Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabbas jikina yai masifar sanyi ina mamakin miyasa Ya Taufiq yakasa mallakar zuciyar shi,wane irin so yake nuna mani ,miyasa dagani har shi bazamu nemi zabin Allah ba idanun mu ya rufe da kaunar junan mu,muna neman fadawa a halaka musamman shi daya afka tarkon fushin iyaye!miyasa muka kasa gane cewa wannan din Qaddarar muce ita ke hana mana mallakar junan mu a matsayin abokan rayuwa sai yaushe zamu fara istigfar kilanma ba alkhairi a auratayyar mu tunda iyayen mu,sunki amincewa bukatar mu,inalillahi wa'inna ilahirraji'un Allah muntuba kayafe mana munyi kuskure Ya Allah ka yafema Ya Taufiq ka fiddash cikin wannan tarkon daya shiga Allah ka bashi hakuri da dangana na rokeka Ya ubanjina ka kawo mana dauki a lamuran mu,Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha Ya rabbil alameen.!"


Ameen cewar Fatash dake ta kuka abinda nasani azuci nike addu'oina ashe ta bayyana Anty Aisha ce ta rungumoni tana bani hakuri kaina harya fara sara mani dan dole na kwanta tunani kuwa kamar an dafa mani takobi a cikin tsohon tabon daya fara warkewa a cikin zuciya ta ya koma sabo dal karfijn hali kawai nike bansan sanda bacci barawo ya saceni ba.



*******Washe gari da safe muka shirya zuwa gidan sitting anbasu Fatash kudin sitting naira dubu dari aka basu,muna zuwa Anty Sadiya can muke zaman amare duk abinda yaka mata muyi,mun gama hadawa musamman abincin da muke tunanin ranar daurin aure za'aci,pride rice,pride cus-cus,dambu jallof,masa,nama da uban gayya tuwo duk anware da wanda su Husna zasuyi da wanda za'akai aiki hakama drinks duk anware duk kwalliyar da zanyi kusan ita Husna keyi domin taimana dinkuna kala hudu iri daya a ciki kala biyu harda Fatash tayi mawa shiyasa ban fara saka kayan bikina ba hidima tai hidima kowa yanajin dadin banda Anty Hafsat da bata zuwa sai yamma likis da antambaye ta saitace bata lafiya shiyasa niko dai nasan muguwar ke cinta wato hassada.



Hidima muke duk da jikina ba dadi amman hakan baisa nabari angane weakness dina ba,yau daren biki ranar muka shirya akaje kwallan amarya da ango a Karkanda Stadium Katsina anyi hidima angama alhmdulilah.


Da yamma muka dawo gidan Sitting muka wuce direct rage kayan jikina nayi na fada wanka,cikin kankanin lokaci na fito cikin material pink color.

Wayata ke ringing dagawa nayi Ahmad ne yace mani gobe zaizo daurin aurena Allah yakaimu nace mashi da haka mukayi sallama,kulla kunun aya sukeyi a leda zama nayi akacigaba da kullin dani dani muna fira.



*******Baba dan Allah kayi hakuri kada ka rabani da Amina dan Allah kada kuhukun tani ta wannan hanyar narasa komai Abba yayi fushi dani dan Allah kaimin lamani ko anan insamu sassauci.!"


Daga Baba har Mum dasu Anty Murja kallan Taufiq suke kamar zautacce sabon kamu.


Tashi kabar wajen bikin nan Hussein ko in dagama maka nono baka da hankali ina kataba ganin anyi neman aure cikin neman aure? Koni nan na hanaka Aminatu,sam baku dace ba tafika hankali,hakuri,juriya da daukar kaddara amman kao kazama babban banza wanda baida kishin zuci baka tausayin ubanka bareni uwar ka,wlh ko kabar wajen nan koka hada da fushina bakai ba Aminatu."



Mum kada kice haka dan Allah natuba kiyi hakuri.!"

