Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ban ga wani alamun mamaki akan kyakkyawar fuskarta ba, sai dai fushi da kuma alamar tsana qarara. Khalil ya ci gaba da yi mata magana ba wani tsoro ko xullumi.
.
"Ba ki ta6a zama da wani masoyi kwatankwacina ba Fauziyya. Shi kansa wannan mijin naki ba son shi kike yi ba, dukiyarsa kike so, da bashi da kudi ba za ki iya zama tare dashi ba ko na sakan daya. Ni kadai ne wanda kika ta6a so a lkcn da bani da komai.
.
Don haka ni ne masoyinki na gsky. Ki rabu da wannan mutumin ki dawo kan soyayyarki ta gsky, mu tsara rayuwarmu ni da ke, zamu zauna tare, har ynxn wannan alqawarin da muka yi yana nan daram a xuciyata, kuma ba zan ta6a canza shi ba.
.
Na ji Fauziyya ta ja dogon numfashi kamar wace aka watsawa ruwan zafi a fuskarta. Ta daga murya ta cewa Khalil,.,.
.
.
Lp=24YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 24
.
.
.
Na ji Fauziyya ta ja dogon numfashi kamar wacce aka watsawa ruwan zafi a fuskarta. Ta daga murya ta cewa Khalil.
.
"Idan baka da hankali ni ina da hankali Khalil. Ta yaya zaka dube ni da aurena da mutuncina ka ce in rabu da mijina kai ka aure ni? Wannan wacce iriyar magana ce haka? Ta yaya haka kawai zan ce wa mijina ya sake ni? Kaima ka san wannan abin ma ba zai ta6a yiwuwa ba."
.
Nayi mamakin yadda ta jajirce ta iya fadawa Khalil haka cikin fushi. To amma babu mamaki tunda dai ynx ya 6oye bindigarsa ba a hannunsa take ba. Da ace bindigarsa tana hannunsa da wahala ta iya yin wannan qarfin halin.
.
Khalil ya hade fuskarsa. Nayi zaton zai sake ciro bindigar a wannan karon tunda dai ga alama Fauziyya ta fara rage ladabin da take yi masa. Maimakon haka sai ya nuna ta da yatsa ya ce da ita.
.
"qarya kike yi baki san komai ba a wajen mutuncin aure.
.
Me yasa zaki riqa amfani da sunan mutuncin aure, kina nunawa duniya ke mace ce mai mutunci da kamala bayan a zahiri ba haka kike ba? Idan kowa bai san ke wacece ba ni na sani Fauziyya.
.
Kullum qoqarinki bai wuce ki riqa nunawa mutane ke macece ta gari ba, kowa ya yarda dake a riqa ganinki da mutunci. Amma ban da ni, sbd na san ko ke wacece a zahiri."
.
Khalil ya yi ajiyar xuciya ya sauko da qafarsa daya ya dorata akan dayar, ya matso kusa dab da inda Fauziyya take ya duqo da kan shi ya tambayeta cikin kwantar da murya.
.
"Na san ke matar aure ce, amma kin san mutuncin auren shi ne kika mayar da mijinki makaho? Haka ake zaman auren dama?"
.
Fauziyya ta yi saurin riqe numfashinta a tsorace. Na juya na kalleta cikin razana da kaduwa.
.
"....kada kayi mani sharri Khalil,,,"
.
Ta ce dashi a fusace
.
"Kowa ya san abin da ya faru da mijina tsautsayi ne. Ko likitoci aka tambaya zasu bayar da shaida, ba wani abu nayi masa ba, turare naxo fesa masa ya fada masa a idanu ya makance."
.
Khalil ya tuntsire da dariya. Na rasa ma wanda zan kalla a tsakanin Khalil da Fauziyya, domin kuwa maganganun da suke yi sun fara wuce inda na sani. Bayan ya gama tuntsira dariyar ne ya ce da ita.
.
"Fauziyya kenan! Shi yasa nake sonki, domin kina da dakakkiyar xuciya. Tun sanda naji labarin abin da ya faru na jin labarin makancewar mijinki, na sha dariya ni kadai har sai da cikina yayi ciwo.
