Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bawani sukuni wajen Asma'u sai tarin damuwa da zullumi.

Kowa na fadin abinda ya sani rabi da kwata duk rumour ne wai ina gantali wa'iyazubillah.

Rayuwa na tafiya abubuwa da dama sunfaru ciki kuwa harda janye neman aure da gidan su Lukman sukayi jin ance na gudu natafi gantali,ciwon zuciya ne kawai bai kama Baba,ba tsantsagoran damuwa da ɗumin jama'ar gari ga rashina yana damun shi.


*After Some Months*

Na warke daga ciwon dana tsinci kaina ina zauna a falor nida Salima Ya Abdulmutallib ya siya mani waya mai tsadar gaske da Sim,saboda sunada kudi na gasken gaske a Gadon Ƙaya suke zaune.

Allah yasa na rike number Husna nasa da number Baba,Mama saita Ya Taufiq suka ɗai ke gareni sai numbar yan gidan mu a halin yanzun su Salima da Ya Abdulmutallib su biyu iyayen su suka haifa a duniya maganar gata kuwa ba'acewa komai.

Mahaifin su Alhaji Abdullatib yakirani a falorn shi,cikeda girmamawa na gaida shi.
"Ya'ta ya karfin jikinki."
Alhmdullh naji sauki Daddy."
Maida kallon shi yayi kaina yace.
"Yakamata ace zuwa yanzun kigaya mana su waye iyayen ki dan ya dace ki koma gida."

Hakanan naji gabana ya faɗi na dake.
"nace insha Allah,ni a Caranci nike nan nagaya mashi details ɗina in berief.

"Shikenan kikara hutawa zuwa nan da wani lokaci inda bakida nisa da gida idan nadawo China sai inkaiki da kaina nida Umman ku."

Allah ya maidoka lafiya Daddy."
"Ameen ya'ta daman kiran kenan jeki Allah yai maki albarka."
Ameen."

Na koma ɗaki duk tunani yashaman kai ya zanyi da case din Baba duk da anjima nasan zai hakuri saidai inajin tsoron lamarin.

Dubara ta fado mani arai inkira Husna ingaya mata inda nike a halin yanzun sai inje gidan ta,dan insamu mafita kafin Daddy ya maidani gidan mu.

Da yamma ranar wata alhamis nakira wayar Husna bugu daya ta daga kamar maijira tace.

"Allah yasa kiran nan alkhairi ne kullin cikin jiran tsammani nike,assalamu alaikum."
Kuka kawai ya kufce mani,sautin kukana kawai taji tace.
"Minal kina ina dan Allah kigaya mani inzo gareki kada kitafi kibarni Aminatu dan Allah."

Kuka sosai nike amman bakaina nike tausaiba illah Husna irin kaunar da take mani na 6ata tsawon watanni amman kullin tana jiran tsammanin kira ace anganni a sanina da Husna bata daga bakuwar number amman asanadi na,tana dauka kai tsaye.

"Kiyi magana inji muryar ki kawata."
"Ina cikin Kano Asma'u dan Allah kada kigayama kowa sai mun samu mafita gobe zanzo gidanki muyi magana."

"To toh Aminatu inajiranki dan Allah kizo ina kewar ki."
Dan karfin hali harda bani adress din gidan ta kilan tana zatan na manta gidan nata

Washe gari kuwa naje lokacin Abdallah yana kasuwa tsayawa fadar murnar datayi cin lokacine.

"Aminatu miyasa kikabar gida kin ɗagamana hankali kuma tunda kinzo Kano sai ki sauka gidana har Baba ya huce sai Abdallah ya maidamu."

"Hmmm Husna kenan kin mata Baba ko?nai niyar inje gidan Anty Zainab sai wannan Qaddarar ta hauni.....

Nan nagaya mata komai da dalilin zuwana,naci gaba dacewa.
"bansan kowa yasan inanan kibari sai Abban su Ya Mutallib yadawo zai maidani gida sai susani kinga anyi suprise dinsu."

"Shikenan yanzun su Kabir da Ya Abdallah zasu dawo."
Wane Kabir din.?"

"Kabir dai kinsan ya dawo Kano shike kulama Abdallah shagon shi na cikin unguwar nan,kullin muna tare."
Jinjina kai nayi nace dole kisama mana wani wajen da zamu haɗu dan bansan Kabir ya ganni zai gaya a gida."
Kabir (kaninta)

"Shikenan da haka mukayi sallama natafi cikin farin ciki yau naga Asma'u saina samu sassauci araina kashi hamsin cikin dari.

