Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fito da litattafan ya ci gaba da yadasu a ko'ina a fadin qasar nan fiye da lkcn farko. Ya sa aka sake buga wadansu, duk inda ka je zaka gansu indai ana siyar da littafi a wajen.
.
Ban san yadda akayi ya riqa turo litattafan har xuwa nan Lagos ba. Ya san in har mijina ya gani ba zai so ba, ransa zai 6aci. Sbd mijina babban mutum ne ba zai so a riqa nuna matarsa a cikin wani bangon littafi ba. Akan haka zai iya rabuwa da ni, don baya son abin da zai riqa xubar masa da mutunci ko dan qanqani.
.
.
Lp=27YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 27
.
.
.
Baya son abin da zai xubar masa da mutunci ko dan qanqani.
.
Da naga haka sai na riqa bin duk inda litattafan suke ina saye su ina xuwa gida ina qonasu. Nayi tsammanin idan suka qare shi kenan na huta, amma idan naje kasuwa naga guda arba'in na saye su yau, gobe idan na je sai inga an kawo guda dari, in na saye su sai in ga an kawo guda dari uku.
.
Da na tambayesu me yasa suke turo litattafan? Sai suka ce da ni wai sun ga ana cinikinsu ne shi yasa suke qarowa. Da zarar sun qare sai Khalil ya sake bugo wadansu irinsu. Ina sayewa yana qara buga wasu.
.
Da na fahimci wannan ba mafita bace sai na nemi lambarsa na kira shi don in bashi haquri mu sasanta.
.
Khalil ya yi mani zagin fitar hankali ya ce kada in sake kiransa a waya, baya magana da matar aure. Na ce mashi ya taimaka ya fadi mani ko nawa ne zan bashi ya taimaka ya daina yadani haka a duniya tunda nayi aure. Ya ce dani bani da kudin da zan bashi in hana shi buga littafinsa, kuma haka zai ci gaba da bugashi.
.
Bari in taqaice maka labarin nan Kamal, har miliyan goma nace zan bashi ya haqura, amma yace ba ruwanshi da kudina, shi sana'arsa yake yi kawai, bani da kudin da zan bashi ya canja ra'ayinsa ya daina buga wadannan littatafan.
.
A lkcn ne na taka mata burki a fusace na ce da ita.
.
"To ki kai shi kotu mana ki sa a daure shi, waye shi da zai riqa yi maki haka kina da miji?"
.
Fauziyya ta girgiza kai ta tsuke baki ta ce.
.
"Ba zan yi nasara ba koto Kamal, sbd ni na dauki hoton na bashi izinin ya buga littafin da hotona, kuma yana da shaidu.
.
Idan kuma nace zan yi amfani da kudi akansa in sa a kulle shi kaina zan jawowa matsala, sbd Khalil zai iya yayatani a duniya ya 6ata mani suna fiye da kowa. Akwai abubuwan da idan ya fadesu na gama yawo a duniya.
.
Zai iya 6ata mani suna ya 6atawa mijina suna. Kada ka mance babban marubucine a qasar nan, yana da masoya 'yan a mutu a ko'ina a qasar nan. Yana da abokai tun daga 'yan jarida, ya san lauyoyi marasa haquri, ya san ma'aikatan gidan rediyo, yana da alfarma a wurare daban-daban. Ta yaya zan yarda in ce zan yi fada da mutum irin wannan? Bana son mijina ya san halin da nake ciki, bana son ma yaga littadin kwata-kwata."
.
Nayi shiru ina jimamin abin da ta fada mani. Tabbas idan haka ne tana cikin tsomomuwa.
.
Na rabu da ita ta ci gaba da fada mani cewa.
.
"Muna nan a haka ina a cikin wannan matsalar, kullum ina xullumin kada littafin nan ya fado hannun mijina, kwatsam! Sai larura ta same shi ya zama makaho. Ban ji dadin makancewar mijina ba, amma hakan wata dama ce a gare ni, don in har yana gani wata rana littafin zai iya fadowa hannunsa ya gani. Ynx kuwa sai dai a bashi labari, amma ba zai ta6a ganin irinsa ba. Balle ya sake ni."