Kai Hussein bakaji abinda akace maka ba,duk abinda zance maka mahaifiyar ka,tagama faɗa,dan haka baka isa ka shure umurnin ba ka saurari abinda zan gaya maka Hussein kuma shine last time dazan kuma yimaka wata magana makaman ciyar wannan kanajina.?"






_Yar Mutan Kankia ce❣️_






Share
Pls
❣️_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E25&26



Ansakani lallai gyara na musamman Anty Murja ke mani da Anty Mubaraka ni kaina nasan na samu canji hankalina yafara kwanciya nasaki jikina da Lukman sosai hakanan naji zabin mahaifin nawa ya kwanta mani arai fiye da tunanina waya muke sosai da Lukman yana bani kulawa zuwan shi ukku kenan,da yamma Asma'u tazo da ya'ta Minah naji dadin zuwan su kwarai kayayyakin da Asma'u takawo na gudun muwarta suna dayawa,godiya su Mama sukai mata,itama anyi mata lallai tayi kyau matukar jibi ake daura mani aure saura kwana biyu kenan hidima ake babu kama hannun yaro,duk lokacin da Ya Taufiq zai fado mani arai sai tausayin shi ya kamani nasan iwar haka ya samu labarin aurena tabbas zai shiga cikin matsananciyar damuwa,wani side na zuciya ta sai ince hmmm yanacan da matar shi nasan ya manta da wata Minal da haka na cireshi cikin sabgata na ware anata hidimar arziki dani naka taba cewa nida Lukman auren hadine domin so yake nuna mani na gaskia



Gudunmuwa Mama tasameta bila adadin haka yan wajen aikinmu sunban gudummuwa kamar me alert kawai ake mani masu kawowa da kansu nayi saidai ince alhmdullh.



Saidai duk wannan hidimar da akeyo dangin Mama kaf sunkawo tasu gudunmuwar amman Anty Hafsat ko abinda ba aso bata badaba sai ya kasance bata zuwa gidan mu sai bayan isha'i tara nayi tayi gida ba abinda tayi na hidimata


A ranar suk kawo lefena akwati bakwai duk da kit dinsu sun zuba mani kaya a ciki gwanin burgewa sun dinka mani kala sha hudu a ciki komai yayi das.


********ni bazan hanaki zuwa bikin yar kanin kiba Maryam kefa uwace ga Amina da Allah namiji kike kece zaki daura auren Amina akan mi zan hanaki zuwa,bari kiji wani abu wlh ni ban tsani Amina ba asalima zanso ta kasance sirika ta a cikin zuriya ta amman bada Taufiq wannan shine akidata,ki shirya kiji hidimar ki,keda Fatima sai Aisha,kema Mufida ranar da zanje saikije masu baici nasan Tariq zaibar Aisha duk sai kuje insha Allah ranar daurin aure zamuzo daga baya,ga gudummuwa nan Allah yakaiku lafiya ya dawo daku cikin aminci."


Ameen Alhaji nagode Allah yasaka da alkairi."
Ameen.


Da rana Tariq yazo shida Aisha da ya'yan su suka biyoma Mum zasu wuce Caranci daurin aure kamar daga sama aka jefo Taufiq kana ganin shi zakasan iya tashin hankali yana ciki yayi ziruziru dashi gwanin tausayi Fatash ke jan troly zuwa falorn kasa.


Kallan su kawai yake koba'a gaya mashi ba yasan unguwa zasuje.

Oyoyo Daddy i miss u.
Cewar Mukhtar (little Major) ya rungume Taufiq.
My son where are u going,Mamana come here,Aira ta iso yai holding din su akalla suna cikin shekara ta shidda kenan zuwa bakwai.

"Caranci zamuje inji Dad."
Kallan Tariq yayi alamun tambaya.



Eh yanzun kuwa zamuje biki mu dukan mu.''
Kallan mahaifiyar tasu yayi yana mamaki.
Mum bikin wa ake a Caranci kona kawu Usman.?"



Aminatu akema aure jibi in Allah yakaimu."

A zarane yaja da baya yana kallan su with shock idanun shi sun kada lokaci guda girgiza kai yake yana


"Never Mum Aminatu tawace ni kadai Qaddarata da tata iri ɗayace miyasa Baba zaimin haka,Allah saina auri Aminatu.!"


Kallan takaici takema ɗan nata ji take kamar tai mashi duka,duk ya rikice gwanin tausayi.


Tariq ya rike shi yana bashi hakuri,ingije shi yayi a jikin shi.


"Kada ka kuskura ka kuma tabani aidaman kace zanyi 2/0 shine kaje ka zuga Kawun ya hanani Minal wlh ko zaka mutu Hassan saina auri Aminatu.!"



Kukane kawai baiyi danshi kukan zuci yafiyi zakaga idanun shi kamar rushi dan tashin hankali.


Kafita idona in rufe Hussein inakai ka haukace mu da hankalin mu zan saba maka."

Mum kitaimakeni kibani Minal na rokeki zan iya rasa raina.!"



Karya kake Hussein inka tashi ka mutu,ni zakucima zarafi a cikin gidana kuke mani maganar Aminatu irin wannan wato ka aure ta ko?kema harda ke dan haka yanzun yanzun kihada kayan ki,kitafi gida bance kikuma dawo mani cikin gidaba saina nemeki,kije can keda mahaukacin danki ku karata!




Kai kuma Hussein bangaya maka na fiddaka a cikin ya'yana ba,maza kabar mani cikin gida keyarka na kuma gani wlh azim saina halbeka uban kowa ya huta,bani bakai har abada.!"



Da sauri Tariq ya riko uban yana kuka yana bashi hakuri.
Abba Mum bata da laifi a cikin case dinnan kada ka tonamana asiri."

Sakin akace maka nayi ina sane,nasan ba abinda zamma Taufiq in kona mashi rai kamar in kora uwarsa shima ya dandanin bakin cikin daya sani dan haka wlh saita tafi,kaima haka.!"



Kuka wiwi su Fatash keyi banda Taufiq daya zube kasa yahade hannayen sa uffan ya gaza furtawa tsabar tashin hankali.


Ke Fatima yiman shiru ko insaba maki,idan baku iya zuwa bikin saiku zauna gidan uban ku.!"


Yana gama fadar haka y tafi Mum kuwa kuka takasa tsabar mamaki da takaici duk abin nan Mami na tsaye tanaji farin ciki kamar tayi sujjada a kufule Mum taja kafa tayi mota suka bita sai kuka suke haka suka tafi bikin Amina rai bace.



Taufiq yakai minti nawa kafin yabar side din kukanma ya kasayi,kota kanshi Tariq baibi ba yabar gidan shima cikin bakin ciki.


Shima fita yayi ya kwashi wayoyin shi da system yayi gidan shi dake kasan layin su inda aka aje Khairat,cikin tsananin tashin hankali.



********Da yamma likis su Mum suka iso baki daya gidan ya gama hargitsewa da murna marar misaltuwa,Fatash ta rungume ni mukayi cikin dakin mu,nida ita sai Asma'u sannu da zuwa mukai mata saidai kana ganin yanayin ta kasan tana cikin damuwa hakanan naji wani iri araina duk ba dadi fira muka hauyi Lukman yakirani waya na daga mika hau firarmu ta masoya banji nauyin Fatima dake gabana ba sai kallona take.

Murmushi nayi,dear ga Fatash ku gaisa."
Mika mata wayar nayi suka fara gaisawa dashi sunjima suna fira sannan sukayi sallama cigaba da wayata nayi aka hauyima Fatash kunshi suna fira da Husna.



Ina cikin wayar Anty Murja takirani,koda naje kiranta a katan falon Baba na iske su,shi da Mum,Anty Murja da Anty Zainab sai Baba Hassan,ina ganin su nasan kiran da sukai mani mai matukar mahimmanci ne duk da kowa cikin su yayi jigum jigum har kwara Baba yafisu karfin hali,zama nayi bisa kafat kaina kasa,gabana na faduwa a hankali.


Aminatu
Na'am na amsa ina kallam Mum.

Naji dadi yanda naga kinma mahaifin ki biyayya Allah yai maki albarka Mamana."
Ameen Mum.


Da'ace kin bijirema umurnin mahaifin ki,lallai da kinsamu matsala awajen shi musamman mahaifiyar ki komai akanya zai kare kamar yanda ɗan uwan ki yayi,kinga halin daya jefamu nida yan uwan shi,gashi da shekaruna ɗan cikina ya jazama mani zaman gida inaji inagani shi kuma mahaifin shi yai fushi dashi yanzun wa gari ya waya.!"


Hakanan naji kwalla sun ciko indanuna,tausayin ta ya kamani tunanin halin da Ya Taufiq ya shiga ya cika zuciya ta.


"Mum kiyi hakuri dan Allah kuma kada kiyi fushi da Ya Taufiq."
Kallona sukeyi zuwa lokacin nafara hawaye raina duk ya gama dagule mani.


Bakomai Aminatu,abinda nikeso ki maida hankali kiyima mijin ki biyayya kifidda komai aranki Mamana kuma ki manta komai da kowa kedai kisa Allah aranki kuma kikiyayi bacin ran iyayen ki.!"


Insha Allah Mum nagode.

Tashi kije Mamana,inji Anty Murja.
Kafata tai mani sanyi sosai haka nasamu na isa wajen su Husna saidai suna ganina sukasan ina cikin rudani abinda sukayi tunani hudubar aure akaimani daman sunsan kuka ya zama farilla inyi shi.


Kwantawa nayi inajin ba dadi acikin raina,ba wanda nike tunawa sai Ya Taufiq ashe ya rabu da matar shi!


Ranar sukuku nayini saida dare yayi wajen karfe shadaya kafa ta lafa Fatash ta tadani nan take gayaman abubuwan da suka faru da Ya Taufiq musamman karyar dayaima Abba,da hukuncin da Abba ya yanke akan shi da Mum tabbas jikina yai masifar sanyi ina mamakin miyasa Ya Taufiq yakasa mallakar zuciyar shi,wane irin so yake nuna mani ,miyasa dagani har shi bazamu nemi zabin Allah ba idanun mu ya rufe da kaunar junan mu,muna neman fadawa a halaka musamman shi daya afka tarkon fushin iyaye!miyasa muka kasa gane cewa wannan din Qaddarar muce ita ke hana mana mallakar junan mu a matsayin abokan rayuwa sai yaushe zamu fara istigfar kilanma ba alkhairi a auratayyar mu tunda iyayen mu,sunki amincewa bukatar mu,inalillahi wa'inna ilahirraji'un Allah muntuba kayafe mana munyi kuskure Ya Allah ka yafema Ya Taufiq ka fiddash cikin wannan tarkon daya shiga Allah ka bashi hakuri da dangana na rokeka Ya ubanjina ka kawo mana dauki a lamuran mu,Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha Ya rabbil alameen.!"


Ameen cewar Fatash dake ta kuka abinda nasani azuci nike addu'oina ashe ta bayyana Anty Aisha ce ta rungumoni tana bani hakuri kaina harya fara sara mani dan dole na kwanta tunani kuwa kamar an dafa mani takobi a cikin tsohon tabon daya fara warkewa a cikin zuciya ta ya koma sabo dal karfijn hali kawai nike bansan sanda bacci barawo ya saceni ba.



*******Washe gari da safe muka shirya zuwa gidan sitting anbasu Fatash kudin sitting naira dubu dari aka basu,muna zuwa Anty Sadiya can muke zaman amare duk abinda yaka mata muyi,mun gama hadawa musamman abincin da muke tunanin ranar daurin aure za'aci,pride rice,pride cus-cus,dambu jallof,masa,nama da uban gayya tuwo duk anware da wanda su Husna zasuyi da wanda za'akai aiki hakama drinks duk anware duk kwalliyar da zanyi kusan ita Husna keyi domin taimana dinkuna kala hudu iri daya a ciki kala biyu harda Fatash tayi mawa shiyasa ban fara saka kayan bikina ba hidima tai hidima kowa yanajin dadin banda Anty Hafsat da bata zuwa sai yamma likis da antambaye ta saitace bata lafiya shiyasa niko dai nasan muguwar ke cinta wato hassada.



Hidima muke duk da jikina ba dadi amman hakan baisa nabari angane weakness dina ba,yau daren biki ranar muka shirya akaje kwallan amarya da ango a Karkanda Stadium Katsina anyi hidima angama alhmdulilah.


Da yamma muka dawo gidan Sitting muka wuce direct rage kayan jikina nayi na fada wanka,cikin kankanin lokaci na fito cikin material pink color.

Wayata ke ringing dagawa nayi Ahmad ne yace mani gobe zaizo daurin aurena Allah yakaimu nace mashi da haka mukayi sallama,kulla kunun aya sukeyi a leda zama nayi akacigaba da kullin dani dani muna fira.



*******Baba dan Allah kayi hakuri kada ka rabani da Amina dan Allah kada kuhukun tani ta wannan hanyar narasa komai Abba yayi fushi dani dan Allah kaimin lamani ko anan insamu sassauci.!"


Daga Baba har Mum dasu Anty Murja kallan Taufiq suke kamar zautacce sabon kamu.


Tashi kabar wajen bikin nan Hussein ko in dagama maka nono baka da hankali ina kataba ganin anyi neman aure cikin neman aure? Koni nan na hanaka Aminatu,sam baku dace ba tafika hankali,hakuri,juriya da daukar kaddara amman kao kazama babban banza wanda baida kishin zuci baka tausayin ubanka bareni uwar ka,wlh ko kabar wajen nan koka hada da fushina bakai ba Aminatu."



Mum kada kice haka dan Allah natuba kiyi hakuri.!"

Kai Hussein bakaji abinda akace maka ba,duk abinda zance maka mahaifiyar ka,tagama faɗa,dan haka baka isa ka shure umurnin ba ka saurari abinda zan gaya maka Hussein kuma shine last time dazan kuma yimaka wata magana makaman ciyar wannan kanajina.?"






_Yar Mutan Kankia ce❣️_






Share
Pls
❣️



_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E27&28



Daga yau kada inkara ganin ka gidana Hussein bakai ba Aminatu wato kazo ka ruɗar mana da ita ko?tunda kai kagaza yimana biyayya,so kake itadin ma ta bujirewa umurnin mu,dubi kaga halin daka jefa mahaifiyar ka duk akan ka,tashi kabar gidan nan kada inkara ganin keyar ka bare har kai ikirarin son Amina kuma ina baka shawara tun wuri kaje kanemi afuwar Mahaifin ka tunkan kasamu matsala fushin iyaye musifa ne ga ya'yan su.!"

Baba dan Allah kuyi hakuri nasan nayi kuskure amman natuba.!"

Munji kuma anyafe maka amman yanda mahaifin ka yai maka umurni kakibi ba wanda zaiji tausayin ka,Allah yaganar dakai don duk Abinda kake baka cikin hayyacin ka da alama."

Gaskia Hussein kasa son zuciya dayawa,idonka ya rufe ka tabka babban kuskure Allah ya yafe maka wasa da hankalin iyayen ka dakayi.

Inna kitausaya mani dan Allah."
Da inada halin taimakon ka,da nayi Hussein kawai ka dauki Qaddarar ka,kuma ka gyara rayuwar ka,ka koma Taufiq dinka nada bana yanzun ba danni bansan ami zan sakaba."
Cewar Anty Murja.

Haka sukaima Taufiq faɗa sosai suka nuna mashi illar ƙin bin umurnin iyaye da hadarin dake ciki saida jikin shi yai sanyi likis.

"Mum dan Allah kiyafe mani kada abubuwan suyi mani yawa.!"
Wani irin tausayin shi yakama ta,kwalla nasan kubce mata tana maidasu dan batason ta zubdawa ɗan nata hawaye gudun kada abubuwan suyi mashi yawa.
Nayafe maka Hussein amman kaji tsoron Allah kuma kadawo hayyacin ka,kaima iyayen ka biyayya ko kasamu yardar ubangijin ka."

Insha Allah Mum,nagode maki Allah yasaka maki da alkhairi.
Baba kuma insha Allah zan dauki Qaddarata zanje wajen mahaifina in samu ya yafe mani."
Daka kyauta Hussein Allah yai maka albarka."
Ameen."

Jiki mace ya mike,zuciyar shi na tafasa banda kukan zuci ba abinda yakeyi,yana fita shida Usama suka tafi,kiran Fatima yayi a waya tai mashi kwantance inda suke zaman setting, suna zuwa yakirata yace suzo ita da Amina zasu gaisa yana sauri,da taki zuwa Husna ta matsa mata,ta tashi suka nufi waje.


Tunda nasako kafata waje naji mummunan faduwar gaba ta dirar mani a cikin zuciya ta,tafiya kawai nike kaina ƙasa duk da banga Ya Taufiq ba amman naji idon shi akaina jikina a sanyaye na isa wajen shi,kamo hannuna Fatash tayi na shiga baya domin kuwa anan yake zaune ina shiga Usama yabar motar Fatash ta zauna gaba tana danna wayar ta.

Shiru mukayi baki dayan mu,inajin yanda yaketa sauke ajiyar zuciya nidai jikina rawa kawai yake inasan inga natsastsar fuskar shi mai sakani nutusuwa amman kwarjinin shi ya hanani,musamman dana san dalilin zuwan shi wajena.

Minal.?"
Ras haka naji faɗuwar gaba jin daddar muryar shi wadda take mani daɗin sauraro musamman idan yakirani da Minal tabbas yafi kowa iya sarrafa kalmar.

Kinga yanda Qaddara tarabamu ko? Kinga halin dana jefa kaina na fushi da iyaye duk akan sonki?
Minal na zauna nayi tunani nagano ba sonki nike ba KAUNARKI nikeyi wannan kuma ajinina yake,nayi imani da Allah bazan daina kaunarki ba saidai dole in tursasa kaina wajen nisantarki da tunanin ki araina dan kaunarki tafi karfin zuciya ta,saidai da ruhina Aminatu ina sonki kuma na kaunace ki sannan zanci gaba da kaunarki har abada ke tawace amman Qaddara ta riga fata.!"

Bani kadai ba hatta Fatash sheshekar kuka take nima shidin nikeyi yatsuna nikebi da kallo zoben daya siya mani nike kallo shine ke tunamani da Ya Taufiq tabbas Qaddarata akan so ne kowa da kalar tashi jarabawar amman ni wannan tana cikin tawa Qaddarar.

Ya Taufiq ina sonka Allah shine shaidana,zanma iyayen mu biyayyane kawai dan banda wani zabi daya wuce wannan amman kasani duk wanda zai aureni gangar jikina kawai zai aura,na soka Ya Taufiq inakan sonka har yanzun da nike maka wannan maganar sonka kullin kara nunkuwa ake a cikin ruhina ban tunanin akwai wanda zai maye mani gurbinka masoyina,dan Allah kayafe mani a dalilina komai ya sameka na zama Qaddarar ka.!"

Kuka nike sosai saidai duk wannan abun daidai da ɗigon kwalla basu sauka a idanun saba,saidai doguwar ajiyar zuciya dayake shiɗewa kuma baki fatan sake,saka idon ki cikin nashi tsabar rinewa da sukayi nima kallo daya nai mashi na sauke nawa idon kasa.

Ban rike dake Aminatu tabbas kedin Qaddarata ce kamar yanda nike Qaddarar ki!sedai bansan kozan samu ladar wannan jarabawar ba Allah masani,amman ina maki fatan alkhairi kuma Allah ya albarkaci rayuwar auren ki kanwata.!"

Ban ansaba dan kukan nema yake yaci karfina

Ya Taufiq ni zan maka fatan alkhairi Allah yabaka wadda tafini komai wadda zata zama rahama a gareka."

Uhmmm Minal kenan nagode,tashi kije kanwata Allah yasa hakan shine mafi alkhairi agaremu.!"
Ameen cewar Fatash kanajin muryarta bako shakka tasha kukanta,ta koshi.

Fita nayi sai naji inama mu dawwama a haka yanzun shikenan bani ba Ya Taufiq har abada zanje gidan wani,inda ba dangina ba wanda nasani sai Lukman,amman jarabawa ce kuma haka ALLAH YASO!

Ina isa daki nafada kan gado naita kukana a hankali,nan fa aka fara cewa kukan rabuwa nikeyi masu bani hakuri nayi masu yimani shaƙiyanci nayi nidai nasan abinda ke damuna!.

Ranar koda Lukman ya kirani ban dauka ba saidai nasa Husna tabashi wani uzurin na daban nayi bacci.

Da Yamma likis Taufiq ya isa Kaduna gidan shi ya sauka duk jikin ba dadi,waya ya kira Tariq yace yazo zasu yi magana da yaki zuwa saida ya takura mashi sannan yazo.

Riko shi yayi cikin tashin hankali yace.
Daga Caranci nike Hassan naje nanemi yafiyar Mum sannan nayi bankwana da Minal tabbas Hassan rabuwa da masoyi akwai ciwo naɗanɗani yanda akeji! dan Allah ka rakani inje inbawa mahaifina hakuri narokeka.!"

Cikeda tausayawa yace.
Hussein duk duniya inaga Mum ce kadai tafini tausayin ka da ace Abba zai saurareka danafi kowa jin dadin haka,dan Allah kadaina damuwar kanka Allah yabaka dangana da hakuri domin sune karasa a cikin wannan tafiyar Allah yasa kazama shugaban zuciyar ka."
"Ameen nidai muje wajen Abba banda nutsuwa ko kadan atare dani dan Allah ɗan uwana.!"

```Allah Sarki rayuwa tsakanin ɗan uwa da ɗan uwa sai Allah bamai shiga duk yanda Hussein yake blaming din Hassan amman shi mafita yake nemawa ɗan uwan nashi,Ya Allah kabarmu da yan uwan mu ka kara mana soyayyar junan mu a cikin zukatan mu💔🙏```


Kadaina kuka Hussein muje insha Allah yau sai Abba ya yafe maka da izinin Allah."

Haka suka tafi gidan mahaifin nasu a compound din gidan suka iske su tareda Mami sai Samir bisa robber chairs,kallan dage Mami ke jifansu dashi hakama Samir.
Dukawa sukayi suka gaidasu ya amsa ta Tariq banda gaisuwar Taufiq.

Sai lokacin kwalla masu dumi suka ziraro bisa kincin Taufiq

Abba dan Allah ka yafe mani natuba nayi nadamar abinda na aikata agareka,naji zan maka biyayya akan zabin ka koma wane irine a shirye nike zanyi maka biyayya.!"
Abba kayafe mashi ya tuba bazai kuma sake aikata makimancin wannan laifin ba.!"
Cewar Tariq.

Kin magana yayi kamar badashi suke ba,da hannu ya dinga nuna masu kofa.

Bakuji mi yace ba eyeh yace kufita bai bukatar ganin ku baki daya.!"

Kallan mamaki suke bin Mami dashi hatta Samir bai tunanin zata nuna tsanar suba agaban mahaifin suba.

"Nayi dake Mufida?ni ban tsani ya'yana ba saidai ban bukatar shi arayuwa ta,a halin yanzun kuma ban tsine masa ba,duk abinda nike har yanzun da sauran hankalina abinda nasani ya nisanta dani bani bashi bai cikin ya'ya na a halin yanzun,kuma da kike magana aiba ruwan Tariq da zakiyi haɗin goro laifin wani baya shafar wani,kuma wannan case din tsakanina da ya'yana ne ba ruwan matana a cikin shi.
kai kuma Hussein kabar mani gidana ganin ka zai iya hargitsani harnayi kalami marar dadi agareka dan haka kada ka,kara furta tak tashi kaje bansan inkara ganin keyarka a gidana ba har sai bukatar hakan ta taso da kaina zan nemeka fatan ka fahimce ni.!?"


Eh Allah nagane ina godiya Allah ya huci zuciyar ka,kuma yabamu ikon yi maku biyayya akowa ne lokaci Allah yajikan mahaifa."

Ameen suka amsa baki dayan su,shima Tariq godiyar yayi suka tafi,suna aikama Mami da kalan tsana ido cikin ido,suna fita Samir ya tsaida su.
yana masu kallan tsana yace.
Anji haushi dai,za'a rayu da fushin iyaye anji kunya wlh.!"
A hargitse Tariq ya shaki Samir zai kai mashi wani wawan punch Taufiq ya rike shi.

Kyaleshi Hassan, komai lokacine,anyi walkiya munga haske ka gayama gyatumar ka insha Allah saita ganni tareda mahaifina.!"

"Kai Mami kake gayama magana.!"

Eh anya mata Hajia Maryam Caranci ce.?"
Janshi Tariq yayi suka tafi yana ba dan uwan nashi hakuri.

Ranar a gidan Hussein,ya kwana,tausar shi ya dingayi da kalamai masu saka zuciya nutsuwa koda safiya tayi Abba yakira Tariq yace shi suke jira zasu tafi Caranci daurin aure wanka kawai yayi yasaka shaddar shi light brown saida yakara kwantatawa Taufiq sannan yai mashi sallama yatafi gidan su,bai jimaba su Abba da Samir sai Mami da Zakiyya suka shiga motoci guda biyu suka dauki hanya.


Shiko Taufiq kamar jira ya tashi yayi wanka,wata troly ya dauko ya zuba kaya cikin ta musamman kananan kaya ya dauki phones dinshi da abubuwa masu mahimmanci ya rubuta letter ya aje tsakiyar gado yaja motar shi ko Usama baisani ba yafita,yace ma maigadi idan Hassan yadawo yace akwai sako bisa gadon room dinshi ya dauka sai yadawo,sallama maigadi yai mashi ya tafi,ba inda ya ansa kira sai Airport aje motar yayi alot, yai komai kafin ya samu damar wucewa ciki tun wajen shadaya ya isa Airport amman sai karfe 12:30 jirgin Taufiq ya tashi bisa sararin subhana.

Zuwa lokacin kuwa su Abba sun iso Caranci yan awanni kadai ya rage masu a daura aure,sosai Baba yaji dadin zuwan Alhaji Mukhtar bikin Aminatu wannan shike nuna bai rike dashi musamman,ta dalilin yar sane ɗan shi mafi soyuwa agare shi ya susuce.

Dangin Mum a falorn Baba suka saka Abba agaba suna bashi hakuri kan hukuncin daya yankema Mum akan Taufiq.

Dan Allah Alhaji kayi hakuri yanzun ka haifi ɗane baka haifi halin shiba kayafe mashi musamman mahaifiyar shi ba laifin ta,dan Allah kataimaka kamaida ta ɗakin ta.!"

Shiru yayi yana kallan matar tashi wadda yakema so na dabban a rayuwar shi.

Bakomai kada ku damu tayi bikin ta tagama komai tadawo dakin ta,nayi hakanne

Please Login or Register in order to submit comment