Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a qafarta, ta doro kallabin rigar a kanta kamar guntun mayafi, ta 6oye iya abin da bata son a gani na daga yalwataccen gashin kanta.
.
Kyawunta yana nan bai ragu ba, kamar yadda na ganta jiya. Kuma wani abu da yaso ya rikita ni shi ne, in har mutum yana rikida ya canza launi, to wannan kyakkyawar mace tafi kowa iya rikida a doron qasa. Ta qara haske ba kamar jiya ba, wata qila kuma ganin da nayi mata a ynx har quruciya tafi jiya, don kuwa ta dawo yarinya shekarunta sun ragu a dare daya. A ganin da nayi mata jiya da wani zai tambayeni sai in rantse da Allah ta kai shekara talatin da biyar, to amma ynx ko shakka ba zan yi ba zai yi wuya ta wuce shekara ashirin da shida.
.
Tayi mani sallama na amsa mata, tana kallona a cikin rashin fahimtar ko ni wanene. Bata lura da jakarta dake a hannuna ba.
.
Ta tsaya daga baya ta tambayeni, da sassanyar muryarta.
.
"Wa ka xo nema a nan gidan?"
.
Na ce da ita kai tsaye.
.
"ke naxo nema Hajiya.
.
Da naga ta tsaya cikin rashin fahimta ne tana yi mani kallon uku da kwabo, sai na fito mata da jakar da ta manta a wajen sana'ata nace da ita.
.
"na kawo maki jakarki ne da kika mance da ita jiya a wajen da nake sayar da katin waya."
.
Cikin sauri ta kalli jakar, a lkc guda naga ta saki ranta tayi mani murmushi, fuskarta ta canza kamar yadda kalanzir yake canza ruwa idan suka hadu.
.
"Oh! Sannu Malam. Ashe kaine nayi waya a wajenka jiya? Ban gane ka ba kayi haquri."
.
Ta qaraso inda nake ta zauna a kusa da ni, na miqa mata jakarta ta amsa cikin farin ciki.
.
"na gode, dama ynx nake tunanin yadda zamu hadu don in kar6i jakata. Ya akayi ka san gidana?"
.
"ki yi haquri na bude jakar ne na samu katin adireshin ki a ciki, dashi nayi amfani na gane gidanki. Duba cikin jakar ki ga kayan dake ciki, ba abin daya 6ace ko?"
.
Tayi dariya da zazzaqar muryarta, sannan ta ce.
.
"Sai ka ce na ajiye wata tsiya a ciki? Ai dama (Complement card) dina ne na (Address) nafi ji, shi kenan ma ni bani da saura, ba komai a cikin jakar. Na gode da ka hutar da ni ba sai na sake komawa ba."
.
Ta dora jakar akan cinyarta sannan ta rage fara'ar dake akan fuskarta ta ce da ni.
.
"Ina da yawan mantuwa....haka kwanaki daga naje yin (Shopping) na mance da motata, sai da na aika aka dauko mani ita.
.
Tunani da rashin kwanciyar hankali sun tarar mani akan nan nawa..na rasa yadda zan yi in samu sauqin wannan masifa da ta same ni."
.
Tayi tsaki sannan tayi tagumi ta qurawa wani hoto dake a bangon falon idanu. Hoton wata 'yar fulani ce da aka zanata da hannu dauke da qwaryar nono akanta.
.
Na san ba hoton ya dauki hankalinta ba a halin ynx, tunanin wani abu marar dadi take yi.
.
Nayi shiru ina kallonta, xuciyata na bugawa a tsakanin haqarqarina kamar ana rawar disko a ciki. Bayan tayi wani dan qaramin tunani ne sai ta ci gaba da magana.
.
"Jiya raina ne ya 6aci har kaga ina yin wannan kukan. Ban san na mance da jakata ba. Wani abu ne yake takurawa rayuwata a duniya, a kwana biyun nan ko abinci bana iya ci, na shiga matsala babba a tsakanina da mijina. Ban san ya zan yi in fita daga wannan matsalar ba.
.
Rashin kwanciyar hankalinta da kuma takaicin da na gani a fuskarta jiya ya sake dawowa kan fuskarta, kamanninta suka canza a cikin sauri, shekarunta suka qaru. Sai ynx na fahimci ashe idan ranta ya 6aci ne take qara girma, amma da zarar tayi murmushi take komawa qaramar yarinya.
.
Nayi ajiyar xuciya sannan nayi qarfin hali nace Nayi ajiyar xuciya sannan nayi qarfin hali nace da ita.
.
"Hajiya ni kaina na fahimci kina a cikin damuwa tun a ganin da nayi maki jiya da daddare. Da zaki fada mani abin da yake damunki da na taimake ki, kome zan yi in har zai taimake ki fita daga cikin wannan matsalar zan yi maki Hajiya."
.
Tayi saurin juyo da fuskarta ta dube ni da dara-daran fararen idanunta sannan tayi murmushi.
.
"Me yasa kake son ka taimake ni bayan baka sanni ba, asalima baka ta6a gani na ba sai jiya a karo na farko?"
.
Na ce da ita.
.
"Haka rayuwa take Hajiya, haqiqa ban sanki ba, ban kuma ta6a ganinki ba sai jiya.
.
.
Lp=9YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 9
.
.
.
Haka rayuwa take Hajiya. Haqiqa ban sanki ba, ban kuma ta6a ganinki ba sai jiya, to amma a zahirin gsky na damu sosai da halin da naga kin shiga. Da abin na kwana yana damuna a xuciyata, haka kawai naji ina son in taimakeki, in har babu damuwa."
.
Ta numfasa bayan ta gama saurarena.
.
"Babu damuwar komai wallahi. Duk wanda ya ce yana son ya taimake ka a rayuwa ai baka da tamkarsa. Ba zan 6oye maka komai ba, zan fada maka abin da yake damuna, amma kai gashi baka fada mani ko sunanka ba, ya kamata in fara saninka tukuna."
.
Ta ci gaba da murmushi tana kallona.
.
"Suna na Kamal."
.
Na ce da ita.
.
"Inda kika ganni jiya nan ne wajen sana'ata, kuma ni Bahaushe ne gaba da baya daga arewa naxo, bana shekaruna shida a nan lagos."
.
Ta gyada kanta alamun gamsuwa. Iyakar tarihina da zan iya fada mata kenan, a duk shekarun da nayi a Lagos ban ta6a fadiwa wani tarihina mai tsawo kwatankwacin haka ba.
.
"Kamal."
.
Ta kira suna na a karo na farko, sannan ta ce da ni.
.
"Nima mutuniyar arewa ce, asalina 'yar Kaduna ce, aure ya kawo ni nan Lagos, nan shi ne gidan mijina, kuma kamar yadda kaxo ka samu gidan nan, ko ban fada maka ba na san zaka fahmci ko wanne irin miji nake aure.
.
Mijina hamshaqin attajiri ne, yana da dukiya sosai, wannan gidan duk girman shi ni kadai ya gina mawa, nawa ne ni kadai.
.
Akwai kishiyata da yake aure, ita ce matarsa ta farko, nata gidan yana can Ikoyi, shima kamar wannAkwai kishiyata da yake aure, ita ce matarsa ta farko, nata gidan yana can Ikoyi, shima kamar wannan ne.
.
Muna jin dadin rayuwarmu, to amma akwai abubuwan dake tattare da zama na da mijina, wanda yake bani wahala, kuma yake sa ni jin tsoron idan ban bi a hankali ba zama na ya kusa qarewa tare dashi, zai iya sakina a kowanne lkc daga ynx..
.
Ka ji abin da ke damuna nake a cikin xullumi Kamal."
.
Na tambayeta ba wani tsoro a muryata.
.
"Mene ne wannan abin Hajiya? Ki fada mani zan taimake ki."
.
Ta sake numfasawa cikin damuwa ta ce da ni.
.
"Suna na Fauziyya."
.
Ta fada mani haka ne don in riqa kiranta da sunan ta. Hakan shi ya ganar da ni tana sha'awar sunanta fiye da Hajiyar da nake kiranta dashi.
.
Ta ci gaba da yi mani magana tana kallona har cikin idanunta.
.
Sunan mijina Muhseen Fataye, sanannen mutum ne a nan Lagos. Amma kuma wani abin takaici da zan fada maka shi ne, mijina makaho ne baya gani. Shekara daya kenan da makancewaSunan mijina Muhseen Fataye, sanannen mutum ne a nan Lagos. Amma kuma wani abin takaici da zan fada maka shi ne, mijina makaho ne baya gani. Shekara daya kenan da makancewarsa.
.
Naji wani abu ya tokare a xuciyata kamar ta6aryar sussuka, nayi tunanin kasancewar attajirin mutum kwatankwacin mijinta amma kuma baya gani. Naji tausayinsa ya kama ni duk da cewa ban ta6a ganinsa ba, sai ynx na fara jin labarin sa a wajen Fauziyya matarsa.
.
Kamar ta san abin da nake tunani a xuciyata saqi tayi murmushi ta ce da ni.
.
"Mijina ba abin tausayi bane Kamal. Duk da makancewarsa bai daina yin komai ba a cikin al'amuransa na aiki da ya saba, yana xuwa ofis ya yi aiki, yana hulda da duk mutanen daya sani kafin makancewarsa. Duk inda zai je ana yi masa jagora, idan a nan wajena yake, ko'ina zai je ni ke yi masa jagora in kai shi. Kwana biyar yake yi a kowanne gida. Yau kwanansa biyu da komawa wajen daya matar tasa, saura kwana uku ya dawo nan wajena."
.
Nayi shiru ina saurarenta, ina jira ta fada mani in ji ta yadda akayi ta shiga matsala da makahon mijinta har take xullumin zai sake ta.
.
Fauziyya ta ce da ni.
.
Tun kafin mijina ya makance akwai wata doka da ya kafa mani, wacce yayi alqawarin in har ban kiyaye da ita ba zai sake ni. Mijina baya so ina karanta litattafan soyayya na Hausa.
.
Ban san me yasa ya dauki karan tsana ya dorawa litattafan nan ba, ko don shi Bayerabe ne shi yasa yake kishin ganin ina karanta litattafan soyayya? Ni dai ban sani mashi ba, tun ina amarya da ya fara kama ni da litattafan ya nuna mani fushinsa sosai, ya gargade ni, sai dai in za6i abin da ya fi so, ko aurena ko karanta litattafan soyayyar.
.
Ni kuma ina masifar son litattafan soyayya, abin ya kama ni kamar jaraba, duk inda zan je in same su sai naje na siya, haka nan nake a 6oye ba tare da ya sani ba. Muna zaune a haka kuma sai Allah Ya kawo masa wannan larura ya zama makaho.
.
Tun daga lkcn na samu 'yancin yin karatuna kai tsaye ba wani xullumi, sbd baya iya gani na, ko xuwa yayi ya same ni ina karatu, baya iya gane karatun nake yi, idan ya tambayeni me nake yi? Sai in ce dashi babu komai, ina kwance ne kawai ina hutawa. Duk da haka ya kan gargadeni, ya ce da ni kada in ga don ya makance in ce zan ha'ince shi in ci gaba da karanta litattafan soyayya, ya ce da ni idan ya kama ni wata rana zan raina kaina. Don haka in kiyaye."
.
Fauziyya tayi shiru, ta kau da kanta daga kaina, ta sake kallon wani 6angare na katafaren falon, wata qila tana jin kunyar abin da take fada mani ne.
.
Na tambayeta a karo na farko tun fara bani labarin da tayi.
.
To shin me yasa ya tsani ki riqa karanta litattafan soyayya?"YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 10
.
.
"To shin me yasa ya tsani ki riqa karanta litattafan Hausa?
.
Ta yi saurin cewa.
.
"Oho masa. Na fada maka ni ban sani ba. Na ta6a matsa masa da tambaya na ce ya fada mani dalilin da yasa baya son in karanta litattafan hausa. Shi ne ya ce da ni wai a nan matan Hausawa suke koyon makirci da mallake miji, shi kuma ba zai amince matarsa ta mallake shi ba. Ka ji dalilin da yasa ya tsani in karanta su, wannan ce kadai hujjarsa. Ni kuwa tsakani da Allah idan nace maka zan iya daina karatun Hausa nayi qarya, sbd litattafan Hausa sun kama ni. Idan aka ce mani sabon littafi ya fito bana samun sukuni sai naje na nemo shi Kamal. Abin ya zame mani kamar masifa."
.
Na sake yin shiru ina saurarenta. Har ynx dai bata kai inda ta shiga matsalar ba, da kuma ta inda zan bi in taimaketa.
.
Fauziyya bata dube ni ba ta ci gaba da sanar da ni cewa.
.
"Kamal ina fama da wata qatuwar matsala a rayuwata. Bayan duk wadannan abubuwan da na fada maka, matsalar kuwa ita ce, duk sanda na kwanta barci in har nayi mafarkin nayi wani abu, da na farka zan ga nayi abin da gaske.
.
A cikin barcin zan tashi in je in aikata abin, sannan in dawo in sake kwantawa a gadona ba tare da na san lkcn da na aikata abin da gaske ba..."
.
Ta dan saurara sannan ta ce da ni.
.
"Yau kwana uku kenan da na kwanta sai nayi mafarkin na dauki wani littafin soyayya da na sayo a kasuwa, naje na bude motar mijina na jefa littafin a ciki. Da na tashi da safe ban ga littafin ba a inda na 6oye shi. Kuma a ranar da abin ya faru, mijina da motarsa direbansa da ya kawo shi da safe yaxo ya dauke shi suka tafi. Hakan shi ya tabbatar mani da cewar da gaske na kai littafin cikin motarsa, mafarkin da nayi gsky ne. Ynx haka littafin yana can a cikin motarsa. To abin da nake tsoro shi ne, wata qila direbansa ya ga littafin ya tambaye shi ko nasa ne, idan har mijina ya tambaye shi wanne irin littafi ne, da zaran ya fada masa littafin soyayya ne, shi kenan tawa ta qare, ba abin da zai hana shi yaxo ya sake ni.
.
Ynx haka ina jiran xuwansa ne Kamal, idan har ba a yi qoqari an je an dauke littafin daga cikin motar ba shi kenan zamana a nan gidan ya xo qarshe....sakina zai yi...."
.
Fauziyya ta fashe da kuka. Tayi saurin rufe fuskarta da siraran yatsunta don kada in ga hawayenta, xuciyata ta narke kamar yadda alewa take narkewa a cikin ruwa. Irin kukan da ta yi ne a daren jiya, sa'ar da taxo wajena ta sayi kati tayi waya. Sautin kukanta ya riqa fita a hankali yana keta xuciyata kamar yadda almakashi ke keta algarara.
.
Na tabbatar idan har ban lallasheta ta daina kukan ba xuciyata nima ba zata iya jurewa ba. Na ce da ita cikin muryar karaya.
.
"Ki yi haquri Fauziyya. Na yi maki alqawarin zan taimake ki, zan je in dauko maki littafinki a cikin motar, ki fadi mani inda motar take zan je in dauko maki littafin."
.
Tayi saurin share hawayenta da hannuwanta, sannan ta juyo ta dube ni, laimar hawayen ta dagula kyakkyawar fuskarta, wani hawayen kuma ya qirqirar mata kogi a madaidaicin kumatunta.
.
"Gidan da ya kai motar a nan kishiyata take, kuma fidan ya fi wannan tsaro nesa ba kusa ba.
.
A can akwai masu gadi dare da rana. Akwai mafadatan karnuka Kamal..
.
Ta yaya zaka iya xuwa cikin gidan ka bude ka ciro mani littafin?"
.
Nayi ajiyar xuciya, sannan nayi tunani. A qarshe na ce da ita.
.
"Ba komai zan gwada in gani Fauziyya. Ki kai ni gidan in gani, in har naga gidan zan san yadda xan yi in shiga. Kada ki damu!"
.
Fauziyya ta dube ni sosai ko qiftawa bata yi, kamar tana tsammanin na samu ta6in hankali.
.
"Ban san me zan yi maka in nuna maka godiyata ba Kamal. Idan har kayi haka ka taimaki rayuwata. Ka ceto ni daga masifar da ta same ni.
.
Ka san ita waccan matar, kishiyar tawa ba ma jituwa ni da ita. Bata qaunata.
.
Ta dade tana neman hanyar da zata raba ni da Alhaji, idan har ta samu labarin littafin a cikin motar da gayya zaya dauka ta nuna masa, tunda ta san ya hana ni karanta litattafan soyayyar.
.
Kuma shi direban Alhajin ba hannun damanta ne. Ni dashi bama jituwa, a 6angarenta yake....da yaga littafin zai tsegunta mata su dauka nunawa Alhaji su ce nawa ne. Sun samu damar da zasu rabani dashi."
.
Na ce da ita.
.
"Ki kwantar da hankalinki Fauziyya, zan taimake ki, zan je in dauko maki littafinki kafin su kaiwa mijinki ya gani."
.
Fauziyya ta ce.
.
Na gode sosai Kamal. Ynx abu na farko da zamu fara yi shi ne, mu je in kaika ka kwaso kayanka dukan su ka dawo nan gidana ka zauna. Daga nan sai mu fara tsara yadda zamu tunkari wannan matsalar.
.
"Bari in shiga in canxo kaya in kaika a mota, daga ynx ka zama dan uwana Kamal, ni da kai MUTU-KA-RABA!"
.
Ta tashi tana murmushin jin dadi.
.
Na ce da ita cikin shakka da wasi-wasi.
.
"Amma ta yaya za ayi kina matar aure kuma ki ce in kwaso kayana in dawo nan gidan ki in zauna? Mijinki kuma fa...?"
.
Tun kafin in kai qarshe Fauziyya tayi 'yar gajeriyar dariya sannan tayi mani fari da fararenidanunta ta ce da ni.
.
"Ba komai Kamal, na fada maka mijina makaho ne baya gani.
.
.
.
Lp=11
YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 11
.
.
.
Ba komai Kamal, na fadi maka mijina makaho ne baya gani, ko shekara zaka yi a nan gidan ba ganinka zai yi ba, ka kwantar da hankalinka ba abin da zai same ka."
.
Har xuciyata zata fara gargadina kada in kuskura in amince da wannan tayin da Fauziyya tayi mani, to amma fararen idanunta su suka hana ni in yi mata jayayya.
.
Na amince da duk abin da ta fadi mani, sbd xuciyata ta narke a sakamakon xunxurutun kyawunta da yake fuxgata kamar mayen qarfe da qusa.
.
.
.
BABI NA UKU
.
.
Kamar yadda na fadi maku ne tun daxu, tunda dai wannan labarin da nake bayarwa ya tattara ne kawai akan Fauziyya, babu dalilin da zai sa in tsaya 6ata lkcn sanar da ke wadansu abubuwan daban, wadanda basu shafi wannan labarin ba.
.
Don haka a cikin abin da bai fi minti talatin ba Fauziyya ta daukeni a motarta muka je sukurkutaccen dakina, ta ce dani suturuna kawai zan diba da kuma 'yan abubuwan da nake so, kada in yi wahalar daukar wasu tarkace, komai nake buqata zan same shi a gidanta.
.
Bayan na gama daukar 'yan ragowar sutturuna ne dake a dakin a yayin da Fauziyya take a waje tana jira na. Nayi wa dakin nawa kallon qarshe, sannan na fito, abin da kawai nayi kewar rabuwa dashi a dakin bai wuce dirkeken 6eran da yake hawa kaina yana sukuwa ba.
.
Na kwaso ragowar katin wayana wadanda ban sayar dasu ba, na xuba su a cikin aljihuna, na samu Fauziyya a waje tana yiwa gine-ginen dake a layin kallon hadarin kahi. Ta dawo da hankalinta a wajena da ta ji na tsaya a kusa da ita.
.
"Mu tafi Kamal?"
.
Ta tambayeni a sanyaye.
.
"Eh, mu je...na dauki duk abubuwan da nake so."
.
Muka shiga motar, ta sake tuqawa muka tafi. Sai da muka fita daga layin muka hau babban titi sannan ta ce da ni.
.
"Daga nan kamata yayi mu wuce in nuna maka daya gidan mijin nawa, inda kishiyata take....Amma daga nesa zamu tsaya bana so wani gane ni ya fahimci abin da muke ciki."
.
Na ce da ita.
.
"To Haj. Fauziyya ba matsala, muje in ga gidan domin in zan dawo anjima in san irin shirin da zan yi."
.
Fauziyya ta dan yi murmushi wanda ya qara mata fiye da kashi hamsin na kyawun da take dashi.
.
"Idan har kayi nasarar dauko mani wannan littafi, zan yi maka babbar kyauta ta musamman Kamal."
.
Ta ce da ni tana kallon motocin dake a gabanta akan titi.
.
Ban ce da ita komai ba har xuwa lkcn da ta ci gaba da cewa.
.
"nayi alqawarin zan baka sabuwar mota Kamal, sannan kuma zan baka milyan daya ka nemi babbar sana'a ka riqa yi. Zan baka gidan da zaka zauna...."
.
Duk da albishir din da tayi mani akwai dadin ji a kunne, hakan bai hana ni tsayar da ita ba ne ce.
.
"Tun farko na fadi maki ba don kudi zan yi maki wannan aikin ba Fauziyy. Ganin irin halin da kika shiga jiya a gaba na shi yasa naji na damu, ina son in ga na taimake ki kin fita daga wannan qatuwar matsala da ta same ki..."
.
Sai da ta qarawa motar guda ta wuce wata doguwar motar kamfani sannan ta ce da ni
.
"Na sani Kamal, na san ba don kudina zaka taimake ni ba, ni kaina na san kome na baka ban biyaka ba, har abada babu abin da zan yi maka in biya ka abin alherin da kayi mani, domin idan har ban fita daga wannan qangin ba, to ni ina ga rayuwata taxo qarshe, ban san inda zan sa kaina ba a wannan duniyar in samu sauqi.
.
Alh. Fataye ne gata na, shine alfaharina, da bazarshi nake yin duk wata rawa a rayuwata, ina shiga cikin matan masu kudin garin nan ana harka da ni. Idan na kuskura ya sake ni shi kenan na gama wulaqanta, gidanmu zan koma in zauna, kuma iyayena talakawa ne, gashi na saba kashe manyan kudi, in ba Alh. Fataye ba wanda zai iya daukar nauyin dawainiar kashe kudin da nake yi a halin ynx. Don haka rabuwata dashi ba qaramin hadari bane a rayuwata."
.
Ta sake 6ata ranta a wannan karon, ta take motar muka qara cillawa aguje, sauran kadan mu daki bayan motar dake gabanmu, nayi saurin rarrashinta don kada fushinta ya qaru ta jefa mu a ckin rami.
.
Ba komai Fauziyya, duk wannan matsalar taxo qarshe in Allah Ya yarda, anjima da daddare sai na dauko maki littafinki."
.
Ta dan sassauta fushin ba tare da ta juyo ta dube ni ba. Na gane haka ne da naji ta rage gudun motar, mun dawo irin tafiyar da muke tafiya tun farko hawanmu titin. Na tambayeta nima ba tare da na dubeta ba.
.
"Amma kina jin har ynx basu ga littafin ba a cikin motar? Naji kin ce tun shekaranjiya kika yi mafarkin kin kai littafin cikin motar..."
.
Tun kafin in kai qarshe Fauziyya ta ce da ni cikin qwarin guiwa.
.
"ba wanda yaga littafin a cikin su, har ynx yana can a cikin motar inda na ajiye shi. Ai da sun ganshi da ynx na shiga uku na lalace! Da tuni sun nunawa Alhaji sun fadi masa ga littafin soyayya an tsinta a cikin motarsa.
.
Na fada maka kishiyata bata da mutunci ko qanqani, tuntuni take neman hanyar da zata kore ni. Ai da ace sun ga littafin da tuni na gan shi yaxo a fusace ya tsare ni da tuhuma.
.
Akwai wani abu dake a muryarta wanda yake nuna alamar ita kanta bata da tabbacin abin da take fada. To amma tunda dai tana so ne in taimake ta, komai ma zata iya fada mani don ta qarfafa mani guiwa.
.
.
Lp=12YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 12
.
.
.
.
Akwai wani abu dake a muryarta wanda yake nuna alamar ita kanta bata da tabbacin abin da take fada. To amma tunda tana so ne in taimaketa, komai ma zata iya fada mani don dai ta qarfafa mani guiwa kada in karaya in ce na fasa in dauko mata littafin.
.
Bamu sake yin wata qwaqqwarar magana ba, har sanda ta sauke motar daga kan faffadan titin muka shiga cikin wata unguwa wacce ke da qarancin mutane gama gari dake xuwa a qasa, sai dai motoci birjik a ko'ina kamar an yi ruwan su.
.
Sai da muka kai inda wata makaranta take sannan naga ta tsayar da motar, ta xuge gilashin kowacce qofa tana kallon wani makeken gida dake a gabanmu sannan na fahimci mun xo gidan kishiyar tata, inda mijinta yake a halin ynx.
.
Fauziyya ta ce da ni a sanyaye.
.
"Kaga gidan can Kamal. Nan ne inda kishiyata Kudiratu take ita da 'ya'yanta."
.
Na mayar da hankalina akan katafaren gidan wanda shima idan aka kwatantashi da gidan Fauziyya dole ne shima a tsaya a dube shi.
.
Doguwar katangar gidan wacce aka qawatata da dunqulallun qwayayen wuta farare ba ita tafi tsorata ni ba, garadan qattin masu gadi biyun dake zaune a bakin qofar gidan kowannen su riqe da zabgegiyar bulala a hannunsa su suka kada hantar cikina.
.
Na san a halin ynx sun riqe bulalu ne sbd qananun yara dake tsinkar fulawa ne, amma idan dare yayi tabbas bindigogi zasu riqe, sbd sun san duk wanda zai xo gidan a lkcn yayi arba dasu ba qaramin yaro ba ne, kuma ba tsinkar filawa zai xo yi ba.
.
Fauziyya ta juyo ta kalle ni cikin xullumi da taga na qurawa masu gadin ido ko qyaftawa ba nayi. Ta tabbatar na karaya dasu tun ynx kafin anjima da daddare in xo muyi gaban zaki dasu.
.
Ta yi ajiyar xuciya ta ce da ni.
.
"Bayan wadannan masu gadin akwai karnukan da na baka labari daxu, kuma sai da daddare ake kwance su. Mafadatan karnuka ne bai kamata in 6oye maka komai ba Kamal.
.
Sau biyu suna kashe 6arayi har lahira a nan gidan, shi yasa da wahala ka ji an ce ga wani ya tsallaka ya shiga cikin gidan nan, akwai tsaro sosai.
.
Ba don komai kaga yafi tsaurara tsaro anan gidan ba, sai don kasancewar yawancin dukiyarsa da muhimman takardun kadarorinsa a nan suke, nan ne tsohon gidansa, amma gidana tamkar gidan hutawa ya mayar dashi, ba wata ajiya da yayi a gidan.
.
Koda yaushe yana tare da yaran sa wadanda suke kula masa da dukiyarsa, amma idan ya koma gidana to hutawarsa kawai yake yi, in dauke shi a mota muje yawo mu zaga gari. Shi yasa matarsa take jin haushina kamar ta kashe ni ta huta."
.
Fauziyya ta dan saki ranta kadan, saura kadan tayi murmushi, ga alama abin da take fada ynxn ya faranta mata rai, duk da haka bata mance da maganar da take son ta fada mani ba.
.
Tayi ajiar xuciya ta tambaye ni.
.
"To Kamal ya kake gani, zaka iya xuwa? Ka dai ga yadda gidan yake me zaka ce?"
.
Ta langa6ar da kai tana kallo na kamar yadda qaramin yaro yake roqon uwarsa ta kawar

Please Login or Register in order to submit comment