.
Na sake tambayarta.
.
"Me ya same shi ya zama makaho? Ciwon ido yayi ko kuwa?"
.
Fauziyya ta yatsina fuska.
.
"A'a, kai ba ma wani abu bane ma ya faru ba, kawai tsautsayi ne ya ratsa naxo fesa masa turare a hula sai ya tsartar masa a cikin idanu, kawai dai in aka ce maka abu yaxo da tsautsayi ba yarda za'ayi."
.
Na nuna amincewa da abin da ta fada ta hanyar gyada mata kai.
.
"Duk da haka hankalina bai kwanta ba Kamal."
.
Ta ci gaba da cewa.
.
"Bana son kishiyata ta ga littafin, sbd ta hanyar wannan littafin kadai zata iya yi mani terere a wajen dangin mijina su sa shi ya rabu da ni.
.
Wata rana naje kasuwa wajen da ake sayar da litattafai, naga littafi guda daya ya ragu duk an saye sauran. Na sayi guda dayan naxo dashi gida, ina shirin zan qonashi sai ga mijina yaxo tare da direbansa, don haka sai na daga matashi na 6oye shi a qarqashi da nufin idan mijina ya gama kwanakin da zai yi ya tafi sai in qonashi don kada ya ji qaurin takarda ya tambayeni abin da ya faru.
.
A ranarsa ta qarshe da zai bar gidana ya koma can gidan kishiyata, shi ne nayi mafarkin na dauki littafin na kai cikin motarsa, da na tashi da safe bayan ya tafi sai na duba littafin ban ganshi ba.
.
Ka ji abin da yasa ka same ni a cikin wannan tashin hankalin, har naxo nayi waya a wajenka, ka ji ina kuka.
.
Wannan wayar da nayi ai Khalil na kira, shi ya jefani a cikin wannan wahalar tunda nayi aure, shi ne na roqe shi da ya xi nan gidan muyi magana. Nace ya xo ko me yake so zan bashi. Yaxo ya fada mani dalilin da yasa ya takurawa rayuwata. Ya yi mani alqawarin zai xo, kuma na san zai xo din a kowanne lkc daga ynx zaka ganshi."
.
Nayi saurin cewa da ita.
.
"Ki barshi ya xo ni zan yi maganinsa, don yaga ke mace ce kina jin tsoronsa, shi yasa yake yi maki duk wadannan abubuwan, amma ynx ki barni dashi zan yi maki maganinsa.
.
Fauziyya tayi ajiyar xuciya. Ga alama na dan kwantar mata da hankalinta a sakamakon wannan albishir da nayi mata.
.
Na sake daukar littafin yaqin da na dauko a motar mijinta Fataye. Na juya shi na tambayeta.
.
"To amma akwai abubuwa da yawa a qasa Fauziyya. In har zaki kai littafin dake dauke da hotonki cikin motar mijinki, ynx kuma in je in samu wannan littafin to tabbas hakan yana nufin yaga wancan na ainahi wanda kika tura in dauko maki.
.
.
Lp=28YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 28
.
.
.
"To amma akwai abubuwa da yawa a qasa Fauziyya. In har zaki kai littafin dake dauke da hotonki cikin motar mijinki, ynx kuma in je in samu wannan littafin kinga hakan ya nuna cewa ya ga wancan littafin na ainahi wanda kika tura ni in dauko maki. Duk wanda ya dauke wancan littafin shi ya ajiye wannan."
.
Naga ta sake kallona cikin tsoro kamar wacce ta ga aljani.
.
To amma wai zai dauke wancan littafin ya ajiye wannan a cikin motar? Sai dai ko direban Alhaji ne zai dauke littafin, tunda su biyu ne kawai a cikin motar daga shi sai mijina. Kaga kenan shi ya dauki littafin tunda mijina makaho ne baya ganin komai, sai an yi masa jagora yake iya tafiya, ba yadda za a yi yaga littafin."
