Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya dace yayi tsakanin kwantawa ko kuma ci gaba da zama.
.
Xuwa can idanuna suna kan shi, sai kuma ya yi hamma ya sake yin tsaki, sannan sai naga ya bi tsawon bencin shima ya kwanta, duk da haka hankalina bai kwanta ba, don kuwa na tabbatar duk lkcn da ya ji wani baqon motsi zai tashi cikin fushi kamar yadda za ka tashi mafadacin maciji a cikin ramin sa.
.
Na dauki lkc mai tsawo a nan ba tare da na motsa koda dan yatsana ba. Mai qaton cikin naji ya fara jan munshari.
.
Bayan na qara 6atar da wasu mintocin kimanin arba'in, sai naji shima mara haqurin ya take masa baya. Dana tabbatar su dukansu sun yi barci sai naja da baya, a haka har na koma inda na sake 6oyewa daxu. Da xuwana ban tsaya jiran komai ba sai nayi jan hali na fara neman ta inda zan hau katangar in tsallaka cikin gidan.
.
Itatuwan dake a jikin katangar gidan su suka taimaka mani a wajen kama saman katangar bayan nayi tsalle, sai da na huta sannan na dora qafafuwana akai.
.
A lkcn ne naga duk gine-ginen dake a cikin katafaren gidan Alh. Fataye, kuma a kalla daya na karance duk wani lungu ko wani saqo dake a harabar gidan.
.
Duk da yake akwai hasken qwayaye, ba ko ina mutum zai tsaya a ganshi ba, in dai ba kusa da hasken mutum zai matsa ba.
.
Na saurara ina wurga idanuna ina neman inda karnukan gidan suke la6ewa, inda naci rashin sa'a shi ne, kamar sun san da xuwana, har wani lkc ba wanda ya kuma yin haushi a cikinsu, balle in san ta inda zan 6ullo musu.
.
Ban tsaya jiransu ba, tunda dai na sha alwashin ba zasu hana ni daukar abin da naxo nema ba a gidan. Nayi qarfin hali na dira a cikin gidan dif, qafafuwana suka sauka a cikin korayen ciyayin dake malale a ko ina a harabar gidan wadanda nake zato suma kwalliya aka yi dasu, don naga an kwakkwafesu sun tashi tsawo daya. Na tsaya cak na kasa kunne don in ji ko wani daga cikin karnukan gidan ya ji motsin dirowata daga saman katangar.
.
Ban ji komai ba har tsawon minti daya, don haka sai na fara bin motsin katangar ina qoqarin matsawa cikin gidan, sannu a hankali daga inda nake ina iya hango wata qatuwar baranda wacce ke lullu6e da xuqa-xuqan motoci har guda biyar a cikinta, gilashinsu sai sheqi yake yi daga nesa a sakamakon dan abin da ba za a rasa ba na hasken qwayayen lantarkin dake a warwatse a ko'ina kamar taurari.
.
A kallo daya na gama nazarin motocin dukansu, guda biyu a ciki farare ne, sai baqa a tsakiyarsu wacce ta kasance yaya babba, a qarshe daga 6angaren hagu akwai ruwan toka da wata 'yar dunqulalliya mai ruwan hanta.
.
Haj. Fauziyya ta fadi mani cewa a motarsu mai ruwan toka mijinsu ya bar gidanta a ranar da ta kai littafin cikin motar, don haka in har yana nan har ynx a ciki, ya rage nawa in san hanyar da zan bi in bude motar ba tare da kowa ya ganni ba....
.
Tunani na ya katse a lkcn da naji motsi daga nesa kadan daga inda nake a raku6e a jikin katangar. Nayi saurin kai ganina inda naji motsin, a lkcn ne nayi tozali da daya daga cikin firda-firdan karnukan dake a gidan.
.
Baqi ne wuluk wanda yake kama da qaramin dan maraqi, yana tafiya yana gurnani yana waige-waige, na manne a jikin katangar kamar cingam na dauke numfashina. Karen yayi haushi sau biyu, sannan ya tsaya da tafiyar yana waiga kowanne 6angare, hakan shi ya tabbatar mani cewar ya ji motsina daga inda yake a can farfajiyar gidan.
.
Yana gama haushin ne naji wadansu guda biyu suma sun dauka daga sauran lungunan dake a gidan. Na sake bushewa a jikin katangar kamar gunki, har xuwa lkcn da ya gama haushinsa ya canja wuri, ya tafi inda sauran 'yan uwansa suke. A qalla dai ynx karnukan sun tona kansu. Na san yadda zan yi in kauce masu ba tare da sun amsheni ba.
.
Sai da karen yayi nisa sannan na ci gaba da rarrafawa na tunkari inda motocin suke a qarqashin doguwar barandar, akwai laima a jikin qanqanun korayen ciyayin dake a lullu6e..
.
.
Lp=18YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 18
.
.
.
Akwai laima a cikin qananun korayen ciyayin dake lulli6e da duk harabar gidan, wannan alamace dake nuna dare ya fara yin nisa ra6a ta fara saukowa daga sararin samaniya.
.
Naci sa'ar kaiwa inda motar take, nayi saurin kwantawa a qarqashinta a lkcn da na ji kamar motsin wani abu a kusa da ni.
.
Na saurara xuciyata na bugawa da sauri, a lkcn wani ganjejen kwado yayi tsalle ya fito daga cikin ciyayin dake malale a qasa ya hawo saman barandar da motocin suke.
.
Na sake kwantar da hankalina, tunda kwado ne ba karnuka ba. Na taso na tsugunna a jikin qofar motar, nayi saurin ciro kayan aikin bude motar a 6oye ba tare da fitar wani sauti ba.
.
Tun kafin in xo dama sai da na kammala nemo duk wani abu da na san zai taimakeni wajen wannan gagarumin aiki da na tasa a gabana.
.
Na lalubi inda mariqin qofar motar yake, na saka siririn qaramin mabudi a cikin kwadon qofar wanda na san amfaninshi tun a wani dadadden lkc a sakamakon zaman da nayi tare da wani direban simogal, na fara juya mabudin kunnena na lura da duk wani motsi dake kaiwa da komowa a cikin gidan.
.
Qofar motar ta bude tare da wani ragon sauti dake kama da sautin 6alla qyanqyaleshe. Ban tsaya jiran komai ba sai na bude qofar a hankali ina durqushe na dafa kujerar motar na saka kaina a ciki jikina na tsima don kuwa na shigo matakin qarshe a cikin aikina.
.
Na fara laluben kujerun gaba na motar, sai a lkcn ne na tuna da maganar Fauziyya da ta fada mani cewar a kujerun 6angaren baya na motar tayi mafarkin ta saka littafin, don haka sai na shiga cikin motar na dora guiwoyina akan kujerun, na miqa hannuna a 6angaren da kujerun baya suke na fara lalubawa a cikin duhun dake cunkushe da motar.
.
Hannuna ya fada kan wani littafi mai laushin bango, nayi sauri na cakumo shi kamar shaho ya cafki dan tsako, don kuwa na tabbatar shi ne abin da naxo nema. Na fito da littafin na riqe shi da hannu biyu, duhun dake a cikin motar ba zai barni inga littafin ba, to amma tunda dai na san babu wani littafi a cikin motar sai wannan, ban tsaya 6ata lkcn wani tantamar sahihancin littafin ba, sai na janye qaramar rigata na cusa littafin a cikin aljihun wandona xuciyata cike da farin cikin nasarar da na samu.
.
Na tabbatar ynx na kawo qashen baqin cikin dake damun Haj. Fauziyya.
.
Ba qaramin farin ciki zata yi ba idan ta ganni tare da littafin da ta ke nema ruwa a jallo. Ta ci sa'a tunda direban motar mijinta ya ajiye motar babu wanda ya sake xuwa ya bude balle ya ga littafin asirinta ya tonu.
.
Ynx matsalarta kawai shine idan ta sake yin wani mafarkin a lkcn gaba, ynx dai mafarkinta bai bani wahala mai yawa ba, tunda dai a cikin motar mijinta tayi mafarkin ta jefa littafin ba a barikin sojoji ba.
.
Bayan na gama 6oye littafin ne sai na zaro qafafuwana na fito daga cikin motar na fara haramar guduwa, don kuwa ban yarda da mahaukatan karnukan dake a harabar gidan ba.
.
A dai-dai lkcn da qafafuwa suka sauka a qasa ne ina dafe da qofar motar, sai naji wani abu mai kama da asuwaki yana gwaiguyar gefen kunnena.
.
Na sandare a waje daya kamar an zare mani rai, jinin jikina yayi tsayuwar wucin gadi.
.
Na juyo a hankali. Jinin jikina yayi tsayuwar wucin gadi a lkcn da nayi arba da busasshen hannunsa dake riqe da bindigar da ya dasa ta kusa da kunne na.
.
Sai da na kalli faskeken qirjinsa dake kama da qofar daki, sannan na daga kaina muka hada ido dashi.
.
Fuskarsa a murtuke yana numfashi sama-sama, a lkcn ne ya ce da ni.
.
"Dama na fadiwa Jibo nan gidan ka xo amma ya qi yarda. Na san abin da ya kawoka kenan tun farkon ganin da nayi maka, ba yau na fara ganin 6arayi ba."
.
Ya qara gyara tsayuwar bindigarsa da yaga ina motsi, na sake daskarewa a waje daya ina jiran ya sakar mani harsashin bindigar.
.
Shi ne mai gadin da nake ta xullumi tun daxu, na tabbatar in har naxo hannunsa kashina ya bushe.
.
"Me ka sata da ka shigo? Yi sauri kayi mani bayani, baka da isasshen lkcn da ya rage maka a duniya....akai zan harbeka inda zaka mutu da wuri, bani abin da ka sata kada in canza ra'ayi in fara karya maka qafafuwa da harsashin bindigata!!"
.
Ya sake daka mani tsawa a karo na biyu.
.
"Kayi sauri ka bani abin da ka sata bana son kana 6ata mani lkc, kada ka bari in yi fushi in yi maka kisan wulaqanci."
.
Na tabbatar duk abin da yake fada da gaske yake yi, tabbas an basu damar su harbe duk wanda ya fado hannunsu. Duk da yake mai gadin qaqqarfa ne na san zan iya jan daga muyi fada, to amma babbar matsalar ita ce kafin fadanmu yayi nisa dan uwansa dake can a waje yana sharar barci zai iya juyowa shima ya bude qofa ya shigo cikin gidan ya same mu. Idan suka rufar min su biyu dole ne su ci qarfina bani da hanyar guduwa. Don haka in har ina da sauran shan ruwa a gaba dole ne in yi qoqarin doke wannan mai fadin qirjin ba tare da mun yi wani bugi in buga ba, don gudun samun tallafi daga abokin aikinsa ko kuma mafadatan karnukan dake bushartarsu da xuwan mara gsky cikin gidan.
.
.
.
Lp=19YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 19
.
.
.
Babbar matsalar ita ce kafin fadanmu yayi nisa dan uwansa dake can waje yana sharar barci zai iya jiyowa shima ya shigo cikin gidan ya samemu. Idan suka rufar mani su biyu dole ne su ci qarfina bani da hanyar guduwa. Don haka in har ina da sauran shan ruwa a gaba dole ne in yi qoqarin doke wannan mai fadin qirjin ba tare da mun tsaya bugi in buga har wani ya ji abin dake faruwa ba.
.
Sai da na juya da idona na kalli yatsansa dake kan kunamar bindigar na tabbatar akwai sauran tazara tsakanin kunamar bindigar da yatsansa.
.
Cikin zafin nama na shammace shi na duqa qasa hannunsa ya goce daga kaina, a lkc guda na dirka masa uban naushi a ciki wanda ya jigata hannuna. Na san da wahala ya iya jure wannan naushin, don haka sai na saurara, a lkcn ne kuma naga bindigar tana rawa a hannunsa, ya sa daya hannun ya dafe cikinsa, sannan ya rage tsawo, qafafuwansa suka kasa daukarsa, ya sa guiwarsa a qasa ya durqusa kamar an kayar da bujimin sa.
.
Duk da wannan azabar da ya ji bai yarda bindigar ta su6uce daga hannunsa ba, sai dai ba zai iya yin harbi ba a cikin wannan mawuyacin hali. Na san idan ya fara samun sauqi ya juyo kaina ba zai sassauta mani ba, don haka ban yarda ya samu sauqi ba, yana a durqushen na sake dunqule hannu na daki muqamuqinsa. A wannan karon ni na sha wahala na shi ba, domin kuwa sai sa qashin hannuna ya motsa kamar na daki qarfen katafila. Naga ya girgiza kanshi yana qoqarin shanye dukan, in har ban sake neman wani wajen da zai yi laushi na daka ba, to akwai matsala, idan har ya murmure ya sake dora yatsansa akan kunamar bindigar nan to sai dai wani ba ni ba.
.
Na sa qafa na daki wuyansa dai dai inda maqogwaronsa yake, a lkc daya ya kife ta gefe ya fadi qasa kamar raqumin da za a yanka.
.
Ya bude baki zai yi ihu, tunda dai ya tabbatar na gami jigata shi don haka ne yake son ya isarwa abokin aikinsa dake a can waje, nayi sauri na riga shi, kafin yayi ihun na sa qafata na bugi hancinsa, ihun da zai yi ya maqale, ya zama dan qaramin sautin da mutum zai ji idan ya take kwado a cikin ciyawa.
.
Yanayin da na gani a lkcn da yayi dai-dai a qasa ya tabbatar mani da ya haqura, ya ba bori kai, duk da haka bai yarda ya saki bindigar ta fadi qasa ba. A tsammanina ko sare hannunsa za a yi ba zai yarda ya saki bindigar tasa ba, na san dai kafin ya farfado nayi nisa sai dai in mun sake gamuwa wata rana, amma a wannan karon nayi nasara akanshi.
.
Na barshi kwance a tsakanin motocin, na tafi cikin sauri. Da na matsa wajen haskene sai na duqa na fara rarrafe don kada wani ya hango inuwata daga cikin gidan. A haka har na kai jikin katangar na ci gaba da tafiya ina qoqarin in kai daidai ta inda na tsallako na shigo gidan. Saura bai fi taku goma in kai wajen ba sai na ji gurnani a gaba na, sannan naji ya kwantsama haushi kamar faduwar aradu a itace. Na ja baya a tsorace ina kallonsa. Shi ne karen da na gani daxu wanda ya kusa ritsani.
.
Kafin in warware daga faduwar da nayi ne naji yayi tsalle ya fado mani, muka fadi qasa tare, ya haye kaina yana haushi kamar zai cinye ni danye.
.
.
Lp=20YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 20
.
.
Muka fadi qasa tare ya haye kaina yana haushi kamar zai cinye ni danye.
.
Ba kayar dani da mahaukacin karen a yi yafi tsorata ni ba, haushin da yake yi yana sanarwa 'yan uwansa dake a nesa su matso kusa shi yafi damuna.
.
Na sa hannuwana biyu na maqare wuyansa da qarfi na tsayar da haushin da yake yi, ya koma gurnani.
.
Hakan shi ya qara mani qaimi, a lkcn ne kuma ya fara kafa mani dogayen faratansa dake kama da reza. Ina ji yana yaga mani kayana to amma in ana ta rai wa ke ta kaya?
.
Karen qaqqarfa ne kuma a yadda nake zato shima irin wancan mai gadin ne bashi da haquri. Muka dauki lkc mai tsawo muna kokuwa, wani lkcn na kan yi sa'a in birkiceshi, in danneshi qasa to amma baya yarda in galabaitar da shi, sai ya yunqura ya sake yi mani dirar mikiya.
.
Ban yarda ya cijeni ko sau daya ba, na san in har ya fara cixona to kafin wani lkc zai wahalar da ni ya kaini qasa, don haka sai na ci gaba da maqale wuyansa na barshi yana ta raunata ni da faratansa.
.
Lkc yayi da ya kamata in yi wani abu, kafin sauran mafadatan karnukan gidan su lura da abin dake faruwa suxo su yi mani dandaxo. Muna nan a haka nayi qoqarin ture Karen daga kaina, sai na matsa jikin katangar ta hanyar jan jiki ina a kwancen, ya sake biyo ni yana gurnani, duk hannuwana sun gaji sbd qarfin riqon da nayi masa.
.
Na tattara qarfina waje guda na saita kan Karen da jikin katangar wacce dutse yafi yawa a jikinta na gwara kanshi da dutsen, na ji qarfinsa ya ragu a lkc guda, na sake mayar masa da kan inda na bugashi da farko cikin azama, sai da nayi haka sau biyar a jere kafin karen yayi saranda ya langa6e kamar tsumman da ya kwana a ruwa, nayi sauri na watsar dashi ya fadi yaraf! a gefa daya.
.
Kafin in yi yunquri in tashi ne naji sautin harbin bindiga, harsashin ya wuce ta saman kaina kamar ayarin qudan xuma. Ba saina tsaya wahalar yin wani tunani ba kafin in gane cewar daya mai gadin ne ya shigo bayan da ya fahimci abin da yake faruwa.
.
Sautin tashin bindigar ne ya jawo hankalin ragowar karnukan gidan suka garzayo aguje suna haushi suka fado harbar gidan.
.
Bani da sauran wata dama da ta wuce in hanzarta tsallakawa in gudu, domin idan har karnukan suka rutsani a wajen da kuma maigadin riqe da bindigarsa to ba sauran hanyar da zan iya nemowa kaina in gudu.
.
Na tashi da sauri kafin qiftawar ido nayi tsalle na kama katangar. Kafin in janye qafafuwana in dora su a saman doguwar katangar ne naji daya daga cikin karnukan ya kama mani saman takalmina da bakinsa yana jawo ni. Saura kadan in fado qasa na sake yunqurawa na ja qafata, karen ya manne kamar mayen qarfe yaqi sakar mani qafar, don kada wani ya kama daya qafar ita ma, sai nayi qoqari ita na dorata a saman katangar.
.
Ragowar karnukan suka xo wajen suka yi dafifi suna haushi suna tsalle, suna qaimin kamo ni in fado qasa gabansu suyi kalaci da ni.
.
Na sake jin sautin harbi, a wannan karon harsashin ta bayan wuyana ya wuce kamar kibiya, ga alama mai gadin yaxo wajen shima, don haka babu shakka idan ya sake harbo binigar a lkc na gaba ba zai yi kuskure ba.
.
Nayi sa'a takalmina da karen ya kama da bakinsa ya sa6ule, duk da haka bai haqura ba sai da ya huda mani yatsun qafata guda uku da dogayen haqoransa, da naji takalmin ya cire sai nayi saurin janye qafata a lkc guda na fada qasan katangar tare da wani harsashi da ya rakoni muka fada waje tare.
.
Lkcn da na dira a waje ne ban tsaya jiran komai ba sai na fara cin gudu akan titi, duk da azabar da nake ji a qafata da sauran raunikan da naji wadanda ke xubar da jini.
.
Ban yi nisa da fara gudun ba naji harbe-harbe a bayana, maigadin bai haqura ba shima ya tsallako katangar ya biyoni, to a qalla dai ynx babu mafadatan karnukan, shi kadai zan fuskanta.
.
Nayi nisa ina kaucewa harashin dake take mani baya, ban yi zaton mai gadin zai iya kamo ni ba a wajen gudu in dai shine wannan mai qaton cikin to bani da matsala dashi.
.
Tunanina ya katse a lkcn da naji sautin jiniyar motar 'yansanda tana tahowa cikin 6urari.
.
.
Lp=21
YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 21
.
.
.
.
Tunanina ya katse a lkcn da naji sautin jiniyar motar 'yansanda tana tahowa cikin 6urari a can bayana daga nesa. Na waiga bayana a tsorace na hango danjojin motar suna dau-dau, na san idan ban nemi ma6oya ba, ba yadda zan yi in 6oye masu tunda dai ni kadai ne akan titin cikin wannan daren, ga kuma hasken qwayayen lantarki a ko'ina a layin kamar gidan gwamna.
.
Na saki titin na shiga wani qaramin layi dake as hannun haguna, nayi saurin fadawa cikin faffadar hanyar ruwan dake a kowanne 6angare na gefen hanyar, na ja jikina da qyar na shiga kwalbati, na ci sa'a ba ruwa a ciki sai dai qananan duwatsun kankare wadanda suka yi mani lale marhabin kamar zasu huda mani jikina. Na kwanta akansu na lumshe idanuna ina numfashi sama-sama ina sauraren abin da zai biyo baya.
.
Ban dade ba a cikin kwalbatin naji xuwan motar 'yan sandan sun hau kwalbatin sun wuce. Ban motsa ba sai da na daina jin 6urarin jiniyar motar, ban san yadda akayi jami'an tsaron suka san abin da yake faruwa ba a cikin dan lkc qanqani.
.
To amma da na tuna cewar Alh. Muhsin Fataye babban mutum ne, kuma wata qila yana a cikin gidan abin ya faru, zai iya kasancewa shi ne ya yiwa 'yan sanda waya ya fada masu 6arawo ya shigo gidan sa.
.
Bayan kimanin minti goma da wucewar motar 'yan sandan xuwa can sai naji sun qara dawowa, amma a wannan karon motar ba gudu take yi ba a hankali take tafiya, me yiwuwa sun ci nemana ne basu ganni ba suka fahimci a baya suka barni shi ne suka sake dawowa.
.
Sun dade a kusa da kwalbatin basu yi gaba ba, basu kuma yi baya ba, naji surutunsu a cikin motar amma bana jin abin da suke cewa.
.
Za su kai su biyar a yadda naji muryoyinsu. Ban san jayayyar da suke yi ba, wata qila wadansu suna qorafin a tsaya a sake duba ko'ina ne, wadansu kuma suna cewa a koma tunda dai na tsere.
.
Bayan minti daya suka ja motarsu suka tafi, nayi ajiyar xuciya bayan da na daina jin sautin motar ne komai yayi tsit, sai tunanina ya fara daidaita. Lkc yayi da ya kamata in kira Fauziyya in fada mata halin da nake ciki, na san a ynx haka tana can a zaune tana jiran in kirata in fada mata yadda al'amarin ya kasance.
.
Na lalubi wayata dake a cikin aljihun wandona ina a kwance na cirota, agogo na fara dubawa naga qarfe uku saura minti biyar. Ban yi zaton lkc yayi gudu haka ba.
.
Na sake lalubawa naji littafin yana nan a cikin aljihuna, shima duk artabun da na sha bai fadi ba. Na nemo lambar wayar Fauziyya na kirata, da shigar wayar naji ta dauka ta fara magana da sauri muryarta na rawa.
.
"Kamal...Hello Kamal kana ina ne ynxn? Me ya faru, ka dauko mani littafin kuwa?"
.
Ban san wacce tambayar zan amsa mata ba. Na ce da ita a sanyaye cikin rada.
.
"Na dauko maki littafinki Fauziyya. Na sha wahala sosai, amma mun yi nasara ynx haka ina tare da littafin."
,
Naji ta ja wani dogon numfashi kamar wacce aka sheqawa ruwan qanqara a tsakiyar kai.
.
"Na gode sosai Kamal. Na gode! Na gode....! Saura qiris ta bushe da dariyar farin ciki, akwai xumudi a muryarta, sai daga baya ta tuna dani ta tambaye ni.
.
"kana ina ne in xi in dauke ka?"
.
Na ce da ita.
.
.
Lp=22
.
"YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 22
.
.
.
"Kana ina ne in xo in daukeka?"
.
Na ce da ita.
.
"A cikin wannan uban daren zaki fito da mota Fauziyya? Ki bari sai nan da asubahi ynx haka ina a 6oye ne a cikin wata kwalbati 'yan sanda ne suka biyo ni da mota suna nema na, amma na 6oye masu. Zan fito idan na tabbatar komai ya lafa."
.
Fauziyya ta ce da ni.
.
"Shi kenan Kamal, duk sanda ka fito ka fada mani in xo in daukeka. Na gode."
.
Na kashe wayar don kada wani ya ji muryarta a cikin kwalbatin aiki ya sake dawowa danye. Farin cikin da naji a muryarta shi ya rage mani zafin radadin da nake ji a ko'ina na jiki na. Ynx dai na cimma burina tunda har na taimaki Fauziyya, gashi har tana doki da murna a muryarta, ynx ba sauran kuka da xullumi. In har ba wani mafarkin ta sake yi ba a lkc na gaba, to komai ya wuce.
.
A lkcn ne naji wata xuciyar tana raya mani cewar in har muka hadu zan cire kunya in fadawa Fauziyya kamata yayi daga ynx idan zata kwanta barci ta samu igiya ta riqa daure kanta a jikin gadonta don kada tsautsayi ya ja ta sake maimata irin wannan mafarkin, ta tashi ta je tayi 6aran6atama a wani wajen kuma.
.
Da ace tuntuni tayi hakan, da ni kaina ban tsinci kaina a wannan matsananciyar wahalar ba.
.
.
**
.
.
Sai da gari ya kusa wayewa na fito daga cikin kwalbatin na kama hanya na tafi kai tsaye ba wani xullumi don kuwa na san ynx babu jami'an tsaron, sun dauka tuni nayi nisa.
.
Sai da na fito daga unguwar sannan na fara haduwa da tsirarun 'yan aca6an da suka fito kan tituna.
.
Gani na cikin halin da nake, duk kayana sun yayyage, ko'ina mutum ya duba rauni ne a jikina, sai na yanke shawarar tsayawa in kira Fauziyya don taxo ta daukeni tunda dai nayi sa'a na fito daga unguwar.
.
Na raku6e a jikin wani sabon gidan mai. Ba kowa a wajen sai masu gadi biyu dake shara wadanda basu dago kai sun kalle ni ba. Na ciro waya na kirata na fada mata inda nake a halin ynxn.
.
Fauziyya ta ce da ni.
.
"Ka jirani gani nan xuwa Kamal. Ka bani minti goma."
.
Na mayar da wayar cikin aljihuna na raku6e a jikin wani diron xuba shara don kada wani jami'in tsaron ya xo wucewa ya ganni.
.
Ko bai san abin da na aikata ba a daren da ya gabata, da ya lura da raunikan da ke a jikina zai matso kusa ya nemarwa kanshi sanin ko ni wane ne?
.
Tun kafin minti goma ta cika ta diro wajen da xuqeqiyar motarta, a lkcn tuni na yada zango a bencin masu gadin gidan man, ta danna hon sau biyu.
.
Masu gadin dake shara suka dago kai suka qura mata idanu.
.
Har daya a cikinsu ya garzaya aguje zai xo ya sameta, ganin na miqe na nufi inda take da xuwana na bude motar na shiga.
.
Tun kafin in gyara zama ta fuxgi motar muka

Please Login or Register in order to submit comment