Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi."

girgiza kanshi yayi yace.
Ina kina zatan hankalina zai kwanta matsawar Taufiq bai kusa dani kuma cikin lalaura,ba wanda zai bishi saini,Tariq yai zaman shi wajen iyalin shi,sunada bukatar shi,ni nawa iyalin sunada jigo ta kowane fanni,kinji yanda za'ayi kwara Khairatun sai aje da ita tunda matar shi ce."

Allah yasa nan dinma adace kafin akaiga zuwa can din."
Ameen,sorry na tasoki cikin dare gashi har 12 pm muje in rakaki side dinki ko kuma kawai ki kwana anan din."
Shikenan Allah yasa mudace,ameen
Suka kwanta.


Bayan sati daya Doctor Asim ya kaima Alhaji tabulet na magungunan Taufiq,yaji dadin ganin maganin saida yakara jadddama Sarki illar lalurar, sannan yai mashi sallama ya tafi,bai jima da fitaba Tariq ya shigo yana gaida mahaifin nasu ya miko mashi leda,ka kaima ɗan uwan ka wannan."

Amsar ledar yayi ya juya zuwa gidan Taufiq kai tsaye side dinshi ya wuce,falo ya same shi zaune,ko zama baiba ya sako mashi maganin bisa jiki,yana daure fuska yace.


"Bansan ɗan uwana da lalura makamanciyar wannan ba,miyasa sai ta wannan hanyar kadai zaka samu ka rabu da Khairat anya Hussein kaima kanka adalci.!?"

Mikewa yayi ya dafa kafar Tariq da sauri ya bige hannun Taufiq ya watsa mashi wani kallo,shiko murmushi yayi yasan muddin Tariq yaji wannan case din sai sunyi ta badadi.

Hassan bakasan lalura na iya zuwa lokaci daya ba miyasa kake zargina.?"

Afusace yace.
Karya kake Hussein nasan duk shirin kane,wlh nasanka nasan hankalin ka, idan ka tsani abu komai zaka iya aikatawa saidai kasani wannan lalurar daka kirkirarma kanka,ta hana Abba sakat kullin cikin zullumi yake,baka zatan idan ya gano karya kake shirya masa bazai iya tsinemaka ba.!"

A'uzubillahi tir da kalaman ka Hassan!insha Allah mahaifina bazai taba tsine mani ba dan kawai ina nemarwa kaina mafita.!"

Anzo wajen ashe dai karya kake,wlh Hussein ka bata komai kasan halin da Mum zata shiga muddin aka ganoka lallai kam zakayi 2/0 kenan ba Amina kuma ba Khairat dan haka in bacci kake wlh ka farka tun wuri.!"

Murmushin takaici Taufiq yayi yace.
Wannan hanyar ita zata bani damar mallakar Minal, ita kuma Khairat ta samu mai sonta.!"

Uhmm bayan duniya tagama shaidawa kaidin ba lafiyayye bane shine kake fadar haka?"
Sai kuma aka cemaka zan dawwama a lalurane.!?"

Hussein kenan Allah kada ya kawo bacin rana ina tausayin ka ɗan uwana,nasan wannan rana bamai kyau bace amman kaji tsoron Allah kullin zuciyar ka mai kyauce amman wannan karan kanka kawai kasani ka cire tausan kowa da komai a ciki kuwa hardana mahaifiyar ka domin duk wannan abun kanta zai kare kasan Abba baida afuwa musamman yayarda da mutum ya ha'ince sa kaiko ba komai kake shiryawa ba sai ha'inci da dai kai using wannan formula din!
Dafa kafar Taufiq yayo yace.
Inabaka shawara kwara kai tsaye ka saki Khairat zai fika maka sauki akan wannan wasan kwaikwayon dakake shiryawa.!"


Kace Abba ya tsinemani kenan.!?"
Ai abun da kake shiryawa shi zai saurin fusata Abban yai maka baki,inko sakin ta kayi nasan zai gyara komai cikin sauki.!"

Look Hassan ya isa kada kasa kaina ya tarwatse.!"
"Wlh yafi maka sauki akan ranar da nike jiye maka zuwan ta Hussein."

Sallama suka tsinkaya baki dayan su suka waiga musamman Taufiq yanda ya raina gaskiar shi ganin Khairat murmushi kawai tayi.

"Ayyah yan uwa aminnai na sirri na shigo ba neman izini kuyi hakuri Ya Hassan barka da safiya."
Ah ah bakomai Antyn Aira dafatn kina lafiya.?"
Alhmdillh,ya mai jikin.?"
ta tambaya tana kallan mijin nata,shima Tariq wani kallo yai mashi yace.
Da sauki na kawo mashi suppliment zanje wajen aiki sai anjima."
Okay Allah ya tsare mungode.

Fita yayi yabar su,ranshi a bace ya rasa kalar halin Taufiq mizaisa bazai dauki Qaddarar shiba ganin shi wannan rashin tauhidine da son zuciya,wannan kenan.


Bayan wasu watanni da suka shuɗe lalurar Taufiq ba wani abu daya sauya ba kulawar da yakeba Khairat wannan karan kam takai karshe wajen hakuri sake samun shi tayi da batun ko kulata baiba haka taita sababi tana kuka.

"Ka daukeni kamar ba mace ba wace irin lalaura ce wannan da har zai hanaka sauke mani hakkina baka kulani Hussein bakacin abincina sau nawa kataba zuwa part dina saunawa kadamu da damuwa ta,koda nidin ba desire dinka bace amman yana da kyau ka kula dani,angaya maka samun makwanci mai kyau,sutura,abinci ko kudi sune kadai damuwa ta,kaine matsala ta bawai tarin dukiyar kaba,sau nawa kasan irin son da nike maka miyasa kake nuna tsana gareni Taufiq.!"
Wani marayan kuka ta sake saki mai sosa zuciya.

Shi kanshi yaji bala'in tausayin ta,duk da bai magana ba,hakan bai hana rikota ba,ya zaunar da ita yana share mata hawaye ba.

Kiyi hakuri Khairat kema ki dauki taki Qaddarar bansan taya zan koyawa kaina sonki ba,ni nasan komai ke faruwa dani Qaddarata ce,ina mai baki shawara ki hakura da duk komai nawa,Allah yasani bansan inci gaba da hurting dinki.!"

Duk jiran da naima wannan ranarta tashi a banza kenan Taufiq? Shikenan sai in rasaka.!"

Kwarai kuwa Khairat kinemi alkhairi nasan Allah zai baki wanda yafini komai nidai kam gaskia banjin zan iya.....

Dakata Taufiq naji abinda kace saidai banji wannan Qaddarar kace kasama ranka kawai tsanata da kina wannan shi ne ainahin gaskia.!"

Tafiyar ta tayi tana jin zafi aranta mi tarasa da mijinta zai mata haka dame wadda yake ikirari tafita dashi wannan wace irin Qaddara ce!


*********Central Market Katsina na tsaya a wani super market ina hada provision na gida kayan tea na dauka da sauran abubuwan bukata,yaron shagon ya daukar mani kayana zuwa mota a boot ya saka naja zuwa gida dan daman natashi aiki dama wurin karfe biyu daidai.

Ina cikin driving hankalina kwance banda wata damuwa araina Ahmad ya kirani dagawa nayi kasancewar kunnena nada head phone.
Doctor Amina barka da rana gimbiya ta."
Yawwa ya aiki.

Natashi inasan in sameki ko kina office.?"
Aaa natashi gaskia yanzun haka na kawo Ɗandagoro."
Okay gaskia inasan muyi muhimmiyar magana dake Amina ko zaki iya bani time.?"
Eh badamuwa saidai kabari gobe insha Allah idan nazo office zan baka time."
Thank you so much."
Ina hanya anjima zamuyi magana."
Okay,bye.


Cigaba da drivern nayi inajin cast din kira'ar Sheik Ahmad Sulaiman Kano Suratul Bakara inabi a hankali,har na iso gida ina parking na shige ciki da sallama bakina.

Oyoyo cewar Zainab data fito da gyale duk da bansan inda zataje ba.
Anty sannu da zuwa,yawwa Zee Zee anshi key akwai kaya boot kwaso su."
ansar key din tayi na ida shigewa ciki,zaune na iske Mama ta gama sallah gaishe ta nayi.

Har andawo.?" Eh Mama
Sannu da gida,mi aka dafa.?"
Shinkafa da miya ce."
Sannu Mamana

Shigewa ciki nayi na shiryowa nayi cikin pink din doguwar riga nayi kitchen dan samun abinda zanci,na kwashi yunwa,saida naci nai nak Mama ta maida kallan ta gareni tace.

"Aminatu nikam sai nike ganin izuwa yanzun ya dace ace kin fiddo miji kiyi aure,kinsan shirun Baban ki,baida dadi tunda kinga alamu sun nuna cewa ya janye kudirin shi akan ki saiki hanzar ta ki fidda wanda kikeso kiyi mashi bazata tunkan shi ya baki mamakin da bakiyi zato ba.!"

Shiru nayi ina nazarin wanda zan fidda a halin yanzun ban tareda kowa sai Ahmad shima shawarar da Husna tabani ita nabi daya dawo mani da tayin soyayyar shi na karba,wannan yana nuna infiddo Ahmad kenan,to inshi na fidda Baba zai aminta da zabina.?!"
Shikenan Mama insha Allah zan fidda."
Allah yasa yai zabin ba kwarai."
Ameen
Ciki na koma naci gaba da nazarin maganar Mama araina.



_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E19&20


Misalin 9am,na isa office banfi minti ashirin ba nafara attending patient duk wanda numbers dinsu ya fado ta office dina, nike dubawa nida Dr Fahad mu kadaine available shiyasa aikin yai mana yawa sosai,one by one ake shiga kowa da matsalar shi,ina cikin duba patient wata baiwar Allah ta shigo matashiya ce bata wuce shekara sha huɗu kana ganin su kasan yan kauye ne ita da wata matashiyar mace itama bazata wuce shekara ashirin da biyar ba tallabe take da patient din,kana gani sunyi kama da juna da gani ya da kanwa ne.
Zama patient din taya tana facing dina mai rakiyar na daga gefe daya.

Mike damun ki.?"
Na tamabayeta.
Fitsari ke kubce mani ko wane lokaci."
Da shakakkar murya tayimin magana."
Shekararki nawa.?"
sha huɗu gareni."

Ansar katin ta nayi naga tana da aure amman dayake aikin mu ya gaji tambaya ga patient dinka sai nace mata.

Kinada aure.?"
Eh inadashi" kinjima da yinshi.?"
Shekara ɗaya kenan."
Tin kinada 13yrs kenan kikayi shi."
Eh."

Kallan yar uwar tata nayi nace.
Micece ita a wajen ki.?"
Ya'ta."
Kallan mamaki nai mata dan baka cewa tayi ya' da ita,dan zatayi tsarata matar dan bata wuce ashrin da shidda ba,ko da ta girmeni kila tabani shekara.

"Amman yarinyar nan Yoyon fitsari ke addabar ta dalilin auren wuri da akai mata miyasa kuke aurar da ya'yan ku suna da kananun shekaru.?"

Malama ba haka bane itadin ma tadanyi kwari sha ukku fa,idan muka barta za'a zage mune shiyasa."

Wani kallo nai nata nace zagi kuma a karamar yarinyar kike cewa haka."
Eh Malama."
Rasa abin cewa nayi nafara bin cikar ta sannan ba rubuta mata magunguna.
Gashi akaima mijin ta tunda shine silar ciwon asai komai abata tana sha kinajina.?"

Malama yaron nan bazai siyaba tunda lalurar nan ta sameta ko ɗakin ta bai shiga sai yace tana wari karshe gidana ya dawo mani da ita ko zuwa baiyi, yasin yanzun haka lahadi zansaida ɗan bunsurun ta sai asai mata magani da kudin."
Wani takaici yakara kamani jin sakaran zancen da takeyi
mani cewa nayi.

"Ai harda laifin ku,da gangan zaku aurar da ya'yanku tun suna kanana dole su tsinci kansu cikin wannan halin yakamata ku daina yima ya'yan ku auren wuri yanzun kinga tun tana karama ta samu matsala shi kuma ya gudu bai damu da itaba saboda tana zarni ga ƙari yaka mata ku gyara shi mijin nata zaikai shekara nawa.?"

Wallai ashirin aggare shi malama yasin."
Kinji fa bugu da kari mijin ma yaro ne Allah ya kyauta."
"Ameen Malama lamarin nan nai mani ciwo araina kuma abin takaicin ma ɗan Yayana ne auren zumunta mukayi wallai Malama bacin haka da nayi karar tai."

Hakuri zakuyi yanzun ba wannan ba kije da yarki kusai magani abata kulawa ta musamman kuma kina kula da jikin ta karki barta cikin kazanta,nan da sati biyu kudawo,inga yanayin jikin nata, da kuki dawowa akwai maganin da zan ida baku tasha ko da bani nan duk Doctor din da kuka taddaba za'abaku maganin,gashi wannan kije pharmacy wajen magani asai mata abubuwan dana rubuta a jiki."


Kai Malama harda dawainiya mungode Allah yakara arziki.
Bakomai."
Abinka da yar ƙauye saita fara lissafa kudin dana bata a gabana sai Murmushi take nima itadin nike kallo.

Kai malama wannan kudin da yawa suke har dubu goma tab,ai kam har tsire zan siya mata da maltina mungode Allah yabiya bukata."
Ameen nace da ita.

Tana fita mutun ukku nakara dubawa sannan na tafi break lokacin sallah yayi kuma zuwa ukku natashi aikin ma baki daya.
Ina dawowa nakara duba mutun biyar sannan na dakatar da ganin patient,biyu da rabi daidai Ahmad yakirani waya ina dagawa yace.
"Idan na canka daidai kingama aikin yau ko.?".

Kwarai ukku nikejira ta ida intafi gida
Okay ai ina cikin asibitin zan iya shigowa.?"
Yes saika shigo.
5mint bata idaba yai mani knocking,come in kawai nace dan nasan shine.
Fuskar shi dauke da murmushi ya shigo ya zauna.

Likita bokan turai,gimbiyata barka da aiki.?"
Yawwa Dr Ahmad bokan boko."
Dariya mukayi baki dayan mu.
Dan shiru ne ya karade office din sannan yace.

"A gaskia Amina wannan karan dagaske na kuma dawowa dan in aureki tinda Allah yasa kin karbeni hannu bibbiyu inasan ki mani izini iyayena su kuma zuwa neman mani izini,asa mana biki."

Ajiyar zuciya na sauke dan zuwa yanzun na fara daukar dangana akan al'amuran Ya Taufiq na maida hankali wajen Ahmad din tinda shima dagske yake ba wasa cikin lamarin shi.

Kana ganin Abba zai aminta da aurena bayan abubuwan da naitayi abaya nasan kai zaka yafe mani amman ba lallai bane dangin ka su manta abunda nai makaba."

OMG!kidaina fadan haka mana zasu yafe maki matukar sukaji mun sasanta."
Nima da zanso hakan ta kasance Ahmad saidai zasuyi tunanin nadawo rayuwar kane dan cimma wani buri nawa na daban akanka."

Dan Allah Aminatu ki kyautatawa dangina zato mana insha Allah ba abinda zai faru kedai ki bani dama kawai."

Naji amman kabari inyi magana da Mama sai asanarwa Baba muji ta bakin shi kabani nan da one week insha Allah."
Yawwa gimbiyata ko kefa Allah yakaimu lafiya."
Ameen.

ba yar soyayyar mu,mukayi duba agogon hannuna nayi naga 15:15 hakan yasa na mike tsaye shima tashin yayi dan yagane manufata muka fito tare har wajen dana aje motata ya rakoni bude mani yayi na shiga yana waving dina na tafi zuwa gida,saidai ina zuwa gab da round din Kofar Ƙwaya ta cikin mirrow din mota,ta na hango fuskar data tsaya mani da tunanina na wucin gadi bisa mashin roba roba da hular da ake sawa akai,sake dubawa nayi still shima ni yake kallona gabana ya kara faduwa ga wajen holdof ne,rufe idanuna nayi na sake budewa still sai saman fuskar Dr JJ kaina ya sara mani,inalillahi wa'inna ilahirraji'un na furta abaiyane zuciyata na duka da sauri da sauri
Ina wucewa nayi parking daga gaban gidan Mangal nahau dubashi ba alamun shi,saina kawo araina tunani ko kuma gizo yake mani,duk dana manta da rayuwar shi baki daya a duniya.

Tada motata nayi na tafi gida ina wuce round din kofar kaura nahau titin kano road wannan kenan.


••••••••••
Hussein³.?"
Na'am Mum."
Sau nawa kaji na kira sunan ka.!?"
Sau ukku Mum,Allah yasa lafiya ba wani laifin naiba."
Inasan kabani aron hankalin ka da tunanin ka baki daya kaji abinda zan gaya maka."

Toh Mum inajinki.
"Daman baka da lafiya kodai wasan kwakwayo kake hadawa.?"

Subhanillah haba Mum in rasa abinda zanma wasa sai wannan lamarin dagaske nike Allah."

Nidai na haifeka Hussein duk girman ka baka isa kaimin wayo ba,nasan lafiyayye na haifeka har kakai wani minzali na hankali kuma narabu lafiya dakai,sai yanzun zaka zo mana da wannan zancen na sakarci! kana tunanin idan shi ubanka ya aminta dakai cikin sauki ni zan aminta dakai da wuri.!"

Marairaicewa yayi yace.

"Haba Mum taya zaki gaza yarda dani dagaske banda lafiya Hassan ma. shaidane."

Yiman shiru Hussein,Hassan shaidane zai gaza gaya mani kana cikin mawuyacin hali!
kaga ina guje maka ranar da mahaifin ka zai juya maka baya.!"

Mum wai kina zargina ne ko kuma angaya maki wani abu akaina na daban.?"
Tambayata kake kenan?
Sorry Mum ai naga....
"Is over Hussein bari in baka amsar da kake nema,zargin ka nike sanin halayen ka danayi in kaki abu toh baka taba son shi komin darajar shi da ƙimar shi,kuma in kaso abu,kana son shi komai kaskancin abun,nasan zaka iya hada komai danganin ka yakice Khairat agareka saidai kasani yima iyaye biyayya ba karamin abu bane, in kasan karya kake kada ka yaudari mahaifinka ya 6annata kudade abanza dan ganin ya sama maka lafiya ka fito kace Khairat ce bakaso baka da desire akanta nasan bazai rasa mafitaba zaifi maka sauki."

Riko hannun ta yayi yace.
Mum trust am telling you the truth blieve me.!"
Alright zaka iya tafiya na aminta dakai kuma nima zan nema maka magani insha Allah.

Allah yasa my Mum my happiness nagode maki."
Sallama yai mata yafi saidai yana zargin kodai Hassan yagaya mata kudurin shi inko har hakae saiya hadu da fushin shi.

*Kash fans kuna ganin wannan abun da Major Taufiq keyi hanya ce mai bullewa anya bai saka kanshi cikin hatsari ba,bai tafka babban kuskure ba,team Taufiq kuna ina.*

Tunda ya koma gida yake sake sake aranshi gashi ya nemi number Hassan bata tafiya dan dole ya hakura.


*******Bayan kwana hudu narasa ta yanda zan cema Baba na fidda Ahmad a matsayin mijin aure na,gashi nima naji ya kwanta mani duk da ba wani son shi nikeba saidai na aminta zan zauna dashi tunda na rasa Ya Taufiq, da Baba ya aura mani wani daban gwara na auri Ahmad tunda shima yana sona,wayata dake bisa table tahau ruri kasancewar yau ba wasu patient sosai,ganin Dr Siddi ke kirana,hakan yasa na dauka na gaida shi.

Doctor Amina kina available kuwa emergency ne ya taso ki samemu theater room."

Hakanan naji gabana ya fadi,da sauri na mike ko wayata ban daukaba na sata jikka na rufo office nayi theater rigar kawai na aza bisa gownt dina.

Ina shiga hankalina ya dugunzuma har saida jiri ya fara dibana wannan shine karon farko dana hadu da kalubale gami da abin tausayi a cikin aikina.

Karamar yarinya ce bata wuce 15yrs mijinta na aure dan kimanin shekaru 48 zuwa 50 yai rape dinta ta karfin tsiya baki daya private part dinta zan iya cewa ya haɗe yanda ya ketata abin ya wuce misali kwakwalwata bata daukar tension.

Bansan kwalla masu dumi sun sakko mani ba,zuciyata,ta tsinke ni daman bansan tashin hankali cikin gaggawa aka fara yimata allurai a wajen sai kuka take,akai mata ta bacci saidi jininta nada karfin gaske batai baccin ba,atakaice saidai akai mata dinki ukku zuwa hudu sannan aka samu nasarar haɗe wajen kuka kam nayi shi,musamman yanda yarinyar ke surutu tsabar ta gama tsorata da lamarin ta zauce.

*wayyo Allah Umma zai kasheni Uncle da zafi ka dagani banso zan mutu ya kasheni Umma na*

Abinda taketa maimaitawa kenan saida akai mata wata allurar aka kait rest room nan nurse ta samata karin ruwa.
kiran mijin incard dinmu yayi yahau yi mashi bala'i yana zagin shi.

U are very stupid kasan shirmen daka aikata kuwa ka lalata yarinyar mutane zakaso aima yarka haka.?"

Doctor ai sai naga matata ce, bawai zina nayi da itaba kawai ansamu akasine.!"
"Shut up wlh ka kuma magana zanyi reporting yan sanda su kama mani kai,anji ba zina kai da itaba amman wannan is rape tunda dole kai mata haiƙe mata kayi,baka ganin kankanuwar yarinya ce,wlh nakira Docton kwakwalwa yace yarinyar nan samu tabin hankali sainayi sanadiyar zaman ka gidan yari stupid.!"
Jin haka yasa shi yin shiru,da yafara burgar shidin mai kudine duk da yanada su.

Mahaifinta Doctor ya kira yahau yima fada.

"Kawai kwadayi yasa kunkai yarku inda za'a kashe maku ita kun mata auren tilas saboda kudi gashi abinda yaima yar taku nan ai."
Nidai banda bakin magana tausayin yarinyar ya cika mani zuciya.


```Iyaye gareku kudaina yima ya'yan ku auren wuri tun suna yara inba yoyon fisari akwai danasi idan aka illata maka yarinya kai za'abari da danasani gashi dai abinda magidanci mai hankali yaima kankanuwar yarinya yar cikin shi, Allah ya kyauta kuma ya tsare mana zuriya ameen```


_KADUNA_

"Harka isa ka haɗani da Mum!wai mikataka Hassan?nace banson Khairat dolene sainayi rayuwa da ita.!?"

Kallan mamaki Tariq ke mashi yace.......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E21&22




"Harka isa ka haɗani da Mum mikataka Hassan? nace banson Khairat dolene sai nayi rayuwa da ita.!?"
Kallan mamaki Tariq ke mashi yace.

"Wai mikake cewa Hussein nikam miye rabana idan na haɗaka da mahaifiyar mu.?"
A kufule Taufiq yace.
"Kanada riba,tunda ka dauki Khairat more than me! shiyasa ka haƙiƙan ce sai nazauna da wadda ban kauna,bansan ta kuma bazan rayu da itaba kayi abinda zakayi.!"

Mamakin Taufiq kawai yake yanda ya haƙiƙan ce wai zai haɗashi da Mum.

"Naji zanyi abinda zanyi tunda kace ni nahaɗaka da Mum naje na haɗa kayi abinda zakayi kuma dole mugaya maka gaskia kaji tsoron Allah,da lafiyarka kake pre-tending."

Anyi Hassan kayi abinda zakayi bansan kana mani haka kwata kwata ka sauya hali,ka gyara wlh da wani yai mani wannan abun sai nayi maganin shi kaci arziki kaine."

Hussein kenan Allah ya ganar dakai gaskia amman ka fito fili ka shaidama duniya kawarke ka rungumi Qaddarar ka."
Qaddara ta?Bazan dauka ba,kuma ba wanda zan cema nawarke daman lafiyata lau ba ciwon dake damuna Khairat ce banso kuma bazan taba rayuwar aure da itaba natsaneta.!"

Rai 6ace Tariq yace.
"Naji abinda kace amman kasani wlh akwai ranar da zakayi danasani wannan abun da kakeyi ba rayuwa bace Hussein kaji tsoron Allah,kuma kada ka kamanta Khairat amanace agareka sannan......

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un nashiga ukku ohni Khairat,mi kunnuwa suke jiye mani!mi zangani haka Allah kasa mafarki nike ba dagaske bane!dan Allah Tariq da gaskene abinda nikeji hazbunallahu wani'imal wakil.?"

A firgice suke kallanta kowa yai shiru saidai ido da suke binta dashi musamman Tariq dakeji kamar ya nutsu dan kunya,amman Taufiq tunda yai shock din farko ya dake kamar ba abinda ke faruwa.

shikenan Taufiq naji zan rabu dakai tinda akaina kake pretending alhalin lafiyar ka lau,kawai dan ka tsaneni, kaje ka rayu da wadda kake so nagode kwarai.!"
Juyawa tayi tana kuka ta tafi, kiranta Tariq keyi kota shi batabi tayi side dinta dagacan ta tafi gida.

Shiko Tariq jiyake kamar yaima Taufiq dukan tsiya dan takaici daya gama kamashi,a fusace yake gwadashi da yatsa.
"Hankalin ka ya kwanta Hussein tabar maka gidan ka ƙwaɗa kaci,wlh baka da tausayi ko kadan .!"

"Ai kuma ba tausayina kuka jiba da zaku tursasani zama da wadda banso ban kauna.!"
Ya ida maganar ko ajikin shi,hakan ba karamin sosama Tariq rai yaiba yace.
Kada kagaya mani maganar banza Hussein wakake cema ya tursasaka Abba ko Mum.!?"
Angaya maka nace an tursasani kuma ban sonta ta tafi Allah yabata wanda yafini."
Ameen stupid,mtsw.!"
Fita yayi yatafi gidan shi yanata fada ranshi a dagule.

********
Koda aka kira Docton kwakwalwa duba yarinyar yayi sosai ya jima yana gwaje gwaje ya gano kwakwaltar bata ta6uba amman tana cikin shock saboda ta firgita dayawa.
Baro ɗakin akai danta samu hutu.

"Doctor gaskia yarinyar nan ancutar da ita,dan haka dole abata hutu kada yakara nemanta akallah tayi wata shidda koma fiye da haka sai nutsuwar ta yadawo jikinta sannan,matsawar ya nace saiya biya bukatar shi,zuciyar ta zata iya bugawa is better abata ingantaccen hutu."

Thank you Dr Aliyu insha Allah zan sanar mashi kuma zan sake yi mashi fada sosai.
Allah yabata lafiya.
Ameen. "
Washe gari da safe Doctor Siddi ya kira mijin nata yai mashi fada sosai.

Sannan kuma dolen ka kabar yarinyar mutane tahuta,kada kara keta mata haddi tunda kai bakasan darajar ya' mace ba,akalla one year kanajina.?"
Wani kallo yaima Doctor badan yaso ba yace shikenan.

Ke kuma kitafi da yarki gida ki bata kulawa wannan baida imani da tausayi."
Malam zanyi hakan insha Allah."
Allah ya kyauta."
Ameen muka amsa kwanan ta bakwai cas aka sallame su tareda magaunguna.


********Kaduna.

Yanzun abinda Taufiq din ya aikata kenan daman can lafiyan sa lau yace baida lafiya dan kawai bai bukatar zama dake ni nasan maganin shi."
Alhaji Mas'ud kenan mahaifin Khairat.

Karanto mani number Taufiq din inkira shi."
Banda number dinshi Daddy."
Saboda bai daukeki da daraja ba kusan wata bakwai bakida arzikin da zai saving number dinki,shikenan ya kyauta.

Tashi muje gidan."
Suna zuwa kuwa akai sa'a yana shirin fita zaije wajen aiki shida Usama,yanda yagan su yasan ba sauki gaida sirikin nashi yayi bai amsa shiba tsabar bacin rai.

"Daddy ku shiga daga ciki mana.!"
Ba wannan yakawo niba,bani takardar ya'ta."
Ai Daddy bai kamata ace anyi haka ba kaga....

Ɗaga mashi hannu yayi alamun ya isa yace.
"Kai Taufiq nizaka yaudara kaƙi ya'ta shine zakai mani roman baka,wlh saika saketa ko inmaka ka kotu a tirsasaka ka sake ta."

"Shikenan Daddy naji ba sai munyi haka ba,tunda hakan shine masalaha na saketa saki ɗaya."

Alhmdullh kaima yanzun saika sarara kowa ya huta Allah ya bata wanda yafi ka,saidai kasa aranka har abada bakai ba Khairat sakin dayan nan da kaimata kasa aranka daidai yake da saki ukku,ke kuma muje kiketa kuka ga wanda bai sonki bai kaunar ki.!"
Janta yayi suka tafi sai kuka take,dan ba son wasa Khairat kema Taufiq ba.



*******Bayan kwana biyu Baba ya kirani a falon shi zama nayi na gaida shi,amsawa yayi atakaice.

"Amnatu.?"
Na'am,na amsa shi fargaba ta dirar mani a cikin zuciyata dan bansan mizaice mani ba musamman daya kirani da cikakken sunana.
"Inasan in shaida maki cewa na yimaki miji nan da wata mako biyu za'a daura maku aure kinajina.!?"

Shiru nayi kaina nasara mani bakina yai mani nauyi.
Badake nike ba."
Toh Baba,nace zuciya ta na bugawa da sauri da sauri.

Alhaji aikam daman inasan in sanar dakai wata magana ayau din nan bansan wannan zancen zakayi mata ba."
Inajinki wace magana ce.?"
Ya maida kallan shi kan Mama.
"Daman jiya na zauna da Aminatu take gaya mani ta fidda miji,toh daman tun jiyan naso in sanar maka sai kuma baka samu zama ba."

Sai gashi kun makara nagama magana ta,amman wanene tafdda sai in bata zabin nata idan ya dace d ita."
Masha Allah gaskia naji dadin hakan."
ta ida maganar tana murmushi.

Wanene shi Mamana.?"
Yai mani tambayar yana kallona
Bakina na kyarma nace.
"Ahmad ne Baba."
Wane Ahmad.!?"
Shiru nayi ina shakkar abinda Baba zaice,sai kuma na dake nace.
"Ahmad Idris Katsina."

Ɗan shiru yayi kamar mai nazarin wani abu sai kuma yace.
Kar dai kice mani wannan yaron wanda aka ta6a saka maku rana dashi kikace baki son shi.?"
Wannan karan ko bakina kasa furta komai yayi,dan tsoro da shakkar mahaifina da suka sauka a cikin zuciya ta.
Badake nikeba?"
Eh Baba,shi ne.

"Wato Aminatu kin mai dani abokin wasanki ko?kince baki son yaron nan har barazana kike mashi in ya aureki zaki kashe shi,sai

Please Login or Register in order to submit comment