Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

watsa ruwa duk jikina yai sanyi wardrope din Mama na duba nayi sa'a da doguwar rigata ta material na saka ko mai ban shafaba na dauki jikka nayi dakina sai tunanin Ya Taufiq nike da kyal naci abinci.

Washe gari da azahur mukayi manyan baki Hafsat (Junior ɗita ta GG Kankia) da Mamar ta sukazo gidan mu.
Oyoyo nayi masu in rungume Hafsat jikina mukayi falorn Mama.

Dukawa nayi na gaida Maman Hafsat ta amsa yawwa Ya'ta gaskia baku kyauta mani ba ace kina aiki Katsina amman kizo agaisa bakiyi haba Aminatu kin kyauta kenan.?"
Umma dan Allah kiyi hakuri lokacin ne ke karanci amman insha Allah zanzo."
Allah yasa ya'ta.

Tashi nayi naje na kawo masu ruwa da juice sai dambun nama a flat,Zainab na dauke da tire ciki fruits ne ayanke sai kular abinci Masa da miyar agushe sai kifi a ciki ajiye masu mukayi muna masu sannu da zuwa nan fa na iske Umman Hafsat nata sababi da alama dagani har Mama tanada cikin mu.

Yanzun tsakani da Allah Maman Aminatu da saidai inji anyi aure har angama,zumunci yace haka aiko Baban Hafsat akakira zai sanar mani sai muzo biki,kuma ga wannan abun ya afku aida munje gaisuwa nidai ba'a kyauta manba gaskia.!"

Gaskia kam sam bamu kyauta ba,amman inamai baki hakuri laifina ne duk da komai yazo a cunkushe saidai insha Allah hakan bazai kara faruwa ba,ina mai kara bada hakuri."

Shikenan bakomai kuma Allah yaimata zabin kwarai mafi alkhairi,shi kuma Allah yajikan shi da rahama."
Ameen ya rabbi."

Abinci suka faraci ana yar fira tashi nayi na koma daki ina duba wasu aiki da zanyi ranar litinin cikin system dita.

Najima ina dubawa,shigowar Hafsat ta yanke mani aikin da nikeyi.
Antyna sannu da aiki."
ta ida maganar tana miko mani wata leda.
Lafiya lau yar kanwata,wannan fa.?"

Kiduba suprise."
Really.?"nace ina Murmushi.
Yes open it."

Budewa nayi ina waro idanuna wajen kayan sa ranane su biscuit chewgam sai kuma Invitation Card.
Kallan tuhum nike mata sannan na maida kallona a IV din.
Naga na bikin tane nan da sati biyu masu zuwa.

Iyeh yan matan ba angirma Allah ya kaimu lafiya naji dadin sosai,da kika kawo mani Allah yakaimu lokaci lafiya."
Murmushi kawai tayi wai kunya.
Kanin nawa ɗan wane gari ne.?"
Kano."
Masha Allah,nayi murnar wannan lamarin sosai Allah yasa muna cikin rayayyu.
Ameen Antyna.

Nan fa muka bude babin fira har saida Mama ta kiramu,koda muka koma falor har Baba ha dawo an gwada mashi yasa albarka nan suka gaisa da Hafsat.
Mikewa Umman tayi zasu tafi Mama na kara bata hakuri.

Gaskia kun maida mani kunya kuma insha Allah da wuri zanzo bikin ya'ta.
Allah yasa,ameen muka amsa.

Har bakin mota muka rakasu,wanda ya kawo su yajasu sukatafi nan Zainab ta dauko kular da takai mashi abinci muka dawo gida.


********Bayan wata ɗaya cousin din Mama Anty Zaliha ta haifi ɗa namiji.
Da kanta takira Mama ta sanar mata haihuwar,Baba na dawowa ta gaya mashi washe gari ita da Zainab suka shirya sukaje barka.

Lafiya lau sukaga baby sunjima can bayan la'asar suka fara shirin dawowa gida,ayam sai ga Anty Hafsat da Umaima.
Saida Umaima takira sunan kowa ta gaida ta banda Mama,ganin haka yasa Mama tacema Zainab su tashi sutafi gida kuma sun gaida Anty Hafsat itada Zainab ko amsawa batai ba.

Anty Zaliha ta mikoma Umaima baby tasowa tayi zata karba tana sane ta takema Mama kafa ta murza da karfi har saida yatsunta sukayi kara,kuma taki dagawa.

Kallan ta kawai Mama take kuma duk abinda takeyi uwarta na kallan ta.
Saida tabari ta mikama Anty Jaririn ta koma ta zauna,Mama tace.
Umaima bakiji kin takani ba.?"
Wani kallo ta watsa Mama taja uban tsoki.
Badake nike ba?
Cewar Mama.
Waike idan antaki saime? Ai nazata dutsi na taka shiyasa."
Mutuwar zaune Mama tayi tana al'ajabin lamarin Umaima.

Ke Umaima kanwar uwarki kike gayama wadan nan maganganun hakurine baki iya bata kome?tsararki ce.?"

Ke Zaliha kada ki kuskura kima ya'ta tsawa miyasa ta aje kafar da aka taka,tayi abinda zatayi.
Inji Anty Hafsat.
Umaima nikike gayama magana kina ikirarin kin ɗauka dutsine ni kanwar uwarki ni Umaima.?"

Eh kedin angaya maki sai kiyi abinda zakiyi,kuma kanwar uwa, uwace.?"

Lallai Umaima Mama kike gayama magana."
Ke dan uwarki waya saka bakin ki."
Tacema Zainab gata uwar tsoro.
Tashi Mama tayi tace,tashi muje Zainab.

Mikewa tayi Anty Zaliha nata basu Mama hakuri har Mama tafita bakin ɗaki Umaima tace.

Umma ta gaida aysha."
A fusace Mama ta tado ta dauke Umaima da maruka har guda biyu,ranta yagama baci.
Kan ubancan lallai Khadija ya'ta kika mara.?"
Eh ko akwai abinda zakiyi.!"

Cakumar Mama Anty Hafsat tayi da dambe harda Umaima sukaima Mama taro Zainab tashigar Mama,ba shiri yan barka suka shiga tsakani sai zabgama Mama zagi take tana tsinema Zainab.
Tinda aka arabasu Mama takama Zainab suka tafi gida.

Suna isowa gida ba kowa tajama Zainab kunne kada tagayama kowa koda Baba ne batace yasan da wannan zancen ba.
Koda nadawo aiki da daddare Zainab tazo ta rada mani abinda yafaru,nima shiru nayi tunda hakan Mama ta bukata.

Nasan batasan Baba yaji tayi fada da yar uwar ta,a ganin ta hakan abun kunyane kuma abin fadi a gari.
Sukuku haka Mama take hardai kowa ya kwanta lamarin ba dadi.

*******Washe gari week end duk muna gida Extra Lesson akema kannena Uncle Kamil shike koya masu Math&English sunjima sunayi har suka gama yabasu Home Work sannan yatafi.
Yana fita lokacin rana tayi Baba yatafi gidan Baba Hassan zai dibo shi bai lafiya.

Mu kuma muka shige falor muka hau kallan wani tsohon film na Trediv.

Mama na tsakar gida zaune cikin inuwa ita kadai duk abin duniya yasha mata kai.
Salatin da mukaji an rafka shiyasa mukayo waje baki dayan mu da gudu.

Anty Hafsat ce ta muƙama Mama wani icce a bisa baya, ita da ya'yan ta Umaima da kanwar ta.
Kamar andasamu haka muka tsaya cak,ganin abinda Anty Hafsat ta aikata.

Sake dagawa tayi zata bugama Mama iccen hannun ta bansan sanda na isaba na kwace shi nima na kwada mata shi,bisa kafaɗa.

Kwala ihu Anty tayi sai dambe ya kaure tsakanin mu sosai muke dakuwa nidai Anty Hafsat nike kaima duka na gaske Umaima suna dukana.
Mama tana gefe su Zainab sun rungume ta,salati kawai takeyi.

duk da taro sukaima mani saida na sage ma Anty Hafsat hannu dan ko ɗagashi ta gaza bare ta dukeni hannu nasa na hankade Umaima itama bahau jibgarta da iccen hannuna.

Salati ahakau rafkawa jinayi an ɗageni kamar baby Ahmad ne da Baba sai salati sukeyi,kuka nahauyi.

Baba kabarni in gota su,Mama suka duka batasan hawaba batasan sauka ba,kubarni in karyasu tunda suka bugar mani uwa.!"

Rungumeni tsam Baba yayi dan saikace banda hankali yanda nike fisge fisge ga Umaima magashiyan hakama Anty Hafsat na kwarara ihu.

Da kyal Baba yasamu nadawo hankalina rungume Mama nayi dake kwaranyar da kwalla.
Dagata mukayi nida Baba muka kaita falorn shi.

Kutashi kubar mani gida wlh Hafsat kinci darajar zumunci da sainasa ya'yana sun karya mani ke tinda da kafarki kikazo har gidana kika dukar mani matata."

Ku shigo mukaji ana cewa,Ahmad ya ɗauko yan sanda su ukku sai mace daya a cikin su.
Mamaki gayama kashe Baba ko magana ya gaza tsabar mamakin Ahmad.

Ku kamasu su ukkun nan har gida suka shigo suka dukar mana uwa.!"
Hannu yar sanda tasa ta dago Anty Hafsat daketa kuka dan hannunta koban karya shiba tabbas a goce yake.

Ahmad abarsu inji Baba.

Wlh Yusuf sai ankaisu yanzun aka sameni aka sanar dani abinda ja'irar yarinyar nan ta aikata kedai Hafsatu so kike kiyi ajalina ko?
Cewar Dada.
Duk yanda Baba yaso yashawo kan Dada taki tace muddin ba'akai Anty cell ta kwana ba tabbas saita tsinemata.

Dan dole Baba yasama sarautar Allah ido yasan dai wannan rigimar tazama abin gori wajen mu musamman ni za'adinga cewa nice na bugi yayar uwata saida na gotata.

Dan unguwar tamu cike take,haka aka fita dasu Umaima,Dada sai zunduma ma Ahmad albarka takeyi.
Muma mota aka samu muka bisu zuwa police akayi satatement kowa ya fadi abinda yasani kaf.

Sai gab da magrib muka baro police duk yanda Baba yaso abashi Bell dinsu anki dan dole mukabar su,kuma mijinta yace ba abinda zai kashi wajen yan doka duk tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa ka doka.
Koda muka dawo gida fada sosai Baba yaima Ahmad banda Mama daketa zirarar hawaye dagani kasan bana dukan bane bakin cikine cunkus a cikin zuciyar ta.

Sai lokacin Baba yaji tausan ta ainun,aka kira mai kamu mace matar sarkin fawa tazo ta duba bayan Mama saidai tace ba karaya ba gocewa magani tabada aka shafa nata da robb mai zafi tajima anagama isha'i tayi bacci marar dadi.

Kana haukane Ahmad kasan abinda kajawo kankai kuna fada da wani za'ai maka gori ace ai daukowa yayar mahaifiyar ka yan sanda waiku baku guduna abin gori kodai kuruciya ke damunka?ina laifin kubarta da halinta kai zakaji dadi ya'yan ka sukai Aminatu ko Zainab wajen yan sanda.?"

Aaa Baba kayi hakuri."
Haka yau zuciyar mahaifiyar ku take bakikkirin ku kiyaye gaba,kema Mamana indai rigima ce tsakanin ta da mahifiyar ku na haramta maku shiga sabgar iyaye kinajina.?"

Eh Baba bazan karaba insha Allahu nima duk na shiga damuwa bansan ina hankalina yatafi ba dana duki Anty Hafsat,ina tsananin jin kunyar hada ido da Mama haka itama inajin nauyin ta dan Allah Baba katayamu bawa Mama hakuri tabbas munsan mun zalince ta,dahar muka shiga rigimar su da yar uwarta.!"

Hakanan naji hawaye sun zuraro mani na tsananin tausayin Mama.

Insha Allah Mamana zata yafe maku amman kada ku kuskura ku kara aikata wannan kuskuren yan uwan iyaye ba abin wasa bane suma iyayen kune kunajina.?"

Eh Baba insha Allah,mukace hatta Ahmad duk jikin shi yai sanyi tabbas yai dana sani.

Haka kowa yatafu daki ba wata lakka a jikin shi,itako Mama nan mukabar ta falorn Baba tana bacci tare da sauke ajiyar zuciya mai zafi,wannan kenan





_Yar Mutan Kankia ce❣️_





Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E39&40




Washe gari da safe tunda natashi na gyara ɗakuna na shiga kitchen nafara hada kalaci sadda tara zatayi nagama hada komai,wanka kawai naje nayi zuwa goma nazuba nawa nahauci haka kowa yaci nashi fitowar Mama kenan daga dakin ta,gaidata mukayi saidai ta amsa ta kowa banda ni da Ahmad.
Baki daya jikin mu ya sakeyin sanyoi ganin da gaske dai Mama fushi take damu.

Zainab zoki kaima yar uwata abinci tinkan yunwa ta illata mani ita."
Toh cewar Zainab ta tashi hijab tasako ta dauki basket din abinci doya da kwai sai kuma fersun anta da akayi,tafiya tayi devision wajen Anty Hafsat.

Nida Ahmad duk jikin mu yagama sanyi tsabar karaya matsawa mukayi gaban ta kasan kafat mukace.
Mama dan Allah kiyi hakuri munsan munyi kuskure insha Allah bazamu sake aikata wannan laifin ba muntuba."

Wani kallo ta sake watsa mana mai kashe sassan jiki baki ɗaya.
"Mama dan Allah kiyi hakuri wlh nayi nadamar abinda na aikata insha Allah bazan kuma aikata makamancin saba koda amafarki ne kiyafe mana dan Allah.!"
Cewar Ahmad da idanun shi suka kada jajir tsabar facin rai da fargaba

Bazan yafeba har sai kun dauko icce kunyimani dukan tsiya sannan ku kira mani yan sanda sukaini cell idan kukai mani haka nayafe maku duniya da lahira."

Ai jikin mune ya kara sanyi bamusan mun daura kuka ba munaci gaba da bata hakuri.
Mu dukan mu munyi danasi iya danasi danko Ahmad kana ganin shi kasan yayi regreating sosai,hakuri mukaci gaba dabata muna kuka
"Dan Allah Mama kada kiyi fushi damu mun rokeki kiyafe mana."

Ganin ko magana bata da niyar yimana duk mika sake shiga damuwa,motsin bude kofa mukaji nida Ahmad mukayi wajen Baba da fitowar shi kenan daga bedroom dinshi muka rike shi sai kuka nike mukahau begging din shi

Dan Allah Baba katayamu bata hakuri ta yafemana bamu sakewa muntuba dan Allah Baba.
Dawowa damu yayi cikin falorn duk muka zauna kasa kowa jikin shi yayi sanyi sosai.

Muna zama Mama ta mike zatabar falorn Baba ya rike mata hannun.
"Haba Nana Khadijatu yar aljanna kiyi hakuri mana nasan yanda zuciyar ki take cikeda alkhairi kiyafema ya'yan ki tabbas sunyi babban kuskure amman tunda sun tuba kiyafe masu na rokeki matata.!"

Komawa Mama tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri hawaye suka ziraro mata ta goge.

Kiyi hakuri Khadijatu kiyi koyi damai sunan ki mana,kidaina damuwar nan dan Allah kiyafe masu rokeki.

Hmmmm haba Alhaji taya bazanyi kukaba ace ya'yana na cikina su kama yar uwata su buga uwa ɗaya uba ɗayafa ba wasaba sannan hakan bai ishesu ba harda kiran yan sanda yanzun ni ina gida zaune ita kuma tana cell inalillahi wa'inna ilahirraji'un!."
Gaskia basu kyauta ba basu da hurumin shiga rigimar ki da yar uwar ki amman Qaddara ta riga fata kiyafe masu tinda sungane sudin masu laifine kuma sun tuba,kuma nai masu fada sosai ni kaina banso hakan ta faruba baccin Dada datace sai ankaita police banso case din yakai can ba kiyi hakuri.

Baban Jidda koda Dada tasa atafi da ita da ace Ahmad bai kira yan sanda ba na tabbta Dada bazatayi tunanin kiran yan sanda ba,daman haka rayuwa take ka haifi ya'ya baka haifi halayen suba.!"

Dan Allah Mama duk abinda kikace shi zamu dingayi mudai kiyafe mana muntuba bazamu sake ba.!"

Magana zatayi Baba ya ɗan kalleta domin gaskia Mama ranta ya baci bamu taba bata mata raiba irin nayau ba shiru tayi sai kuma tace.
Shikenan zan yafe maku amman inada sharadina da zangindaya maku.?"
Eh munaji zamuyi.

Idan aka sako Anty Hafsat inaso kuje har gidan ta kubata hakuri kunajina.?"
Eh munji zamuje Mama mungode.

Shikenan Allah yai maku albakarka ya kyauta gaba."
Ameen duk muka amsa sai lokacin muka samu sassauci a cikin zukatan mu,kowa yai shiru Baba yace.
Wai ina Zainab take.?"
Tana Police na aiketa kaima Anty abinci.

Shiru Baba yayi yana kallan ta baice mata komai ba inda dane kafin wannan abun yafaru saiyayi magana amman dayake so yake ya shawo kanta sai baice komai ba.

Cigaba da nasihohi Baba yaimana mai ratsa sassan jiki,yana nuna mana darajar yan uwan iyaye da girman zumunci yana cikin mana nasihohi saiga Zainab tadawo saidai kallo ɗaya zakai mata katabbatar da yanayin ta ya sauya kowa ya fuskanci hakan aka share lamarin Zainab musamman Mama da batason adata maganar ko kadan.

Kindawo Zainabu A'bu.?"
Eh Baba sannu da hutawa.
Yawaa ya'ta ya Antyn taki?
Lfy lau take."

Sallamar mu akayi direct daki na wuce na kwanta saboda ciwon kan daya addabeni Zainab ce ta shigo dakin ta zauna gefena cikin raɗa tace.

Anty kinsan mi Anty Hafsat tace.?"
Girgiza mata kaina kawai nayi.

Wai ceman tayi to yar iska tsinannu anzo aimani bin kwakwaf to da sauran raina ban ida mutuwa ba.
Hakuri nabata na mika mata abincin,shine ta bude sai kuma tace wai ammata barbaɗe ta Allah batamu ba,kuma saida dan sanda yasa naci abincin sannan aka bata na taho,gaskia banji dadi ba Anty Amina raina ya baci.!"

Kiyi hakuri Zainab dole muyi hakuri da halayen Anty itama tana cikin Qaddarar mu,kuma kada ki bari kowa yaji wannan labarin koda Mama ce.
Shikenan Anty ba wanda zan gaya mawa.

*********wasa wasa kwanan Anty Hafsat ukku a cell ba yanda ba'ayi da mijinta ba yace bai zuwa Bell dinsu hakama Dada tace ya'yan ta ba wanda zaije duk wanda yaje Belling dinta bata yafeba dolen su suka kyaleta.

Ita kuwa wahala ta isheta ba yanda ta iya dole ta bada numbar Baba tace yazo ya fiddota,bakaramin mamaki yaiba acewar shi ansaketa.

Tafiya yayi zuwa station din yai Belling Anty Hafsat dasu Umaima har gidanta yakaita,yabawa mijinta hakuri sannan itama yakara bata hakuri abinda muka aikata,daga gidanta,gidan su ya wuce gaida step mother dinshi da yamma ya dawo gida.

Da dadddare muna zaune falor kowa da sabgar gaban shi,Baba yace ansaki Anty Hafsat.
Murmushi fal a fuskar Mama tace.
Alhamdulillah kutashi muje munemi afuwarta.

Aaa Maman Zainab kibari saida safe mana.?"
"Aganina kasan ance dare sirrine kamar hakan zaifi ba tareda ansan abinda ke faruwaba.

Hakane kema kin kawo taki shawarar kuje saidai bansan ku wuce karfe taran dare baku dawowa ba.

Insha Allah,cewar Mama.
Da haka muka dunguma zuwa gidan Anty Hafsat neman afuwa.

Muna isa gidan wani matsiyacin kallo suka watso mana ita da ya'yan ta, ko amsa sallamar mu basuyi ba,jiki sage muka karasa dakin ta,muka sake sallama Baban su dake can cikin Sitrum din shi ya amsamu yana sannunku da zuwa shima falorn ta ya shigo ya zauna,duk muka gaidashi ya amsa cikeda fara'a.

Wani kallo Mama ta aikamana aiko duk muka gane abin da take nufi nida Ahmad muka duƙa gaban Anty muka hau bata hakuri.

Anty dan Allah kiyi hakuri munsan abinda mukai maki bamu kyauta ba ki dubi girman Allah kiyafe mana muntuba dan Allah Anty.!"

Kunnen shaggu tayi damu kamar bada ita muke ba.
Anty mun rokeki kisamana albarka kiyafe mana munyi kuskure bazamu kumaba har abada.!"

Cewar Ahmad data watsa mashi matsiyacin kallo dan dole ya sauke kanshi kansa.

Zuwa lokacin nafara ƙulewa ganin yanda muke bata hakuri amman tayi kunnen shaggu damu naga ko uwar mu da mukaima laifi munbata hakuri kuma daga baya ta yafe amman maganar da mukai tafi goma kamar muna neman aljanna.

Riko hannunta nayi ina cigaba da bata hakuri.

Anty kunya da nauyin ki sun gagari in haɗa ido dake dan Allah kiyafemana ko munsamu sassaucin abinda mukeji ran mu tabbas munsan mun aikata abun kunya amman kiyafemana kodan surutun mutanen gari dan Allah Anty."

Sakar mani hannu yar iska ni zakima tambaɗa da bariki, ki dukeni sannan ɗan uwanki yakaini gun yan sanda duk akan uwarku wato ku kunsan zafin uwa niko dayake daga sama na diro banda uwar aka rufeni harda ya'yana ku kuwa ya'yan so shafaffu da mai yan gata aka barku kuka kwana cikin jindadi,kwanana ukku ubanwa ya hana kubini can police din kunemi yafiyata sai yanzun dana zama mutun nadawo muhallina wlh Amina saikin haɗu da bala'i masifa a cikin rayuwar ki,kai kuma Ahmad yanda kakaini station da hannun ka, kai zakakai uwarka Khadija gun yan sanda tambaɗaɗɗu watsastsu.!"

Araina kuwa neman tsarin Allah nikeyi akan jafa'in da take turomana nida ɗan uwana,Mama kuwa ranta yakai karshe gun baci yanayin ta kadai zaka kalla ka tabbatar da hakan.

Haba Hafsat ya'yan yar uwarki kike jifa da Jafa'i waike wace irin Kafura ce baki da imani a kirjin ki ko kadan kin manta ke da kafarki kika iske ta har cikin gidan ta keda ya'yan ki kuka duketa dan sun rama har laifine ita bata tsinema ya'yan kiba kike tsinema nata,wlh Hafsat ki guji ranar da mugayen kudirin ki zai fara bibiyar ki,ina saura ma tunda ga Umaima ta zama karamar bazarawa kugunki danata ai wannan kadai ya isa abin kunya.!"
Cewar mijin ta.
Murguda mashi baki tayi tana hararmu nasan da Anty nada dama tabbas zatayi ajalin mu musamman ni.

Insha Allah ba Jafa'in da ya'yana zasu gani kake maganar Umaima tazama karamar bazawara kanta farau ko karau kuma data zauna tayi cun6u a gida ai kwara taje tasan miye auren ga albarkar aure tunda ansamu rabo har in dauka in gwada ince jikana ne wasuko sai karyar arziki saidai aci aje a gundura katon kashi kaɗai akasani.!"

Wannan statement din nata dariya ya bani kannewa kawai nayi dan wlh da ace ba Mama a wajen tabbas inayin dariya ta.

Khadija kiyi hakuri yar uwarki da kike gani shaidaniya ce batasan harkar arziki ba,nagode maki da kika tiso ya'yan ki dan sunemi afuwa kuma Allah ya shaida ya gani Allah yaimaku akbarka Aminatu kukara hakuri da rayuwa haka Allah yaso watara sai labari,kunji ya'yana."

Jinjina kai mukayi mukace ameen Abba mungode.

"Yaya bai kamata inbar gidan nan hakaba batareda na sasanta da yar uwata ba,nabarta tagama faɗin ta cikin ta domin kuwa an zalinceta kuma bai kamata a duki mutun ba sannan a hanashi kuka ba,fatan zaka fahimce ni dan Allah.!"

Hakane Khadija Allah ya sasanta kuma ya kyauta gaba.
Ameen Yaya.
Maida kallan ta tayi wajen Anty dake cika tana batsewa tace.

"Anty Hafsat nasan idan yau na kwanta damata na mutu ke mai kulamani da ya'yan dana barine,ke mai saka masu albarkane a matsayinki na uwa dan Allah kijanye mugayen kalaman da kike masu kisa masu albarka a gaban idona kafin in rasa raina dan nasan tabbas Khadija tabarmu su Aminatu uwa ta gari dan Allah Anty.!"

Tabb ai wlh bazan sama waɗannan watsatsun albarka ba wa'anda basu da banbanci da ya'yan zina.!"

Ba Mama ba dagani har Ahmad bamusan sanda muka mike tsaye ba jikin mu na bari tabbas lamarin Anty Hafsat yafi karfin duk tunanin mai tunani.

Shiko Ahmad ganin an sheganta shi baisan yafara kwalla ba ya juya zai fita Mama tace.





_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️



_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E41&42




Idan ka kuskura kabar gidan ban yafe maka ba Ahmad.!"
Cak ya tsaya jin kalaman Mama,jiki sanyaye ya dawo ya zauna jijiyoyin kanshi kuwa sunyi raɗo raɗo zama yayi Allah kadai yasan abunda yakeji a cikin zuciyar shi.

Ke Khadija kinada hankali kuwa akan wannan marar arzikin zakinemi yima ɗanki baki amman dai kin cika wauta gaskia."
Cewar Baban su Umaima.

Shiru Mama tayi saida murmushin data kakaro wanda ake kira kafi kuka ciwo.

Toh Anty nasan inkika huci tabbas nasan zakiyi hakuri amman a madadin ya'yana muna baki hakuri Allah ya tsaremu daga sharrin shaiɗan ."

Ai kece shaidaniyar Khadija wake gata Allah ni har akwai burgar da zakuyi mani ai babu ita wlh,kuma daga yau kada inkara sake ganin tsinannun ya'yan nan naki gida na dake kanki in kunne yaji.!"

Haba Anty wake wace marar imani ce tun dazun Anty Khadija da ya'yan ta sun baki hakuri amman sai kace mai zuciya irin ta kafiran farko wai shin ke uwartace nace ke Dada ce da zatace inbaki yafe mataba ta shiga ukku ko Dada iyakar abinda zataimata kenan bareke yar uwa,wlh ke kika fisu duk abinda kukeyi najima a zaure naji komai ke kuma ki maida hankali kima ya'yan ki baki akan wadda batasan arziki ba.!"
Kawu Usman kenan keta faɗa ji yake kamar yaima Mama duka data dage kan ba Anty Hafsat hakuri."

Kai Usman ni ba tsarar ka bace zan baddaka ka isa kazo gidana kana mani hauragiya da 6a6atu ku tattare inaku inaku kubar mani gidana.!"
Kema kuwa yau dinnan da baki kwana da igiyar auren kiba wlh.!"

Baki dayan mu muka mike mika hau bashi hakuri banda Kawu dakejin haushin yar uwar tashi,da kyal Mama tashawo kan mijin ta.

Duba agogo mukayi shaɗaya saura kwata (10:45) mun tabbata Baba yagama ƙulewa shida yace kada mu wuce karfe 9 amman muka shantaƙe.

Hmmm shikenan Anty Hafsat zamu tafi kuma kisani ni Khadija nayafe maki keda ya'yan ki abunda kukai mani duniya da lahira Allah ya yafemana baki daya,kutashi muje gida dare yayi."
Mikewa mukayi mukai masu sallama sai bala'i take.
Daman kicema baki yafeba kiga wazai damu aikin banza aiki wofi yan iska matsiyata.!"

Mijin tane ya biyomu a hanya yana bamu hakuri har kofar gida anan muka iske Baba da alamu muyake jira gaisawa sukayi sannan mukai mashi godiya muka shiga ya rufe kofar.

Shiko Kawu muna fitowa gida ya wuce ranshi a bace.

Duk mun tsargu saboda mun karya dokar Baba amman bai nuna nama komai ba,amman yanayin mu ya nuna mashi ba nasara shiyasa baice komai ba saida zamu wuce yace, Allah ya kyauta gaba ya sansanta.

Da haka kowa yai daki ina cewa amin.
Wannan kuma dabi'ar Baban muce daya kalli yanayin mutun yake gane nasarar lamari ko akasin haka,musamman idan baisan jin yanda akayi saidai yai addu'a kuma yabar zancen har abada.

Ina shiga daki naga miscall birjik awayana harda na Dr Siddi yakirani karfe goma da rabi,jikina a mace nabi kiran shi.

Dr Aminatu ina kikar wayarki anata kiran ki call,karfe shabiyu za'a shiga theater.!"
Hakanan naji kasala ta saukar mani,yanzun nagani,am sorry Sir.!"

Kishirya ga mota nan za'azo a daukeki ya kusa isowama"
Ok Sir."

tashi nayi na iske Baba falor yana Kallan news dukawa nayi nagaida shi.
"Baban zanje asibiti inada call yanzun haka antaho daukata.!"

Shikenan Aminatu ai aikinki ga gaji haka ba dare ba rana kowane lokaci ya taso dole kifita dan ceton rayuwar al'umma Allah yasa a mizani kuma yakareki daga kowane sharri duniya da lahira yaima rayuwarki albarka Mamana."
Ameen Baba nagode,Allah yakara girma.

Wani karfi ya lullubeni take, duk wata kasala da gajiya sun tafi Mama naje sanarmawa ta samani albarka sannan na shiga wanka ina fitowa yakirani gashi kofar gidan mu,ganinan fitowa nace.

Kaya kawai na saka na dauki lapcourt dita da system bna fita Baba ya rufe gida yana mani fatan alkhairi driver yaja muka tafi Katsinan Dikko har asibiti 11:40 muna ciki tsindum aiki kawai zamufara gadan gadan...


********Kaduna

Zuwa yanzun Abba ya dangana da tafiyar Ya Taufiq saboda duk inda ake tunani an duba kuma kullin wayoyin shi akashe suke basu aiki har Usama ya kira ya tambaye shi amman yace basu waya dashi.

Addu'a kawai yasa ana mashi masallatai da sauran tsangayu ana sadaka Allah ya yakado hayyacin shi gida,idan kuma ya rasu Allah yagafarta mashi,haka kuwa aka dukufa da addu'a ba dare ba rana.

Itako Mami bata da wani kuduri sai ganin Ya Taufiq ya farraka har abada kada akara

Please Login or Register in order to submit comment