayar, kaima ka samu riba."
.
Na yi masa dariya na ce.
.
"na fasa sayar dasu ne. Zan koma ne in sake sayo wasu, akwai saura da yawa ynx a kasuwa."
.
Ya bini da kallo cike da takaicin yadda na raina masa hankali. Ban sake waiwayar inda yake ba. Na ciro wayata na sake kiran Haj. Fauziyya.
.
"An gama komai. Ynx haka ga litattafan a gabana suna cin wuta a wani daji da muka xo.
.
Na ji tayi dariyar farin ciki da zazzaqar muryarta.
.
"Don Allah Kamal ka sa wayarka ka dauko mani bidiyon yadda wutar ke cin litattafan, idan ka dawo gobe in gani hankalina ya qara kunciya.
.
.
Lp=40
YARO BAI SAN WUTA BA....
.
.
Page 40
.
.
.
Don Allah Kamal ka sa wayarka ka dauko mani bidiyon yadda wutar ke cin litattafan gobe idan na dawo in gani ko hankalina ya qara kunciya. Ba wai ban yarda da kai bane. Na sani har cikin xuciyata kayi mani duk yadda na sanya ka, ina so ne in riqa ganin yadda litattafan suka qone gabaki dayansu don in samu abin da zai riqa faranta mani rai idan na gani. Na fadi maka Khalil ya bani wahala da litattafan nan...."
.
Na ce da ita, zan daukar mata hoton kada ta damu.
.
Na saita wayata na daukar mata hoton bidiyon yadda hadamammiyar wutar ke hadiye tarin litattafan na tsawon minti daya. Na ce da direban ya shiga motar mu koma. Naga duk yayi xufa yana kallona a tsorace, kamar yana tsammanin na zare. Sai da muka shiga motar ya tayar muka tafi, sannan na tambaye shi nawa ne kudinsa?
.
Direban ya juyo da fuskarsa a cikin ladabi ya ce da ni.
.
"Mai gida kada ka damu kyauta na dauko maka ba sai ka biya ba, ba komai ai muna tare.".
.
Na fashe da dariya da na fahimci ya tsorata da ni. Yana tsammanin ni mahaukaci ne. Na ciro dubu biyar na miqa masa na ce.
.
"Amshi haqqinka Mallam, ni ba mahaukaci bane. Wannan abin da kaga ya faru wani 6oyayyen sirri ne wanda ko an yi maka bayayani ba zaka iya ganewa ba. Ka mance kaga wannan abin da ya faru."
.
Na waiga baya a lkcn da motar ta fara gudu. Na hango hayaqin dake a saman wutar yayi baqi wuluk yana tashi sama kamar ana qona taya.
.
A karo na farko na fara ji a xuciyata babu shakka wannan aikin da muke aiwatarwa ni da Haj. Fauziyya akwai 6arna a cikinsa. Kuma tabbas zamu yi nadama a qarshe.
.
.
.
**
*
.
.
Ban qarar da kudin da ke a wajena ba, amma na kashe na kashewa. Sai da na nemi inda asibitin kudi yake mafi kusa da ni naje na kwanta aka duba ni. Aka bani magungunan da zan sha, sannan aka yi mani allurar rigakafin cixon kare.
.
Na wuce Otal na kama daki na kwanta na huta. Dare ya yi. Sau biyu Fauziyya tana kirana tana tuntu6ar halin da nake. Na ce da ita ta kwantar da hankalinta bana cikin matsala zan dawo washe gari, zan biyo jirgin safe. Kafin ta kashe wayar ne na tambayeta yaya Khalil, fatan bata samu wata matsala dashi ba? Yana nan a cikin dakin?"
.
Fauziyya tayi dariya ta ce.
.
"Kaima ka san dole ne ya bani matsala. Na je na kai masa abinci, ya yunquro yana a dauren ya ture ni da jikinsa abincin ya xube a qasa. Na kalle shi na rabu dashi. Ban sake komawa wajen sa ba. Har ynx kuka yake yi bai haqura ba. Na ci sa'a ba ranar da mijina zai xo gida bane. Shi yasa na qosa ka dawo mu gama aikin nan Kamal, kada ranar xuwan mijina ta xo, ya ritsa mu a cikin wannan matsalar."
