Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzun zakizo kigaya mani maganar banza ga Yusuf ɗin mahaukata! Shi kanshi uban shi bazai yardaba tinda tun farko kika nuna baki son ɗansu to bakison shi!
Yanzun tsabar munafunci zaisa kice kina son shi dan bayanda zakiyine shiyasa,ni Yusuf ubanki na kashe wannan maganar baki dayan ta,har abadan abada!
dan haka badajimawa ba,za'a daura maki aure da Lukman fatan kin fahimta?kuma ranar juma'a zaizo ku gaisa dan Allah idan kin tashi shima kice zaki kashe shi,idan ya aure ki.!"
Kuka nafara marar sauti murya ashake nace.

Shikenan Baba Allah yasa haka yafi zama alkhairi agareni."
Ameen Mamana Allah yai maki albarka."
Ameen ya rabbi,nace inajin wani irin ciwon kai yana sauko mani cikin kankanin lokaci.

tashi nayi na koma dakina ina hawaye tausayin Ahmad yakara kamani miyasa Qaddara takara hadamu a wannan lokacin yanzun ma zan kara breaking heart din Ahmad kenan? Inalillahi wa'inna ilahirraji'un.

Kuka nike mai tsuma rai har kaina saida yakara mani nauyi ga sarawa yanayi,Mama ta shigo cikin dakina da sallama abakin ta.
Ko amsata banba ta zauna gafena cikeda tausayawa tace.

"Aminatu tashi ki zauna."
Zama nayi tace.
"Kuka ba naki bane Amina yanzun lokacin kuka ya kare ki dauki Qaddararki,kuma kima mahaifin ki biyayya Lukman yaron kirkine mahaifin shi yanada mutunci da ƙima a idon mutane kuma zai rikeki bisaga amana kinji ya'ta?"

Goge kwalla fuskata nayi na riko hannun mama nace.
Mama tausayin Ahmad ya cika mani zuciya shiyasa nafara kuka,amman insha Allah zanma mahaifina biyayya bazan taba watsa mashi ƙasa a idoba amman ya zanyi da Ahmad.?"

Kuturo shi wajen mahaifin ki nasan zai kwantar mashi da hankali."
Shikenan Mama na,nagode maki Allah yasaka da alkhairi."
Ameen yar albarka.

Da haka nasamu sassaucin abinda nikeji araina naci gaba da hidimata kamar ba wani abu dayake shirin faruwa dani.

Washe gari ina zuwa office nacema Ahmad yaje yasamu Baba,sosai ya nuna jindadin shi.

Haka rayuwa ta kasance gwanin dadi banda wata matsala,jibi Lukman zaizo ganina,nakira Husna na gaya mata addua taimani da Allah yasa haka yafi zama alkahiri shima Ahmad Allah yai mashi zabin alkahairi.
Ameen,nace da ita nan muka taba fira sannan nakashe wayar.

Washe gari kuwa....

Akan hanyata ta dawowa gida na hango Dr JJ nabin bayana gabana ya faɗi nasara dalilin dayasa JJ ke bibiyata,kusan sau ukku ina ganin shi,saida nayi nisa daidai lambar rimi nayi parking mota ta,kamar ina neman wani abu,amman hankalina kaf yana kan JJ daga can nesa yai parking motar shi,kin tafiya nayi tsorona kada yabini zuwa gida shiyasa naki tafiya na jima a haka ganin dai baida niyar barin wajen nashiga mota na tafi saidai still ni yakebi direct gidan kakannina na wuce na shige ciki,shima parking yayi daga nesa ba shiri na wuni gidan Dada sai gab da magrib na leko harya tafi jiki mace nahau mota zuwa gida,gabana na dan faduwa amman abin mamaki banga wani canjin da zai nuna mani yazo gidan muba.

Washe gari karfe takwas nabar gida natafi aiki,ranar kuwa Ahmad yazo ya sami Baba suka gaisa.
"Ahmad daman Aminatu ta sanar mani da zuwanka akan neman auren ta,a gaskia ba uban da bazaiso ka kasance sirikin saba domin kaidin mutumin kirkine hakama mahaifin ka,dan haka inamai baka hakuri akan abinda zan gaya maka.

Aminatu dai nayi mata miji nan da sati biyu za'a daura mata aure nasan bazakiji dadiba zakaga tayi maka wasa da hankali ba haka bane ita kanta bata saniba sai satinnan nike gaya mata zabina,sai lokacin mahaifiyar ta,ke sanar mani kuma kaima kasan harumne neman aure cikin neman aure inafatan zaka fahimce ni Ahmad."

Sauke ajiyar zuciya yayi yace.
"Nafahimta Baba,duk yanda Allah yatsara shine daidai Allah yasa haka yafi zama alkairi agaremu baki daya nagode sosai."

Ameen Ahmad wlh da'ace Zainab ta girma bako shakka zan aura maka ita kashiga raina tun farko naso ace dakai akai auren sai kuma aka fasa,da ace nasan zaka dawo da banyi alqawalin bada Aminatu ba,Allah yai maka albarka."
Ameen Baba nagode kwarai Allah yakara girma karka damu zan dauki Qaddarata."

Masha Allahu naji dadin hakan daga gareka."
Baba zan koma kahuta lafiya."
Kagaishe da mahaifin ka.

tafiya Ahmad yayi,sai lokacin Mama ta fito cikeda tausayin Ahmad aranta nan ta zauna sunajin ba dadi aransu.

Yakama gobe Lukman zaizo ganina ranar friday naje wajen aiki kasancewar kurarren lokaci ne shabiyu muke tashi misalin karfe sha daya Ahmad yazo office dina wani irin nauyin shi da kunyar shi duk suka kmani karfin hali kawai nayi na iya hada ido dashi da suka canja kala tsabar tashin hankali,bude baki nayi nafara bashi hakuri ya dakatar dani.

"Naji komai Amina basai kin bani hakuri ba kuma nafahimci komai karki zargi kanki Amina wlh baki yaudareni ba, asalima nina matsa maki na komo cikin rayuwar ki akaro na biyu saidai kisani kofa abude take idan kina neman taimako agareni,kuma kisani ina kaunarki,sannan ina maki fatan alkhairi akoda yaushe kisa ranki zan dauki Qaddarata.!"
Kwalla naji sun ziraro mani tsananin tausayin Ahmad ya rufeni gaskia shidin masoyine na gaskia.

Insha Allah kana cikin amintattun yan uwana Ahmad ka shiga cikin dangina ina fatan Allah yabaka wadda tafini komai mace ta gari mai tsoron Allah,ina kaunar ka,nasan wannan yana cikin Qaddarata.!"

Nagode maki Amina,bari zan koma sai wani lokaci kuma in biki yazo dan Allah kisanar mani."
Insha Allah
Tare muka fita kowa ya shiga motar shi,yai gida nima na tafi garin mu wannan kenan.

Fatima da Zakiyya ne a gidan Taufiq shiga sukayi,suka gaisa da maigadin gidan,direct side din Khairat suka nufa maigadi ne ya biyo bayan su yace......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_



S3/E23&24



*Kaduna*


Fatima da Zakiyya ne a gidan Taufiq shiga sukayi,suka gaisa da maigadin gidan,direct side din Khairat suka nufa,maigadi ne ya biyosu yace.
"Hajiar bata nan."
Juyowa sukayi suka ce.
"Ina taje.?"
Gaskia yau satin ta guda da komawa gida.
Gida kuma,,
Duk suka hada baki cikeda shock suke kallan shi.

Kiran Khairat tayi tana dagawa tace.
"Anty Khairat wai kina munzo maigadi yace bakyanan sati daya kenan."
Eh Fatima ina gidan mu."
Gamu nan zuwa nida Zakiyya ne."
Toh sai kunzo.

Tafiya sukayi gidan su a falor suka iske su ita da yan gidan su,tarar mutunci tai masu suka gaisa.
"Yanzun Anty sai kizo gida kiyi har sati haba gaskia baki kyauta mike faruwa.?"
Hmmm Fatima kenan dolene inzo gida kinsan abinda ke faruwa ai."
Amman Anty Khairat insha Allah Ya Taufiq zai warke kiyi hakuri kikoma dan Allah."
Cewar Zakiyya.
"Wai kuna nufin bakusan Taufiq ya sakane niba?kuke mani wannan maganar.?"

Baki dayan su suka mike tsaye a razane musamman Fatash data hau salati,wani irin kunyar ta duk ta dabaibaye su.

Wlh bamu da labari Anty Khairat dan Allah kiyi hakuri bamu saniba."
Bakomai Fatima nasan baku sani bane."
Amman saki nawa yai maki.?"
Ɗaya ne.

A surkurkuce suka tafi gida jiki ba kwari suna komawa gida side din Abban su,suka nufa a babban falorn shi suka iske shi tareda su Mami sai Samir,kuka suka fashe dashi baki daya hankalin su ya gama tashi Mum ke jefo masu tambayoyi banda kuka ba abinda sukeyi.

Shut-up idan bazakuyi ma,mutane bayani kutashi ku fita sakarcin banza dana wofi."
Samir ya ida maganar a hautsine.
Ya Taufiq ya saki Anty Khairat tana gida."

A razane Major Sarki ya mike tsaye yana huci.
Kun tabbatar da maganar ku."
Ya tambayesu yana mai tabbatar da abinda ya'yan nashi suka faɗa.
Wlh Abba dagaske mukeyi tana gidan su kimamin sati ɗaya kenan.
Tabbas indan har wannan labarin ya tabbata bani ba Taufiq har abadan abada.!"

Wayar shi ya dauko kira daya yaima mahaifin Khairat ya daga Alhaji kana ina.?"
Yanzun nan nashigo gida ko lafiya.!"
Ba lauba ganinan zuwa yanzun nan,Samir tashiga ka kaini."
Fita sukayi sai gidan Alhaji Mas'ud.
Falorn shi suka shiga ko zama Abba ya gazayi yace.

"Yanzun Alhaji har da'na ya saki yarka bansani ba sati daya dafaruwar wannan lamarin haba Alhaji Mas'ud.!"
Kayi hakuri dakaina nasa saida yasake ta saboda nagaji dacin kashi irin na Taufiq ace kawai saboda kiyayyar da yakema Khairatu zai jazawa kanshi lalura irin wannan dan kawai ban son ta.!"
Bangane! ba kana nufin lalurar Hussein duk shirine.!?"
Kwarai kuwa wannan dalilin yasa da kaina saida nasa ya saketa."

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un aikuwa yau sai Hussein ya gamu da fushi kuma wlh tallahi yau bani ba.....
Da sauri Alhaji Mas'ud ya rufema Abba baki yace
Haba Alhaji Mukhtar akanmi zakaima danka baki kaje ka karajin ta bakin shi.!''

Alhaji kayi hakuri wlh bani Taufiq baitaba bata mani rai ba kamar yau dinnan da wannan mummunan labarin ya sameni ba amman nasan maganin shi.
saki nawa yai mata.?"

Saki ɗayane amman kayi hakuri wlh blh bazata kara komawa wajen shiba har abada,dan haka kayi hakuri Taufiq baisan ya'ta ni kuma bazan kai ya'ta inda ba'ason taba fatan zakai mani uzuri."

Shikenan banga laifin kaba,ko nine nan abinda zanyi sai yafi haka dan haka kabar komai a hannuna nagode.!"

A fusace ya fita yana bugo kofar da sauri Samir ya bude mashi mota suka tafi tun a hanya Major ya kira Doctor Asim yace.
kasameni gida yanzun nan."

Kusan tare suka isa gidan parking kirki Samir bai idaba Sarki ya fito ya shiga falorn shi yanda yabarsu haka ya samesu kowa yai jigum bamai cikakkar lakka a cikin su.
tareda Doctor Asim Samir ya iso falorn.

Zama sukayi kowa yai shiru.
Wani irin kallo Major ya aikama Doctor yace.
Doctor Asim bani labarin lalurar Taufiq bansan karya tell me the truth."
Sosa kai yafara duk ya rikici bakin shi yafara bari hannun shi duk yahau rawa yace.
Kaiman aikin gafara ranka shidade badason raina hakan yafaru ba."

Shut up tell me,the truth that's all.!"
Ba gaskia bane planing ne aka haɗa,kuma shiya umurceni da intabbatar maka da hakan wlh banda wani za6i.!"
Mikewa Major yayi tsaye a fusace yace.
Nawa ya biyaka dahar kaci amanata.!?"
Ya linka mani kudun daka bani dan Allah Alhaji kaiman aikin rai natuba kayafe mani.!"
Good,ka kyauta dacin amanata da kayi kaida ɗan cikina.!"
Ku shigo ciki,yace yana aje waya.
Kuratan sojoji ne suka shigo,sawa yayi suka kama Doctor Asim.
Da yatsa yake nuna su yace.

Ku ladabtar mani dashi sannan ku mika mani case din shi hannun police maza ku kama shi,bani ba maci amana har abada.!"
Alhaji karufa mani asiri ba laifi na bane na rokeka....

Haka sukaja shi, yanata kuka sukayi waje dashi
Kamar anjefo Tariq ya shigo falorn dan Fatima ta kirashi waya ta nasar mashi abunda ke faruwa.

Abba ya kalli Hassan yace.
Within a 5mint kaje ka nemo mani Taufiq yanzun yanzun nan.!"

To Abba yace,da sauri ya juya zai fita suka rafka uban karo da junan su.
Lafiyan ka kake wannan...
Ganin kowa jugum yaji mummunan faduwar gaba ta dirar mashi,gakan yasa sauran maganar shi ta makale a bakin shi, jiki mace ya iso ciki yana shirin dukawa ya gaida mahaifin nashi,dan ba karamin raina gaskiar shi yaiba. tunkan ya duka Major Sarki ya ɗauke Taufiq da lafiyayyun maruka har ukku,saida ya danne kunci shi tsabar razana,shi kuwa Abba rai a matukar 6ace yace.

"Dan uban daya haifeka ni zaka zubdama ƙima da mutunci nizaka ha'inta Hussein baka da lalura ka jajiboma kanka bala'i dan kawai karabu da Khairat ashe baka da mutunci ban saniba.!?"

Abba kayi hakuri tabbas na tabka babban kuskure dan Allah....
"Ka ida maganar nan saina tsine maka albarka!marar mutinci akan Amina kaki zabina ko? Kai mani wasa da hankali ko? Ka maidani tsaran wasan ka duk akan Amina ko?,to kasani indai nine ubanka kai ba ɗan zina bane bani bakai har abada kuma bazaka ta6a samun Amina ba har ka mutu,tunda har kaƙi bin umurnina duk irin so da kauna dana gwada maka a cikin ya'yana ashe kaine maƙiyina bansani ba,kaje bazan tsine maka ba amman kasani na fiddaka a cikin jerin ya'yan dana haifa.!"
Zubewa Taufiq yayi kasa ya riko hannun mahaifin shi yafara bashi hakuri.

Dan Allah Abba kada kayi mani baki kayafe mani tunda saki ɗayane kadawo mani da ita wlh naji na aminta zan rayu da ita.!"

Karya kake Hussein bakin Alqalami ya bushe Khairat ta subuce maka har abadan abada Allah zai bata wanda yafika!kuma kajini da kyau, within a 10mint umurnine kaje kayi resign aikin ka, daman ai kafaɗa akan mace zaka aje aikin ka ko? Yanzun kaje karubuto resign latter saika koma wajen Amina za6inka.!"

Alhaji dan Allah kayi hakuri wannan hukunci yai tsauri dayawa kayafe mashi.!"
Kema kiyi mani shiru kada ki hadu da fushina yanzun nan.!"
A kufule yai maganar zuciyar shi natafasa.
Allah ya huci zuciyarka cewar,Mum sai kuka takeyi hakama su Fatash.


Abba na tuba nabi Allah nai maka biyayya ka rufaman asiri kada alhakinka ya hanani sukuni a rayuwara kayafe mani kadawo mani da Khairat zan zauna da ita."

Tashi kabar wajen nan,kuma ka kawo mani resign letter sannan bani bakai har abada,aiki zai haɗani dakai ka'aje shi bansan inkara ganinka kusa dani har gaba da abada kaje nabarka da zabin ranka,nima kabarni da sauran ya'yana masu sona.!"

Na rokeka Abba kayafe mani dan...
Wlh ka ida wannan maganar Hussein ba abinda zai hana ban tsine maka ba.!"

Dan dole ya fita yana kwallan takaici take yafara dana sanin ƙinbin umurnin mahaifin shi,gaskia yasan yayi babban kuskure a rayuwar shi.

Hakan akayi kuwa ya dauko uniform dinshi da letter ya kawoma mahaifin nashi.
Ya aje mashi gaban shi.
Gobe kazo office kasa hannu."
Abba kayafe mashi dan Allah."
Cewar Samir shima duk ya damu.

Samir da'ace Hussein yai mani biyayya ya zauna da Khairat bai yaudare niba,harna gano desired dinshi wlh dana nema mashi auren Amina da kaina ni Mukhtar amman tunda harya ha'inceni ina uban shi yaje bakomai."
Abba kayi hakuri nayi nadama zan zauna da Khairat din.!"

Tashi kada insake ganin keyarka a sashena bani bakai,magana ta karshe da zanyi agareka kenan.!"

Fitar yayi yanaji kamar yai hauka jin irin hukuncin da mahaifin shi yayi mashi.
a kufule Major Sarki ya shige bedroom din shi,yanajin bakin cikin abinda Taufiq ya aikata mashi.
Suko su yar jiki mace kowa ya watse Mum taci kuka ta gode Allah.

Tariq yai karfin halin zuwa wajen Taufiq ya iske sh kife da kanshi a jikin kan gado sai jijjiga kai yake kamar zai fado kasa.

Da sauri ya iso wajen Tariq ya riko shi.
Minene mafita Hassan nashiga ukkuna Abba ya barrantani a cikin ya'yan sa.!"

Cikeda tausayin halin da Taufiq ya shiga yace.
Wannan ranar itace najima ina gudar maka Hussein dagani saikai sai Allah na nuna maka hanyar tsira kakibi karshe nida kai dambe ne kawai bamuyi ba abinda bamu taba yiba nida kai sai ranar,narasa lokacin da ɗan uwana ya zama mai yawan son zuciyar shi,narasa sadda ka zamam marar tausayi,yaushe kakoma mai yawan son kanka? Dan haka nidai banda wata shawara da zan baka saidai kajira idan ya hucie saika nemi afuwa agare shi.!"

Rasa abincewa yayi saidai ido daya kurawa Tariq kana ganin fuskar shi kasan tashin hankali yakai tashin hankali.
Wayar Tariq tafara ringing ganin Mum a jiki yasa shi dagawa.

Kusameni side dina kaida shi yanzun nan.
Toh Mum.
Miyafaru da ita Tariq.?"
Halin daka sakata mana ai nasha gaya maka ka dauka tatsuniya nike maka muje Allah ya kyauta gaba."
Jiki sanyaye suka je,taje ta dawo haka take faman yi idanun ta sun gama rinewa suna shigowa tace.
Allah dai ya wadaran halinka ya lalace Taufiq Allah dai ya.....

Mum kada kiman baki mana dan Allah kiyi hakuri na shiga ukkuna!"
Bazan maka baki ba amman kasani ban alfahari da kai a matsayin ɗana ka yaudaremu nida mahaifin ka da makusan tanka kasa mahaifin ka jin kunya ka zubda mashi mutunci kai Hussein wannan halin naka baiba ka sauya sam ka canza ba Taufiq dina bane wannan,Taufiq dina yana kishina yana gudun fushin mahaifan sa,shidin gwarzon zuciyar shine,shine Sarkin ta ba ita ke mulkar shiba,amman kai kuwa bawan zuciyar kane,kasani indai baka gyara komai ba,kada ka kara kirana da sunan mahaifiyar ka,ni ban haifi maci amana ba.!"
Mum natuba kice zan zauna da Khairat dan Allah kuyafeni.!"

Bansan ganin ka a gabana Hussein,tashi kaje duniya wanda ke cikima tana jiran shi bare kai da inda amace kazo bako shakka kilan ka auras fita kabani wuri!"
Natuba Mum kiji tausayina dan Allah.!"

Ranar Taufiq, rana zafi inuwa ƙuna ya rasa inda zaisa kanshi yaji sa'ida a cikin zuciyar shi.
Haka rayuwa ta kasance agidan duk hanyar da zaibi dan ganin mahaifin shi Sarki ya dakile ta,bakaramin azabtuwa yake da hukuncin iyayen nashi ba.


********Zaune nike a falorn Baba nida Lukman gaisawa mukayi saidai daga ni harshi kowa yanajin nauyin ɗan uwan shi.
Lukman Saurayi ne kyakkyawa dashi dandai shi bakine amman bakin shi mai kyaune.

Mutumin Gusau ne dake cikin Jahar Zamfara State,daidai gwalgwado Lukman yanada rufin asiri kuma ba wani attajiri bane,duk da yau muka hadu dashi amman shidin wayayyene yana da sabo da mutane.

Ranar munjima muna gaisawa har yamma,Ahmad ya raka shi gidan Kawu Usman a dakin shi ya kwana kasancewar shi baida aure.

Washe gari misalin karfe 11am,ya dawo muka kara gaisawa,Baba yazo sukayi sallama sannan ya tafi Gusau.

Zuwa yanzun nasaki raina sosai,saidai jefi jefi Ya Taufiq yakan fado mani araina addu'a kawai nike har insamu nutsuwa cikin zuciya ta

Bayan kwana biyu baifi kwana ukku zuwa hudu aimani aureba ansai mani komai bakin ciki wajen Anty Hafsat fadar shi bata lokacine,Baba yakira Mum awaya inaji yana gaya mata bikina ranar asabar zuwa karfe biyu na rana,banji abinda tace mashi ba,naji yace insha Allah da haka suka sukayi salllama da yar uwar tashi wannan kenan.





_Yar Mutan Kankia ce❣️_






Share
Pls
❣️



_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E25&26



Ansakani lallai gyara na musamman Anty Murja ke mani da Anty Mubaraka ni kaina nasan na samu canji hankalina yafara kwanciya nasaki jikina da Lukman sosai hakanan naji zabin mahaifin nawa ya kwanta mani arai fiye da tunanina waya muke sosai da Lukman yana bani kulawa zuwan shi ukku kenan,da yamma Asma'u tazo da ya'ta Minah naji dadin zuwan su kwarai kayayyakin da Asma'u takawo na gudun muwarta suna dayawa,godiya su Mama sukai mata,itama anyi mata lallai tayi kyau matukar jibi ake daura mani aure saura kwana biyu kenan hidima ake babu kama hannun yaro,duk lokacin da Ya Taufiq zai fado mani arai sai tausayin shi ya kamani nasan iwar haka ya samu labarin aurena tabbas zai shiga cikin matsananciyar damuwa,wani side na zuciya ta sai ince hmmm yanacan da matar shi nasan ya manta da wata Minal da haka na cireshi cikin sabgata na ware anata hidimar arziki dani naka taba cewa nida Lukman auren hadine domin so yake nuna mani na gaskia



Gudunmuwa Mama tasameta bila adadin haka yan wajen aikinmu sunban gudummuwa kamar me alert kawai ake mani masu kawowa da kansu nayi saidai ince alhmdullh.



Saidai duk wannan hidimar da akeyo dangin Mama kaf sunkawo tasu gudunmuwar amman Anty Hafsat ko abinda ba aso bata badaba sai ya kasance bata zuwa gidan mu sai bayan isha'i tara nayi tayi gida ba abinda tayi na hidimata


A ranar suk kawo lefena akwati bakwai duk da kit dinsu sun zuba mani kaya a ciki gwanin burgewa sun dinka mani kala sha hudu a ciki komai yayi das.


********ni bazan hanaki zuwa bikin yar kanin kiba Maryam kefa uwace ga Amina da Allah namiji kike kece zaki daura auren Amina akan mi zan hanaki zuwa,bari kiji wani abu wlh ni ban tsani Amina ba asalima zanso ta kasance sirika ta a cikin zuriya ta amman bada Taufiq wannan shine akidata,ki shirya kiji hidimar ki,keda Fatima sai Aisha,kema Mufida ranar da zanje saikije masu baici nasan Tariq zaibar Aisha duk sai kuje insha Allah ranar daurin aure zamuzo daga baya,ga gudummuwa nan Allah yakaiku lafiya ya dawo daku cikin aminci."


Ameen Alhaji nagode Allah yasaka da alkairi."
Ameen.


Da rana Tariq yazo shida Aisha da ya'yan su suka biyoma Mum zasu wuce Caranci daurin aure kamar daga sama aka jefo Taufiq kana ganin shi zakasan iya tashin hankali yana ciki yayi ziruziru dashi gwanin tausayi Fatash ke jan troly zuwa falorn kasa.


Kallan su kawai yake koba'a gaya mashi ba yasan unguwa zasuje.

Oyoyo Daddy i miss u.
Cewar Mukhtar (little Major) ya rungume Taufiq.
My son where are u going,Mamana come here,Aira ta iso yai holding din su akalla suna cikin shekara ta shidda kenan zuwa bakwai.

"Caranci zamuje inji Dad."
Kallan Tariq yayi alamun tambaya.



Eh yanzun kuwa zamuje biki mu dukan mu.''
Kallan mahaifiyar tasu yayi yana mamaki.
Mum bikin wa ake a Caranci kona kawu Usman.?"



Aminatu akema aure jibi in Allah yakaimu."

A zarane yaja da baya yana kallan su with shock idanun shi sun kada lokaci guda girgiza kai yake yana


"Never Mum Aminatu tawace ni kadai Qaddarata da tata iri ɗayace miyasa Baba zaimin haka,Allah saina auri Aminatu.!"


Kallan takaici takema ɗan nata ji take kamar tai mashi duka,duk ya rikice gwanin tausayi.


Tariq ya rike shi yana bashi hakuri,ingije shi yayi a jikin shi.


"Kada ka kuskura ka kuma tabani aidaman kace zanyi 2/0 shine kaje ka zuga Kawun ya hanani Minal wlh ko zaka mutu Hassan saina auri Aminatu.!"



Kukane kawai baiyi danshi kukan zuci yafiyi zakaga idanun shi kamar rushi dan tashin hankali.


Kafita idona in rufe Hussein inakai ka haukace mu da hankalin mu zan saba maka."

Mum kitaimakeni kibani Minal na rokeki zan iya rasa raina.!"



Karya kake Hussein inka tashi ka mutu,ni zakucima zarafi a cikin gidana kuke mani maganar Aminatu irin wannan wato ka aure ta ko?kema harda ke dan haka yanzun yanzun kihada kayan ki,kitafi gida bance kikuma dawo mani cikin gidaba saina nemeki,kije can keda mahaukacin danki ku karata!




Kai kuma Hussein bangaya maka na fiddaka a cikin ya'yana ba,maza kabar mani cikin gida keyarka na kuma gani wlh azim saina halbeka uban kowa ya huta,bani bakai har abada.!"



Da sauri Tariq ya riko uban yana kuka yana bashi hakuri.
Abba Mum bata da laifi a cikin case dinnan kada ka tonamana asiri."

Sakin akace maka nayi ina sane,nasan ba abinda zamma Taufiq in kona mashi rai kamar in kora uwarsa shima ya dandanin bakin cikin daya sani dan haka wlh saita tafi,kaima haka.!"



Kuka wiwi su Fatash keyi banda Taufiq daya zube kasa yahade hannayen sa uffan ya gaza furtawa tsabar tashin hankali.


Ke Fatima yiman shiru ko insaba maki,idan baku iya zuwa bikin saiku zauna gidan uban ku.!"


Yana gama fadar haka y tafi Mum kuwa kuka takasa tsabar mamaki da takaici duk abin nan Mami na tsaye tanaji farin ciki kamar tayi sujjada a kufule Mum taja kafa tayi mota suka bita sai kuka suke haka suka tafi bikin Amina rai bace.



Taufiq yakai minti nawa kafin yabar side din kukanma ya kasayi,kota kanshi Tariq baibi ba yabar gidan shima cikin bakin ciki.


Shima fita yayi ya kwashi wayoyin shi da system yayi gidan shi dake kasan layin su inda aka aje Khairat,cikin tsananin tashin hankali.



********Da yamma likis su Mum suka iso baki daya gidan ya gama hargitsewa da murna marar misaltuwa,Fatash ta rungume ni mukayi cikin dakin mu,nida ita sai Asma'u sannu da zuwa mukai mata saidai kana ganin yanayin ta kasan tana cikin damuwa hakanan naji wani iri araina duk ba dadi fira muka hauyi Lukman yakirani waya na daga mika hau firarmu ta masoya banji nauyin Fatima dake gabana ba sai kallona take.

Murmushi nayi,dear ga Fatash ku gaisa."
Mika mata wayar nayi suka fara gaisawa dashi sunjima suna fira sannan sukayi sallama cigaba da wayata nayi aka hauyima Fatash kunshi suna fira da Husna.



Ina cikin wayar Anty Murja takirani,koda naje kiranta a katan falon Baba na iske su,shi da Mum,Anty Murja da Anty Zainab sai Baba Hassan,ina ganin su nasan kiran da sukai mani mai matukar mahimmanci ne duk da kowa cikin su yayi jigum jigum har kwara Baba yafisu karfin hali,zama nayi bisa kafat kaina kasa,gabana na faduwa a hankali.


Aminatu
Na'am na amsa ina kallam Mum.

Naji dadi yanda naga kinma mahaifin ki biyayya Allah yai maki albarka Mamana."
Ameen Mum.


Da'ace kin bijirema umurnin mahaifin ki,lallai da kinsamu matsala awajen shi musamman mahaifiyar ki komai akanya zai kare kamar yanda ɗan uwan ki yayi,kinga halin daya jefamu nida yan uwan shi,gashi da shekaruna ɗan cikina ya jazama mani zaman gida inaji inagani shi kuma mahaifin shi yai fushi dashi yanzun wa gari ya waya.!"


Hakanan naji kwalla sun ciko indanuna,tausayin ta ya kamani tunanin halin da Ya Taufiq ya shiga ya cika zuciya ta.


"Mum kiyi hakuri dan Allah kuma kada kiyi fushi da Ya Taufiq."
Kallona sukeyi zuwa lokacin nafara hawaye raina duk ya gama dagule mani.


Bakomai Aminatu,abinda nikeso ki maida hankali kiyima mijin ki biyayya kifidda komai aranki Mamana kuma ki manta komai da kowa kedai kisa Allah aranki kuma kikiyayi bacin ran iyayen ki.!"


Insha Allah Mum nagode.

Tashi kije Mamana,inji Anty Murja.
Kafata tai mani sanyi sosai haka nasamu na isa wajen su Husna saidai suna ganina sukasan ina cikin rudani abinda sukayi tunani hudubar aure akaimani daman sunsan kuka ya zama farilla inyi shi.


Kwantawa nayi inajin ba dadi acikin raina,ba wanda nike tunawa sai Ya Taufiq ashe ya rabu da matar shi!


Ranar sukuku nayini saida dare yayi wajen karfe shadaya kafa ta lafa Fatash ta tadani nan take gayaman abubuwan da suka faru da Ya Taufiq musamman karyar dayaima Abba,da hukuncin da Abba ya yanke akan shi da Mum

Please Login or Register in order to submit comment