Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nemeta insha Allah,itadai burinta ya cika tinda ta auri Major Hussein daman burin ta kenan.

A wajen Taufiq kuwa tunda ya shige side dinshi ko waje bai lekoba yana cikin side dinshi daga saman bene kuma duk wanda zai shigo ko fita yana kallo,sallah kawai ke sauko dashi daya dawo ya koma ciki,haka yaitayi harya manta da yanada wata mata a duniya.

Bayan kwana biyu sanye yake cikin wani sky blue din boyel ba kadan ya amshe shiba fitowa yayi yanasan zuwa gida ya gaida Mum dinshi,bakin mota ya tsaya da sauri Usama ya iso zai bude mashi ya tuka shi,ya dakatar dashi,bari inje bazan jima ba je kayi harkokin ka."
Thank you sir.

Bude kofar yayi zai shiga sai ga Antyn Khairat da yan mata guda biyu dan dai ɗaya ta girmi daya kowan nan su da troly janye kallo daya yai masu ya kauda kai suna isowa yan matan duk suka gaida shi,amsa yayi ya gaida Anty Lubna cikeda girmamawa,ita amsawa tayi,sannan tace.

Daman wadan da zasu kama mata aiki ne aka kawo mata."
Da kamar ba zaiyi magana sai kuma yace.
"Aikuwa munji dadi,sannun ku tana cikin side dinta."

Yana gama fadar haka ya shige mota,su kuma suka shiga cikin side din Khairat.
Suna isa falorn ba kowa sai karar tv dake aiki a hankali kofar bedroom dinta Anty Lubna tayi ta shaida mata zuwan su,sanye take cikin gown ta material coffee ba karamin kyau yai mata ba,kasancewar ta fara masha Allah.
Tare suka fito har falorn nan taga mai aikin ta Hassina sai cousin dinta Laurat,gaisawa sukayi ta gwada ma mai aikin dakinta da aikin da zatai mata sannan taba Laurat dakin ta yana facing na Khairat din,sosai sukai fira saidai bata nuna masu damuwar taba,har Anty tai mata sallama ta tafi gida.


""""""""
Yana isa gidan su parking yayi compound dan ba kowa direct side din Abban shi ya wuce ya iske shi yana kallan News fuska cikeda annuri ya amsa sallamar dan nashi ya zauna yana gaida shi,amsawa yayi.

Ya ya'ta ita kadai kabaro haba Hussein kaga akwai bakunta a tare da ita."
Sosa keya yayi yace.
"Aaa Antyn ta tazo tare na barsu kafin su tashi zan koma ai Abba."
Yawwa ko kaifa Allah yayi albarka."
Ameen

Dan jim kadan yayi sannan yai mashi sallama ya fito,har zai wuce side din Mami sai kuma ya shiga, as usual Wasila nanan tsuke fuska yayi,tana ganin Taufiq fuska sake ta tare shi.
Oyoyo ga ɗana sannu da zuwa Major Hussein Mukhtar."
Kirkiro murmushi yayi ya zauna kusa da ita.
"Mami barka da safiya."
Yawwa Son ya ya'ta fatan tana lafiya.
Alhmdullh."

Ina kwana Taufiq."
Lfy yace.
Sanyaye Wasila tabar falorn duk tasha jinin jikin ta.
Oyoyo Yaya mukaita zuwa bamu taddaka sai Anty kadai."
Oyoyo Auta tagaya mani ai kun kyauta ya aikin naki."
Lfy lau Yayana,ai zamuzo maku yini jibi saika zauna dan zamu sha fira sosai."

Serious.?"
Yes Yayana.
Okay shikenan Mami zan shiga ciki sai anjima.

Allah yai albarka yabada zaman lafiya da zuriya dayyi ba."

Bai amsata ba ya fita,side din Mum ya shiga tana zaune,Aisha na kwance bisa cinyar ta,Fatash ta sakko bisa bene zuwa falorn daga nesa tafara Yaya munyi fushi baka zama saidai kabar Anty ita kadai.

OMG complainers keda Zakiyya kun cika problem ta fada mani ai."
Sorry Yayana ai zamuzo insha Allah."
Okay Allah yasa.

Mum zanje aiki saina dawo auta mi zan siyo maki.?"
Choculate nikeso.
Alright.
Bye
Allah ya tsare hanya sukace baki dayan su.
Haka Fatima ta tafi aikinta

Mum ina kwana."
Lafiya lau Hussein ya ya'ta take.?"
Lafiya lau
Aisha jeki ciki zan magana da yayanki."
Toh Mum.

Hussein inasan ka saurari abinda zan gaya maka,a matsayina na mahaifiyar ka,inasan in gaya maka gaskia,duk da bansan abinda ke wanzuwa tsakanin ka da matar kaba,nasan ba lallai kana bi ta Khairat ba,kaji tsoron Allah shine abinda zan gaya maka."
Mum ba haka bane ina bata kul......
"Ya isa Hussein nafi kowa sanin abinda zaka iya da abinda bazakayi ba,da ace Hassan ne banda fargaba dashi nasan ya fika saukin hali da hakuri,kaji abinda nace maka."
Insha Allah Mum,zan kiyaye.
Haka nikeso Allah yai albarka.
Ameen

Sunjima suna fira kafin tasa shi,ya tafi gida yana dawowa side din shi ya wuce abin shi.


*********ina zaune a office nafara waya da Ahmad wanda yanzun shi kadai nike waya dashi duk da ba wata soyayya na bari ta sake shiga tsakanin muba,amman mun shaku kuma yana cire mani kewa,muna gama waya na jinjina kaina jikin kujera na maida idona na rufe.

Bayan sati ɗaya

Ba abinda ya sauya a tsakanin Taufiq da matar shi har tafara gajen hakuri da abinda yake mata.

Tashi tayi ta fito compound din gidan ta zauna ranta a hade tajima tanasan taga shigowar mijin nata amman shiru har tagaji.
Laurat idan kinga Major ya dawo ki sanar mani.
Toh Anty."

Sai bayan la'asar sakaliya sannan ya shigo tareda Tariq sai littile Major,yanzun ya fara girma side dinshi suka nufa.

"Hussein mu biya ingaida madam ko.?"
Badan yaso ba suka shiga cikin falon daidai tana sakkowa zata nufi side dinshi cak tsaya tana kallan su kamar wasu baki.

The first time daya shigo side dinta tun ranar da aka kawo ta.
Sannun ku da zuwa oyoyo son."

Zaunawa sukayi fuska dauke da murmushi Tariq yace.
Mrs Taufiq barka da yamma."
Yauwa ya Anty Aisha.
Lafiya lau tace a gaidaki.
Major taho mu gaisa,ina Aira.?"
Zuwa yayi wajen ta suka gaisa,tana wajen Amma."

Laurat ta kawo masu drinks,wajen yai shiru,Tariq kejansu da fira,tana maida mashi jefi jefi banda latsa waya ba abinda Taufiq keyi,shiko Tariq kamar ya nutse dan kunya ganin ba wata alaka ko jituwa da zata nuna sudin ma'aurata ne kuma yasan bawai dan ɗan uwan nashi bai waye ba sanin shidin kaifi dayane tunda yace bai sonta ba canji.

Duk jiyayi zaman ya gimshe shi mikewa yayi yace.
"Mrs Hussein zan koma,sai Antyn taki tazo maki wuni."
Aikam danaji dadi ina gaidata sosai.

Zataji,sai lokacin gogan naku ya mike ko kallanta baiba yayi gaba abin shi,side din shi suka nufa kamar jira Tariq ya rufe shi da faɗa

"This is stupidity akanmi zakana ganama yarinyar mutane azaba irin wannan,kasan halin da mace ke shiga idan mijin ta ya kaurace mata kanaso aima Fatima ko Aisha ko Zakiyya haka.!?"

No ammn idan suka nace sai sun auri wanda bai son su wlh ko abinda yafi haka akai masu damuwar su,ai daman ance son maso wani koshin wahala."

Tir da wannan ra'ayin naka Hussein kabani kunya koda ita kesan ka amman tanada hakki kanka karda kamanta."

"Hassan ya isa haka,i think nike zaune da ita mafi girman muni shine inga Khairat a gidan nan matsayin matata wlh na tsaneta.!"
Lallai Hussein ashe daman baka da tausayi ban saniba.?"

Ni tausayin nawa akaji da aka aura mani wadda banso anya Hassan kasan yanda auren dole yake?ga mace ma bare ni namiji taya zan iya neman wani abu gareta never.!"
"Ai daman nasan bazaka nemaba domin yanayin ka kadai ya nuna ba wata alaka dake tsakanin ku da ita.!"

Yes offcourse domin kuwa kusantarta shi zaisa inkara tsanar ta,tsana mafi muni wanda ban taba yima wani ɗan adam itaba a duniya Tariq na tsani Khairat a cikin zuciya ta.!"
Yayi kaje kayi abinda kai niya ai hakkin ta kake dauka kuma kasan girman hakki aikin banza aikin wofi ga sani ga 6anna mtsw.!"

Jan hannun MM yayi suka fice a fusace,ko ajikin shi ya fada bedroom yana jan dogon tsoki ranshi a bace.


*Atakaice rayuwar gidan Taufiq ba dadi ko magana bai bari tana hada shi da Khairat batada mararraba da namiji a gare shi dan bata birgeshi baima tsaya yaga kwalliyar taba bare taja attension dinshi!*


_Allah katsare mu da auren hadi ameen kabarmu da masu son mu👏🏻_


Duk abinda ke faruwa Laurat ke kai rahoto gidan su Khairat,itakam bata gayama kowa fargabar ta daya ace za'a rabata da Taufiq wanda shidin burintane a rayuwa.

Shiko bai fasaba hidimar shi kawai yake son ranshi haryafi kwanciyar hankali akan gidan su,dan nan din kullin tsit ba mai takura mashi,abinci ma da yayi order Usama zai shigo ya kawo mashi wannan kenan.

Kwanaki sunja Khairat ta samu wata biyu gidan Taufiq amman daidai da yatsan hannun ta bai taba rikewa ba bare tasa ran wani abu zai shiga tsakanin su,yau dai hakurin ta ya kare direct sashen shi taje akai sa'a abude main entrance din take ciki ta wuce,tana shiga ta iske shi da waya a kunnen shi sai dariya yake mai sauti mutuwar tsaye tayi domin murmushin Taufiq bata taba ganiba bare dariya tana mamakin wayake ma dariya irin wannan a fadin duniya idan akwaita kuwa ya kamata ace itace tafi cancan ta da ita.

Niko ina kwance naga Ya Taufiq yanata kirana har rejecting saida nayi karshe ya turomani sako na begging dan Allah in daga pls.

sake kiran nawa yake sai ana ukku na daga tsoro na daya kada inkara komawa ruwa tunda nasamu kaina, kuma bansan inyi waya dashi kodan matar shi nasan ba dadi kuma ance ciwon ya' mace na mace ne,bazan so ai mani haka ba.
Muna cikin waya yace.
"Queen of heart inasan ganin ki i really miss u Minal pls.!"

Aaa Ya Taufiq dan Allah kadaina yaudarar kanka dan ba ganina zakaiba kasa aranka Qaddara ta sake nisan tamu pls leave me alone.!"

Never Minal Qaddara bazata rabamu ba koda ta rabamun itace zata sake hadamu pls help na rokeki.!"

Nidai sai anjima bazaka samu wannan alfarma ba,ina aikima a halin yanzun?"

Hmmm Minal baki sona ko.?"
Eh mana kamanta kenan.!"
Naji ba komai nidai ina sonki.!"

Kara naji ta mace tana
Yanzun ni zaka yaudara Taufiq daman warewar da kakeyi soyayya kake da wata ina cikin gidan nan hakkina ma baka bani ba shine zaka wulakantani.!"

Jikina na bari nafara karanto inalillahi wa'inna ilahirraji'un,karki kashe Princes.
Da sauri na kashe ina rabka uban salati wannan dalilin yasa ban yarda in waya da Ya Taufiq tunda yai aure gudun halin da matar shi zata shiga.
Ke kinada hankali kuwa?kinsan mi kike zaki mani ihu bisa kai.?"

Cewa tayi......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_





Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E15&16



"Duk abinda zakace naji,I deserved it,tunda ba sona kake ba ka tsaneni saidai ka sani igiyar auren dake tsakanin mu ta tunkude tsanar ka agareni Taufiq,inada hakki akanka matsayina na matar ka,akan mi zaka dinga waya da yar iska cikin gidana w.....

"shut up zan bata maki rai! kinsan wacece ita.?"
A fusace yai maganar

''ta wuce abinda na danganta, ta da shi tana bibiyar mijina, kuma koda nan din yake part dinka inada iko da komai naka tunda ni matar kace itafa.?"

Enough u re very stupid!dalilin dayasa kika aureni shi zaisa kije kicema mahaifin ki da mahaifina kin fasa zama dani shine masalaha agareki in bahaka nan ba sai kinyi danasanin zama a matsayin matata.!"

Bazan jeba, zama dakai daram kuma dole ka sauke mani hakkina dake kanka.!"
"Get out of my apartment.!"

Fashewa tayi da kuka kamar karamar yarinya wlh bazan fita ba saidai ka kasheni.!"
Mtsw fool.
Yai cikin bedroom din shi yanasa lock.

Zubewa tayi bisa kujera tana rera kuka mai taba zuciya.
saida ta gaji dan kanta sannan taja kafarta tayi side dinta ranta a dagule.



********Ni kam danasani iya danasani nayi dana dauki wayar Ya Taufiq nasan matar shi tana cikin yanayi,tambayoyi nikema kaina banda amsar su,mizai sa inyi waya da mijin wata? Koda yake dan uwana ai da alaqa atsakanina dashi,ina ilimina ya tafi da nayi wannan aika aikar gaskia anan fagen sam ban aiki da ilimina ba,ranar ganina kawai ake amman ina cikeda tausayin Kharait araina.

Bayan kwana biyu ba laifi na saki jikina saidai ban kuma gigin daga kiran shiba duk da shima ya ɗaga kafa amman text ba abinda ya fasa,indai na soyayya ne ban replay saidai in normal gaisuwa ce shima cikin biyar baifi na maida mashi guda ba,kasancewar yau lahadi banda wani aiki sainaji zaman ba dadi,tambayar Mama nayi mukaje gidan kakar mu (Dada) acan na wuni sainaji na sake duk damuwana ta tafi najini wasai alhmudllh.
Sai gab da Baba zai dawo na rigashi dawowa nasan ba zai mani fada ba amman yanzun bansan in sa6a mashi fatana ma ya yafe mani ya daina fushi dani bazanso inkara wani laifin ba.


Da kaina na kira Ahmad jin shirun yaimani yawa fira mukai mai dadi da tsafta,labaran ban dariya yake bani,munjima muna fira sannan mukai sallama sakamakon isha'i da ake kira.


Kaduna"""""

Watanni sunja na auren Taufiq akalla cikin basu jimaba wata na biyar amman ba wani sauyi saida,Laurat tayi bin diddiƙi ta gano ba wani abinda ya taba shiga tsakanin Taufiq da Khairat shima din labe tayi taji tana waya da kawarta tana kuka take fada mata damuwar ta,recording tasa a wayar ta duk abinda Khairat ke fadawa kawar tata,da alama hakuri kawai take bata har suka gama wayar tasu.

Da yamma Laurat ta iske Antyn tata tambayar ta tayi zuwa gida,gaido Mamar ta,bata hanata ba tabata kudin mota ta tafi.

Daman ba taya zama bane kadai ya kawo Khairat dinba harda zama yar C.I.D a gidan Anty Lubna tabata wannan kwangilar saboda bata yarda da Khairat ba sam,ko antabayeta cewa take bata cikin matsala lafiya lau.


Tana isa gidan su Khairat,ta iske su (Umma) mahaifiyar Khairat suna gaisawa ba wani bata lokaci taba su recording data nada,haka suka gama sauraro banda kuka ba abinda Khairat keyi.

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un ohni Salamatu,shiyasa nifa auren nan bai kwanta mani ba,idan ana takamar ai Khairatu nasan Taufiq shifa?daman taya za'aima ɗa namiji auren tilas azauna qalau macen ma ya takaya.!?"

Ta'ajjabi lallai kam akwai sake ba yanda za'ayi in aurar da ya'ta ta zama bora a wajen miji.!"
Mamaki sosai sukayi tura recording din tayi ta wayar ta ta ajema mahaifin Khairat din dan yaji shaida da kunnen shi.

Haka Anty Lubna ta sallami Laurat ta tafi suko mamaki ya gama cika masu zuciya.


Shiko Taufiq Company ya tafi kada ku manta shi Arcthector ne yana zuwa yaci gaba da hidimar shi musamman yan kwangila zanin ka gidaje iri iri singles harda zanen Estate ba abinda Companyn shi basuyi.


Ranar can ya wuni ya samu alkhairi kwarai yana zama office friday saturday & sunday, sau ukku a sati,agajiye ya dawo yana shiga part dinshi,a falon daga shi sai bedroom ya iske Khairat kwance cikin riga da sicket sun mata kyau ainun kallo daya yai mata yai cikin bedroom din shi da sauri tasha gaban shi.

Mi kake nufi dani wai.?"
tayi mashi tambayar cikin bacin rai.
Sake kallan ta yayi ya kauda kai yace.
Kije kice kin tsaneni bazaki iya zaman aure daniba kinga in kikai haka kin zama adala mai kwatanta gaskia kuma cikin sauki munrabu ba tareda kinsa mahaifina ya zargeni ba.!"

Kuka takeyi,karkatata yayi ya shige dakin shi.
bin bayan shi tayi da kallan takaici tana gani yarufo kofar bedroom dinshi kamar baisan tana wajen ba.

Haka taja kafa ta koma side dinta tana kuka.
tana shiga ciki cak ta tsaya ga kwalla na kwaranya a fuskarta, Anty Lubna ke aika mata wani matsiyacin kallo,ranta kuwa duk ya baci.
Da sauri Khairat ta goge fuskarta,ta isa wajen su gaidasu tayi wani irin kallo ta watsa mata ba tareda ta amsaba tace.


"Yanzun Khairat kinma kanki adalci ki zauna a inuwar da ba'ason ki ba'a muradin ki,yanzun kin zama kamar marar yanci keda miji ba abinda ke shiga tsakanin ku abincin ki baici dakin sa baki shiga komai nashi bakida iko dashi,amman dayake ke shashasha ce kikai zaune sai kace ubanki.!"

A razane Khairat ke kallan Antyn tata tace.
Haba Anty ina kikaji wannan maganar, nifa banda wata matsala da mijina ki yarda dani.!"

Yanzun ubanki na gani nace ubanki ne,duk kukan da kikeyi namenene kingane mani yar banzar yarinya watanki biyar ana shidda har yanzun baki san abinda aure ya kunsa ba,kedai kin rako mata duniya toh mu bazamu lamin taba kinada gata idan auren zaiyiyu to in bazai iyaba kwara kowa yakama gaban shi."

Anty nifa inasan mijina kuma komai ai lokacine kinga auren hadine yakamata kuyi mashi uzuri."

Uwaki nace auren haɗi?ashema auren haɗi! koke baiwa ce ai yaka mata ace zuwa yanzun ya 'yantaki,ki zama cikakkar mace toh kiji da kunnuwan ki wlh sai mun dauki mataki.!
Kuma da kike karyatawa ai ga shaida nan kinsa kawomaki Laurat da mukayi zaman cin shinkafa tazo,ai dan musan halin da kike ciki,tunda munsan wa kika aura ba sonki yake ba.!"

Anty nifa ba wani abu bane kawai dai....
Yiman shiru kuma nan zanbar Laurat din kallan banza kikai mata nidake ne.!"

Tafiyar ta tayi tabar Khairat jugum kamar marar lakka a jikin ta,banda kallan banza ba abinda takema Laurat,sadda kanta tayi ƙasa sumisumi tayi dakinta.


********Bayan sati daya mahaifin Khairat ne wajen mahaifin Taufiq a sashen shi gaisawa sukayi cikin mutunci irin na abokai kuma aminai yace.

Alhaji kaji abinda ke tafe dani,shine nace bari in shaida maka,duk da nima mai dakile abun ne amman yanada kyau muji ta bakin Hussein din.?"

Cikeda mamaki Abba ke juya zancen aranshi ya kalli aminin nashi yace.
"Ikon Allah shi Hussein din yakema Khairatun haka?wata shidda amman ba wani mu'ammula a tsakanin su bai kyauta ba,kuma zanyi maganin shi.!,,

Aaa Alhaji Mukhtar ba nufina kenan ba kakira shi ka zauna dashi kaji dalilin shi, kada a yanke hukunci cikin fushi."
Shikenan Alhaji Mas'ud kayi hakuri komai kenan zakajini insha Allah."

Toh nagode sosai Alhaji sai anjima.
Rakiya yai mashi yana jin abin har cikin kokon ranshi.

Washe gari da safe Abba yakira Taufiq yace yana son ganin shi.
Koda yafito gida zaije Company wucewa yayi wajen mahaifin nashi,iske shi yayi da Mami sai mahaifiyar shi gaidasu yayi suka amsa a mutunce

"Hussein nasan zakayi mamakin jin kirana ko? to ba'abin mamaki bane,daman magana ce akan zaman auratayyar ka da matar ka,labari ya sameni tunda ka auri yarinyar nan baka taba sauke hakkinta agareka ba, na auren ku miyasa hakan ke faruwa.?"

Shiru yayi baisan ta ina zai fara yi mashi bayani ba shidai abinda yasani baison Khairat kuma baiji komi zai hada shi da ita.

Sosa keya yayo yace.
"Abba kayi hakuri inajin nauyin yanda zan fara yi maka wannan bayanin ne shiyasa.!"

Aaa kayi bayani Hussein kada kaboye mani komai maganar aure ake kuma ba wasa a cikin wannan lamarin."
Sake sosa kanshi yayi a kunyace yace.

"Abba a gaskia banda lafiya shiyasa na gaza sauke mata hakkin ta.!"
Salati suka dauka kowa na mamaki, musamman mahaifiyar shi tafi kowa mamakin maganar dan nata.

A kidime Abba yace.
"Yanzun Hussein baka lafiya ina mahaifin ka baka sanar maniba In sama maka magani ba har saida kayi aure sannan gaskia baka kyauta mani ba."
Abba kayi hakuri inajin nauyin maganar ne.!"

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un,koda naji nasan bazaka taba yin hakaba dan ka wulakanta ni dole kana da naka dalilin Hussein,yau ba sai gobe ba zan kirawo babban Doctor wanda ya kware a wannan fannin ya duba mani kai,zan kashe ko nawane dan samun lafiyar ka Hussein koda zanfi kowa talauci a duniyar nan insha Allahu zan nema maka lafiya.
sannan daga yau kada ka sake cutar da kanka mu iyayen kane ba amfanin kai mana boye boye.!"

Insha Allah Abba nagode Allah yakara girma."
Ameen saidai kasani a matsayina na uba agareka wannan hakkina ne, koda na aurar dakai akwai abinda yake hakkina ne inmaka musamman lafiyar ka, barima in kira Doctor Asim yanzun nan."

Shidai Taufiq yasan karya yake, yayi hakan ne dan auren shi da Khairat ya rabu har abada,jin maganar mahaifin nashi yasa shi kallan shi.

"Doctor dan Allah ina bukatar taimakon ka,ɗana ne baida lafiya."
Okay yaushe zaka dawo kasar ko muzo nan mu iskeka.?"
Okay yau Allah yadawo dakai lafiya."
Thank you Doctor saina jika."

Kallan su yayi yace,yau Doctor zai dawo kasar yaje Egypt ne,gobe zaizo ya sameni komai kenan ka shirya wajen karfe goma har gidan ka zanzo nida Doctor din kanajina.?"

Eh Abba nagode sai kunzo."
Tashi kaje ka kwantarwa matar ka da hankali kaji Allah yai maka albarka."
Ameen ya Abba.

Allah ya kyauta gaba yabaka lafiya."
Cewar Mum.
Ameen suka amsa,da haka ya fita saidai zuciyar shi, cike take da tausayin mahaifin nashi,saidai a wajen shi hakan shine mafita.


******Washe gari kamar yanda Abba yai alqawali haka yaje da Doctor Asim gidan Taufiq ba karamin tashi hankalin mahaifin shi yayi ba,suna zuwa sashen shi suka iske shi zaune falo yana kallo wani irin tausayin ɗan nashi ne yakama Abba gaisawa sukayi da Doctor din sannan ya gaida mahaifin nashi.

Aikin shi Doctor yafara ta hanyar tambayar shi sign da yakeji,duk ya bashi amsa.

Alhaji inasan mu kebe akwai test din da zan mashi,kaga baida feelings akwai matsala."

Duk abinda ya dace Doctor kayi ko nawane zan baka fatana ɗana ya wayar ke."
Insha Allah."
cikin bedroom dinshi suka shiga ya maido kofa ya rufe.

Major inasan kabani hadin kai zan maka wannan test din dan insan maganin da zan daura ka akai.!"

Murmushi yayi yana juya baya tare da goya hannayen shi yace.
"Doctor nawa Abba zai baka kai mashi wannan aikin.?"

1.5 million ne zai bani kamar yanda aikin yake miyasa ka tambaya Taufiq.?"
Uhmm Doctor Asim kenan.......





_Yar Mutan Kankia ce❣️_





Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E17&18



"Zan linka maka abinda mahaifina zai baka amman idan zakayi abinda zan umurceka."

Ranka shidade minene wannan abun.?"
"Inasan kaba mahaifina saka makon karya kace banda lafiya bazan iya sauke hakkin matata ba,kuma aikin da za'ai mani akalla zan kai nan da one year kafin aci nasarar aikin sannan ka shaida mashi zaka iya aikin kada yakaini kasar waje,zaka daurani bisa Suppliment muddin kaiman haka zan maka double din abinda Abba zai baka, saidai sirrine karka kuskura wani yaji wannan sirrin koda kuwa mahaifiya tace.!"

Zaro idanu yayi jin kudin da zai bashi banda wanda Abba zai bashi.

Amman Major miyasa bazaka bari ai checking matsalar ba kodan jin dadin rayuwar ka."

Wani irin murmushi Taufiq yayi mai ma'anoni yace.
Kana nufin baka gane yare naba,ni da kake gani nafi kowa shi'awa kuma nidin nan cikakken namiji ne kamar kowa inada feelings kamar kowa saidai wadda aka aura mani itace ba desire dina ba,wannan dalilin yasa nike kaurace mata kuma zanbi kowace hanya ganin narabu da ita,amman saika taimaka mani kayi duk abinda zan saka.!"

Jinjina kai yayi alamun gamsuwa.
Nagane Major insha Allah angama kamar yanda ka bukata kuma ba wanda zaiji."

Good ka kyauta kuwa anjima kai mani text din details dinka zakaji alert."
Thank you Major Hussein."

Jinjina kai kawai yayi Doctor yagara fita bada jimawa ba Taufiq ya fito yana ɗan yamutsa fuska,da sauri Alhaji Mukhtar ya tari ɗan nashi yana rungomo shi jikin shi.
"Sannu son zauna,Doctor ya ake ciki."

Toh Alhaji yanzun zanje da sample din dana dauka zanyi test sosai akai zuwa gobe ko jibi insha Allah zaka jini."
Zan wuce inada aiki a hospital."
Nagode maka Doctor sai najika."

Sannu Hussein Allah ya baka lafiya jinike wani iri duk hankalina yatashi."
Sorry Abba komai zai zama normal insha Allah kadaina damuwa pls."

Allah yasa wai ina Khairat din yaka mata ace tana nan kodan baka kulawa."
Uhmm hakane kilan tanada uziri shiyasa."
Aaa kirata tazo nan inasan ganin ta,,

Shiru yayi dan yasan baida numbar ta,yi yayi kamar ya kirata yace number bata zuwa,kiran Usama yayi.

''Kaje side dinta kace tazo zasu gaisa da Abba,,
Shiru kowa yayi da kalar tunanin shi a kasan zuciyar shi.

Bada jimawa ba tazo part din ta gaida sirikin nata cikeda girmamawa.

Wani irin tausayin ta yake ji aranshi yace.
Yata ki kara hakuri kinji insha Allah mijinki zai warke Allah yai maki albarka."
Kasa amsawa tayi dan taji nauyin maganar musamman data gane manufar shi saidai bata tunanin abinda Taufiq yake ikirari gaskia ne
Bai jima sosai ba yakara yi masu huduba sannan ya tafi gida.


Haka rayuwa ta kasance Sarki Mukhtar baida wani kwanciyar hankali tunda yaji damuwar ɗan nashi, dan yasan ba karamin lalura bane ke damun Taufiq,waya ya dauka kira ɗaya yaima Mum ta daga hankalin ta a tashe ganin 11pm.

Alhaji Allah yasa lafiya.?"
Eh amman ba lau ba,kisame ni side dina yanzun nan.
Mikewa tayi daga baccin da takeyi cikin kayan bacci masu kauri ta yafa gyale zuwa side din mijin nata direct bedroom dinshi ta nufa shiko sai zagaye yake kamar jira ya tarota.

Maryam daman kinsan da wannan lalurar ta ɗana tun yaushe yake dauke da ita baki sanar mani ba.!?"

Sauke nauyayyar ajiyar zuciya tayi dan batai zatan wannan maganar bace,ita sai takega kamar shirin Taufiq ne,dan ta tabbata da ace baida lafiya da gasken gaske tabbas Tariq zai sani,cikin siffar kwantarwa mijinta da hankali tace.


"Abban Taufiq ka kwantar da hankalin ka insha Allah ba wata damuwa bace mai yawa ba,kuma sai musa aimana rokon Allah insha Allah kafin nan da wata zai warke."
Really? Yes mijina dan Allah kabar damuwar kanka."

"Hmmm Maryam kenan kamar yanda ake cewa ciwon 'ya mace sai mace hakama ciwon da' namiji sai namiji nifa inaga India kawai zan kaishi kinga Doctor Asim daga Egypt yake shiyasa na yarda da kwarewar shi.

Aaa lalurar batakai nan ba Alhaji kabari kaga nan da wata ukku inba sauyi sai ka kaishi dan uwan shi da matar shi sai suyi jinyar

Please Login or Register in order to submit comment