.
Na ce da ita.
.
"Ba zai xo ya same mu ba, tunda saura kwana biyu ya sake dawowa. Zamu gama aikin kafin lkcn."
.
Fauziyya ta ce da ni tana dariya.
.
"Daxu Alhaji ya kira ni yake sanar da ni cewar wai 6arawo ya shigo masu gida jiya da daddare. Amma an yi bincike bai dauki komai ba, sai dai ya raunata mai gadi daya, sannan ya kashe karensu guda daya. Wai jami'an tsaro suna bincike sun sha alwashin gano kowanne 6arawo ne ya shigo gidan."
.
Nayi murmushi kawai. Na ce da ita.
.
"A yadda kuka yi waya da Alhaji akwai alamar ya samu littafin ko bai nuna maki cewar an tsinci littafin ba?"
.
Fauziyya ta ce da ni.
.
"bai yi mani wani zancen littafi ba. Babu mamaki kuma ni nake damun kaina da tsoron banza, wata qila ma babu wanda ya ga littafin har ynxn a cikinsu. Wata qila har ynx yana a cikin motar."
.
Na ce da ita.
.
"Muna fatan haka. Koma dai mai zai faru zai xo da sauqi. Ga alama ba zamu fuskanci wata matsala ba."
.
Ta sake yi mani gdy sannan ta kashe wayar.
.
Na kwana a Otal din dana kama. A cikin daren ne nayi mafarkin Hak. Fauziyya ta yafewa masoyinta Khalil, sun hada kai sun ritsa ni da bindiga zasu kashe ni. Ina cikin ja da baya ne suna biyo ni na farka dafa barcin. Na dade kafin in sake komawa in kwanta.
.
Washe gari tun da wuri na shirya, bayan na karya kumallo na dauko jakata na fice daga Otal din na samu mai tasi na ce ya kai ni tashar jirgin sama. Na kwashe ragowar kudin dake a cikin jakar na xuba su a aljihun wando na, tunda dai sun zama nawa.
.
Kamar yadda muka tsara. Jirgin farko da ya tashi xuwa Ikko da ni ya tafi. Da qarfe daya na rana muka dira. Haj. Fauziyya ta xo a mota ta daukeni fuskarta cike da annashuwa.
.
.
Lp=41YARO BAI SAN WUTA BA....
.
.
Page 41
.
.
.
Kamar yadda muka tsara, jirgin farko da zai tashi xuwa Ikko da ni ya tafi. Da qarfe daya na ranamuka dira. Haj. Fauziyya ta xo a mota ta daukeni, fuskarta cike da annashuwa. Ta ci kwalliya da wadansu kaya 'yan ubansu, kayan kalar sararin samaniya, hade da ratsin fari, an yi masu ado . Idan Fauziyya tana cikin farin ciki babu abin da ya kai ta kyawun gani.
.
"Ynx me ya rage kuma?"
.
Na tambayeta da naga mun fita daga gosilon da ya tsayar damu akan titin (Airport). Ta jingina da kujerar motar, hannuwa biyu suna kada sitiyarin motar kamar abin wasa. Ta yi kamar bata ji abin da na c ba, amma na san tana neman amsar da zata bani ne. Bayan kimanin minti daya sai ta ce da ni.
.
"Ni kaina abin da nake tambayar kaina kenan tun wayewar garin nan Kamal. Ynx dai mun yi nasarar qarar da litattafan Khalil. To amma in har muka saki Khalil ya tafi to tabbas zai sake fitar da wadansu, na san a yadda nayi masa wannan ramuwar gayyar, muka daure shi matuqar ya kucce ya tafi to na shiga uku. Domin sai ya rubuta mani fiye da litattafai goma ya yayata ni a duniya har kowa ya san kowace ce Fauziyya. Ba qaramin hadari bane in bar Khalil ya tafi."
