Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Siddi sai nurse guda biyu aka fara aikin cikin kwarewa da takatsantsan na aikin likita cikeda tawalu'u mun mika Allah lamarin shi,cikin ikon Allah one hour bamu daukaba muka fiddo yan ukku duk maza zar tubarakallah,haka aka gama nan naci gaba dayi mata dinki bayan nurse sunfita da babies din dan shiryasu.

Ina gamawa na zare kayana aka kaita rest room,ina fitowa lokacin har ukku tayi,banjima ba na shirya fita nayi kawuna yazo muka tafi siyen mota daman already sunyi magana da MD cars din, ina zuwa na dauki matrix light red sai daukar ido take,muka basu kudin su,nan muka shiga yaja mukayi gida saboda ban wani kware da iya mota ba.
Ranar nasha murna sai zuwa tayani murna akeyi maƙota da sauran yan uwa da abokan arziki.

Koda nakira Husna sawa tayi nai mata snap sai murna take,hakama Ya Taufiq na tura mashi hoton ta,Uncle Ali yaita koya mani motar cikin ikon Allah banyi one month ba,na kware sosai har Baba shima yana koya mani,yanzun nafara zuwa aiki da kaina da Ahmad ke kaini,shima ya tafi school Udu yana karanta Mass come,haka rayuwa takasance gwanin dadi masha Allah.

*Kaduna* """""

Tunda Mun tayima Ya Taufiq maganar ya fidda Amina a zuciyar shi bata kuma kara mashi maganar ba,tasama sarautar Allah ido tasan har yanzun.......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E5&6



*******tunda Mum tayima Taufiq maganar ya fidda Amina a zuciyar shi bata kuma kara mashi maganar ba tasama sarautar Allah ido,tasan har yanzun suna tare da juna saidai tana guje mashi abinda kaje ya dawo musamman haduwar shi da mahaifin shi tasan wannan karan ba mai kyauba ce,shiyasa kullun da zullumi take kwana tana tashi aranta.


Taufiq ne, a Nmandi AZikuwi International Air port Abuja Soldiers ne suka sauke shi dan dai shi jikin shi Suit ne blue black bai jima sosaiba jirgin su ya tashi zuwa kasar Paris shida wasu sojoji amman basu dayawa.

Koda ya isa already anka masu hotel kowa da room dinshi akwai aikin da zasuyi na tsawon sati biyu akasar.


Hadin gamayya ne tsakanin abokan aikin kasashen guda biyu,da Major Sarki zaije saiya maida Assignment kan Taufiq dan akwai abu mai mahimmancin gaske dayake son ya aiwatar kafin dan nashi ya dawo gida.

Aiki Taufiq yake sosai,ba kama hannun yaro,tinda ya iso Paris sau daya sukayi waya da Amina tinda sukai magana basu karaba anan yake gaya mata aiki zaiyi na sati biyu bazai jimaba zai dawo.



*Kaduna*


A tafkeken falon Major Sarki Mukhtar kannen shine da matan sa sai ya'yan sa kowa ya nutsu ga tarin kaya aje gaban su,biscuit,sweet da sauran kaya kana gani kasan kayan sa rana jibge abin ba'acewa komai tsabar yawan su.

Maida kallan shi yayi garesu yace.
"Inafatan kun gane Hamza yanzun zansa Osama yakaiku gidan su Khairat munyi waya da iyayen ta sunsan da zuwan ku."

Tom Yaya Allah yasa ayi asa'a ai lamarin nan yai mana dadi kwarai dagaske."
Ameen suka amsa musamman Mami harda tayasu fidda kaya aka zuba cikin motar hilux Usama yaja suna biye dashi a kananun motoci harda Samir suka tafi gidan Alhaji Mas'ud dake tudun Wada Zaria.


