Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sheqa da gudu.
.
Na waiga baya na hangi masu gadin gidan man sun yi turus a tsaye cike da mamakin abin da ya hada kyakkyawar matar da yamutsattsen saurayi irina.
.
Na dawo da hankalina kanta, fuskarta a cike take da farin ciki. Tana tuqin tana murmushi, tana sanye da baqaqen kaya riga da siket wadanda suka dace da kalarta da xubin jikinta fiye da kowacce sura da na ta6a ganinta da su.
.
"Sannu Kamal ga alama ka sha wahala. Sannu!"
.
Ta ce da ni tana murmushin jin dadin taimakon da nayi mata.
.
Nayi ajiyar xuciya.
.
Kafin in ce da ita wani abu ta ce da ni.
.
"Bari muje gida zan kira wani likitana ya duba ka, ba sai mun je asibiti ba, zai xo har gida ya baka magani, naga duk ka ji ciwo, ina fatan dai shegun Karnukan nan basu cijeka ba?"
.
Na ce da ita ina murmushi.
.
"sai dai kuma kada a qara, amma aikin gama ya gama."
.
Fauziyya ta juyo ta dube ni, hannunta biyu riqe da sitiyarin motar.
.
"Ba kpmai Kamal, tunda dai kayi nasara ka dauko mani littafin nan, ba mu yi wahalar banza ba."
.
Kafin ta qara cewa komai ta miqo hannunta daya tana murmushi ta ce da ni.
.
"Bani littafin in gani ko hankalina ya dan kwanta. Kwata-kwata ban yi barci ba a daren jiya, a zaune na kwana ina ta addu'ar Allah Ya sa dai kayi nasara ka samu damar dauko mani littafin nan. Bani shi in gani."
.
Na sa hannu zan ciro littafin naji zan takurawa kaina da yake a cikin aljihuna (Jeans) na sanya shi.
.
Na ce da ita.
.
"Ki yi haquri Hajiya, bari mu je gida mana, saurin me kike yi ne?
.
Ta tuntsire da dariya sannan ta qarawa motar gudu tana kallon faffadan titin da muke kai.
.
Bamu sake yin wata magana ba, muka isa katafaren gidan. Da xuwanmu tun kafin mu tsaya a bakin qofar gidan wani saurayi dake a zaune yana wanki akan teburi a kusa da gidan ya taso da gudu ya bude mata qofar muka shiga ciki.
.
.
Lp=23YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 23
.
.
.
Da xuwanmu tun kafin mu tsaya a bakin qofar gidan wani saurayi dake a zaune akan wani teburi a kusa da gidan ya taso da gudu ya bude mana qofar muka shiga ciki.
.
Ban san dalilin da yasa matasan dake a layin suke girmamata ba, wata qila sbd xunxurutun kyawunta yasa suke hanzarin yi mata aiki ko bata sa su ba.
.
Wa ya sani kuma ko ruwan kudi take yi masu?
.
Bayan ta kai motar inda take ajiyeta ne muka fito. Fauziyya ta shiga gaba tana sauri, ta riga ni xuwa falon a yayin da na biyota a baya, na san ba wani abu take yiwa xumudi ba da ya wuce in yi sauri in ciro mata littafinta, don ta gani hankalinta ya kwanta.
.
"Ka cika ja min rai Kamal....don Allah yi sauri ka ciro min littafin in gani...na qosa ya xo hannuna in kekketashi don kuwa ya kusa kashe mani aurena in banda Allah Ya kawo mani kai ka taimake ni. Ciro shi ka bani."
.
Ta sake miqo mani santalelen hannunta. A wannan karon ne na ciro littafin daga cikin aljihuna na miqa mata.
.
Ta cafe littafin da sauri kamar tana xullumin zai yi fuffike ya tashi sama daga hannunta.
.