.
Na ce da ita bayan nayi tunani.
.
"Wata qila kuma kishiyarki ce, tunda kin ce baku jituwa ke da ita, zai iya kasancewa ita ce ta ga littafin ta daukeshi, ta mayar maki da wannan don ta ga irin yunqurin da zaki yi akai, wajen dawo da littafin wurin ki."
.
Fauziyya tayi shiru tana juya maganar a xuciya, ga alama tafi yarda da abin da nake zato fiye da wanda take zato da farko."
.
Da naga kanta yayi dumi tana motsa bakinta amma ta kasa ci gaba da magana sai na ce da ita.
.
"Ynx saurarawa zamu yi na wani dan lkc har sai mun ga abin da zai faru, idan direban ya dauki littafin ba zai kaiwa mijinki ba, kudi zai nemi ki bashi ya rufa maki asiri. Kinga a nan sai mu san yadda zamu yi da shi idan ya yi haka. Idan kuma kishiyarki ce ta dauka ita ma dole akwai wani abu da zata fara yi kafin ta sanarwa shi Alhajin, don haka ki kwantar da hankalinki mu sa ido mu ga wa zai fara tunkararmu a cikinsu."
.
A dai-dai lkcn da na rufe baki kamar dama yana tsaye a waje yana jiranmu, sai muka ji an fado cikin falon ba neman izini.
.
Muka kai ganinmu bakin qofa a lkc daya ni da Fauziyya, ita ta fara riqe numfashinta a cikin kaduwa kamar wacce ta ga maciji akan gadonta. Ta matso kusa dani jikinta yana tsuma.
.
Yana sanye da baqar (kwat) da baqin takalmi, ya rufe fuskarsa da baqar hula kaboyi mai fadi, yana riqe da jakar matafiya a hannunsa na hagu.
.
Tun kafin in tambayi Fauziyya ta nunashi da yatsanta tana kuka.
.
"Shi ne.... Khalil ne da nake baka labari.....shi ne wanda ya jefa rayuwata a cikin matsala. Khalil ne!"
.
Na tashi a fusace don in tarbeshi, ni da shi muka kalli juna.
.
Sai da na matsa kusa dashi ne sannan na ga guntuwar bindigar dake a hannunsa kalar kayan jikinsa, hancin bindigar yana fuskantar qirjina.
.
Nayi saranda a lkc daya kamar wanda aka riqewa rai, na tsaya cikin tsoro, don kuwa naga mutuwa gaba da gaba.
.
Da ya ga na ja na tsaya ne cikin sauri sai ya saki fuskarsa ya yi murmushi ya ce da ni.
.
"Koma ka zauna shashasha, an fada maka haka nan naxo ban shirya ba?"
.
Ya sake aunani da bindigar, wannan karon kuma a saitin goshina ya saita ta.
.
Fauziyya dake a zaune a bayana ta qwalla ihu ta ce dashi a cikin magiya.
.
"kada ka harbe shi Khalil! Don Allah ka tsaya mu fahimci juna. Ka mayar da bindigarka cikin jaka ba fada zamuyi ba, na kiraka ne mu sasanta.
.
Khalil ya harareta.
.
"Wa zai yarda da maganarki muguwa? Ba zan qara yarda dake ba a duniya har abada Fauziyya. Da kika ce in xo in sameki ba muyi dake za ki dauko wani sojan gona ba, sbd haka ke kadai nake son in gani.
.
Na lumshe idona a lkcn da naga ya juyo kaina yana shirin sakar mani harsashin bindigar. Abu na qarshe da naji shi ne kururuwar Fauziyya tana cewa.
.
"Khalil ka tsaya....kada ka harbeshi, tsaya Khalil....khalil....!
.
.
KARSHE
Wannan shi ne karshen littafi na daya. Gobe war haka inshaa Allah mun dora da littafi na biyu.
.
.
Har kullum dai sadaukarwata gare ki take Khadija Musa Shehu.
.
.
Lp=29YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 29
.
.
.
"Kada ka harbeshi Khalil.... Na ce maka ka tsaya don Allah. Ka tsaya muyi magana...."
.
Fauziyya ta ci gaba da kururuwa tana yi masa magiya. Ban bude idanuna ba, na ci gaba da sauraren harsashin da na gama sakankancewa zai samu matsuguni a wani 6angare na jikina.
.
Na ji Khalil ya tambayeta a fusace.
.
"Sai ki yi sauri ki fada mani in ji. Wacce magana kike son muyi? Ba zama naxo in yi a nan ba a hanya nake. Don in banda kin dameni da in xo gidanki ban ga abin da zai sa in sake hada hanya da mace butulu irinki ba. Wacce bata san mutuncin alqawari da soyayya ba. Wacce bata san wanda yake sonta tsakani da Allah ba."
.
Na ji Fauziyya ta ce dashi.
.
"Ko me zaka ce da ni naji na amince. Na yarda ni butulu ce Khalil, amma ka tsaya muyi magana ta fahimta, don Allah ka mayar da bindigar.
.
Ayi mani afuwa zan shiga uxuriYARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 29
.
.
.
.
Don Allah ka mayar da wannan bindigar. Ka san tsautsayi gare ta, kada ta tashi a hannunka baka sani ba kayi kisan kai."
.
Na ji Khalil ya ce.
.
"Ai ko bata kucce ta tashi ba, ni da kaina ma zan harbata Fauziyya. Ban sayi wannan bindigar don in yi ado da ita ba.
.
Dama don ta kashe mani maqiyana na sayeta. Ba zan yi nadama ba idan ta tashi ta kashe mani ku, domin rayuwarku a cikin al'umma masifa ce ga mutane."
.
Fauziyya ta ce dashi.
.
"Haka ne Khalil na yarda. Amma kayi haquri ka zauna. Duk abin da ka fada gsky ne ba ka yi qarya ba, amma dan yi haquri ka zauna. Kaga kai baqo na ne, ko ruwa ban kawo maka ka sha ba, gashi ka yo tafiya mai nisa, koda zaka kashe mu ka jira tukuna in kawo maka abinci ka ci ka huta, sbd har ynx kana da matsayi na musamman a rayuwata."
.
Na ji sun yi shiru na dogon lkc shi da ita, ban sani ba wata qila kallon kallo suke yi. Wa ya sani kuma ko maganar da ta fada masa ne a halin ynxn tayi tasiri a xuciyarsa ya canja ra'ayinsa ya fasa sakar mani harsashin bindigar? Duk da haka ban yarda na bude idanuna ba sai da naji Fauziyya ta ce da ni.
.
"Ka zauna Kamal...ya fasa yin harbin. Ka zauna muyi maganar da zamu yi tare da kai."
.
Na bude idanuna a karo na farko tun fara badaqalarmu da Khalil baqon Fauziyya. Na same shi a inda yake tsaye yana kallona cikin tsana da qunan rai. Banbancin da aka samu daya ne kawai, ynx ya mayar da bindigarsa inda ya 6oyeta. Duk da haka ga alama bai yarda da ni ba. Ya za6i inda yafi yi masa a cikin shirga-shirgan kujerun falon ya zauna kafin ya tambayi Fauziyya.
.
"Wanene shi a nan gidan? Ko shima tsohon masoyinki ne da ki ka ta6a yaudara a baya?"
.
Na juya inda Fauziyya take a tsaye. Akwai alamar tsoro dake a fuskarta ya fara raguwa. Ta nuna ni, sannan ta dan yi murmushin qarfin hali ta ce da Khalil.
.
"Ka kwantar da hankalinka wannan ba masoyina bane, sunansa Kamal. Kuma mutunci kadai ke a tsakanina dashi, wallahi ba wani abu tsakanina da shi sai mutunci da taimako."
.
Khalil ya gyara zaman hular dake a kansa kaboyi, ya sake kallona sosai, ba tsana ynx a fuskarsa da yake ya ji ni ba masoyin Fauziyya bane. Ban san me yasa yake jin haushin masoyan Fauziyya ba. Babu mamaki kuma duk da rigimar dake a tsakaninsu har ynx bai cireta a xuciyarsa ba.
.
Fauziyya tayi saurin komawa ta zauna a inda ta taso daxu. Ganin haka nima sai na samu wuri na zauna, duk da haka ina tsakaninsu. Wani abu yana raya mani cewar, in har wannan azzalumin baqon ya matso kusa da Fauziyya, babu abin da zai hana ya yi sufa ya dirar mata ya murde mata wuya ta mutu. Sbd tsananin qiyayyar dake a tsakaninsu.
.
Wata qila Khalil ya gane abin da nake tsoro ne, shi yasa na shiga tsakaninsa da Fauziyya. Naga ya ajiye fankaceciyar hularsa dake kama da fai-dai, ya gyara zama ya kalle ni ya ce.
.
"Sai ka yi a hankali da ita, domin bata san a yi mata rana ba. Kada ka sakankance cewar wannan matar ba zata ha'inceka ba wata rana, komin halaccin da kayi mata a duniya, wata rana sai ta zalunceka, kada ka ce ban fadi maka ba yaro, kayi a hankali da ita."
.
Maganarsa bata yi tasiri a xuciyata ba. Na ji kamar in tashi in haureshi da qafa, to amma na san hannunsa bai yi nisa da inda ya 6oye bindigarsa ba. Motsi kadan idan ya ji bai yarda dashi ba zai iya cirota ya nuna ni da ita, don haka ya zame mani wajibi in jure duk maganganun da zai fada mata a wannan zaman da zamuyi in har ina so in sake ganin fitowar rana da faduwarta.
.
Maganar ta dan 6atawa Fauziyya rai. Na fahimci hakan ne da na juya naga tayi shiru tana tunani. Na san akan dole take lalla6a Khalil, tana yi masa ladabi. Ita ma bindigarsa da ta gani take tsoro. Kuma tana tunanin zai iya harbinta kamar yadda zai iya harbina ya yi tafiyarsa inda ya fito ba tare da kowa ya ganshi ba.
.
To amma duk baqon da ya kawo xiyara da bindiga, ko ba a so dolene a yi masa ladabi, sai an qwace bindigar sanna za a yi fada dashi. Khalil ya fahimci tsoron da muke ji ni da Fauziyya. Don haka sai ya saki ranshi ya dauki qafarsa daya ya dora akan dayar. Na sake mayar da kaina kanshi, sai ynx da ya cire hular naga yadda yake a zahiri.
.
Baqi ne amma yana da fuska mai kyau. Yana da manyan idanuwa, zai iya zama komai a tsakanin shekara talatin xuwa da biyu. Akwai wani yanayi dake tattare da fuskarsa, wanda zai yi wahala mutum yayi saurin gane abin da ke 6oye a xuciyarsa.
.
Bayan ya gyara zamansa ne, ya sa hannu a cikin aljihun kwat dinsa ya ciro kwalin taba, ya bude kwalin ya ciro guda daya ya mayar ya rufe. Sai da ya dasa tabar a bakinsa yana laluben makunnin tabar ne naji Fauziyya ta riqe numfashinta ta tambayeshi mamaki cike da muryarta.
.
"Lah...Khalil yaushe ka fara shan taba?"
.
Ya bita da kallo ko qyaftawa baya yi. Sai da ya ciro mukunnin ya qyasta yaba tabar wuta, ya fesar da hayaqin sannan ya cire tabar ya bata amsa hayaqi yana fitowa daga bakinsa.
.
"Tun ranar da kika yaudareni kika auri mai kudi ki ka barni, tun a ranar na fara shan taba, kuma ba taba kadai nake sha ba ynx. Babu abin da bana sha cikin kayan maye.
.
.
Lp=30
YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 22
.
.
.
.
Tun ranar da kika yaudareni kika auri mai kudi, tun a ranar na fara shan taba. Kuma ba taba kadai nake sha ba ynx. Babu abin da bana sha a cikin kayan maye."
.
Ya sake xuqar tabar ya fesar da hayaqinta, wanda ya tashi sama yana ninqaya a cikin falon, muna a zaune muna kallonsa. Khalil ya sake kallon Fauziyya ya ce.
.
"Ta yaya zan iya daukar fansar rashin mutuncin da kika yi mani in har ban kama shaye-shaye ba? Ni kaina na san ni mai mutunci ne mai haquri da sanin ya kamata. Idan na tsaya a hayyacina dole ne in yafe maki, shi kenan kin cuceni kin ci bulus. Shi yasa na fara shaye-shaye domin in zama mutum marar mutunci. Ta haka ne kawai nima zan iya yi maki rashin mutunci. Don ke kawai nake yin wannan shaye-shayen Fauziyya."
.
Ya ci gaba da shan tabar yana harararta. Na sake matsawa kusa da ita, domin kuwa ban yarda da irin kallon da yake yi mata ba. Ina zargin a kowanne lkc idan kanshi ya dauki caji, zai iya tasowa ya maqareta ta mutu.
.
Fauziyya ta yi ajiyar xuciya ta ce dashi a sanyaye.
.
"To Khalil naji duk maganganun da ka fada. Amma ynx me ka ke so da ni? Kashe ni kake so kayi ko kuwa me ka ke so? Ka fada mani duk buqatar da kake son ka cimmawa ynx a rayuwarka, in dai a kaina ne zan baka goyon baya ka cimma burinka. Ko kashe ni kake son kayi zan baka hadin kai ka kashe ni in har wannan shi ne abin da ka ke so."
.
Na juya inda Fauziyya take na kalleta a kidime. Ban san yadda aka yi ta qeqashe ta iya fadawa Khalil haka ba. Na san tana jin tsoron mutuwa fiye da komai, ban san ya akayi ynx ta canja ra'ayinta ta amince ya kasheta ba.
.
Khalil ya yi murmushi ya gyara zama ya ce da ita.
.
Tabbas akwai abin da nake son in cimmawa a rayuwata. Amma ba kashe ki nake son in yi ba Fauziyya. Da ace ina son in kashe ki da tuni na kashe ki, sbd na sha ganinki a gurare da yawa tare da mijinki. Duk inda kike a qasar nan akwai mutane na a wajen, kuma zasu iya fada min komai akan ki. Ko'ina kika shiga na sani ba zaki iya 6oye mani ba. Na san abubuwa da yawa dake a tattare da ke wadanda baki ta6a tsammanin na sani ba. Sbd haka ba kashe ki nake son in yi ba, so nake ki ci gaba da rayuwa a duniya, kamar yadda nima nake son in ci gaba da rayuwa."
.
Fauziyya ta tambayeshi cikin sauri akwai alamun fushi a muryarta.
.
"To me kake son ka yi mani Khalil? Ka fi son ka ganni cikin tashin hankali a rayuwata? Kafi son ka yi ta yada ni duniya bayan ina da miji? Kada ka mance ni fa matar aure ce ina da miji, ko ma ba don kada mijina yaga hotona a bangon littafi ba, ko don albarkacin aurena ai ya kamata ka canja wani bangon littafin ka daraja mani aurena mana khalil. Mutane nawa suke ganin hotona a kullum suna sha'awata? Sbd Allah ya dace ayiwa matar aure haka? Ka tuna fa wata rana zan haifi 'ya'ya, idan suka girma suka ganni a bangon littafi don Allah zasu ji dadi? Ka taimeni don Allah ka taimakeni ka daina buga littafin nan da hotona gwargwadon yadda zai yadu har 'ya'yana su girma su gani. Ni dai ka taimaka kayi haquri, duk abin da ya faru a baya ka taimaka kayi haquri ka yafe mani."
.
Fauziyya ta fara kuka, ta sa hannu ta share hawayen da yake xubo mata. Na duvi Khalil dake zaune yana kallon guntuwar tabar dake a hannunsa wacce ke bulbular da hayaqi. Na san ta ishe shi ne haka nan yana neman inda zai jefar da ita ne a falon bai samu ba. Fauziyya ta ci gaba da rusa kukan. Ta kifa kanta akan guiwarta. Khalil ya miqa hannunsa inda wani gilashin saka filawa yaka ya kashe sauran tabar a jikinsa ta mutu. Sannan ya gyara zama ya ce da Fauziyya.
.
"A wani zamani da ya wuce ba zan iya jurewa in zauna ina sauraren kukanki ba, amma a halin ynx don kin kwana kina kuka babu wani abu da zan ji a xuciyata Fauziyya. Bana jin tausayinki, na tsane ki, sbd nima nayi irin wannan kukan. Na sha kuka ba dare ba rana, tun daga ranar da kika yaudareni kika tafi kika barni. Kullum sai nayi kukan baqin ciki da takaici. Ki daina tsammanin wannan kukan munafuncin da kike yi zai sa in ji tausayinki. Ba zan sake jin tausayinki ba a rayuwa ta hat abada."
.
Ya dan saurara kafin ya ci gaba da cewa.
.
"Maganar in taimakeki in daina buga littafin da hotonki, wannan kina 6atawa kanki lkc ne, domin ba zan daina ba har sai kin amince da wani sharadi guda da zan gindaya maki."
.
Fauziyya tayi sauri ta dago kanta, fuskarta cike da hawaye. Ta yi saurin dakatar da Khalil ta tambaye shi.
.
.
Lp=23YARO BAI SAN WUTA BA...
.
Page 23
.
.
Maganar in taimakeki in daina buga littafina da hotonki, wannan kamar kina 6atawa kanki lkc ne, domin ba zan daina ba har sai kin amince da wani sharadi guda daya da zan gindaya maki."
.
Fauziyya tayi sauri ta dago kanta, fuskarta cike da hawaye. Tayi saurin dakatar da Khalil ta tambaye shi.
.
"Wane sharadi kake son in ba? Ka fada mani ko mene ne zan amince in dai zaka daina buga wadannan litattafan da hotona zan amince Khalil, ka fada mani."
.
Ta qura mashi idanu cikin qosawa da ya yi magana, sai da ya kalleta na wani lkc sannan ya ce da ita.
.
"Ina son ki rabu da mijinki in aure ki. Wannan shi ne kadai abin da za ki yi in har kina so mu zauna lfy mu daina yin wannan rigimar, ki ce ya sallame ki. Har ynx babu wata mace da xuciyata ta ke so in mallaka a duniya sai ke Fauziyya. Kasancewarki mata a ne kadai zai kawo qarshen matsalar, amma in har baki kashe aurenki ba, to kin gama zama lfy a duniya, don kuwa ba zan ta6a qyaleki ki samu kwanciyar hankali ba."
.
Har ya kai qarshen maganar babu wanda ya iya mosawa tsankan ni da Fauziyya. Ni kaina duk da yake dan kallon fadan ne, sai da naji wani qululun abu ya tsaya mani a wuya. Na dade ina jin maganganun hauka iri-iri, na dade ina jin maganganun 'yan shaye-shaye amma ban ta6a jin wata magana ta hauka da rana tsaka wacce ta gigita ni irin maganar da Khalil ya fadawa Fauziyya ba.
.
Wannan maganar tana daga cikin maganganun da nake yawan tunawa a duk lkcn da na tuno da labarin wadannan masoyan guda biyu. Ina dai jin ana fadar soyayya amma ban san haka take ba. Ban san wacce iriyar soyayya zata sa mutum ya kalli matar aure ya ce dole ta kashe aurenta sbd yana son zai aureta ba. Ban ta6a tsammanin bayan duk irin munanan maganganun da Khalil ya fadawa Fauziyya, har ynx akwai sonta a 6oye a cikin xuciyarsa ba.
.
Na juya na kalli Fauziyya a nata 6angaren.

Please Login or Register in order to submit comment