Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

awa daya,lsmail yayi murmushin takaici,babu laifi matsawar lokacin sallar azahar ba zai shigo ba,alhaji ya ce,sai batun albashi,hajiya ta ce min ka ce duk abinda aka baka,lsmail ya ce haka ne. alhaji ya ce,aa zai fi kyau ka fada,lsmail ya ce,alhaji me karantarwa ladan shi yana gurin ALLAH,abinda zaa ba mu kyautatawa ce,alhaji ya ce,to da kana samu dubu hamsin a wata?lsmail ya ce,aa gaskiya basu kai ba,ya ce,to zan dinga baka dari. da sauri lsmail ya kalle shi, sai MIMI ta fashe da dariya kudin sayan kayan kwalliya na kenan fa,ta kalli na'ima, dubi yanda ya rude,ashe ni ma zan iya biyan shi da kaina,alhaji ya ce,ka iya tafiya,sai lokacin ya yi.lsmail ya ce to,tare da mikewa, ransa bace ya fita,lallai yarinyar nan 'yar wulakanci ce,anya kuwa zai jure?. Alhaji ya kalli MIMI,uwata ki daina irin wannan a gaban mutum.ta kalle shi,dad wallahi duk duniya ba wanda na tsana kamar shi,na'ima ta ce,shine to zai dinga yi miki karatu?ta ce, eh,amma na tsane shi,ta ce to mu fa karatun mu yaushe ne sis?
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (62)MIMI ta ce,ku kan sai karshen sati.alhajin ya mike cikin murmushi bari na fita,mommy nafisa wadda kallo ya daukar mata hankali,ta mike don yi masa rakiya,ya shafi kumatun MIMI ki yi min addua uwata, ta ce,sai ka dawo dad ALLAH ya baka saa,na'ima ta ce,sai ka dawo dad,ya ce,yawwa na'ima. mommy nafisa ta zauna a kan kujerar madubi tana kallon na'ima wadda ta fada kan gado ta yi ruf da ciki,ta ce,na'ima taso ki ji,ki taso mana na'imata,ta dago fuskarta da jurwayen hawaye,ta ce,mommy dad ba ya so na,komai sis MIMI, ni kam na gaji.nafisa ta ce. amma me nike fada miki kullum?ba ke kadai ba ce yake yima haka,ku duka ne, amma nayi miki alkawarin sai ya so ki fiye da MIMI. na'ima ta soma kuka,na gaji da jin haka mommy,sai yaushe ne haka zata faru?mommy nafisa ta tashi ta koma bakin gado ta zauna,ta janyo na'ima zuwa jikinta,kar ki damu,mu bi a hankali da sannu za ki zama 'yar gaban goshi. akwai shirin da na jima ina shiryawa,na'ima ta kalle ta da gaske?mommy nafisa ta ce,kar ki yi shakka.ta share hawayanta,shikenan zan so in yi kamar abinda take yi,ko kuma fiye suka sa dariya. Shadaya daidai lsmaik ya shiga cikin falon,bayan me aikin ta zo ta bude,na'ima ce kadai a falo tana kallon fim din india,ya ce,ki fada mata nazo,ta yi mishi kallon banza,ba ta ce, in kazo ka jira ta bane?ga falon da kuka zauna can a jiya,zaka iya jiranta a ciki.ya nufi falon ransa bace,anya rayuwar gidan nan zata yiwun masa?mintinsa goma shabiyu,sannan ya soma da jin kamshin turaren ta,gabansa ya fadi,ta ja kofar wadda ta kasance ta gilashi,kallo daya ta yi masa yana sanye da jallabiyya fara sal,ya yi kyau matuka,ta tabe baki,ta zauna shima ya kalle ta kamar koyaushe shigarta babu tsari,ya kauda kai,ya ce,ta ina za mu fara?ta daga wayarta ta sa a kunne,hello dear ka tashi lafiya?ta dai yi jim,ok zamu yi waya anjima,yanzu ina tare da talakan nan ne,sai kuma tasa dariya,khalil kenan sai anjima din.ta kalli lsmail me ka ke fada?ya ce,ta ina zamu fara?
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (63)Yanda ya kafa mata ido hadi da hade ranshi,sai ta ji yayi mata kwarjini,ba za ta iya kallon shi ba,yayi da zata yi masa rashin mutunci,ta kauda idanunta gefe,ko ta ina ka fara mana,ka tsare ni da idanunka,yayi dan murmushin takaici,ya ce,to zamu fara daga huruful hija'iyya,alifun kenan.ta dube shi da sauri tun ina 'yar nursery na yi wannan, yanzun kam university nike, don haka sai ka koya min karatun da yayi daidai da ajina,lsmail ya ce,zan so in baki shawara,dul me neman ilimi ko bana addini ba zai fi kyau ya zama me biyayya da saukar da kai, girman kai ba ya kai mutum ga gaci. ta daga mishi hannu,baa dauke ka don ka bani shawara ba,an kawo ka ne kurum ka koya min karatu. ya ce,to bari mu fara daga fatiha sai mu shiga bakara zuwa kasa ko?ta tabe baki,ina jin ka,ya ce,zan karanta miki kamar sau uku,sai ke ma kiyi.tunda ya soma karatun danna wayarta ma take yi,ya gama ya dube ta,yanzu sai ki karanto fatihar in ji ke ma daga nan sai in dora miki daga bakara aya biyar-biyar zamu dinga yi duk kwana biyu sau biyu a sati sauran kwanakin kuma sai mu saka fikihu,hadisi da tauhidi.ta ce,me kake fada ne?ni fa duk ban jika ba,ya ce,karatun na ce kiyi,ta harare shi,yanzu fa ka ce, sai ka fara sannan zanyi ya daga murya,kina nufin baki ji karatun da nayi ba?ta ce,shine gaskiya,da kayi ai da naji,ya rufe kur'anin cikin takaici,ya zuba ma kafet din kasan idanu, shi kam ya gaji.ta katse mashi tunani,a banza zaa ba ka dubu dari?ya ce,in na fasa koyarwar fa?ta ce,ka rasa,zan fin son ma ka ce ka fasa,don ni dole idanu na suke kallon fuskar ka,kuma bana son in kore ka saboda hajiya zata yi min fada,amma in ka tafi da kan ka shikenan.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (64)Ya ce,yanzun zan kira hajiyar in fada mata komai,gabanta ya fadi,ta yi shiru cikin fargaba. ya ce,zan fada mata komai don kar ta zarge ni,ta ce,bari in riga ka fada mata,ga mamakinsa sai ya ga ta saka wayarta a handsfree ta kuma kira layin hajiyar,ba ta jima tana ringing ba ta daga.sun gaisa ta ce,ya ya kuwa karatun ki na yi?ta ce eh! hajiya yanzu haka ina kan yin karatun,na kira ne nayi miki godiya,ki yi wa malamin godiya in kun yi waya,don ina fahimtar karatunsa,ta ce,ai lsmail yana da himma ALLAH ya taimaka,ta ce amin,suka yi sallama. ta kalle shi,ka gane nufi na?na san yanzun dai za ka ji nauyin ce mata bana karatu,tunda na ce ina fahimtarka,ka ga kenan sai ka nemi dalilin ka na kin koyar da ni da zaka yi,yayi banza da ita ya ci gaba da kallo agogo minti goma da suka rage sun yi mishi nisa,sai da ya ga saura minti biyu,ya kalle ta, tana ta chatin,ya ce,ki yi amfani da lokacin ki tun kina da kuruciyarki,ki nemi sanin addininki sannan ki bauta ma ubangijinki kafin lokaci ya kure miki.ta ce,kai har ka samu sake da yawa irin haka ne?ganin ka ka kai ka dinga fada min magana son ranka ne?ya yi murmushi,in kin gaji da kallon kyakyawar fuskata zan tafi,don lokaci ya cika, kin san lokaci baya jira. Ta mike tsaye,shima ya mike tare da kwasar littafansa,ta ce,har wani kyau ne da kai?
