Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan in kuntatama Taufiq kuma na kuntata mashi zaiji inda daɗi ta hakane kawai zan iya hukunta shi,nidai Allah yasani inasan ɗana bazan iya yimashi baki ba wannan shine dalilina na aikata wannan,amman ina son Maryam araina kuma tana da mahimmanci agreni."

Wani irin dadi sukaji aransu godiya sukaita sheka mashi banda Mami dakeji kamar ta fasa ihu ya'akai komai yazo cikin sauki har haka,barin falorn tayi baki daya taja Anty Hafsat sukai cikin dakin Amina wanda Allah kadai yasan abinda suka tattauna a tsakanin su.

Anty Murja ce rike da Amina zuwa falorn Baba,mahaifin Taufiq ya bukaci akawo mashi ita kafin a daura aure,kanta kasa ta duka tana gaidasu ya amsa a mutunce yace.

Aminatu nasa akira mani ke domin in baki hakuri akan tsaurara ra'ayina danayi akanki da kiyayar da nike nuna maki,kisani bakece na tsana ba,ɗabi'un Hussein ne na tsana da rashin nuna da'ar shi ga iyayen shi,na nuna mashi zai iya neman komai yarasa arayuwar shi dan yasan girman Qaddara,wanda shi sam bai santaba,amman badan na tsaneki ba Aminatu,kefa ya'ta ce ina maki fatan alkhairi Allah yabaki zaman lafiya a gidan mijin ki ya'ta.

Sannan kuma naji dadin yanda kikaima iyayenki biyayya insha Allah bazakiyi dana sanin wannan auren ba Allah yaimaki albarka ya'ta."

Ɗago kaina nayi na kalli Abba sannan na maida kaina ƙasa nace.....


*Masoya ina ganin sakon ninku akan labarin Qaddarata saidai ina mai kara baku hakuri musamman masoyan Taufiq da Minal,fatan Allah yabamu ikon cinye jarabawoyin mu idan kuma ya tashi ɗaura mana Qaddara yabamu wadda zamu iya dauka ameen,ina maku fatan alkhairi,Allah yabar so da kauna🥰🤝🏻*




_Yar Mutan Kankia ce❣️_






Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E29&30




"Sannan kuma naji dadi yanda kikaima iyayen ki biyayya insha Allah bazakiyi dana sanin wannan auren ba ya'ta Allah yai maki albarka."

Ɗago kaina nayi na kalli Abba sannan na maida kaina ƙasa nace.

Nagode Abba Allah yakara girma."

Ameen duk aka amsa daidai Mami sun shigo dakin ita da Anty sukaji Abba nata samani albarka,take fuskar su ta nuna tsantsar bakin cikin su,daurewa kawai sukayi suka wuce ciki sosai akai mani huɗuba mai kashe jikin mai sauraro Anty Mubaraka ta maidani gidan sitting ina ganin Lukman nata kwaɗa mani kira amman ba yanda zanyi inkira shi,ina isa nakirashi yana ɗagawa yace.

Haba my wife sai kiranki nake kinki picking call dina,saiki daga mani hankali inyi tunanin ko baki da lafiya muna hanya mun kusa Jibia."

Alhmdullh,Allah yakawo ku lafiya,kayi hakuri ankaini wajen su Baba shiyasa ba samu damar daga kiran ba,agaban su."
Wow kice an maki nasihohi ance ki mani biyayya kiji dani,ki tsaremani mutuncina,dukiyata ya'yana,ki mutunta iyayena da yan uwana,wow ohni ɗan gata naji dadina."

Dariya yabani sai surutu yakeyi waishi zai zama mijina yanajin dadi zan mashi biyayya.

kaima yanzun nan zakazo kaji sharuddan ka, nasan naka sunfi naka sunfi nawa wahalar kiyayewa."

Aaa nakidai suni wahala, sai zaki fita ince No idan kin hakura kin zauna kinman biyayya kishi aljanna kinsan dai ance aljannar mace na kalkashin kafar mijinta."
Oga sir naji Allah yabani ikon kiyayewa."
Ameen my wife i love you."
Love u too."