.
Na san ke ce kika makanta shi da gangan. Ban san akwai wani turare da yake makanta mutane a duniya ba. Na san dalilin da yasa kika mayar da mijinki makaho. Ba ki so ne ya ga littafina wanda yake dauke da hotonki.
.
Kin san idan ya gani dole ne ya ji haushi ya sake ki. To amma baki yi dabara ba, ina da hanyar da zan aikewa mijinki littafin ko bai gani ba za a fada masa.
.
Har ynx baki fita daga cikin tarkona ba Fauziyya. Ba zan ta6a saurara maki ba, sai naga na cimma burina mijinki ya sake ki."
.
Ya ci gaba da keta dariyar mugunta har yana 6ingirewa akan kujerar. Fauziyya ta buge ni cikin sauri na juya na kalleta, yanayin da na gani a fuskarta ya ganar da ni abin da take nufi. Khalil ya sakankance yana tuntsira dariya ya mance da mu a zaune a tare dashi.
.
Fauziyya ta fara miqewa cikin zafin nama kamar wacce aka jefo.
.
Ta jawo wata filawar roba dake hade da qarfen wuta a qasa. Wacce aka ajiyeta don ado a kusa da tangamemen hoton taswirar hannu na wasu yara.
.
Kafin in motsa daga inda nake zaune tuni har ta kai inda Khalil yake a zaune ta kwada masa qarfen filawar akai, tus!
.
Khalil ya mayar da dariyarsa ta koma 6urari, ya kai hannu daya ya dafe kanshi. Ya kai daya hannun zai ciro bindigarsa.
.
A lkcn ne nayi nawa aikin. Na kai qafa ina a zaune na doke hannunsa, wanda hakan ya tilasta masa canja ra'ayi na dauko bindigar, domin hannunsa ba zai iya bashi hadin kai ba.
.
Na tabbatar in har ban karya masa qashin hannu ba, to nayi masa lahani wanda zai dauki lkc mai tsawo kafin ya warke.
.
Na san in har yana tare da bindigar akwai sauran hadari. Nayi sauri na tashi na tattara qarfina na buga masa uban naushi a muqa-muqinsa. Tun a zaune ya suma kafin ya sulmiyo daga kan kujerar ya fado qasa tim! Kamar an jeho buhun siminti.
.
Fauziyya ta matsa baya tana mayar da numfashinta. Nayi sauri na duqa na fara laluben inda ya 6oye bindigar a kwankwasonshi.
.
Na samu nasarar gano inda ya 6oyeta. Na cirota sannan nima na ja da baya na matsa inda Fauziyya take. Muka jere muna kallon Khalil, a lkcn da siririn jini ya fara fitowa daga cikin kan shi yana biyowa ta gefen idanun shi. Gilashin da Fauziyya ta buga masa ne ya yi masa wannan raunin.
.
Muka kalli juna ni da ita, nyai....
YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 25
.
.
.
Muka kalli juna ni da ita, nayi tsammanin zata tsorata. Domin kuwa irin wannan dukan da ta yiwa Khalil idan da tsautsayi sai ta kashe shi har lahira. Amma ba wani alamar tsorata ko razana.
.
"Na gode Kamal."
.
Ta ce da ni tana numfashi kamar ta ci wani aiki. Sai ka ce ba kan tsohon masoyinta ta fasa ba ta barshi kwance.
.
"Na gode da ka taimake ni, muka yi maganin wannan mara mutunci azzalumin...."
.
Ban ce da ita komai ba domin kuwa ni aiki ne nawa. Ita ke da abin cewa tunda dai maganarsu ce ita da baqonta. Na nuna masa bindigar dake a hannuna, na saita goshin sa da ita, na rama irin abin da ya yi mani daxu.
.
Na ga yayi saranda cikin sauri, ya lafe da jikin kujerar falon, ya daga hannayensa sama don mu yarda cewa ya bayar da kai, ya yarda mun yi nasara. Fauziyya tayi murmushin kunciyar hankali, ta ce dashi a sanyaye.
.
"Tun daxu mun barka sai magana kake ta yi bamu ce komai ba, sbd kana taqamar kana da bindiga."
.
To ynx bindigar ta dawo hannunmu, mu zamu yi magana kai kuma zaka sauraremu, kuma dole ne ka yi abin da muka umarceka, in har kana son ka ci gaba da rayuwa kaima."
.
Fauziyya ta matsa tana rausaya kyakkyawan jikinta dake kama da jikin tarwada. Ta zauna akan kujerar da Khalil ke a qasa. Na ci gaba da tsare matashin da bindigar raina a 6ace kamar wani sojan gaske.
.
Kun ji yadda rigimar ta kasance a wannan babin.
.
.
BABI NA TAKWAS.
.
.
Idan mutum ya dan shiga duniya, ya dan yawata, dole ne ya hadu da mutane iri-iri, masu tunani daban-daban. Mutum ko bai ta6a xuwa makaranta ba dole ne ya koyi wani babban darasi, domin kuwa an ce "Duniya makaranta ce ta musamman."
.
Idan kuka hadu da wani ya fada maka wata maganar sai kayi zaton shashasha ne. To amma yau da kullum kana nan zaka ga maganar nan ta tabbata in dai da rayuwa.
.
A cikin maganganun da nake tsammanin shirme ne, akwai maganar da wani abokin leburancinmu ya ta6a fada mani a lkcn ban dade da xuwa birnin Ikko ba.
.
Muntari ya ta6a fada mani cewar.
.
"Kowacce mace tana da shashasha ko wawa a gefe daya, wanda yake yi mata amfani idan buqatar hakan ta taso."
.
Lkcn da ya fada mani maganar, sun yi fada ne shi da budurwarsa. Don haka nayi zaton takaicin abin da tayi masa ne yasa yayi saurin yiwa mata kudin goro. Lkc ya yi da ya zama dole in fara amincewa da wannan maganar, tunda ga alama na fara ganin hakan akaina.
.
A cewar Muntari.
.
"Mace dole ne ta ajiye wani wanda zai riqa yi mata hidindimu. Akwai wanda shi ne masoyinta, shi take so har a cikin xuciyarta."
.
Ya ce da ni.
.
"Kamal kana zaton mace don tana da masoyi na gsky da take so shi kenan ba ruwanta da kowa?
.
Dole ne ta ci gaba da tarayya da sauran samari, su wadannan a xuciyarta ta san matsayin su. Sunan su 'Wawaye' su zasu riqa yi mata aikin da zai tallafawa soyayyar da take yiwa wani a can gefe, wanda shi ba wawa bane, masoyi ne.
.
Su zasu riqa turo mata da kati ta sa a wayarta ta kira masoyinta.
.
Su zasu riqa bata kudin da in masoyinta ya xo zata sayi kayan qwalama ta tarbe shi dasu. Wawaye ne zasu jajirce su riqa yi mata duk wata dawainiya, daga anko har xuwa kayan kwalliya, domin su burgeta ta amshi soyayyarsu.
.
To amma ba zasu ta6a burge mace ba. Wannan masoyin wanda take so ba zata ta6a ya sha wahala ba, ko ya bata wani abu ba zata amsa ba, sbd bata da matsala tana da wawaye masu yawa a gefe guda dake yi mata aiki.
.
A qarshe sai dai su ji labarin har an yi mata aure ta tafi ta barsu!"
.
Da yake a lkcn da na fara jin wannan maganar ina son hirar. Na tambayi Muntari.
.
"To amma ta yaya mutum zai gane shi masoyi ne ko kuma shi wawa ne a wajen mace?"
.
Muntari ya ce da ni.
.
"Baka isa ka gane ba, domin duk wanda ya xo ya ce yana son mace in har zata tsaya ta saurare shi, magana iri daya zata yi dashi, irin wacce take yiwa sauran samarinta.
.
Dukkansu zata fada musu tana son su, amma a cikin masoyanta guda dari ta san masoyinta na gaske. Ta san guda casa'in da tara wawaye. Zai iya kasancewa kana daga cikin wawayen wata budurwar baka sani ba.
.
Kuma ka sani mace zata iya auren wawa koda bata son shi, in dai har zai yi mata amfani a rayuwarta. Misali: zata iya amfani da dukiyarsa ta taimakawa masoyinta wanda bai samu damar aurenta ba sbd bashi da kudin aurenta a lkcn da iyayenta suka ce ya fito ayi dashi. Wata qila yana karatu ne bai gama ba. Zata yi masa komai na rayuwa ba tare da wawan mijinta ya sani ba. Don haka in kana soyayya da mace. Baka da tabbacin kai masoyinta ne ko kuma wawanta ne. Lkc ne kawai zai fayyace maka matsayinka ka fahimci ko kai wanene a wajen mace tsakanin wawa da masoyi."
.
Ga dai magana nan wata iriya Muntari ya fada mani. Ban yi wata soyayya ba a tarihin rayuwata ballantana in gane ni wawa ne ko masoyin gaske a wajen wata macen. To amma a ynx in har zan iya zama wawan, ba shakka na zama wawan Fauziyya. Don kuwa ni ne wawan da ta samu a cikin sauqi wanda nake taimaka mata wajen gudanar da wani aikin da ta sa a gabanta.
.
Lkcn da ta zauna akan kujerar ne tana murmushin samun nasara tana harar Khalil
.
.
Lp=26YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 26
.
.
.
Lkcn da ta zauna ne akan kujerar tana murmushin samun nasara tana hararar Khalil da ke maqare a jikin kujera a qasa. Sai ta ce dashi.
.
"Na fada maka daxu ka yi magana, ynx ni ce zan yi magana. Abu na farko da nake so in fara sani shi ne, da ina da ina kake kai littafinka kake bugawa da hotona ka 6oye. Ina so ka lissafo mani duk inda suke ynx-ynxn nan."
.
Khalil ya sunkuyar da kanshi, ya yi shiru bai ce komai ba. Na sake matsowa kusa dashi ina riqe da bindigar ina zare masa idanu.
.
A tsammaninsa zan iya harbata in har bai yiwa Fauziyya magana mai dadi ba. Ya dan 6ata ran shi.
.
"Ta yaya zan gane adadin inda kayana suke xuwa a qasar nan?"
.
Fauziyya ta 6ata ranta ta daka masa tsawa a fusace.
.
"Na san akwai su a ko'ina, amma dole ne a samu manyan kantinan sa ka fi jifgesu. Sunayen kantinan nake so in fara sani a halin ynxn."
.
Khalil ya sake sunkuyar da kansa xuwa can kamar ba zai yi magana ba, ni da Fauziyya muna kallonshi muna jiran shi. Ya sake cewa
.
"To ni wai ya zan yi in sansu duka? Nima ba ni ke rarraba kayan ba idan an bugasu."
.
Fauziyya ta kalleni cikin takaici ta ce da ni.
.
"Kamal kana fa jin irin amsar da yake bani, amma ba zaka yi masa komai ba?"
.
Kamar ta yi mani allura. Tana gama rufe baki na daga qafafuwana na mangare Khalil ya sake komawa ya kife a qasa. Na bishi da hannuna na fara jibgarsa kamar na samu ganga. Ya fara 6urari yana kai hannu yana tar6e wanda zai iya tar6ewa. Sai da na barshi a kwance na tabbatar ya yi laushi sannan na rabu dashi na sake komawa baya na tsare shi da bindigar.
.
Khalil yana fara murqususu a tsakar falon ya fara juye-juye kamar macijin da ke shirin mutuwa bayan yara sun yi masa rufdugu.
.
Fauziyya ta hade ranta a wannan karon babu alamar murmushi a fuskarta. Ta sake ranqwafawa kusa da kunnen Khalil kamar zata yi masa rada ta ce dashi.
.
"kada ka jawowa kanka wahalar banza Khalil. Ba zan ta6a barinka ka bar gidan nan ba sai ka fada mani duk abubuwan da na tambayeka. Bari in sake maimaitawa, a wadanne manyan kantina ka ke kai littafai ka ajiye? Ina so ne in aika aje a saye su baki dayansu a qonasu. So nake duk inda suke a qasar nan a bisu lungu-lungu a saye mani su in daina ganinsu raina yana 6aci.
.
Khalil ya ce da ita muryarsa cike da tsoro da karaya.
.
"Kema kin san bamu da inda muke sayar da kayan nan fiye da Kano. Idan kika qarar da littafi a can in dai na soyayya ne to babu inda zaki je ki sake ganin shi yayi tasiri a ko'ina a fadin qasar nan. Suna a can manyan shagunan sayar da litattafan Hausa na Kano.
.
Fauziyya ta ja dogon numfashi. Ta dago kanta ta kalle ni ta ce da ni.
.
"Wani aikin ya sameka Khalil. Ina son ka shirya ynxn nan in aike ka Airport ka hau jirgi ka je Kano. Zan baka kudi ka bi duk wani shagon sayar da litattafan Hausa ka saye mani littafin Khalil dukansu ka xubosu a mota ka kaisu wani daji ka watsar da su ka cinna musu wuta su qane duk! Mutumin nan ya sa mani ido a litattafansa, a saye su duk a hana mutane karantasu. Idan har litattafansa suna yawo a cikin qasar nan to bani da sauran kwanciyar hankali."
.
Na ce da Fauziyya cikin ladabi.
.
"Duk abin da kika ce haka za a yi ranki ya dade."
.
Fauziyya ta kalli Khalil dake a qasa yana cije baki, sbd azabar dukan da ya sha a hannuna. Ta yi tunani na wani dan gajeren lkc. Sannan ta ce
.
"Ynx dole ne mu 6oye shi kafin mu gama 6atar da litattafansa a doron qasa. Bayan mun 6atar da litattafan sun qare, sai mu san yadda zamu yi dashi. Domin in har muka bar shi ya sake kuccewa ya tafi, to zai sake rubuta wasu ya ci gaba da bugawa, ka ga an yi ba a yi ba kenan."
.
Na ce da Fauziyya abin da ta fada haka ne. Na tambayeta to a ina za ta 6oye shi inda ba wanda zai san abin da yake faruwa?"
.
Fauziyya ta sake yin tunani, ta dubi Khalil da ke kwance a qasa ta ce da ni.
.
"Akwai safayan dakuna masu yawa a nan gidan wadanda bamu yin komai da su, a ciki ya kamata mu samu kaishi dakin, ya kamata ka daureshi, kada ka tafi ka barni da shi ya 6alle qofar ya fito ya same ni ban sani ba. Ka daureshi tamau da igiya yadda ba zai kwance ba."
.
Na ce da ita, idan akwai igiya ko wayar wuta a gidan ta nemo ta kawo mani. Jikinta yana rawa don xumudi ta warware wayar labulen faffadar qofar shigowa falon daga waje. Ta jefo mani igiyar na amsa na ajiye bindigar a gefe daya, domin na san ynx ko babu bindiga ba abinda Khalil zai iya yi mani tunda dai ya sha wahala.
.
Na dauki wayar na hada qafafuwanshi waje daya na fara tamkesu da qarfi. Ya yi kuwwa a dalilin xugin da ya ji na shigar wayar cikin qafafunshi.
.
Bayan ya yi kuwwar ne ya ce da ni.
.
"Xufa nake ji, ka cire mani rigata ta sama ka barni da ta ciki."
.
Na kalli Fauziyya dake tsaye tana kallon aikin da nake yi. Don in ji ko ta amince. Ta gyada mani kai sau daya alamar in cire masa rigar. Na 6alle ma6allan baqar kwat din, sannan na warware masa naketayin din wuyansa dake maqure da kwalar farar rigarsa ta ciki mai dogayen hannuwa. Na sa6ule masa kakkaurar rigar na jefar da ita gefe daya.
.
Jinin dake tsiyayowa.
.
Lp=27YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 27
.
.
.
.
Na yi sauri na fita na jawo qofar na kulle shi a ciki, don kada Fauziyya ta fusata ta sake afka masa da wani sabon dukan. Duk da na kulle qofar bai daina aiko mata da zagin ba. A qarshe ne naji ya fashe da kuka iya qarfinsa. Na kalli Fauziyya dake tsaye, ga mamaki a wannan karon bata ji haushin zagin da yake yi mata ba. Akwai alamar dariya akan kyakkyawar fuskarta. Ta ce da ni a cikin murmushi.
.
"Kamar da gaske! Duk wannan zagin da yake yi mani da zan ce ina son shi zan kashe aurena in aureshi sai ya fi kowa farin ciki a duniya. Haushina yake ji ban aureshi ba, shi yasa yake yi mani wannan zagin. Da zai ji labarin mijina ya sake ni na koma gida, shi zai fara xuwa ya ce yana so zai aure ni."
.
Fauziyya ta tuntsire da dariya. Ban san abin da ya bata sha'awa ba a cikin abin da ta fada.
.
Ta jagoranceni muka sake komawa falon, tayi saurin dauke bindigar Khalil da muka barta a yashe akan kujera. Ban ta6a tsammanin za ta iya sa hannu ta dauki bindigar ba. Na dauki ludayin miya kawai. Na dauka ludayin miya kawai zata iya riqewa. Na tsaya kawai ina kallonta.
.
Ta juya bindigar a hannunta ta ce da ni.
.
"Bari in 6oye wannan bindigar a hannuna. Ban yarda da wancan mugun ba. Idan ya 6alla qofar ya fito a qalla zan iya sarrafashi ya bi umarnina in har akwai bindigar a hannuna.
.
Bana son ta bar bindigar a hannunta domin a yadda ta tsani Khalil, idan ya ci gaba da dukan qofar yana zaginta, zata iya bude qofar ta harbeshi. Faruwar hakan kuwa ba qaramin tashin hankali zata jawowa kanta ba tare da ni da nake taimakonta.
.
Wata qila ta fahimci tunanin da nake yi ne da ta ga na tsaya ban ce mata komai ba.
.
Fauziyya ta yi dariya ta ce da ni.
.
"Ba zan harbeshi ba Kamal. Wannan rigimar da muke yi babu wanda zai iya kashe wani a cikinmu. Na fadi maka a baya cewar Khalil yayi mani halacci a baya, shi ne masoyina na farko a rayuwata, in ba don ynx ya canja ya zama azzalumi ba yana takurawa rayuwata, da ba zan iya yi masa abubuwan da muka yi masa a ynx ba. Kome zai yi mani ba zan iya kashe shi ba. Ka shirya ka tafi Kanon. Amma kayi wanka ka canja kayan jikinka. Ban sani ba ko raunin da kaji ya fara yi maka sauqi, zaka iya lalla6awa ka tafi a haka."
.
Na ce da ita.
.
"ba matsala zan iya tafiya a haka. Raunin da naji ba mai yawa ba ne, idan na dawo sai muje asibiti a bani maganin da za a bani.
.
Fauziyya ta ce da ni cikin murmushi.
.
"Na gode Kamal. Na gode sosai. Da ba don kai ba, da ban san yadda zan yi da rayuwata ba, ka taimakeni sosai, na gode."
.
Na ce da ita.
.
"Ba komai, ni na sa kaina.
.
Ni dai fatana kawai ta fita daga cikin wannan matsalar, ta zauna lfy da mijinta. Fatana ta daina xuwa tana yin kuka a bakin titi, domin ba mutuncinta bane. Ni dama don ta daina kukan ne na sa kaina zan taimaketa. Ban san abin da yasa bana son in ga kyawawan mata suna kuka ba a duniya.
.
Fauziyya ta kai bindigar dakinta ta 6oyeta. Ta dawo ta gyara falon. Ta kawar da rigar Khalil da jakarsa da yaxo da ita wacce bamu budeta mun ga abin da yake ciki ba.
.
Ku yi mani afuwa zan shiga uxuri.
.
Lp=28YARO BAI SAN WUTA BA....
.
.
Page 38
.
.
.
Fauziyya ta kai bindigar dakinta ta 6oyeta ta dawo ta gyara falon, ta kawar da rigar Khalil da jakar da ya xo da ita wacce bamu bude ta mun ga abin da yake a ciki ba.
.
Komai na falon ya dawo yadda yake. Ta kai ni danin baqi na musamman dake a gidan. Na shiga nayi wanka. Kafin in fito ta debo mani qananan kaya masu kyau, sababbi, koriyar riga da kuma baqin wando da takalmi mai rufi. Ta hado mani da agogo dan ubansu. Ta dauko mani jakar matafiya 'yar qarama ta xuba mani maqudan kudi a ciki 'yan dubu dai-dai.
.
A lkcn da na shiga wani daki da ta nuna mani ne ta ce mani in shiga in sanya kayan da ta kawo. Bayan na fito na dawo falon na same ta ina gyara zaman wuyan rigar.
.
Fauziyya ta ce da ni.
.
"Ga milyan daya nan ka tafi dasu duka Kamal. Duk abin da ya kamata kayi a ciki. Idan kaga dare zai yi maka ka samu otel mai kyau ka kwana a can, gobe sai ka dawo amma idan son samu ne ka dawo a yau."
.
Na ce da ita.
.
"Zan yi iya qoqarin da ya dace in yi in ga na dawo yau din. Na amshi jakar a lkcn da wani abu mai kama da kiyashi yake yi mani yawo a cikin qwaqwalwar kaina. Ban ta6a riqe milyan daya a dunqule a hannuna ba sai a wannan rana.
.
Lkcn da Fauziyya ta dauke ni a motarta muka nufi tashar jirgin sama ne ta ce da ni.
.
"Idan kudin basu kai ba, ka yo mani waya zan fadi maka inda zaka je ka kar6a."
.
Aikin ba wani wahala. A cikin awa biyu Fauziyya ta gama komai a tashar jirgin, ina zaune ina jiranta.
.
Jirgin ya shiryya tafiya, aka kiramu muka shiga. Da ace na nemarwa kaina sauqi, daga wannan lkcn na qara gaba da kudin na bar Fauziyya ita da baqon ta, in kashe kansu zasu yi su kashe. To amma idan wautar son mace ta sarqafi xuciyar namiji, ba zai iya fita daga sawun wawaye ba, sai yaga uwar bari yake guduwa. Don haka ban yarda xuciyata ta ribace ni kan in gudu da kudin ba. Shi yasa daxu na fada maku cewar in har Fauziyya tana da wawaye a gefe guda. To ina daga cikin manyan wawayenta.
.
Na xo qarshen wannan zangon, bari in sake daukarku mu ci gaba da tafiya a cikin wannan dan qaramin labari mai cike da ban tausayi da ban haushi.
.
Idan kuka yi haquri muka tafi a haka, wata qila a qarshe ku tsinci abin da zai baku sha'awa a cikin labarin, ku ji cewar baku tsaya kun 6ata lkcnku a banza ba wajen saurarena.
.
.
.
Yawace-yawacen da na sha a Birnin Kano, ina bin duk wani babban kanti na sayar da litattafan hausa ina saye litattafan Khalil. Abin ya baiwa 'yan kasuwar litattafan mamaki, don haka wadansu sun fahimci abin da yake faruwa, sai nayi masu qaryar cewa, wani masoyin littafin Khalil ne hamshaqin mai kudi yake son ya saye duk littattafansa ya kyautarwa mutanen da ba zasu iya saye ba.
.
Sai da naje kasuwar ne naga littafin Khalil da ya sa hoton Fauziyya mai suna "KASHE NI KA HUTA!" Dole ne Fauziyya ta rude wajen ganin ta 6atar da littafin an daina ganinsa, domin kuwa dan guntun kallabin da ta dora akanta bai yi komai ba wajen sakaya

Please Login or Register in order to submit comment