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (65)Dube ka,ya ce, sosai kuwa,don na san nafi ki nesa ba kusa ba.ta ce, karya kake yi,na sha jin mutane suna gulmar kyau na,ban da wadanda suke fada a gabana.ya yi 'yar dariya,da son ya cusa mata takaici,sanna ya ce,ina zaton suna tsoron ki ne,ko jin nauyin ki,ki je ki roki masu fada maki cewa kina da kyau su fada maki tsakani da ALLAH.ya kalli agogo,kash har na kara minti biyu,ya face,kafin ta kai ga cewa wani abu, ranshi kar,ya san cewa ya guma mata.don ya san mata ko basu da kyau,sun tsani a fada,shi kuma yayi ne kawai don shakar da ita,bai yi nisa ba,ya ji ta saka kuka,sauri ya kara ya fice daga gefen na su. Mommy nafisa ta fito da sauri jin kukan MIMI, abinda ta dade bata ji ba, ta ce, mene ne?MIMI ta ce, mommy kalle ni sosai da gaske bani da kyau? mommy ta ce,in ji wane makahon?MIMI cikin shagwaba ta ce,wancan talakan malamin mana, mommy nafisa ta ce,barshi kawai karya yake,MIMI ta ce,bari dad ya dawo dole ne malamin nan yayi kwanan cell,mommy ta ce,ki share shi ne kawai, hajiya sauda ba za ta ji dadi ba,in har ki ka kai shi gurin 'yan sanda. MIMI ta yi samanta cikin matsananciyar damuwa,kai tsaye dakin ta ta wuce,sai gaban madubin ta na jikin sif dinta,don shine zai nuna mata siffarta tun daga sama har kasa,ta dinga juya kowane gefen ta tana kallo,zantukan malamin suna yi mata yawo a cikin kai.ki je ki roki masu fada maki cewa kina da kyau,su fada maki tsakani da ALLAH,wadannan kalaman sun sa ta a cikin rudani,ta dauki wayarta,ta kira layin na'ima,bayan ta daga ta ce, ki je ki ce ma hamisu direba zamu fita,na'ima ta ce to sis,ni ma zan bi ki,cikin tsawa ta ta ce,aa ki je aike na kawai. gidan su amina dakingari ta nufa,mina ta yi mamakin ganin MIMI ba ko sanarwa,bayan sun shiga daki,MIMI cikin kuka ta ce, mina don ALLAH ki fada mun gaskiya tsakani da ALLAH.mina ta dafe kirji,me ya faru MIMI?MIMI ta ce,ni dai ki fada min,ina da kyau?,mina ta ce,ko makaho ya shafa,MIMI ya san kina da kyau sosai ma.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (66)Wai duk me ya kawo wannan tambayar? MIMI ta ce,hum!wannan malamin ne talakan banza nan dai,MIMI ta sanar da ita yanda suka yi.mina ta yi tsaki,na zata ma wani na kirki ne ya ce miki haka,ya fada ne kawai don ya baki haushi.ke to me zai dame ki tunda ba khalil ba ne ya ce baki da kyau!ln duniya za a taru a ce baki da kyau, na tabbata khalil ba zai ce ba. MIMI ta sauke ajiyar zuciya,ta isa gaban madubin mina tana kallon kanta,ta ce,mina cewa fa yayi kawai ana dai jin tsoro na ne ake cewa ina da kyau,mina ta zo ta dafata, kar ki ruda kanki MIMI,dube ki fa doguwa fara sal ga gashi har baya,idanuwanki masu haske.MIMI hatta hakoranki abin birgewa ne, so kar ki damu kanki.MIMI ta dauko wayarta ta soma kiran layin khalil,ta zauna daidai lokacin da ya daga ta ce,zan tambayeka wani abu,ka fada min gaskiya.ya ce,ina jin ki,ta ce,kana so na?ya tausasa murya,haba khadija wannan tambayar ai kin dade da sanin amsarta,amma in kina son in sake maimaita mi ke ne, sai in ce ina sonki,ina sonki sosai fiye da yanda ni ke son kaina,ta ce,saboda me kake so na khalil?ya ce, abubuwa da dama khadija, amma daga ciki akwai halinki da kuma kyawunki, MIMI ta ce,hali na kuma? khalil ko dai gaskiya ne mutane basa son fada min gaskiya?ban taba jin wanda ya yabi hali na ba, daga daddy na sai mommy nafisa,sai kai yanzun,ta kashe wayar,hawaye na zuba mata. Mina ta ce,MIMI kin cika son sama kanki damuwa, wani banza talala ya rikitaki duk ki damu kanki,ki dawo hankalinki mana? wayarta ta soma ringing ta duba ta ga khalil ne ta jefar da wayar.mina ta ce,shi kuma me ya shafe shi? MIMI ta ce,tsakanin da ALLAH mina kin taba jin wanda ya ce,ina da hali mai kyau?hatta mahaifiyata kullum fada take yi min in gyara hali na. ke ma in na yi wani abu,kina ce min irin hakin nan ba shi da kyau,amma yanzu khalik yana min wai yana sona don hali na. maganar malamin nan ta zama gaskiya,kenan masu cewa ina da kyau basu fada min gaskiya.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (67)Mina ta ce,oh my god,don ALLAH ki daga wayar khalil,in kowa zai ce halinki ba kyau,khalil ba zai gani ba,don so yana hana ganin laifi,ka da ki dama ma kanki lissafi,shawara ta ki kori malamin nan ki huta mana.MIMI ta ce,kina nufin khalil iyaka gaskiyar shi ya fada min?mina ta ce kina dai karatun englis novel na soyayya dama baki fahimtar komai?MIMI ta yi shiru tana nazari,can ta yi ajiyar zuciya,ta dauko wayarta daidai lokacin khalil ya sake kira.wanda ba ta san ko kira nawa kenan ba.ta daga muryarta tana rawa ya ce,khadija fada min gaskiya nayi miki wani laifi ne?ta ce,aa na i ka ce kana so na don hali na,ni kuma kullum kowa ce min yake ba ni da hali,fada min gaskiya.ya ce,ni halayen ki sun mini,ko da ba su yi ma kowa a duniya ba,zan iya yin komai a kan sonki,ki yi min izini in zo abuja mu yi magana a cikin tsanaki.ta ce,na fada maka dad dina bazai so ya ga ina hira da saurayi bai san lokacin da muka hadu ba,ka bari na bashi labarin ka,sai ka zo ku gana.ya ce,ko wani guri daban sai mu je, in na zo sai mu yi maganar kin ji?don ALLAH dama ina son ganin ki,ta yi shiru.can ta ce shikenan,gobe ka zo, amma zan turo maka address din gidan su mina sai mu hadu a can,ya ce, shikenan sai kin turo,ki kwantar da hankalin ki kin ji?ta ce,babu komai. mina ta riko mata hannu, kar ki damu da sauraran shi,ki kore shi kawai.MIMI ta ce,bani da damar yin haka, don dazun na kara daure kaina na fada ma hajiya cewa ina jin dadin karatunsa ina fahimta,in na ce a kore shi bisa ga wane dalili?mina ta ce,kin hadu da alakakai,ta tashi,bari in je gida,duk da haka zan nemi shawarar mommy nafisa a kan shi.lokacin da ta iso gidan mommy nafisa, mommy nafisa suna dakin na'ima suna tattaunawa a kan matsalarsu,wato MIMI, mommy ta ce,na'ima ai na ji dadin zuwan malamin nan,saboda na jima ina son in ga ran yarinyar a bace,sai dai ni bani da damar in bata mata.na'ima ta ce,don ALLAH mommy kar ki bari ta kore shi,ai ni ya birgeni da yake mata abinda take yi wa mutane.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (68)Kira da take yi wa mommymomy shine ya sa ta yin sauri ta fito daga daki,ta ce,ya ya ne MIMI,kin dawo?ta ce,eh,ni mommy kina ganin ba zaifi kyau in kori malamin nan ba? mommy ta ce,a'a bana son hajiya sauda ta zarge ni,don haka kiyi hakuri 'ya ta, bari in sa folina ta kira shi,in gargadeshi,don kada ya ci gaba da fada miki magana,ta ce,shikenan, amma ina son a yi mashi fadan a gabana don ya san ni ba sa'ar shi ba ce. Haka kuwa folina 'yar aiki ta kira lsmail,a gaban MIMI tayi mi shi gargadin kar ya kara cewa ba ta da kyau.ya ce,lnsha ALLAHU, ko ba komai dai lsmail ya ji dadin bata mata ran da yayi. A katsina kuma kwana biyu da tafiyar lsmail zainabu ta soma yin tallar ta,kuma a ranar ne ta hadu da wani alhaji,babban mutum ne a shekaru haka kuma a aljihu.direban shi ya tura ya tsaida ita,ya tambayi sunanta da kuma gidansu,ba ta boye ba don mahaifiyarta ta shirya mata cewa,ta saurari duk wanda ya zo,tunda lsmail ba ya gari,a nan ma za su samu kudin siyan mata kayan kicin.zainabu tana son lsmail sosai,don haka ta yarda tana son ta ji ana yin zancan auran su.alhajin ya zo da dare kuma ya tura uwar da kanta ta dinga gyarawa zainabu kwalliya har zaure ta rako ta, tamkar ta bi ta wajen a yi hirar da ita,tunda 'yar ta ba ta labari,ta ji a jikinta cewa irin wanda ta ke so ne ya zo.alhajin yaji dadin fitowar zainabu,don yarinyar ta yi masa,ya ce mata auranta zai yi,shi sunansa alhaji lawal,ta ce,ta yarda,da zai tafi nan ya cika su da kudi masu dama,wanda suka sa mahaifiyar rawa,ta kuma yarda cewa 'yarta ta samu miji. washegari da safe lsmail ya kira mahmud ya roke shi don ALLAH ya kaima zainabu wayarsa, don yana son su gaisa yaji muryarta,mahmud ya ce,shi fa ba ya son yaje ne a raina mishi wayo.lsmail yayi ta rokon shi,da kyar ya yarda,ya ce,zai je da yamma.suna gama waya ya mike ya debi takardu don zuwa cikin gida koyar da 'yar mulki,sunan da ya fi kiran ta kenan in zai yi maganar ta da hamisu direba.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (69)Ta fi minti talatin sannan ta fito,tunda ya ga hakan ya san yau akwai matsalar da ta fi ta kullum. ALKUR'ANI da ma yake karantawa tun kafin ta zo, ta kalli inda yake,ta ja tsaki ta zauna,ya kai aya sannan ya dube ta barka da shigowa fatan kina lafiya? ta zaro ido,ba ruwanka da lafiya ta,ko kai likita ne? bai ce komai ba,amma idanunsa suna kallon ta,ta ja tsaki tare da fadin aikin banza shishigi kawai.ya ce, ki na ji na ko?yau ba neman fada nike yi ba,don ALLAH ki tsaya mu yi karatun nan shine ya kawo ni garin nan,ni na roke ki kin ji?ta ce bazan yi ba,ya ce, to zan kira mahaifiyarki in fada mata gaskiyar komai, sannan ni kuma in tafi abina,na soma gajiya da zama haka.ta ce,zan so haka,na fi kowa son ka tafi don na tsani kallon fuskar ka,amma bai kamata in barka ka tafi haka nan ba,ya kamata ni ma in yi maka abinda ba zaka mance ba.kamar yanda kaine mutum na farko da ka soma cusa min bakin cikin da bazan manta da shi ba.ba a taba bata min rai ba tunda ni ke sai kai,ya yi shiru,don shi ya gaji da wannan wasan kwaikwayon,ya ce,to in na baki hakuri fa?ta ce,ka rike kar ka bani don bazan karba ba,ka barni in rama. ya ce,ba laifi,daga nan yayi banza da ita,sai kuma ya mike tare da kwasar littafansa,ta ce,na sallame ka ne?lokacin ka bai cika ba,ya ce,ba amfanin zaman,tunda ba karatun zaayi ba ya ta fi abinsa. yana zuwa dakin shi ya kira hajiya sauda da nufin ya fada mata komai,suna gaisuwa sai ta soma yi masa godiya har ya kasa fada mata,suka yi sallama, ya kwanta yana tunanin abin yi.haka suka yi ta yi har ranar lahadi,wacce ta kasance ranar da alhaji bishir zai amshi bakuncin sabon abokinsa,ministan man fetur.karfe takwas zai zo,amma tun shida an hana kowa sakat a gidan.girki an yi shi yafi kala goma,ban da nau'in kayan sha na kanti,ga busassu tun daga kan goro dabino,kayan marmari ma gasu na kala-kala.takwas zai iso gidan, don haja zuwa lokacin kowa na ta shiri.ya kira alhaji bishir ya ce,alhajin ALLAH zan zo fa da nawa iyalan ne.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (70)Alhaji bishir ya ce,na yi murna sosai,ina yi maku maraba. Ya fito daga dakinsa yana kiran nafisa,ta fito cikin sauri tana cewa,sun iso ne?ya ce,aa da iyalansa zai zo,ta ce,ALLAH ya kawo su lafiya.cikin azama ta shiga dakin na'ima ta same ta tana yin kwalliya, sai ta ce,yawwa na'ima ki yi gayu sosai,da iyalansa zai zo,inda namiji kiyi kokari ki ja raayin shi,ta haka ne za ki samu shiga gurin dadinku.zai so ki fiye da MIMI,na'ima ta ce,ya fada ne?mommy nafisa ta ce,aa ba ya fada bane,kin san yana son zama kut-da-kut shi da minista,in surukanta ta shiga tsakanin su yaya kike gani?na'ima cikin murna ta ce,zan yi kokari, amma in shi kanshi ne mommy ai yayi tsufa. ALLAH ya sa yana da yara maza mommy,nafisa ta ce,ina ruwanki da tsufansa?daura shi zaki yi a wuya?kudin muke bukata, ballantana a ce kin haihu,randa duk ba shi mu sha gado,ga gata gurin dadinku,na'ima ta ce,lnsha ALLAH za ta yi hakan. MIMI tana daki tana shirin ta,ita ba gwanar shafa abubuwa rakwacan ba ce,amma man ta da hodar ta zuwa turare tsadarsu ta isa.jambaki kurum ta shafa pink ta saka riga da wando damammu bakake a sama ta dora pink din shimin kayan ta zo mata gwiwa,ta tattare gashin kanta zuwa gefe ta kama shi da pink din ribom kasa-kasa,ta fesa turaranta na yau da kullum,don ta fi son turarukan arabia,takalmin ta flat baki mai ratsin pink. ta dauki wayarta daidai lokacin da wayar ta soma ringin,ta daga dad ya ce, uwata sauko sun iso,ta ce to daddy.lokacin da ta sauko falon kasan babu kowa,sun tafi tarbo bakin, bata bisu ba,sai ta samu kujera ta kame.suka shigo da sallama,ta tashi ta nufe su,matar minista ce suka shigo tare da mommy nafisa,sannan su alhaji bishir din,sai wani saurayi sannan na'ima da wata budurwa saar MIMI,sannan kananan suka shigo tare da su ahmad.kan kujerun fakon alhaji suka zauna,sun gaisa inda suka gabatar da junansu,ko in ce alhaji akilu ya gabatar da iyalansa.ya nuna uwar,ga madam dina hajiya bilkisu,sai yaro na na farko abbas.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (71)Ga shi nan ina ta fama ya yi aure yaki.ya gama karatunsa,yanzun yana aiki da central bank ne,alhaji bishir ya ce,ya kamata kam a yi aure.abba zai shekara talatin ko?alhaji akilu ya ce,talatin din ce kuwa,alhaji bishir ya ce,saan abba kenan dana na fari.shi kam yayi aure har sun yi min takwara, alhaji akilu ya ce,ka gani ko abinda ni ke buri kenan in ga 'ya'yan.alhaji bishir ya ce,ka kokarta ka ji dana? abba cikin murumushi ya ce,lnsha ALLAHU. ya nuna ta mace,waccen kuma aisha ce tana shekarar ta ta farko a jami'a ta kasar ghana,sai samira da azima da jamil duk 'yan primary ne da j.s.s. alhaji bishir ya ce,masha ALLAH,ALLAH yayi masu albarka.kai ba su da yawa ni yara na ishirin da biyu, mata na uku,alhaji akilu yayi 'yar dariya,ku manya ne, amma hakan yayi kyau, dama ka yi kokari ka cike, suka dariya,alhaji bishir ya ce,mu yi tare,kai ta biyu sai a yi rana daya.suka kalli matan wadanda suma dariyar suke har suna hada baki gurin fadin ku yi ta yi mana,ga dai yaranku nan,sun girma.bayan sun gama gabatar da iyalansu sun dan yi wasa da dariya, sai kuma mommy nafisa ta ce,ya kamata mu je dining, nan fa aka hau kan teburin cin abincin. MIMI ta kalli na'ima cikin maganar nan ta ta a hankali ta ce,ki lura tun daga kan aisha zuwa kasa ni zan ji da su daddies, mommies da brother abbas.yanda tayi maganar, iyayen suka sa dariya,haka ta yi ta zuba masu sai da kowa ya ce,yayi,ita ma na'ima ta kula da na ta gefen.bayan an kammala aka koma kan kujeru, MIMI da ba son hayaniya take yi ba,sai ta kama hannun aisha zo mu je sama na.haka yayi wa mommy nafisa dadi,har ma ta dauki wayarta ta tura ma na'ima messege,inda ta ce,ga dama nan ta samu,ki lura da abbas kuma ki ja hankalinsa.a sama,aisha sai santin falon MIMI take yi, MIMI ta kai ta ko'ina a saman ta,ta ce,gaskiya MIMI kin ji dadi,ke kam 'yar gata ce,duk nan ke daya?a ina ki ke karatu?MIMI ta ce,dubai,ai in fada maki aisha dad yana ji da ni fiye da zaton ki,duk abinda ni ke son.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (72)A sama,aisha sai santin falon MIMI ta

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

9 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment