Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hali yayi,fatan kin gane.?"
Eh Doctor insha Allah."
Allah yakaimu,ameen na amsa.

Kashe wayar yayi na sake maida idona na rufe inata nazarin rayuwa nayi zurfi a cikin tunani can na kuma jin wayata tahau ruri wannan karan bude idanun nawa nayi ina daukar wayar na kafe screen din da kallo ganin Prince (Taufiq) ya bayyana kin dagawa nayi hakanan naji kirjina na bugawa zuciya ta,ta tsinke jikina yai sanyi,sake kirana yayi sai na fahimci 3 times kenan yana kirana,dagawa nayi na kasa magana,inajin ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya.

"Minal.?"
Shiru nayi kamar ruwa ya cinyeni kuka nason kubce mani.
"Minal pls talk."
Na'am.!"
Nace murya a sanyaye.

Sauke ajiyar zuciyar ya kumayi.
Bansan ya nikejina ba ayau din nan Aminatu inama ban kasance a cikin rayayyu ba,ina cikin tashin hankali da fargaba duk saboda zan rasaki Minal,ina sonki ina kaunarki dan Allah ki kasance taredani har abada.!"
Kukan zuci nike dan bansan mi zance ba idan nace zan bude baki nayi magana tabbas kukan zai nasarar kubce mani.


Amina dan Allah kiyafe mani tabbas nasan kamar yanda kike Qaddarata haka nima nike Qaddararki,saidai inaji araina wlh Minal kece uwar ya'yana.!"

Ya isa Ya Taufiq so kake ka kara yaudarata!so kake ka sake breaking heart dina nasan bazamu mallaki junan muba dan haka kadaina cewa haka kaje ka auri wadda kakeso nima kabarni Allah zai kawo mai sona, dan Allah kada ka kuma nemana.!"
Shiru yayi ya rasa mi zaice mani jin shirun yayi yawa da zan kashe wayar sai naji anacewa,Katashi Taufiq lokaci na kurewa kuma kaga ba nan ake daura auren ba."

Hassan pls......
Tsinke wayar nayi,jin ana mashi maganar shirin zuwa daurin auren shi.
Kuka nafara mai ɗan sauti,sake kirana yayi naki dauka banda aikin kuka ba abinda nikeyi.
Sake kirana akayi wannan karan Ya Tariq ne.

Badan naso ba na daga ina sallama murya sanyaye.
"Haba Amina kuyi hakuri mana ku dauki Qaddarar ku,addu'a ita mafita agareku bawai kuka ba,ke kina cikin mawuyacin hali,Hussein ma haka bai iya tsinanama kanshi komai,miye haka dan Allah kusa salama a cikin ranku,gashi yace bai zuwa daurin auren kuma hakan zai haddasa rigima tsakanin shi da Abba pls convence him yaje daurin auren nan Aminatu."

Uhmmm,na furta ina goge kwallan idanuna,cikin karyayyar muryar shi yace.
"Minal kidaina kuka dan Allah bansan yanda akai hakan ya faruba ni kaina iske lamarin nan nayi,ki tausaya mani Minal kukan ki,shi zai kara tarwatsa mani zuciya,nayi maki alqawali rayuwa dake tahar abada Minal."

Ya isa dan Allah wannan kalaman naka suna karya mani zuciya naji na dauki Qaddarata dan Allah Ya Taufiq katshi kuje daurin auren nan kada kasamu matsala da Abba,kaima ka dauki Qaddara haka Allah yaso ina maka fatan alkhairi."

Muryar shi na breaking yace.
Minal ke kecewa inje daurin auren nan mafi ƙi da tsana agareni."
"Eh Ya Taufiq nice kuma da bakina,indai da gaske kana sona kaje,Allah yasa albarka da zuriya dayyi......

Kuka ya nemi kwace mani dan dole na datse wayar,Mama tsaye bisa kaina ban damuba saboda zafi da zuciya ta ke mani da sauri nayi daki ina kuka mai taba zuciya haka na wuni a daki jikina ya dauki zafi mai tsananin gaske.


******Da kyal aka samu Ya Taufiq ya shirya zuwa daurin aure mota daya suka shiga shi da Abba,suka zaune a baya sai Ya Samir da Tariq shike driving din suka tafi.

Ina cikin wahalallan baccin daya daukeni kawai na tashi firgigi zuciyata,tabada sauti da salati bakina na shiga bathroom na watsa ruwa banda zufa ba abinda ke tsatsafo mani doguwar riga ta material nasaka,yunwa ta taso mani kamar hanjina zasu tsinke dan dole na zubo abinci,dawowa nayi daki,nafaraci kallan bangon dake facing dina nayi naga karfe biyu daidai wata kasala na karaji nasan yanzun haka anacan dubban mutane na shaida auren Ya Taufiq,kwalla naji sun ziraro mani.
"Kawata anata sallama kinki amsawa mike damunki.?"

Kamar daga sama naji muryar Husna,tashi nayi na rungume ta ina kuka mai sauti.
Mama ke cewa.
Taya zata amsaki tunda tasaka kanta shiga ukku ya'yan zamani baku data ido ko kunyata bakiji kina kuka akan soyayya wlh Aminatu bakida kunya ko miskali zarratin ka haifi ɗa baka haifi halin shiba Allah ya shiryeki kuma kada ya hadaki da mahaifin ki a wannan halin da kike ciki."

Nidai kukan nike,Asma'u takama hannuna muka shige bedroom ta zaunar dani ta goge mani hawayena cikeda tausayawa.

Kawata kukan mi kikeyi miyasameki da harkika kasa sanar mani dan nemawa kanmu mafita dan Allah kidaina kukan nan jibi yanda kika jeme kikayi wani irin haske na wahala miyafaru gaya mani."
Bakomai Husna."

Jinjina kai tayi ta mike,lallai kam ba anfanin zamana kenan ko minti talatin ban kulla garin nan ba inata zumudin ganin ki,amman zaki mani haka yaushe muka fara yar boyeboye dake,ashe kin sauyani a matsayin aminiyar ki,ga yarki nan nina tafiyata."

Juyawa tayi na rikota ina rungume da Minah ko wasa ban iya yimata sai kwalla.
Ki tsaya Husna zan gaya maki dan Allah kada kitafi kibarni."

Zama tayi tana kallona tace.
"Naji kukan mi kikeyi.?"
Yau aka daurama Ya Taufiq aure Husna.!"

A razane ta mike tsaya tana sallallami tare da tafa hannu,dan danan ta shiga cikin damuwa,tai jugum,munjima a haka sannan ta riko hannuna ta cigaba da bani hakuri cikin tausayawa.


Kiyi hakuri Amina wannan jarabawa ce kuma mai imani ne kadai Allah ke Jaraba dan yaga imanin shi,tabbas nasan kin shiga tarkon rayuwa iri iri daga wannan sai wancan amman kisani badan Allah baison kiba ki dauki Qaddararki,wlh Minal da zakiga halin da Ya Taufiq ke ciki dole ki tausaya masa,auren dole ga ɗa namiji a wannan zamanin ba abune mai saukiba musamman shi daya jima bai aure ba,ace wai hadi akai mashi kina ganin zaiji dadin hakan kidaina kuka Allah yasa haka yafi zama alkhairi kema Allah yai maki zabin alkhairi ko kin huta da wannan rayuwar.!"

Share kwallana nayi ina kallan Asma'u wadda itama daurewa kawai take dan ta shiga wani hali itama nace.

"Husna kina ganin dama can Ya Taufiq baisan yarinyar nan,dacan ba aimashi auren hadin ba sai yanzun daya zama babban mutun wanda yasan right dinshi ban tunanin Abba zai masa auren dole,kawai dai yaga no way bazai sameni bane,shiyasa ya fidda zabin ransa.!"

