Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ake yaqi ta shiga cikin gawawwakin da aka karkashe aka xube su fululu a qasa, indai zata dade a cikinsu ba abin mamaki bane a samu wadanda zasu farfado su dago kansu su bita da kallo....wata qila sai bayan ta tafi sannan su sake kwantawa su kuma mutuwa.
.
Ban san lkcn da tayi mani magana ba, na dai ji sassanyar muryarta wacce ta fi kowacce iriyar sarewa dadin saurare koda kuwa a birnin Hindu ne.
.
"Kati nake so.... Kana da (MTN)) na dubu daya da dari biyar?"
.
Muryarta ce ta narkar da xuciyata na dawo ga hayyacina kamar yadda qanqara ke narkewa idan rana ta hau kanta. Na fara laluben jakar da nake sa katin, don kuwa ganin Fauziyya yasa na manta inda na sa ta. A qarshe na bankadota na zaro babban katin da ta tambayeni na miqa mata cikin girmamawa. A lkcn ne naga ta ciro jakarta ta bude ta dauko wayarta. Hakan shi ya ganar da ni cewar ta matsu da tayi maganar, wayarta kuma babu kudi.
.
Ganin haka yasa na dakata ban bata katin ba, na sa farce na kankare mata lambobin suka fito, ta tsaya tana jirana a cikin qosawa.
.
A dan taqaitaccen lkcn ne na shaqi qamshin jikinta, ban san ko qamshin me take yi ba, irin qamshin da mutum zai shaqa ne ya ji haka kawai yana tausayin kanshi.
.
Bayan na kankare katin sai na dago kai na ce da ita.
.
"kawo wayar na sa maki."
.
Ta miqo mani ba tare da tayi mani gdy ba. Na amshi dalleliyar wayar nayi amfani da haskenta a wajen shigar da katin, babu wuta kuma duk da masu injinan dake tayar da injina sun kulle sun tafi gida. Amma da yake motoci suna ta kaiwa da komowa, hakan shi yake taimakawa wajen rage kaifin duhun daren.
.
Na shigar mata da kudin na miqa mata wayar, ta ciro kudina dubu daya da dari biyar ta miqo mani.
.
Nayi zaton zata shiga motar ta ne ta tafi tayi wayarta a hanya, maimakon haka sai naga tayi hanzarin nemo wata lamba ta kira ta dora wayar a kunneNayi zaton zata shiga motar ta ne ta tafi tayi wayarta a hanya, maimakon haka sai naga tayi hanzarin nemo wata lamba ta kira ta dora wayar a kunnenta.
.
Na matsa baya na bata wuri don tayi wayarta a natse. Ta dora jakarta akan teburina, wacce ban san ko me ke a cikinta ba.
.
Duk da na matsa baya na zauna a daya daga cikin kujeruna na roba. Ina iya jin maganar da kyakkyawar matar take yi a wayar.
.
Naji ta ce cikin damuwa.
.
"Khalil...me yasa za ka yi mani haka? Don Allah ka rufa mani asiri ka taimakeni ka daina bugasu haka nan. Na ce ka xo ka same ko nawa ne zan biya ka qona su..."
.
Tayi shiru tana sauraren wata magana da ake fada mata a wayar. Xuwa can ta ci gaba. A wannan karon muryarta har karkarwa take yi, wanda hakan yasa na fahimci kuka take yi.
.
Ta ce a sanyaye.
.
"Ka ci amana ta Khalil. Baka kyauta mani ba, amma ba komai, ka yiwa kanka!"
.
Naga ta sa ha6ar gyalenta ta share hawayen fuskarta.
.
Wata mota taxo ta wuce ta haskemu ni da ita. Na kai ganina xuwa kyakkywar fuskarta, na hango qyallin hawayen da yake cin gudu akan fuskarta wanda bata samu nasarar share su ba a wannan karon.
.
Naji na damu sosai, xuciyata ta motsa. Ga dai kyakkyawar mace da kyakkyawar mota da rufin asiri, amma taxo tana waya tana kuka a titi sbd wani tashin hankali da ya same ta.
