Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

masa da kyankyaso a kusa da shimfidarsa.
.
Da ace bani da rabon shan wahala a wannan lkcn ya kamata in ce tayi haquri ba zan iya yin wannan tarar aradun ba.
.
A wannan lkcn ya kamata in bude qofar motar in ficewana in rabu da ita, in yaso tayi tsalle ta fada a kogin maliya, wannan matsalarta ce ita kadai.
.
To amma da yake tun farko na fada maku xunxurutun kyawunta shi yake hana ni qaurace mata in yi ta kaina.
.
Sai kawai na ce da ita.
.
"Ba matsala Hajiya zan xo....kuma nayi maki alqawarin komai rintsi sai na shiga cikin gidan nan na dauko maki littafinki. Kada ki damu!"
.
Fauziyya ta kada idanunta sbd tsananin jin dadi....
.
Lp=13YARO BAI SAN WUTA BA....
.
.
Page 13
.
.
Fauziyya ta kada idanunta sbd tsananin jin dadi sai kace wacce iskar asubahi ta ratsa. Na tabbatar wannan albishir din da nayi mata ya fi qanqara sanyi a xuciyarta.
.
"Na gode sosai, Allah Ya bamu sa'a muyi nasara a wannan gagarumin aiki da muka sa a gabanmu."
.
A nan tayi kwana da motarta muka juya, bayan ta tabbatar na gama nazarin gidan.
.
Ta sake hawa titin da gudu tana tuqa motar tana fara'a, haqoranta farare sol kamar gonar auduga suka haske gaban motar.
.
.
**...**
.
.
A shekarun baya farkon xuwana Lagos bayan nayo hijira daga qauyenmu na taho birni yawon duniya na ta6a ganin wata tsaleliyar budurwa kamar nunanniyar tsada ta wuce ta gabana ni da wasu leburori 'yan uwana.
.
A lkcn ne na rude da addu'ar inda zan samu mace mai irin wannan kyau a duniya to ko mayya ce taxo, ina sonta!
.
A lkcn da na fadi wannan magana akwai wani mutum mai dan hankali a cikinmu wanda shima Lebura ne. Ba zan mance da kalaman Malan Audu ba sanda yake cewa da ni.
.
"Lallai kai yaro ne danye Kamal, baka da hankali. Bari in fada maka wata magana ka kiyaye da ita ko don gaba.
.
Ka ga mace idan ta cika kyau?....to wani lkcn hadari ce, kamar ka kunna wuta ne a cikin gida ka barta ba ruwan kashewa a kusa.
.
Bari in baka wani misali, ka lura da kyau, duk wanda aka ce yana neman auren wata mce wacce kyanta ya shahara aka santa a ko'ina, to zaka same shi bashi da wani sauran sukuni da kwanciyar hankali.
.
Kullum aikinshi kenan gwagwarmaya da samarinta, yana xullumin kada wani yaxo yayi masa qafa daya ya ture shi ya aureta. Idan ya sameta ya aureta da qyar, to da anxo wajen zaman auren in dama ba wani sonshi take yi ba, to bai isa ya ce zai riqa juyata yadda yake so ba.
.
Kamar yadda take sarauniya sanda tana gidan su maza suna rububinta, wannan tunanin ba zai ta6a barin xuciyarta ba.
.
Da kayi mata laifi daya zata nuna maka ita fa mai kyau ce, taimaka maka kawai tayi ta aureka don taga ka mutu wajen sonta, ta san ko fita tayi akwai wadanda suke jiranta, kodayaushe suna lale marhabin da su mallaketa, da wahala darajarta ta fadi in har ba tsufa tayi ba.
.
"Idan kana da wata matar bayan ita, in ba hankali kayi ba sai ta turaka cikin hallaka ka zama mai nuna banbanci a tsakanin iyalinka.
.
Sannan a 6angarenta in ba tarbiyya ta samu tun a gida ba, in har ba mutuniyar kirki bace, sbd wannan xunxurutun kyawun nata sai an samu wani shaidanin da zai lalla6a ya ce zai neme ta, tana da auren amma wani ba zai iya haqura ya rabu da ita ba, dole sai ya nemi ya cimma burinsa akanta sannan hankalinsa zai kwanta.
.
Sannan kome ta ce tana so ko ba alheri bane da rawar jiki zaka yi mata, da ka auri mace mai kyau to ka zama bawanta, in kana da kudi ne kawai zaku zauna lfy ta bika sau da qafa, amma in har baka da qumbar susa to ka zama abin tausayi, duk wata wahala akanka zata qare, komai ka nemo nata ne ita kadai. Dole ne ka bita a haka in dai kana son ta zauna.
.
Don haka kayi a hankali Kamal, mace mai kyau hadari ce, da ka sanyata a xuciyarka shi kenan ka qulla abota da rashin kwanciyar hankali."
.
Lkcn da Mal. Audu ya fadi wannan maganar, da yake yawancinmu 'yan bana-bakwai ne duk sai da muka qaryata shi.
.
Wani wanda ya fi ni zuciya da zafin rai sai da ya gargadi Mal. Audu cewar, in har aka qara fitowa aiki yana fadar irin wannan maganar sai ya tsinkeshi da mari.
.
Ni kaina duk da ina girmama mutumin sai da na nuna masa damuwata. Na ce dashi gsky ba girmanshi bane ya rinqa fadar irin haka a gaban yara.
.
Duk aikin wahalar da muke yi burinmu bai wuce mu tara kudi mu nemi mace ta fita kunya mu aura ba. To idan ya ce kada mu auri mai kyau ai ya 6ata taku kenan.
.
Mutumin ya yi mana dariya ya ja girmansa. Tun daga lkcn bai sake yi mana nasiha irin wannan ba.
.
Wannan al'amarin ya dade da faruwa, lkc-lkc maganar Mal. Audu ta kan fado mani a rai. Ban ta6a yarda gsky ya fada ba har xuwa ynx da na hadu da Fauziyya.
.
To amma a can cikin xuciyata akwai wani abu guda daya a cikin maganarsa wanda ya fara yi mani tasiri kada-kadan a halin ynxn.
.
Babu shakka in har duk abin da mutumin ya fada qarya ne ya zama dole in gasgata maganarsa daya da yake cewa.
.
".....Da zarar ka sanya mace mai kyau a xuciyarka, shi kenan ka qulla abota da rashin kwanciyar hankali...."
.
Nayi saurin amincewa da hakan ne a lkcn da dare yayi na tunkari gidan Alh. Fataye dake Alkoyi inda Fauziyya ta kai ni na gani da safe.
.
Da daren yayi ma ita takai ni a motarta ta tsaya a nesa ta sauke ni don kada wani ya ga motarta ya gane ita ce ta kawo ni.
.
Ni kaina na san abin da zan aikata kuskure ne. Kuma tabbas zan jefa rayuwata ne a cikin hadari. To amma ta yaya zan iya hana kaina bayan kyakkyawar fuskar matar tayi mani kane-kane a cikin xuciyata?
.
Duk sanda nake tare da kyakkyawa Fauziyya, idan tana yi mani magana da sassanyar muryarta na kan mance matar aure ce tana da miji. Na kan ji kamar wata masoyiyata ce, wacce har abada ba zan iya rabuwa da ita ba.
.
.
Lp14YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 14
.
.
.
Duk sanda nake tare da ita, idan tana yi mani magana da sassanyar muryarta na kan mance matar aure ce tana da miji. Na kan ji kamar wata masoyiyata ce, wacce har abada ba zan iya rabuwa da ita ba.
.
Don haka indai kyau hadari ne, to babu shakka na gamu da babban hadari a rayuwata, domin a yadda na tabbatar Fauziyya ta shiga raina, ko raina zan rasa in har hakan zai faranta mata rai to na shirya hakan, don haka abin da ya faru ya riga ya faru.
.
Lkcn da ta tsayar da motar a nesa, sai ta ce da ni.
.
"Idan ka je ynx ka samu wani wurin ka 6oye a cikin shuke-shuke Kamal. Kada ka fito sai qarfe daya na dare. Idan ka samu nasarar shiga gidan zaka ga inda suke ajiye motocinsu, motar Alhaji ruwan toka ce qirar (Ford), da ita yaxo gida na shekaranjiya, kuma cikinta nayi mafarkin na jefa littafin, sbd haka ita zaka yi qoqarin budewa, ka shiga ciki ka laluba kujerun 6angaren baya, in har littafin yana nan to a nan zaka same shi."
.
Na ce da ita cikin qarfin hali.
.
"Shi kenan ki koma gida sai na dawo."
.
Na bude motar zan fita.
.
Ta kira suna na.
.
"Kamal."
.
Na saurara, sannan nayi saurin juyawa na kalle ta.
.
Hasken fitilar dake a jikin rufin motar ya bayyanar mani da fararen idanunta wadanda suke motsawa tare kamar tagwayen qwayaye.
.
Ta kasa fada mani abin da take son ta sanar da ni. Sai da ta dade a haka tana kallo na sannan ta ce.
.
"Ka bi a hankali, bana son wani abu ya same ka. Idan har wani abu ya faru da kai ba zan ta6a yafewa kaina ba, sbd ni ce sanadi."
.
Na ce da ita.
.
"Babu wani abu da zai same ni Fauziyya sai alheri. Zan shiga cikin gidan in dauko maki littafinki a cikin motar mijinki. Idan na fito zan kira ki a waya in fada maki inda nake."
.
Fauziyya ta numfasa. Xuciyarta a karye ta ce da ni.
.
"Idan ka kirani zan xo da mota in daukeka Kamal."
.
Muka sake yin shiru muna kallon juna. Ban san me yasa take yi mani irin wannan kallon ba.
.
Tausayina take ji, ko kuwa kallon mahaukaci take yi mani? Ita kadai ta san abin dake a cikin xuciyarta.
.
Da naga zamu sake 6ata lkc a wajen sai na fita daga cikin motar na rufe na ce da ita.
.
"Ki koma gida sai na kira ki anjima."
.
Na sa kai na tafi ba tare da na sake waigawa na hango fararen idanunta ba wadanda wataqila da ba don su ba da ban shiga cikin hadarin dake shirin faruwa da ni a nan gaba kadan ba.
.
Sai da nayi nisa naxo gab da katafaren gidan, sannan na waiga a karon farko, don in ga ko Fauziyya tana nan ta kasa tuqawa ta tafi sbd tsananin tausayin nawa da take ji?
.
Babu motarta babu dalilinta. Tuni tayi ribas tayi tafiyarta.
.
Komai ta fanjama-fanjam!
.
.
.
.
**....** BABI NA HUDU.
.
.
Duk inda na kai ganina a harabar gidan haske ne tarwai kamar rana, babu inda quda zai shiga ya samu mafaka ya 6oye, to ballantana kuma ni bil Adama.
.
Qartin masu gadi biyu da na gani daxu da safe har ynx suna nan zaune akan benci kamar an dasu su sai faman zazzare idanu suke yi, kowanne da gashin baki buxu-buxu kamar sun manna fuka-fukai.
.
Daya yafi daya qiba da qaton ciki, shi ne wanda yake sanye da baqin takalmi sau ciki iya guiwa kamar zai je haqo man fetur.
.
Dayan shima qato ne, amma yafi auki a qirjinsa, da ace zai koma wasan danbe zai fi kwarjini fiye da aikin gadi.
.
A halin ynx babu wanda yake riqe da bulala a cikin su, haka nan suke zaune sankayau hannunsu babu komai.
.
Wannan ba zai sa in saki jikina ba, sbd na san shegiyar tana nan a manne a jikin kwankwaso.
.
Ba zai ta6a yiyuwa masu gadin wannan katafaren gida a rasa su da bindigogi ba.
.
Ban san me ke a cikin gidan ba a sakamakon doguwar kantangar da ta kusa shanye dogon ginin dake a ciki.
.
To amma shiga cikin shi ne mai wahala, idan har zan samu nasarar doke wadannan qartin guda biyu in shiga cikin gidan, duk sauran abubuwan da zasu biyo baya masu sauqi ne.
.
Fauziyya dai ta gargadeni cewar kada in yi sakaci domin akwai mahaukatan karnuka a cikin gidan, ta ce suma suna da hadari, sai dai na san cewar hadarin su bai kai na harsashi ba.
.
Na san zan iya tserewa kare, amma ba zan iya tserewa harsashin bindiga ba. Don haka babban aikin dake jirana bai wuce wadannan qartin guda biyu ba.
.
Na qara matsawa kusa da gidan, babu kowa idan aka dauke masu gadin. Na xo daidai inda suke zaune na wuce su kamar ban san dasu a wajen ba.
.
Duk da ban kallesu ba a lkcn da zan wuce ta gabansu in nufi jikin doguwar katangar gidan, wani abu yana sanar da ni cewa ni suke kallo, kuma basu yarda da ni ba.
.
Ban yi taku goma da wuce su ba naji wani daga cikin su ya daga murya ya kwada min kira.
.
"Kai ina zaka je?"
.
Na tsaya cak. Sannan na juyo na dube su. A lkcn ne naga sun tashi sun nufo inda nake da sauri kamar suna tsammanin zan ruga aguje.
.
Mai fadin qirjin yafi mai qaton cikin zafin nama da sauri, shi ne a gaba. Hakan shi ya bani damar sanin wanda zai fi bani matsala a cikinsu.
.
Suna cimma inda nake.....
.
.
Lp=15YARO BAI SAN WUTA BA...
.
Page 16
.
.
.
Ban yi taku uku da wuce su ba naji wani daga cikinsu ya daga murya ya kwada mani kira.
.
"kai ina zaka je?"
.
Na tsaya cak! Sannan na waigo na dube su. A lkcn ne naga sun taso sun nufo inda nake da sauri kamar suna tsammanin zan sheqa a guje.
.
Mai fadin qirjin ya fi mai qaton cikin zafin nama da sauri, shi ne a gaba. Hakan shi ya bani damar sanin wanda zai fi bani matsala a cikin su.
.
Suna cimma inda nake a tsaye, hasken qwayayen wutar da suka mayar da gidan rana suka haskeni ta ko ina. Da xuwansu mai fadin qirjin ya tsaya a gabana kamar zai karya kumallo da ni.
.
"Ina zaka je, kuma wa kake nema a nan?"
.
Na ce dasu ba wani tsoro a muryata.
.
"Hanya ce ta biyo da ni, ko an hana bi ta nan ne?"
.
Mai qaton cikin ya tambaye ni.
.
"Wanne gida kake nema a nan layin? Bamu ta6a ganinka ka biyo ta nan ba."
.
Na dubi fuskokinsu dake kallo na a fusace kamar dodanni, na ce.
.
"Na fadi maku hanya ce ta biyo da ni, idan kuma an sa dokar bi ta nan ne sai in sani daga yau."
.
Mai dadin qirjin rigar ya riga dayan saurin cewa cikin barazana.
.
"bari mu fada maka ka ji da kyau, idan ma kai 6arawo ne gara ka canza shawara ka koma domin ba zaka yi nasara a nan unguwar ba. Mun san baka da gsky kuma sata ka xo yi.
.
Kada ka ce bamu gargadeka ba, idan ka kuskura ka fado hannunmu to sai dai uwarka ta haifi wani!!"
.
Na ce dasu nima cikin fushi.
.
"Ni ba 6arawo bane.....amma tunda kuka ci mutuncina kuka dafa mani zargin sata, zan bi haqqina, na gane ku, zaku san ko ni wane ne anan unguwar."
.
Mai qaton cikin ya dan ji tsoro, ya dafa mai fadin qirjin alamar ya bar maganar a hannun sa, kada su ta6o abin da zai zame masu matsala.
.
Ya dan sa tunani kadan a cikin maganarsa ya ce da ni.
.
"Dole ne mu zargeka Malam, ka duba agogonka ka gani, qarfe nawa muke ynx?
.
A qa'idar wannan unguwar in har qarfe takwas na dare tayi ba wanda zaka gani a waje, duk wanda yake zaune a wannan eriyar ya san da wannan dokar, don haka in har a nan kake ya kamata ace ka san da haka kaima."
.
Na ce dasu cikin daga murya da naga sun fara saukowa.
.
"To amma idan wani abu ya tsare ni na dawo a makare sai aka ce daku ku tsare ni? Ku 'yan sanda ne? Ba gadi kuke yi ba a nan gidan? Kun ga na shiga cikin gidan ne?"
.
"Zan je in kai qararku wajen 'yan sanda gobe, Yayana abokin Alhajinku ne, zan fada masa, zaku raina kanku....gobe ma idan kun ga wani ya taho ku ce zaku raina shi."
.
Mai qaton cikin ya fara lallashi na.
.
"Ba haka bane Masta, ka san yanayin aikin nam, bamu san anan eriyar kake ba, mun sha kai baqo ne, amma kayi haquri, ka tafi kawai ba wani abu tunda mun gane ka daga yau irin haka ba zai qara faruwa ba."
.
"Shi kenan, ku kiyaye a lkc na gaba. Ku riqa tsayawa a bakin aikinku kawai."
.
Na ce dasu sannan na sa kai na ci gaba da tafiya. Naji sun koma bakin aikin su, mai fadin qirjin yana cewa mai qaton cikin.
.
"Ynx haka barazana yake yiwa mutane, kayi saurin tsorata Jibo, naso ka bar ni in yi masa ladabi daga baya sai ayi bayani in ma yana da gsky.".
.
Wanda ake cewa Jibo ya ce da mai zafin xuciyar.
.
"Gara da muka lalla6a shi muka rabu lfy, ka san halin yaran eriyar nan ba mutunci ne dasu ba. Tana iya yiyuwa dan wani qusa ne, daga baya yaxo ya fadiwa Mai gida mu shiga matsala."
.
Dayan yayi qunquni ban sake jin abin da yake cewa ba.
.
Har nayi nisa ban sake waigowa na kalle su ba, amma na tabbatar daga inda suke zaune a qofar gidan ni suke kallo don su ga inda zan nufa.
.
Katangar gidan Alh. Fataye bata qare har xuwa lkcn da na shiga duhun bishiyu dake a nesa daga iyakar gidan da bakin titi da ya keto a cikin layin daga baya.
.
Na shiga cikin duhun itatuwa na raku6e a jikin katangar na saurara.
.
Ba wanda zai xo wucewa ya yi zaton akwai mutum a wajen.
.
Na dade a zaune a cikin duhun ganyayen shuke-shuke, a lkc-lkc motoci sukan xo su wuce, amma har nayi kusan awa daya ban ji motsin wucewar wani mutum a qasa ba, hakan shi ya tabbatar mani da dalilin zargin da masu gadin gidan Alh. Fataye suka yi mani.
.
Ban fito ba, na zauna na ci gaba da sauraren haushin karnukam dake tasowa daga kusan kowanne gida kamar suna gasa.
.
Haushin karnukan da nake ji daga cikin gidan Alh. Muhsin Fataye shi yafi tayar mani da hankali, don kuwa na san dasu zan yi arba nan da dan lkc kadan.
.
Bayan qafa ta dauke ba wani motsi a ko'ina in ka dauke haushin karnukan dake amsa amo, sai na fara shirin aikin da ya kawo ni. Kafin in nemi hanyar da zan tsallaka doguwar katangar gidan Alh. Fataye, ya zama dole in sake komawa wajen masu gadin don in tabbatar sun yi barci.
.
Na fara bin jikin katangar a hankali ina tafiya kamar hawainiya. Yawancin shuke-shuken dake a jikin katangar ba wadanda suke bayyana sauti bane idan aka taka su.
.
Har na kai kusa da faffadar qofar shiga gidan inda masu gadin biyu suke ban yarda nayi wani qwaqqwaran motsi ba.
.
Tun kafin in qarasa kusa dasu na fara jin maganarsu dake tasowa a sama-sama kamar wadanda suke yin rada. Naji daya yana cewa da dayan
.
"Ka kwanta kayi barcinka ba matsalar komai.
.
.
Lp=17
YARO BAI SAN WUTA BA...

Lp=17YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 17
.
.
.
Ka kwanta kayi barcinka ba matsalar komai, na fada maka ba wani mara gaskiya bane, kawai hanya ce ta biyo dashi ta nan, ba 6arawo bane. Shi mahaukacin ina ne da zai yi gigin shigowa nan gidan ya ce zai yi sata?"
.
Dayan ya ce cikin damuwa.
.
"Ban yarda da yaron nan ba Jibo, da ganinsa ka san bashi da gsky....lkcn da muke magana dashi ba inda yake kallo sai katanga, yana qoqarin fahimtar tsawonta. 6arawo ne, sata yaxo yi. Na tabbatar ynx haka yana nan a 6oye a wani wajen yana jiran muyi barci ya haura katanga ya shiga cikin gidan.
.
Dayan ya ce cikin damuwa.
.
"Matsalarka kenan Dari, kai kullum baka yarda da kowa, in dai mutum zai wuce ta nan sai ka ce 6arawo ne. Don Allah ka kwanta kayi barci, ni na gaji da wannan surutun, barci nake ji."
.
Na ji wanda yake qorafin wanda na tabbatar shi ne mai fadin qirjin ya yi tsaki ya jawo benci.
.
Na sa hannu daya na ture wadansu ganyaye da suka hanani ganin masu gadin, na leqo a hankali numfashina yana fita a hankali. Naga mai qaton cikin a kwance akan dogon benci ya miqe qafafuwa, te6arsa kamar an dora masa kayan wanki. Shi kuma dayan yana zaune akan naa bencin ransa a 6ace yana qoqarin fitar da shawarar abin

Please Login or Register in order to submit comment