Kaico Aminatu bakima Ya Taufiq adalciba yanda ya tsaya tsayin daka yace kece zabin sa amman yanzun kina zargin shi gaskia banji dadin wannan maganar taki ba,kema ya kamata ki shedi waye Ya Taufiq mutumin da magana bata dame shiba,bare har yai wani soyayya saida ya hadu dake harya saba da mutane shine kike cewa haka,kin bani kunya Minal."

Ajiyar zuciya na sauke nima sainaji ba dadi araina Ya Taufiq bai cancanci wannan zargin agareni ba,shiru mukayi baki dayan mu,kiran Abdallah ne ya shigo wayar ta, ta daga hankalina bai kansu naima Minah kuri da ido kuma ba ita nike kallo ba,nayi nisa a tunani.

Ki ansa Daddyn Minah ne."
Amsa nayi ina kirkiro murmushin karfin hali mukayi waya sannan na bata sukayi sallama.

"Minal nikam da zan baki wata shawara kila tai maki anfani."
Inajinki Husna wace shawarace.
"Kinga yanda Qaddara tazo maki mi zai hana bazakiba Ahmad dama ba akaro na biyu,kinga mutumin nan yana sonki,so na hakika gani nike keda Ya Taufiq kowa ya dauki Qaddara a yanda tazo maku,kiyi tunani kawata karki bari wannan damar ta wuce a karo na biyu Amina."


Jinjina kai nayi ina mamaki taya zan tari Ahmad da wannan zancen bayan dakaina nace na tsane shi kuma ban son shi infact hardai barazana da kisa naima Ahmad dan kawai ban son shi,Ya Taufiq nikeso.


Yanzun Asma'u kina ganin Ahmad zai kuma dawowa gareni bayan abubuwan dana aikata mashi abaya dan Allah kibar wannan maganar banji akwai ɗa namijin da zanba wani gurbi a cikin zuciya nadaina soyayya kiyi hakuri."

Aaa karkice haka kawata kedai ki bashi dama."

Dan Allah kibarni in samu nutsuwa ta Husna."
Shikenan kibar komai hannuna in kinzama normal kofa bude take kawata."
Naji,kawai nace mata nan kowa yaita sakar zuci.


*******Kaduna gidan Major kuwa yan daurin aure ne suka dawo su Mami keta rangyaɗa guɗa ganin Taufiq ya shigo cikin milk din yadi ko babbar riga bai saka ba.
Ango kasha kamshi Allah yakawo kazantar daki da zaman lafiya."
Cewar Anty Wasila.

Ameen Anty Murjanatu ta amsa su tana kara cewa.
"Wannan ranar farin ciki ce agaremu ɗan mu yai aure Allah yaimaka albarka yabaku zaman lafiya."

Shidai side dinshi ya nufa,kota kansu baibi ba,Allah kadai yasan yanda yakeji.

Ganin Anty Murja ta nata rangada guɗa sadaf su Mami sukayi part dinta kamar ruwa ya cinye su,sai lokacin Anty Murja tayi side din Ya Taufiq itada Tariq sai Fatash da Anty Aisha.

Falo suka taddata shi ya buga uban tagumi kamar wanda akaima mutuwa.
Taufiq,Taufiq,Anty Murja keta faman kiran shi,amman baiji suba,saida Hassan ya taba shi yace,Hussein ana ta magana miye haka.?"


Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kanshi
"Sorry Hassan banji bane,inna barka da rana.?"
Yai maganar yana kallan Anty Murja data zauna kusa dashi tana riko hannun shi,cikeda da tausayi irin na dangin uwa da sukema ya'yan yar uwar su tace.


"Kuka ba naka bane Hussein,kai namiji ne damuwa kuwa ba taka bace lokaci yayi da zaka rungumi Qaddarar ka,lokaci yayi da zaka sharema mahaifiyar ka kwallan ta,lokaci yayi da zaka danne damuwarka musamman a idanun makiya! Lokaci yayi da zaka maida komai ya zama tarihi a rayuwar ka,kaifa ba yaro bane Major shekarar ka nawa kasani, ya dace ace kaima kanada iyali so kake ka tazure har lamarin yai kamari,karka kullaci mahaifin ka gata yake so yai maka,mu kanmu dangin mahaifiyar munso ka auri Amina kasancewar ta jinin ka,amman Allah baiso ba,yanda Allah ya hukunta shine daidai Hussein kasa aranka haka Allah yaso komai ke faruwa kaji ɗana.?"

Jinjina kai kawai yayi kamar bazaiyi magana ba yace.
"Nagode Inna ta,Allah yasaka maki da alkhairi tabbas kin daurani bisa wani ƙaimi wanda nakasa zuwa zanbi shawarar ki,kuma na yarda da Qaddarata."
Allah yai maka albarka."
Ameen ya rabbi.

Yanzun kayi wanka kazo kasameni side din mahaifiyar ku,ka nuna komai ba komai bane kaji sannan kaje ka gaida mahaifin ka a side dinshi ka saki ranka,kaifa Soja ne sa maza fama haba Hussein na Hassan ka saki ranka mana."

Murmushi yayi kawai ya jinjina kai,bai tsaya jin ta bakin suba ya shige bedroom baki dayan su suka fita banda Hassan daya tsaya jiran dan uwan nashi.


Haka akaita hidima kowa ya maze duk yanda su Mami sukaso suga damuwa a wajen dangin Mum sun gaza gani kowa ya dage sai hidima ake kai kace Amina Caranci ce Taufiq din ya aura kowa fuskar shi fal da annuri.

Basu gama saduda ba saida sukaga ango Taufiq ya fito shida Tariq sai Murmushi suke gwanin shi'awa saidai kowa da kayan shi,Taufiq black din yadi yasa komai na jikin shi black ne saidai sun mashi kyau direct side din Mum suka nufa,a private falon ta suka isketa da yan uwanta zama sukayi suka gaidasu.

Wani irin dadi Mum taji ganin ɗan nata ya saki jikin shi nan aka hau labarai Anty Murja na dama fura tana ganawa ta zubama Taufiq saida ta matsa mashi ya shanye hakama Tariq shima bai wani samun kwanciyar hankali sosai bare yaci abinci cikin kwanciyar hankali,shima furar yasha,nan Mum taima Taufiq nasiha akan adalci kuma yaji tsoron Allah sun jima suka wuce side din Abba,nan suka same shi da kannen shi,zama sukayi suka gaida shi,cikin jin dadi ya kalli ya'yan nashi yace....





_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E11&12



"Masha Allah Hussein gaskia naji dadin ganin ka haka yanda ka saki jikin ka kuma kai mani biyayya Allah yai maka albarka,kaima Tariq daka dage wajen kwatantama ɗan uwanka ina fatan Allah yasaka maka da alkhairi duk yai maku albarka baki dayan ku,naji dadi da kuja girmamani kun nuna lallai nidin mahaifin kune."

Kirkiro murmushin karfin hali Taufiq yayi yace.
"Insha Allah Abba zaka sameni mai yawan biyayya agareka nima nagode da gatan da kai mani."
"Haka nikeso ɗana saidai wani hanzari ba gudu ba,yanada kyau ka zama mai adalci ga iyalinka kuma ka sauke hakkin matar ka,ka mutunta ka mutunta iyayen ta lafiya,iliminta,cinta da duk wani abu dakasan addini ya tanada shi akan miji wajibine ka sauke shi Allah yabaku zaman lafiya da zuriya dayyiba.
Ameen duk suka amsa shidai jinjina kai kawai yake.
Haka kowa ya tofa albarkacin bakin shi kafin nan suka tafi side dinsu.


********ina 6are dabino za'a zuba cikin markaden aya Baba yai sallama ya dawo daurin aure,hakanan naji kirjina na duka,sannu da zuwa mukai mashi ya amsa ba yabo ba fallasa yai cikin ƙurar dakin shi,kallo mukeyi amman sam ba dan ina fahimta ba.

Baijiba kwarai ba ya fito cikin Jallabiya zama yayi yana kiran Zainab ta zauna kusa dashi yana zolayar ta.
Baba yanada wasa da yaro duk zafin shi,saidai bai fiye yafiyaba musamman idan ya aminta dakai ka ha'ince shi,kuma idan ya rufe babin mutun kota kanshi baibi zaiyi kamar baisan Allah ya ajeka a waje ba.

Ya gajiyar tafiya Alhaji.?"
Alhmdullh an gama daurin aure cikin aminci alhmdullh."
Ya Umma take,nasan gobe Murjanatu zasu dawo."

Bansan ya Anty Maryam takeba kinsan iyakata Zaria ban isa canba ana gamawa muka dawo gida,tun safe da nayi waya da ita ban sake ba amman nasan komai kalau insha Allah."
Allah yasa kuma Allah yabasu zaman lafiya."
Ameen ya rabbi."

A sanyaye na tashi zan fita.
Aminatu dauko zobon nan ki kawoma Baban ki."
Toh nace,harna zira kafata waje naji Baba yace.

"Ban bukata ke baki da kafa indai bazakije ki dauko mani da kanki ba,bazan shaba,kisa Zainab mana.!"

Gabana ya bada sauti jin kalaman Baba wannan shike nuna Baba yana fushi dani kenan,kwalla naji zasu kubto mani da sauri na ida fita.

"Allah ya huci zuciyar ka."
Zuwa tayi ta dauko zobon nan ta iskeni ina kuka.
"Daman kin daina wannan sana'ar ke kikajawa kanki dagajin Taufiq zai aure ba kunya kika hau kuka,bayan kinsan waye uban ki,kuma kinsan ma'anar shirun shi,wlh Amina baki kyautawa kanki ba Allah ya kyauta.!"
Fita tayi abinta,nima aje dabinon nayi na shiga dakina.


Washe gari lahadi aka kawo Khairat gidan Sarki,direct side din Mum aka nufa da ita,su Anty Murja sun dage guɗa sai kace maroƙa,waisu ace basu bakin ciki dan bai aureni ba,haka suka zage akaita hidimar arziki dasu.

Da yamma akayi walima aka gama komai yai dadi,ana gama magrib aka dauki Amaryar Ya Taufiq zuwa gidan sa dake cikin unguwar Sarki ba wani nisa sosai da gidan su,Ali ɗan Anty Murja shi ya tuka motar amarya har gidan,Ya Tariq baije ba suna sashen Ya Taufiq shidasu Fatash,itako duk abinda ake tana wajen su itama kana ganin ta batajin dadin auren.


"Haba Hussein yakamata ace ni zan kaima amaryar ka har daki haba miye haka shine zaka hanani."
"Hmmm Hassan indai amaryata kake so kakaiman kasha kurumin ka idan na auri Minal kaine zaka kaita har gidan Major Taufiq,wanda na gina shi dan ita kadai kuma alqawali ba wadda zata fara shigar sa sai ita,kaidai katayimin addu'a Allah ya cikamani burina kafin ajalina.!"

Hmmm Taufiq problem ameen ya rabbi."

Ankai amarya an dawo sai yabawa akeyi da komai na gida,Khairat farace kuma tanada kyaunta masha Allah,yar babban gidace ma'ana mahaifin ta nada arziki abokin Abba ne sosai saidai shi custome ne.


Karfe tara su Ya Tariq suka raka Taufiq gidan shi bayan albarka dasu Mum suka sama lamarin,haka suka raka shi gidan shi cikin aminci suka taho dayake bikin nashi ba wasu abokai dan komai a kure akayi shi bai wata gayya yaiba,kannen shi (Cousin) sune abakon nashi har aka gama bikin suka raka shi gida.

Washe gari kuwa yan biki duk an watse hatta su Anty Murja ranar monday suka dawo,nikam naje wajen aiki munyi theater sai gab da magrib na shigo gida dayake evening nayi,a gajiye nadawo wanka kawai nayi banjima da zamaba su Anty Murja suka shigo oyoyo ga yan biki Mama ke masu,nima sannu da zuwa nai masu har zan tafi ta kirani na dawo da zauna kaina kasa saboda kallan da Baba ke auna mani mai kashe mani duk wani hope dina duk sai in kara raina kaina,jinayi ta kamo hannuna tace.
"Mamana.?"
takirani cikin sanyin murya na amsa.
Na'am."

Inasan ki bani aron hankalin ki,kiji abinda zance maki,jinjina kaina nayi dan nasan abinda zatace mani,ni kuma bansan ai mani zancen Ya Taufiq musamman a gaban Baba.

"Kinga yanda Allah ya tsara maku keda ɗan uwanki,inaso kiyi hakuri ki rungume komai a yanda yazo maki,ki daina damuwar kanki,kodan lafiyarki koba komai ke likitace bai kamata kina shiga cikin damuwa ba kodan lafiyar al'umma ki dauki Qaddararki sannan kita addu'a kema Allah yaimaki zabi na kwarai.!"

Magana zanyi Baba ya dallama mani wani matsiyacin kallo dole na hade magana ta.
A fusace yace.
"Wai mikike haka Murjanatu wannan ba maganar yi bace,kada ta dauki Qaddarar tata,mana inta tashi dan Allah ta mutu,Aminatun wofi da za'a zauna ana tattashin ta! kada kisa raina ma ya baci a banza da wofi,ni naji dadin auren nan wlh kuma kada ta fidda Hussein din aranta,sakarcin banza sakarcin wofi.!"
Haba Yaya bai kamata kace haka ba kaga.....

"Yiman shiru Murjanatu zan saba maki bansan sakarci, zakizo kina wata magana wai tayi hakuri kada tayi ta mutu wa taima asara.!"

Tashi yayi ya fita yana bugo kofa har saida cikina ya katsa,itako Anty Murja tana mamakin halin ɗan uwan nata,nikam fargabar haduwa ta,da Baba ta cika mani kasan zuciya.

Hakuri Mama taitaba Anty Murja dan bataji dadiba musamman yanda taga Baba ya nuna halin ko in kula,a ganin ta ina bukatar ja ajiki dan adinga bani baki amman Baba ya dauka da zafi.
Haka suka jima saida akai isha'i Ali ya shigo ya dauke su suka tafi gida.

Mama tafara yiman fada najawa kaina,Allah ya kyauta mani,nidai shiru nayi,kiran Asma'u naga ya shigo naki dauka.

Yanzun kiran ke bazaki dauka ba ko.?"
Kamar in kurma ihu na dauka.
"Minal gobe zan koma gida fa,kizo da wuri dan Allah."
Shikenan Allah yakaimu.
Ameen tace.
Daki na shiga na kwanta inajin bacci mai nauyi saidai baki daya daren gaza bacci nayi dana fara sai in farka ina tunanin shikenan Ya Taufiq yanacan da amaryar shi nasan daya kwana biyu zai share babin rayuwa ta baki daya zai koma ga matar shi
Sai kusan ukkun dare bacci ya saceni.

Washe gari kuwa da wuri naje gidan su Husna kitso nai mata, bayan da zanyi dan dole nai mata sai jana da firar Ahmad takeyi ina mazewa har nagama mata,saida aka kiran sallah mungama,ukku daidai Abdallah yazo daukar ta,sallama taima su Mama na rakata har bakin mota ina daga mata hannu suka tafi har saida suka bacema ganina sannan na dawo gida.

•••••••••••

da misalin karfe biyu na rana na shirya zanje wajen aiki ranar Ahmad nanan yazo gida hutu,shima zaije Katsina Continectal Computer zaiyi wani payment,tare dashi muka fita shike jan motar muna yar fira,saida yafara saukeni hopital sannan ya tafi harkokin gaban shi,ina shiga office bada jimawa ba,patient suka fara shigowa kowa da kalar matsalar dake damun shi,na jima a office dan ma likitocin mu ukkune 01,02&03 sai layin yai sauri sadda za'ayi la'asar kusan kowa an duba shi,kuma angama buking ganin Doctor sai gobe,tafiya nayi department dinmu can na iske Inchard din mu Dr Siddi gaida shi nayi.

"Lafiya lau Dr Amina,ya aikin.?"
Alhmdullh.
Cikin ku waye zaiyi Call a Theater.?"
Nice ranka shidade.
Allah yakaimu lafiya."
Ameen.

Rest room na shige zare lap court dina nayi na shige toilet banjima ba na fito da awallah salla nayi sai karfe biyar Ahmad ya kirani awaya,ina dagawa.

"Anty ina bakin OPD ke nike jira.
Toh nace na dauki handbag dina na fito naima masu night duty sallama natafi,ina zuwa kuwa na iske shi bude mota nayi na shiga muka taho gida,duk na gaji ba mai magana a cikin gwara shi dake waya kunnen shi sanye da head phone,muna isowa gida daidai Baba yana parking motar shi sannu da zuwa mukai mashi ya amsa ba yabo ba fallasa.

Sameni palo na Ahmad."
Toh yace yanabin bayan Baba nikuwa daki na shiga ina sauke sanyayyar ajiyar zuciya,zare kayan jikina nayi na fada bathroom dan watsa ruwa.

Fitowa ta keda wuya wayana yaci gaba da ringing,dauka nayi ganin Fatash ke kirana.

"Minal kenan inba yaki miya kawo gaba."Dariya nayi saboda maganar tabani dariya.

Fatima kenan wane irin gaba kinsan aiki yanda yake shiyasa amman ba wani abu wlh."

Toh Allah yasa ya Husna da babyn mu."
Kinsan basu jima da komawa ba."
Allah Sarki,ke kawata na samu aiki fa.

"Dan Allah natayaki murna."
"A ina kika samu.
NEPA ne nasamu."
Yayi Enginear Fatima Sarki Mukhtar Munzali Kaduna,Allah yasa albarka."

Ameen wannan sunayen duk sai anjero mani su,kedai kinada abin dariya wlh."
Dariyar na sakeyi,ban kaiki ba."

Da haka muka kara fira sannan mukayi sallama,kaya na saka na kwanta.

Koda dare yayi dakin Mama naje ina tayata fira nidasu Ahmad,yana bamu labarin School dinsu.
"Wai payment din mi kayo."
IT zamuyi muna komawa school kuma inasan inyi nawa a Abuja insha Allah."
Allah yasa,ameen."

Assignment nafara yima Hauwa'u wadda ke Pri 1 munjima muna fira kafin nan kowa ya koma daki ganin har 11 tayi dare ya yafara.
Ina kwanciya bacci yai gaba dani hankalina kwance.


*******Koda safiya tayi aikin gida na taba duk da munada mai aiki,abinci na dafa mana ina gamawa,na zuba na koma falo ina kallan Geet indian Series.
Sosai na maida kallona bisa tv dan ina enjoying din films.

Sallamar Anty Hafsat naji ban dago na kalleta ba na gaidata,amsawa tayi.
Kowa yai shiru nida ita kamar wasu kurame.
Ina Mamar ki.?"

Tana dakin ta.
Kira mani ita ko.?"
Kallan ta nayi sai mukaji shigowar Mama tana waya shiyasa bance komai ba.
Zama tayi tana gama wayar gaishe da Yayar tata tayi.

Ashe Taufiq yai aure Khadija shine ko a gaya mana ai da mun masu kara ko nice aida naje ko.?"
Dariya Mama tayi,tana kallan Anty.

Haba Anty wa'anda ya zamema tilas ai sunje bikin,ba wani abu, su Murja da Baban Amina duk sunje.

Amman ina laifin wanda yace zai maka kara."
Babu laifin sa, dana sani na shaida maki amman ai akwai sauran yara agidan in za'akara aurarwa insha Allah zan sanar dake."

Da kin kyauta kuwa,ashe yar Zaria ce ya aura.?"
Ina kikaji."
Mama tai mata tambayar.

Duniya da fadi aishi zancen duniya bai boyuwa."
"Gaskia kam nima dai haka naji inaga yar cance."

Baki tabbatar ba kenan.?"
taima Mama tambayar tana mata wani irin kallo
"Gaskia kam kinsan abinda bai shafeka ba,baka bashi wani mahimmanci shiyasa."

Uhmmm kawai tace,sai lokacin na tashi kashe tvn nayi na shiga daki,a raina nace gulmamma wai bugun cikin Mama zatayi Allah ya wadaran naka ya lalace.
Cigaba da kallona nayi daki ta system nai connecting Wifi da wayata.

Haka rayuwa ta kasance a gidan mu,saidai har yanzun Baba bai saki dani ba,ina gaidashi yakan amsa amman bai bari fira ta hadamu,wannan kenan.





_Yar Mutan Kankia ce❣️_






Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E13&14


_Wannan page din Sadaukarwa ne ga dukkan masoyana da fatan anyi Juma'a lafiya kardai amanta dayima annabi salati Allah yabamu akbarkacin shi ameen ya rabbi🙏🏻_

••••••

Tunda aka ɗaurama Taufiq aure ba wani maganar kirki data hada shi da Khairat asalima tinda aka kawota da daddare abokan shi natafiya ya wuce part din shi bata kara ganin shiba.


Haka Khairat ta zauna ita kadai ga bakunta amman ba ango ba alamun shi,ranar haka ta kwana sukuku da ita ga tsoro duk ya addabeta.

Washe gari da safe Mum tahada masu break fast Fatash da Zakiyya sukaje kai masu,knocking sukayi Khairat ta taso ta bude masu ganin su Fatima ta kakaro Murmushi a fuskatar ta,shiga sukayi ciki suka zauna sukayi falo.
"Anty Khairat ina kwana ga break nan inji Mum."
Lafiya lau mungode.
tace cikeda sakewa

Dan taba fira sukayi kadan saidai ba Taufiq na alamun shi har suka tashi zasu tafi.

Ina Yayan yake.?"
Cewar Zakiyya.
Yadan fita yakusa dawowa."
Tace a sanyaye.
Kigaida mana dashi,inji Fatash.
Zaiji tace masu,tafiya sukayi saidao ba lallai bane in sunyarda da maganar taba,sunsan halin yayan nasun koda yake gida bai fitar sassafe bare yanzun da yai aure.

Itako bin abincin tayi da ido takaici ya isheta ace kana amarya ba wata kulawa da kake samu wajen angon ka.
Haka taci abincin tagama bata da wani karfi duk jikin ta yai sanyi.


Da yamma su suka sake kawo masu Dinner nan ma basu tadda ɗan uwan nasu ba,still da suka tambayeta amsa daya ce,wannan karan kuwa tafiya suka basuce suna gaida shiba,dan Fatash tafara tunanin akwai matsala daman da wahala ta samu Taufiq cikin ruwan sanyi,saboda bai ganin kowa a halin yanzun baiji zai sota aranshi
Haka rayuwa ta kasance gidan Major Taufiq tsakanin shi da Khairat.

Koda dare yayi tsoro da fargaba ya cikata,tana son tai bacci amman ta gaza dan shakka gani take kamar za'a iya dauketa koda rana daurewa kawai take bare dare hakan yasa ta yanke shawarar sawa akawo mata yar aiki da mai tayata zama,kafin mijin ta ya dawo gareta,uzurin da tai mashi sanin auren hadɗne amman tasan idan ya sauko zai

Please Login or Register in order to submit comment