Dan Allah malamai kun ishemu sai kace ba yau zaku mallaki junan kuba miye haka.?"

Kaga Aminu barni lokaci nane,wlh ganin garin nike yayi mani nisa,koda yake mun shigo Katsina insha Allah nan da 30mint zamu iso."
Allah yakawo man kai lafiya masoyina."
Ameen,I miss u wife.
Miss you too."

Husna ta anshe wayar tana mashi lalata,Fatash tasani na shiga wanka na sauya kaya akai mani make-up ina duba agogo naga 1:35 munajiyo hayaniyar yan daurin aure a unguwar mu,har karfe 2:30 shiru mutane suka fara complains abinda za'a daura karfe 2pm gashi har ukku ta matso ba'a daura ba.
kiran wayar Lukman nike bata zuwa yafi a kirga har zuciya tafara tsinkewa duk na tsure na shiga damuwa,kara kiran shi nayi still not reachable,harna fidda rai na kara kira aka dauka.

Haba my love lafiya inata kiran ka ban samu?"

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un naji ana fada cikin wayar bama asan an daga ba cewa ake yan daurin aurene daganin su,daga Zamfara suka fito inalillahi wa'inna ilahirraji'un,kamar basu numfashi akaisu general......

Yayi daidai dana saki wayar hannuna ƙasa na zube ina kiran hasbunallahu wani'imal wakil inalillahi wa'inna ilahirraji'un....
baki ɗaya mutanen wajen aka ida,dib jina ganina ya dauke na wucin gadi bankara sanin inda kaina yake ba.

komai yagama hargitsewa da sakon hatsarin su Lukman ya iso musamman yan daurin aure kowa yayai jigum dashi sai salati ake ana gayama Allah

Cikin gida kuwa matane keta kuka suna kiran inalillahi wa'inna ilahirraji'un,baki ɗaya biki saiya koma gidan koke koke.

Abban su Taufiq da mahaifin Lukman wanda su already sun iso anguna kaidai ake jira suka dauki hanyar zuwa Katsina.
Shiko Baba yakasa ko motsin kirki tsabar tashin hankali da fargaba.

Motoci akaita hawa zuwa Katsina dan ganin halin da Lukman suke ciki.
Mum da Anty Hafsat sai Anty Murja da maman su Asma'u suka tafi suma a hargitse kowa ka gani hankalin shi yai bala'in tashi.

Kuka nike kamar raina zaibar gangar jikina bansan abinda akeba sallallamin mutumin daya ɗaga waya ta,kawai ke mani yawo acikin kunnena kana ganina kasan banda banbanci da tababba ko zautatta.

Kawu Usman da Ya Tariq sukazo suka daukeni nida Husna cikin mota nidai bansan inda ake tafiya dani ba banda inalillahi ba abinda nike kira.

Ba inda na tsinci kaina sai asibitin gwamnti ta Kt ancika anbatse da yan gari kowa yanata zullumi.

Mum ta janyoni jikin ta,duk na rude kuka kawai nike koma inci hawaye ki zararowa idona ina kuka marar sauti.

Baki daya mukayi kan Doctor a rude lokacin daya fito Emergency Minor theater.
Jan Abban su Taufiq da Baban Lukman yayi zuwa wani office.

Sunjima suka fito kowa jugum dasu,tambayoyi ake jefo masu sun kasa magana.
Buɗe bakin da sirikina zaiyi mahaifin Lukman kawai ya yanke jiki ya fadi a sume,kanshi akayi ana rabka salati.
Jikina yahau mazari lokacin da Abba yace kowa yai hakuri basu aɗauki Qaddara.

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un na kwada wanda ya jawo attension din kowa a gareni nima a sume na faɗa jikin Mum.

Tinda Amina ta sume akayi da ita female ward aka fara bata agajin gaggawa.
Hakama mahaifin Lukman,kowa yakasa komai yan biki rabi da kwata ana asibiti.

kuka kuwa mata ketayi kamar ba gobe.

Baba Hassan yaita maza yafara faɗa yace miyasa mata suka biyo nan ai bai kamata ba,dan haka kowa ya hau mota tatafi gida.
A hankali aka fara ragewa ana komawa gida rai ba dadi.

Sai gab da magrib aka sallami Amina hakama Abban Lukman.

Ranar kowa baida lakka ajikin shi.
Maryam ku tafi gida kama Aminatu kuyi hakuri."
Cewar Abba.

Sai lokacin nafara kuka mai sauti nace
Abba dan Allah inasan ganin Lukman.
Kiyi hakuri Aminatu."

Nanfa na daga hankalina matuka,da Doctor Maha yaki bari ingan shi,sanin nima aikina kenan kuma muna haɗuwa a Saminar saiya barni cikin tausayawa.

Gawar sune kwance a lullube,ina shiga ciki nahau jefa kafata kawai nike harna isa wajen Lukman wanda shaddar jikin shi data fito ita tasa nagane shi,domin anko mukayi nida shi.

Hannuna na rawa nakasa bude fuskar shi tsabar rudewa.

Saida Doctor yazo ya yaye mani marufin.
Ƙur nai mashi da ido kamar ince ya tashi amman ba dama.

Kanshine ya fashe saidai fuskar shi fayau take gwanin shi'awa.

Nakai minti goma ban dauke idona a kan shiba wanda nike gani mafarki a wajena.

Doctor Amina yaka mata kifito hakanan cewar ogana Doctor Maha.
Hannuna nasa bisa fuskar shi na shafi sajen shi ina mai addu'a agare shi tareda dinbin kewar shi.

*Allah yaimaka rahama Lukman yasa damu agidan aljanna annabin rahama yasan da zuwan ka,yasa kana cikin samarin aljanna ya rabbil alameen*

Da ameen suka amsa,haka naima sauran abokan sa guda hudu duk dashi biyar ikon Allah rayuwa kenan kana taka Allah na nashi amman ta Allah itace daidai kowa datasa Qaddarar wannan itace Qaddarar Lukman,ni kuma tawa Qaddarar akan rashin masoyane lallai kam wannan Qaddarata ce!

Saida Mum tazo taka mani sannan muka fito ina kuka,yanzun shikenan wannan shine kallan karshe da zanyima masoyina Lukman,ashe daman wayar da mukai ta sallama ce! Ashe ba raban mu sake ganawa,rayuwa kowa da nashi silar.

Nidai nasan na shiga mota bansan an iso gidaba lokacin kuwa goma ta wuce na dare.

Ina isa gida nan ma gidan a rude yake niko zuwa lokacin idanuna sun bushe sanadiyar ganin gawar Lukman danayi.

Saidai ido nike binsu dashi nakasa magana.
Karfe biyu daidai na tashi nahau salloli ina rokarwa Lukman afuwa wajen mahaliccin mu.

Har akayi assalatu inaga ba kowa yai bacci sai kalilan ciki kuwa harda Anty Hafsat da Mami suna shan baccin su.

Tunda aka fara hidimar bikina Anty Hafsat bata kwana gidan muba sai yau.
Ana asuba na maida salla ina lazumi da addu'a
Mama kuwa kallo daya zakai mata kasan halin da take ciki.

Washe gari karfe goman safe Baba ya kira wayar Mum yace ashirya ga motanan an turo za'a tafi zamfara jana'iza baki daya.

Kamani tayi mukaje daki ta matsa mani nayi wanka nasa doguwar riga da katuwar hijab morish.
Muka fito harda Husna dan kuka idanun ta sun kumbure.
Mum,Mama,Anty Murja,Anty Hafsat,Anty Aisha,Mami,Anty Zainab,Anty Mubara,Husna,Fatash,Mamar su Husna Dada saini damu za'aje gidan su Lukman ashe bada auren shi zan taka gidan su,saidan gaisuwar rashin shi Allah mai iko shike tsara komai yanda yaso rayuwa kenan.