.
Na ce da ita bayan na kalle ta.
.
"Amma dai kin san ba zai yiwu ba ki ci gaba da tsare shi ba a gidanki har abada. Dole ne ki sake shi ya tafi, idan mijinki bai ganshi ba tunda makaho ne, wani wanda yake da ido zai shigo wata rana, kinga asiri ya tonu kenan."
.
Ta yi ajiyar xuciya ta ci gaba da tuqa motar tana tunani. Na ce da ita don in kwantar mata da hankali kada ta saki kan motar mu fada rami.
.
"me zai hana ba zaki hada kai da wani jami'in tsaron ba wanda ku ke mutunci. Ki ce masa Khalil yana yi maki barazana da rayuwarki a xo a kama shi a daure shi. Idan kika dauki Lauya za a iya tura shi gidan yari a 6oye shi a can har abada in dai kina da kudi."
.
Fauziyya tayi saurin girgiza kai cikin rashin amincewa.
.
"Akwai matsala a nan ma Kamal. Idan kana son ka hana marubuci ya yi magana ba gidan yari zaka kai shi ba. Kafin ya fito, tun daga can yana iya rubuta litattafai ya turowa duniya, da zarar an karanta za a san abin da yake faruwa. Daga nan zai hada ka rigima da talakawa. Shi ya sa jiya na fada maka cewar rigima da marubuci ba qaramar wahala ake sha ba. Kana gani Gwamnati ma fama take yi dasu, a kama su a daure, wadansu a kashe su, amma basu da tsoro. Gobe sai ka ji wani ya dora daga inda wancan ya ajiye. To ina mafita ynx? Kai ynx aka ce Khalil ya kucce ya gudu ai na bani a qasar nan, asirin ya tonu."
.
Na yi shiru ban ce da ita komai ba, sbd ban san abin da zan ce mata ba. Ni kaina ynx bani da mafitar wannan matsalar.
.
Har muka koma gida babu wanda ya gano wata sahihiyar mafita a tsakanin ni da ita. Muka zauna a falo muka yi hugum! Daga inda muke zaune a falon muna jiyo 6urarin Khalil dake a daure a can cikin dakin da muka kulle shi, yana dukan qofar da qafafuwansa yana zagin Fauziyya.
.
Ta yi ajiyar xuciya ta kalle ni cikin damuwa ta ce a sanyaye.
.
"A haka muka kwana ban yi barcin kirki ba. Kwana ya yi yana dukan qofar nan, yana zagina. Khalil ya zame mani qadangaren bakin tulu. In bar shi ya 6ata mani ruwa, in zan kashe shi kuma in fasa tulun."
.
Bayan mun sake yin shiru ne na ce da ita a qarshe.
.
"To amma me zai hana ba zamu biyo masa ta hanyar lumana ba mu sasanta dashi. Ki ce kin yarda zaki rabu da mijinki ki aure shi, idan kuka sasanta ku ka daina rigimar wata qila daga baya ya ji tausayinki ya rabu da ke ki ci gaba da zama tare da mijinki."
.
Fauziyya ta sake girgiza kanta.
.
"ba ka san ko wane ne Khalil ba a wajen soyayya. Baka san yadda yake so na ba shi yasa ka ce haka. Yana bala'in sona fiye da yadda ka ke tsammani. Lkcn da muka fara soyayya idan ya xo gidanmu aka ce masa nayi tafiya naje unguwa, sai an hada shi da yaro ya kai shi duk inda nake ya ganni. Sannan zai iya komawa gida. Idan kuwa bani da lfy bana yarda ya sani, domin kuwa a rude zaka ga ya xo gidanmu. Ynx idan nayi masa alqawarin zan rabu da mijina in aure shi. Ba zai ta6a samun sukuni ba sai yaga na rabu da mijin nawa. Ya riga ya gama haukacewa akan sona. Ba wani abu da zan yi masa ya daina so na.
.
Muka sake yin jugum-jugum ni da ita, kowa ya kasa samo sahihiyar mafita. A qarshe na ce da ita.
.
"ni ina ganin ida babu matsala da a ci gaba da zama a haka ana wannan rigimar, kawai ki rabu da mijin naki ki aure shi. Hankalin kowa ya kwanta."
.
Fauziyya ta ciro kanta a kidime kamar an tsira mata allura ta kalle ni cikin rudani.
.
"Aure...me kake fada Kamal? Wa zan aura?"
.
Ta tambayeni muryarta na rawa.
.
"Kalil zan aura? Me ke gare shi da zai iya riqe ni? Duk abin da ya mallaka in an tara bai ishe ni kashewa na rana daya ba. Khalil ba irin mijin da zan iya zama dashi bane a matsayin mijina. Na saba kashe manyan kudi, na saba jin dadin rayuwa. Ina fita qasashe daban-daban ina yawon shaqatawa. Ta yaya zan auri Khalil? Ai sai in mutu a cikin 'yan kwanaki qalilan bayan auren, domin zan ji kamar a kurkuku nake a daure.
.
.
Lp=42YARO BAI SAN WUTA BA...
.
.
Page 42
.
.
.
Khalil ba irin namijin da zan iya zama dashi bane a matsayin mijina. Na saba kashe manyan kudi, na saba da jin dadin rayuwa. Ina fita qasashe daban-daban ina yawon shaqatawa. Ta yaya zan auri Khalil? Ai sai in mutu cikin 'yan kwanaki kadan bayan auren, domin zan ji kamar a kurkuku aka daureni."
.
Fauziyya ta ce da ni cikin sauri.
.
"Ynx tunda mun kasa fahimtar mafitar wannan matsalar, kamata ya yi ka je ka kwanta ka huta, nima ynx barci nake ji, na san daga ynx xuwa dare zamu gano abin da ya kamata muyi."
.
Na ce da ita.
.
"Ba komai, zan je in huta.
.
Fauziyya ta jagorance ni na bita muka koma sashin da muka kulle Khalil marubuci. Ynx ya koma ya natsu ya daina rusa kukan da yake yi.
.
Fauziyya ta bude mani wani daki wanda yake fuskantar dakin Khalil. Ta ce in shiga in huta, akwai komai a cikin dakin wanda zan buqata. Sannan ta koma dakinta cikin sauri.
.
Na shiga cikin dakin na samu tanqasheshen gado, wanda ya cika fal da tanqasheshiyar katifa da lafiyayyun shimfidu. Ga kayayyakin kallo a gefe daya da kuma na'urar sanyaya ruwa. Na cire takalma na na zauna akan gadon na kunna tibin wanda yake jone da tauraron dan adam. Na fara kallon wasanni
.
Rayuwata ta canza a kwana biyu kawai da haduwata da Haj. Fauziyya. Ga muhalli mai kyau, ga abinci lafiyayye, ga kudi a cikin aljihuna fal. Ba ruwana da fita bakin titi da sassafe ina shan sanyi ina tashi ina tar6ar kwastomomina dake xuwa sayen katin waya.
.
Ga dai hanya nan mai fadi, amma da wahala idan zata 6ulle a qarshe. Na ta6a jin an ce duk hanya mai sauqin bi da dadin tafiya bata cika 6ullewa ba a qarshe. Sau da yawa idan dan adam yayi haquri, ya bi hanya mai wahala yana neman na kansa, wannan ce hanyar lfy, wacce take 6ullewa xuwa wata babbar hanya a can gaba....ynx dai gashi na baro hanyata mai wahala na samu hanyar sauqi. Ban san inda na nufa ba, ban san inda zata kai ni ba.
.
To amma akan me zan ta janku da magana daya tunda dai abin da ya faru ya riga ya faru tuntuni? Duk abubuwan nan da nake fada maku wani shudadden al'amari ne wanda ya faru shekaru masu yawa da suka wuce. Don haka akan me zan yi ta magana daya? Bari in yi sauri in fada maku ragowar abubuwan da suka faru.
.
Har dare yayi ina gidan Haj. Fauziyya. Ta soya mana naman kaji da rana ta kawo mani nawa har dakina. Na tambayeta ya take ganin Khalil kuwa, zai bayar da hadin kai ya ci abinci? Ta da ni Oho masa. Idan naga zan kai masa in xo in amsa, ita dai ba zata qara shiga inda yake ba tunda dai bai shirya sasantawa da ita ba. Da ta shiga zai fara zaginta, yana qoqarin kwance daurin dake hannunsa domin ya maqure mata wuya.
.
Na je na amso abincin hade da ruwan sha na bude dakin na shiga na ajiye a kusa da shi. Har zai fara yunqurin tasowa, da ya dago kansa ya ga ni ne sai ya koma ya lafa. Na taimake shi na zaunar dashi na jingina shi da jikin bango. Na fara bashi haquri a karo na farko don ya daure ya ci abincin kada yunwa ta kama shi ya xo ya mutu a hannunmu. Duk da rashin hankalina, na san cewar in har Khalil ya mutu a hannunmu to mun shiga babbar tsomomuwa, kuma tabbas da wahala mu ma mu kai labari.
.
Na kwance masa hannunsa na ce ya ci abinci zan jira shi ya gama, sai in sake daure shi tunda dai ina bin umarnin Hajiya ne nima. Khalil ya girgiza kai a cikin takaici. Akwai hawaye cike da idanunsa amma basu xubo ba. Ya dauki abincin ya fara ci, ba don dadi ba, don kuwa a yadda ransa yake a 6ace, ko naman dawisu aka bashi da wahala ya ji dadin sa.
.
Bayan ya gama cin abincin ne kafin in sake daure shi ya ce da ni.
.
"Ina jin tausayinka Kamal."
.
"ban san yadda aka yi ya san sunana ba. To amma da na tuna cewa Fauziyya ta sha kiran suna na a gaban shi tun bayan kawo shi gidan, sai na kawar da wannan tunanin daga xuciyata.
.
"Ina jin tausayin ka."
.
Ya sake maimaitawa.
.
"Baka san ko wace ce wannan matar ba, shi yasa har ka yarda da ita. Ina tabbatar maka da cewa wannan matar ita zata kashe ni, kuma kaima ita ce ajalinka, ita ce zata kashe ka. Na kalli idanunta na fahimci muguwar manufarta akanmu, muguwa ce, azzaluma ce, wacce bata da tausayi. Bata da tunani, babu komai a cikin xuciyarta sai hauka da rashin tunani, duk abin da mahaukaciyar qwaqwalwarta ta karanta mata shi take yi. Kayi sauri ka gudu ka bar matar nan, in ka qi kuwa zaka ce ni na fada maka wannan maganar, kuma zaka gane gsky na fada maka in har baka bi umarni na ba.
.
Na kama hannunsa na sake daureshi. Ya rabu da ni bai sake cewa da ni komai ba, amma har na jawo qofar dakin na sake rufeshi muna kallon juna, akwai wani abu dake a cikin idanunsa dake nuna cewar duk abin da yake fada mani har cikin xuciyarsa abin da yake nufi kenan. Kallo ne wanda yake mani gargadi da in bi a hankali, akwai babban hadari a gabana.
.
Na koma dakina ba tare da na sake tuno maganganun da Khalil ya fada mani ba. Da dare ya yi ne Fauziyya ta ce da ni zata kwanta da wuri, idan ina so in je yawo ga motarta nan in dauka in fita. Na ce da ita nima bana jin xuwa ko'ina. Barci zan yi da wuri.
.
Ta ce da ni sai da safe.
.
Lp=43YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
.
Page 43
.
.
.
Ta ce da ni sai da safe. Ta koma dakinta.
.
Na yi kallo har xuwa qarfe goma na dare, kafin barci ya rufe mani idanu sai da na kashe wutar dakin kana na kwanta akan gadona, barci ya dauke ni da sauri.
.
Ban san iya awoyin da na dauka ina sharar barci ba. Wani motsi da na tabbatar ba a cikin dakin nawa yake ba, wanda ban san ko na mene ba, shi ya farkar da ni daga nannauyan barcin da nake yi. Na farka a tsorace. Na zauna akan faffadan gadon kafin idanuna su saba da duhun dake a cikin dakin. Nayi saurin lalubar makunnin wutar, na kunna qwan dake a saman rufin dakin, haske ya gauraye ko'ina.
.
Na kasa kunnena na sake saurarawa da kyau, don in tabbatar motsin da ya farkar da ni ba kunnuwana bane suke yaudarata ba. Na ji gabana ya fadi. Tabbas motsin da naji har ynxn yana nan, na riqa jin kamar tafiya a waje, kamar an ta6a qofar wani daki dake a cikin gidan.
.
Da farko nayi tsammanin ko Khalil ne yake kusur-kusur a dakin da muka kulle shi, yana qoqarin 6alle qofar dakin ya fito waje, kamar yadda tun safe ya wuni yana gabzar qofar da qafarsa. Yana 6urari yana xundumowa Haj. Fauziyya zagi, domin mu je mu kwance shi.
.
To amma da naji an ci gaba da tafiya sannu a hankali kamar ana sanda sai gabana ya fadi.
.
(Wane ne yake tafiya haka a cikin wannan dare?)
.
Na tambayi kaina a dai-dai lkcn da nake duba agogon bangon dakin. Na ga qarfe biyu da minti goma na dare. Wane ne yake tafiya a cikin wannan daren? (Shin Khalil ne ya kwance daurun dake a hannunsa da qafafuwansa, ya bude dakin ya fito waje?).
.
Na sake tambayar kaina sannan nayi sauri na sauko daga kan gadon, na bude qofar dakin na leqa kaina waje don ganin abin da yake faruwa......
.
A lkcn ne na ganta ta kamo hanyar dawowa daga dakin da Khalil ya ke. Tana sanye da rigar barci iya guiwarta fara sol, wacce ta manne da jikinta kamar rigar balobalo. Gashin kanta ya warwatsu bisa kafadunta, qafafuwanta babu takalmi. Tabbas komai duhu, sannan komin dare dole in gane Haj. Fauziyya. Ba aljana ba ce, FAUZIYYA CE!
.
Na saki qofar dakin na fita da sauri domin in tarbeta in tambayeta ko lfy ta fito a cikin wannan uban daren haka? Sannan kuma da ta fito me ya kai ta dakin abokin rigimarta Khalil?
.
Lkcn da na kusa isa inda take ne tana tahowa, na tsaya cikin sauri kamar an zare mani rai sbd abin da na gani a hannunta, shar6e6iyar wuqa ce tana qyalqyali a cikin dan guntun hasken wutar da ya shigo lungun, wanda ya sauka akan gilasan tagogin dakunan.
.
Wuq ce a hannunta!!
.
Na tsaya a tsorace na kasa motsawa ina jiranta ta qariso tayi mani bayanin abin da idanuna suke gane mani, don kuwa a ynx bani da qarfin halin da zan iya tambayarta. Fauziyya ta qaraso inda nake a tsaye kamar an dasa ni, naga tana murmushi tana motsa bakinta kamar tana magana a xuciyarta. Amma abin mamaki idanunta a rufe suke, bata ganin komai. Ta xo har inda nake ta wuce ni, tana tafiya a hankali, na bata wuri da naga bata da niyyar tsayawa ko kaucewa maimakon haka sai niyyar ture ni take yi kamar zata tsaga jikina ta wuce. Sai a lkcn na fahimci barci take yi.
.
Shin barcin ta ne ya sake tashi wanda ta bani labarin tana yi akai-akai? Na ci gaba da tambayar kaina a tsorace. Kamar naga aljana..
.
Na

Please Login or Register in order to submit comment