Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi ta 'yan maza na bita da sauri a lkcn da ta kusa xuwa inda zata sha kwana ta shiga dakin barcinta. Na sake shan gabanta na tsaya don in ga ko tana ganina. Idanunta a rufe suke har ynx, kamar yadda taker yi idan tana barci, bakinta ya ci gaba da motsawa tana magana a hankali tana murmushi da dan tsukakken bakinta. Na ji bayan da ta xo inda nake zata ture ni akan hanyarta.
.
Na saurara don in ji ko me ta ke cewa a cikin murmushinta. Na ji tana cewa a cikin rada.
.
"Khalil ba zai sake takura mani ba daga ynxn.....na 6atar da litattafansa, sannan shima na...."
.
Ban jira ta qarisa fadar abin da take cewa ba, na kauce na bata wuri ta wuce.
.
Ga mamakina qafafuwanta basu mance hanyar da zasu bi ba, a haka har ta nufi dakinta. Na garzaya a guje cikin fargaba da tsoro na nufi dakin da Khalil yake. Na samu dakin a bude. Tabbas Fauziyya ce ta bude ta shiga.
.
(Me ta yi a ciki)?
.
Na ci gaba da jerowa kaina tambayoyi sannan na fada cikin dakin don in ga ko a wane hali Khalil yake.
.
A lkcn da na shiga cikin dakin ne na samu dakin a haske tarwai an kunna wuta. Na samu Khalil yana a daure tamau da waya a hannuwa da qafufuwanshi kamar yadda na tafi na barshi. Banbancin kawai shi ne jiya ban bar jini yana fitowa a guje daga qirjinsa kamar an bude famfo ba. Idanunsa a bude amma basu kallon komai. Ya bude bakinsa kamar yana mamakin wani abu. Ban yarda na qara matsawa xuwa inda yake ba, sbd na tabbatar ya mutu!!
.
Babu shakka Khalil ya mutu! Kuma Haj. Fauziyya ce ta xo ta kashe shi.!!
.
.
Na juyo da sauri na koma dakina na rufe na zauna a qasa jikina yana tsuma kamar wanda ya ga fatalwa. Na runtse idanuna na mari kaina har sau biyu, ina son in mayar da abin da ya faru ya zama mafarki, kada ya zama gsky, to amma ni kaina na san ina ihu ne bayan hari.
.
.
Lp=44YARO BAI SAN WUTA BA...
.
.
Page 44
.
.
.
Na rintse idona na mari kaina har sau biyu, ina son in mayar da abin da ya faru ya zama mafarki, kada ya zama gsky. To amma ni kaina na san ihu nake yi bayan hari, duk wadannan abubuwan da suka faru, wadanda idanuna suka nuna mani gsky ne. (Tabbas Fauziyya ta kashe masoyinta Khalil).
.
Na tuno yadda na same shi a kwance, yadda na daure shi tamau da waya. A haka baya iya kare kanshi, baya iya tashi ya gudu, ta same shi a dakin yana kallonta, yana ji yana gani ta danqara masa wuqar tsakiyar qirjinsa. A haka a yadda idanunsa ke a bude yana kallonta ta kashe shi. Yana mamakin abin da ta aikata masa. Na ji hawaye sun fara xubo mani. Na girgiza kaina na daure na hana kaina kuka.
.
Wannan kisan gilla ne kuma akwai hannuna a ciki. Da ace ban taimakawa Fauziyya ba wajen tsare Khalil a gidanta tun xuwansa, da ba zata iya kama shi ta daure ba, har ta biyo dare ta kashe shi.
.
Na rabu da ita na fasa tashin ta in sanar da ita abin da yake faruwa, na yanke in koma dakina in rabu da ita har gari ya waye, idan ta tashi don kanta sai mu yi maganar.
.
Wata xuciyar ta fara raya mani cewar, me zai hana ba zan gudu in bar gidan ba a wannan lkcn, tun kafin 'yan sanda su shigo cikin wannan rigimar? Ya kamata in gudu in bar Haj. Fauziyya.
.
Zan ci gaba anjima.
YARO BAI SAN WUTA BA....
.
.
Page 37
.
.
.
Wannan kisan gilla ne kuma akwai hannuna a ciki. Da ace ban taimakawa Fauziyya wajen tsare Khalil a gidanta ba tun xuwansa, da ba zata iya kama shi ta daure ita kadai ba, balle kuma har akai ga batun kisa.
.
Tsoro da xullumi na abin da na tabbatar zai biyo baya ya buwayeni. Na kasa samun sukuni a xuciyata. Ynx idan 'yansanda suka ritsa mu da gawar Khalil me zai faru damu ni da Haj. Fauziyya? Dole ne a kama mu dumu-dumu da laifin kisan kai. Don haka ya zama dole in yi sauri in nemo mana mafita kafin tonuwar asirinmu.
.
Shin ya zan yi in je in sanarwa Haj. Fauziyya abin da ta aikata? Barci take yi bata sani ba ta taso ta kashe Khalil ta koma ta kwanta. Shin idan ta farka zata tuno wannan mafarkin da tayi? Zan bari ne sai da safen idan ta tashi barci sai in same ta in fada mata abin da ta sake aikatawa a wannan sabon mafarkin da ta sake yi. To amma ya kamata ace a cikin daren nan na tasheta daga barcin domin in fada mata halin da muke ciki.
.
Na sake tashi na nufi dakinta a tsorace ina tafiya a hankali kamar ina xullumin zan hadu da ita a hanya riqe da wuqar a hannunta ta sake dawowa. Har na shiga dakin barcinta, na sameta a kwance akan gadonta tana ta sharar barcinta. A halin ynx ba wuqar a hannunta, ban san inda ta kai ta ta 6oye ba.
.
Na dade a tsaye a bakin qofar dakin barcinta ina kallonta, ina mamakin ynx wannan kyakkyawar macen da ke a kwance tana barci ita ce ta kashe mutum a wasu 'yan mintoci da suka wuce?
.
Na rasa ta yadda zan bi in tashe ta ta fahimce ni. Idan na tashe ta a daidai wannan lkcn da nake a cikin dakin barcinta, wane kallo zata yi mani? Ba zan iya hada idanu da ita ba tana a cikin wannan yanayin sanye da kayan barcinta a cikin dakinta.
.
Na rabu da ita na fasa tashinta don sanar da ita abin dake faruwa, na yanke shawarar in koma dakina in rabu da ita har gari ya waye idan ta tashi don kanta sai muyi maganar.
.
Wata xuciyar ta fara raya mani, me zai hana ba zan gudu in bar gidan ba a wannan lkcn, tun kafin 'yan sanda su shigo cikin wannan rigimar? Ya kamata in gudu in bar Haj. Fauziyya ta san yadda zata yi da matsalarta.
.
To amma koda ace na gudu idan asirinta ya tonu nima nawa ya tonu, don kuwa duk inda na shiga za a bini a kamoni, in har ta ce nine na taimaka mata muka tsare Khalil a gidan.
.
Don haka gara ma in tsaya in taimaketa mu san yadda zamu yi da gawar shi, idan na tabbatar mun 6atar da gawar sai in gudu.
.
.
Ku motsa tunaninku da wannan xuwa jimawa, zamu dora bi'izinilLah.YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 38
.
.
.
Don haka gara ma in tsaya in taimaketa mu san yadda zamu yi da gawarshi, idan na tabbatar mun 6atar da gawarshi sai in gudu in bata wuri.
.
Na ci gaba da zama a dakina nayi tagumi. Maganganun da Khalil ya fada mani suka fara kuruwa a cikin xuciyata.
.
"Ina mai tabbatar maka da cewa wannan matar ita zata kashe ni. Kuma kaima ita ce ajalinka! Ita zata kashe ka....muguwa ce, azzaluma ce, bata da tausayi!"
.
Maganar ta ci gaba da yi mani kururuwa kamar ynxn nan yake sanar da ni. Khalil ya tabbatar mani cewar Fauziyya ce ajalinsa, ita zata kashe shi, gashi kuma maganarshi ta zama gsky ta kashe shi. Sannan ya ce nima ita ce ajalina, shin da gaske nima ita zata kashe ni kamar yadda ya tabbatar mani?
.
Idan har abin da ya fada gsky ne, to tabbas bata da tausayi, a wanne dalili zata kashe ni? Bayan duk taimakon da nayi mata wajen cimma burinta, daga baya kuma ta kashe ni?
.
Wannan wani abu ne mai wahala wanda ba zan ta6a amincewa dashi ba, sbd babu wani rashin jituwa a tsakanina da ita. Babu laifin da nayi mata.
.
To amma tunda dai a mafarki take tasowa ta kashe mutum ta koma daki ta sake kwanciya, wata qila Khalil ya san tana fama da wannan matsalar shi yasa ya ce nima ita zata kashe ni in har na ci gaba da zama a gidan.
.
Na ci gaba da tunane-tunane, ina kwance in saqa wannan in kwance in saqa wancan. Har aka kira sallar asubahi, na tashi da sauri naje ban daki, na bude famfo nayi alwala na yi saurin fita domin xuwa masallaci.
.
Bayan an yi sallah ban fito daga masallacin ba sai da naga hasken gari ya fara wayewa, sannan na fito na koma gidan Haj. Fauziyya. Da na shiga ne sai naji tsoron da yake damuna ya fara raguwa, domin ko babu komai ynx gari ya waye. Duk abin da za a yi da rana ido na ganin ido zai fi na dare.
.
Na samu Fauziyya a babban falo tana zaune tana kwalliya, ta riqe qaramin madubi a hannunta tana zana gazar a girarta. Da shigana ta dago kai ta kalle ni tana murmushi. Ta yi kyau sosai, amma abin da ta aikata a cikin daren ba zai bari in ga kyawunta ba.
.
"Ashe kana masallachi tun daxun?"
.
Ta ce da ni ba wani alamun tsoro a muryarta. Hakan shi ya qara tabbatar mani da cewar lallai bata san abin da ya faru ba. To amma a yadda ta bani labarin ciwonta, ta ce duk abin da tayi a cikin mafarkinta idan ta farka tana sani, to me yasa ynx bata ga aika-aikar da tayi a wannan mafarkin na jiya ba?"
.
Fauziyya da ta ga na tsaya sororo ina kallonta na kasa qarisawa kusa da ita, sai ta tambaye ni.
.
"Ya naga ka tsaya daga baya? Ka zauna mana ina son dama zamu yi magana, kwalliya nake yi ba wani abu zan sake yi ba."
.
Ta kalli jikinta, ta sake tabbatarwa kanta bata yi wata iriyar shigar da zai sa in ji nauyin xuwa kusa da ita ba.
.
Na qarisa cikin falon jikina a sanyaye, na zauna nesa kadan kusa da ita, xuciyata na bugawa da sauri da na tuna da gawar Khalil dake a cikin gidan.
.
Fauziyya ta ajiye madubi da gazar din, ta dube ni qamshin jikinta yana yi wa hancina barka da shigowa.
.
Ta kada idanunta farare sannan ta ce da ni.
.
"Ina ganin zan dauki shawar da ka bani jiya domin mu huta da wannan rigimar, haka nan zan rabu da mijina in auri Khalil! Ynx kamata yayi ka je ka kwance shi ya xo muyi maganar, sbd mu sasanta mu yafewa juna."
.
Ta bi ni da kallo tana sauraren abin da zan ce. Qwaqwalwata tayi zafi sosai, domin kuwa ban san inda al'amarin ya dosa ba.
.
Shin Fauziyya tana nufin bata san abin da ya faru ba tsakanin ta da Khalil? Idan bata sani ba ta wacce hanya zan bi in sanar da ita har ta fahimce ni....?
.
"Kamal tunanin me take yi ne haka naga kayi shiru, ko har ka fara gajiya da taimakon nawa ne?"
.
Ta katse mani tunanina da muryarta wacce take karkarwa. Na san halinta da saurin kuka. Na kawar da tunanin da nake yi, na mayar da hankalina akanta, a lkcn da ita ma ta qura mani idanu ba ko qiftawa.
.
Nayi ajiyar xuciya sannan na tambayeta a cikin karaya.
.
.
MU SHA RUWA LFY.YARO BAI SAN WUTA BA....
.
.
Page 40
.
.
Ina ganin zan dauki shawarar da ka bani jiya domin mu huta da wannan rigimar hakan nan. Zan rabu da mijina in auri Khalil! Ynx kamata yayi ka je ka kunce shi ya xo muyi maganar, sbd mu sasanta mu yafewa juna."
.
Ta bi ni da kallo tana sauraren abin da zan ce. Qwaqwalwata tayi zafi sosai, domin kuwa ban san inda wannan al'amarin ya dosa ba.
.
Shin Fauziyya tana nufin bata san abin da ya faru ba a tsakaninta da Khalil? Idan har bata sani ba, ta wacce hanya zan bi in sanar da ita ta fahimce ni?....
.
"Kamal tunanin me kake yi ne haka naga kayi shiru? Ko har ka fara gajiya da taimakona ne?"
.
Ta katse mani tunanina da muryarta wacce ke karkarwa. Na san halinta da saurin kuka. Na kawar da tunanin da nake yi na mayar da hankalina akanta, a lkcn da itama ta qura mani ido.
.
Nayi ajiyar xuciya sannan na tambayeta cikin karaya.
.
"Fauziyya baki san abin da ya faru bane a gidan nan a daren da ya gabata?"
.
Ta ci gaba da kallona da fuskar katako..
.
"Wanne abu ne ya faru a nan gidan Kamal? Don Allah me ya faru?"
.
Ta tambayeni muryarta cike da tsoro. Shirun da nayi ban ce da ita komai ba, ya sa ta kasa haquri ta daka mani tsawa.
.
"me ya faru Kamal? Me yasa ka ke bani tsoro? Ka yi mani magana mana, me ke faruwa?"
.
A yadda ta rude a cikin dan lkc qanqani, idanunta suka canza kamanni na tabbata a cikin abu biyu dole ne a samu daya, ko dai da gaske take yi bata san abin da ya faru ba, in kuwa har ta san abin da ya faru to tafi ko wacce mace iya makirci a duniya.
.
Na yanke shawarar an fada mata abin da ya faru kai tsaye. To amma a yadda ta rude da wahala qwaqwalwarta ta iya daukar wannan sabon tashin hankalin in har bata san abin da ya faru ba. Don haka ynx na yanke shawarar zan fada mata labarin mutuwar Khalil. Amma ba zan fada mata cewar ita ta kashe shi ba.!
.
"Bamu da buqatar sake yin magana da Khalil."
.
Na ce da ita kai tsaye.
.
"Sbd Khalil ya mutu a daren jiya!
.
Na kalli fuskarta naga wani abu mai kama da walqiya ya gifta, ta bude bakinta cikin firgici da rudani ta kasa yi mani magana, wanda hakan ne ya ganar da ni cewar tayi suman tsaye ne. Don haka ya rage nawa in san hanyar da zan bi in shawo kanta in bata haquri, in kuwa ba haka ba to lallai zata yanke jiki ta fadi wata sabuwar gawar ta sake samuwa.
.
"Kwanansa ya riga ya qare ba yadda zamu iya Fauziyya, sai dai muyi haquri mu nemo hanyar da zamu bi mu rabu da gawarsa ba tare da kowa ya san abin da ya faru ba."
.
Ta farfado a lkc guda tare da fashewa da kuka.
.
"Ya aka yi ya mutu Kamal? Me ya kashe shi?"
.
Ta tambaye ni jikinta yana tsima kamar wacce ta kwana a cikin qanqara.
.
Na sake yin ajiyar xuciya, na tabbatar idan nace ita ce ta tashi da daddare ta kashe shi da wuqa, da wahala idan jininta bai hau sama ba.
.
Na ce da ita.
.
"Nima kaina ban san abin da ya kashe shi ba. Na leqa dakin ne na same shi ya mutu!"
.
Ta fara rusa kuka tana cewa.
.
"Mu muka kashe shi Kamal! Da ace bamu daure shi ba abin da zai same shi."
.
Fauziyya ta dafe qirjinta kamar tana tsoro xuciyarta zata faso ta fado waje.
.
Ta ci gaba da rusa kuka tana cewa.
.
"Mu muka kashe shi Kamal. Mu je na gan shi!"
.
Ta tashi a kidime hawaye na xubowa daga cikin idanunta kamar ruwa."
.
Na girgiza kaina na ce da ita.
.
"Ki yi haquri ba sai kin ganshi ba, ki yafe masa duk abubuwan da suka faru a tsakaninki dashi, sannan ki yi masa addu'a."
.
Fauziyya ta koma ta zauna akan kujera ta kifa kanta akan cinyoyin ta ta ci gaba da rusa kuka kamar ranta zai fita. Nayi mamakin yadda ta rikirkice akan mutuwar Khalil. Da na tuno irin rashin jituwar dake a tsakaninta dashi. To amma kuma idan na tuna cewar kafin rashin jituwar ya shiga tsakaninsu masoya ne, don haka cikin kuskure komai ya faru. Tabbas a baya Khalil ya nuna mata soyayya mai yawa a baya.
.
Na dade ina bata haquri a cikin falon, ina ta faman rarrashinta, amma bata daina kukan ba, sai da ta gaji, kanta ya fara ciwo, sannan ta ta saurara ta ciro kanta ta kalle ni, idanunta sun koma jajaye, fuskarta ta jagule, ban tsammaci ko mijinta ne ya rasu zata yi irin wannan uban kukan ba.
.
Muka dauki lkc a zaune muna tunani. Ni ina tunanin yadda zamu yi da gawar. Ita kuma ban san irin tunanin da take yi ba, ta yi shiru.
.
.
Daga baya ne tayi ajiyar xuciya, ta jingina da jikin kujerar tayi tagumi ta ce da ni.
.
"Da ace tun farko na san haka abin zai kasance da tun farko ban yaudari Khalil ba. Da ace na aure shi da ynx muna nan muna soyayya dashi. A rayuwata ba zan ta6a samun masoyi irin Khalil ba....."
.
Ta sake fashewa da wani kukan. Na ci gaba da bata haquri kamar yadda uwa take rarrashin shashan dan autan dan ta.
.
Bamu karya ba har rana ta daga. Fauziyya tana aikin kuka, ni kuma ina aikin bata haquri. Ta ci gaba da fada mani maganganu wadanda karatu ne da ynx na haddace. Wato Labarin soyayyarta da Khalil.
.
"Khalil ba wani mai kudi bane amma haka nan yake iya qoqarin sa wajen ganin yayi mata abin da zata yaba.
.
Ko tafiya Khalil yayi idan sun dade basu hadu ba, sai ya fara biyowa ta wajen ta idan ya dawo.
.
.
Lp=41YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
.
Page 41
.
.
.
Ko tafiya Khalil yayi idan sun dade basu hadu ba, sai ya gara biyowa ta wajenta idan ya dawo.
.
Khalil ga mutunci, yana son 'yan uwanta. Ba ma iyayenta kadai ba, har kakanninta sun san Khalil, sbd yadda yake son ta yake kulawa da ita.
.
Ta ci gaba da magana, ina zaune ina saurarenta kamar tana fada mani tatsuniya.
.
Bayan ta gama nace a xuciyata.
.
"Kina sane da irin son da yake yi maki, matsalarsa kawai bashi da kudin da zai iya riqe ki."
.
Amma a zahiri sai na ce da ita.
.
"Ynx ba wannan maganar zamu tsaya yi ba Fauziyya, kamata yayi mu hanzarta rabuwa da gawarsa. Idan 'yan sanda suka san abin dake faruwa, ni da ke duka hukuncin kisa za a yanke mana a kotu. Don haka muyi qoqari mu nemo mafita tun kafin asirinmu ya tonu."
.
Ta sake kollona a tsorace. Na tabbata a wannan karon babu sauran gudunmawar da zata iya bayarwa wajen ganin mun fita daga wannan matsalar. Hawaye ya ziraro daga cikin idontas guda daya. Bata san ma ya xiraro ba, ta bar shi ya xirara har qasan wuyanta.
.
Ta tambaye ni.
.
"To ya zamu yi Kamal? Zamu nemo mutane ne su xo a kai shi maqabarta ko kuwa?"
.
Na numfasa da na lura 6ata lkcna nake yi a banza wajen tambayarta yadda zamu yi da gawar Khalil.
.
A qarshe sai na ce da ita.
.
"Ki shiga daki ki kwanta ki huta. Bani mabudin motarki, ni na san abin da ya kamata in yi, ki bar komai a hannu na."
.
Ta nuna mani inda ta ajiye mabudin motar akan wani kofin ado na gwal dake fuskantarmu. Na tashi naje na dauki mabudin motar, tana zaune jangwam! Ta kasa motsawa akan kujerar.
.
Na sake cewa da ita.
.
"Ki shiga daki ki bani wuri, zan yi wani aiki ne ynxn nan."
.
Ta dube ni cikin rashin fahimtar abin da nake nufi. Har zata tambaye ni sai kuma naga ta fasa, ta tashi, daqyar qafafuwanta suka iya daukarta. Ta nufi dakinta jikinta a sanyaye kamar kazar da ruwa ya jiqa ta. Nayi saurin ficewa daga falon na nufi dakin da gawar Khalil take.
.
Ba qaramin qoqari nayi ba wajen sake komawa inda gawar take. To amma na san in har na biyewa Haj. Fauziyya muka kasa ta6uka komai wajen kawar da gawar daga gidan mu zamu kwana a ciki. Tunda dai dole ne a xo a same mu da mataccen mutum, wanda kuma kashe shi aka yi.
.
Da na shiga dakin ne na duqa na fara kunce daurin da nayiwa Khalil da wayar. Na tuno lkcn da yake kallona a sanda nake daure shi. Naji hawaye nima ya xubo min, domin kuwa ni na daure shi har Fauziyya ta xo ta ritsa shi a dakin ta kashe shi a sakamakon ciwonta na mafarki da ya sake tashi.
.
Bayan na kwance shi ne na fara tunanin inda ya kamata in kai shi. A tunani daya na yanke hukuncin inda ya kamata in kai shi. Bakin teku zan kai shi in jefa shi a ruwa, in kuwa ba can ba to lallai babu inda zan iya kai shi ba tare da asirina ya tonu ba. Na fara neman abin da zan lulli6e gawar dashi. Babu komai a dakin sai daddumar dake a malale a tsakar dakin, na tashi naje dakina da Fauziyya ta saku ni, na dauko daya daga cikin mayafan dake kan faffadan gadon, na koma dakin da gawar Khalil take nayi saurin lulli6e ta da mayafin. Idan bana ganin fuskarsa zan fi sakin jikina in dauke shi in kai shi cikin motar Fauziyya dake a waje. Amma in har ina kallonsa, babu abin da zan iya yi da ya wuce in zauna in yi ta shar6ar kuka nima. Domin kuwa har abada ba zan ta6a manta maganganun da Khalil ya yi mani ba, da irin dukan da nayi masa yana kuka ba, don kawai in cika umarnin Fauziyya.
.
Na nannade gawar a cikin mayafi na dauke shi a kafadata na fita dashi. Babu kowa a gidan, daga ni sai Fauziyya, amma duk da haka da na fito farfajiyar gidan sai da na tsaya na duba ko'ina, na tabbatar bamu da wani baqo. Na ajiye gawar nayi saurin xuwa na bude motar Fauziyya na shiga ciki na tayar da ita na tuqa nayi ribas sannan na fito na bude motar.
.
Tsuntsayen dake ta shawagi a gidan suna zagaye kwatamin wankan dake a faffadan garden din gidan, wasu kuma sun sauka akan wata gajeruwar fulawa mai reshika sun xubo mani idanu, suna koke-koke kamar sun san abin dake faruwa a gidan. A yayin da giza-gizai ke ta kaiwa suna komowa a sararin samaniya suka ci gaba da zirga-zirga wadansu kuma suna toshe hasken rana daga lkc xuwa lkc.
.
Na sake kinkimo gawar da kyar ina nishi, na sakata a bayan motar, nayi saurin rufe but din, wanda hakan ya tsorata tsuntsayen dake kallona a can nesa, suka tashi firgigit suna qorafi a cikin yaren su mai wahalar ganewa. Duk da haka basu bar gidan ba, suka koma sama inda suke da ofix akan rufin gine-ginen dake a cikin gidan.
.
Na shiga motar na tuqa na tafi. Nayi hon sau biyu kamar yadda naga Fauziyya tana yi idan ta xo fita. Daya daga cikin matasan dake zama a wajen gidan ya bude mani qofa na fita. Shi da abokansa suka dago mani hannu cikin girmamawa, a tunaninsu Fauziyya ce ta fita, to amma kuma ba ita ba ce, ko ma dai ba haka bam duk wanda zai fito a cikin sullu6e6iyar mota irin tata to da wahala ya yi nisa ba tare da an rusina an gaishe shi ba ko da kuwa ba motarsa ba ce.
.
Na tafi a tsanake ban yi gudu ba. Na hadu da jmi'an tsaro kashi-kashi a hanya.
.
.
Lp=42
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography

Please Login or Register in order to submit comment