Bayan wani lokaci saura kwana ukku Abba ya dawo yana dawowa zai maidani gida,nacema Ummi zanje kanti siyen Credit tace saina dawo zamewa nayi nakira Husna tana ɗagawa tace.
"Kawata muhaɗu Hotel nayi mana bucking ɗaki yini ɗaya zamuyi,kinga sai muyi maganar mu cikin sirri batareda kowa yasani ba."
"toh shinkenan nace mata.
Bayan ta turo mani sunan hotel din.

Kama hanya nayi natafi room number din na duba nai knocking saidai tsit ba alamun magana sake kwankwasawa nayi nanma tsit,turowa nayi azatona tana toilet kukan Haidar ya karaɗe ɗakin,magana nafara inacewa.
"Asma'u wai kina ina kinbar mani yaro yana kuka?"
Namma tsit ba alamun taina duba toilet wayam a rude nafara neman ta jinayi nayi karo da kafar mutum gefen gado jikin bango,kwalalo idanu nayi ganin Husna kwance cikin jini face face ga wuka kafe a cikin ta.

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un!
Shine na furta da karfin bala'i na zube gabanta na kama wajen kaifin wuƙar tsabar firgita da razana harna yanke wajen zare wukar a cikin ta,buɗe idonta tayi kadan sai ta rufe bakinta na furta J bata kara magana ba.

Ihu na saki na kifa kaina bisa cikin Husna ina kuka

"Ki tashi Husna kada kiman haka ban shirya rabuwa dake ba dan Allah karki barni Habibti."
Kuka nike wanda bantaba yin makamancin shi naji ance.
"U are under arrest."
naji bisa kaina.
Dagowa nayi da idanuna masu kama da rushi na kalli yan sanda agefe daya kuma Dr JJ ne yai holding hannayen shi yana smile,daga lokacin duk wata magana ta tsaya cak a cikin bakina.

Kuka nike saidai bana kamanin da akayi bane, Aaa na rabuwa da Asma'u masoyiyata wadda banda kamar ta.

Inaji inagani aka saman unkwa akatafi dani Bomfai tareda wukar a cikin tissue.

Haka aka tafi da gawar Husna akaita gwaje gwaje sannan aka nemi number Abdallah aka kaita gida.
Cikin kankanin lokaci kowa yaji har gida.
Waya aka bani nasaka number Baba bazan iya magana ba ɗan sanda yagaya mashi ina gun a police ya gaya mashi wajen da nike.
Baijira cewar shi ya tsinke kiran.

Bashi number Ya Mutallib nayi suma aka gaya masu, akidime suka iso sai kuka Salima takeyi duk wanda kagani suna cikin tashin hankali.

Washe gari kamar garinmu aka juye cikin Kano kowa yana al'ajabi idan akace ni nakashe Husna da hannuna.
Saidai wasu na karyatawa wasu kuma sun yarda.

Saidai Baban Husna da Mamarta sun karyata hakan take saidai iyayena basu da bakin magana dan Mama saida ta suma jin irin tuhumar da ake mani.

Anyima Husna jana'iza zuwa gidanta na gaskia angama komai.
Saidai kwalla sune abokaina kullin suna zirara a bisa kuncina nagaza furta uffan saidai zuciya na cike da kewar Husna ga matsiyaciyar kaunarta dal a raina bansan haka nikeson Husna ba saida na rasata inalillahi wa'inna ilahirraji'un.

Addu'a kuwa ita nikema kawata a zuciya ta samun rahama danni ban fatan agane wanda ya kasheta na daukarma raina karbar laifin ko ankasheni nima inbi Husna inhuta da kuncin rayuwa nidai bansan wani abu ba waijin dadi a duniya taba,Qaddarata sai dai Allah.

Washe gari aka kaini Kotu High Court aka fara shari'a da yan sanda suka kai case din.

Lauyen Gwamnati ke kare Husna ni kuma Ya Mutallib suka daukar mani lauya,aka hau shari'a a statement din cewa kai.
*Ƙawa ta kashe kawarta dan tana son ta mallaki dukiyar ta shine takaita hotel ta kasheta*

Nidai ina ganin ikon lillahi.
Aka fara sharia JJ ke cew shi shaidane duk abinda yafaru ya fadi da zuwa hotel da mukayi,saidai inda yai karya dayace yana ganina na sokawa Husna wuka shine yaje yakira masu hotel da yan sanda.
saidai narasa taya JJ yasan nida Asma'u zamuyi haɗaka Hotel?taya yasan ina cikin garin Kano! Bayan kowa yasan nidin na mutu tinda annemi ba wani labarina.

Tambayar da nikema kaina kenan ataikaice dai haka yagama bada shidar shi.
aka tambaye ni minene shaidata na aminta da zargin da akemani ɗaga kaina nayi sai kuma naji nace.
"Na amince nice na aikata wannan laifin na kashe aminiyata da hannuna."

Inalillahi aka dauka baki daya musamman wa'anda suka san wacece Husna a wajena.

Baban su ya mike yace karyani ke bazan taba kashe Asma'u ba.
Alqali ya daka mashi tsawa yace tunda harni mai laifi na amince magana ta kare.

"Aminatu kin amince wanene shaidan ki.?"

"Allah shine shaidana kuma na amince da duk wata hujja akaina."
"Miyasa kikai saurin amince tunda wuri.?"

"Saboda Qaddarata ce kuma Haka Allah Yaso sannan bansan inba shari'a wahala."

Nan Alqali ya yanke mani hukuncin ɗaurin rai da rai akani gidan yarin Ƙurmawa za'akaini da hanging ɗina za'ayi saboda banba shari'a wahalaba akai mani sassauci,ana gama fadar hukunci aka kamani za'akaini gidan yarin da Alqali yace akaini.

Take Mama ta sume akahau kuka takan kowa banba domin naso ai hanging dina amman koba komai zan samu sauki akan in rayu a cikin Jama'a ba Asma'u ana mani kallan nina kasheta

Za'afita dani Dr JJ yaimani murmushi itama Anty Hafsat bata cikin wata damuwa saidai abinda ban fada makuba su Mum duk sunzo harda Abba su Ya Tariq su Fatash sunsha kuka amman Anty Hafsat da Mami suna game waje ɗaya ko damuwa basuyi ba.

Nashiga ruɗani haka akai gaba dani har gidan yarin da aka kaini, rayuwace wadda sai wanda yata6a dandanata zai iya tantance ta ranar........


```QADDARATA kenan wadda tazo da kalubale iri iri na rayuwa musamman Amina da ahalinta,labari mai cike da tsantsar tausayi wani abun ma sai kaji kanka bai dauka haka Qaddara take kuma kowa da kalar tashi saidai ta wani tafi ta wani gadai yanda Qaddarar Amina Caranci tazo aciki kuwa harda rasa aminiyarta masoyiyar ta Asma'u Caranci turkashi ya wannan lamarin zai kaya sai kun biyoni a cikin labarin HAKA ALLAH YASO Season Four danjin da wane salon yake tafe dashi.```


*Shin waya kashe Husna?*


*Ya Taufiq ya tafi zai dawo?*

*Ga Minal a Prison zata fito,in tafito taya hakan tafaru?*


*Miyakawo JJ cikin wannan case din?*

~Abubuwa dama suna tafe a cikin Haka Allah Yaso.~

_Addu'arku agareni ta musamman ce kusani duk ina ganin sakonin ku ni Amina Caranci ina maku fatan alkhairi_


Assalamu alaikum.
*ƴan uwana masoyana,ina mai shaida maku cewa insha Allah ni Yar Mutan Kankia zan ɗage Alqalamina zuwa na wani lokaci,saboda yanayin karatu da nikeyi abubuwa sun mani yawa,fatan zakuyi mani uzuri insha Allah sai mun haɗu a cikin Season Four mai taken Haka Allah Yaso! Ina maku so dan Allah.*

_Lokaci bazai barni in lissafo tsantsar masoyana ba saidai kusani ina godiya da kaunar ku agareni kuma ina maku fatan alkhairi masoyana sune yan amanata wanda kullin kuke nuna mani ita ba dare ba rana kusni ni Jameey Yar Mutan Kankia bansan taya zan musilta son da nike maku ba,Allah yabar mu tare ameen._

*Kuma inakara ba yan Daukar Fansar Budurcina Paid grp and VIPs kuyi kara hakuri kusani kuna raina a kullin zaku sakejin gwanar taku,insha Allah.*

_inaima kowa da kowa fatan alkhairi,kardai ku manta👇🏻_


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls
❣️



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment