Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko
sha. Da makilin ya soma cin karo, gasu nan kala kala,
ko wanne da kudinsa manne a jiki. Sai ya dauki mai
tsadar ciki, ya sai brush da sabulun dettol na wanka.
Sannan ya koma gurin kayan sha. Ya rasa wanne irin
drink take sha. A qarshe sai ya dauki maltina a nasa
tunanin kowa yanasha. Ya sai katan din ruwan gora
guda biyu, sai kayan tea na manyan gwangwani. Suga
na kwali. Ya sai flask din ruwan zafi. Daya fito wajen
gurin ne kuma ya isa gurin masu saida kayan
marmari, ya sayi Apple, lemon zaqi, sai kankana da
abarba. Dan acha6a yace, gsky malam za fa kaimin
qarin kudi. Ismail yace, babu komai, Allah dai ya
kaimu lfy.
Da kaya niqi-niqi ya hau samansu, gabansa har
faduwa yake yi daya tunkaro asibiti. Haka dai ya nufi
dakinsu, tunaninsa a wane hali zai samu mimin aciki?

Don yasan zaiyi wuya in bata farka ba. Ya tura qofar
cikin sallama, k idanunsa suna kan gadon. Yaya
Amina ta amsa Sallamar tana kishingide a dayan
gadon. Yace sannu yaya na barki ko? Ta sauko tana
tana fadin, banyi zatonka a wannan lokacin ba, ko
har kunje zariyan? Ya nufi gadon mimi yana cewa,
mun bari sai gobe, sbd yau yamma tayi. Bata farka
bane? Yaya Amina ta iso gaba gadon.
Tace, ta farka, ko ido bata bude ba, kuka kawai take
yi. Don nima nishin kukan ta yasa nasan ta farka.
Tsaki yaja cikin damuwa yace, nidai Allah ya sani
wannan kukan yana damuna. Yasa yatsansa ya debe
mata gashin kanta daya watso kusa da idonta, ya
maida mata shi bayan kunnenta. Ya tsura ma
fuskarta ido, wadda tayi jajur don kuka. Idanunta
kuwa sun kumbura sunyi luhu-luhu. Ya dora tafin
hannunsa akan goshinta. A fusace ta bude idanunta,
qwayoyin idon sunyi jajur. Ta zuba masa harara,
sannan ta girgiza kanta, alamun ya cire mata
hannunsa daga goshinta. Yace bakisan in dafa miki
goshi ne?
To na cire. Amma ynxun ki tashi kici wani abu. Ya
rusuna ya soma ciro abubuwan daya siyo daga cikin
ledar. Yaya Amina tace, Yauwa yanada kyau ta wanke
baki kuwa, ga makilin da brush. Amma ka manta
baka siyo roba ‘yar mai fadi ba, da FO sbd fitsari, don
kaga tana varcin nan duk ta fitsare kayan jikinta da
na kwanciyr. Gashi Kaje gida amma baka dauko
mata kayan sawa ba. Ismail yace, fitsari kuma? Ya
dago ya kalli mimi, fitsarin lfy? Sabon kuka mimi ta
saka. Domin farkawar da tayi taji ta sharkaf cikin
fitsari ya tada mata hankali.
Wai ita mimi ce haka? Mimin daddy mai shanawa.
Sam bata son ta bude ido ta kalli asibitin bare malam
Ismail, wanda ta tsana fiye da kowa. Ta tuna lokacin
da tayi wani zazza6in mura, waje suka fita, can
England aka duba lafiyarta. Tunda ta taso, duk bayan
wata uku dad yake kaita a duba lafiyarta a qasar
Misra. Amma yau gata a wani qazamin asibiti kwance
cikin fitsari. Ina ma dai mutuwa tazo ta dauke ta. Da
ma da sukayi hadarinnan itama ta mutu da yafi mata
wannan Rayuwar.
Ismail yace, ba zaki yi magana a saki ba mimi? Yaya
Amina tace, haba Ismail, Kalli yadda take mana
qafafu a sagale taya za’a sata tayi fitsari? Yace hakane.
To ynxun sai dai ta dinga yi a kwance? Yaya Amina
tace, dole a samu robar fitsari, amma mu nemi
Shawarar likitan. Ismail yace, to zan sameshi. Amma
ynxun ya kk ganin za’ayi gurin cire mata kayan? Ko
inje in fara dauko mata wasu in dawo?
Yaya Amina tace, to kayi sauri don inason inje gida
sbd abincin dare. Insha Allahu yanxun zan dawo.

Duk akwatunanta ya chaje su tsaf, babu riga da zani,
mafi yawa daga cikin kayanta ‘yan kanti ne, riga da
wando, sai dogayen riguna. Na atamfan ma daga
doguwar riga sai riga da siket. Tsaki yayi, cikin haushi
ya bude qaramar Jakarta, wadda ta dauko zata gudu
da ita. A ciki yaga Jakarta wadda ta zuba kudadenta
data debo sbd guduwar su.
Ya ciro jakar yaje ya daga can qasan katifarsa ya sata
cikin tsohuwar malum-malum. Ya daga ledar tsakar
daki, ta qasan katifar ya saka, sannan ya maida
katifar. Yayi hakane sbd tsoron 6arayi, tunda shi ba
wai yana kwana a gidan bane, kar a zo a bude dakin.
Ya dawo ya bude akwatin da yaga kayanta na ciki.
Aciki ya ciro siket da dan kanfenta, sai best. Baisan
meyasa ya zuba ma rigar mamanta ido ba, qila kyau
tayi masa, amma duk da haka bai dauka ba.
Qamshin turarenta kayan sukeyi, sai ya dauki ‘yan
shirt guda uku, tunda babu zannuwa. Yace zaibi ta
bakin kasuwa ya sai turmin zani ya tsaga su gida uku.
Ya dauki bargon rufarsa da zanin gado, sannan ya
nufi kasuwa, daga can ya wuce asibitin. Yauma ya
hangi innar su Zainabu acan baya gurin wanki.
Yauma haka ya hau sama yana tambayar kansa wai
wa take jinya? Ya samu yaya Amina da taimakon
nurse din dake aiki a wannan lokacin suna cire mata
kaya. Ido hudu sukayi da ita, lokacin daya shiga an
cire mata riga. Cak ya tsaya, domin idanunsa sun
kalli abinda bai ta6a gani a fili ba
Runtse idanunsa da yayi, sunzo daidai da ihun data
yi. Yaya Amina tace, “mun yi miki fami ko? ” Malam
Ismail ku rufemin jikina. Tun farfadowarta, sai ynxun
tayi magana. Ismail ya ajiye kayan hannunsa a gurin.
Idanunsa a Runtse ya juya. Sannan ya bude idanun.
Abin daya gani suna yi masa gizo. Ya fita kan benci,
ya zauna tare da tura hular kansa baya. Sannan yasa
hannunsa ya shafe fuskarsa. Wani yanayi ya samu
kansa a ciki, wanda ba zai iya tantance shi ba. Wata
zuciyar tace, ba fa haramun ka gani ba, duk ka rude
haka, matar kace.
A cikin dakin kuwa, yaya Amina ce ta zo ta dauki
kayan da uwanta ya ajiye taje kan daya gadon ta
zazzage su tana dubawa tare da cewa, shikenan
tunda ya fita sai kiyi haquri. Nurse tace, wane haquri,
ba kunce mijinta bane? Yayan tace ai bata ta re bane
shiyasa. Nurse tace, to kuwa kina da aiki. Mimi dai sai
kukanta takeyi, saboda baqin cikin qirjinta da malam
Ismail ya gani, har suka gama kintsa ta bata daina
kuka ba, sunce zasu sa mata robar fitsari, tace ita dai
bata so, Nurse din ce taba yaya Amina Shawarar su
sai mata pampers na manya. Shi sai dai kawai a cire
a yar, ayi mata tsaki, yaya Amina tayi mata brush,
taqi cin komai, sai ruwan data sha kusan rabin gora.

Baiji fitowar nurse din ba, sai dai muryarta yaji tana
cewa, kana zaune anan ne? Ya kalleta, kun gama?
Tace eh, ya ce na gode. Tace ba komai, sai kaje kayi
lallashi, don shagwa6ar matarnan taka tayi yawa.