.
Naji kamar in matsa kusa in tambayeta wanene wannan Khalil din da take roqonsa ya fitar da ita daga qangin da ta shiga?
.
Naji na matsu in taimaketa, to amma ta yaya hakakawai don tsabar shiga sharu ba shanu zan shiga cikin rayuwarta ba ta san dani ba, daga kawai ta tsaya tana waya a wajen sana'a ta?
.
Don haka sai na zauna kawai nayi tagumi ina sauraren kukanta.
.
Ba kowa a wajen, daga ni sai ita. A can nesa damu akwai wasu yara da suka kasa biredi a teburi, to amma ba zasu iya ganin me ke faruwa a wajen ba.
.
.
Lp=5
.
"YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 5
.
.
"Ka ci amanata Khalil. Baka kyauta mani ba, amma ba komai, ka yiwa kanka.".
.
Naga tasa ha6ar gyalenta ta share hawayen fuskarta.
.
Wata mota taxo ta wuce mu ta haskemu ni da ita. Na kai ganina xuwa kyakkyawar fuskarta na hango qyallin hawayen da yake cin gudu akan fuskarta wanda bata samu nasarar sharewa ba a wannan karon.
.
Naji na damu sosai, xuciyata ta motsa. Ga dai kyakkyawar mace da babbar mota da rufin asiri, amma taxo tana waya tana kuka a titi sbd wani tashin hankali da ya dameta.
.
Naji kamar in matsa kusa da ita in tambayeta wane ne wannan Khalil da take roqonsa ya taimaketa ya fitar da ita daga wani qangi da ta shiga?
.
Naji na matsu in taimaketa. To amma ta yaya haka kawai don tsabar shiga sharu ba shanu zan shiga cikin rayuwarta bata san da ni ba, daga kawai ta tsaya tana waya a wajen sana'ata?
.
Don haka sai nayi tagumi na zauna ina ta sauraren kukanta.
.
Ba kowa a wajen daga ni sai ita. A can nesa da ni akwai wasu yara da suka kasa biredi a teburi, to amma ba za su iya sanin me yake faruwa a wajen ba.
.
Ni dai abin da ya faru a gabana ni kadai zan iya bayar da labari, na san in ba domin a gabana wannan kyakkyawar mace take yin wannan kukan ba tana waya, wani idan ya ganta ta wuce a mota, zai iya rantsewa tunda take bata ta6ayin kuka ba a rayuwarta sbd jin dadin duniya.
.
Na zauna ina saurarenta, ta dade tana kuka tana riqe da waya a kunnenta. Ban sa me take saurare ba. Bayan wani lkc sai naga ta cire wayar a kunnenta.
.
Ta jingina a motarta ta juyo mani baya tana tunani.
.
Hakan shi ya sanar da ni hankalinta ya tashi sosai, ta damu har ma ta mance tana tare da ni a wajen. Ta mance ina zaune ina saurarenta.
.
A wannan sana'a tawa da nake yi ta sayar da katin waya, na dade ina ganin mutanen da suke xuwa suna yin waya a wannan wajen nawa.
.
Wasu sukan xo suyi ta magana a fusace suna zage-zage.
.
Wasu kuma akan fada musu wani abu da zai sa ma su fita a hayyacin su, suyi ta banbami, to amma babu wanda ya ta6a xuwa yayi wani abu wanda naji ya motsa xuciyata kamar wannan kukan da kyakkyawar matashiyar keyi. Mun dade a haka, ban ce mata komai ba, ita ma bata juyo ba, ta ci gaba da tunanin da take Wasu kuma akan fada musu wani abu da zai sa ma su fita a hayyacin su, suyi ta banbami, to amma babu wanda ya ta6a xuwa yayi wani abu wanda naji ya motsa xuciyata kamar wannan kukan da kyakkyawar matashiyar keyi. Mun dade a haka, ban ce mata komai ba, ita ma bata juyo ba, ta ci gaba da tunanin da take yi.