Lkcn da ta amshi littafin ne ta juya shi a hannunta, ta kalle shi, sai naga fuskarta ta sauya, wani abu mai ban tsoro ya garzayo ya kori annurin dake a fuskarta ya maye gurbi. Naga idanunta sun firfito kamar zasu fado qasa sbd tsananin firgici. Hannunta ya fara kyarma. A lkcn ne littafin ya su6uce daga hannunta ya fadi qasa.
.
Fauziyya ta fashe da kuka ta juya mani baya da sauri ta 6oye hawayenta da na tabbatar ya fara cin gudu akan fuskarta.
.
A lkcn ne ta ce da ni a fusace.
.
"Kayi wahalar banza Kamal! Wannan ba littafin bane!! Bashi bane littafin da nayi mafarkin na kai motar mijina ba....wancan yana can ka bar shi baka dauko shi ba....yana can a cikin motar, ba na ainahi ka dauko ba, wannan na bogi ne!!!"
.
Ta sake fashewa da wani sabon kukan. Na bushe a tsaye kamar gunki. Kalamanta suka amsa kuwwa a kunnena.
.
.
.
**
.
.
.
Mun dauki fiye da minti goma a tsaye a falon ba wanda ya sake yiwa wani magana a tsakanina da Fauziyya. Ta ci gaba da kukanta bata juyo ta fuskanceni ba, na san ba wani abu yake damunta a xuciyarta ba sai tsoron halin da rayuwarta zata fada, don kuwa ciro littafin daga cikin motar mijinta shi ne rufin asirinta, gashi kuma ba shi bane littafin dana dauko.
.
A 6angarena in banda tafarfasa babu abin da xuciyata ke yi. Ni kadai na san wahalar da na sha kafin in samu nasarar ciro littafin in fito daga gidan Alh. Fataye.
.
Har ynx radadin ciwon da naji a sakamakon fadan da nayi da karen gidan shi ne ke azabtar da fatar jikina. Ba qaramin takaici bane ace duk bayan wannan wahalar, littafin da na dauko ba shi ba ne ainahin littafin da Fauziyya ta kai cikin motar.
.
Nayi ajiyar xuciya sannan qwaqwalwata ta fara caji. Na tabbatar in har da gaske Fauziyya take yi akwai littafin a cikin motar, to shi ne wannan da na dauko mata, domin kuwa babu irin vinciken da ban yi ba, babu inda ban kai hannuna ba a cikin motar, amma ban samu littafi ba sai wannan da naxo mata dashi.
.
In har duk wadannan abubuwan zasu faru na tabbatar akwai abin da Fauziyya ta 6oye mani, akwai sauran wani labari a qasa wanda bata ginoi mani shi ba. Akwai wata qulalliya a cikin wannan maganar tata wadda ta 6oye mani bata sanar da ni ba.
.
Na matsa inda ta jefar da littafin na duqa na daukoshi, a lkcn ne nima na fara duba shi naga kowanne irin littafi ne. Bana soyayya bane, littafin Hausa ne amma na yaqi ne.
.
A bangon littafin akwai wani garjejen aljani da kan Zaki yana aman wuta. Tabbas a wancan labarin da ta bani ba littafin yaqi ta ce ta kai cikin motar Fataye ba. To amma in har wannan wani ne daban, to wancan din me yasa ba a same shi a cikin motar ba aka samu wannan?
.
Babu shakka in har Fauziyya zata fito ta fada mani gsky, to akwai sauran magana a 6oye.
.
Ta share hawayen dake a fuskarta a karo na farko ta ce dani.
.
"Duk farin cikin da nake yi na samu wanda zai taimakeni ashe matsala tana nan bata qare ba. Na tabbatar in har mijina yaga wancan littafin ynx to asirina ya tonu, lkcn rabuwata da shi yaxo, zamana ya qare a nan gidan."
.
Wani abu dake kama da qwan kaza ya maqale mani a wuya, daqyar na samu na hadiye shi.
.
Na ce da ita kai tsaye.
.
"Kada ki ga laifina, duk abin daya faru laifinki ne Fauziyya. Akwai abin da kika 6oye mani tun farko, da ace kin fito kin fada mani gsky da bamu sha wannan wahalar ba."
.
Kamar wacce aka cakawa allura a kunne, tayi xumbur! ta juyo ta fuskanceni fuskarta cike da tagwayen hawaye, idanunta sun canza a dan lkc qanqane, shekarunta sun sake qaruwa akan nata na ainahi.
.
"Me na 6oye maka?"
.
Ta tambayeni cikin damuwa tana nuna ni da santala-santalan yatsun yatsunta biyu.
.
"babu abin da na 6oye maka, abin dana 6oye maka shi ne gskyr abin da na san ya faru, daga haka ban san wani abu daya faru ba.
.
A lkcn ne na kasa danne fushin da ya taso mani kamar amai. Na daga murya nima na nunata da yatsa nace da ita.
.
"Fauziyya baki fada mani gsky ba! Ya kamata ki san cewa duk da ban yi karatu ba kaina ba a duhu yake ba.
.
.
Lp=24YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 24
.
.
.
Fauziyya baki fada mani gsky ba. Ya kamata ki sani cewa duk da ban yi karatu ba, kaina ba a cikin duhu yake ba. Wannan abin da nayi maki ni na sa kaina , ba don kudinki na taimakeki ba, na sa kaina a cikin hadari na sadaukar da rayuwata akan in ga na faranta maki rai, amma ke a 6angarenki ba haka kika dauki abin ba.
.
Da ace tun farko na san baki son in san gskyr abin da yake faruwa da ke, da ban sa kaina a cikin matsalarki ba."
.
Jikinta ya fara sanyi, don kuwa bata yi tsammanin zan fada mata irin wannan maganar ba."
.
Na ci gaba da fada mata.
.
"Tun farko kin san baki amince da ni ba me yasa kika fada mani labarinki? Me yasa baki kore ni daga gidanki ba da na tambayeki abin da ya ke damunki? Wannan sirrinki ne, bai zama dole dama ki fadawa kowa ba in har xuciyarki bata son hakan. Amma ta yaya za ki qirqiri wani labari na qarya wanda ko qaramin yaro ya ji ya san ba haka abin yake ba. Ta yaya zaki tura ni cikin hadari bayan kin san duk abubuwan da kika fada mani ba gsky bane? Mecece hujjarki ta yin hakan? Dama ba don in taimakeki ya sa kika fada mani halin da kike ciki ba? Me yasa kika 6oye mani gsky Fauziyya?"
.
Ta numfasa cikin sauri ta nemi wajen zama a cikin babban falon ta zauna, har ynxn akwai alamun tsoro a fuskarta, na gane haka ne da naga alamun raxana da takurewar da jikinta yayi kamar tana jin sanyi. Na bi ta da kallo ina sauraren in ji abin da zata fada mani.
.
"Samu wuri ka zauna Kamal."
.
Ta ce da ni muryarta na kyarma.
.
"Zauna muyi magana ta fahimta. Na amince akwai abin da na 6oye maka da farko, amma ynxn nan zan warware maka komai tun daga farko har qarshe. Zauna Kamal."
.
A halin ynx akwai karaya da nadama a muryarta, kuma in har ba wata sabuwar qaryar take shiryawa ba a xuciyarta, tabbas fuskarta da muryarta sun nuna alamar gsky zata fada mani.
.
Na matsa kusa da inda take zaune na zauna akan tattausar kujera daya, nayi shiru ina saurarenta.
.
Sai da ta qanqame yatsun hannunta sannan ta ce da ni.
.
Duk abin da na fada maka a baya gsky ne Kamal. Sai dai akwai abin da na 6oye maka ne ban fada maka ba. Wannan shi ne kuskuren da nayi, amma ka gafarceni zan fada maka ynxn nan."
.
Ban ce da ita komai ba, sai da ta 6ata kimanin daqiqa goma sannan ta yanke shawarar ci gaba da fada mani abin da bata so.
.
"Gsky ne ina da ciwon mafarki, kuma tabbas nayi mafarkin na kai littafin motar mijina, amma littafin wani marubucine wanda kafin in yi aure masoyina ne. Shi ya rubuta littafin.
.
Ba tsoron kada mijina ya ga littafin nake yi ba, duk da cewar ya hana ni karanta litattafan soyayya, ya sha kamani dasu yana yafe mani. Da ace wani littafin daban nayi mafarkin na kai cikin motarsa ba zan ta6a damuwa ba don mijina ya tsinta na san hanyar da zan bi in bashi haquri ya rabu da ni, to amma shi wannan littafin da na fada maka yana da matuqar hadari a gare ni, idan mijina ya tsinta duk da baya gani makaho ne, idan har wani ya bashi lasbarin yadda littafin yake ba zai ta6a yafe mani ba, na san hukuncina saki uku ne!"
.
Fauziyya ta sake qanqame hannuwanta cikin tsoro, sbd na qosa ta fada mani yadda abin yake sai na tambayeta.
.
"Akan me zai sake ki don yaga littafin? Ya san kin ta6a soyayya da marubucin littafin ne kafi kuyi aure ke dashi?"
.
Fauziyya ta girgiza kanta cikin damuwa sannan ta lumshe idonta. A lkcn da ta bude idanun ne ta dube ni ta ce da ni.
.
"Hotona ne a bangon littafin....ni ce yarinyar da ke a bangon littafin Kamal...."
.
Muka sake yin shiru ni da ita na tsawon lkc. Naji tsoro nima ya fara kama ni, don kuwa a yadda ta fada mani halin mijinta in har tsautsayi ya gifta yaga littafin dauke da hotonta, tabbas saki uku ya tabbata akanta."
.
Hawaye suka sake xubo mata. Na dauka zata sa hannu ta share su, amma sai ta barsu har suka gaji da tserensu suka fado qasa.
.
Wata qila ta gaji da sharewa ne tunda dai ba daina xubow zasu yi ba.
.
"Sunansa Khalil..."
.
Ta ci gaba da fada mani a sanyaye.
.
Fitaccen marubuci ne wanda na fara haduwa dashi tun shekaru biyu da suka wuce a lkcn ban fara wayewa ba, ban san ko ni wacece ba a duniya. A kaduna muka hadu a shagon sayar da litattafan Hausa.
.
A lkcn da nake karanta litattafasn soyayya kullum sai na je kasuwa na sayo sabbin fitowa. Bana karanta littafin maza sai na Khalil shi kadai... Na karanta litattafansa duka tun kafin mu hadu, ban ta6a ganin sa ba amma ina qaunarsa."
.
Fauziyya ta saurara kadan sannan ta ci gaba.
.
"A ranar da zamu fara haduwa kamar ance in je kasuwa, na ganshi a shagon da nake sayen litattafai amma ban gane shi bas, ban san shi ne Khalil ba don ko ganinsa ban ta6a yi ba. Da na sayi litattafai guda hudu sai mai shagon ya miqo mani wani littafin Khalil sabo da ya fito, a lkcn bani da kudi, sauran kudin dake a hannuna na mota ne kawai da zan koma gida.
.
Na amshi littafin na ce da mai shagon, ina son idan na dawo washe gari na bashi kudinsa. Ya ce sai dai in ajiye goben idan na dawo na saya, muka yi ta jayayya ni dashi ina cewa bashi da kirki.
.
A lkcn ne Khalil ya sa baki yace da ni.
.
.
Lp=25YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 25
.
.
.
A lkcn ne Khalil ya sa baki ya ce da ni.
.
"Me yasa ba zan iya yin haquri da littafin ba sai goben idan naxo na saya?"
.
Na ce.
.
"gsky ba zan iya ganin sabon littafin Khalil in yarda ya wuce ni ban saye shi ba. Ina masifar son littafin Khalil."
.
Fauziyya ta dan yi murmushin qarfin hali duk da yake tana a cikin halin damuwa, ga alama abin da take sanar da ni yana birgeta a duk lkcn da ta tuno shi.
.
Ta ci gaba da cewa.
.
"Maimakon ya ji dadi lkcn duk da ya ji ni mai qaunarshi ce, sai ya ce da ni. Shi kuwa sam-sam wannan Khalil din bai yi masa ba, ko kyauta aka bashi littafin Khalil ba zai iya karantawa ba, sbd bai iya komai ba sai shirme.
.
A lkcn raina ya 6aci, sbd kawai naji ya ta6a mani babban gwanina, na shiga fada masa maganganu cikin fushi, ina tambayarsa shi wane ne? Me ya sani a rubutun littafi da zai ce Khalil bai iya rubutawa ba?"
.
Mutanen dake a shagon suka bani haquri suka ce in rabu dashi haka nan. Ya dauki jakarsa ya ce zai tafi ya ce da mai shagon ya bani littafin Khalil din zai bashi kudin tunda nace ina so.
.
Na ce dashi.
.
"To na gode."
.
Na amshi littafin, sai da ya tafi sannan mai shagon ya ce da ni shi ne Khalil, wasa yake yi mani, haka yake da son raha.
.
Abin ya bani dariya, kima naji ya bani sha'awa sosai. Bana son mutum mai girman kai da alfahari. Wadansu marubutan idan suka xo wuri har so suke yi a riqa nuna su ana fadawa mutane, amma Khalil baya son haka kwata-kwata, baya son a san shi ko a yabeshi a riqa kambama shi, idan kana yabonsa sai ya riqa kushe kansa.
.
Fauziyya ta ci gaba da murmushin da take yi. Duk da hawayen dake cike fal a idanunta. Na yi shiru ina kallonta, ina sauraren labarin da take ba ni.
.
A ranar ina komawa gida sai na nemo lambar wayarsa a cikin littafinsa, na kira shi nace dashi ni ce yarinyar da ya 6urma daxu a wajen mai sayar da litattafan nan.
.
Ya yi dariya kawai bai ce da ni komai ba. Na ce dashi ina son mu sake haduwa, yaushe zai xo gidanmu? Ya sa mani rana ya ce in Allah Ya yarda zai xo.
.
Kafin ranar ta xo kullum sai mun yi waya ni dashi, a cikin dan lkc qanqani muka shaqu. A ranar da ya fara xuwa gidanmu da yamma ya xo, an kusa kiran sallar magriba, na fito cikin murna muka tsaya a qofar gidanmu. Ya ce da ni daga wata doguwar tafiya yake, don kawai kada ya karya mani alqawarin daya dauka ne ya sa shi ya xo, amma in yi haquri wata rana zai samu lkc ya xo mu sha hira har sai na gaji dashi.
.
Muka yi sallama ya tafi ya barni cikin begensa. A ranar da farin ciki na kwana a xuciyata. A zamanin da wannan abin ya faru ina matuqar son Khalil, ban ta6a yin saurayin da yake fada mani irin kalaman da Khalil yake fada mani ba.
.
Bamu kai shekara da fara haduwa ba sai da kowa ya san Khalil a gidanmu. Da an ce ya xo zaka ga qannaina sun garzayo sun kewaye shi, yana son 'yan uwa da dangina, ba zan ta6a samun wani saurayi kwatankwacin shi ba a duniya. Duk wani sha'ani da ya tashi a gidanmu, ko idan ana bikin qawayena ko 'yan makarantarmu shi kadai nake gayyata ya xo ya fitar da ni kunya. Komin ruwa komai iska, in har zan ce ina son ganin Khalil sai ya taso ya xo inda nake. Da yake ya san ina son karanta litattafai, musamman ya hada ni da wani mai shago ya ce duk sanda na je in har akwai litattafan da nake so a dauka a bani ko na dubu nawa ne, duk sati sai sun yi masa bil ya je ya biya su kudaden su.
.
Fauziyya ta girgiza kai sannan tayi ajiyar xuciya ta ci gaba da fada mani cewa.
.
"Muna cikin soyayyarmu wani lkc yaxo waje na muna hira, na tambaye shi sai yaushe zai fitar mana da wani sabon littafinsa da yake talla tuntuni?" ya ce da ni rashin hoton da zai sa a bangon littafin ne ya tsayar masa da aikin, amma an gama bugawa.
.
Kamar ta6in hankali ya same ni, na ce dashi zan bashi hotona ya sa a bangon littafin. Khalil ya ce da ni yana kishina ba zai iya sa ni a bangon littafin da ya rubuta ba. Na nuna masa 6acin raina na ce dashi ni dai ina sha'awa sai yasa hotona a bangon littafin.
.
A ranar baram-baram muka rabu dashi, da ya koma gida sai ya kira ni ya bani haquri ya ce ba wai baya son ya sa hotona bane, yana gudun kada in samu matsala ne a gida.
.
Nayi masa qarya na ce ai na tambayi mahaifiyata ta ce ba matsala ta amince.
.
Ya sake dawowa bayan kwana biyu na sake maimaita masa abin da na fada masa a waya. Na ce masa in akwai matsala ai nima ba zan yarda a sa hotona ba, kada ya daukeni qaramar yarinya mana.
.
Khalil ya yi dariya. Baya son ya sa hotona a bangon littafin, amma sbd baya son 6acin raina ya amince ya amshi hoton ya tafi dashi.
.
Bayan sati uku aka buga littafin ya xo mani dashi na gani. Nayi kyau sosai a bangon littafin. Jikina ya fito yadda ake so. A ranar da aka ga littafin a gidanmu a ranar na gane kuskuren da nayi. Na sha dan banzan duka kamar jaka. Washe gari wani qanin babanmu shima ya ji labari ya xo gidanmu a fusace ya qara mani.
.
Na shiga masifa a dalilin wannan littafin. Na kira Khalil ina kuka.
.
.
Lp=26
YARO BAI SAN WUTA BA....
.
.
.
Page 26
.
.
Bayan sati uku aka buga littafin ya xo mani dashi na gani. Nayi kyau sosai a bangon littafin. Jikina ya fito yadda ake so. A ranar da aka ga littafin a gidanmu a rananr na gane kuskurena. Nasha dan banzan duka kamar jaka. Washe gari wani qanin babanmu ya xo shima da ya ji labari ya xo gidanmu a fusace ya qara mani.
.
Na shiga masifa a dalilin wannan littafin. Na kira Khalil ina kuka na fada masa halin da nake ciki. Ya ce dani ya akayi na san ba a yarda ba a gidanmu nayi masa qarya? Ya ce da ni kada in damu zai kwashe littafin daga kasuwa ya 6oyesu don a daina ganinsu a gari ana xuwa ana fadiwa iyayena.
.
A cikin kwana uku Khalil ya bi duk wasu manyan kantina dake a fadin qasar nan ya kwashe litattafan ya kaisu wani wuri ya 6oyesu sai daga baya na samu kwanciyar hankali da aka daina sayar da litattafan.
.
Ya xo har gidanmu yana yi mani dariyar wautar da nayi, bai damu da asarar da na jawo masa ba.
.
Fauziyya ta sake yin ajiyar xuciya sannan ta ce da ni.
.
"Ina fada maka duk wannan dogon labarin ne don ka san ko menene ya faru tsakanina da Khalil
.
Sai da mukayi shekara biyu tare, sannan manyan masu kudi suka fara xuwa wurina. A lkcn na zama babbar budurwa cikakkiya, na zama babbar yarinya har ta kai bani da tsara a kaf fadin unguwarmu. Kafin wani lkc ajina ya qaru fiye da yadda Khalil ya sanni. Na fara riqe manyan kudi, na fara harka da manyan mutane 'yan birni. Gashi tuntuni munyi alqawarin aure ni da Khalil. Ya dauki amanar soyayyarsa kacokan ya damqa mani. Gashi kuma na canza ra'ayina akansa.
.
Ban fadawa Khalil bana sonsa ba, ban fada masa na canza ra'ayina akansa ba. Ya ci gaba da xuwa wajena ina ta yi masa shigo-shigo ba xurfi. Har na hadu da Alh. Fataye mijina da nake aure ynx. Wanda ko wata daya ba a yi da haduwarmu ba ya biya mani kujerer aikin hajji ni da iyayena ya bani kyautar qatuwar mota (Discussion continioue).
.
Tun a lkcn na tsayar dashi a matsayin mijin da zan aura. Aka tsayar da lkcn bikinmu, ya ce wata daya kawai yake son a sa bikin ya gama shirya komai. Aka amince akan haka. Sbd Alh. Fataye ba qaramin mutum bane.
.
"Duk abin nan da yake faruwa ban ta6a fitowa na fadiwa Khalil gskyr abin da yake faruwa ba. Ya san ina mu'amula da masu kudi, amma bai san har na tsayar da mijin da zan aura har an sa lkcn bikinmu ba.
.
Ni hikimata ita ce in dai na samu na lalla6ashi xuwa lkcn da zan yi aure, to na jefar dashi na huta. Ban san akwai sauran tsiya a gaba ba."
.
Fauziyya ta murtuke fuskarta, hakan shi ya ganar da ni cewar labarinta ya fara xuwa daidai inda bata so a tarihin rayuwarta, ta dan 6ata lkc kafin ta ci gaba da cewa.
.
"Saura kwana uku a daura aurena, ranar wata laraba da daddare Khalil ya kira ni a waya cikin tsoro ya ce da ni, ya yi wani mummunan mafarki ne da ya razana shi ynxn nan.
.
Na tambaye shi wane irin mafarki yayi kuma? Ya ce da ni wai yayi mafarkin ana daura mani aure ne da wani ba shi ba. Nayi masa dariya na ce dashi. Ya kwantar da hankalinsa mafarkinsa ba zai ta6a zama gsky ba. Na ce ni matarsa ce, ba zan ta6a karya masa alqawari ba.
.
Bayan mun gama wayar ne nayi tsaki na ce masa shashasha, nai san saura kwana uku a daura aurena ba. Bai ta6a sanin anyi mani miji ba.
.
A ranar asabar din da aka daura aurena ya samu labarin ana bikina. Ya xo gidanmu a rude da yaga abin da yake faruwa. Ya kira ni a waya ya ce da ni yana yi mani fatan alheri. Ya tambayeni dalilin da yasa ban fada masa bikina akan lkc ba sai dai ya ji labari a wajen mutane? Na ce dashi abin ne yaxo a qurarren lkc. Na kashe wayata tun kafin muyi bankwana, na cire layina na jefar dashi, na canja wani layin wayar, sbd bana son in riqa tuno wani abu da ya wuce a baya.
.
Bayan an gama shagalin bikinmu a Kaduna, mijina da yake anan ya gina mani gida a Lagos, ya dawo da ni hankalina a kwance na yiwa Khalil nisa, ban ta6a tsammanin duk inda nake zai bi ni ya dauki fansar cin amanar da nayi masa ba. Ban ta6a zaton ba zai yafe mani ba.....Khalil ya sani a cikin gagarumar matsala ba 'yar qarama ba.
.
Ta fara rusa wani kukan wanda ya dakatar da ita da labarin da take bani.
.
Don kada ta mance da sauran abin da take so in sani a tarihin rayuwarta sai nayi saurin tambayarta.
.
"Me ya yi maki daga baya? Wane mataki ya dauka akan abin da kika yi masa?"
.
Fauziyya ta share hawayenta a wannan karon ta ce da ni.
.
"ka san na fada maka a shekarun baya sanda muna soyayya na bashi hotona ya sa a bangon littafi? Daga baya ya kwashe littafin da yaga na shiga matsala?
.
Bayan an yi aurena sai

Please Login or Register in order to submit comment