Hannu yasa ya shafa fuskarsa tare da yin guntun
murmushi. Ta wuce gurin aamansu shi kam ya kasa
shiga dakin.\Yaya Amina ta fito, cikin jin nauyi ya
kalleta. “tafiya zakiyi? “Tace, eh, kaga yamma tayi, ga
girki. Ummi ba girki ta iyaba. Nasan dai zata share
min gd tsaf, har ma ta hana su Saddam yimin wasa a
cikin daki. In ba ayi sa’a ba sai yayi ta dukanta.
Ismail yace, ai rigimar sako da sako na gurin saddam
da Ummi, kamar masu ganin hanjin juna. Tayi
dariya. Haka suke, amma in daya baiga daya ba, ayi
ta damuna, mama ina take, ko ina yake? Ismail yace,
haka suke fa. Cikin zaulaya yace to kisa abbansu
saddam ya qaro aure mana. Kin ga kin huta, baki da
tunanin yin wani girki. Tace oho, sakamakona kenan
nayi maka jinyar mata? Cikin dariya yace, yaya laifi
ne? Tace, ban sani ba, ni kaga tafiya ta, sai anjima.
Yace yaya ki vari sai gobe mana. Tunda ma da kayan
tea, sai in sha ruwan zafi. Tace shikenan sai goben.
Yace, zaki zo da wuri ne, sbd inason zamuje zariyar
nan. Tace, zanzo dai kamar qarfe goma. Yace, Allah
ya kaimu. Har gurin matattakalar ya rakata sannan
ya dawo. Tsaye yayi a bakin qofa yana tunanin yadda
zai shiga dakin. Daga bisani yayi ta maza, ya tura
qofar tare da yin sallama. Tana zaune akan gadon, an
cire mata qafafun daga sagalewar da akayi musu.
Sannan an dago gadonta, gurin kwanciyr, ta yadda
zata iya kishingida.
Ya kasa kallon fuskarta. Yace, meyasa bakici komai
ba? Ya isa gurin fridge ya bude, ya ciro gwangwanin
maltina. Kisha maltina mana? Tsakin da ta ja shine
yasa shi kallon fuskarta. Harara take ta zabga masa
da jajayen idanunta. Ya sauke idanunsa, yasan kan
abin da ya kalla dazu ne. Sannan ya sake kallon
fuskarta. “kiyi haquri, dazun bansan ana shiryaki
bane. Kuma ni banga komai ba ma.
Bata dai tanka shi ba. Yace, kisha maltina ko kadan
ne kinji? Tace, ni bana sha. Yace to fadamin kk so
kici? Ta soma kuka. Yace, kinga matsalarki. An ce
miki kuka yana maganin matsala ne? Wannan kukan
sai dai ya qara miki ciwon. Tace, ni da zan mutu sai
nafi murna. Rayuwata ba tada amfani. Yace sbd me?
Tace, khalil ya mutu. Shine kawai ya ragemin a
duniya. Ismail yayi murmushin takaici. Ko zaki bishi
ne? Ta Kalli Ismael a fusace, ai da ace inada izinin
tashi, to da tuni na fada ta wannan windon. Ismail
yace, in kuma Allah baiga dama ba, kk karye, kuma
yaqi daukan ranki, kizo kiyi ta jinya ba. Wai shin ma
in tambayeki, da kk ta burin mutuwa, me kk tanada

na ibada ko na alheri, wanda zaki kare kanki, ko
kuma ince wanda zaki amsa tambayoyi a gaban
Allah? Mimi ta sunkuyar da kai. Yace, inaso kisan
wani abu, fushin iyaye ba qaramin bala’i bane.
Dakin mutu a hadarinnan, kin tafi da fushin iyaye a
gudun da kk yi, kinsan illar dake cikin guduwar ‘ya
mace kuwa? Koda yake kece zaki bada labari tunda
gaki a gadon asibiti. Sannan gudunki na farko ma
nasan kin hadu da wani qalubalen, sai dai in ba zaki
fada ba. Ta daga masa hannunta mai lafiyar, ni bance
maka kaimin wa’azi ba. Da zama da kai a matsayin
miji, gara min mutuwa. Yace sbd me? Tace ni ban
son ka, na tsane ka. Ismail baya varin bashin
magana. Don haka yace, ashe duk daya muke. Nima
mimi bana sonki. Sam bakya cikin tsarin macen da
nake so.
A ra’ayina inason mace mai kyau, mai son addini,
kuma maijin maganar mahaifanta. Kalamansa sunyi
wa mimi zafi. Har ta kasa cewa komai, sai kai data
sunkuyar ta soma kuka. yasa hannu ya daga fuskarta.
Karki damu in kin samu sauqi, zamu san yaya za’ayi
,ta goce kanta da qarfi, kar hannunka ya sake ta6a ni.
Yace, nifa damuwa ta kici wani abu, tace bazan ci ba,
ni ka barni, ya koma bakin dayan gadon ya zauna. Ya
soma shan maltina tare da cewa. Na barki.
Har bayan isha’i tana kukan maganganun da Ismail
ya danqara mata, lokacin kuma likita yazo. Bayan
sun gaisa, ya tambayi jikin nata. Ismail yace, jikin da
sauqi, amma taqi taci komai. Likitan ya kalleta,
khadija! Ta dago ta dubeshi. Yace me zakici?
Cikin wata murya mai ban tausayi tace, ba komai.
Ismail ya ta6e baki, barta likita, cikinta ne zai fada
mata. Sai kuma maganar pampers, dazun wata nurse
ta ba yayata Shawarar mu sa mata pampers sbd
fitsari, tunda taqi a sa mata roba. Likitan ya kalleta, ki
bari mana a sa miki robar fitsari? Tace doctor bana
so. Ta sunkuyar da kai tana tuna zuwansu katsina, ita
da hajiya. Ta matsa wai sai an kai ziyara asibiti da gdn
marayu. Daddy baiso zuwa ba yace zai bada abinda
za’a kai, amma hajiya ta cije tace dashi za’aje. Aka tafi
harda ita, a wani asibiti ne taga marasa lfy an daura
musu ledar fitsari.
Ta tambaya menene wannan? Aka ce mata ledar
fitsari ce, saida tayi rashin lfy sanadin ganin marasa
lafiyan. Sannan ace za’a sa mata. Shikenan ka sai
mata pampers din, amma amma dai zaku sha kudi,
in kuma zaka dinga sata a toilet din da kanka, da sai
yafi muku. Da sauri mimi ta daga kai, Allah ya
tsareni, ko hannuna karka sake ta6a min. Ba mijinki
bane? Ko pampers din waye zaisa miki in ba shi ba?
Duk wahalar da yake miki, yana kashe kudi akanki
shine zaki dinga yi masa haka?

Mimi tasoma kuka,”Ni bana son yasake tabani,na
tsaneshi”. Kuma ai kudina ya dauka yakemin
magani.Ai bashida kudin dazai kashemin.
“Likita kar ka damu da ita,nima inayi mata ne don
Allah,da Lima tausayin halin da take ciki,amma
rashin mutunci halintane ko tayi min bazae dameni
back.Ita ikirarinta bata sona,nima kuma bnga abinso
a gurinta ba”.
Likitan yayi murmushi ,don ya fahimci Isma’il yana
maganar ne don son cusa haushi ga marar lafiyar.
Yace “khadija wae bakya son shi?” Tace “eh”. Saboda
me? Tanuna isma’il da yatsanta,”saboda abubuwa da
yawa. Ina zargin sa da shiga cikin rayuwata. Kuma ya
taemaka gurin shigata wannan halin.
Isma’il yazaro ido yana kallonta,a zuciarsa
yace”sharri zatayi min?” Likitan yaja kujera, yazauna
tare da tattara hankalinsa gareta. Sanar dani
hujjoinki,kila inada taemakon dazanyi miki. Tasoma
kula “Ranar wata asabar nasoma jin lavarinsa a
wurin kannaina. Sunaji dashi a matsayin malaminsu.
Ranar farko Dana dora idanuana a Kansa,ranar ya
raena min wayau,tare dafada min maganganu na
wulaqanci.
Abinda baa taba yi min ba a rayuwa ta. Sannan shi ne
mutum na farko da banyi nasarar rama abinda
yaemin ba, duk da cewa yayi min abin da baa taba
yimin ba. Sannan shine mutum na farko dana taba
kae qaran shi wurin daddyna bae amshi korafina ba.
Tundaga ranar asabar din daya dira gidanmu
Abuja,van qara samun kwanciar hankali ba.A qarshe
shine daddy ya daura min aure dashi a ranar asabar
kuma. Kalli wannan abin doctor,ta yaya zan
yafemasa wannan zunubin?
Salis yayi qoqarin danne dariyar da ke qoqarin kufce
masa,sannan cikin zolaya yacee “gaskia yayi babban
zunubi”. Ismail kam dariyarsa yayi harda
qwalla.sannan yace, “Mimi kenan ,kiyi haquri,don
nifa haka nake, duk inda nashiga sae nayi nasara
akan duk mae ja dani, saboda na dogara ga
Allah.kinsan duk Wanda ya mika lamuransa ga
Allah,to fa Allah ya Isar masa.kinci sa’a ma wannan
guntun labarin naki agaban likita kika fada,ba agaban
alqali ba, da sae ya daureki.Domin babu abinda ya
hada labarin nan da halin dakike ciki.ni na hanaki bin
umurnin mahaefinki? Ni nace miki ki gudu? To, in
baki sani ba kisani,bijirewa mahaifinki da kuma
gudun dakikayi kika bar iyayenki sune silar shigarki
wannan Hamlin. Likita have, wai-wai-wai kin gudu
ne dama? Ta sunkuyar da kai, hawaye ne kawai ke
zuba. Lallai kinyi babban laifi.
Ko dani ba alqali bane. Kamar yadda Ismael yace,
amma na yarda gudunki ne ya jawo miki wannan

halin da kk tsinci kanki a ciki. Ta soma tuna yadda
suka auna arziki a gudun farko. Ashe gargadi ne suka
tsallake. Na biyu kuwa shine masoyinta ya mutu, ita
kuma gashi ta kakkarye, Burinta in ta warke ta sake
guduwa inda iyayenta da danginta ba zasu ta6a jin
labarinta ba. To kenan mezai faru in ta sake guduwa?
Duk zatonta a zuciya takai qarshen maganarta. Ashe
a fili ne. Sai kurum taji yace, in kk sake guduwa na
uku, qila qafafunki da hannayenki su gutsire, ki koma
gundulmi, kinga kenan sai bara. “Bara? ” ta zaro ido.
Likita cikin son firgita ta yace, “bara kuwa” sabon
kuka ta dora, tare da cewa, ” Allah ya dauki raina in
huta. ”
Ismail yace kinata burin mutuwa, an fada miki sauqi
zaki samu in kin mutu a haka? Na tambayeki guzurin
da kkyi na zuwa lahira, amma baki ban amsa ba. Kk
yarda kk mutu a haka, ai kwanciyr kabari ma kawai
ya isheki. Ta Runtse ido cikin tsoro, tana tunanin
kalmar likita. Wai tayi bara, Nan ta tuna wani English
novel data karanta yadda Yarinyar cikin labarin ‘yar
sarauta, sakamakon son zuciya, ta qare da
gutsurarrun qafafu kuma a gidan yari. A firgice ta
dago ta Kalli likitan, sai taga ya yagi kwalin magani ya
ciro biro a gaban aljihunsa ya soma rubutu. Ya
gama, sannan ya miqa ma Ismael tare da cewa, duba
ka gani, kasan wannan magani? Ismail ya kar6a tare
da cewa to, Ya soma karantawa kamar haka. “Ismail
inason ka sauke duk abinda ke ranka game da
Yarinyar nan. Ynxun na san bata san tunanin da
zatayi ba. Amma ni da kai in mun hadu zamu saita
mata tunanin ta. Ismail ya dago kai, ya kalli likitan
sannan ya kada kai, na san shi.
Likita yace, to kasai mata shi a hada cikin
magungunan. Ba damuwa, inji Ismail. Likitan ya sake
kusantar gadon mimin, “yanxun, menene tunanin ki
a gaba, ko ince burinki? Inason in taimakeki ne
matuqa. Mimi cikin kuka tace, banda wani sauran
tunani, tunda malam ya dage wai mutuwa ma ba
hutu bace a gareni. Da farko na daura aniyar dana
warke zan gudu, in nesanta kaina da mahaifana,
yadda baza su sake samun labari na ba. Inason su
manta sun haifi ‘ya irina. Kai in mutu ma yadda zan
nesanta dasu gaba daya. Amma ynxun kunce haka.
Likita kai ka taimakeni ka nesanta ni dasu mana.
Doctor salis yace, “yi shiru daina kuka, in miki abinda
kk so, ta tsagaita saidai ajiyar zuciya da takeyi. Yace,
na tabbata in kin kwantar da hankalinki, Ismail
dinnan zai nesanta ki dasu, kamar yadda kk so
domin shi mijink… “Ta katse likitan da cewa, bana
buqatar yaci gaba da zama mijina. Doctor salis yace,
dukda haka zai iya, zaka iya ko? Ya kalli Ismail. Yace
zan iya matsawar zatayi min alqawari guda daya,

sannan zata kwantar da hankalinta tare da bani
hadin kai, to zan nesanta ta da mahaifanta, sannan
ba aanci gaba da zama mijin nata ba, in ta buqaci
hakan. Tace, menene tabbacin, zaka bar gari dani ko
qasar? Ya ce, kina cikin garin katsina amma ba dole
ku hadu ba, ko susan inda kk. Ta danyi shiru, sannan
tace, fadi alqawarin inji.
Yace, zaki dauki alqawarin cewa, ba zaki gudu ba,
duk wuya, duk runtsi. In kinyi haka, ni kuwa zan
6oyeki, tare da yi miki duk abinda kk so, iyakar iyawa
ta. Haka kuma in bakya buqatar inci gaba da zama
mijinki, sai in koma wanki. Likita yace, bakida wani
za6i sama da wannan. Kuma asirinki rufe. Tace, in
kuma hajiya ta kirashi fa ko Alhaji don jin inda nake?
Yace daga yau zan kwafe duk numbers din dake
wayata banda nasu, sai in baki sim din ki karya, ki
zubar. Tace, to in akazo gidanku fa? Ai kafin mubar
asibiti zan nemi haya a wata unguwa daban, kuma ko
‘yan gidanmu ba zasu sani ba. Dama basu san
gidanmu ba. Dama Hamisu direba ne kawai ya sani.
Tayi shiru, domin qaramar kwanyarta ta yarda da
abinda akace. Ta kalli Ismail, kenan daga ynxun kai
ba mijina bane? Ismail yace, a’a wannan shine zai
zama a qarshe, ko yaya kace likita? Likitan yace,
wannan hakane.
Ta girgiza kai, tare da dan yatsina fuska, sbd dan
radadin da ciwonta keyi mata. Tace ban fahimta ba.
Likita yace, kinsan za’a bi abin daki-daki ne. Farko dai
zamu fara ta lafiyarki. Zanso ki bada hadin kai gurin
ganin anyi jinyar ki cikin sauqi. Ki dinga cin abincinki,
kina shan magani har a sallameki. Kinga wannan ne
farko. Sai mu koma kan abu na biyu, bayan an.
Sallameki ki zauna dashi tamkar ‘yar uwa, kiyi haquri
da duk abinda ya samo ya baki na abinci, ko na
sutura, ki kuma nutsu, babu batun guduwa, don
kamar yadda yace, zai zamar miki wa. Ko ince kun
riga da kun zama daya ma, domin jininsa ne aka
zuba miki yake hade da naki.
Ta dago ido ta Kalli Ismael, sannan ta Kalli hannunta
mai lafiyar. Ta runtse tafin hannunta tana kallon
tsintsiyar hannunta, kamar mai kallon jinin yana
haduwa. Likitan shiru yayi, daya ga tayi hakan, don
yasan zantukan nasa sun shigeta sosai. Ta katsewa
likitan tunani da cewa, Doctor in nayi haka fa? Ina
nufin sai menene a gaba? Yace, sai batun raba auren
ku dashi. Ismail yace, kuma in kin samu wanda kk so,
ba zai hana muyi miki aure dashi ba.
Da sauri ta Kalli Ismael. “Ni bazan qara soyayya ba.
Nayi ta na gama, don na haqa rami na binne ta. Zan
rayu ne ni kadai. Ismail yace, duk wannan babu
matsala, matsawar zaki cika alqawarinki na qin
guduwa ko ina. Ni kuma zanyi miki duk abin da kk

so. Ta soma qoqarin zamewa don ta kwanta. Sai dai
amma ta kasa.
Likitan yace, yayanki ya taimaka miki? Tace a’a likita,
bana so ya dinga kai hannunsa jikina. Likita yace,
wannan babu matsala. Ya miqe ya nufi waje, nurse
ya kira yace tazo ta taimaka mata. Sannan ya kira
Ismail, zo mana, mu danyi wata magana. Sun jera
tamkar abokai. Likitan yace, Ismail banaso ka damu
da duk abinda Yarinyar nan zatayi. Ka ceci Rayuwar
ta ta hanyar kyautata mata don kar tace zata sake
guduwa. Kabi da ita ta hanyar da muka sata akai.
Sannan kayi mata qoqarin nesanta ta da mahaifanta
na wani lokaci, sbd a samu ta nutsu, ta kuma saba
daku. Ismail yace, Allah yasa ta iya. Domin in kaji
labarin gatan da take ciki zaka sha mamaki. Allah dai
ya shige mana gaba. Doctor salis yace, Ameen.
Sannan inason duk lokacin da kk buqatar taimakona
a game da wannan matsalar taku, ka kira number ta,
sannan ya ciro katinsa ya miqa ma Ismael, “akwai
numbers dina a jiki, ko da bana nan a asibiti. Ismail
yace, nagode sosai Doctor.
Na’ima kuwa, yadda taga rana, haka taga dare, sbd
mijinta yana samanshi tare da wata mace, wadda ba
halalinsa ba. Tayi kuka ta gaji, idanunta sun
kukkumbura sunyi jajur. Maimakon Na’ima ta tashi
cikin darennan ta miqa kukanta ga Allah, madadin
kukan da takeyi. Saidai kash ba zata iya yi ba. Tasan
ma anayin hakan. Allah ka ganar damu, Ameen.
Bata qara tsurewa ba saida gari ya waye kusan goma
da wani abu tayi wanka ta fito. A tunaninta sun bar
Gidan. Ta nufi kicin ne don tasa masu yi mata aiki su
hada mata abin kari. Cak ta tsaya sakamakon ganin
karuwar tare da angon nata suna hada abin da zasu
karya. Batasan sadda zuciya ta kwashe ta ba, ta
qarasa kicin din cikin fushi ta daqumi wuyan ‘yar
best din da Jennifer ta saka, tana kuka tana cewa, “zo
ki fita a gidana, shegiyar karuwa. Saukar marin da
taji ne ya sata sakin Jennifer cikin sauri, ta tallabe
kumatunta.
Ta kalli Abbas, wanda yake cewa, kinsan dawa kk son
yin fada? In baki sani ba, to tsaya in sanar dake.
Sunanta Jennifer kuma itace ta musamman dina. Ko
da ace mimin da nakeso ce na aura, dole ta barni da
ta musamman dina, bare ke wadda baki cikin
ra’ayina! Karki sake ki sake kai wannan baqin hannun
naki jikinta. Sannan ya juya gurin Jennifer, wadda ta
koma gefe, ta 6ata rai matuqa, ya janyo ta jikinsa.
Kar ki damu da wannan ‘yar wahalar kinji ko? Banida
lokacinta.
Na’ima tace, cikin kukan takaici, Akan wannan zaka
mareni? Yace kadan na miki na gargadi. In kin sake
kuma, zaki bada bayani. Sannan ki fita anan, in mun

gama, mun fita kina iya shigowa kiyi abinda zakiyi,
haka Na’ima ta fita, ta koma daki, cikin nadamar
auren Abbas. Bakin gado ta zauna, tare da daukar
waya ta soma kiran layin momi, tare da fadin cewa,
ko momy bata zo ta tafi dani ba, yau na gama
Rayuwar gidannan.
Momy tana dagawa, kafin Na’ima tayi magana, ta
katse ta da cewa “ga daddyn ku kiyi masa sannu da
jiki, kafin mu gaisa sbd Jikinsa yayi zafi yau. Na’ima ta
fahimci tayi hakane sbd ta sanar da ita tana tare da
daddy. Sbd batason daddy yaji wannan matsalar.
Muryar daddyn ce ta katseta da cewa, “Na’imatu.
Tace, Na’am daddy ina kwana? Yace lafiya lau
Na’imatu, yaya kuke da maigidan naki? Tace, lfy
daddy yaya jikinka? To da sauqi kenan za’ace tunda
ina gd.
Amma sugar din yaqi sauka sam. Tace to Allah ya
sauwaqe daddy, sai nazo duba ka. Yace a’a Na’imatu
karki soma fitowa da wuri haka, in dai ba mijinki
bane yace kuzo tare. Tace to daddy, Allah ya qara
maka lfy. Yace Ameen. ga Momyn taku. Ta amshi
wayar, sannan ta nufi fita. Alhajin yace, kizo ki bani
maganin. Tace to Alhaji ina zuwa. Alhaji bashir ya
kwanta shiru, yana tunanin yadda sukayi da likitansa
daya fita ynxun. Bayan likitan ya auna shi ne yace,
“Alhaji meyasa sugar dinka bata sauka? Alhaji yace
kuma ina qoqari gurin shan magani da kuma kiyaye
duk abinda aka hanani. Doctor yace, to kuwa kana
tare da wata damuwa. Saboda shima sugar haka
yake, kamar hawan jini 6acin rai yana tayar dashi.
Alhaji yace, ni bana tare da 6acin ran komai likita.
Likitan yace, to ynxu zanyi maka allurar da zata
saukar da sugar din inqha Allah. Sannan kasha
wannan maganin. Ya dago daya daga cikin
magungunan ya nuna masa. Sannan yace, Allah ya
qara sauqi. Kuma yana da kyau kadan qara samun
varci.
Momy Nafisa ce ta katse masa tunani da cewa,
“Alhaji ga ruwan kasha maganin. Ta dauki kwalin
maganin ta bude masa tare da cewa, likita fa yace, ka
rage wannan tunanin. Wai tunanin me kkyi ne Alhaji?
Saida ya afa sannan yace, ko na fada bakida
maganinsa. Amma ni burina ynxun in dan samu
sauqi inje katsina. Inason ganin sauda sosai, don
tana buqatar lallashina. Na tabbata ban kyauta mata
ba.
Nafisa ta ta6e baki, ka 6ata mata rai, ko mimi ta 6ata
mata rai? Shawarata dai a gareka Alhaji. Ka kauda
kanka ga komai din lafiyar jikinka ta samu. A
tunanina tunda Na’ima ta share maka Hawaye, bai
dace ka tsaya tuna wata damuwa ba, wadda zata
hana ciwonka sauka, “hannu ya daga mata, alamun

tai shiru. Sannan yayi mata alamun cewa ta fita daga
dakinsa kurum.
Rigingine yayi, tare da dora qafafunsa wadanda
sukeyi masa zafi tamkar ana hura musu wuta akan
filon, ya kalli qafafun nasa wadanda ciwon sugar din
yasa suke masa radadi, ya mai da kansa gefe, yana
tuna sai zuwa yaushe kenan zai rabu da wannan
ciwon? Domin kuwa damuwa agurinsa ta zama dole.
Bai ta6a tunanin cewa, don ya yi wa mimi abin da
yayi mata zai dameshi ba. Duk da qoqarin da yakeyi
na tanqwasa kansa don fada da zuciyar sa. Mimi ce
dai, har ynxun sonta a zuciyar sa bai canza ba.
Harma wani sashen na zuciyar sa yana fada masa
cewa, bai yi wa ‘yar tashi adalci ba, domin yasan har
ynxun mahaifiyar ta kawai yake yiwa tsantsar SO. Sai
yaji tamkar ya daga waya ya kirata, ko kuma ya tashi
yaje gurinta. Amma in ya tuna qudirinsa, sai ya fasa,
ya lallashi zuciyar sa da cewa, lokaci baiyi ba da zan
nemeta. A fili yace, ynxun sauda ce babbar damuwa
ta.
Yakama in je inyi mata bayani, yadda zata fahimci
dalilina. Ya karkata kansa, ya kalli wayoyinsa dake
saman durowar

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

9 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment