Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin shi,acewar ta shida ba Abba har abada musamman dataga ya damu da rashin ɗan nasa tana gudun so da kaunar da yake mashi ya dawo a cikin zuciyar shi bayan disashewa da tayi duk wahalar tuggun da tajima tayani yana neman rushewa abanza a wofi musamman da taji yana ikirarin duk ranar da Hussein ya dawo zai nema mashi auren Aminatu da kanshi ba dan aike ba,wannan shi yakara jagula mata lissafin bari hakan ya faru kamar tawaya ne a gareta,wannan kenan.

Bayan kwana biyu da rigimar mu da Anty Hafsat Kawu Usman yazo yacema Mama kakanmu yana kiranta hardamu kanmu,waya mukaima Baba muka sanar mashi sannan muka dunguma sai gidan Alhaji Baba acan muka iske Anty Hafsat da ya'yanta dasu Anty Mubara da sauran ya'yan shi mata masu aure garin duk mun samesu saida ya bari kowa ya naba'a yace.


"inasan kowa daga cikin ku yabani aron hankali shi kuji abinda zance maku amatsayina na mahaifi agreku,musamman Hafsat da Khadija da ya'ya yenku wannan zaman nakune baki ɗayan ku.


Tabbas da ace iyaye basu kai zuciyar su nesa da sunma ya'yan su baki arayuwar da muka tsinci kanmu a ciki,kamar ni ace ya'yana suna faɗa da junan su agaban bainar nasi,wannan wane irin musibace ke Hafsat kece ja'irar tunda har zakibi kanwarki har ma'auri keda ya'yan ki,kuhauta da duka dan rashin sanin ciwon kanki wlh,kinyi asara.

Baku da wani bakin magana a cikin garin nan kunbarma kanku abin fadi da gori agari baku kanku ba,hattani ubanku inajin kunyar yawo cikin garin nan.!"

KowA yai shiru banda Mama dake hawaye daman ance nai neman kuka bare anjefe shi da kashin awaki.

Baba dan Allah kayafe mana munyi kuskure ni kaina ina danasanin faruwar wannan al'amarin amman munyi danasani dan Allah Baba kayafe mana.!"
Cewar Mama.

"Khadijatu kidaina kuka kowa shaidane yanda komai yafaru har gidan ta kinje kin bata hakuri takiyi dayake ke Hafsat bakison Allah baki tsoron rayuwa kiji tsoron ranar nadama nidai bazan maki baki ba amman kisani abunda kikai mani a garin nan banji dadi ba.!"

Saifa lokacin Anty Hafsat tafara kokarin kuka tana ba Baba hakuri.

Baba kayi hakuri kada kayi fushi dani na tuba dan Allah kayafe mani.!"

Bani zakiba hakuri ba yar uwarki zakiba hakuri da kikaje kikaci zarafinta kuma taje gidan ki,kika wulakanta ta agaban ya'yan ki,kenan kin basu damar cigaba da wulakantata a kowane lokaci.!"

Ina kallan Anty Hafsat yanda ta wurgama Mama kallan tsana dantaji ance ita zataba hakuri,amman saita kanne ita kanta Mama taga kallan da take mata,dayake tasaba da tuggu harda riko hannun Mama tana kukan kissa tabata hakuri.

Kiyi hakuri Khadija bacin rai yasa nagaza rugumarki a matsayin ki na kanwata dan Allah kiyi hakuri kiyafeni nida ya'yana.!"

Nayafe maku Anty dan Allah nima kiyafe mana."
Shikenan nayafe maku nima Allah ya yafemana."

Ameen aka amsa,Mama taima Anty godiya.

Kowa ta nemi afuwar kowa ke Umaima kunemi afuwar kanwar mahaifiyar ku,ko bakusan ya kamata ba.!"
Cewar Alhaji Baba.

Inna kiyi hakuri akan abinda mukayi maki."
Bakomai Allah yaimaku albarka nayafe maku ya'yana Allah ya yafe mana kurakuren mu."
Ameen su ukace sukai mata godiya.

Muma Anty Hafsat tace tayafe mana muyi hakuri rashin sauraren mu datayi da mukaje gidan ta bata hakuri.
Haka dai muka yafi junan mu gwanin ban shi'awa itako Dada banda zirarar hawaye ba abinda take.

Allah yaimaku albarka take ta cewa tana mana addu'a baki dayan mu Allah ya karemu da fitinar shaidan ya kara hada kanmu baki daya,ranar can mukayi lunch sai yamma muka dawo gida kowa yanajin dadi aran shi.

Haka rayuwa ta kasance gwanin dadi muda Anty Hafsat zumunci kuwa kamar Da,haka muka koma tana son mu muma muma sonta,saidai har yazun nagaza sakin jikina da ita jana take ajiki sosai abinda baku sani ba hausawa nacewa idan maciji ya cijeka sau daya idan kaga igiyama guduwa zakayi hakan yasa nagaza sakin jikina da Anty Hafsat dan inaji ajikina har abada bata sona tinda ta fito fili ta gayama duniya nasan dafinta agareni.


Bayan kamar wata daya dafaruwar komi Mum tazo Caranci gidan mu ta sauka da kaya a ƙatan jikka ba abinda dake ciki sai su sweet biscuit da sauran kayan sa rana kwamu lashe tace kayansa ranar Fatima ne (Fatash) kowa yaji dadi musamman ni duk da bata gayamani ba hakan ya samo asali dajin haushina da takeyi tana Blaming dina akaina ɗan uwanta ya gudu yabar su.


Fira sosai sukayi da Mama da Baba sai Baba Hassan da Anty Murja nan suka raba kayan sa ranar aka tada Ahmad ya dinga kaiwa gidajen dangi.

Baba ke tamayar Mum labarin Ya Taufiq.
Wlh Baban Yara ba labari nidai na hakura hakama mahaifin shi ancigita duk kasar da mukasan zai izuwa munsa mutanen mu nacan dubashi amman bashi ba labari kasan duniya da fadi take namu shine addu'a."

Inalillahi wa'inna ilahirraji'un gaskia lamarin nan ni kaina yana damuna nima na ba tsangayoyi da masallatai ana addu'a kuma duk ranar juma'a ana sadakar fanke ga almajirai insha Allah Hussein zai dawo gida."

Allah yasa danaji dadi,ai Hussein yasani cikin damuwa ainun Allah dai yaima zuriyar mu albarka.
Ameen Umma.

Haka sukaita firar su inaji nidai bance komai ba domin duk sanda za'a dauko labarin Ya Taufiq ana tado mani wani irin tsohon ciwo a cikin zuciya ta dakyal nike dawowa normal ranar haka zan wuni da kunci araina.

Inajin shigowar Anty Hafsat sai fira ake da ita harda dariya suke ta likema Mum suna fira har aka gama sallar la'asar sannan ta tafi gida itama anbata kayansa ranar.

Washe gari Mum zata koma gida Ahmad yakaita Airport din Aminu Kano ta tafi gida.

Rayuwa mai dadi wata kuma saidai agode Allah haka ake maneji kowane dan Adam na tafiya ne bisa Qaddarar shi dan dai ta wani tafi ta wani kai idan kaji rayuwar wani saika godema Allah domin kai a al'janna kake tsundum.


*************

Bayan kwana biyu da komawar Mum nakira Fatash waya naimata murnar sa ranar ta da akayi da Bashir (Bash) saidai a dakile take amsa mani kamar ina mata dole,sanin dalilin ta nayi mani hakan shiyasa ban wani damuba nasan watarana sai labari kuma da sannu zata gane cewa shima Ya Taufiq din yana rayuwa ne akan Qaddarar shi haka Allah ya tsara mashi zata gane cewa ba laifina bane haka Allah yaso dandai nice sila dole a dangantani da laifin tafiyar shi.

Ganin munyi shiru harna wulla cikin tunani hakan yasa nai mata sallama da Okay ta amsani kashe wayar nayi ina mamakin hali irin na Fatash,ganin raina na neman baci abanza a wofi nakira Husna muka hau firar mu ta masoyan ainihi amana so da kauna duk dan Allah mukema junan mu nan take gaya mani watan haihuwar ta ya kama nai murna sosai nai matan fatan haihuwa lafiya nagaya mata ansama Fatash rana taji dadi tasa albarka.

Kema kawata Allah yaimaki zabin miji nagari wanda zai rikemani ke amana yabaki kulawar data dace wanda bazai taba samani ke kuka ba,wanda zai zama jigonki kuma ya tarairayi marainiyar zuciyar ki.!"
Murmushi nayi inajin dadi araina nace.

Yanzun kawata kina ganin akwai irin wannan mijin da kike mani fata,idan ma kawai shi yai mani nisa ahalin yanzun."

Hmmm Minal kenan......



_Yar Mutan Kankia ce❣️_





Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA. ❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E43&44




Yanzun kawata kina ganin akwai irin wannan mijin da kike mani fata,idan ma akwai shi yai mani nisa ahalin yanzun."

Hmmm Minal kenan waya gaya maki kina zaune Allah zai kawo shi cikin rayuwarki."

Husna aituni Allah yakawo shi nisane kawai yai mani domin nasan wannan qualities din dakike lissafa mani bada kowa ya dace ba sai Ya Taufiq ada Lukman yaso yaka manta akwata a cikin waɗannan abubuwan amman Ya Taufiq daban yake shi kadai zai iya maidani haka kawata.!"
Na ida maganar cikeda rauni.
Insha Allah watarana zaku mallaki junan ku keda Ya Taufiq nima inaji araina kece matar shi.!"
Anya Husna akwai wannan ranar kuw.?"

Kobayan raina zakice ni Asma'u nagaya maki haka masoyiyata.!"
Kefa daɗina dake kenan Husna muna cikin nishadin mu saiki kawo zancen mutuwa haba."
Na ida maganar cikin rashin jin dadi.

Kaiya kawata aibata noticing any time take zuwa gwara nu dinga tunawa da ita a kowane lokaci.!"

Naji malama insha Allah nice zan rigaki tafiya."
Nidai,mukahau musu nace
Nidai mubar zancen nan banson shi dan Allah.!"

Naji mu kama wani tace mani.
Kuma kisa a ranki idan ina taredake Husna nasan bazan taba kuka ba gashi yanzun ma kin wanke mani bacin raina.!"

Kisa wannan ranki saidai in ban numfashi amman kawata bazata taba kukaba hakanan inagani in gaza share mata hawayen taba.!"

Allah yabarmin ke kawata ina kaunarki Husna."
Ameen Habibti Allah ya nuna mani aurenki in kwashi shoki musamman ace keda Ya Taufiq ne."
Murmushi nayi nace amin tawan.

Sosai mukayi fira da Husna mun kusa awa sannan mukayi sallama bayan na gaisa da Mina.


*Two Weeks Letter Ago*

Ina zaune a office dina nagama duba patient tunanin duniya ya dame ni musamman na Ya Taufiq wanda ya zaman mani ruwan dare sai yanzun nafara shiga damuwa da nisan da yai mani da nafi dakewa musamman da nike yawan mafarkin shi da nikeyi ba dare ba rana hakan yana taba mani zuciya.

Ban ankaraba naji an shigo mani office ba wani notice bude idona nayi da suke rufe na jinjina kaina bisa Sofa inadan jujjuwa kadan JJ ne tsaye bisa kaina yaimani ƙuri irin kallan maitar nan,dan faduwar gaba naji kadan na dake ina mashi kallan ko lafiya.?"

Kema kinsani ai kaunarki ta hanani sukuni shine nazo ki taimaka mani zanbaki ko nawa kikeso kibani just a fifteen minute in ɗanɗani zumarki dan Allah Amina.!"

Kallan wawa jaki dakiki kidahumi duk nike mashi a lokaci ɗaya gami da tsanar shi fal a kwayar idona.
Nuna mashi kofar fita kawai nayi da yatsana manuniya!

Ke harkin isa ki koreni? Ke har wani arziki kike gadara dashi? Harkin isa duk matsayin da kike gadara dashi mune sila malamanki.!"
Get out of my office Dr JJ.!"
Nayi maganar atsawace.

Kinyi kaɗan Amina kici mani mutunci kuma wlh billahi sainasa kinyi nadama saina saki kukan dahar ki mutu bazai taba tsayawa ba sai nasaki kukan da inkika fara sai kwayar idanun ki ta tsiyaye tsabar bakin ciki da danasi.!"

Kallan shi kawai nike amman a zahiri bawai shidin nike kallo ba Dr Ahmad Idris nike kallo wanda yai mutuwar tsaye da alama maganganun JJ suka zautashi.

Kikai mani kuri da ido idan sunana Junaid Jamilu saikin sha mamakina.!"

Juyawa yayi zai fita yai kicibis da Ahmad wanda nike kallo tun shigowar shi,fuuu ya fita yana bugo kofar sai lokacin na koma na zauna bisa kujera ina fidda iska mai zafi,duk da ban wani dauki kalaman JJ da mahimmanci ba musamman danasan baida buri sai yaga ya lalatani abinda nasani nai mashi nisa har abada kuma bazai samu nasarar sakani kukan dayake ikirari ba.

Sai lokacin ya iso kafa sage ya zauna murmushi kawai nayi mashi.
Waye wannan nasan shi a seminar da muka hadu Lagos miya hadaki dashi.?"

Sona yake amman dole yakeson yimani kuma shidin ba Allah aranshi shiyasa."
Jinina kai yayi yana mamaki.
Gaskia kikara kula Allah ya tsare,amman kalaman shi sun tsoratani sosai."
Insha Allah nace.

Dagani da magana abakin shi yakasa mani ita,koda na tambaye shi cewa yayi gaidani yazoyi dan dole na barshi kamar yanda ya fadi.
Tare muka fita nayi gidan mu hankalina kwance.

Bayan kwana biyu,ya kama week ends ba inda nike zuwa ina zaune nida Zainab tagama samani lalle Ja na sallataf,wayar Mama tahau ruri dayake tana gefena dan waigawa nayi naga sunan Umman Lukman ya bayyana.

Hakanan naji faduwar gaba dan bansan asake yimani maganar Sadiq kanin shi,infact a halin yanzun ban ra'ayin wata soyayya inma aure akeson inyi nidai ayafe mani in auri Ya Taufiq domin hankalina yafi kwanciya dashi,maganar da naji Mama nayi tasa na maida kallona gareta.

Insha Allah Hajia gaskia banga aibun yarinyar ba amman dai kibawa Alhaji hakuri dan kyautawa bata kyauta ba,dan Allah kuyi hakuri."
Bansan mi tacema Mama ba,naji tace.
Nagode kwarai dagske Allah yasaka da alkhairi yaimana jagoranci."
Toh sai anjima zasuji.

Kallan ta mukayi musamman ni saidai ance wasa wuri gareshi nasan koda gigi ban isa intambayeta mi akace mata ba da haka na kori zance araina baki daya.

Kizo gida yanzun ki sameni Mubaraka."
Aaa lafiya zance dai amman kedai kizo dan Allah."
Okay sai kinzo."

Mudai fira muke nida Zainab dagata gama daure mani kunshin hannuna saidai kaf hankalina nakan Mama.

Ba'awani jimaba Anty Mubara ta shigo gai data mukayi ta amsa,tace Anty lafiya dai ko.!?"

Janta tayi uwar daka saidai kaf kunnuwana na kansu tunda naga Mamar Lukman takirata waya na tabbata koma minene ya shafeni.

Mubara wai kinji abinda Anty Hafsat taje ta aikata a Gusau.?"

Mi kuma ta janyo mana.?"
Zuwa tayi gidan su Lukman wajen mahaifiyar shi wai tanason Sadiq yazo ya nemi auren Khadija tabashi duniya da lahira.!"
Hakanan nima naji faduwar gaba har saida muka kalli junanmu nida Zainab.

Inalillahi wai mi yasamu kwakwalwar Anty Hafsat anya bata haukace ba,taya zataje tayi wannan abun kunyar Sadiq din da akeso a hada shi aure da Aminatu yazo ya nemi izini dan dai ance ya daga kafa da yanzun wannan maganar aita jima da nisa,wannan wace irin Qaddarace Anty Hafsat na neman zama fitina a cikin zuriyar mu.!"
Inji Anty Mubaraka

Kidaina cewa haka Mubara fata Allah ya shiryeta,dalilin kiranki shine mahaifiyar Sadiq tace,yaron yace shidai bai son Khadija tayi hakuri,bazasu iya gaya mata bane,shine sukace insamu wani in sanar mashi su tunkareta da maganar kuma mahaifin yaro yace indai tasan wannan zancen zai kawota kada takara zuwar mashi gida koda ba maganar Aminatu bazaima dansa auren dole ba.!"

Kinji kayan kunya inalillahi ohni jikanyar Hafsat da Khadija duniya cike take da kayan kunya wlh ji nike kamar infasa ƙasa in shige dan takaici.

Nima banji dadi ba amman ya zanyi tunda Allah ya hadani da yar uwa bankaura dole nazauna da ita a yanda take nasan dai Anty Hafsat Qaddarata ce."

Kiyi hakuri Anty Khadija bata kyauta ba kam.!"
Hakuri dolene Mubarka,inasan ki mata wannan maganar kila taji ta gyara."

Ni asuwa inji yan caca wannan zancen kamar agaban Dada kikayi shi yanzun haka gaban ta zan sauka ingaya mata komai watakil taji maganar mahaifiyar ta.!"

Shikenan hakan ma yayi Allah kyauta wlh har bansan Aminatu taji wannan labarin saboda zata dinga ganin yayata uwa daya uba daya ta tsaneta.!"
Hakane kada kigayama kowa hatta Baban su bari inje da zafi zafi akan bigi karfe sai anjima.

Da haka ta tafi mukai mata sallama saidai abinda basu saniba komai munji dagani har Zainab kamar agaban mu akayi shi saidai banji komai ba inda sabo yaci ace nasaba da halayen Anty Hafsat agareni na hassada da tsanata da tayi.
Dada da kanta taje gidan Anty Hafsat taimata fada akan abinda take shirin aikatawa.

"Kiji tsoron Allah Hafsat ni mahaifiyar kice dole ingaya maki gaskia,akan mi kinsan Sadiq dinnan yazo nemann izinin auren Yar kanwarki shine ko kunyar Allah bakyaji zakije da wannan zancen ina kikeson kikai sa ranar dake kan yarinyar nan Khadija.?"

Haba Dada waini miyasa duk abinda zanyi baku ganin kyauta wata ita Aminatu ai batason shi da batakai haka ba,tunda sunama lamarin tafiyar hawainiya aini sai indauki abin da mahimmanci!

Kuma naga aisa rana ba daurin aure bane idan har Sadiq zaice yana son Khadija ni kuwa sai inhani Muntari in bashi ga arziki wazai so tsiya.!"

Ke Hafsat ki guji duniya ba gidan zama bace wlh inajiye maki ranar dana sani kuma indai nice uwarki na haramta maki wannan zancen kuma kijini da kyau,uban yaro yace kada ki kuma jemashi gida inkunne yaji gangar jiki ya tsira fatan zaki kiyaye.!"

Haba Dada ga samu ga rashi kenan!"
Ana dolene ko zaki kai yarki inda ba'asonta bayan iyayen shi da kansu sukace ai maki
magana kuma yaro yace Aminatu yakeso.!"

Shikenan Dada magana ta wuce Allah ya kyauta.
"Ameen sannan kibar zancen nan kinga dai bikin Khadija bai wuce nan da wata daya ba kadama kibari aji.!"

Magana ta wuce Dada daman ance rashin tayi kanbar arha sai tayi maneji da Muntarin ya zatayi.!"
Ke Hafsat yaron nanfa yanada rufin asiri zaima yarinyar nan komai."

Dada ci dasha kadai shine arziki tunda kince haka bakomai Allah yasa hakan yafi zama alkhairi."
Ameen ya rabbi,nidai zan koma dan Allah duk abinda zakiyi kidinga dubawa karkiyi aikin dana sani."
Insha Allah,da haka ta raka mahaifiyar tata.

Da yamma kuwa kwatsam saiga Anty Hafsat gidan mu,lokacin Kawu Ali nanan munata fira tahau bala'i.

Khadija harkin isa kije ki hadani da uwata na fahimta baki da buri daya wuce kiga ta tsinemani ko? ta Allah bataki ba,Khadija.
Kuma dakike maganar wai anki ya'ta aiman magana naga aiba harum na aikata ba dan nane mama ya'ta aure,kuma Allah ne bai nufa ba,sannan dan wani yaƙiƙa da yini wani da kwana zai soka naga ai tanada sa ranar a kanta ke yar taki tasami arzikin sa ranar ma inta isa,anyi cin6u.!"

tankata Mama bataiba.

Kedai Anty Hafsat inaga dai bakison kigama lafiya anya kinada hankali kuwa waike komai saiki kwaso kima Khadija,inkin isa dan Allah kima Mubara mana ko Rukayya kiga tsantsar rashin kunya wlh.!"
Kawu Ali yai maganar a fusace.
Dan batai mani bane angaya maka ni tsoron Mubaraka zanji ke kuma ki kiyayi ranar haduwata dake."

Sai lokacin Mama tai mata magana tace.
Allah kada ya nuna mana wannan ranar Anty Hafsat ni kaina basan mizai faruba a wannan ranar wadda ni awajena ki kirata da bakar rana.!"

Shikenan Khadija muzuba mugani!."
Fuuuuuu ta fita,hakuri Kawu Ali yaba Mama shima ya fita.
Bayan kwana biyu.....


********

Dada ce tazo gidan mu wajen Mama nagama ɗaurin tuwo cikin leda kenan ta shigo gaisawa mukayi ta shiga cikin falor itada Mama.

Khadija naji abinda Hafsat taimaki bayan naje na kashe magana da kaina har gidan ta,wannan shike nuna ta rainani bata ganin girmana dana mahaifin ku,kuma muddin nace in yawaita yi mata wannan maganar tabbas baki zai kamata kinsan dai yanda bakin iyaye yake,tunda ke uwace nasan zaki fahimci haka,amman ita Hafsat gata uwa ta manta hakan,dan Allah kiyi hakuri da abubuwan da take maki koma ince kikara akan wanda kikeyi kinji.!"

Bakomai Dada ni ban rike da Anty nasan dai abaya ta soni so na hakika bansan dalilin dayasa take kina ba a halin yanzun ba.!"

Kema kinsani Khadija saidai kike faɗa,hassada ce kawai ke dawainiya da yar uwarki kuma Allah ya shiryeta,ada kece ke mata hidima saboda mijinta nada kudi yanzun da Allah ya jarabce da rashi shi takasa dangana, ganin mijinki yafi nata wadata shine soyayya ta zama kiyayya ta manta Allah shikeyi,kedai kida ki sake ki zama mai yawan hassada, harumce tana cinye kyawawan ayyuka kuma tana maida masu arziki talakawa,talaka ta maidashi fakiri,amman wadatar zuci shine arziki Khadija kikara hakuri Komai lokacine.!"

Naji dadin wannan nasihar taki Dada insha Allah zan kara."
Allah yaimaki albarka.
Ameen.
Rakiya taima mahaifiyar ta,tatafi gida,wannan kenan.


*Comment dinku da fatan alkhairin ku agareni na musamman saidai ince Allah yabiyama kowa bukatun shi na alkhairi,barkan mu da Juma'a Allah ya hadamu da mafificin alkharin dake cikin wannan rana,ameen ya rabbi🤲🏻*



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E45&46



Dawowata daga wajen aiki kenan na iske unguwar mu tamkan da 'yan Adam kana gani kasan ba lafiya abin da idanuna suka gane mani shi yakara razanani Umaima da Khadija (Kanwarta) ake dambacewa abin takaici Umaima daga ita sai ɗan kamfai(fant) kanwar ta bisa ruwan cikinta sai jibga take duk ta fasa mata lebba da hanci ita kuma ta gartsama Khadija cizo a yatasa jini nata shatata,Mama naga ta fito gida da gudu tayo kansu tana kokarin bambare su,sai ga Anty Mubara itama tai maka mata tayi da kyal aka kwace Umaima hannun Khadija taimata lis tana kuma wlh ko uwarki Hafsat ta dawo saikin bani kudlɗin sitting dina tunda ba ubanki yabani suba matsiyaciya ba'a da aiki sai Dadiro."

Wannan kalma ta caki kunnena ainun Anty Mubara ta wasgama Khadija mari.
"Dan ubanki yar uwarki kike tozartawa gaban mutane.!"
"Gaskia ne faɗa Anty aikinta kenan yoh wazai aurarma kanshi kingi."

Mama taja Umaima zuwa gidan mu bawani nisa sosai itako sai kuka take jini na zuba abin takaici duk taron mutanen kowa yace bai rabawa abarsu su kashe kansu har uwarsu tadawo tagani,naji takaicin hakan.
Maye masu baya nayi ana zuwa gida Mama tahau fada.

"Ke Khadija bakida kirki bansaniba jibi abinda kikaima yayarki bakiji kunya ba."

Lallaima Inna, kunyar mi zanji yanda bata fasa daukar mani kudin sitting ba nakamata taki bani wlh bazan fasa dikar banza ba,kisha bugun banza kuma wlh saikin badasu ko in kara maki wanda yafi wannan."

Wa'anne kudine nawa ne.?"
Cewar Ahmad.
"Dubu talatin ne cif ta daukar mani kuma dasu zanba kawayena asai kayan abincin da za'aci a bikina."

Idan na baki magana ta mutu ko.?"
Cewar Ahmad dake shirin konawa makaranta Final year a UDU Sokoto.

Kusan hakan dai."
"Kamarya mi kike nufi tunda yace zai baki ai shikenan."

Nifa gaskia nafison nawa wanda mijina yabani eheh tana son kudi ta kashe auren ta saboda mugayen halaye andawo gida ana kurɗe kurɗe saboda dandi."

"Ke Nana kikara maganar nan zan ballaki dan ubanki Umaima kike cewa haka ba yayarki bace wlh zan fasa maki baki marar kunya."
Tsit tayi kamar ruwa yacita tasan tsaf Ahmad zai dirki banza dan bawai wasa yake dasu ba ko kadan.

"Ke kuma bata kudinta."
Bata iya yima Ahmad musu ta kwance habar zani wanda yagama zama jajir dan burgima ƙasa data sha gun Khadija ta bata kudin,fisgewa tayi tace.

An badasu ta wahala ga jibga mutun yasha ai ance jiki magayi."
Ahmad yai kan Khadija tayi waje da gudu tana surutai.

Zaro dubu ashirin yayi yaba Umaima duk kunya ta kamata,ta amsa tana godiya.
Mama tasa tai wanka nabata kayana wajen kala hudu zuwa biyar tasa ɗaya daga ciki,jiki mace ta zauna gidan mu har Anty ta dawo daga Kano taje siyen kayan kicin wa Khadija.

tana dawowa gida ta iske bakin labari ba kunya ba tsoron Allah Khadija tagaya mata komai dayake tafi karfin uwar ba yanda zatayi da ita saidai tasa mata ido,tana aje kayan Kicin din data siyo ta wuto gidan mu direct nan ta iskeke anyima Umaima dressing tasha magani.

Da borin kunya ta iso cikin gidan tana fada.
"Ni za'aima dibar albarka ya'yan nawa za'bari suna dambe a tsakar duniya dan ɗibar albarka daman ga mahassada sunyi mani dabaibayi......
Yanda taga fuskar Umaima dole sauran maganarta ta makale bisa leben ta.

Kamar jira Umaima tahau kuka tana magana ahade dan lebenta a suntume yake.
"Umma kinga abinda Khadija taimani akan kudi saida tayi mani tsirara agaban jama'a.

"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un ni Hafsatu mi zan gani haka saidai kace kafurai na faɗa kamar ba jini daya kuka futo ba,sai kace ba mahaifa daya kuka kwanta ba,kukasha nono daya anya Khadija nada hankali irin wannan bugu har haka kekuma kikai kwance tabas kanwarki tahau ruwan cikin ki taita murza wlh kin bani kunya Umaima."
"Haba Anty ai ba wannan maganar zakiba wane irin kunya samu zakiyi ki masu fada ki hada kan ya'yan ki tunda aikin gama ya gama sai addu'a."

"Yiman shiru nasan yau burinki ya cika harda wani tattara mani ya'ya dan kiji dadin mani dariya saikiyi da hujja."
"Haba Umma Anty fa ita taceceni wajen Khadija kuma ita da kike gani wlh bata wani bakin ciki dake har kudi saida Ya Ahmad yabani kingansu naira dubu Ashirin."

"Eyeh muga kudin dubu ashiri waddda nasani(20,000) dai.?"
"Eh mana shiya bani kuma Anty Amina tabani kayan sawa duk kingansu nayi bacci naci abinci harda magani ina laifin waɗan nan mutanen."

Kamar ta nutse dan kunya tace.
"Hakane kam nagode maki Khadija,ke kuma muga kudin da ɗan nawa yabaki."
Gasu kigani."

Warcesu tasoyi Umaima ta amshe har dubu daya taso yagewa tace.
"Ke akaba koni kagane mani ikon Allah da Umma."
"Dan ubanki ba da'na ya baki suba da ban haifekiba ya baki.!"

Duk da haka ai hakkina ne ba nakiba Umma."
Fitowa Ahmad yayi yaba Anty Hafsat dubu goma yace gashi takara a biki.

"Allah yaimaka albarka Amadu Allah yasa akare rayuwa cikin albarka yabaka duk abinda kake nema duniya da kiyama nagode maka."

Baki dayanmu kallan juna mukeyi first time da Anty Hafsat taima ya'yan Mama fatan alkhairi aduniya dayake anbata kuɗi.

"Ke kuma tashi muje gida ko?"
Haka ta dauki jikan nata suka lallaba sai zabga godiya suke sukayi gida.


*********
Bayan sati daya anfara shirin bikin Khadija gadan gadan saidai wannan karan Mama bata zira jikinta ba sosai ba kamar bikin Umaima ba.

Mama takirani tace inzo inkaima Anty Hafsat gudummuwar da zata bata,mikomani tayi tace.
"kikaimata injini ga dubu hamsin nan sai Baban ku ya bata dubi ishirin kinga sun kama saba'in kenan,ke mi zakibata.?"

Shiru nayi dan banji zan iyaba Anty dukiyata tunda ba kaunata take ba.
Ganin nayi shiru take Mama tagane manufata tace.
"Shikenan nafahimta watarana kunyi tsakanin ku da ya'ya shi zumunci ba awasa dashi tashi kitafi."

"Toh Mama kinga keda Baba kun bata saba'in

Please Login or Register in order to submit comment