.
Xuwa can kuma sai naga kamar an soketa da allura tayi xumbur a fusace ta bude motarta ta shiga ta tayar ta bata wuta, ta fuxgeta a fusace. Sai a lkcn nima na dawo hayyacina na miqe tsaye, da naga zata tafi.
.
Bayan motar ta fara tafiya ne, na lura da jakarta da ta mance akan teburina. Nayi saurin daga hannuna na fara qwala mata kira.
.
"Hajiya....ga jakarki kin mance...ki tsaya ki..."
.
Na saurara sbd na sani 6atawa kaina lkc nake yi ta riga tayi nisa ba zata ji ni ba. Na hango danjar motar a nesa...akan titin tana dau! dau? a cikin ayarin motacin dake xirga-zirga suna kaiwa da komowa.
.
Na tsaya a wajen ni kadai a cikin daren kamar an dasa ni. Sai alkcn na fahimci cewar duk da sanyin da ake yi a garin, xufa ce ke qoqarin ketowa a bayan rigata.
.
.
**.....**.....**
.
.
Sai daga baya tunani na ya dawo dai-dai, qawaqwalwata ta ci gaba da aiki. Na tsaya ina kllon jakar da matar ta mance akan teburina.
.
"Me ya kamata in yi da wannan jakar?"
.
Tambayar da na fara yiwa kaina kenan a karo na farko. Shin zata dawo ta dauki jakarta idan ta fahimci ta barta a wajena? Ko kuwa tafiya zan yi da ita gida in yaso washe gari sai taxo ta dauki abarta? Na zauna akan kujera na sake yin tagumi na xubawa jakar idanu. Ba jakar tafi damuna ba a halin ynxn, kukan da matar tayi shi yafi komai tayar mani da hankali. Ban santa ba, kuma ban ta6a ganinta ba, ban san a inda take ba a wannan birni na Ikko. Amma haka kawai naji ina son in taimaketa.
.
Bayan wani lkc da na tabbatar ba zata dawo ba, sai na yanke shawarar tafiya da jakar can dakina. A can ne zan tantance abin da ya kamata in yi. Shin binta gida zan yi in kai mata jakarta? To amma ai ban san inda take ba....da na tabbatar kome zan zartas ba zan samu mafita ba, sai na haqura na tashi na fara hada tarkacena na sana'a.
.
Na hada kujerun waje guda, na saka daya a cikin 'yar uwarta, na daukesu da hannu daya na kaisu saman wani shago inda nake 6oye su kafin gari ya waye. Na dawo na sake daukar laimar na nannadeta, na dauke jakar matar na ajiye a qasa, na dauke teburin na kai shi inda nake 6oye kujeruNa hada kujerun waje guda, na saka daya a cikin 'yar uwarta, na daukesu da hannu daya na kaisu saman wani shago inda nake 6oye su kafin gari ya waye. Na dawo na sake daukar laimar na nannadeta, na dauke jakar matar na ajiye a qasa, na dauke teburin na kai shi inda nake 6oye kujerun.
.
Na dawo na dauki laimar da jakar na kama hanya na tafi makwancina. Dakin da nake zaune bashi da nisa da wajen sana'ata.
YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 6
.
.
.
Dakin da nake kwana bashi da nisa da wajen sana'ata. Bana tsayawa neman abin hawa, wato a qasa nake xuwa kullum, kuma a qasa nake komawa.
.
A wannan karon ban yi sauri ba, ba kamar yadda nake komawa ba. Kada ku tambyeni dalili, sbd ko ban fada maku ba kun san duk guiwoyina sun yi sanyi.
.
A haka na isa dakin nawa, wanda yake a qasan wani gida da ba a kammala gina shi ba, akwai kayayyakin gini a warwatse a wajen. Na ciro mabudi na bude kwadon qofar na tura ta bude.
.
Akwai wuta a layinmu kuma da yake a kowanne lkc qwan dakina a kunne yake da shigata na ci karo da dirkeken 6eran da yake taya ni kwana ya fito tsakar dakin yana ta gadarsa ganin bana nan.
.
Da jin motsina yayi tsalle ya fada qarqashin wani akwatu wanda naxo na same shi a dakin.
.
Da ace hankalina a kwance yake ba zan qyale wannan taqadarin 6eran ba, dole ne muyi artabu ko razana shi ne in yi.
.
Na dade ina fakon shi har ynx ban samu sa'arshi ba.
.
Koda yake in banda ta'adin da yake yi mani a dakin yana gwaguyar mani tsohuwar katifar tawa da ba zan damu ba, tunda ko ba komai shi ne abokin kwana na tun sanda abokan kwana na mutane biyun suka koma garuruwan Koda yake in banda ta'adin da yake yi mani a dakin yana gwaguyar mani tsohuwar katifar tawa da ba zan damu ba, tunda ko ba komai shi ne abokin kwana na tun sanda abokan kwana na mutane biyun suka koma garuruwan su.
.
Da shigata dakin na kulle qofar, na zauna dirshan na sake dawo da tunanina kan wannan qarama jaka da matar ta mance a wajen sana'a ta.
.
Na tasa jakar a gabana ina tunanin abin da ya kamata in yi tsakanin bude ta ko kuma sa6anin haka.
.
A qarshe na yanke shawarar in budeta in ga abin da yake ciki, ban sani ba wata qila in ga wani abu wanda zai sa in gane inda matar take in je in kai mata kayanta idan ba zata xo ba.
.
Na sa hannu na xuge xif din jakar, wacce ke kama da sa6ar maciji, amma ba baqa ba ce.
.
Na bude na leqa naga abubuwan dake ciki.
.
Ba wasu kayayyaki masu yawa, cek din banki ne da kuma wata hadaddiyar hoda mai tsada, sai audugar share xufa.
.
Na sa hannu na fito dasu waje na sake leqawa cikin qaramar jakar.
.
Ba sauran wani abu sai dan qaramin katin adireshi wanda yake dunqule bandir guda bata cire ko guda daya ba.
.
Na yi saurin ciro shi don kuwa in har akwai abin da zai taimakeni a cikin jakar in gano ko wannan kyakkyawar mace wacece kuma a ina take, to bai wuce wannan kati na adireshi ba.
.
Da na ciro shi ne nayi nazarin rubutun dake a jikinsa, wanda aka yi su sirara da kuma kololi daban daban kamar haka.
.
ALH. MUHSEEN FATAYE
no; 53 Independence way
Victoria Island Lagos
.
Na sake karanta katin adireshin a karo na biyu, sannan na girgiza kaina, sbd na san sunan hamshaqin mutumin da naga an rubuta a jikin katin, kenan shi ne mijin wannan matar wacce take da wannan Na sake karanta katin adireshin a karo na biyu, sannan na girgiza kaina, sbd na san sunan hamshaqin mutumin da naga an rubuta a jikin katin, kenan shi ne mijin wannan matar wacce take da wannan jakar.
.
Na tattara duk kayayyakin da na ciro daga ciki na mayar mata dasu a cikin jakarta.
.
Inda take ba 6oyayyen waje bane a Ikko, sashin manyan masu kudi ne da kuma manyan ma'aikatan dake riqe da madafun iko na Jiha da na Tarayya.
.
Na rufe mata jakarta kamar yadda na same ta na kaita jikin bango na jingineta kafin in san abin da zan yi gobe.
.
Na kashe wutar dakin na kwanta barci kan dan abin da taqadarin 6eran ya ci ya rage na daga katifar tawa wacce itama a dakin na sam ta lkcn da abokan kwana na suka bani matsugunni a dakin.
.
Da na kwanta barci ne naji tunanin kyakkyawar matar ya buwayi xuciyata....a haka har barci ya kwashe ni.
.
A cikin barcin ne nayi mafarki ta shigo dakina ta zauna a kusa da inda nake kwance tana kallona tana kuka tana cewa.
.
"ka taimake ni Kamal....ka taimakeni ka fitar da ni daga wannan qangin rayuwa da na tsinci kaina a ciki...."
.
Na tashi a tsorace na zauna ina mayar da numfashina.
.
Babu wani motsi a dakin sai bugun xuciyata da kuma kusur-kusur din taqadarin 6eran da yake taunar wani abu, wanda ya saurara da ya ji na tashi.
.
Har garin Allah ya waye ban sake runtsawa ba.
.
.
.
BIYU
.
.
IDAN ZAKU IYA TUNA WA tun a farko na fada maku in ba domin wannan mace da nake son in baku labarinta ba da wannan littafin ma bai wanxu ba a duniyIDAN ZAKU IYA TUNA WA tun a farko na fada maku in ba domin wannan mace da nake son in baku labarinta ba da wannan littafin ma bai wanxu ba a duniya.
.
To idan haka ne a wanne dalili zan tsaya ina ta 6ata maku lkc da wasu qananun al'amura wadanda basu bane dalilin labarin?
.
Bari in yi tsalle duk in wuce komai in je kan abubuwan da suka faru a tsakanina da Fauziyya tun farkon haduwarmu wacce ban san me ya kamata in kira ta ba tsakanin TSAUTSAYI ko KADDABari in yi tsalle duk in wuce komai in je kan abubuwan da suka faru a tsakanina da Fauziyya tun farkon haduwarmu wacce ban san me ya kamata in kira ta ba tsakanin TSAUTSAYI ko KADDARA.
.
To ko ma dai me na kira wannan haduwar tamu tsakanin wadannan abubuwan biyu, ban yi kukure ba. Na tabbatar zaku yarda idan kuka yi juriyar bin wannan labari nawa sannu a hankali har xuwa babin qarshe.
.
Da gari ya waye ne naji xuciyata ta kasa samun sukunin yin komai, naji na qosa in je gidan wannan hamshaqiyar kyakkyawar mace don in kai mata jakarta...koda yake wa zan yaudara? Ba don in kai mata jakarta kadai yasa na qosa in sake ganinta ba.
.
Tun a ganin da nayi mata daren jiya, tun sanda ta juya mani baya tana rusa kuka, sa'ar da ta jingina da motarta tun a sannan naji wani abu da ban san ko menene ba naji yana fuxgar xuciyata xuwa gare ta, kamar yadda mayen qarfe yake jawo qusa a jikin kwano.
.
.
Lp=7YARO BAI SAN WUTA BA....
.
Page 7
.
.
.
Tun sannan naji wani abu da ban san ko menene ba naji yana fuxgar xuciyata xuwa gareta tamkar yadda mayen qarfe yake jawo qusa a cikin kwano.
.
Na kasa tsayawa in karya kumallo. Haka kawai naji ina xumudin xuwa inda take. Kukan da taxo tana yi a wajen sana'ata yasa naji tausayinta ya kamatni. Na san xuciyata ba zata ta6a samun sukuni ba idan har ban taimaki rayuwar wannan kyayyawar ba. Haka kawai naji bai kamata ace kyakkyawar mace irinta tana kuka a duniya ba. Don haka kome zan yi in taimaki rayuwarta ta daina kuka, to zan yi shi ko wane irin hali zan jefa rayuwata a ciki.
.
Wata qila wannan shi ne babban kuskuren da na fara yi a rayuwata. To amma tunda na riga na fada tsundum wajen kai kaina inda take kome zai biyo baya ya rage nawa a halin ynxn. Don haka tun da sassafe na fito dauke da jakar a hannuna na fita bakin titi, ina sanye da kayana na jiya, na tare mota na shiga na nufi babbar unguwar da gidanta yake, ko kuma gidan mijinta kamar yadda na gani a rubuce jikin katin adireshin dake cikin jakar.
.
Ban sha wahala wajen gane katafaren gidan ba, a cikin hadaddiyar unguwar wacce ke cike da tsaro a ko'ina.
.
