Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 1
.
.
.
'(M. F)'
Su ne siraran haruffan dake a jikin duk wani abin kwalliya ko kayan qarau din dake a cikin katafaren gidan. A bayan kujeru, a qasan kilisai, da dardumai, a jikin gilasai da qofofi. Kai hatta kwatamin wankan gidan sai da aka yi masa kwalliya da da'irar ciyayi masu nuna wadannan haruffan guda biyu.
.
Baqo ne kawai zai xo ya wuce gidan, bai san me wadannan haruffan suke nuni dashi ba, to amma duk wanda ya kwana ya tashi a shahararriyar unguwar da tayi fice a birnin Ikko, wato (Victoria Island), ya san ko wanene Muhsin Fataye. Wanda shi ne yake inkiya da haruffa biyu na (M. F).
.
Alhaji Muhsin Fataye matashin attajiri ne dan shekara talatin da shida, wanda idan mutum ya ce zai tsaya lissafa kadarorinsa, da gine-ginensa na alfarma a garin Lagos to aiki ja ya same Alhaji Muhsin Fataye matashin attajiri ne dan shekara talatin da shida, wanda idan mutum ya ce zai tsaya lissafa kadarorinsa, da gine-ginensa na alfarma a garin Lagos to aiki ja ya same shi.
.
Abin da kawai yayi fice akansa kuma kowa ya sani shi ne, kasancewarsa babban ma'aikaci a madatsar ruwa ta tashar jiragen ruwa da kuma hada-hadar shigowa da kayayyakin waje xuwa cikin gida Najeriya. Duk da kasancewarsa bayerabe, yana jin hausa sosai, sbd duk kusan rayuwarsa tun yana yaro a Kano yayi. Aiki kawai ya dawo dashi Ikko, amma mahaifinsa dan kasuwa ne a Kanon dabo har Abin da kawai yayi fice akansa kuma kowa ya sani shi ne, kasancewarsa babban ma'aikaci a madatsar ruwa ta tashar jiragen ruwa da kuma hada-hadar shigowa da kayayyakin waje xuwa cikin gida Najeriya. Duk da kasancewarsa bayerabe, yana jin hausa sosai, sbd duk kusan rayuwarsa tun yana yaro a Kano yayi. Aiki kawai ya dawo dashi Ikko, amma mahaifinsa dan kasuwa ne a Kanon dabo har ynx.
.
Wata tara kenan da yin auren sa na biyu, wata bahaushiya ya samu a Kaduna, wacce ya hadu da ita a wani bikin amininsa wanda suka yi Jami'ar Bayero tare.
.
Yana matuqar son amaryarsa kamar yadda itama take son sa. Kuma bai samu wata matsala da matarsa ta farko ba mai suna Kudiratu. Ko da yake ba a gida daya suke zaune tare ba. Kowacce tana nata katafaren gidan, to me zai yi masu zafi tunda dai komai na duniya sun samu?
.
Alh. Muhsin kwana biyar-biyar ya tsara zaman sa da matanshi, kowacce idan yaxo gidanta ya kan yi kwana biyar.
.
A cikin irin wadannan ranakun ne sanda yana a wajen amaryarsa ya tashi da safe yayi wanka ya sa manyan kaya farare da hularsa ha6ar kada, wacce yake lanqwasheta gefe daya. Ya fito falo yana gyara daurin agogonsa, a lkcn ne amaryar tasa ta fito da turare a hannunta tana yi masa murmushin da ta saba na soyayya.
.
Ya riga ya saba da wannan turaren da take sa masa na qauna, kowacce rana in dai zai yi wanka yasa kaya, to ko ya fesa nasa turaren ya zama dole itama ta dauko nata ta fara fesa masa.
.
Ya tsaya jiranta ta qariso riqe da qaramin turarenta a cikin wata siririyar kwalba mai baqin murfi. Da xuwanta gabansa ta bude turaren ta saita gefen babbar rigarsa ta dannan kan gwangwanin, turaren ya fito da qarfi caa!!
.
Alh. Muhsin yana tsaye yana jiranta ta gama kafin suyi magana, sai yaga ta juyo da gwanwanin dai dai kanshi zata fesawa hularsa. Ta danna gwangwanin, maimakon turaren ya feshe hular, sai ya tsartu a saitin idanunsa biyu. Yayi saurin rufe idanunsa yasa hannu ya dafe fuskarsa da ya ji radadi ya gauraye idanunsa. Ganin haka yasa amaryar ta tsaya da fesa masa turaren, ta tambaAlh. Muhsin yana tsaye yana jiranta ta gama kafin suyi magana, sai yaga ta juyo da gwanwanin dai dai kanshi zata fesawa hularsa. Ta danna gwangwanin, maimakon turaren ya feshe hular, sai ya tsartu a saitin idanunsa biyu. Yayi saurin rufe idanunsa yasa hannu ya dafe fuskarsa da ya ji radadi ya gauraye idanunsa. Ganin haka yasa amaryar ta tsaya da fesa masa turaren, ta tambayeshi.
.
"Ya shigar maka ido ne....ban sani ba Alhaji, bude idonka in goge maka....oh...."
.
Har zai bude idanun, sai kuma ya ji kamar ana yankarsa da reza a ciki, ya dawo ya ji kamar ana soka masa allura. Yasa daya hannun ya dafe idanun nasa ya fara qaraji, yana juye-juye a falon.
.
Amaryar tasa ta rude ta fara kuka, ta dauko tawul ta jiqa shi da ruwa, ta fara qoqarin 6an6are hannun mijin nata zata goge masa idanun, ya qi tsayawa sbd ji yake kamar idanunsa zasu tsiyayAmaryar tasa ta rude ta fara kuka, ta dauko tawul ta jiqa shi da ruwa, ta fara qoqarin 6an6are hannun mijin nata zata goge masa idanun, ya qi tsayawa sbd ji yake kamar idanunsa zasu tsiyaye.
.
Qarajin da yake yi da kuma kukan da amaryar take yi ya jawo hankalin wani maqwabcinsa, ya shigo gidan a rude yaga abin dake faruwa.
.
A lkcn tuni Alh. Muhsin ya fadi qasa yana birgima, yana dafe da idanunsa yana kururuwa.
.
Maqwabcin nasa bai tsaya sauraren matar ba dake ta 6urari ya dauke shi yayi waje dashi yana kwadawa direbansa kira, ya fito da mota yayi sauri su je asibiti.
.
Awa daya bayan sun kai shi wani asibitin ido dake a garin. Likitoci suka amshe shi suka fitar da sakamakon da ya firgita kowa.
.
"Ba turare amaryar tasa ta fesa masa ba, wani azababben sinadari ne wanda aka yi shi musamman don makanta mutane, duk idon da aka fesawa ba zai qara ganin komai ba a duniya.!
.
Wannan maganar da ta fito daga bakin likitocin ta sabbaba kace-nace a tsakanin amarya da 'yan uwan mijinta wadanda suka shigar da qararta a kotu. Amaryar ta kare kanta da rantsuwar ita turare ta san ta fesa masa, kuma tunda suka yi aure kullum idan zai fita sai ta fesa masa turare. Ynx ne aka samu matsala tsautsayi ya ratsa ta fesa masa a ido bata sani ba.
.
Aka shiga kotu aka fara fafatawa. Da amaryar ta dauko turaren taxo dashi ne aka ba qwararrun masu auna sinadarai suka yi aiki akan shi, sai suka ce turaren baya dauke da wata guba, babu komai a cikinsa. Likitocin da ke yiwa Alh. Muhsin Fataye aikin idon, suka xo suka qaryata bayanin da cewar.
.
"Turaren da ta bayar a kotun ba shi bane turaren da ta fesawa mijin nata ba."
.
Hakan yasa dole aka tura jami'an tsaro gidan nata domin su je suyi binciken qwaqwaf ko wata qila za a ga ainahin turaren da aka ce yana dauke da guba a cikinsa.
.
.
Lp=2YARO BAI SAN WUTA BA......
.
Page 2
.
.
.
Hakan yasa dole aka tura jami'an tsaro gidan nata suka je suka yi binciken qwaqwaf ko wata qila za a ga ainahin turaren da aka ce yana dauke da guba a cikinsa, , amma da suka je basu ga komai ba.
.
Da aka dawo kotu ne Lauyan dake kare amaryar ya tabbatarwa kotu cewar lallai wacce ake zargi bata da laifi.
.
"Ta yaya zata mayar da mijinta makaho bayan duka-duka watansu tara da yin aure? Dama kashe shi tayi sai ace dukiyarsa take so, amma idan ta makantashi me zata samu a sakamakon hakan?"
.
Ba a kotu ba, ko a waje abin da mutane suke ta cewa kenan. Akwai zaman soyayya a tsakanin sabbin ma'auratan. Babu dalilin da zai sa matarshi ta makantashi.
.
Shi kansa mijin nata duk da yana kwance a asibiti ba a sallame shi ba, ya goyu bayan matar tasa, kuma yana qalubalantar kotu bisa tuhumarta da suke yi. Da wata jarida ta je tayi hira dashi a asibitin, ko me zai ce dangane da wannan mugun abu da ya faru dashi, sai ya ce dasu.
.
"Ina zaune da matata lfy, bamu ta6a samun wata matsala ba. Na san tana sona, kuma ba zata iya cutar da ni ba.
.
Ta saba fesa mani turare kullum, bata ta6a cutar da ni a dalilin haka ba, kuma ba zata iya cutar dani ba. Wannan abu daya faru ba laifinta bane. Abin ya xo da tsautsayi, ko bata fesa mani turaren ba, idan lkcn makancewata yayi ba yadda zan yi, wajibi ne sai abin ya faru....don haka bata da laifi, bana zarginta."
.
Jaridar ta sake tambayarsa.
.
"Kana nufin kenan idan Likitoci suka sallameka zaka ci gaba da zama tare da ita a matsayin matarka?"
.
Ya amsa masu.
.
"(Why not) me zai hana kuwa? Zamu ci gaba da zama mana tare. Na san don na zama makaho ba zata guje ni ba, zamu ci gaba da zama kamar komai bai ta6a faruwa ba."
.
Haka kuma abin ya kasance. Alh. Muhsin ya zama makaho, ga dai idanunsa a bude, amma sun mutu, basa iya ganin komai.
.
Ya samu wani kwantareren baqin tabarau ya 6oye matattun idanunsa, ya samu sandar qarfe ta makafi 'yan gayu ya riqa laluben hanya da ita, ya dawo wajen iyalansa suka ci gaba da zama, ya tara 'yan uwansa ya basu haquri, ya ce baya son ana tayar da wannan magana, kada su tsani matarsa komai muqaddari Ya samu wani kwantareren baqin tabarau ya 6oye matattun idanunsa, ya samu sandar qarfe ta makafi 'yan gayu ya riqa laluben hanya da ita, ya dawo wajen iyalansa suka ci gaba da zama, ya tara 'yan uwansa ya basu haquri, ya ce baya son ana tayar da wannan magana, kada su tsani matarsa komai muqaddari ne.
.
Matarsa ta farko Kudiratu tayi kuka ba dan kadan ba, 'ya'yanta uku da Muhsin Fataye, gashi ynx ya zama makaho suna cikin jin dadin duniya, bata san yadda rayuwa zata kasance masu ba ynx.
.
Alh. Muhsin ya ci gaba da harkokinsa ana yi masa jagora, yana da yara masu amana a ko'ina, babu abin da ya samu dukiyarsa.
.
Duk abubuwan da ya saba yi bai daina komai ba. Idan wata yarjejeniya zai yi da wani kamfani, akan yi masa jagora ya je ya zauna ayi duk surutun da za a yi.
.
Idan zai sa hannu a takarda sai a nuna masa ita ya laluba, a dora masa yatsansa a kan takardar inda zai sa hannun.
.
Rayuwar aurensa da amaryarsa wacce ta zama sanadiyyar makancewarsa ba wata matsala, suka dawo suka ci gaba da aman soyayyarsu. Ko'ina zai je a gidan sai ta riqe masa habby ra kai shi.
.
Da yake yana son karatun jatida, kullum sai ta karanta masa sabbin jaridu da mujallun da suka fito, yana zaune akan kujera sanye da faskeken baqin tabarau ya na saurarenta har ta gama.
.
Idan zasu yi tafiya ita ce ke tuqa mota, duk wasu wajen shaqatawa da suke xuwa ada kafin ya makance basu daina xuwa Idan zasu yi tafiya ita ce ke tuqa mota, duk wasu wajen shaqatawa da suke xuwa ada kafin ya makance basu daina xuwa ba.
.
Iyakarta dai ta riqe masa sandarsa ta qarfe ya bita a baya tana yi masa jagora.
.
Duk da shi bai damu ba, amma mutane suna tausayawa yadda rayuwarsa ta koma.
.
Babban mutum mai kudi da kamala ya zama makaho!
.
Ba zai sake ganin duniya da abin dake cikinta ba.
.
.
FARAWA.
.
Tun farkon faruwar al'amarin, ban ta6a kawowa a raina zan fadawa duniya wannan labari ba. Wani lkcn ni kadai idan na tuno al'amarin na kan yi mamaki da al'ajabi in tambayi kaina, wai da gaske nine wanda wannan gagarumin al'amarin ya faru da ni? Na kan ji abin kamar aikin mafarki ne bai faru da gaske ba. Don haka wa zan fadawa labarin, tunda na san ba kowa zai gasgata ni ba? Shi yasa na dauki shekara da shekaru ina 6oye da labarin a xuciyata kamar kudin adashiTun farkon faruwar al'amarin, ban ta6a kawowa a raina zan fadawa duniya wannan labari ba. Wani lkcn ni kadai idan na tuno al'amarin na kan yi mamaki da al'ajabi in tambayi kaina, wai da gaske nine wanda wannan gagarumin al'amarin ya faru da ni? Na kan ji abin kamar aikin mafarki ne bai faru da gaske ba. Don haka wa zan fadawa labarin, tunda na san ba kowa zai gasgata ni ba? Shi yasa na dauki shekara da shekaru ina 6oye da labarin a xuciyata kamar kudin adashi.
.
Duk tsawon lkcn da nayi ban fito da wannan labarin ba, na san wata rana dole ne in amayar dashi, wadansu su ji, kamar dai yadda zan sanar daku a halin ynx.
.
Al'amarin ya fara samo asali ne a wani dare da na mance ko wacce rana ce. Alhamis....? Asabar...? Bana jin zan iya tuna kowacce rana ce a halin ynx, to amma dai abin da ba zan mance ba shi ne. Na san an tashi da hadari tun safe har dare yayi ana ta walqiya da cida. Ba a yi ruwan ba, kuma sararin samaniyar bai washe ba.
.
Wannan ba wani sabon yanayi bane a birnin Ikko, don kuwa sai a dauki kwana da kwanaki a haka. Ko kuma a yi ruwan, ana daukewa ba a jima ba wani ya sake saukowa.
.
Irin wannan yanayin baya hana mu fitowa ga qananun sana'o'in da muke yi. Musamman ma dai ni da nake da qaramin teburi da kujerun zama biyu, da tsohuwar laimata ta kamfanin sadarwa na (Glo) wacce ta kode duk rubutun jikinta ya fara kodewa.
.
To amma duk da kodewar da laimar tayi, kullum in har zan budeta a wajen wannan sana'ar da nake yi in zauna a qarqashinta.To amma duk da kodewar da laimar tayi, kullum in har zan budeta a wajen wannan sana'ar da nake yi in zauna a qarqashinta...
.
.
Lp=3YARO BAI SAN WUTA BA
.
Page 3
.
.
kullum indai zan budeta a wajen wannan sana'a da nake yi in zauna a qarqashinta, ko daga nesa in mutum ya qura ido zai iya ganin rubutun dake a jikin laimar da baqin fenti, wato (Kamal Communicat kullum indai zan budeta a wajen wannan sana'a da nake yi in zauna a qarqashinta, ko daga nesa in mutum ya qura ido zai iya ganin rubutun dake a jikin laimar da baqin fenti, wato (Kamal Communication).
.
Kada in yi tsallake in mance da wani abin, bari in dawo in fara baku labarin daga farko, don kusan tushen al'amarin.
.
.
'SUNA NA KAMAL.'
.
Kada ku tambayeni asalina ko garin mu, sbd a zama irin na Lagos, na kaxo-naxo, da wahala ka ji wani ya bude ma cikin sa ya fada maka gskyr inda ya fito.
.
Don haka nima ban ta6a fadawa kowa ba, kodai ban fadi gsky ba an san daga arewa nake, kuma ni Bahaushe ne wanda yaxo neman kudi.
.
Shekaruna zasu kai ashirin da bakwai a duniya, a ciki idan ka debe shekaru shida na sama, duk nayi su ne a wannan gari na Ikko. Farkon xuwa na a shekarun baya wasu 'yan garinmu na biyo, wadanda suke xuwa sana'ar gwari, wato safarar kayan lambu dangin tumatiri da albasaShekaruna zasu kai ashirin da bakwai a duniya, a ciki idan ka debe shekaru shida na sama, duk nayi su ne a wannan gari na Ikko. Farkon xuwa na a shekarun baya wasu 'yan garinmu na biyo, wadanda suke xuwa sana'ar gwari, wato safarar kayan lambu dangin tumatiri da albasa.
.
Daga baya da idanuna suka bude, sai naqi komawa gida, na samu wurin zama a nan na fara yin sana'o'in qarfi tunda dai ban yi karatu ba, ballantana in sa ran samun wani aiki mai tsoka a wani kamfani.
.
6ata lkc ne tsayawa lissafa sana'o'in da nayi a wannan gari, sbd duk wani aikin wahala in dai zai kawo kudi kuma ba na laifi bane baya bani tsoro, sbd bani da matsalar qarfi da kuma jurewa wahala.
.
Daga baya ne na samu wannan sana'a nake yi a halin ynx ta sayar da katin waya a bakin titi.
.
A da bani ke da wajen ba, na ubangidana ne da ya bar garin sai na maye gurbinsa ina cin gashin kaina.
.
To ko dai ba komai ynx nafi da ci a huce, sbd bana tashi in je ko'ina. Idan na zauna har inda nake masu buqatar katin suke xuwa su miqo mani kudi in ciro in basu. Wasu kwastomomin kuma idan manyan mutane ne masu kudi wadanda suke xuwa a motocinsu, da sun xo sun yi fakin sai in tashi in tarbesu in matsa kusa dasu in ji wane kati zan basu?
.
A 'yan kwanakin nan wannan yanayin na ruwa da hadari akai-akai shi yake damuna tare da sauran mutane wadanda suke da tebura a bakin titi irina. Sbd koda ruwan bai tashe mu ba, idan mun mun ji zamu iya zama, ai dai zai hana mutane su fito su yi walwala da hada-hada, idan kuwa babu mutane a bakin titi ko ba a ce komai ba, an san kasuwa sai addu'a.
.
A daren da al'amarin zai faru, kamar kullum ni kadai ne a zaune a wajen, ina sanye da qananun kaya da hula hana sallah, itama ta kamfanin sadarwa ce da suke bamu idan mun je sayen kati.
.
Zaman da nayi a wajen, ni kadai na san abin da xuciyata ke saqawa, don kuwa kasuwa tayi nauyi, sanyin ruwan da ake yi yau da kullum ya hana mutane sakat a waje, shi yasa kasuwa ta tsaya, sai a kwashe kusan sa'a guda wani bai tsaya a wajen ya sayi kati ba. Gashi kuma gobe nake so in je in saro wani, shi yasa na ci gaba da haquri na zauna, duk da yake kuwa a zahiri nima sanyin yana damuna.
.
Na fara shawarar in tashi in tattara kayana kenan, sai naji sautin tsayuwar mota dab da teburina. Ban san ma lkcn da ta gangaro da motar dab da ni ba. Na dago kaina da sauri kamar wanda yake gyangyadi, a lkcn ne ni da ita muka kalli juna, tana zaune ita kadai a cikin motarta ta qanqame sitiyari da hannuwanta biyu, kamar tana xullumin xuqeqiyar motar zata qwace ta gudu ita Na fara shawarar in tashi in tattara kayana kenan, sai naji sautin tsayuwar mota dab da teburina. Ban san ma lkcn da ta gangaro da motar dab da ni ba. Na dago kaina da sauri kamar wanda yake gyangyadi, a lkcn ne ni da ita muka kalli juna, tana zaune ita kadai a cikin motarta ta qanqame sitiyari da hannuwanta biyu, kamar tana xullumin xuqeqiyar motar zata qwace ta gudu ita kadai.
.
Wannan shine haduwarmu ta farko ni da Fauziyya, wacce da ba don ita ba da wannan labarin bai wanxu a duniya ba. Na tashi cikin sauri don in je kusa da tagar motar in tambayeta katin da take so, tunda dai na san shi ya tsayar da ita a wajena, ba xuwa tayi ta kalli tsofaffin kujeruna na roba ba wadanda yawancin kwastomomina suke tsoron su zauna akai, don kada tsofaffin kujerun su karye su bayar dasu a titi.
.
Kafin in fito daga lungun dake tsakanin kujerun da teburin nawa ne, sai naga ta saki sitiyarin ta bude motar ta sako qafa ta fito waje, wannan shi ya dakatar dani na tsaya jiranta.
.
A lkcn ne na sake tsayawa na dubi motar, wacce ban san sunan ta ba.
.
Na tabbatar sabuwar shigowa ce, kuma ko makaho ya xo ya lalubi motar, wacce take ta sheqi da walqiya a cikin daren, ya san ba motar yara ba ce, kamar yadda ita ma wacce ke da motar bata kasance yarinya ba.
.
Na dawo da hankalina wajenta. Na dubeta cikin girmamawa, sbd duk kwastoman da zai xo wajena a irin wannan motar, shi kansa ya san zai samu kulawa ta musamman.
.
Ban san ta yadda zan zana maku hoton Fauzaiyya ba a wannan littafi, sbd komai na fada na san dole ne sai na rage maku wani abin.
.
Idan aka xo wajen maganar kyau da cikar halitta bani Adamu, sau da yawa wadansu suna kuskure. Domin kuwa wani zai nuna mace ya ce tana da kyau mutane su qaryatIdan aka xo wajen maganar kyau da cikar halitta bani Adamu, sau da yawa wadansu suna kuskure. Domin kuwa wani zai nuna mace ya ce tana da kyau mutane su qaryatashi.
.
Wata kuma idan ta wuce wani ya ce kyakkyawace, to ko mutane dubu aka tara in dai zasu ganta dole ne su amince.
.
Na san kowa zai yarda da ni in har zai yi sa'ar ganinta.
.
Ba zaka kira ta da doguwa can ba, kuma bata da girman jiki. Duk da haka a ko'ina cikakkiya ce, kuma qosasshiya wacce idan ta motsa jikinta, ko ina sai yayi mubayi'a.
.
Farar fatarta ba mai qarfi bace, ya fiwa mutum ya ce mata tsaka-tsaki. Ganganci ne ka kalli fuskata in zaka tsallaka titi.
.
Lp=4YARO BAI SAN WUTA BA...
.
Page 4
.
.
Ba qaramin ganganci bane mutum ya kalli fuskarta a yayin da zai tsallaka titi, don kuwa mutum zai iya mancewa akan titi yake har mota taxo ta same shi tayi awon gaba dashi ba tare da ya sani ba.
.
Wannan shi ne abin daya faru da ni sa'ar da na kalleta, fararen idanunta suka hasku akan nawa.
.
Tana sanye da kaya masu ruwan ganye, wadanda aka qawata dinkinsu da baza a qasan zaninta. Ta dora qaramin gyale a kafadarta wanda dashi da babu duk daya, tunda dai bai hana ganin dogon wuyanta da kuma dogayen gororin kitsonta da suka xubo a bayan wuyanta sbd yawan da suka yi babu wurin da zasu 6oye a cikin kallabiTana sanye da kaya masu ruwan ganye, wadanda aka qawata dinkinsu da baza a qasan zaninta. Ta dora qaramin gyale a kafadarta wanda dashi da babu duk daya, tunda dai bai hana ganin dogon wuyanta da kuma dogayen gororin kitsonta da suka xubo a bayan wuyanta sbd yawan da suka yi babu wurin da zasu 6oye a cikin kallabinta.
.
Bana son ku ce na xuxuta Fauziyya a wannan labarin, kada ku ji haushina da na ce ko me zan fada dole in bar abubuwa da yawa a tattare da ita, don haka a wanne dalili zan ci gaba tunda dai na tabbatar Fauziyya kyakkyawa ce?
.
Kuma ina tunanin da ace zata kai xiyara sansanin da

Please Login or Register in order to submit comment