Mum kuwa tunda lamarin yafaru saita gaza sukuni tashiga damuwa mai tarin yawa Tariq ke tausar zuciyar mahaifiyar tasu,hardai ta gaza hakura washe gari da yamma taje falon Major yana zaune shida Mami waya yake da Taufiq akan aikin da sukaje gabatarwa Paris,da sallama abakin ta ta zaune kujerar dake facing ta mijin nasu cikeda kulawa tace.

"Barka da yamma Alhaji."
Yawwa ya autata yau batazo gaida Abban nata ba."
tana karatu shiyasa Extra lesson Obinna ke mata."
Allah yataimaka hakan yana da kyau."
Ameen suka amsa.

Shiru tayi tarasa ta ina zata fara banda kallan kasa da Mami ke mata ta cikeda tsana.

Shima jin shirun yayi yawa hakan yasa ya kalleta cikeda kulawa yace.
"Hajia Maryam akwai abinda kike boyewa minene fadamani.?"

"Alhaji nagaza samun sukuni araina ganin hukuncin daka yankewa Hussein sa ranar nan da akayi mashi kaga baisani ba,bansan wane hali zai shigaba Idan yadawo ya tadda wannan labarin ba.!"

Wani kallo ya akaima Mum a fusace yace.
"Idan ya dawo nace ya mutu saime? shi kadai na haifa,wlh Maryam wannan shine karon farko da Hussein zai ketare umurnina matsawar hakan tafaru tabbas na barranta shi a cikin ya'yana wlh bazanyi kaffara ba.!"

Kwarai kuwa Alhaji shi Hussein din wani yafi da zaiki yima uban shi biyayya."
Cewar Mami tayi maganar cikeda tuggu.

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un haba Alhaji kada kaiman haka ɗan nawa kake nema yima baki!karufamani asiri komai zaizo cikin sauki dan Allah."


Yiman shiru ban fatan komai yazo cikin sauki tsakanina da Taufiq muzuba mugani nidashi waya haifi wani,kigaya mani kaf ya'yana ba wanda nafi so da kauna irin Taufiq bansan inga ya shiga damuwa ko tashin hankali akan Taufiq ba abinda banba dan inganta rayuwar sa sau nawa kikasan ya'yana sunfara challanges dina ina nuna banbanci tsakanin su, Arthtactor ya karanta amman dan kusanto dashi a jikina nasa yaje yai Course kan Soja duk dan ya gajeni ni uban shi! Shine zakizo mani da wannan zancen banzan Amina daice ko bazai aureta ba alqawali in zai dauki Qaddarar shi tunkan dare yai mashi ya dauka,maganata baja da baya ,saidai inshi din ba jinina bane shi kuma bani zatan haka,ina jan kunnenki Maryam ki fidda kanki cikin shirgin nan,karki manta zan iya sauyaki amman bazan iya canza Hussein ba koda na cireshi cikin jerin ya'yana dole a kirashi da Hussein Mukhtar kuma ya amsa har abada,fatan kin fahimta.!?"

Wani irin bugawa kan Mum yayi kwalla na ziraro mata ta gyada kai tasan wannan karan ya zama dole Taufiq yabi zabin mahaifin sa indai yana san gamawa lafiya."

Mikewa tayi jiki sanyaye tayi side dinta kuka sosai take,Tariq da Aisha suka tareta suna bata hakuri haka ta wuni cikin tashin hankali.


*****Nikam banda wata damuwa saboda sport dina da mahaifina keyi zuwa yanzun aikina nasa agaba na aje komai da kowa,duk da Ya Taufiq yana yawan fado mani araina kuma kadan kadan sai inji gabana na faduwa ,sai nayi niyar kiran shi sai intuna bai kasar kuma yace mani aiki zaiyi mai mahimmancin gaske na tsawon Sati biyu,saina zamana kullin ina cikin lissafi abin kiyayewa.

Yau ni nai mana girkin abinci Jallof rice and beans saikifi dataji a ciki sai alayyahu,daman indai zanyi girki ina zuba ganye a ciki saboda mahimmancin sa a jikin dan adam,ina gamawa Baba kawai na zubamawa akula na juye sauran cikin kular gida na zuba nawa,komawa nayi falo inaci hankalina kwance,inaci ina chat da Asma'u,tana gwada mani kayan da Abdallah ya siya mata masu karen kyau da tsada video call mukeyi ina ganin yanda Minah takara wayau sosai,gwanin ban shi'awa.
munjima muna fira rabi duk kan Ya Taufiq ne take tambayata har yanzun cikin mu ba wanda ya hakura da juna bare muyi aure.

Eh nace mata,kinsan lokacine koda mun hakura da juna aikin san akwai sabo atsakanin mu."
Hakane kam Allah yai zabin na kwarai."

Ameen ya rabbi nace mata,mun kara fira sannan mukayi sallama da junan mu.


*******Ansaka ranar Ya Taufiq cikin sati biyu za'ayi komai agama Abba shike kidin shi yana taka rawar shi sai Mami da takoma kamar uwa dan tafi kowa farin cikin lamarin,kuma yajama kunnen sa , ya'yan sa da matan shi,harda ma'aikatan gidan musamman makusantan Taufiq yace kada wanda yagaya mashi hakama Usama ba karamin warning Major yai mashi ba.

Da kanshi yasa akayi ordern lefen kaya akwati takwas yayima Khairat ana saura kwana biyar bikin yasa aka kaisu gidan su.


Mum takasa hakuri kullin aikin ta kuka dan dole takira Anty Murjanatu tana kuka tafara gaya mata abinda ke faruwa da tayi fushi bata gayama kowa a cikin dangin ta ba,ganin da gaske Alhaji keyi ba shiri tafara gayama yan uwan ta halin da ɗanta ke ciki.

Hankalin Anty Murja yai masifar tashi zan iya cewa nida ita bansan wayafi wani shiga kiɗima ba,saidai nafita shiga damuwa tunda naji abinda ke faruwa tsayiwar kwarai na gaza banda kyarma ba abinda nikeyi tareda zufa keta keto mani kace aikin gona nayi.
Ban tsinke da lamarin ba saida naji Baba yana cewa.

"Alhmdullh hakan shine daidai wlh Allah yasa abokiyar arzikin shi ce,yabasu zaman lafiya da zuriya dayyiba"
Ameen Mama ta amsa bisa labban ta itama duk bataji dadi ba,domin yanayin kadai ya nuna hakan ainun.

Haba Ya Yusuf taya zaka dinga goyon bayan Alhaji Mukhtar zaima yaron auren dole ai bai kamata agoyi bayan shiba haba dan Allah.!"

Kinga Murjanatu wannan shine daidai akan mi zai sakama Taufiq ido shiba yaro ba,yaki aure so kike ya tazure har abin ya wuce misali komi kike nufi!?"
Azafafe ya jefa mata maganar.

Aaa ba haka nike nufi ai ya zabi Aminatu yace ita yakeso akan mi,bazai aura mashi itaba.?"
Mikewa yayi wannan karan yace.

"Ko nine uban Taufiq bazai auri Amina ba,tunda yagaza yima uban shi biyayya,sannan nine uban Amina ko,kuma Taufiq dan yayata ne banji har abada zan iyaba Taufiq Aminatu dan......


Fashewa nayi da kuka mai sauti har saida attension dinsu ya dawo kaina da gudu na afka daki ko ganin gabana banyi,take wani masifar son Ya Taufiq da kishin sa suka addabeni har bangani sai uban kuka nike kamar raina zai fita a jikina.

Bantaba zatan haka nikeson Ya Taufiq ba saida labarin bikin shi yazo kunnena abin tashin hankali gobe saura 4days a daura mashi aure da wata daban bani ba!.....


*******Tunda nayi kuka akan maganar Ya Taufiq Baba ya sauya mani ko gaida shi nayi zai amsa ba yabo ba fallasa amman bai wasa dani kamar yanda yasaba,a susuce nike rayuwa kullin kukan zuci nikeyi amman nace Ya Taufiq ne ya yaudareni daya dasa mani son shi araina tun ina yar kankanuwa ta.

Mama ke mani huduba dabani shawara cikin nutsuwa.

Yauma ta iskeni na buga uban tagumi hawaye ba zirara bisa kuncina naji ta riko hannuna tana share hawayena tace.

"Musulmin Kwarai shike daukar Qaddara a yanda tazo mashi Aminatu,kada ki damu yanda Allah yaso shine daidai kidaina kukan da kikeyi kibarma Allah ikon shi kinji Aminatu na.?"
"Toh Mama amman bansan ya Qaddarata ke zuwar mani ba,nasaba da Ya Taufiq amman kuma......


Kukan daya taho mani dan dole nahade kingin maganata ina jan majinar data taho mani kaina na ciwo.

Aminatu karki manta kefe likitace akan mi zakisa damuwa aranki kuma kinsan illar hakan! Sannan inkika zama counciousnes a damuwa kikaje duba patient kinaso kiyi kwaba a wajen aikin ki.?"
Aaa Mama."

To idan hakane ki maida komai ba komai kisa aranki Qaddarki ce kuma kowa da kalar tashi Qaddarar!
"To Mama zanyi iya kokarina in dauki Qaddarata aduk yanda tazo mani nagode maki."
Allah yaimaki albarka."
Ameen.

Cigaba da rayuwa ta nayi,ina addu'a amman son Ya Taufiq kamar aikin sihiri kullin kara lunkuwa yake a cikin zuciya ta.


```Ya Allah karabamu da Qaddarar soyayya a rayuwar mu babbar jarabawa ce,ameen ya rabbi```


Duk abin nan ban gayama Husna ba banso ta shiga damuwa dan na fahimci idan nashiga damuwa takan fini shiga saina danne tawa damuwar naci gaba da gudanar da al'amurana kamar ba abinda ke damuna.


Yau saura kwana biyu biki, Major Taufiq kuma yau yake dawowa daga Paris zuwa lokacin Major Sarki yagama hada komai hatta abinci da ruwan sha yayi Order lokaci kawai yake jira har fenti sabo saida ya sauyama gidan yasake ma matan shi furnitures sai rawar kafa yake ɗan shi Taufiq zaiyi aure,tin Mami najin dadin lamarin dan ganin Mum cikin kunci nasata nishadi, itama harta fara jin haushi badan komai dan ganin mijin nasu yanata murna kamar bai taba aurar da ɗaba a duniya,komai da kanshi yake sai Tariq da Samir dake taya shi har an kammala komai,hatta dunkunan da Ango zaisa yayi komai ya damka hannun Tariq shidai baida zabi saibin umurnin mahaifin nashi yake kuma bai sanarwa dan uwan nashi ba.


Yau Jirgin su Major Hussein Sarki Mukhtar Munzali yai landing a birnin Abuja already anzo daukar shi direct gidan su na Maitama aka wuce dashi saida suka huta sosai da yamma likis aka dauke shi sai Kaduna direct part din Major ya wuce kallan gidan nasu kawai yake ga mutane daketa zuwa anata shige da fice saidai ya kalli Tariq shiko ya soke kai kasa bai gama mamaki ba saida ya shiga private falon mahaifin nashi yaga an sauya furniture kamar jira Sarki yake ya mike ya rungume dan nashi yanajin dadi na musamman.

U re well my son,my hero General Major Hussein Sarki Mukhtar Munzali,well come back to home.
Shima kara rungume mahaifin nashi yayi cikin so daukana yace.......





_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E7&8



"Thank u Sir am proud of you."
Zaunawa sukayi baki dayan su,saijin dadi Major Sarki yakeyi.
Mami ce ta shigo cikin falon da sallama,baki daya suka amsa mata ta zaune bisa kushin tana facing Taufiq.
Kallo ɗaya yaimata ya gaidata batareda ya kuma kallan taba.

Itama amsawa tayi fuska sake dan wani dadi takeji na musamman tasan alakar Major da Taufiq ba ko shakka tazo karshe.
"Abba wai naga an fente gida kayi sabbin furnitures kamar dai ana wata hidima a gidan,Abba kodai su Mum zaka karowa kanwa.?"
Ya ida maganar a sifar zolayar mahaifin nashi.

Murmushi Alhaji yayi yana rike hannun ɗan nashi a hankali yadan murza yatsun shi cikeda so da shauƙi yace.
"Ko daya saidai kamar yanda ka canka bikin ne za'ayi kuma nan da jibi asabar insha Allah."
Jijjiga kai yayi alamun mamaki a fuskar shi yace.

"Ikon Allah ashe dai na canko daidai ko bikin Maimuna yatashi yar Baba Hamza.?"
Aaa sai watan gobe ne za'ayi nata."
Wannan karan shiru Taufiq yayi baisan mi zaice ba kuma bai son ya cika yawan tambaya.

Fatash ce da Mum suka shigo cikin falon,kallo daya yaima mahaifiyar tashi ya gano tsantsar damuwar ta,itama zama tayi,cikeda kulawa ya gaida mahaifiyar tashi,amsawa tayi ba yabo ba fallasa,kannen shi sukai mashi sannu da hanya,ya amsa.
"Mum ko baki jin dadi naganki wani iri.?"
Girgiza kai tayi alamun lafiya lau.
Lafiyan ta lau Hussein hidima ce da take fama da ita ta wannan bikin shiyasa."

Cikeda mamaki ya kalli mahaifin nashi yace.
"daman bikin ya shafi Mum ne,nikam wace hidima ce wannan anki gaya mani ita saidai kace hidimar saida gold."
Murmushi Major yayi har saida hakoran shi suka bayyana"
"Ai wanda akema wannan hidimar yafi gold daraja a wajena Hussein kaunar da nike masace tajawo hakan nafi kowa son inganshi a matsayi mafi daraja da daukaka saidai kash bansan ko son da nike mashi,irin shi yake mani ba,bansan ko zai iya karbar wannan kwarkwaryar girmamawar dana shirya mashi ba,da ace zai ansheta lallai kam daya gama biyana har gaba da abada."

Murya sanyaye Taufiq yace.
"Abba nifa bani ganema irin wannan yaren wanene zakaima wannan girman yaki?kuma wane abune kake shiryawa harka.?"


Kaine Hussein kuma biyayyar ka kawai nike bukata a wannan tafiyar ba wani abu ba.!"
Wani matsanancin faduwar gaba ya daki zuciyar Taufiq dakewa kawai yayi yace.
"Abba minene wannan abun da har kake bukatar biyayyata.?"

Mikewa yayi ya kalli Taufiq dake zaune kamar an dasa shi yace.
"Kaine Hussein kuma biyayyar ka,nike neman akan abinda zan sanar dakai,ada nayi niyar saidai kaji anyi angama saboda babu abinda zaka nema karasa sai kuma na sauya shawara in sanar maka hidimar da akeyi,jibi asabar iwar haka kazama magidanci mai iyali kamar kowa ma'ana za'a daura maka aure insha Allahu."

A hargitse Taufiq ya mike har yana cire holar kanshi ta Soja zufa duk ta gama wanke shi kanshi na bala'in sara mashi jin maganganun mahaifin nashi da yake mashi mai rikitarwa da ɗimauta.

Tattaro Jarumtar shi yayi yace.
"Abba aure fa kace?ni Hussein za'a daura ma aure nan da kwana biyu ban saniba kuma wacece yarinyar Abba ka tausaya mani dan Allah.!"

Dole ya baka tausayin domin ya gama dimaucewa kamar karamin yaro kuka kawai ya rage ya fashe dashi dan takaici.
Juya mashi baya Major yayi dan baisan tausan dan nashi yayi tasiri agare shi yace.
"Kwarai kuwa Hussein kai zanma aure kuma ba kowa bace sai Khairat yar aminina Alhaji Mas'ud Kwangila ita na zaba maka matsayin mata har lefe ankai da sadaki naira dubu sittin lakadan ba ajalan ba,jibi shaidawa kawai za'ayi ɗana."

Zubewa yayi bisa guiwowin shi ya riko hannun mahaifin nashi idanun shi da basu da banbanci da rushi dan ja yace.
"Katausaya mani Abba ka soni koda sau ɗayane kada karabani da zabina dan Allah ka auraman Aminatu ita nikeso,bansan ya zan rayu da wadda banso ba pls am beg of you Abba.!"
Fizgi hannun shi yayi yana sake shan kunu ba alamun wasa.

Bansanka da kowaba sai Khairat ita na zaba maka amatsayin mata,ni zakace in soka koda sau ɗayane Hussein kasan tarin son da nike maka? Zan iya cewa nafi sonka fiye da yanda kake kaunar kanka,dan haka dole kabi umurnina matsawar ka yarda nine ubanka.!"

Wannan karan kuwa ya gaza magana tsabar ɗaurewa da kanshi yayi yana mamakin lamari irin na mahaifin shi wannan shine son a hana mutun auren abinda yakeso anya Abba yana cikin hayyacin shi ina son dayake masu ya tafi ya zaiyi da ranshi mike shirin faruwa har haka cikin kankanin lokaci daga yaje PARIS ya dawo komai ya canja cikin kankanin lokaci WHY.?

Sake matsawa yayi gaban mahaifin nashi yace.
"Abba dan Allah na rokeka kayi hakuri karka zartar da wannan al'amarin.!"
A fusace Major yace.
"For the last time da zankara maimaita maganar nan Taufiq wlh blh saidai in mutuwa kayi amman aure anyi angama muddin ka bijirema umurnina a wannan karan BANI ba KAI kuma har abadan abada nayafeka a cikin ya'yana wannan kuma alqawali ne Hussein.!"
Dafe kanshi yayi yana son ya karaba mahaifin nashi hakuri bakin shi yai mashi nauyi,itako Mum takasa magana saidai kallan data watsa mashi tana girgiza mashi kai alamun kada ya kuma cewa uffan!
Kifewa yayi kanshi kasa kamar mai sujjada saboda kanshi tabbas idan yai kwakkwaran motsi zai iya tarwatsewa


Mami kuwa sai jin dadi take,Tariq daya gama share kwallan idanun shi ya kama Taufiq zuwa side dinsu wanda yakeji inama mutuwa yayi ya huta da ganin wannan rana wai shi za'aima zabin mace,inalillahi wa'inna ilahirraji'un shine abinda yaketa karantowa.


```Tirkashi masoyan Taufiq kunji halin da gwanin naku ya shiga kudai kuyi hakuri komai lokacine,amman auren dole ga ɗa namiji akwai matsala```


*********Zaune nike gefen gado na haɗe kaina da guiwa,kaina ke mani ciwo dan kukan da nike kwasa ga zazzabi daya rufeni,ko abincin kwarai banci zullumi ya rufeni dana tuno da Ya Taufiq zai aure sai naji jikina ya kara rikicewa,hawaye keta zirarowa bisa kuncina.
A kidime na ɗago kaina saka makon taba sholder dina da akayi,Mama ce ke share mani hawayen idanuna.
Rungumeta nayi na saki marayan kuka.
Mama Ya Taufiq zaiyi aure yabarni.!"
Bubbuga bayana ta shigayi tana bani hakuri.

"Aminatu kidaina kuka,kinga bansan ki samu matsala da mahaifin ki,wannan Qaddarar kice dashi kanshi Hussein kuyi hakuri Allah yayi ba zaku kasance a kalkashin inuwa ɗayaba,ki cireshi aranki ya'ta."
Mama Allah inason Ya Taufiq dagaske nike bansan ya zanyi ba."

"Aminatu ki tashi daga nauyayyen baccin da kikeyi yaushe kika faɗa son Hussein?"
Mama bansani ba dan Allah kiba Baba hakuri yaje yace ma Abba yayi hakuri kada yarabamu wlh munasan juna!."


"Hakurin mi zan bashi,kinga Amina ki shiga hankalin ki wlh,kika bari mahaifin ki yaji wannan maganar kinsan sauran.!"
Mikewa tayi ta shige daki,tana faɗa.
Nidai kukana naci gaba dayi ina ganin Ya Taufiq yaci amanata,ya koya mani son shi gashi zaiyi aure yabarni.


Daren bikin ƙannen Baba sukazo gidanmu zasu tafi Kaduna biki,already Anty Murja ta tafi,kudi suka hada wanda zasu kaima Mum gudunmuwar su,basu jimaba sukaima Mama sallama sukatafi Kaduna,su Baba sai gobe zasuje daurin aure.


******Taufiq Pov"""""""""
Hassan ya Abba keson inyi da raina! Gaskia bazan iya bin wannan umurnin nashi ba,ina son Minal akan mi zai hadani da wannan yarinyar natsaneta.!"

"Hussein kayi hakuri dan Allah ka dauki Qaddarar ka mana kodan Mum ka tausaya mata,kaima Abba biyayya wlh kin bin umurninsa a wannan karan zai iya yimaka baki,karfa ka manta shidin mahaifin kane why not bazaki mashi biyayyaba duk irin kauna da gatan da yake nuna maka.!"

"Tariq kana son in auri yarinyar da banzan iya sauke mata hakkin aure ba,ko kasan sisin kwabo bansa a cikin wannan hidimar ba,taya zansan darajar ta bare har insota gobe ɗaurin aure ko kasan fuskar ta bazan shaida sosai ba,taya kake tunanin ni Taufiq zan iya son wannan yarinyar.!"
Ya ida maganar idanun sun sauya launi tsabar bacin rai.

"Look Hussein i undersatand but kaima mahaifin mu biyayya nasan bazakaso kaga Mum cikin haliba ka nuna baka cikin damuwa kaga Mami farin ciki take za'ai maka auren dole,dan Allah kanuna ka yarda ka kwantar da hankalin ka kodan bawa maraɗa kunya.!"
Mikewa yayi yana goya hannayen shi bisa bayan shi ya kalli Hassan yace.

"Naji Hassan kasa aranka komi ya biyo baya banda laifi zanma Abba biyayya in auri Khairat amman bata kalkashin ikon aurena tunda tilas akai mani.!"

"Hussein ina kataba ganin anyi haka mace nada igiyar aurenka akanta kace bata kalkashin ikonka.?"


Kwarai akaina za'afara tayi komai zatayi tasa aranta kamar bata da wani aure danni bazan iya sonta ba,wlh Tariq wannan shine babban kuskuren da Abba ya tafka na yimani auren dole duk shekaruna.!"

"Hmmm Taufiq kenan Allah ya kyauta nidai in zakaima Abba biyayya kodan Mum ai shikenan saidai kaji tsoron Allah!
Kaga bari inje wajen Anty Murjanatu takirani tun dazun saina dawo."

Jinjina kai yayi ya faɗa bathroom zuciyar shi na kuna.

Shirin biki akeyi babu kama hannun yaro,masu farin ciki nayi masu hassada nayi a wannan fannin zan iya cewa nima ina cikin masu jin haushi,na ɗaga hankalina fiye da kima abincin kwarai banci bacci barawo sai dagaske yake saceni,saina dauko waya zan kira Ya Taufiq sai in fasa,wani irin haushin shi nikeji musamman yanda ya shareni alamu sun nuna yanajin dadi zai auri wata bani ba,daman ance namiji zuma ne saida wuta,kukan zuci ya zamar mani ibada.

washe gari tunda sassafe Baba suka shirya suka tafi daurin auren Ya Taufiq,tunda natashi ba wani lakka jikina ko Fatash bata tani tunda bata kirani ba,hakan ya nunaman cewa kowa yanajin dadin auren da zaiyi zazzzabi mai zafi ya rufeni narasa dalilin dayasa nikejin kishin Ya Taufiq har haka,kwalla keta ziraro mani bisa kuncina.

Ahmad keta kwada mani kira ina gani naki dauka banji zan iya waya da kowa a halin da nike ciki.
rufe idanuna nayi kamar mai bacci tsabar ciwon kai daya matsa mani inajin shigowar Zainab akaina ta tsaya.

"Anty kizo inji Mama tana dakin ta."
Kamar badani take ba naki ko motsawa bare in bude idanuna da sukai mani nauyi kamar mai hawan jini.
A hankali na bude idanuna na sauko bisa gadon naje kiran Mama.

Kallo daya taimani ta kauda kai tareda daukar mataki a saman fuskar ta.
Dukawa nayi,gani Mama.
"Kije kiyi aikin gida tunda kin nade kafa ko asibitin yau bakije ba,kin azama kanki abin da Allah bai daura maki ba wlh Aminatu ki rufama kanki asiri muddin Baban ki ya fahimci halin da kike ciki wlh ki kuka da kanki,mutuniyar banza,shi Taufiq din ɗan autan mazane da bazaki cire shi a ranki ba,mahaifin shi yace bai son wata alaka tashiga tsakanin ku amman dayake taurin kaine dake saida kika fara soyayya da Husseini."
Mama dan Allah....

Yiman shiru idan da ina kareki a gaban mahaifin naki ince baki soyayya dashi yanzun fa?uwar me kikeyi,ke yanzun ko kunyar mahaifin ki bakiji yaji kina kuka dan kawai Taufiq zai aure Aminatu na kiyaye ki wlh,ki rufama kanki asiri tun wuri tunkan dare yai maki.!"

Kuka nike marar sauti kaina duk ya gama kullewa ni kaina ina mamakin kaina dana shiga wannan halin duk akan Ya Taufiq taya akai nai nisa cikin son shi,ashe haka rashin masoyi yake a cikin zuciya ashe haka masoya sukeji daman har nasan dadin so irin haka,inalillahi shine abinda nike maimaitawa araina.
Tashi kije kiyi aiki dan nacema Asibi kartayi komi ke zakiyi yanda kikayi dojing zuwa aiki,nan kuwa sai kinyi shi,kuma ranar monday kina zuwa aiki ko zaki mutu ki godewa da week end bakida duty Allah da saikin je baceman da gani mutuniyar musawa.!"
Tashi nayi sukuku na shige dakina ina kuka wanko fuskata nayi nahau aiki jiki amace.





_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E9&10



Yau asabar da misalin karfe biyu naji ance za'a daura auren Ya Taufiq su Baba sun isa Zaria tun wajen sha biyu na rana zama nayi bisa kujera idanuna rufe as usual,domin idan na budesu da iska ya kaɗasu inajin zafi sosai kamar tashshi aka watsa mani a cikin su,wayana ya hau ruri,a hankali nadan bude idanuna Dr Siddi ya baiyana a bisa screen sanin maganar aikice yasa na daga.
"Dr Amina kece on duty monday evening ko?"
Yes sir."

Akwai wani theater da za'ayi insha Allah yanzun patient din namu yana under medication kafin lokacin muga abinda

Please Login or Register in order to submit comment