Ya Tariq shiyaja motar da muke,inda Samir shima ke tuka ɗaya sai Ahmad kejan guda mota ukku mukai ta mata.

Sadda muka isa Katsina anbada gawar su,har dangin su sunyi gaba dangina muka hadu motar maza hudu sukayi a cikin wanda kejan motar harda Abba,sai Baba dakejan tashi,sai Baban Husna muka tafi Zamfara.

Karfe daya muka isa lokacin angama kimtsasu aka fara bankwana.
Tinda naje Maman Lukman ke rungume dani tana kuka,koda akaje bankwana hardani akaje nasake ganin shi tareda yimashi addu'a inakara jin son shi na shiga a zuciya ta.

Ana gamawa akai sallar jana'iza aka tafi kaishi gidan shi nagaskia.
Sai a lokacin kukan zucin da nike ya ninku kamar zan sike.

Fita akahau yimani tareda kunna mani Ox fanka.
Munjima nasamu nutsuwa ta ina addu'a ga masoyina.

Tashin hankalin daya kara tashi nadaga sisters dinshi cousins Nins dinshi hakan yasa kowa ya shafa'a da tuna gida,sadda za'a samu sassaucin lamarin magrib tayi.

Hakan yasa su Abba suka kama hotel cikin Gusau mu kuma agidan su muka kwana.
Da dare kowa kagani sallah yake yana nemawa mamatan rahama.

Washe gari da safe akahau kalaci saidai nida Mama sai Umman shi daidai da pure water mun gaza sha,har mantawa nike da abinci saboda banjin yunwa.

Da rana muka shrya zamu tafi,sosai Umman shi ke kuka kamar kada intafi inbarta dan munshaku har waya munayi da ita.

Su Tariq suka shigo gaisuwa cikin gidan su Baba da sauran mazan ciki kuwa harda Ahmad shima ya shiga damuwa.

Ana la'asar muka dauko hanya zuwa gida,sai isha muka iso kowa cikin damuwa.

Washe gari kofar gidan mu kamar makoki sai gaisuwa akema Baba saiya kasance makokin biyu ne Gusau da Caranci.

Saida akayi azahur yan biki aka fara watsewa.
Ana la'asar su Abba da Mum,Mami da sauran yan gidan su Ya Taufiq sukai shirin komawa Kaduna,Abba sosai yai mani nasiha ta dangana naji dadin hakan.

Washe gari kuwa kowa ya gama watsewa dagani sai iyayena da kannena,Husna ma takoma gida ba dadi.

Haka nazauna sukuku banci saidai ruwa shi nike iya sha.

Ranar da akayi kwana ukku yan aikin mu sukazo mani gaisuwa sun jima suka tafi tareda bani hutun sati biyu.
Murna nayi da hutun dana samu.

Wasa farin girki ashe sai yanzun mutuwar Lukman zata zama sabuwa agareni bacci gazawa nike banda sambatu ba abinda nikeyi sai hawaye dake sintiri bisa fuskata.

Mahaifina shi yazama abokina domin shike kwantar mani da hankali ko abinci da kanshi yake bani musamman abu mai ruwa ruwa sosai ya tausaya mani.
Ina mamakin sanda son Lukman ya kamani har haka,saina yarda cewa nidin saurin sabo ke gareni.

Addu'a ban fasa yimashi itaba ba dare ba rana.

Ina kwance bisa kushin din falorn Baba text ya shigo wayata karantawa nafara.

*Assalamu-alaikum*

_Beauty ya karin hakuri Allah yai mashi rahama yasa ya huta ameen._

*Ayyah kwara daya tafi domin koda kin aure shi nidin bazan bari ku zauna lafiya ba kin dauka alqawalina na banza ne,zan yarda makamaina akanki,bayan kedin desire dita ce,kisa aranki zan dawo rayuwar ki,kuma komai kikeyi a tafin hannuna yake,kuma duk inda kikaje ni JJ ina taredake!*

Sauke ajiyar zuciya nayi ina mamakin hali irin na Dr JJ,araina ina jinjina Qaddarar dake neman danno mani kofa bayan wadda nike ciki!


*Assalamu-alaikum.*
_My Fans nasan zakuyi mamakin ganin two post in a day ko? to ina mai shaida maku insha Allah zakuna samun double saidai ba lallai kusamu week end ba,nayi hakan ne saboda yanayin karatu da nikeyi_ _makaranta abubuwa sunyi mani yawa ina barar addu'ar ku Allah yabamu sa'ar karatun mu baki ɗaya,ni Yar Mutan Kankia inaganin sakonin ku DM dama na grps nagode,kudai kuci gaba da ruwan comments sannan Amina Caranci tana godiya da addu'oin ku agareta Allah yabar tare inayinku masoyana kardai ku manta👇🏻_


_Yar Mutan Kankia ce❣️_





Share
Pls
❣️

_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E31&32


Tariq yana komawa gidan shi ko zama baiba wanka kawai yayi domin tashin hankalin da aka shiga bazai bar mutun yayi ko wankan kirki ba.

Yana fitowa wanka sallama kawai yaima matar shi ya nufi gidan Taufiq koda ya isa Horn ya danna mai gadi na lekowa yaga Tariq ne baibude mashi kofaba ya fito waje gaidashi yayi yace.

Bainan amman yace inkazo ingaya maka sako nanan ya aje maka a dakin shi bisa gado

Ikon Allah yacen sannan ya bude motar ya fito,ina yace maka zaije.?"

Ai ranka shidade bai gaya maniba saidai harda akwatin shi naga yasa a mota yafita amman yace mani zai dawo.
"Toh tun yaushe ya fita.?"
Allah yataimakeka tun ranar da kuka tafi biki Caran....
Bai bari ya idaba ya banka kofar kai tsaye dakin Taufiq ya shiga yana zuwa bisa gado yaima tsinke hannun shi na rawa ya dauki letter din.


Bin bayanta da ido yayi yaga ansa Sorry!
Hakan yasa Hassan kasa karantawa zuciyar shi na bugawa da kyal yakai kanshi gidan iyayen su.

Parking din kwarai baiba ya isa side din Abba kowa nanan anata jimamin mutuwar Lukman saiga Tariq ya fado a hautsine duk suka mike baki dayan su.

Da kallan tuhuma suke binshi.
Latter kawai ya iya mikoma mahaifin nasu,shima jiki a mace ya karba yafara karantata kamar haka.


```Assalamu alaikum
Yaku iyayena da yan uwana dan Allah kuyi hakuri da sakon da zaku gani nabar maku,naso nazauna taredaku domin in ida rayuwata a cikin ku saidai hakan bamai yuyuwa bane saboda na bata komai,musamman iyayena dake fushi dani akan soyayyar da nikema Minal,na yanke shawarar barin rayuwar ku baki daya da ita kanta na hakura da ita Abba,dan Allah kuyafe mani abinda na aikata maku musamman Abba da Mum kusamani albarka,nine ɗanku Hussein Sarki Mukhtar!```

Sakin takardar Abba yayi ƙasa kowa jiki ya gama mutuwa musamman Mum data zauna dabas danko Tariq duk dauriyar shi yafara kwallah.

Shiko Abba jikin fara rawa dan dimauta
Waya yaciro yakira number Taufiq akashe duka layi kanshi.
Inalillahi wa'inna ilahirraji'un cewar Abba.

Muryar shi na haɗewa yafara magana a ruɗe.
Miyasa zakai mani haka Hussein miyasa zaka gujeni bayan kasan zuciya bazata iya daukaba ko korar da nai maka nasan kanada inda zakaje zan dingajin motsin ka shiyasa nai maka haka ɗana inason ka ban fatan wani bala'i ya sameka Hussein,kuma goben nan nai niyar yafe maka duk wani laifi dakai mani ɗana,sai yanzun nagane cewa ba laifin ka bane gaza biyayya dakai mani ashe kafini gaskia Hussein......

Kuka ya kece dashi mai sauti yana dana sanin kin karbar uxurin dan shi.
Ganin Abba na kuka yasa kowa yahau kuka domin basu taba ganin hawayen shiba a tsawon rayuwar su da mahaifin su sai yau.

Alhaji kayi hakuri mu ringumi Qaddara dan Allah.
Inji Mum itama kwallan take.

Kaicona Maryam da naki da'na na girmama ra'ayina akan cikar burin ɗana bayan nasan nidin zan mashi gata yaki aure tsawon lokaci,har ya fidda macen dayake so,ban duba girman shiba najuya mashi baya akan wani reason dina marar tushe bayan gashi shi Samir haryayi Ya'ya ashe zai iya rayuwa batareda Aminatu ba,na hana Taufiq yar uwar shi bayan shi Samir tashi yar uwar ya aura anya naima kaina adalci nafita hakkin ɗana kuwa?anya lamarin Aminatu da Hussein ba akwai babban rabo a tsakanin suba,shiyasa Qaddarori suke ta afkuwa saidai mai hankaline kadai zai gane hakan.!"

Dan Allah Abba kayi hakuri zansa ayi tracking asan wace kasa ya tafi.
Ayyah Tariq kasan Taufiq is so smart bazai bari agan shiba.

Nasan dai na cuci ɗana baita6a bijiramani ba sai akan Qaddarar shi baita yiman karyaba sai akan wannan lamarin duk da haka nakasa gane Aminatu Qaddarar shi ce,ɗana dana sani Jarumi mai aji akan kankanuwar yarinya ya susuce miyasa bangane hakan ba sai yanzun da Lukman yarasu nakara tabbatar da kilan rabone ya kashe shi saboda baida rabu ajikin Aminatu,hakan yasa naji araina akwai babban al'amari tsakanin Aminatu da Hussein.!"
Ya ida maganar yana kwalla masu dumi
Haba Alhaji sai magana daya kake taya hakan zaifaru sai kace mai duba.!"

Amman Mufida ke jahilace bakisan rabo na kashe mutun ba,ni kaina dan inada tsawoncin kwana shiyasa nakai haka,nafahimci kamar kinajin haushin ɗana ki aje makaman ki,ki ɗaure harshenki,sannan ki doɗe kunnenki dan ba abinda zigar baka zata kumayi akan ɗana."
Sukuku Mami tafara kama kanta.

Tariq inama ɗan uwanka zai dawo tabbas dana barshi ya auri Aminatu dakaina ba dan aike ba zannema mashi aurenta,Allah natuba akan shishigin danaso da kutse a cikin lamarin dakai kadai kasan gaibun shi ina kaunar ɗana Allah yadawo mani dakai cikin aminci kuma Allah yai maka albarka."
Ameen suka amsa banda Mami daketa kananun gunguni aranta,wannan kenan.


********Bayan sati ɗaya ba laifi nasamu nutsuwa kashi 70 cikin 100 alhmdullh.

Ina samu inci abinci kuma akai akai ina waya da Umman Lukman saina kara sabawa da ita sosai yau ina tareda Mama tana jana da fira duk dan ta kwantar mani da hankali sai ga Anty Hafsat tazo gidan mu,akai sa'a muna dariya dan labarin yasani dariya sosai,zan iya cewa first time dana samu dan nishadi araina tunda Lukman yarasu.

Salati tahau rafkawa tana sallallami,mi zangani haka ni Hassatu!yanzun Khadija dan rashin tsoron Allah dariya kukeyi ko?daman kukan munafunci kukeyi kenan ace yaro bai kulla sati biyu ba aƙasa shine ku harkun faracin duniyar ku da tsinke ko.?"

Harara na banka mata,jinike kamar in shaketa.

Haba Anty miye haka so kike mita ihu kamar maguzawa addu'a kadai yake bukata awajen mu.!"
Cewar Mama.

Yoh ai abinda kuke shine aikin maguzancin,kun rike dukiyar yaro kunzo kuna arerewa yanzun jibi kiga duk uwayen lefen nan mutanen nan sukace ku rike aikodan haka kun samu ko makokin wata kuyi kafin kufara cin karanku ba babbaka.!"

Mikewa Mama tayi ta isa wajen Anty Hafsat ta dafa kafadar ta tace.
Takaba ya'ta zatayi kenan? da kike maganar lefe kuma anci kinsan dukiyar shi muke bukata,in zaki iya kema kina iya yimashi zaman makokin koba komai aike uwace kuma suruka.!"

Ke Khadija ni zaki gayama magana kuma ba rike masu dukiya kukayi ba.?"
Anje anrike Hafsat kizo ki kwata insa kema kin rike dukiyar wasu kinciye baremu da kyauta aka bamu.!"
Nikike kira da Hafsat kuma dukiyar ubanwa naci.?"

Ba sunan kibane Hafsatu nace kuma dukiyata ni makiyiyar ki ta dubban kudi kika cinye,har zakizo kina mana burga.!"

Eh anci azo akwata in kin isa."
Ina romon yake Hafsat aini nafi karfin haka wlh."
Ke Khadija kada ki kara gaya mani maganar banza da wofi."
Takawo ma Mama wani irin mari ta rike hannun tai wurgi dashi.

Ke uwata ce angaya maki,kuma da ace kinyi gigin tabani agidana wlh dana baki mamaki,dan haka ja munafukar kafarki kibar mani gidana kin dauka bansan wainar da kike toyawaba kyar nike kallan ki,nasa zaki yarda makamanki ashe kidin baki rabewa to kisani daidai nike da zamanin ki.!"

Zuwa lokacin Anty Hafsat tarasa abin cewa niko sai smile nikeyi musamman idan idanuna danata suka haɗu sai kara kulewa take.

Nidai kika wulakanta ko Khadija wlh zaku gani sai kunyi kuka da idanun ku keda yarki."
Anzo wajen daman tuni nasan baki sona nida ya'yana,ta Allah batakiba insha Allah saidai muga alkhairi,kuma ni bani nufinki da sharri keda zuriyar ki.!"
Ni ina nufin ku yan iska tsinannu insha Allah saikun watse a titi.!"

Wannan kuma sai Allah yayarda kamar yanda kikace kin mani addu'a ke kuma mala'ikun rahama sun maki irin ta,cikin mu tawa zatayi saurin karbuwa,kije kitubarna Allah.!"
Mtsw taja dogon tsoki tabar gidan afusace.


*******Bayan sati biyu alhmdullh na saki jikina sosai na dauki Qaddarata kuma a yanda tazo mani,misalin karfe tara taimani wajen aikina,ina zuwa bada jimawa ba akaita zuwar man gaisuwa har abin yafara bi mani jiki kona fara damuwa saina dangana,fara duba patient nayi cikin nutsuwa saidai yau ba marassa lafiya sosai sadda sha biyu zatayi harna gama zaune kawai nike har zuwa daya aka tafi masallaci nima alwalla nayi na tada sallah.

Ina cikin sallah naji shigowar mutun office ɗina,har nagama sallah alamu sun nuna koma wanene zama yayi,naɗe sallaya nayi na aje gefe,ina juyowa nayi arba da Dr JJ yana bina da shu'umin kallo tabbas naɗan tsorota sai kuma na dake ina mashi kallan ko lafiya.

Beauty kina mamakin ganina ko?kibar mamaki nazo yimaki ta'aziya face to face sannan na jadda mamaki son da nike yananan ba inda yatafi.!"

Wani kallan tsana na watsa mashi na watsar cikeda da gadara nike takona na isa kujerata na zauna ina lilita a hankali irin isassar nan na kafe shi da idanuna masu yalwar girma,duk da ina danjin faduwar gaba kadan saidai ban bari ya fahimci hakan ba.

nayi maki kyaune ai nasan bazaki bata samun kamata ba,dole kiyi tsumayina.
Jin abinda ya fada ya fusatani dan nasan Allah ya bani wanda yafishi da komai musamman Ya Taufiq, daya gaya mani haka.
Get out of my office."
nace a tsawace.
Wani kallo yake mani yana nuna kanshi alamun shi.

Kana mamaki ne,wannan ai ba abin mamaki bane,dan na kori kaskantacce irin ka,sannan inasan injaddada gaya maka na tsaneka tsana mafi muni.!"

Gelele yayi yana kallona har saida ya zare glass din idon shi yace.
Ni kike gayama magana Caranci.?"

Call me Amina Yusuf Caranci,if u can understood.?"

Wow kin burgeni fa gaskia kinada karfin hali saidai da ace kinsan tarkunan da nike maki da baki ganganci maida mani bakar magana ba.!"

Ayyeh sannu ashe tarko? kayi takan ka JJ narigada nai maka nisa nahar abada kai kasan wannan dan haka maza kabar mani office ko insa azo ayi waje dakai.!"

Nifa kikace kinsan waye ni kuwa.?"
Junaid Jamil Kano (DrJJ) sai kuma me?
Kaga malam get out."
Mikewa yayi yana mani kallan tsana mai rudarwa ya gwadani da yatsa.

Kisani komai wayon amarya sai anlashi zumar ta,kuma matsawar bansa mekiba zan jefaki cikin kuncin dahar kigama rayuwar ki,kina zirarar da hawaye kisa wannan aranki da JJ kike magana.!"

Furzar da iska yayi ya fita yana bugo mani kofa rufe idanuna nayi sai kuma na bude ina zaro wayata wadda nasaka a recording dan tunda yai mani text naima kaina alqawali koda tari zaiyi sai nayi recording din shi,dagani JJ baida imani kuma zai iya aikata komai dan cikar burin shi,tinda harya iya dawowa rayuwa ta akaro na biyu tabbas ba Allah aranshi.
Saving dinshi nayi cikin wayata natashi matarnity naje ban jimaba naje wajen wata kawata a Lab,can najima ina dawowa na rufo office nashiga mota na tafi gida.

Koda nakoma gida su Mama na iske sunyi mana awara taji kayan yanke yanke sosai naci.
Nan aka hau yar fira da kannena munayi muna kallan wani tsohon film na Koyla saidai rabi da kwata bashi nike kalloba daga intina Lukman sai Ya Taufiq ya fado mani rai ko wane hali yake shida Abba ko sun shirya,sai kuma JJ da mugayen kalaman sa suka dawo mani a kwakwalwa dan guntun tsaki nayi na shige daki banjima ba ina gama waya da Asma'u na kwanta bacci ya daukeni,wannan kenan...




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E33&34




As Usual kusan kullin Tariq saiya nemi number Taufiq baisamu hakama Major Sarki yanzun duka gidan basuda wani buri daya wuce ya dawo gida.

Mum kuwa tun tana kukan rashin ɗan nata harta dangana aranta tasan haka Qaddara tazomasu dole suyi hakuri.

Major Sarki ne yai shawarar raba agents a sassa daban daban domin a dubo masa ɗansa saidai iyalansa sun nuna hakan ba mafita bane saboda duniya dafaɗi take,ta ina za'asoma addu'a itace mafita.
Shima zuwa yanzun ahakan ya tsaya yasan indai da rai tabbas da rabo yanaji aranshi insha Allah Hussein dinshi zai dawo gare shi.

Akwana atashi a sarar mai rai wasa wasa marigayi Lukman sunyi wata shidda da rasuwar su,abubuwa da dama kuwa sun faru musamman a caranci gidan su Amina.

Yan uwan Lukman ne sukazo da kokon barar su na auren Amina wa ɗan uwan Lukman ɗin Sadiq saidai mahaifin ta yabasu uzuri,akan bazaima yarsa dole ba amman amman su samu

Please Login or Register in order to submit comment