Tun daga wajen gidan na hango wasu gabza-gabzan haruffa guda biyu a sama, suna ta sheqi a cikin tattausan hasken ranar da ya tarwatsa gajimaren safiyar. Duk da yake an yiwa haruffan launi mai qayatarwa a tsayuwarsu hakan bai hana ni gane su ba kamar haka (M.F)
.
Ban san me suke nufi ba, to amma dai na tabbatar shine gidan da naxo nema. Na ciro katin adireshin na sake karantawa, shi ne gida na hamsin da uku akan babban layin, don haka shi ne gidan da naxo nema.
.
Na matsa kadan jikin faffadar qofar dake yiwa baqi marhabun jikina a sanyaye, don kuwa ban san da wanda zan ci karo ba a gidan. Babu mai gadi a gidan, sai doguwar katanga dake zagaye da gidan wacce aka qawata ta da shuke-shuke na ganyaye shuwada da jajaye sun lullu6e saman katangar, sun shiga tsakanin gine-ginen dake a cikin gidan, da kuma idanun masu ganin qwaqwaf akan Na matsa kadan jikin faffadar qofar dake yiwa baqi marhabun jikina a sanyaye, don kuwa ban san da wanda zan ci karo ba a gidan. Babu mai gadi a gidan, sai doguwar katanga dake zagaye da gidan wacce aka qawata ta da shuke-shuke na ganyaye shuwada da jajaye sun lullu6e saman katangar, sun shiga tsakanin gine-ginen dake a cikin gidan, da kuma idanun masu ganin qwaqwaf akan hanya.
.
Na tsaya a qofar gidan ina tunanin abin da ya dace in fara yi, shin qwanqwasa qofar zan yi? To amma a yadda al'adar irin wadannan manyan gidajen suke da wahala baqo ya xo ya qwanqwasa qofa, ta hanyar mai gadi kawai ake iya ba mutum damar shiga, to gashi kuma gidan babu mai gadi. Don haka ban san me ya kamata in yi ba don ta san cewar naxo.
.
Ina nan a tsaye sai naji motsi a kusa da ni. Na waiga cikin sauri 6angaren da naji motsin. Nayi tozali da wani qaton surayi, yana sanye da farar sngileti da gajeren wando iya qwauri, yafi kama da 'yan dambe.
.
Kafin in yi masa magana ya fara tambayata da yarensa na yarbanci.
.
"wa ka xo nema a nan gidan?"
.
"Ban shekara shida a Ikko a banza ba, na iya yarbanci kamar yadda rariya ke xubar da ruwa.
.
Na ce dashi.
.
"Na xo wajen Hajiya ne, an bani wani saqo in kawo mata.".
.
Gabjejen saurayin wanda nake kyautata zaton maqwabcinsu ne ya ce da ni.
.
"mu je in kaika gidan."
.
Ya shige gaba, na bi bayansa a lkcn da ya sa hannu ya bude qaramar qofar dake hade da faffadar qofar shiga da mota, yadda naga ya hagorance ni mun shiga cikin gidan ba wani xullumi yasa na fahimci ya saba shiga gidan, kuma ya saba da hajiyar da naxo wajenta.
.
Tsayawa bayyana kayayyakin jin dadi da more rayuwar duniya dake a katafaren gidan 6ata lkc ne, gidan yafi kama da shahararren otel din da masu yawon bude ido suke yada zango.
.
Bayan faffadan kwatamin wankan dake a 6angare guda, ko'ina mutum ya kai ganin sa shuke-shuke ne na alfarma, da kuma jefi-jefin fararen tantabarun dake yawo a tsakar gidan, wadansu kuma suna fuffuka suna hawa kan shuke-shuken, suna wasannin su a sanyin safiyar gwanin sha'aBayan faffadan kwatamin wankan dake a 6angare guda, ko'ina mutum ya kai ganin sa shuke-shuke ne na alfarma, da kuma jefi-jefin fararen tantabarun dake yawo a tsakar gidan, wadansu kuma suna fuffuka suna hawa kan shuke-shuken, suna wasannin su a sanyin safiyar gwanin sha'awa.
.
Ga manyan motoci na kece raini a jere a wani 6angare. A kallo daya da nayi wa motocin, na gano motar da taxo da ita jiya wajen sana'ata. Hakan shi ya tabbatar mani cewar ban yi kuskure ba, babu shakka nan ne gidan da take.
.
Nayi ajiyar xuciyar na ci gaba da bin saurayin da ya shigo da ni cikin gidan har xuwa lkcn da muka tunkari wani babban falo da qofarsa ke bude yana fuskantar harabar gidan.
.
Wani abu da ya daure mani kai shi ne, ko'ina a cikin gidan, duk inda na kai duba na sai na ci karo da wadannan haruffa da na gani a wajen gidan haruffan (M.F). Har wasu ciyayi aka gyara aka fitar da haruffan a kusa da kwatamin wankan, har xuwa lkcn da muka shiga cikin tsararren falon.
.
Ban san me wadannan haruffan suke nufi ba sai daga baya na tuna ai sunan mutumin dana gani a jikin katin adireshin dake a jakarta Muhseen Fataye. Ba qaramin qoqari nayi ba wajen gano sunan mutumin ne aka taqaita da wadannan haruffa biyu da ake ta kwalliya da su a cikin Ban san me wadannan haruffan suke nufi ba sai daga baya na tuna ai sunan mutumin dana gani a jikin katin adireshin dake a jakarta Muhseen Fataye. Ba qaramin qoqari nayi ba wajen gano sunan mutumin ne aka taqaita da wadannan haruffa biyu da ake ta kwalliya da su a cikin gidan.
.
Don haka wannan Muhseen Fataye din duk yadda aka yi shi ne mijin wannan tauraruwar matar wacce naxo wajenta a halin ynxn, domin bata jakarta.
.
Da muka shiga cikin tsararren falon ne naga saurayin ya danna wata qararrawa ta amsa kuwwa a ko'ina a cikin falon, ya dube ni ya ce.
.
"ka jira ta zata fito ynxn nan."
.
Ya juya ya yi ficewarsa yana fiito.
.
.
Lp=8YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 8
.
.
.
YA juya yayi ficewarsa yana fiito bai tsaya sauraren gdyr da na fara yi masa ba. Sai da naga yayi nisa ya kusa ficewa daga gidan, sannan na dawo da hankalina a cikin katafaren falon wanda ya fi cancanta a kira shi da aljannar duniya.
.
Duk wani abu da ake nema na jin dadin rayuwa da hutawa akwai shi a cikin faskeken falon. Kilisan da aka malala masu launin ciyawa, wadanda suke barazanar hadiye qafar mutum idan ya taka su, suma an qawata su da haruffan Duk wani abu da ake nema na jin dadin rayuwa da hutawa akwai shi a cikin faskeken falon. Kilisan da aka malala masu launin ciyawa, wadanda suke barazanar hadiye qafar mutum idan ya taka su, suma an qawata su da haruffan (M.F).
.
Fankacecen tibin dake manne a jikin bango daga sama yana ta nuno namun daji, ba tare da ya bayyana koda sauti daya ba.
.
Ina nan zaune ina ta kallon abubuwan da ban ta6a ganinsu a duniya ba, sai naji an bude wata qofar gilashi dake a cikin falon, wacce idan ba mutum ya qura ido sosai ba da wahala ya san akwai ta a cikin falon, sakamakon sajewa da tayi da dogayen labulayen da ka yiwa fallon kwalliya dashi.
.
Bude qofar keda wuya ta sako santalan-santalan qafafuwanta ta fito sanye da doguwar riga fara, ba takalmi a qafarta, ta doro kallabin rigar a kanta kamar guntun mayafi, ta 6oye iya abin da bata son a gani na daga yalwataccen gashin Bude qofar keda wuya ta sako santalan-santalan qafafuwanta ta fito sanye da doguwar riga fara, ba takalmi

Please Login or Register in order to submit comment